Free chapter · Read without an account

15

by Azizat Hamza · Mutum Mugu Ne

*MUTUM.....Mugu ne*


LAGOS

Tashan MBC 2 ne a wajen lokacin da Dr Sajid ya kunna TV, tashar suna film d'in Queen of Katwe wadda fitacciyar film maker wato Mira Nair ta directing nashi. Sajid ya d'auki remote zai chanza, batasan lokacin da tace "Uncle Dan Allah kar ka chanja, film d'in nada dad'i"

ganin yana kallonta yasa taji haushin kanta, stupid Naziha shi ya kunna TV amma zaki masa gadara.

Ta sunkuyar da kai tace "Sorry Uncle ka chanja"

Ya ajiye remote d'in yazo ya zauna yace " kince film d'in yanada dad'i, to bani labari"

Labarin film d'in ta fara bashi cikin yanayin maganarta mai sanyaya zuciya, ba wai siririyar murya gareta ba amma maganarta yanada sanyi gashi she's very eloquent. Haka ta fara summarizing mishi film d'in, harta gama kallonta yakeyi, Bai san dalili ba amma yanason jin magananta. Ta k'ara da cewa "lokacin dana kalli film d'in nan na fara son koyan game of Chess, dama Daddy yana dashi amma ni idan sunayi da Tim sai naga kamar shirme suke yi, but when I watched Queen of Katwe I just fell in love with Chess" ta yi murmushi.

Shi dai kallonta kawai yake yi, kome tayi yana karantar yanayinta.

Ta sake cewa " Uncle ka kalla film d'in Wazir? shima akan chess aka yi"

Dr Sajid ya girgiza kai

"Kayya Uncle ka missing, amma ka kalla film d'in....."

" Ziha" ya katseta. Ta bi shi da ido tana jin daɗin yadda ya kira sunanta.

"Ni ban cika kallo ba fah, bazan iya tuna film dana kalla last ba, in kin ganni a gaban TV I'm watching news ko wasan lawn tennis, wrestling ko karate. Though, I used to play chess when I was in school amma na fi shekara goma ban yi ba"

Ba ta yi mamakin hakan ba kasancewarsa babban mutum mai iyali.

Ya cigaba da bayani " I fancy reading books, gaskiya I'm not a movie person, in ba dan Zaytunah bama da wani lokaci ke takurani muje cinema lokacin muna abroad da zan iya irga miki iya films ɗin dana kalla"

'Zaytunah?' Ta maimaita a zuciyarta. Sai kuma ta kwaɓi kanta 'you dummy matarsa kenan. kyakykyawar matarsa da kika ga hotonsu tare'

"Wow! nima inason karatu amma Ina kallo sosai, though Papa yace karatu yafi kallo k'ara ilimi"

Dr Sajid yace " Papa yayi gaskiya, Allah ya jikanshi, Amin"

Jiki a sanyaye ta amsa da Amin. Kafin waninsu ya sake magana wayar Ziha yai ringing.

Sajid ne ya dauk'a kiran, ji tayi yace "Ok" sannan ya ajiye wayar yace mata taje bakin layinsu akwai taxi na jiranta zai kaita wajen da zata je.

Ta amsa masa da toh, shiga d'aki tayi ta saka hijab bak'i ba babbba bane amma ya rufe mata hips, ta fito. Sunan driver d'in ya gaya mata cewa Ishola sannan ta fita da wayarta.

Tana Isa bakin titi ta hango wata taxi an parker gefe amma bata k'arasa wajen ba saida ta kira numbar ta tabbatar shine sannan taje ta shiga, ta gaisheshi da yarabanci. Jikin Dr Sajid ya fara tambayarta tace masa da sauk'i, nan fa Ishola ya fara bata labarin kirkin Sajid, sai murmushi kawai take dan taji dad'in da Ishola yake yabon kyawawan halayen Dr Sajid.

Gidan Barrister Idris suka je, bayan sun gaisa da shi da iyalinsa sannan ya basu kayan Sajid. K'atuwar akwati da wata jaka Ishola ya ja ya shiga dashi cikin mota ita kuma ta rik'e jakar laptop ɗinsa da wayar iPhone.

Barrister Idris ne ya je ya tattaro masa kayan a hotel d'in, da ya ke tare suka lodging a wajen bai samu matsala wajen karɓan key ɗin ɗakin ba.

Ishola ya tsaya a ƙofar gidansu Ziha. Suka shiga gidan tare, tana ji yana gaishe da Dr Sajid ta wuce da kayan guest room da a yanzu ya koma d'akin Sajid. Tana fitowa Ishola ya musu sallama ya tafi.

"Thank you, Ziha" Sajid ya fad'i bayan ta rufe k'ofan falon

"Uncle ba komai fah, is there anything else I can do for you?"

"Oh yes, zaki taimakamin na fitar da kaya na"

Tare suka shiga d'akin ta jawo jakar ta bud'e yana zaune bakin gado, turarukane masu tsada guda biyar. Ta fara fitarwa ta d'aura su kan k'aramin bedside drawer dake gefen gadon, sannan ta ciro brushes nashi guda uku, toothpaste,shower gel da wasu mayuka da bata lura da sunansu ba, suma ta shirya su. Ganin singlet ne ya saura wanda ta tabbatar sauran kayan cikin ma inner wears nashi ne yasa ta rufe jakar ta jawo akwatin ta bud'e designer shoes ɗinsa ne a sama ta firfito dasu, sneakers guda biyu na kamfanin Nike da Gucci sai wasu had'ad'd'un Italian shoe na kamfanin Luis Vuitton da Prada, sai wani room slippers nashi mai kyau kalar sky blue. Wani box bak'i mai d'an fad'i ta gani a ciki har zata fito dashi sai kuma ta mayar. Duk abinda takeyi yana hankalce da ita ta jera masa takalmansa a k'asan wall closet na d'akin, guess room d'in girmansu d'aya da d'akin Tim sai dai shi wannan gado d'aya ne mai d'aukan mutum biyu aciki. Ta dawo zata rufe akwati d'in yace mata ta fitar mai da kayan da zaisa, abin ya mata banbarak'wai, ta tuno lokacin da Papa ke da rai sau tari ita ke za'ba masa kayan da zaisa amma yanzu "Can I really do it?" Ta tambayi kanta.

"Ina jiranki" ya katse mata tunani

"Uhm Uncle ban san wanni kaya kake on sakawa ba"

Yai murmushi "kowanne kika za'ba zan saka"

Ta fara duba kayan da suke ninke a goge cikin jakar, designer suits ne a ciki sai jeans da denim jackets da shirts haka, duk dai kayan babu native aciki.

"Uncle banga native clothes a ciki ba?" Ta tambaya

"Akwai guda biyu suna k'asa but gaskiya ban cika son sa su ba"

"Uncle amma sun fi maka kyau"

"Oh really!"

Tayi saurin sunkuyar da kanta tana murmushi.

"Karki damu zan saka amma ba yau ba"

Ta fitar mai da wani button T-shirt bak'i da jeans bak'i, ta ajiye gefe sannan ta rufe akwatin ta jashi zuwa wajen closet d'in tasa a ciki.

"Uncle Ina zuwa"

Kafin yace wani abu tuni ta fice a d'akin ya gane nufinta wato ta bashi dama ya chanja kenan....

Tunda ta shiga d'aki take juyayin Dr Sajid, Allah ya bashi komai, kyau, ilimi, kud'i, wayewa ga shi yana daraja Dan Adam.

" Some people are blessed with everything tun a duniya" ta fadi a fili.




........JOS...........

Nazima tana zaune tana chatting a wayarta wani bak'uwar number ya mata magana ta whatsApp, sunana Muhammad yace da ita wanda yazo office d'in Hajiya Raudha jiya.

"Ayya ko kaine Yaya Muhammad Shabbir k'anin Hajiya Raudha?"

Ya amsa mata da "Eh" Nan dai sukayi chatting sama sama daga k'arshe suka yi sallama.

Washe gari da Nazima ta tashi taga Muhammad ya tura mata katin dubu biyu, abin ya bata mamaki, nan ta nunawa Khairy, Khairy tace mata ai ba komai bane k'ila ya gani yana sone.

Nazima ta kai mata naushi Khairy ta goce.

Ta kira numbarsa bai d'auka ba saita tura masa text na godiya.

Koda taje restaurant Hajiya Raudha bata mata wani magana ba dan haka ta d'auka batasan zancen ba.

Da dare Muhammad ya kirata ta sake masa godiya suka d'an ta'ba hira kafin ya kashe wayar.

Tun daga lokacin Muhammad ya fara nuna mata soyayyarsa. Abinda ya d'aure mata kai shine, Har yau Hajiya Raudha bata yi mata maganar Muhammad ba, da ta faɗawa Hajiyarsu sai tace mata tabi a hankali karta yi saurin amincewa da soyayyarsa.

Bayan sati biyu da suka fara waya ranar yace mata yanaso yazo ya gisansu su gaisa. Ta nuna masa gaskiya sai ta tambayi Hajiya idan ta yarda toh.

Data tambayi Hajiya tace mata ba yanzu ba sai idan har Hajiya Raudha tayi mata maganar. Hakanan ta bashi hak'uri tace Hajiya Bata amince ba.

Wasa wasa suna waya har ta fara jin tana ra'ayinsa.

Abinda bata sani ba shine Muhammad Shabbir k'anin Hajiya Raudha yana can Minna wajen da aka turashi aiki, wannan kuma data had'u dashi Muhammad Kabir ne mijin Hajiya Raudha.......



.....KADUNA........


Tafiyar Layla da kwana biyu ya fara missing d'inta ada ya d'auka kawai dan sun d'an saba ne amma yanzu zuciyarsa na son k'aryata masa hakan. Duk lokacin daya zauna shiru tunaninta ke cika masa zuciya duk yadda yayi ya yak'ice hakan abun ya gagara. Tun da ta tafi sau d'aya yaje gidansu suka gaisa da ma'aikatan. Bayan sati biyu da tafiyarta direban Mom yai tafiya, ta kirashi akan ya zo ya rik'e Masa aiki kafin ya dawo.

Fara aiki da Mom ya sake karantar wasu abubuwa gameda binciken da ya keyi. Mom ita ke kula da gidan marayu na Alhaji Kadi.

Sati d'aya direbanta ya dawo bai ji dad'in hakan ba saboda ya fara samun wasu informations akan gidan marayu na Alhaji Kadi wanda da bai sansu ba.

Sai yanzu ma yake sakejin haushin tafiyar Layla gashi tunda ta tafi ko sau d'aya bata kirashi ba.

Haka dai ta kasance lokaci zuwa lokaci yakan d'an je gidan su gaisa da ma'aikatan. Yanaso ya kusanci sauran Ma'aikatan Alhaji Kadi ko zai samu wasu information amma hakan bai yiwu ba. Tun daga direbansa zuwa bodyguard duk shi ya d'aukesu da kansa sa'banin sauran Ma'aikatan gidan da Mom ce ta d'aukesu.




........Bauchi.........


Nazira kwanan nan mugayen mafarkai take yi akan Waheeda dan haka ta kirata bayan sun gaisa take tambayarta ko lafiya tunda watan cikinta ya shiga na tara. Waheeda tace mata lafiya sai dai itama yanzu bata samun baccin kirki saboda tana yawan munanan mafarkai.

"Kodai nazo ne kinga gidan da kike ke d'ayace idan wani abu ya faru ya za ki yi?" Inji Nazira

Waheeda tace " lah karki damu jiya Jameel ke cemin yau da dare zai kaini gidan Alhaji Kadi na zauna har na haifu matarsa ta tafi Umara jiyan"

"Gaskiya dole nazo kaduna na dubaki, yau zanje gida zan fad'awa Abba gobe da sassafe zan hau hanya"

Waheeda ta mata godiya.

...........Laure na zaune a falo tana kallo hannunta d'auke da dambun kifi tana ci, ga wani k'aton exotic juice a kan side table ta tsiyaya a glass cup tana korawa dashi. Shamsiyya ta shigo babu ko sallama, daga shigan jikinta kasan macen duniyace. Atamfa ce riga da skirt amma d'inkin duk sammakal, rabin k'irjinta a waje yake sannan duk shape d'in jikinta ya fito ta sak'ala wani k'aramin gyale a kafad'arta.

Cikin sauri ta ajiye jakarta kan center table ta shige d'akinta. Laure ta bita da ido "o'o ni Lauratu ko daga ina 'yar nan take oho" ta cigaba da kallon da take yi.

Minti biyar da shigan Shamsiyya d'akin ta fito rik'e da k'aramar purse a hannunta " Umma sai na dawo" ta ja Jakarta da k'arfi da niyyar ta fita, jakar ta su'buce ta fad'i ƙasa.

Shamsiyya ta shiga tattare kayan kwalliyar nata.

"Na shiga uku Shamsiyya! Mi nake gani?"

Shamsiyya ta juyo ta kalli mahaifiyarta dake tsaye tana nuna abin hannun Shamsiyyar ta wani zazzaro ido kamar wanda ta ga dodo.

Shamsiyya ta yi tsaki tace "abinda ki ka gani shi d'inne"

Laure ta fara salati da sallallami tana tafa hannu " mi kikeyi da con....dom Shamsiyya?"

Shamsiyya ta jefa su cikin jaka ta rataya jakar tace " ni na fita"

Laure tayi saurin janyo ta baya ta wanka mata mari ta shak'ota "Ina miki magana kina tafiya dan ubanki"

Shamsiyya ta fara kici kici da mahaifiyartata harta k'wace kanta ta koma gefe ta ce " Umma wai minene haka wai kina abu kamar wata saliha. Condom kika gani a jakata ba kan mutum ba, to minene aciki?"

Laure cikin masifa tace " Dan ubanki dama iskanci kikeyi a makarantar, duk burina akanki kin watsa min k'asa a ido"

Shamsiyya ta fara tafa hannu " lallai Umma kin rik'a, har ke muguwa ta k'arshe irinki kina tunanin bayan kin lalata yaran 'yar uwarki ta jini, ni zan ku'buta ne. To ki sani tun kafin ki lalatasu na riga na wuce tunaninki. Ko kinsan lokacin da kike kunna musu film na batsa kina tursasa musu su gani, Ina la'be Ina kallo, ko kin san tun kafin kisa a raping ɗinsu ni na riga na rasa budurcina, idan ma baki sani ba tun kafin Waheeda tayi ciki na riga na zubda cikin shege sau uku, Kuma ki sani fita dana keyi sana'ar da nafi k'aurin suna nake zuwa domin tuni an riga an koreni a makaranta"

Ba Laure kad'ai ba harta Abba da shigowarsa kenan kunnuwansa suka jiye masa wannan bad'ala da Shamsiyya ke fad'i dafe k'irji sukayi suna salati.

Abba da k'yar ya jawo k'afarsa ya k'arasa gaban Shamsiyya yace "Shamsiyya kice mini abinda naji k'arya ne, kinji?. Waheeda tah bata da ciki"

Shamsiyya cike da tausayinsa tace "Abba yau zan gaya maka gaskiya Umma ta dad'e da watsar maka da tarbiyan yaranka"

Laure ta daka mata tsawa "kina da hankali kuwa Shamsiyya, Dan ubanki ki fice kibar min gida" ta fara k'ok'arin tureta

Abba da idonsa yai ja saboda maganganun Shamsiyya yace cikin tsawa "Laure ki barta ta gayamin gaskiya"

Laure ta fashe da kukan munafurci "wallahi k'arya take yi, duk abinda zata gaya maka k'arya takeyi"

"Kaga Abba nasan Umma ita ta haifeni amma yau zan tona mata asiri......." Ziryan ziryan ta fara bashi labarin tuggun Laure da halin da yanzu Nazira da Waheeda suka shiga saboda ita.

Abba ya dafe k'irjinsa da yake masa wani k'una gumi na karyo masa idanunsa sun rikiɗa sun yi jaa...

Laure tuni jikinta ya fara rawa dan bata ta'ba zatan Shamsiyya tasan abinda take yiwa su Nazira ba

Sallamar Nazira yasa dukkansu suka juyo suna kallonta. Ganin halin da Abbansu yake yasa tayi saurin k'arasawa wajen shi tana fad'in "Innalillahi Abba lafiya, mi yake faruwa?"

Shamsiyya tace " ba lafiya ba Nazira dan yau Abba yasan komai dake faruwa agidan nan, komai ma ta fanjama fanjam. Duk zundumemen hijab da kike sawa na bogi ne, dan da ni dake duk d'aya ne"

Nazira ta zaro ido tana kallon Abba da yake k'ok'arin magana amma maganar ta sark'e. Da k'yar ya iya cewa " Why? Nazira miyasa baki sanar dani ba, why Nazi..." Ya kasa k'arasa maganar numfashinsa na fita sama sama.

Nazira ta fashe da kuka tana fad'in "Abba Inna Laure ita ta kashe Umminmu shi yasa..."

Abba ya duba inda Laure take tsaye jikinta na rawa "kika kashemin ita....kika...." Abba numfashinsa ya sark'e hannunsa dafe da k'irjinsa ya yi luuuu ya fad'i sume. Nazira tayo kansa tana kiran sunansa tana kuka, Laure ma ta rik'e kai tana ihu.........



.......KADUNA.....


Tun suna cikin mota da Jameel take jin yanayinta ya sauya wani abu na bin k'afarta, ta gayawa Jameel yace mata ta daure sun kusa isa gidan. Suna isowa ya tallafa mata ta fito yana rik'e da ita suka shiga gidan dayake dare ne duk ma'aikatan sun koma bangarensu musamman ma yanzu da Mom ta tafi Umara ba wani aiki sosai da suke yi.

Kai tsaye elevator suka shiga har third floor na Alhaji Kadi, a falo suka sameshi yana zaune ya d'aura k'afa d'aya kan d'aya. Da k'yar Waheeda ke jan k'afarta.

"Jameel ya haka? ko dai haihuwan ne ya zo?"

Jameel yace " Alhaji ina ganin yazo fa bari na shiga da ita d'akin"

Ya taimaka mata suka shiga wani d'aki kafin ta kai tsakiyan d'akin ta dire a k'asa tana nishi. Jameel ya taimaka mata cikin abinda baifi minti biyar ba ta haifo jaririyarta kyakyawar gaske.

Jameel ya d'auka baby d'in ya fita da ita wajen Alhaji Kadi bayan ya yanke cibin. Kai tsaye Alhaji Kadi yace ya je ya gyara Waheeda tukun yana zuwa ya k'ar'ba jaririyar yana murmushi.

Jameel ya shigo ya fara kimtsa wajen, ya shiga bathroom dake d'akin yana wanke jini wayar Waheeda yai ringing. Cikin jin jiki ta d'auka Kiran ganin sunan Nazira ne.

Nazira cikin tashin hankali take cewa "Waheeda gobe ki hau mota ki tafo Abba ba lafiya tunda yamma muke asibiti sai yanzu ya farfad'o"

Waheeda ta doka salaty tace " Nazira ya zanyi yanzu na haifu kuma banajin dad'i amma zanzo, kice Abba ya yafemin"

Nazira tace " ki tafo da jaririn naki kawai kizo kinji"

Kaman an tsikareta ta tashi ta fita daga d'akin tana daddafawa. Ɗakin da take tunanin shine na Alhaji Kadi nan ta shiga, bata ganshi ba, amma ta jiho magananshi ta jikin wani bangon d'akin da aka yiwa fenti jaa. Ta k'arasa ta ta'ba bangon. ....ɓut ta ji ta shige cikin wani d'aki. Abinda ta gani ne ya tada mata hankali. "Alhaji ....'yata ....'yata ka bani 'yata na fasa saidawa ashe yankan kai ka keyi kace gidan marayu kake dashi"... Alhaji Kadi ya nunata da yatsarsa nan wani haske ya shiga mata ido ta fad'i sume a wajen. K'arasa yanka 'yar jaririyar yayi ya miƙawa Gunki jininta sannan ya d'auki Waheeda ya fita da ita daga d'akin ta baya baya..........

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.