Free chapter · Read without an account
10
Kai Mujaheed meye haka saketa mana waye ya fad'a maka ana jan amarya haka?" Auntyn maska tayi maganar cike da b'acin rai, bashiri ya saketa yana d'an jada baya itama laylah tsayawa tayi cak dukansu sunyi cirko-cirko suna kallon Auntyn maska baki wangale ta saki tana kallon su.
"Lafiyan Ku za kuxo ku tsaya min akai?"
Da sauri mujaheed ya shiga Sosa mata kai harara sa tayi .
"Ke laylah
Wuce muje ganin nan zuwa lokacin wankan ki yayi."
Turo baki tayi gamida buga kafa tace.
"Aunty fita zamu yi da yayah mujaheed fa."
Bud'e baki Auntyn maska tayi tana kallon rashin hankali irin nasu kafin tayi magana mujaheed ya karb'e zancen da fad'in.
"Please Aunty minti talatin yayi yawa saqo kawai zamu karb'o nan cikin A. b. u."
"Kaje kai kaɗai, mutafi laylah kina b'ata min rai." Cikin had'a rai laylah ke kallon Auntyn maska dad'in baki mujaheed yayi mata akan yanzu zasu dawo ya mata alkawari, Shuru tayi tana kallon su babu mai gaskiya acikin su musamman mujaheed.
"Please-please Aunty." suka fad'a lokaci d'aya "naji amma karku dad'e idan kuka dad'e zan b'ata muka rai mujaheed."
Sumbatar gefen Cheek's d'inta yayi kafin yace "naji na kuma amin ta."
daria Auntyn maska tayi, hijab ta d'auko dogo har k'asa ta saka sa'anan suka fice batare da sanin kowa ba.
***
"Yah mujaheed ya haka babu kowa a gidan kuma kace min nan ne gidan su budurwar taka..?!"
"Wai mekike yiwa sauri haka?!" ya fad'a cikin basarwa da had'e rai, ganin yadda ya had'e rai yasa tace "afuwan yayah."
Ga mamakinta da kansa ya bud'e gidan har lokacin mamakin sa ya kasa barin fuskar ta. Katon falo ne mai d'auke da set d'in kujuru aciki, abunda idonta ya fara gani bai wuce pic's d'in ta dake manne a ko'ina a bangon d'akin ba. Sai kuma wasu pic's din Wanda da ita da mujaheed ne amma pic's d'inta sun fi yawa a falon.
Tsaye tayi tana kallon mujaheed maska Wanda shima kallonta yake yi. Hannunta ya shiga ja har zuwa cikin falon ya zaunar da ita.
Baki bud'e take kallonsa hannunsa yasa ya rufe mata bakin yace "Rufe bakin kada k'udaje su fad'a miki." ture masa hannu tayi tana turo baki.
"Yaya ina ne nan?" Yace "gidana ne laylah" "ban tab'a sanin gidan nan ba." "Yanzu kin sani ai." Ya fad'a yana d'aga mata gira.
"Jirani ina zuwa." Ya fad'a yana nufar wata k'ofar. Girgiza kai tayi tana binsa kurum da ido.
"Ina sonki...! Ina sonki laylah maska, ban san tun yaushe ba ban sani ba na wayi gari na tsinci kaina cikin soyayyar ki lokacin da kika ce an saka ranar aurenki bana son kina min zancen, lokacin da muke yawan fad'a akan maganar aurenki duk lokacin ina sonki na kasa fad'a maki ban san ya zan fada ba." lokacin da naji labarin saka ranar aurenki sai da na kwanta gadon asibiti sati na biyu ban san Wanda ke kaina ba, haka na hana friend's d'ina su fad'awa kowa sanida na riga na fidda ran zan sameki na hakura dake duk atunanina nasan kin min nisa Ashe ba haka bane zuciyata ta kasa mantawa da sonki..."
Girgiza masa kai ta shiga yi tana Jin yadda zuciyarta ke wani irin bugawa haka tana ja da baya so take yace mata wasa ne amma sai dai yana yin dake tattare da fuskan sa babu wasa a ciki. wani irin ciwo takeji azuciyarta addu'a take yi Allah ya tada ta daga wannan mummunan mafarkin da take yi.
"Mafarki nake mafarki nake yi yaya............" Ta fad'a cikin ihu tana rufe duka kunnenta biyu. Dafa kafad'ar ta mujaheed maska yayi muryarsa na rawa yake fad'in.
"Ba mafarki kike yi ba Laylah da gaske ne."
Babu shiri ta bud'e idanun ta tana dafe da kanta dake neman tarwatsewa.
Murmushi laylah maska ta saki Wanda yafi kukan jaki ciwo. "bana sonka Yayah mujaheed ina jin ko babu badar bana iya aurenka, bana maka irin wannan soyayyar." Ran mujaheed yayi mugun b'aci domin yaji zafin kalaman laylah maskan.
Had'eta yayi da bango idonsa jawur tamkar Wanda yasha kwaya yace.
"Mekike fad'a haka? You are not fall in love with me? you love badar haan....? Look at me.." Ya fad'a gamida riqo mata kugu, wani irin k'arfi taji yazo mata ta turesa hanyar fita ta nufa a fusace cike da tashin hankali mujaheed ya bita yana fad'in.
"laylah..."
Ya fad'a yana riqo hannunta wani irin mari ta d'auke shi dashi kafin ya dawo hayacin sa ta kara d'aukesa da wani marin, muryarta d'auke da wani irin yana yi take fad'in.
"Ka kyaleni..Ka kyaleni yayah mujaheed....!"
Ficewa tayi daga falon tana sakin wani irin kuka wanda ke fitowa tun daga k'ark'ashin zuciyarta, haushin mujaheed takeji me yasa zai yi mata haka.
Adaidaita ta shige har lokacin kuka takeyi tamkar ranta zai fita, Suna isowa k'ofar gidan dai-dai lokacin motar Khaleepha maska ta k'araso hangota yayi tafito daga cikin taxi tana kuka da gudu ta fad'a cikin gida da sauri mai adaidata ya fito yana kwala mata k'ira yana fad'in "Hajia baki bani kud'i na bafa?"
Ganin haka yasa Khaleepha maska yayi parking ya fito ya karasa wurinsa yana tambayar lafiya.
Nan ya fad'a masa ya d'auko ta bata biyasa ba.
"Nawa ne kud'in naka?" "D'ari biyar ne."
Naira dubu d'aya Khaleepha ya Ciro ya miqa masa zai basa canji ya d'aga masa hannu ya juya ya koma mota, horn yayi maigadi ya bud'e masu gate sai da yayi parking ya juyo yana kallon Anas yana fad'in
"kai Lafiya kuwa?" "Wannan rigimammar ce mana ina ji ajikina something is wrong Anas..!"
"Kamar yaya?"
Anas ya fad'a yana kallonsa.
"Tsoro na keji Anas idan tace bata sona fa?"
Tallabo fusakar Khaleepha maska Anas yayi wani irin tsoro yake hangowa cikin idanunsa a zuciyar sa yake fad'in "lallai Lailah maska taciri tuta!"
Bai tab'a ganin abun da ya d'aga hankalin Khaleepha maska ba karo na farko a rayuwarsa da yaga karaya a tare dashi.
"Zata soka mana be a man, babu maccen da zata ki Abubakar Khaleepha maska, jeka kawai ina maka fatan Alkahiri." ware ido Khaleepha yayi yana kallon Anas yace,
"Ban gane ba, kana nufin ni d'aya zanje wajan nata?"
"Yes kai kadai mana." Ya kune fuska Khaleepha yayi haka lokaci d'aya ya shiga girgizama Anas kai tare da cewa "wallahi tsoro nake ji Anas, kaji yadda zuciya take harbawa kuwa."
Ya fad'a yana d'aura hannun Anas dai-dai saitin zuciyarsa yana jin yadda zuciyar tasa ke harbawa da karfi tamkar zata fito duk uban A.c d'in da suka kunna a motar amman Khaleepha maska gumi yake had'awa....
Fitowa yayi daga motar hularsa a hannunsa sabida irin yadda yake had'a gumi. Dariya Anas yayi yace "kai maska be a man mana, kaga yadda ka wani gigice kuwa sai kace ba kaine kake yiwa 'yan mata tsawa ba atiti, please maida hular mana."
Rai a had'e Khaleepha ke fad'in "zafi na keji fa." "Auh haka zaka shiga babu hula?" "yes mana bazan iya ba kada zafi ya ka'sheni wallahi.." yadda yayi maganar ya baiwa Anas dariya. cillawa Anas hular yayi yana fad'in "babu good wishes..?!" Dariya Anas yayi tare sa cewa "Allah ya bada sa'a."
Bai amsa ba ya Juya ya fara tafiya a hankali sai dai karku so kuji yadda kirjin Khaleepha maska ke bugawa. Har zai nufi Reception d'in shiga cikin gidan ya hangota a garding zaune akan grass carpet d'in da aka malala a wurin. Tsayawa yayi cak! yana kallonta hawaye na zuba a idonta take kallon hannayen ta, mamakin kanta take yi yau ita ta mari yayanta akan kawai yace yana sonta.
Girgiza kai tayi tana fad'in "Am so sorry Yah mujaheed ban san mezan ce maka ba a lokacin wallahi rud'ewa da gigicewa yasa na mareka, amma fa ba k'inka nake yiba, nauyin bakin da kayi har badar yariga da ya gama maye wannan gurbin! meh yasa meh yasa baka tab'a yi min zancen ba koda a cikin wasa ba?why?!"
Kuka ta k'ara fashewa dashi haka ta danna kanta acikin cinyoyin ta, haushin mujaheed takeji bata tab'a jin haushin sa irin na yauba.
"Ina mamakin duk wannan tsiwar taki da rashin kunyarki kuka baya yi maki wuya." Sassanyar muryar Khaleepha maska ce ta daki dodon kunnen ta hakan yasa ta d'ago da dara-daran idannun ta da suka yi ja ta watsa masa wani irin Irritating look kafin ta maida kanta ta cigaba da kukanta da alama bata da lokacinsa shi bai kai matsayin da zata yi masa magana ba, tana cikin wannan halin yama barta da abunda ya isheta.
Kukan ta ke tafasa masa zuciya da bata farga ba taji yace "be kamata kiyi wannan kukan ba taso mu shiga daga cikin kin san ma kuka yafi yima fuskarki kyau kuwa?" d'agowa tayi tana binsa da wani matsiyacin kallo mai cike da takaici, murmushi yayi gamida bata hannunsa na dama yace, "Shall we?" sai taji kamar ba Khaleepha maska ke magana ba, Still yana miqo mata hannunsa na dama.
Afusace ta miqe tsaye cike da tsiwa take fad'in "ban son rigimar ka kyaleni kawai.!"
"Ni kuma Ina son rigimar ya za'a yi kenan?" ya fad'a yana d'age mata gira guda d'aya, baki wangale ta saki tana kallonsa tana tunani anya Aljannu basu shafi wannan bawan allahn ba? ko dai yay zaton meermarh ce a gaban sa.
Ga mamakin sa sai yaga takai hannu ta shafi fuskarsa,wani irin shock yaji lokaci d'aya, da sauri ta ware idanunta duka biyu tana kallonsa juyawa tayi ta fara tafia ji tayi an fisgota lokaci d'aya taji ya matseta ajikin sa tana Jin yadda zuciyar sa ke harbawa numfashin ta taji yana bara zanar d'au kewa. A fusace tace mai.
"Ya isheka...!"
Tayi maganar cikin buga masa tsawa tana k'ok'arin zare jikinta daga nasa, haka taji wata sabuwar tsanarsa cikin ranta, "Meh kake so? Meh kake nema a tare dani? Ana dole ne, nace bana son rigima da kai ka kyaleni mana haan..."
"Bazan rabu dake ba sai naji meke da munki?" Yayi maganar in a low tune. karo na farko da taji Khaleepha maska yayi mata magana cikin kwantar da kai, "Akwai abunda ke damunki ki fad'a min meh yasaki kuka? mutane suna bina su fad'a min damuwarsu amma ni kao na farko da nabi wata macce dan naji damuwar ta don haka dole ki fad'a min abinda ke damunki." Yayi maganar yana shagwab'e fuska. sai taga ba karamin kyau yayi ba tamkar wani k'ara min yaro.
Ta hararesa game da fad'in "idan naki fah?" "Zan baki mamaki ne..!" Ware masa idanunta duka biyu tayi tana kallonsa da mamaki, Lallai wannan majnun guy d'in da gaske yake yi tace,
"Ina ruwana da kai? dan Allah ka tafi kabani wuri bana son kallonka..!"
"Oh haba? Ni kuma ina son kallonki ya za'ayi yanzu?"
"Wallahi wannan da gaske yakeyi." ta fad'a aranta sai kuma a fili tace "dan Allah kayi hakuri ka sakeni kayi min nauyi.!" Karo na farko da yaji Kalmar hakuri abakin ta, yadda tayi maganar ne ya sashi yin murmushi, Ashe tana iya magana dashi haka cikin sanyi murya? Wani irin kamshi ne ke tashi A jikinta mai fisgar masa zuciya, haka kawai yaji yana son kamshin hakan yasa shi kallon kyawawan pink Lip's d'inta, Jin tafia aba yan su ne yasa yayi saurin sakinta da gudu ta wuce daga wurin. Da ido yabita yana sakin smile duk abunda ya faru akan idon meemarh takaici da bak'in ciki kamar zasu kasheta.
"Sai nasa kun tsani Junanku fiye da yadda kuke tsanar junan ku a ayanzu."
Ji yayi anyi hugging d'insa kamshin turaren sa na dukan hancinta tace "saukar yaushe yah leefah?" Tayi maganar cikin sanyi murya. zare hannunta yayi cikin Jikinsa tafia ya fara yi batare da yayi mata magana ba dan shi kam a yanzu meermah tafi karfinsa ya riga da ya rufe babin ta. Shan gaban sa tayi tana b'ata fuska gamida hard'e hannayen ta akan Kirjinta. Matsawa yayi ya bata hanya k'ara tare hanyar tayi cike da bala'i yake fad'in "meermah wai ni sa'anki ne?" Lokaci d'aya ta fashe masa da kuka tana cewa "baka sona baka kaunata kana son kawai wadda bata san darajar ka da girmanka ba."
Juyawa tayi da gudu tabar wurin tana kuka, maganganun ta sun d'aure masa kai sosai. wayarsa ce ta fara k'ara ya duba yaga Anas ne mai kiran d'agawa yayi a sanyaye.
"Ka fad'a mata kuwa?" tambayar da Anas ya fara jefo masa kenan, shuru yayi dan bai san mexai ce masa ba. Karshe ma kashe wayar yayi dan bai san mezai cewa Anas d'in ba.
***
Tun safe mujaheed maska ke kiranta a waya tak'i ta d'aga ya turo mata texts na ban hakuri data karanta take deleting d'insa, bata san me zata ce ba bata san wace amsa zata basa ba kunyar had'a ido dashi ta keyi.
Yau ta kama laraba 'yan uwan Hajja wa 'yanda suka zo daga maska aka sakata lalle musamman abokanin wasan ta wanda suka yi mata wanka dashi. Sai ihu take tana fad'in su kyaleta da kyar Aliyu maska yazo ya sata ajikin sa yana fad'in "karku kasheta mugaye kawae." daria a kayi duka yayin da wata tsohuwa tayiwa Aliyun wankan Lalle da farar shaddar sa,
Amma ko gizau bai yi ba.
Laylah na kwance ajikin sa tana ihun kuka tana fad'in "ka tafi dani yayah kashe ni zasu yi wallahi."
Dariya duka akayi aunty Rumah taxo taja hannunta dan yin wankan Lalle.
Sanye take cikin wani farin less mai ratsin black a jikinsa d'inki riga da skirt ne Wanda ya zauna d'agwas a jikin ta. Sai bakar alkyabbah da aka d'ora mata akan kayanta auntyn maska taxo taja hannunta ita da aunty Rumah tana fad'in "Hajjah bari mukai amarya wajen dangin mamanta suna so su ganta." "ya kamata kam, amma taci abinci kuwa?wannan yarinyar akwae shegen kafiya tun safe babu abunda ke cikinta Sae fama kuka take ban san ko kukan me take yi ba."
Aunty Rumah ta amshe zancen da fad'in "Ayyah Hajjah kukan rabuwa dake ne." "ai nima xanyi kewar Laylatu." cewar Hajja "ku tafi dare nayi bara na dama mata fura kafin ku dawo."
Tun safe yake kwance a d'aki yau kumah Baban Kaduna yace Mami ta shirya zasu wuce Zari'a dama hajiar su Aliyu tun jiya ta wuce daga ita sai Khaleepha ne a gidan sai Daddy. "da sallama Mami ta tura kofar bedroom d'in nasa a kan Rug ta hangosa dunkule yake a wuri d'aya sai rawar sanyi ya keyi salati Mami tayi gamida k'arasawa gabansa tana dago kansa, jikinsa yayi zafi sosae,
"Khaleepha! Khaleepha!!." Mami ta shiga fad'a da sauri jin muryar Mami yasa yayi saurin bud'e idonsa, ya rungumeta gamida fashewa da wani irin kuka mai fitowa tun daga k'ark'ashin zuciyar sa yana cewa "Mami! Mami..sauran...sauran kwana biyu Mami tafia zata yi kina gani zata tafi ta barni? ya zanyi Mami??!" ya fad'a gamida cusa kansa cikin kirjinta ya cigaba da kuka tamkar k'aramin yaro jikinsa ko'ina rawa ya keyi.
Rungume sa tayi gagam a jikinta tana tofa masa addu'o'i dan har ga Allah Mami ta d'auka aljannu ne suka shafesa, cikin sanyi Jiki ta d'aga waya ta kira Daddy Wanda shima yana hanyar zuwa gidan shida driver.
Jin muryar ta yasan babu lafiya kashe wayar yayi gamida baiwa driver umarni ya kara gudun motar.
***
"Kayi wanka muwuce zari'a yanzu akwae malamin da zan had'aka dashi." Fashewa yayi da kuka tamkar k'aramin yaro yace "Nifa daddy bani da wani jinnu wallahi." "karya kake yi mai Jinnu kawai xai riqa yin abubuwan da kake yi." "Toh ni bana son zuwa Zari'a daddy Plss...." baki wangalau daddy ya saki yana kallonsa ita dai Mami tagumi ta zuba musu gamida zuba masu ido domin abubuwan Khaleepha tsoro suke bata. Daddy ya miqe tsaye ya qaraso gaban Khaleepha hannunsa ya basa babu musu Khaleepha ya baiwa daddyn hannunsa miqar dashi tsaye yayi Yaja hannunsa suka fice daga falon kwallah ta taru a idon Mami. waya ta d'auka ta kira Hajiar su Aliyu dan fad'a mata ciwon Khaleepha ya tashi zasu dai shigo zari'a zuwa anjima...
.tsayar da motar da yaji anyi ne yasa shi bud'e idonsa da suka yi masa nauyi. Baban Kaduna ya kallesa kafin yace "fita mutafi." Sannan ya kalli Mami yace ta jirasu a mota suna zuwa.
Da gaske daddy ya keyi wurin malamin sa suka zo yaji yace masa "fito mutafi." Baban Kaduna ya umarci Khaleepha maska wanda ya zama mutum-mutumi. "Daddy nifa babu abunda ke damu na zazzab'i ne kawai da gajiar aiki." Baban Kaduna ya kalli Mami cikin b'acin rai yake fad'in "kinga halin nasa kenan ko?" "daddy nifa ina ganin ba wannan bace matsalar Khaleepha kawai mu tafi."
Jin mamin ta sanya baki yasa Khaleepha ya sauqe ajiar zuciya ko kad'an baya son zuwa wurin Mu'allim d'in daddy dan baya son a tsare shi da tambayoyin da bai san taya zai amsa suba.
A can cikin gidan Hajja kuwa shirye-shiryen waleema ake tayi wadda za'ayi ta da misalin k'arfe goma na safe anan cikin Estate d'in Abubakar maska. Tun safe aka fita da amarya make up da gyaran jiki ita da su Meela da feenah maska.
Drivern Baban Kaduna na gama yin parking d'in motar tasu da misalin k'arfe 9:00am na safe gidan ko'ina mutane ne dank'am. Tsaki ya buga aransa Mami ta kallesa gamida fad'in "muje ka huta cikin gida." Yayi saurin cewa "Nooo Mami ki tafi kawai zanje BQ." "Meh zaka yi acan ko'ina akwae baki..?!" Yakune fuska yayi gamida fad'in "inda zan tafi babu mutane." "Toh naji kaje ka gaisa da Hajjah."
Wannan karon bai yi magana ba yabi bayan Mami wadda ke gaisawa da mutane. Mugun kallo Hajja ke binsa dashi. d'auke kai yayi ya had'e rai lokaci d'aya dan baya son magana da kowa. "Kai ba zaka gaishe da niba ne? Sai kace Wanda zai koma cikin uwarsa kana can tare da uwarka k'ato dakai..." hararar ta yayi gamida d'auke kansa baki wangalau ta saki tana reqe hab'a tace "yanzu ni yaron nan ni kake harara?"
Bai yi magana ba ya miqe tsaye yayi hanyar fita Hajja na kwala masa kira amma bai saurareta ba. Haushin kowa ya keji baya son magana da kowa ma gabaki d'aya. Da misalin k'arfe goma aka shigo da amarya cikin estate d'in da aka kawata shi sosai. Sanye take da Red less Wanda kud'in sa zasu kai kima nin dubu d'ari biyu mai adon stones a jiki black. sai bak'ar alkyabbar da aka saka mata da talkamin k'afar ta hill masu belt wanda suka k'arawa kafafunta kyau sosai wanda aka yi mata Jan lalle acikin su sai digon baki acikin su,
Wani irin kamshi take yi Wanda duk Wanda ya rab'eta shima xaiji yana kamshin. Aunty Rumah da Auntyn maska suka sanya ta a tsaka har gurin stage d'in da ya kamata ta hau acan ta hago badar cikin wani black yadi yayi masifar kyau. Zaunar da ita aka yi gaf da badar Wanda kamshin turarensa ya cika mata hanci.
Manyyan malamai ne aka gayya toh, tana jin yadda k'afar badar ke tab'o k'afarta murmushi kurum tayi bata kulasa ba. minti biyu da zaman su taji badar yana Auch!.......cikin wata irin murya da sauri ta yaye alkyabbar dake rufe da rabin fuskarta, Suna had'a ido ya kashe mata ido gami da langab'ar da kansa yana kallon cikin kyawawan idanunta. Tayi masa masifar kyau saurin rufe fuskar ta tayi. sai kusan k'arfe d'aya na rana aka gama waleemah da waazi Wanda duka ya kashe masu jiki musamman Laylah wanda kuka ta fara yi mai cika zuciya.
Da kyar ta yadda suka yi pic's da friend's d'in badar da nata badar sai tsokanar ta suke yi. Sunyi pic's dasu Mujaheed maska da Aliyu maska duka familyn maska sun ci ankon farar shaddah iri d'aya. Khaleepha maska ne kurum babu awurin, bata son wannan fad'an bata son wannan rayuwar yanzu zata bar rayuwar maska family zata fuskanci wata rayuwar ta da ban. "Yah Aliyu." Ta k'ira sunan sa cikin sanyi murya shi kuma yace "yes my princes ya aka yine?!" "yah Khaleepha fah ban ganshi ba yayah ba'a yi pic's dashi ba ko d'aya. Yayah baya sona na sani baya kauna ta, amma wannan ai ranata ce tawa ta daban ka rok'esa ko sau d'aya ne yaxo muyi pics ban san wace rayuwa zanyi a gidan badar ba, bana son na tafi gidan badar Khaleepha maska na fushi dani, na yafe masa duka abunda yayi min ni. Muje yayah dan Allah muje na nemo sa."
Ta fad'a idonta cike da hawaye tana jan hannun Aliyu wanda ya saki baki yana kallonta tace "Yayah kasan meye? Ni na daina fad'a na daina fad'a da Khaleepha maska, zo mutafi Yayah ina son ko so d'aya ne Khaleepha maska ya shiga cikin hidimata."
Cikin gida babu inda basu duba ba amma babu Khaleepha maska babu alamar sa, "Mami yayah Khaleepha fah?" Laylah ta fad'a tana kallon Mami Wanda ke famar hidama da baki tace "Baki gansa wurin waleema ba?" "Eh baije ba Mami." Laylah ta fad'a cikin sanyi murya "Toh kudu ba sa a BQ mana." dai-dai nan wayar Aliyu maska tayi k'ara Abban maska ne mai kiran ya kalli Laylah yayi mata alamar taje yana zuwa. Falo na farko babu kowa hakama na biyu na ukku ma, lokaci d'aya taji gaban ta na wata irin fad'uwa Wanda tara sa ko na menene. Cikin falo na hud'u ta hangesa zaune akan soofa kafafun sa na ajey akan center table, muryarta a karye ta matsa gaban sa tana fad'in. "Yayah...!" wannan karon idanun sa a lumshe suke haushin ta ya keji bai san uban da ya ka wota wurinsa ba yaji ta kuma cewa, "Yaya Khaleepha...!"
Ta kira sunan sa a hankali, nan ma banza yayi mata tace "Toh kayi hakuri bada rigima nazo ba pic's xaka taso muje muyi dan allah badan niba ko dan zumuncin mu plsss......." Zata kara magana taji ya fisgo ta gaba d'aya ta jita ajikin sa a tsora ce take kallonsa. Ido ya zuba mata wanda ke cike da b'acin rai. Cike da bala'i yake fad'in "Toh ana dole ne? ki kyaleni bana yi waya 'yanda suka zamar maki dole kinyi pic's dasu mana dole sai dani?
Kin san abun da na keji a cikin zuciya ta ne??!" yayi maganar cikin rawar murya gashi ya rik'e ta gagam a hannunsa.
Wani irin tsoron taji ya shigeta girgiza masa kai ta shiga yi hawaye na zuba a idonta shima hawayen ya keyi haka ko'ina na jikinsa rawa ya keyi. k'ok'arin sauka ta keyi ajikin sa ya riqeta gagam, A haukace ya shiga shinshinar ko'ina ajikin ta yana had'e fuskarsa da tata. ihu take yi tana turasa da qarfi kwantar da ita yayi da karfi akan soofa lokaci d'aya ya fisge Alkibbar dake jikin ta da d'an kwalin kanta shin-shinar gashinta yake cikin ihu da masifa take fad'in "nooo Yah Khaleepha ka daina mana bana soooo..."
Har ya d'aga kwalbar beer ya kai bakin sa kawai yaji an zare bottle d'in daga hannunsa, jajjayen idanunsa ya d'ago yabi Ayan dake neman wurin zama gaf dashi. kallon sa kawai Ayan ya keyi yana girgiza kansa tare da fad'in. "Sau nawa zaka sha beer ne Jaheed? kasan meh doctor's suka fad'a maka akan yawan wannan shan beer d'in? kasan a kwanakki sai da ya tab'a hanjin ka ko? meh yasa kake son halaka kanka akan abunda bai kai ya kawo ba?"
Ayan yayi maganar cikin tsawa da b'acin rai dan shi aganinsa Mujaheed maska shida kansa ya keson ya rasa Laylah maska rabuwa ta har abada. Kuma k'arya ya keyi yace yana sonta, da yana sonta da tuni yabi shawarar da aganinsa itace k'arshen wahalar sa.
Lumshe ido Mujaheed yayi ba tare da ya cewa Ayan ko uffan ba dan shi yana hangowa kansa babbar matsala muddin yayi wa Laylah fyade. Yes ya san idan ya mata fyade ba zata tab'a auren badar ba. shi kuma Idan ya aureta ba zata tab'a kwantar da hankalin ta tayi zaman aure dashi najin dad'i ba.
"Kayi wani Abu akai maska lokaci na tafia fa."
Hannu ayan ya saka cikin al-jihun wandon sa ya fito da wasu tablet ya ajey akan center table. Wata Leda ya d'auko again ya bud'a ta allurai ne a ciki yace.
"Zamu yi mata wannan allurar wadda zata yi bacci mai tsawo kai kuma zaka sha wa 'yan nan tablet d'in yadda zaka fice daga hayacinka cikin kan-kanin lokaci, kabar komai a hannu na nizan tsara komai koda tare da baraak ne kai zaka yi mana hanya shiga part d'in Laylah maskan."
D'aukar tablet d'in Mujaheed maska yayi ya shiga juya su a hankali yana k'are masu kallo.
*****
Khaleepha kuwa jin muryar Aliyu maska ne yasa yayi saurin bud'e idonsa a gigice sai had'a gumi ya keyi ta ko'ina duk sanyin a.c dake cikin room d'in. Waige-waige ya shiga yi sai yaga Laylah maska tare da Aliyu qura mata ido yayi zuciyarsa na harbawa kayan jikinta ya shiga qarewa kallo, magana ya keso yayi amma ya kasa gaba d'aya a rud'e yake, mafarki yayi kenan?" Ajiar zuciya ya sauke gamida d'auke kansa, Aliyu ya zauna gaf dashi cike da tausayin kanin nasa tamkar ba Khaleepha maskan da ya sani ba. Duk ya wani rame yayi zuru -zuru lokaci d'aya.
"Wai meke da munka ne? Baka da lafiya ne?"
Aliyu maska yayi maganar yana kai hannunsa saitin forehead d'insa. zafi yaji zau, janye hannunsa yayi hankali tashe yake fad'in "baka da lafiya ne?" "No naji sauqi yayah." ya fad'a a takaice gamida miqewa tsaye hanyar toilet ya nufa da sauri dan ko kallon Laylah maska bai yi ba. Saurin shan gaban sa tayi tana da'kune masa fuska take fa'din "munyi pic's da kowa banda kai kaxo mutafi ayi pic's dakai." wani irin irritating look yayi mata gamida d'auke kansa. "ka fad'a masa yayah Aliyu wannan karon babu rigima babu fad'a tsakanin mu domin kwana biyu ya rage!" Au murna ma take yi zata yi auran? kowace magana da take yi b'ata masa rai take yi, bai kulata ba ya cigaba da tafiya. k'ara shan gabansa tayi gamida folding hannunta kan kirjinta shaye da to'ka take fad'in. Na fad'ama babu rigima wannan time d'in da gaske na keyi Khaleepha maska..!"
Tayi maganar tana kallon cikin fuskar sa wanda ya wani had'e ta. "To kibasa hakuri mana." cewar Aliyu maska dake tsaye agefe yana kallonsu yana masu murmushi. ware idanunta tayi tana kallon Aliyu maska sai taga ya d'aga mata gira alamar tayi. Da'kune fuska tayi tana d'aga kafad'a kafin ta juyo kan Khaleepha maska,
"Am sorry!.. am sorry!!.. am sorry..!!" Haka tayi ta fad'a da dukkan k'arfinta tana riqe da hannunsa na dama tana buga k'afan ta a k'asa tamkar wata baby doll. Babu shiri ya fisge hannunsa yayi hanyar toilet gamida bugo k'ofar.
Juyowa tayi kan Aliyu maska wanda dariya ke son ta tahowa. Yanzu da ya hanata da laifinsa zata gani ae yanzu taxo da kanta. A fusace tayi hanyar fita tana fad'in I so much hate him I don't love him yayah...!" tayi maganar cike da masifa, bayan ta Aliyu maska yabi yana kwalla mata kira amma ko kallonsa ba tayi ba.
Shower ya sakarwa kansa yana jin zuciyarsa na wani irin bugawa haka hawaye na zuba a fuskarsa tamkar an bud'e fanfo. yafi k'arfin minti talatin a toilet d'in yana wanka.
******
Yau tun safe suke shirin yin dinner da familyn badar suka shirya masu Wanda anan cikin Zari'a zasu yi ta sun kama hall. Yau tun safe take Jin fad'uwar gaba wanda ta rasa kona menene. badar ya kirata yafi sau 10 amma ta kasa d'agawa haka kurum ta tsinci kanta cikin Jin haushin sa. Tun safe take kiran Aliyu maska a waya amma a kashe shima Mujaheed maska haushinta ya keji tun daga ranar da ta maresa bai qara kulata ba.
Ta tura masa texts babu adadi na ban hakuri amma yaki hakura jiya ma a wajen waleemah da kyar ya tsiya suka yi pic's. Zaune take gefen bed d'in Hajjah da misalin k'arfe biyu da rabi na rana da yake sai zuwa 8 na dare za'a fara dinner. furar da hajjah ta dama mata tasa agaba gamida buga tagumi wata koriyar atamfa ce ajikinta super Sheraton mai ratsin red a jikin ta gown ce bata d'aura d'an kwalin atamfar ba ta ajiye sa agefe gashinta sai kyalli yake Wanda yaji Gyara sai siririyar sarkar goal dake danqare a wuyanta,
Simple make up ne akan fuskarta tayi kyau tayi wani irin fresh.
Maman tace ta shigo d'akin tsiyawa tayi tana kallon ta baki bud'e a hankali takira sunan ta. A d'an riki ce ta d'ago kai tana kallon mamanta, k'arasowa wurinta tayi gamida yin tsaye akanta tace, "lafiyar ki kuwa? waton furar da Hajja ta dama maki baki masha ba kenan?" "Na koshi Mama." Ta fad'a cikin sanyi murya tana kallon Maman tasu. "Aikin ma kanki tashi kije kinada bako a falon baki." Ta shagwab'e fuska tana kallon Maman ta gamida fad'in "waye Mama? Ni bacci zanyi." "idan kinje kya gani bacci kuma idan kin dawo kyayi." zata yi magana Mamanta ta d'aga mata hannu "bana son musu oya tashi mu tafi." mayafinta ta d'auka kalar kayanta tabi bayan mamanta Sai wani cinno baki ta keyi. A falo taga su feenah maska dasu Meela da sauran friend's nasu binsu tayi da ido, meermarh ke fad'in "Gara da kika sakota gaba Mama da mune muka tafi zagi za musha."
Shewa suka yi ko kallonsu bata yi ba aranta take fad'in "Ku kuka sani banzaye ." Kamshin turaren da taji yana fitowa daga k'ofar falon yasa taji gaban ta yayi wani irin bugawa.Dara-daran idonta ta d'aga ta sauqe cikin nasa yana sanye cikin brown shadda sai kyalli ya keyi kansa babu hula sai wani lumshe ido ya keyi yana bud'e su da alamar jia baisa mu wani bacci ba. Kafafunta taji sunyi nauyi ta kasa k'arasawa cikin falon anan k'asan rug ta zube idonta sunyi rau-rau kiris take jira ta fashe da kuka gaba d'aya. Sam bata Jin dad'in zuciyar ta. Kallo badar ya bita dashi d'an girgiza kai yayi yana jin-jina rigimarta yana jin sonta na kara fisgarsa. Miqewa yayi tsam ya isa gareta shima zama yayi kan rug d'in dake malale a tsakiyar falon ya tankwashe k'afafunsa yana kallon ta hannunta na dama ya riqo yana bin hannun da kallo wanda aka yiwa zanen lallen flower. yana son wannan lallen yana jin yarda hannun ta ke rawa da sauri ya kalleta cikin sanyi murya yake fad'in "meya fa'ru Jewel?" Fashewa tayi da kuka tana fisge hannun ta cikin nasa tace "tsoro nakeji badar tun safe na tsinci kaina cikin fad'uwar gaba, am not happy 2 day tun safe nake jin bad mood, ni dai a d'aga auren nan kace masu su d'aga dan Allah ta fad'a." kara fashewa da kuka tayi, Kanta ya d'ora kan kafad'ar sa cikin sanyi murya yake fad'in "ban maki alkawari ba princess, ba zan iyaba wallahi, Idan aka d'aga auren nan zan iya mutuwa." da sauri ta d'ago kanta akan shoulder d'insa hawaye na zuba a idonta take fad'in "Ba gaba d'aya za'a fasa ba abarsa zuwa wani time d'in."
Ta k'arasa maganar tana shesshek'ar kuka gaba d'aya ta fara b'ata kwaliyyar ta,bai yi magana ba taji kawae ya jawota gaba d'aya ajikin sa abunda bai tab'a gwadawa ba koda da wasa, tana Jin yadda heart d'insa ke bugawa murya na rawa yace "Kinji yadda zuciyata ke bugawa ko Aysha? ko kin daina sona ne?!" Rungumesa tayi gagam a ajikin ta tana fad'in "ina sonka wallahi, tsoro nakeji badar." tayi maganar jikinta na rawa sosai, haka tana kara k'ank'ame sa. sanyi take ji babu shiri ya d'ago fuskarta bai yi magana ba taji yana had'e bakin sa da nata harshenta ya kama yana socking d'insa sosae, yayin da d'ayan hannunsa yake riqe da kugun ta. shuru tayi tana k'arbar saqunin sa haka takasa hanasa dan da alamr yana jin ddin moment d'in. Sai da ya gaji dan kansa yayi saurin sakinta da shanyayyun idanun sa yake kallon ta...
#Asmy b Aliyu
#Lailah Khalifa
#maska family