Free chapter 路 Read without an account

Chapter 8

by 饾櫧饾殬饾殬饾殯饾櫢饾殩饾殜饾殫 路 MunayaMaleek

馃崌MunayaMaleek馃崜





_By NoorEemaan_馃摎鉁嶏笍




Wattpad: NoorEemaan

Arewabooks: nooreemaan



xiii

(8)


Munaya da tunda ya matso kusa da ita taji kamshin turaren sa na hawan mata kai, ta dinga jin tashin zuciya, sai dai ta cigaba da daurewa, a gefe daya kuma tana mamaki, domin ita din ma'abociyar son kamshi ce, duk da bata taba samun ku蓷in mallakar turare na kan ta ba, amma tana son jin kamshi ko da wani ne ya saka, ta cigaba da daurewa yayinda take jin jiri jiri tamkar zata fadi, sai dai yana kai karshen maganar sa ta ji amai ya taho mata, ta yi saurin durkusawa bakin kwatan dake wajen tana kwarara amai sosai... Gabanta yayi mummunar bugawa a lokacin da take 茩o茩arin tuno wani abu, sai dai jirin da take gani yasa ta kasa ha蓷a tunanin ta waje daya. Bugun zuciyar ta ya cigaba da karuwa, murya a mugun raunane ta samu hada kalmar "Inna lillahi wa inna ilaihi raju'un" ta karasa wasu hawaye masu zafi na biyo kuncin ta...

Doctor Abbas da hankalinsa ke tashe yana mata sannu ya yi saurin bu蓷e motar sa ya dauko mata ruwa hadi da mika mata, Munaya ta kasa karba, gaba-daya komai ya tsaya mata cak, ta rasa abinda ke mata dadi, kana ta rasa wani irin tunanin ya kamata tayi, ta mike a hankali ta juya zuwa cikin gida, taku uku tayi ta ji wani duhu ya gilma ta idanun ta, wani mugun jiri ya sake dibar ta, ta tafi luuu ta zube, cikin sauri doctor Abbas ya karaso inda take, ya shiga kiran sunan ta "Munaya! Munaya!!" Amma ta gagara amsa wa, hankali a tashe ya dauke ta zuwa wajen motar sa, da hannu daya ya bude murfin motar ya sanya ta a ciki, ya zagayo ya shiga gaban motar ya tayar da ita da saurin gaske ya bar layin, duk bayan seconds biyu sai ya juyo ya kalle ta, maimakon ya nufi asibitin su sai ya nufi wani asibitin dake kusa sosai, musamman daya fahimci cewa tana bukatar taimakon gaggawa...

Mintuna biyar kacal ya kawo su asibitin, ya dauke ta cikin sauri ya nufi cikin asibitin, nurses dake kan duty suka yi saurin karban ta, sannan ya nuna musu ID card din sa, hakan yasa suka bar shi ya shiga, sosai likitan asibitin ya shiga duba Munaya, tsawon mintuna sittin ana abu daya, domin har test ya yi mata running domin ya fahimci matsalar ta kana a 茩arshe ya daura mata drip domin babu karfi ko digo a jikin ta, yana mikawa nurses kayan da yayi amfani da su ya kalli doctor Abbas yace "see me in my office doctor" ya karasa hadi da ficewa, doctor Abbas ya bi Munaya da kallo, sosai zuciyar sa ta karye, ba sai an fada wa mutum ba kallo daya za a mata a fahimci tana cikin halin rayuwa, numfashi ya sauke, yana fatan Allah ya sa ba wata Matsala ce babban ke damun ta ba...

"Ban san ya kuke da yarinyar daka kawo ba, may be your sister, neither your wife, ba hurumina bane lallai sai na sani, i won't say anything much tunda kai likita ne, You re already

into the system ka san komai, that girl is in a critical condition, nayi mamaki sosai da har karamar yarinya kamar ta jininta ya hau har haka, sannan the worst part is she's 6weeks pregnant, banason shiga hurumin da ba nawa ba, amma yarinyar nan tayi kankanta da haihuwa gaskiya...." Ya dan yin shiru kamar mai tunanin Wani abu sai kuma ya kara da cewa "any way ga drug's da za a siya mata" ya kai karshen maganar da rubuta masa magunguna.


Doctor Abbas was so speechless at first, ko kusa bai taba kawo hakan a ransa ba, Banda innalillahi babu abinda yake maimaita cikin ransa, sosai maganganun likitan suka dake sa, tausayin Munaya mai yawa ya sake rufe shi, yasan Munaya tayi wauta, ta kuma yi kuskure da laifi mai yawa, amma ya mata uzuri, musamman idan aka yi duba da karancin shekaru ta, ya mike a sanyaye ya fice zuwa siyo mata maganin.


_WASHEGARI_

A hankali ta fara bude idanunta da suka bata awanin a rufe, a kallo daya da ta yi wa inda take kwance ta fahimci asibiti ne, komai daya faru da ita a jiyan ya shiga dawo mata, bugun kirjin ta ya fara bada sautin dim! dim! dim! Har tana jiyo sautin sa tamkar zai fasa kirjin ta ya fito, hawaye suka zubo mata, can kasan makoshi ta furta "ya Allah kasa ba abinda nake tunani bane, ya Allah ka yafe min na tubaaa!" Ta karasa wanna karon cikin dan karfin sauti yayinda ta fashe da kuka....


Ta jima tana kukan, har sai da taji kanta kamar zai cire dan ciwo sannan tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya a jejere.


****

A hankali doctor Abbas ya turo kofar ya shigo, Ganin idanun Munaya biyu ya saka ya karasa gareta cikin sauri, cikin murya mai cike da kulawa yace "Munaya sannu kin tashi, I'm sorry na samu kiran emergency ne shiyasa na fita, ya kike ji yanzu?"


Munaya ta zuba masa innocent idanun ta masu tarin rauni, tana mai yaba kirkin sa a ran ta, ya taimaka mata sosai duk da basu hada komai ba, amma har yau ko godiya ta kasa masa, still bai tsare ba ya cigaba da taimaka mata, ta sauke idanun ta kasa, a hankali tace "da sauki"

"Alhamdulillah!" Yace cikin tausayin ta, bai ma san ta ina zai fara bata wanna bakin labarin ba, numfashi ya sauke kana yace "i brought you breakfast na san kina jin yunwa koo"


Ta kalli ledar hannun sa ba tare da tace komai ba, ya fito da takeaway mai dauke da chips da egg ya mita mata, ta girgiza kai alamun bata ci, ya ja kujera ya zauna yace "kin san baki da lafiya ko? Kina bukatar Energy, babu karfi ko digo a jikin ki, kici Please"


"Banason kamshin wanna abincin" Tace tana jin sabon tashin zuciya. Cikin sauri doctor Abbas ya matsar da ledar mai 蓷auke da abincin a kusa da ita kana ya dawo ya zauna.


"Menene yake damuna doctor?"

Ba tare da ya shirya wa hakan ba ya ji saukar Muryar ta mai cike da rauni a kunnen sa .

Shiru doctor Abbas yayi ya kasa bata amsa, domin bai san yanda zata dauki maganar ba, a rayuwar sa bai taba ganin yarinya mai shekaru irin na Munaya dake fuskantar 茩addarar rayuwa kamar haka ba.


"Please" ta kara rokon sa.


Jin shirun yasa jikin ta 茩ara sanyi, jikin ta na fada mata cewa ciki ne da ita, amma tana bukatar a 茩aryata hakan, tanaso taji wani yasa mata hope din cewa zazza蓳i take, ta runtse idanun ta kana ta bude su, tsawon mintuna biyar sannan tace "Ciki ne dani ko doctor?" tace cikin Muryar kuka yayinda hawaye suka cika idanun ta.


Cikin mamaki mabayyane doctor Abbas zaro idanun sa, ta faru da kare, shi da yake tunanin hanyar boye mata, ya sauke karamar ajiyar zuciya yace "ciki! How did you know that Munaya?"



Lumshe idanun ta tayi, sai Yanzu ta tuna rabon ta da period kusan wata biyu kenan, tunda tana 13yrs ta fara gani, bata taba fashi a ko wanne wata ba sai wanna karon,

sai a lokacin hawayen suka zubo kuncin ta, ta saka bayan hannun ta na hagu ta share hawayen tace "baya ga Amnah Umma ce mutum ta farko da muka Shaku, Umma nah ta fadamin symptoms na masu ciki idan muna hira domin na kasance ni yarinya ce mai son sanin abubuwa musamman 蓳angaren mata, ina da yawan tambaya kan wanna fannin, Umma na ce ta sa min sha'awar karatun likita, domin har alkawari ta min na cewa matukar ina son karatun likitan da gaske, ita kuma zata tsaya min da duk abinda take da shi domin cika burina, na kan ce mata Ummah idan na girma na zama likita zan yi wa Amnah aiki a asibitin da za gina har ta warke, a lokaci sai dai ta min murmushi, ashe bazasu rayu tare da Ni ba. Tayi shiru tana 茩o茩arin danne kukanta kana ta 蓷ora da cewa, Umma ta bani labarin irin laulayin data yi a cikina, irin shi nake ji a jikina doctor, da gaske ina da ciki doctor? hasashena gaske ne? Please say no doctor, ya Allah na tuba"


Jinjina kai likita yake cikin mamakin wayo irin na Munaya, lallai ta wuce inda yake tunani, tana da kaifin tunani daya girmamawa shekarun ta, lallai bawa baya iya tsallaken 茩addarar sa, idan ba haka ba, Munaya na da wayo da bazata Bari wani namiji ya tara da ita ba, ya shafa fuskar sa cikin rashin sanin abin yi, can ya numfasa hadi da cewa "Munaya kiyi hakuri, ki sani cewa bawa baya wuce 茩addarar sa, Allah gafurur Raheem ne, ki cigaba da istigifari, ni ma zan taya ki"


"Dan Allah doctor ka cire min cikin nan, wallahi Bazan iya ba, na tsani shi dan Allah doctor" ta karasa cikin rokon sa.


"Subhnanallah Munaya karki kara fadin haka, ya za'a cire cikin, bayan wancan zunubin kina son yin kisa, kina so Allah yayi fushi dake?"


Kuka sosai Munaya ke yi, har majina na zuba daga dogon hanjin ta, tsana mai yawa na Maleek ya kara cika zuciyar ta, hatta abun da ke cikin ta ta tsane shi, da ba dan karta zama mai tarin laifi ba data kashe kanta, domin komai ya daina mata dadi ko burge ta a wanna duniyar mai cike da kalubale, doctor Abbas kam ya ma rasa wani kalma zai yi amfani da ita wurin kwantar mata da hankali, ya cigaba da zuba mata idanun sa yayinda take kuka, can ya jif kukan ya dauke, ya kalleta da kyau sai ya ga jikin ta ya saki, hankalin sa yayi mummunan tashi, tsoron sa kada ta hadiyi zuciya ta mutu, ya ma manta cewa shi din fa likita ne, hankalin sa a tashe ya fice domin kiran

Likita, Babu bata lokaci likitan ya biyo bayan sa, cikin ikon Allah ta farfa蓷o daga suman data yi bayan likitan ya bata taimakon gaggawa, sai dai jinin ta ya sake hawa, abinda ake son ya sauka musamman ga ita mai ciki.


***

Kwanan ta uku kafin aka sallame ta, doctor Abbas ya Kai ta gida, Bayan ya sake kwantar mata da hankali ya kuma roke ta tana dan cin abinci ko yaya ne, ya kuma yi mata al茩awarin cewa zai dawo jibi ya duba yanayin jikin ta, jinjina masa kai tayi kana ta fice daga cikin motar tamkar wacce kwai ya fashewa a jiki, doctor Abbas ya bi ta da kallo har ta bacewa ganin sa, ya sauke ajiyar zuciya ya tada motar sa ya bar layin .


A daren Munaya ta yi mafarkin da Umman a dan baccin daya dauke ta kasance allurar baccin bai gama sakin ta ba, abin data gani yayi matukar daga hankalin ta, ta tashi zaune ta jingina da bango, tana jin yanda jikin ta ya jike da gumi, abinda yafi daga mata hankali shine ko yaya ta kifta idanun ta ko ta lumshe su sai ta hangi umma tsaye fuskar ta babu annuri yayinda hawaye ke zuba daga idanun ta tamkar an balle famfo, ta kasa gane kan wanna mafarkin, domin tun bayan rasuwar Umma da kwana biyu bata kara yin mafarki da ita ba.




***

Kamar yadda doctor Abbas yayi al茩awari ya dawo, bayan sun gaisa, ya 蓷an ja ta da hira wanda yawanci shi kadai ke maganar sa, domin ba wata amsar kirki yake samu daga gare ta ba, a karshe yace. "Munaya ina ganin ya kamata a sanar da who's responsible for pregnancy abinda ke faruwa, dole ya san abinda ya aikata, a ina yake, ki bani address d峄媙 sa Ni zan je na sanar masa, idan ma yaki amincewa zan hada shi da hukuma" Girgiza kai Munaya ta shiga yi, hawaye cike a idanun ta.


Ya kara tausasa murya yace " na fahimci yanda kike ji, kiyi hakuri Munaya, Ni kai na bana son wata mu'amala ta 茩ara hadu ku, amma jaririn da bai san komai ba, bai kamata laifin baban sa ya shafe shi ba, duk abinda nake yi ina yi for your own good, tamkar kanwata haka nake jin ki, bazan cutar da ke ba, kin ji koo?"


Ta runtse idanun ta, cikin jin ciwon kalmar jariri da uban da likita ya ambata, bata bukatar su, ko jin sunan, yaya za ta yi da rayuwar ta? Yanda ta tsani Maleek, ha茩a ta tsani jininsa dake kwance a mahaifar ta, ta ja wata doguwar ajiyar zuciya daya sanya doctor Abbas kara tausaya Mata domin ya fahimci tunani ta fada.






Su waye MunayaMaleek???

We will find out as from next page, ku biyo ni dan ji tarihin MunayaMaleek...

Wanna tafiyar mai tsawo ce Fiye da sauran books dina, kuzo muyi tafiyar nan da ku fam, come one, come all鉂わ笍




I know today's chappy is short, shhhhhhh馃か馃槀鉂わ笍




MunayaMaleek is 500 via 3200689890 Haruna Rukayya

first bank, zaku iya fara payment Kafin mu gama free pages ngd.





NoorEemaan

***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol