Free chapter · Read without an account

7

by Asmy b Aliyu · LAILAH KHALIFA






 haka kawae Wani bangare na zuciyarsa yaji shawarar Ayan itace mafita ta haka kawae ne zai samu Auren Laylah maska cikin sauqi.

Hakan shine mafita kawae Maska da'ga baya za'ka iya Warware komae za'ka iya mantar daita komae ,

Ayan ya fa'da idonsa na akan Mujaheed saurin bu'de idonsa yyi yana fuskantar Ayan gaba day'a yaji jikinsa ya mutu likis ,

batareda mujaheed yyi magana ba ,ya miqe tsaye ya dauki car key dinsa da'ke kan center table din dake tsakiyyar da'kin Ayan yyi hnyar fita ,sae da yakai ko'fa ya Juyo yace zamuyi wya,fita zamuyi da Laylah yanzu.

Nodding kai Ayan yyi batareda mujaheed ya ka'ra fa'din komae ba yabar falon.da misalin karfe shidda suna kan hanyar komawa gida itada mujaheed bayan sun dawo daga shopping din da mujaheed yyi ma'ta na ban mamaki.wayar tace dake cikin handbag dinta ,ta fara ka'ra zuge zip tayi lambar honey boo dinta ta fa'ra ya'wo akan screen din wayar na'ta satar ka'llon mujaheed tayi Wanda hnkalin sa na kan tu'ki samun kanta tayi da Rashin da'ga wayar badar danbatta .tanaji tana gani wayar ya tsinke ka'ro na biyu kiran ya ka'ra shigowa hnkalinsa Ya maida akan ta Dan bu'de ido yyi yana ka'llonta ana kiran ki bazaki da'ga ba ,

Idan kiran yana da muhimmanci fa?

Zatayi magana kiran ya ka'ra shigowa narke mata idanuwansa yyi masu cike da azababbiyyar soyayyar ta ,

Jiki sanyayye ta da'ga wayar lokaci day'a take fa'din ."hello sallamu Alaikum sanyayyar muryarsa CE ta da'ki dodon kunnenta,

Natsuwa tayi sosae tana sauraren ko'rafin barister badar danbatta ,Wanda yake yimata cikin shagawaba tamkar ya'ro dan shekaru #3 wasu lokuttan badar yana yimata shagawabar tanajin Kunya ,

Lallausan murmushi take sa'ki Wanda badar najin hakan har cikin ko'kon zuciyarsa muryarsa CE ta ka'ra dukan dodon ku'nnenta ,

Wato baza kiyi magana ba.?

Sassauta murya yyi cikin sigar lallashi ya'ke fa'din kiyi hkuri kibani dama na ganki a yau wlhi zan iya mutuwa!

Ki tausayawa bawan Allah!"ya ka'rasa maganar cikin wata irin murya wadda bazata fassaru ba.lokaci day'a ta langabar da kanta tamkar tana ganinsa ya tsunta biyar ta shiga warewa haka tana binsu day'a bayan day'a tana lankwasa su .

Ka'fin ta amsawa badar taji wata irin ka'ra agigice ta sauqe wayar tana baza ido taji ta inda ka'rar ke fitowa ,

Har ga Allah ta manta suna tare da Yaya mujaheed .

Idan tana tare da badar ko tana wya dashi mantawa takeyi da ko'wa sai yanzu idonta su'ka sauka kan wani ya'ro da mujaheed ya bangaje da mo'ta ,,shikuma kishine da Rudewa ya'sa yyi cikin ya'ron batareda ya sani ba.lokaci day'a mutane suka zagaye motar tasu cikin sanyi Jiki Jaheed maska ya fito da'ga motar yyin da Laylah ke bayansa gaba day'a hankalinta atashe ya'ke addu'a takeyi Allah yasa yaron ba mutuwa yyi ba ,hawaye suka fa'ra sauqa akan kyakkyawar fuskarta .dama ku'ma Laylah macce CE mai tausayin gaske Abu ka'lilin ne zay girgizata ko ya ka'ssara tunanin ta.

Hannun ya'ron mujaheed ya ka'ma Wanda bawani ciwo babba bane bu'gewa yyi a babban ya'tsan sa ,ya goge sosae wurin sae Jini ya'keyi ya'ron bazai wuce shekara go'ma ba A dunia .

Nan mutane ko'wa ya riqa to'fa albarkacin bakinsa ,

Yyin da wasu ke durawa Mujaheed Ashariyyah ,

Suna ganin tu'kin ganganci ne ku'rum irin na'su na ya'yan masu hannu da shuni farin yadin da'ke Jikinsa baisa shi Jin kankamin ya'ron ba Wanda ka'llo day'a zakayi masa kasan yana cikin wahalar Rayuwa ,

Bai bi takan mutane ba ya nufi motarsa dashi .Laylah CE ta amshi car key Tajasu zuwa wani privet clinic .

Cikin minti talatin aka yiwa ya'ron komae ,har lokacin mujaheed bai cewa Laylah komae ba.

Laylah tana lura da Mujaheed da yabi yyi wani sanyi .

Tambayoyi Laylah ta fara yiwa ya'ron a hnkali ya'ke bata amsa yana yimata kwatancen ungurwarsu ,

Sae da suka kaisa har gidan su ,Wanda ka'llo day'a zakayiwa gidan ka'san suna cikin wahalar Rayuwa Laylah tasha mamaki sosae ,

Bata ta'ba tunanin Akwae way'ndda talauchi yyiwa yawa har haka ba.

Godia ta ka'rayiwa Sarkin sarakai.sae da sukayiwa iyayen ya'ron Alkhairin gaske sa'annan sukabar unguwar ,

Gaf da magrib suka shigo cikin gidan .dai dai lokacin da Aliyu ya fito da'ga compound din gidan waya sa'kale a kunnen sa.

dukan su bbu mai magana har suka ka'raso gurin Aliyu datse Kiran yyi yana ka'llonsu day'a bayan daya'a .

Kafin ya sauke kyawawan idanunsa cikin na Laylah maska ,

Ware idonsa yyi yana ka'llonta da'ga ina haka Amarya?

Yyi maganar cikin sigar tsokana turo ba'ki tayi tana qa'llonsa batayi magana ba ta Ra'ba ta gefensa zata wuce yasa hannunsa ya dawo daita gaban sa ,

Cike da shagawaba take fa'din ."yaya mana.

Aysha mana."

Yyi maganar cikin wata siga wanda duk lokacin da Aliyu maska ya kirata da Aysha ,

Takejin wani iri aranta .

Lokacin sallah yyi za'ka makara za'ka rasa Jam'i ta fa'da tana zare hannunta cikin na'sa tana Jifansa da murmushin ta mai tsumasa ,

Shafa sajensa yyi ya da'ga mata gira yana fa'din wayo ko??

Juyawa tayi gun mujaheed sae taga wayam!

da alamr ya dde da wucewar sa ,

Tana Juyo kan Aliyu taji yana fa'din wakike nema?

Abokin tafiar ki?

da'ga gira tayi Dan kwa'be baki yyi ni nafita sai na dawo ya nufi pkn lot Dan daukar mota itakuma ta wuce cikin gida.

dukan su ya'mmatan gidan zaune suke a babban falo ,

Suna shirya yarda partyn Laylah maska zai kasance a gobe Laylah na zaune day'a da'ga cikin soofa's din da'ke zagaye da falon ,yyin da mujaheed maska ke zaune a gefenta yana sipping Juice acikin glass cup ,

Meemah feenah Amra na zaune akan lallausar Rug din dake malale a tsakiyar falon ,

Meemah keda Yah Jaheed zakuyi Rawa ,

Feenah keda Yah shaddad ke ku'ma Auta Amra sae kiyi ke'da Hafees Laylah ta ka'rasa maganar tana ka'llonsu ,

Ni ku'ma zanyi da Yayah Aliyu Laylah ta fa'da tana ka'llonsu Ihu sukayi ,

Kafin meemah tace ni bazan yi Rawa da Yah Jaheed ba ,

Da yayah Khaleepha zanyi.

Ko'wa baki ya saki wangalau yana ka'llonta lokaci day'a suka saki daria cikin dari'a

Mujaheed maska ke fa'din "yhu are sick in the head!

" cikin ba'ta rae gamida tu'ro baki take fa'din

Yaya mana,

Harara mujaheed ya watsa mata ka'fin ya cigaba da fa'din sae kace bakisan waye Leefah maska ba!

Yayah Khaleepha ne zaiyi Rawa da'ke ku'ma partyn ma na Laylah maska?

Oh yah Mujaheed mana!

In banda kai da Abunka ko ka manta maryam bamalli ya'r gaban go'shin Khaleepha maska CE!

Shin ko ka'manta yafi kusanci daita fiye da ko'wa acikin zuri'ar maska ,

Laylah ta fa'da tana ka'llon mujaheed ,kabarta kawae kinga meemah ya kamata ki San abunyi akan wannan arrogant yayan na'ki kije Ku fa'ra practical tun yanzu ,Dan kar yaba damu gaban In-laws dina ko ya kukace guy's?

Laylah maska ta fa'da tana ka'llon su feenah shewaaah sukayi gamida fa'din yessss hakane pah!

Murmushi ku'rum meemah tayi ganin suna so su maidata mahaukaciyya akan soyayyar Khaleepha maska.

Yayah mujaheed wannan ka'ron bazamu yarda ba do'le ka nuna mana girl friend dinka ,

Laylah maska ta ka'rasa zancen gamida narke masa kyawawan idanunta ,

do'gon hancinta Yaja gamida fa'din banda budurwa Laylah maska ware masa ido tayi haka lokaci day'a ta dauki pillown dake day'a da'ga cikin soofa tana buga masa tana fa'din ban yarda ba Yayah duka ina girl friends naka suke?"wannan ka'ron zamuyi fa'da zamuyi rigima abun kunya ne ace baka da budurwa ka Girma ka girma da yawa Yayah!

Laylah maska ta ka'rasa maganar tamkar zata sa'ka kuka ganin yarda ta kwa'be fuska yasa mujaheed maska yin daria ,su Feenah na tayasa Afusace Laylah maska ta miqe tsaye zatabar ma'su falon Jaheed maska yyi saurin fisgota sae akan Lap's dinsa ,

dukan su wani irin shock sukaji lo'kaci day'a .

bu'do ko'far falon yyi cikin sanyayyen kamshin turaren sa na oud ,

English wears ne Ajikinsa Wanda sukayi balain karbarsa ,

idonsa ne suka sauqa akan Laylah da mujaheed cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa .

Numfashin sa yaji yana fita a wahale haka Yaji zuciyarsa na Neman tsinkewa ,

Jin kamshin turaren da duk dunia bbu mai amfani dashi sae Khaleepha maska ,dara daran idanunta ta da'ga ta ka'lli ko'far shigo'wa hnkalinsa gaba day'a yana wurinsu mujaheed maska Wanda har lokacin mujaheed ya'ki sakin Laylah."

Kishi taji ya kamata haka Taji wani irin kuka yazo ma'ta bbu shiri ta miqe tsaye tana Rufe bakinta da gudu ta nupi hanyar da'kin barcin su Feenah ,bbu Wanda ya kula da yanayinta .

Sae lokacin Khaleepha maska ya maida hnkalinsa kanta.

binta yyi da ka'llo har ta bacewa ganinsa ,ka'ro na farko A rayuwarsa da Yaji baya kyautawa meemah ,

Haka kawae yakejin nadamar wulakanchin da yyi mata .

Ko'da baya sonta bata wannan hnyar ya ka'mata ya bu'llo mata ba,

Haka kawae zuciyarsa ta ba'sa umurnin da yaje ya lallasheta kai tsaye da'kin da yaga ta nufa shiyah nu'fa Laylah da feenah da ku'ma Amra suka ka'lli Juna gamida bu'de idanunsa ,

Ka'fin su sa'ki ihu lokaci day'a saurin ture mujaheed tayi Wanda baisan me sukeyiwa Ihu ba.

Rarrafowa Laylah tayi agabansu Feenah maska Wanda har lokacin suna zaune Akan rug .game Kansu sukayi wuri day'a suna kus'kus !"lokaci day'a suka kya'lkyale da daria suna ha'de hannayen su wuri day'a tamkar wasu ya'n wasa kwaikwayo.

Ka'llonsu kwae mujaheed ya'keyi musamman Laylah maska ,

Wanda komae na'ta abun burgewa ne a wajen mujaheed .

suna ha'da ido dashi tayi masa alama da hannu alamar minene?"

Wyar ta dake hannun mujaheed ta fa'ra ka'ra da'ga ido tayi tana ka'llon sa miqa mata wayar yyi yana fa'din bestyn ki nakiran  ki .jin ance besty tasan Meela CE ,

Hannu tasa zata karbi wayar ya bu'ge hannun ware ido tayi tana ka'llon sa ,

da'ga wayar yyi cikin kashe murya ya'ke kwaikwayon muryar Laylah maska ,

Sae ka rantse da Allah macce CE ,

Mesu feenah zasuyi idan ba daria ba .

Shewa su feenah keyi suna fa'din Yayah da macce ne kai da kayi kyau da gaske Yayah da macce ne kae da Ka gigita mazaaah#

Shewarsu ya'sa ya miqawa Laylah wyar bbu shiri Dan koka'rin suke su fa'sa masa dodon ku'nne!

jini ke zuba sosae a damtsen hannunta daura hnnun tayi akan mirror dressing hawaye na zuba a idonta haka Jini na fita sosae a damtsen hannun damanta ,

Yana tu'ro ko'far da'kin ya hangeta ajikin mirror dressing tana fuskantar ,

da sassarfa ya nufeta yana da'fa ka'fadatarta ya lura da hannunta da sauri ya riqe hannun na'ta idonsa ya ka'da yyi Ja ,

Tana kokarin fisge hannunta .

Ya dakama ta wata uwar uban tsawa!"

Cikin fa'da yake fa'din stop it meemah !

Bata damu da tsawarsa ba ,sabida tariga tasaba Jin fiye da hakan cikin fashewa da kuka matsanachi ta'ke ko'karin fisge kanta da'ga rikon da Khaleepha maska yyi ma'ta ,

Zan mareki meemah baki da hankali ne wai?"

Yyi maganar cikin fushi da za'fin rae ,

Bbu musu ta sakar masa hannun waige-waige ya shigayi ya'ga inda zai hango Abun daure hannun na'ta ,

Lalubar Aljihun wandon Jena's dinsa ya shigayi ,anan ya Ciro farin hankacif ya daure hannun na'ta ,Jan hannunta ya shigayi har suka fice daga da'kin .

Har suka sauko kan down stair's yana riqe da hannun na'ta har lokacin su Laylah na falon lokacin Rawa sukeyi itada Feenah da'kuma Amra yyin da mujaheed ,ke tsakiyar su yana tayasu bai ko ka'lli inda suke ba.

Laylah CE tayi saurin ka'rasowa hnkalinta a tashe ta'ke ka'llon hannun meemah,cikin Rawar murya ta'ke fa'din meemah ya haka?"

Wani mugun ka'llo Khaleepha maska ya'ke Jifanta dashi bata damuba ko'karin riqo hannun na meemah takeyi cikin tsawa ya'ke fa'din karki fa'ra !"

dara daran idonta ta da'ga tana ka'llon sa wani irin yanayi ne tattare da fuskarsa ,

dan Ja dabaya tayi hannun meemah yaja zuwa part dinsa.

Tsoki ta bu'ga tana bin bayansa da ka'llo Aranta take fa'din majnoon guy !"

da kansa yyi dressing din hannun na'ta har lokacin bata daina zubar hawaye ba,

Sae da ya gama ya ko'ma kan day'an kujerar da ta'ke zaune yana fuskantar ta fuska bbu walwala ya'ke fa'din ."kashe kanki zakiyi?

Kan wane dalili ?"hakan shi zaisa kaddarar ki ta chanja akan abunda kk so?

Haka shi zaysa ki samu Abun da kikeso Maryam?"

Khaleepha maska ya ka'rasa zanchen muryarsa na karyewa ,da jajjayen idanunta ta da'ga tana ka'llonsa .

Ko gizau babu ya tsareta da manyyan idanunsa masu kassara ta.

Bbu musu ta saukar da idanunta ka'sa !"batareda ta Amsa saba.

Cikin sanyin murya ya'ke fa'din Maryam ki fidda damuwar dake Ranki ,

Kan wannan ya'r kan kanuwar matsalar bana son zumunchin mu ya Rushe !"bana son wannan tashin hankalin meemah ban San meye shiba iya tsawon Rayuwata sae a wannan lo'kachin da Maryam bamalli ta zo min da wani irin babban Al'amari mai girma mai wuyar misiltawa .

Yi maki ka'ryar baya da amfani ban maki Alkawarin zan so'ki ba.bana maki soyayyar Aure!

Ina yimaki ka'llon Amra maska ne wadda muka fito ciki day'a daita.

Ina rokon ki kada ki rusa mana wannan zumunchin ka'da mubari abunda baikasa muhimmanchi ba ya Rusata."

Nasarar ki na nufin nasarata kwanciyar hankalin ki shine tushen samun nasarar ,nasara bata zuwa da sauqi ,nasara sai ansha gwagwarmaya ake samunta .soyayyar da ba'a samu tangarda ko bambanche-bambanchen Ra'ayi ba,bata kaiwa gachi.

Meemah kisa aranki ba zamuyi Aure bane kawae !

Cikin sa'kan biyu sae ga meemah durkushe agaban Khaleepha maska ,hannayenta du'ka biyu ta sa'ka ta riqe ka'fafunsa idanunta ke fitar da wasu irin hawaye masu zafin ga'ske ke sauka akan fuskarta da gudu tamkar an ku'nna famfo tana Jin yarda kirjinta keyi mata za'fi ,

Ba'kinta na Rawa take fa'din .

Na hkura !na hkura dakai Khaleepha maska !"tunda naji a bakinka ba wanine ya fa'damin haka ba, amma ina tunanin soyayyarka za'ta iya zama Ajalina wlhi ."

Zan yi addu'a zanyi Addu'a Yayah Khaleepha kafin Allah ya dauki raina na'ga aurena zanyi addu'a nima Allahu ya bani gwarzon miji tamqar kai mai hali da aqida mai kamannin Abubakar maska.kudin shafukkan Rayuwata will be incomplete with out d scenery of Yayah Khaleepha..... "A hnkali meemah ta miqe tsaye ta shiga Ja da baya hawaye na bulbula akan fuskarta Khaleepha maska bai iya cemata komae ba ,sae hannayensa da ya riqa bu'gawa ajikin bango ,kifa kai yyi ajikin bango ya Rushe da wani irin kuka kukan da bai ta'bayi ba A rayuwarsa ,kukan da baita ba yiba akan macce!........azahirin gaskiyya ba meemah bamalli bace ta sa'shi kuka ,

Akwae wata damuwa da'ke ka'san ransa Wanda duk lokachin da ya tu'no da hakan haukane kawae baya yi!

da sassarfa ya nufi cikin wani study room dinsa ,

Wanda duk dunia bbu mai shiga da'kin sai shi.

da'kine na musamman Wanda ya killache dan sirrin sa ,

Yana tu'ro ko'far study Room din katon pic dinta ne ya fara yimasa murmushi sanye take da Riga da wando na Pakistan pink and lemon green ,bbu wata kwaliyya a fuskarta tana shan ice cream aka dauki pic din Wanda da alamr bata ma San an dauketa ba .

Rarumar pic din yyi yayi jifa dashi akan marbles din da'ke malale a tsakiyar da'kin ido jawur yabi pic din da ka'llo ,still ka'llon sa takeyi tana murmushi ,

Sauran pics din na'ta ya shiga bi da ka'llo wani wuri tana murmushi wani wuri tana daria wani wurin kuma ta ba'ta rae ,

Zube gwiwon sa yyi duka ka'sa haka ya da'fe kansa da hannayensa biyu wani irin ciwo kansa keyi masa ,

Bae ta'ba zaunawa yyi kuka mai tsayi ba sae a wannan lo'kacin bbu Wanda ya ta'ba ganin kukan sa da wayonsa da girman sa na yanzu sae meemah bamalli !#yana kukane sabida azababbiyar soyayyar AYSHA LAYLAH MASKA!"

Baisan yaushe hakan ta fa'ru dashi ba ,komae na Laylah maska yana sonsa sa'annan its so special agaresa.duk abunda yyi mata ne domin kaunarta da pretending bayada za'bin yin hakan na farko bai isa ya furta ba na biyu kishin yarda Aliyu maska da mujaheed maska suka kaikane komae na'ta na 3 itakanta Laylah maska ta daukesa makiyinta na bugawa a Jarida ,baya da abunda zaiyi Wanda zai goge kiyayyarsa a zuciyarta .A zahirin gaskiyya ya so'ma son Aysha Laylah maska ne tun Ranar da ta fa'do a dunia .

Bbu abunda Khaleepha maska ya'fi tsana adunia ,yaga irin yarda Laylah ke shiri da Aliyu maska da ku'ma mujaheed maska yana kishin yarda suke tarai rayarta suke nuna mata soyayya duk lokacin da yaga hakan yakan ji wani irin kishi aransa,

Ta hanya day'a CE yake ganin idan ya ba'ta Laylah wurin Aliyu da mujaheed maska zasu tsaneta shiyasa yake kiranta dakikiya !ka'ruwa mai yawo a hotel-hotel Wanda a zahirin gaskiyya ,yana fa'dane bada son ransa ba.yana fa'dane dan su daina kulata Ashe shi bai sani ba yyi wauta da tazo ta zamar masa bala'i,ko ace Alhaki yazamo masa dan kwaikwayo .wautar da tazamo Laylah maska ta tsanesa fiye da ko'wa a dunia ,azahirin gaskiyya ya nunawa Laylah maska kiyayyah domin kawae soyayarta da'ke barazana da zuciyarsa A kowane dakikah da numfashin da nake fitarwa .duk kiyayyar da nakeyiwa Laylah maska kishi ne kawae da pretending na nuna hakan ne dan SAMARIN ZU'RI'AR MASKA su kita ,daga baya sai nazo na aureta tunda bbu maiso Ashe shi yyi wauta ,

Ba samarin maska kawae keson Laylah ba daga waje ma wani zai iya cewa yana sonta !"

Yyi kuka dan soyayyar Laylah maska abunda bai ta'bayi ba akan wata ya'h macce ba.

Shi kansa yasan mutun ne miskilin da akan ra'sa gane inda ya do'sa mutane irin Khaleepha maska basa karantuwa .bakinda ya furta zalunci da kazabi ka'la -ka'la daga baya ku'ma ya da'wo yana furta SO (will never be trusted at all)".

Yyi kuskuren da bazai iya gyarasa ba.

shi da kansa ya'ke fa'din ayiwa Laylah maska Aure sabida kawae mahaukachin kishin da ya Rufe masa ido lo'kachin da ya'ganta da barister badar d/batta.

Acikin kwanakkin da suka biyo baya, kowane sakan ,kowane Minti kowane da'kika da ko'wa ne awa son Laylah maska ke ka'ruwa a zuciyarsa !"hnkalinsa bai gama tashi ba sae da Yaji ansa Ranar Auren Laylah maska nan da watannni Biyar 

Aranar da Yaji haka a ba'kin Abban sa  ku'lle kansa yyi a da'ki yyi kukan da tunda uwarsa ta kawosa a dunia baitaba yinsa ba.ya tabbata koda Mami CE zata mutu ba zaiyi kukan da yyi Ranar ba.

Har yau bai cire Ran zai sa'mu Laylah maska ba ,

Bai cire Ran zata zama matarsa ba.

"Am sorry meemah kinji dalili kinji dalilin wlhi bakin ki nakeyi ba,

Ina sonki tamkar yarda nakeson su Amra maska ,

Sae dai bana yimaki irin son da nakeyiwa Laylah maska.

Hannunsa ya sa'ka ya jawo dan karamin pics dinta ,

Shafa pics din nata yyi tun daga kan dogon hanchinta har zuwa ba'kin ta.

Kishi na shine matsalar ki ?"

Kishinki da nakeyi shiyasa nake hantarar ki ina yimaki fa'da !

Nasan this is All my problem only and its my problem then zanje nasamar wa kaina mafita . am very very sorry My Assha!"kansa ya Daura akan desk ya cigaba da zubar hawaye haka yana riqe da pic dinta.

La'yi ta farayi a tsakiyar falon da gudu mujaheed yaje ya tarota yana kwa'la mata kira cike da tashin hnkali ,

Gaba day'a ba'ta mo'tsi bani Ruwa Laylah ta su'ma wlhi ta suma !mujaheed maska ya ka'rasa maganar muryarsa na karyewa da gudu Laylah ta nufi kitchenHajiar su Aliyu da mamin su Khaleepha ne akanta Wanda har lo'kacin meemah bata San Wanda ya'ke kanta ba ku'san sumarta ukku ,ta ukkun ce da ta farfado ta fa'she da wani irin kuka mai Sosa rai Wanda ko'wa ya rasa gane ma'anarsa ,kwance take akan bed din su hajiar su Aliyu yyin da ko'wa ya tsaya cirko-cirko akanta Juya masu baya tayi ta cigaba da kukanta.Aliyu ne ya ka'rasa gareta gamida zama gefen ga'don ,cikin sanyi murya Aliyu ya kirata murya ka'sa -ka'sa tamqar kada taji murya Aliyu saurin miqewa tayi zaune gamida rarrafowa gabansa do'ra kanta tayi akan ka'fadar sa hawaye na cigaba da zuba akan kyakkyawar fuskarta take fa'din."Yaya Aliyu ina jin komae ba dai -dai ba .

Aliyu da baisan metake nufi ba ya tallabo fuskarta yana share hawayen idanunta ,

Cikin taushin murya gamida ta'llabo fuskarta da tafukkan hannunsa biyu .fa'damin meye damuwar Maryam bamalli?"

Cikin Rawar murya ta'ke fa'din mutuwa mutuwa zanyi yaya.!"cike da mamaki ko'wa ke ka'llonta cikin kunar Rai Laylah ta fice da'ga da'kin ba tareda ko'wa ya ku'la daita ba.kwance ya'ke akan soofa idonsa a lu'mshe sai dai ba barci ya'keyi ba .abun dunia ya ta'ru yyi masa ya'wah bbu wadataccen ha'ske a falon na'sa ,yana Jin qa'rar bu'de ko'fa sai dai haka baisa ya bu'de ido ba.Dan baya wuce Aliyu ne ya shigo part din na'sa ko mujaheed ,Dan ka'kaf kannensa mata ba kasa fai suke shigowa part din Khaleepha maska ba.Dan acewarsu komae na'sa na daban ne ,

ga mamakin sa sai yaji an ku'nna fitila mai ha'ske acikin fa'lon na'sa still bai bu'de idonsa ba.

Ran Laylah ya ka'ra ba'ci ganin sa kwance akan soofa da alamr bbu abunda ke damunsa.farin tree quarter ne ajikinsa sae bakar vest wadda ta ka'masa sosae ,tsaye tayi akansa tana ka're masa ka'llo wata irin tsanar Khaleepha maska takeji aranta.yyinda wani sashe na zuciyarta ke tausayawa meemah ,Jin anki magana ya'sa ya'dan bu'de idonsa da sukayi ma'sa nauyi yana bu'de idonsa sae akan fuskarta ,mamaki ne sosae ya bayyana akan fuskar Khaleepha maska.

Mamakin ba wani bane ganin Laylah maska tsaye agabansa ,

tsawon rayuwar da tayi agidan su ba'ta ta'ba ta'ko kafarta a part dinsa ba ko'da wasa sai dai yajita a part din Aliyu ko na mujaheed wasu lo'kuttan Wanda hakan ba ka'ramin ta'fasa ma Khaleepha maska zuciya ya'keyi ba.

Meyasa baka damu da damuwar ko'wa ba sai ta'ka ?"meyasa bbu zuciar tausayi da imani a tattare dakai ,meyasa kake wasa da zuciyarta ?nasan meyasa kake waya'nnan abubuwan .bcoz yhu don't care about any one yhu don't have any feeling and emotions ,duk mutunen da bayada way'annan abubuwan bazai ta'ba damuwa da A mutu ko ayi rae ba duka day'a ne a wurinsa ,

Bazai ta'ba damuwa ba sabida bbu imani a zuciyarka.Idan meemah ta Rasa ranta a sanadin ka ,

Zakayi nadama Khaleepha maska !".ka'llonta kawae ya'keyi mamakinta ya'keyi duk lokacin da Laylah maska ke magana dashi batajin shakkar gaya masa ko wace irin magana da zata fito a ba'kinta kai tsaye take fa'da masa magana.maimakon ya ba'ta amsa ko ya damu da maganganun ta ,kai tsaye ya miqe tsaye batareda ya ka'ra ka'llon inda take ba ya fa'ra tafia cikin isa haushi ya ka'mata batasan lokacin da ta ri'qo soft hand din'sa ba wani irin shock yaji lo'kaci day'a ka'llon cikin idonsa takeyi still tana riqe da hannun na'sa ,

Kai wane irin mutun ne?"tayi maganar cikin rawar murya ,kayiwa Allah karka ka'she kanwarka ta wannan hnyar,meye ajikinta Wanda ba'kaso ?"inajin Maryam bamalli ta chancanci ka 'sota Khaleepha maska ,sabida ta ha'da duk abubuwan da ake bukata a tareda macce ."

Fisge hannunsa yyi acikin na'ta yana binta da mugun ka'llon da baisan yaushe ya iyasa ba.

Fuskar nan ta'sa bbu fara'a a tattare daita.cikin kakkausar murya ya'ke fa'din ke wacece ?"

Ware ido tayi tana ka'llonsa da mamaki zatayi magana  yyi gaba batareda ya qa'ra kulata ba. A daren bbu Wanda ya runtsa acikin su kowane da damuwar meemah ya kwana aransa,kowane Juyin da zatayi cikin barcin ta Khaleepha maska take ha'ngowa Wanda batasan meye azuciyar saba.

da safe tamkar bbu abunda ya sami meemarh tayi shirinta cikin doguwar rigar abaya maroon colour wadda tayi balain ka'rbarta sauri sukeyi saloon zasuje daganan su wuce wurin ku'nshi Dan basu da isasshen lo'kaci ,da sauri Laylah maska take saukowa akan stair's ,Riga da wando ne na Jean's ajikinta sae boy friend jacket da ta Daura ,sai kanta da tayi rolling da black veil fuskarta fayau bbu kwa'lliyya dai-dai lokacin Khaleepha maska ya fito part din mamin sa ,cikin suit coat milk Wanda sukayi balain karbarsa.

Ya'mmatan gidan gaba day'a suka gaishesa banda meemarh bamalli wadda ta dauke kai ,

shima ko takan su baibi ba .

Yayah ka sauke mu wurin saloon mana!

Amra ta fa'da tana ka'llonsa ,

Amra Sauri nakeyi muna da meeting mujaheed ya sauke Ku mana.

Yana maganr yana tafia Laylah CE ta amshi car key din mamin su mujaheed taja motar ,achan suka ha'de da Meela.

Ka'rfe biyar da Rabi na yammah ya'mmatan gidan da ku'ma friends din Laylah maska sun ha'de cikin wani material maroon colour mai stones ajikinta farare ko'wace gown CE ajikinta sae head din Kansu da yakasan black ko'wacen su tasha kyau ,

Amma sai dai meye bbu Laylah maska bbu alamr ta mujaheed maska ne ya ka'raso cikin farar shadda Hilton ,Wanda gaba day'a samarin zuri'ar maska kalan shaddar ne komae iri day'a.


Feenah ya ka'lla wadda ke fa'mar danna waya ,

Laylah fah?"ya tambaya yana ka'llon feenah .

Ban saniba yaya muma ita muke nema na kira wayanta ta'ki ta da'ga badar sai kirana ya'keyi awaya tun da'zu suna wurin plsss feenah Ku tafi kawae kar suga bamuzo ba ni zan ta'ho da Laylah da haka ya Juya ya nufi cikin gidan su.

Ahankali ya tu'ra cikin bedroom din mamin su ,

Hangota yyi zaune akan bed ta ha'de cikin wata gown kalar orange sai head din kanta da yakasan CE Golding.

doguwar ajiyar zuciya mujaheed maska ya sauqe jin sa ya'keyi sa'ma -sama gaba day'a kwaliyyar Laylah maska ta daburta masa lissafi.talkamin ka'farsa ya cire ya ka'rasa cikin room din ba'kinsa dauke da sallama.

Zaunawa yyi akan soofa yana fuskantar Laylah maska ,Wanda gaba day'a jikinta ya ga'ma yin sanyi.


Sis kefa ake Jira. !"

Mujaheed yyi maganr cikin wata irin murya da'gowa tayi tana ka'llonsa idonta na cikowa da hawaye lokaci day'a.ban san meyasa nake jin tsoro ba yaya Jaheed ina jin komae na tafia da sauri da sauri inajin komae na auren nan na tafia kamar ba dai dai ba yaya."ta karasa maganar cikin rawar murya.ni ba aure na keso ba yanzu yayah mujaheed bansan meyasa yayah Aliyu yakeso nayi aure yanxu yanzu ba.

Komae sauri yakeyi komae da na tsara ba haka ya'ke tafia ba.lokaci day'a yaji hnkalinsa ya ta'shi ta Sosa masa inda keyi masa kai kayi. baya iya jure ganinta da wani d'ah namiji amma sai dai wannan ka'ron zai Jure zai kai zuciyarsa nesa ,

Bayason ya ba'ta wannan moment din.gwiwon sa duka biyu ya zube a kasa yana ka'llon idonta da suka cicciko da hawaye.

A hnkali ya shiga girgiza mata kai alamr karta fa'ra ,

Cikin taushin murya ya fa'ra magana. Kefa kika kawo sa dakan ki Laylah meyasa yanxu zaki fa'sa?"

Ban Fasa ba yayah .amma bana son auren yanzu ,yanayin da tayi maganar yaji wani Abu ya tsiya masa arai ko'karin ya'ke ya ha'desa ya ka'sa ,kefa kk kawo badar dakan ki shin baki yarda dashi bane?"yyi maganar yana tsareta da kyawawan idonsa waya'nda suka fa'ra chanja wa da'ga farare zu'wa Jah.


"Na yarda dashi.

Yawwah to meye dalilin damuwar?ko ranar auren idan su baba su kaga abunda bai ka'mata ba zasu sa a warware .bana son wannan tashin hnkalin bana son ganin wannan tsoron acikin idanuwan kanwata,ki tashi mutafi Dan nikam bana son komae na wannan partyn ya wuceni.sae kace ba sis Laylah maska ba wadda bata missing kowane party."daria Laylah tayi gamida miqewa tsaye Dan jada baya yyi gamida harde hannayensa akan kirjinsa yana ka'llonta.

Ware ido tayi tana ka'llonsa.

Give me a hug plsss !" Mujaheed maska yyi maganar cikin wani irin tone Wanda ta ka'sa fassarasa .ya ka'rasa maganar yana ware mata hannayen sa hugging dinsa tayi sosae tana jin kamshin turaren jikinsa Wanda ta Riga ta ga'ma sabawa dashi.

Idan tayi aure ba karamin kewar su zatayi ba.

a hnkali ya zare jikinsa cikin na'ta hannunta ya riqa suka nufi ko'far fita har lokacin bbu Wanda ya ka'rayin magana.

Seventeen hall.

Acikin hall din mujaheed maska yyi parking motarsa ,fitowa yyi da'ga motar ya bu'da back seat inda Laylah maska ke zaune.

Fito mana."ya fa'da yana ware mata idanunsa,

qa'ro na farko a rayuwarta da taji tsoron fita cikin jama'a kuma jama'ar waya'ndda suka taru dominta.

Fito mana sis

Tsoro nakeji yaya."

Tayi maganar a raunane ,

Girgiza kai mujaheed yyi yana ka'llonta ,idan baki fito ba zan daukeki a ka'fada na kaiki har wurin.

Ware masa ido tayi tana ka'llonsa tasan zai iya ba wani babban aikin mujaheed maska bane ,ya dauketa ya ratsa daita cikin taron nan.

Kwabe fuska tayi tana miqa masa right hand na'ta ,

Ka'mata yyi ta fito da'ga motar ka'llo day'a zakayi mata kaga tsoro cikin kwa'yar idanunta.

Mujaheed na rike da hannunta suka fa'ra ratsa tsakiyar mutanen ,koina sai bin su akeyi da ka'llo sai da yakaita gafda badar ya zaunar daita Wanda shima sanye ya'ke ciki wani ba'kin yadi Wanda akayiwa aiki da Golding zare ajikinsa ba qaramin kyau yyi ba.

Bakinsa yakai gafda kunnenta tayar da zata jiyosa ya'ke fa'din kinyi kyau my princess.

Kaima haka.ta fa'da gamida sauqe idanunta cikin na'sa lokaci day'a suka sa'ki kayataccen murmushi masu pic sai dauka sukeyi.

Agurguje aka shiga gabatar da komae tsayawa fa'dar abubuwan da akayi a wurin zai dau lo'kaci ne.

Can ta hango Aliyu maska tsakiyar su feena yana kwasar Rawa abunda ba'ta ta'ba gani ba Aliyu maska yyi Rawa.mamin su mujaheed da mamanta sai Likin ku'di akeyi masu ,day'an gefe ta hango Khaleepha maska cikin kaya irin nasu yaya Aliyu hajja na riqe da hannunsa ,ya wani ha'de rai .

Tana hango wani irin yanayi a tattare da fuskarsa ,

Zagayesu su mujaheed sukayi lo'kachi day'a tareda riqa hannayen junan su gaba day'a jikokin abobakar maska.

Hajja ta shiga ta'ka rawa ,

Tanayiwa Khaleepha maska li'kin ku'di Wanda ya tsaya kikam."

Kana hango wani irin ba'cin rae acikin kwayar idonsa ,Amra CE ta shigo tsakiyar filin ta riqa hannunsa ta shiga rawa dashi bin ko'wa yakeyi da ka'llo haka mamin sa ta tsallako tana yimasa likin dollar's na fitar hnkali Aliyu mujaheed shaddad su hafeez suka zagayesa tamkar shine angon.

Kansa ciwo yakeyi yana jin wani irin za'fi a zuciyar sa,

Meemah da'ke tsaye agefe tana ka'llon yanayin sa ,duk wani mo'tsi na'sa akan idonta yake yinsa.

Suna cikin wannan yanayin Laylah maska ta taho da gu'du tayi hugging din Aliyu maska ,

Lokaci day'a ta sa'ki kuka .

Girgiza kai yashiga yi gamida dawowa daita gabansa ,

Ka'ra rungumesa tayi .thank yhu so much yayah Aliyu !

Thank me for what?

Aliyu maska yyi maganr yana riqe da fuskarta haka hawaye na zuba a idonta."

Kabani komae yayah bansan da mezan sa'qa maka ba yaya.........saurin rufe mata ba'ki yyi hawayenta na sauqa akan hannunsa,

Hannunta shaddad ya ka'ma feenah ta kama hannun na hafees Amra ta ka'ma na mujaheed ,mujaheed ya ka'ma na Amra .da sauran kannensu. haka suka riqa hannayen juna sai da suka ha'da circle suka turata tsakiyya tsayawa ka'llonsu tayi cike da Sha'awa daria takeyi hawaye na zuba a idonta.

Gaba day'a tana son family dinta ,wannan rana tana daya'a da'ga cikin ranakkun da'ke da tarihi a rayuwarta Wanda ku'ma suke da muhimmanci.Aliyu yajawo badar ya turasa ,

Ka'llonta ya tsaya yi hannunsa ya'saka yana share hawayen idonta ,haka masu pics da masu vedioting suka hau daukarsu cike da Sha'awa.

Idan ya cigaba da tsayuwa anan zuciyarsa na iya bugawa.........tuki ya'keyi daukar wayarsa yyi yana kiran wayar Anas.

Har ta katse bai da'gaba ,

Kara danna ma'sa kira yyi sai ga na biyun ya da'ga. 

Ka'sa magana yyi sai dai Anas din ke fa'din ya akayi ne maza? har kun ga'ma bikin? "Tambayoyin da ya Jerowa bf din na'sa kenan lo'kachi day'a.

Kana ina? Ya fa'da cikin wata irin murya da ya'sa Anas ya gane something is wrong!" Wai wat wrong with yhu maska your sounds is bad.

Anas ya fa'da yana sauraren Khaleepha yyi magana.

I don't want to be strong any longer Anas !"

Everything is finally over !

Yhu ask me to fight for my Right so I faults. Bbu mai go'yamin baya ,I'm all a lone................ya ka'rasa mganar muryarsa na karyewa.wait maska kana ina ?

Anas yyi maganr cike da tashin hnkali ,

Ko'karin Amsa masa ya'ke yaji motar tasa tayi ka'ra lo'kaci day'a wayan ta tsinke ,wata babbar motace ta ka'ra masa salati ya hauyi.

gaba day'a motar Khaleepha maska ta shige cikin katuwar mo'ta Wanda hayaki yagama ci'ka cikinta mutanen da'ke tsaye a gefe da masu tafian ka'sa masu ababen hawa su'ka ka'raso wurin suna salati,Wanda nan ta'ke driver mai Jan babbar mota ya Ra'su yyin da aka dau'ko Khaleepha maska cikin Jini ga'ba day'a farar shaddar sa tagama jikewa ,da alamr shima bbu rai ajikinsa Dan ko mo'tsin kirki bayayi cikin mintuna go'ma sha biyar sai ga motar ya'n sa'nda.minti biyar kacal suka ga'ma rubuce -Rubucen su Aka wuce da Khaleepha hospital din Garkuwa ,tunda privart CE zasu amshe shi cikin gaggawa fiye da government da ki'la baa samu Dr.ku'sa ba.

Ku'san likitoci 3 ne akan Khaleepha maska ,

Acikin motarsa aka bincika ID card na'sa nan aka ga cikakken address na'sa.

Anas ne yyi parking din motar sa ko'far gidan su Khaleepha baima shiga da motar dai dai lo'kacin motar ya'n sa'nda ta parker ko'far gidan Alh.Habeeb maska,

da ido Anas ya bisu haka kawae Jikinsa ya ba'sa wani mummunan Abu ya sa'mi Khaleepha maska ,

Ka'rasawa gurin su yyi hannu ya basu sukayi musabaha,

day'a da'ga cikin su ya fa'ra yimasa bayani tun ka'fin ya'karasa Anas ya ka'tsesa cike da tashin hnkali ,cikin rudewa da tashin hnkali ya'ke fa'din awane hospital aka kwanatar dashi?"

Day'a da'ga cikin su ke fa'dawa Anas a Garkuwa hospital aka kwantar dashi ,

Jiki na rawa Anas ya Ciro wayarsa layin daddyn su Khaleepha ya fa'ra nema cikin sa'a ya da'ga wayar gamida yin sallama ,ko tsayawa amsa sallamar baba baiyi ba ya fa'ra yimasa bayani cike da tashin hnkali ,salati baba yyi ka'fin ya baiwa Anas umurni akan yabi ya'n sa'nda gashinan zuwa tare da Aliyu.

****

Misalin ka'rfe 8 na da're har lokacin Khaleepha maska baisan Wanda ke kansa ba,ka'farsa ta da'ma ta karye anyi masa dauri,

Sae dayan hannunsa na ha'gu kan ka'fadarsa ya gwafce sae gefen fuskarsa da ya goge ,baya numfashi sai da taimakon oxygen.

gaba day'a zuri'ar maska babba da ya'ro suna Asibitin Garkuwa ,

Har lokacin bbu Wanda ya iya ganin Khaleepha maska ,

Yyin da feenah da meemarh Amra ke Rusar kuka.

Cikin fu'shi Aliyu maska ya daka masu tsawa!"

Ya isheku haka!

Idan kunsan kuka za kuyiwa mutane mujaheed ya kaiku gida.

Nooo yayah plsss ka'rkayi mana haka ,cewar meemarh ta fa'da tana ka'ra fa'shewa da kuka gamida Rufe bakinta da hannunta Laylah CE mai karfin halin Lallashin su.

Kusan karfe tara Abban maska wato mahaifin Laylah yaba Mujaheed makullin motarsa ta Rager Rover ya'ce ya maida su Hajia gida da dukan ya'ra ,

Cikin kuka meermah ke fa'din Abba zan kwana gurin yayah Khaleepha plsss karkace No Abba.

girgiza kai yyi gamida shafa kanta A'ah maryama Ku tafi gida kuyi masa addu'a.

Gobema zaa daukesa a maida sa maska hospital.

Ko cikin mota kuka sukeyi dukan su.

Yyin da aka baro Aliyu da Abban maska sai Baban Kaduna gurin Khaleepha.

Cike da jimami hajja ke fa'din Allah ya tashi ka'fadun Abubakar allahu yabasa tsawon rai na'ga aurensa na'ga ya'yan Khaleepha maska.

Ko'wa ka'llonta ya'keyi yyin da mamin Khaleepha ke famar goge kwa'llah.

Kusan sha day'a da Rabi na dare Laylah ta ga'ma shafa,i da wutri miqewa tayi ta linke abun sallar da Hijab ta canja kayanta zuwa kayan barci dukan su ya'mmatan gidan suna part din Hajja Wanda aka ware mata Idan tazo ga'rin Kaduna .

Ku'ryar da'kin hajja ta danna kanta achan ta ha'go meemarh karshen ga'do ta dukun kule kanta wuri day'a,

Haka kawae Jikinta yabata meemah ba barci takeyi ba .kuka takey,

Cike da sanyin Jiki Laylah ta zauna ge'fen bed 

Ta kira sunan meemarh a hankali ,shuru meemarh tayi batareda ta amsa layla ba.

Ajiar zuciya Laylah ta sauqe ka'fin ta cigaba da fa'din nasan kina Jina meermah ki tashi magana zamuyi.

bbu musu meemarh ta miqe zaune batareda ta iya ha'da ido da laylah maska ba.

Wannan kukan da kk yi shine maganin matsalar ki mermah?"shi zaisa Khaleepha maska ya warke ,

Haba Dan Allah sai kache wacce batayi imani da Allah da kaddarar ba."a iya fahimta ta kaddara wata abace wadda ta'ke Jerawa da Rayuwar Dan Adam.suna gogayya da Juna kyakkyawa ko mummuna.

Ma'anoninta suna da girma da ba'kina bazai iya furta hakan ba meemah.abunda zan iya fa'da kawae shine.............a tsakanin ko'wace ka'ddara muka tsinci kanmu acikin ta fatan mu Allah ya bamu ikon Juriyarta ya bamu ikon ka'rbarta da hannu bibbiyu.

Addu'a ya'ke bukata ba kukan kiba meermah ,

Mubi ta fuskan duk yarda Rayuwa ta zomana ya'kamata mudaina Jayayyah da nufin Allah.

da haka Laylah ta kwanta gefen meermah a hnkali ta'ja duvet tana ka'ranto addu'ar barci.

Washe gari........

Tunda duku-dukun safiya Meemah tayi wanka cikin wata do'guwar rigar atamfa ,sae veil dinta mai ka'ma da atamfar fuskarta fayau bbu kwa'liyya ,

Amma tayi kyau.

Lokacin Laylah na zaune akan carpet tana karanta azkar.

A hnkali meemarh ta maida kallonta gurin Laylah ,

Cikin sanyi murya ta'ke fa'din ke baza kije kiduba yayah Khaleepha ba ?

Yanzu su Mami zasu tafi,

Dan murmushi Laylah tayi ka'fin ta rufe hisnul musleem din hannunta.

Shafa addu'a tayi ka'fin ta ka'lli meermah wadda ta zuba mata ido tana son Jin amsarta.

Ke'ma kin sani Idan ban ko'ma barcin safe ba ko'da na minti talatin ne yana sani ciwon kai ,

Sai natashi barci ka'fin na ko'ma Zari'a zan biya na'ga Jikinsa.

da mamaki meermah ke fa'din 

Zari'a kuma keyi meye?

Yayah Khaleepha bayada lfy shine zaki ko'ma Zari'a yau?"

Ta'be baki Laylah tayi .

Allah yabasa lfy Idan na zauna mezan yimasa ?

Yafi bukatar ko'wa fiye dani ,

Zan ko'mawa karatuna meermah.

Allah dai yabasa lfy kawae.

Amin meermah ta amsa gamida ficewa da'ga da'kin ,

Kan bed ta ko'ma tayi kwanciyar ta .

Tana mamakin irin son da meermah keyiwa Khaleepha maska Wanda baya boyuwa....


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.