Free chapter · Read without an account

012

by Badeelah Yakubu Mahdi · WASA DA RAI

A yaune ɗubbin jama'ar dake unguwar Malam Inna da ma kewaye suka shaida auren Ƴaƴan malam Usman Mele,Fatima Usman Mele da Angon ta Bashir Tukar Sai Hauwa Usman Mele da Angon ta Ayuba Isma'il,Biki yayi Biki komai na tafiya yadda ya kamata duk da cewar ba'ayi wani event ba sai walima na mata daban maza daban, amare sun sha kyau iya kyau haka ma iyayen su da yayan su Abdullahi , kana ganin sa zaka gane cewar kwata kwata baya cikin wal wala an kasa gane kansa mutane sai tambaya suke , sabida duk wanda yasan Abdullahi yasan shi ɗin mutum ne mai fara'a da yawan dariya da mutane amma yau yayi shiru kamar ba shi ba, acikin ƴan sati biyu zuwa uku ya lalace yayi baƙi ya rame kamar ba shi ba, ƙannen sa da ma baaban sa suna matukar tausayin sa amma banda maama sabida ita ran ta feess yake ,duk wanda ya tambayi me ke da min Abdullahi sai tace yayi zazzaɓi ne, a haka har biki ya fara watsewa.


  "Maman Abdullahi biki yayi armashi gaskiya kunyi kokari sosai wallahi a Wannan marar aurar da ƴaƴa biyu ba wasa ba" faɗin maman Sani tana cikin matan da suke Zazzau ne basu tafi ba tukunna.

Ɗayar matar ce tace "wallahi kuwa sunyi kokari matuƙa, fatan mu shine Allah Ubangiji ya basu zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba" duk suka amsa da Ameen.

"Saura auren auta zamu kuma dawo wa baɗi idan Allah ya yarda" faɗin maman sani tana murmushi.

"Ke kuwa wa ke maganar Salima ita da haryanzu bata gama makaranta ba, ai da sauran ta" maama ta faɗi tana ƴar dariya.

  "Hakane kam kin ma tunasar da Ni wata mai kamawane bikin Abdullahi da Zainab ƴar gidan saratu ko?"

  Nan da nan annuri da ke fuskar maama ya ɗauke kamar bata taɓa dariya ba tace "Ai Abdullahi bazai......"

 "An ɗan ɗaga bikin ne zuwa wani lokaci akwai abubuwan da Yakamata ace ya kammala kan bikin ƙila zai kai wata shekara ma"

Larai kanwar Maama ta chaɓi zancen tana gyarawa gudun kar maama ta daɗi wata maganar da bai kamata ba.

Ƙirkirarren murmushi tayi tace "Eh kin san abubuwan ne sai a hankali ga yanayin Rayuwar da tsada baya ga haka kuma kusan komai na bikin ƙannen nan nasa shi yayi"

"Allah sarki Abdullahi akwai kokari ai, Allah dai ya masa albarka ya dafa masa" da Amin suka amsa da ɗaɗɗaya suka fara watsewa aka bar wa'anda zasu kai amaren. Cikin su akwai dangin maama ƙannen ta da kuma wasu daga cikin dangin Baaba.


Bayan maama da baaba sunyi wa amaren nasiha mai shiga jiki kamar yadda ko wane Uba da uwa suke wa ƴaƴan su suka sanya musu albarka haɗe da fatan zaman lafiya da samun zuri'a ta gari. 

Ƙarfe Uku nayi motocin ɗaukar amare suka fara zuwa motan da zai ɗauki Fatima ne suka fara zuwa kasantuwar ita Bauchi za'a Kaita mijin nata ɗan Gombe ne Amma lecturer ne a Bauchi State University, ba jimawa masu ɗaukar Hauwa suma suka zo, ita kuma nan cikin Gombe gidan ta yake a Buba Shango, Abdullahi ne ya riko hannun su , Fatima na daga dama Hauwa na daga hagu, takawa suke gwanin burgewa amaren sunyi kyau cikin suturar da suka sanya kana gani su kasan ya ci kuɗi dai dai arzikin su sannan zaka gane wankan na amare ne, har motar da zai ɗauki Fatima yayi rungumar shi tayi tana kuka shafa kanta yayi yana mai share mata hawaye ya buɗe motar sai da suka rungumi juna da ƴar uwar ta suna kukan rabuwa da juna , ganin suna ɓata lokaci ne ya ɓanɓari Fatima a jikin Hauwa ya sa ta a mota yana musu fatan a sauka lafiya, hannun Hauwa ya rike ita ma ya buɗe mata ƙofar motar kuka ta fashe dashi ta rungume shi tana kuka sosai , kaf cikin ƙanen sa sunfi sabawa da Hauwa kasantuwar itace mai sanyin hali a cikin su, kuka take sosai tun yana rarrashin har yayi shiru sai bubbuga bayan ta kawai yake ,don ya tabbata idan ya buɗe baki shima zai iya yin kukan, matan dake gun ne suka zo suka janye ta daga jikin shi tana ƙara tsananta kukan da take, maama kuwa kasa fitowa tayi tana tsakar gida tana jin kukan da suke itama kukan take sai faman share hawaye take da bakin zanin ta , Salima ce ke zaune a gafen ta tana ta bata baki kasantuwar duk matan suna waje. Ana sa Hauwa a mota yayi saurin barin wurin ya wuce cikin gida.

Salima najin karar motoci ta fito da gudu ta shige cikin motocin da zasu Bauchi sabida da ita dama za'a yi rakiyar.


 Auwal na ganin Abdullahi ya shige ɗaki yayi saurin bin bayan sa , a ɗaki ya tarar dashi yana zaune a bakin gado kan sa a ƙasa yana tuna abubuwa da dama ta wani ɓangare matsalar sa da Zainab gefe guda kuma kewar ƙannen sa.


 Dafa shi a kafaɗa Auwal yayi ɗan ɗagowa yayi yaga Auwal ne maida kansa yayi bai ce dashi ƙala ba hawaye na sauka kamar famfo,zama Auwal yayi "Abokina lafiya kuwa wani abun ne ya faru?" Girgiza kai Auwal yayi sai yanzu ya lura da hawayen da ke kwaranya a idanun sa.

"Haba Abdullahi sai kace ba na miji ba? nasan shakuwar dake tsakanin ka da ƙannen ka amma gaskiya banyi tunanin haka da ga gare ka ba ,kana zubar da hawaye? Kar ka manta fa aure suka yi Sunnah zasu raya addu'a ya kamata ka musu ba kuka ba sai kace mace"

Shessheka Abdullahi yake yi cikin Muryar kuka yace "Ni ba kukan tafiyar su Fatima nake ba duk da cewar nasan gidan zai min faɗi zanyi kewar su sosai, kawai tunawa nayi daba don matsalar nan da ta faru ba da yanzu za'a fara lissafin aure na da Zainab saura 3 weeks."

"Kaga Abdul Ka daina zubar da hawayen ka akan wacce bata damu kai, just focus on yourself Ka ganka kuwa duk ka fita hayyancin ka ka rame ka lalace kamar ba kai ba wannan ma abin kunya ce wallahi ace akan mace ka shiga wannan halin." Cike da ɓaci rai yayi maganar sabida ya fara ɓata mishi rai akan maganar Zainab ɗin.

"Baka san mene ne so ba Auwal da baza ka ce haka ba"

"Na sani mana tun da dai soyayyar nima nayi ko kuma nace ina kanyi, amma Ni ba haukar da kake na ke yi ba wacce nake so tana so na nima kuma ina son ta, ba kamar ta ka ba da kake ta haukar ka kai kaɗai" yana hararan sa.

  Murmushi Abdullahi yayi "kai kan ka shaida ne Zainab ta soni"

"Alhamdulillah....." Ya ɗaga hannu "Nagode wa Allah da kai da kan ka kace ta so ka meaning yanzu bata son ka, Ni wallahi takaici da mamaki ka ke bani yarinyar da tace ba ta son ka kuma tace baza ta aure ka ba amma ka tsaya kana damin kan ka akanta mtswww." Ya karashe yana mai jan dogon tsaki.


  "Point of correction.... Zainab bata ce bata so na ba" ya faɗa yana murmushi.

Auwal ji yayi kamar ya kai masu bugu "Enough Dan Allah idan ka cigaba da maganar ƴar iskar Yarinyar nan tabbas zan iya fasa maka baki, ya Maganar zuwan ka saudi ka gama komai ne ko kuwa?"

"Eh na gama komai ,jira nake idan muka je gidan su Zainab sai na sa ranar tafiya,amma Dan Allah na roke ka kar ka kuma kiranta da ƴar iska zuciya ta baza ta iya ɗauka ba" ya faɗa haɗe da haɗa hannu wuri guda alamun roko.

Baki a buɗe yake kallon sa haɗe da faɗin "eh lallai na yarda na kuma amince da kalmar da ake faɗin cewar so makaho ne wato love is blind, Allah ya taro Ka ya kuma baka lafiya"

"Ba Amin ba,in dai akan Zainab ne"

"Idan na fahimce ka zaka fa iya auren ta kuma ka zauna da ita ko?"

"Tsaf ma kuwa, idan har zata amince da hakan" ya amsa yana kallon cikin idon sa

"Amma kuma ka faɗa wa maama ka fasa auren"

"Na faɗa ne kawai ba ka ji irin maganganun da take a kanta bane?" 

 "Gara kai.....Ni yunwa nake ji" ya nufi inda aka jera food flask daga gefen ɗakin. bakin gadon ya dawo ya zauna haɗe da mika masa spoon shima yana rike da ɗaya, kwanciyar sa yayi yana kallon saman ɗakin yace "Na koshi" 

"Toh ai hikenan ya ƙara yawa" Auwal ya faɗa yana mai Bismillah ya fara cin abinci sa hankalin sa kwance.


Zainab

Kwance take a ɗakinta tana huta gajiya sabida jiya suka dawo da Alhaji Yusuf duk a gajiye take, tana latse latse a wayar ta ta shiga nan ta fita chan,tana tsaka da haka ne call ɗin Nussy ya shigo ɗagowa tayi da faɗin "Hello mutuniyar yane?"

 "Lafiya lau,kina gida ne?" Nussy ta tambaya.

 "Eh ina nan akwai labari ne?"

"Eh to kusan hakan ,zan zo ne akwai inda anke so muje"

  "Okay to ba damuwa sai kin zo ɗin" a tare suka kashe wayar.


Nusaiba

ɗakin Umma ta nufa akan sallaya ta tarar da ita da alama ta idar da sallah ne , har ƙasa ta durkusa ta gaida ta cike da sakin fuska ta amsa sabida kwana biyu ba tayi rashin jin da ta saba ba, kuma yanzu babu inda take zuwa kullum tana gida.

"Lafiya kuwa auta kamar da magana a bakin ki?" Umma ta tambaya ganin Nussy na ta rarraba idanu.

"Lafiya lau umma dama na zo ne na nemi izinin ki, jiya ne Zainab ta ƙira Ni cewar jikin baba ya tashi shine nake so naje na duba shi."

"Allah sarki bawan Allah nan na shan wahala, Allah ya bashi lafiya" ta amsa da Amin.

"Amma Nusaiba da yamman nan zaki je? Baza ki bari sai da safe kije ba?"

"Jiyan da ta ƙira Ni kuka take sosai wallahi , kuma kinga idan nace zan bari sai gobe abin baiyi yi ba"

"Eh to kuma hakane , shikenan ki je amma kar ki daɗe idan kuma kika je kika zauna kin san sauran da Ahmad zan haɗa ki ya Chasa min ke na kuma taya shi kin san zan aikata"

"Insha Allah bazan jima ba zan dawo, idan ma da wani abin zan ƙira na sanar da ke"

"Da dai kin taimakawa kan ki, idan kinje ki haɗa Ni da Maman Zainab ɗin kan na zo na duba shi,ki kuma gaishe shi da jiki"

Mikewa tayi tana murmushi "Tohm insha Allah.....Bari naje na shirya"

Ta fice da sauri, ɗakin ta ta shiga ta shirya a gurguje hijabi dogo har ƙasa tasa golden color tayi kyau sosai kamar ba ita ba, har ɗakin umma ta shiga tace mata ta shirya, a dawo lafiya ta mata ta fice daga gidan.


  


  Adaidaita ta hau kai tsaye ya Kaita gidan su zainab, kwankwasa gate ɗin tayi mai gadi ya ɗan buɗe kofar yana tambayar waye, bata ce dashi ƙala ba yana ganin ta ya gane ta sabida ya shaida fuskar nata,wangale mata gate ɗin yayi ta kusa kai ko amsa sannun da yake mata bata yi ba "Hegiya da ƙafa kamar na sauro yara ƙanana sai rawar kai da rashin ji Allah ya kyauta" ya faɗa yana kwaikwayon tafiyar da Nussy ke yi, wurin zaman sa ya nufa haɗe da ɗaukar Radio sa yana jin gidan Radio yana aswaki.


  Da sallama ta shiga parlor ganin babu kowa ne hakan ya sa ta wuce ɗakin Zainab ɗin ,sallama tayi haɗe da kusa kai cikin ɗakin, a gaban mirror ta hango ta tsaye , ƙirjin ta ɗaure yake da towel da alama da ga wanka ta fito .

"Amma wallahi kin san kan tsiya ,don wulakanci wai tun ɗazun nan baki gama shiryawa ba har na zo?"

Ta faɗa tana mai zama a bakin gadon dake ɗakin.

"Amma dai ke ba makauniya bace ko? Kina dai ga abinda nake yi" tana kallon ta ta cikin mirror, wayar ta ta zaro ta duba lokaci tace "Ko da yake ma da sauran time so na ke sai magriba zamu fita.

Ɗan waigowa Zainab tayi tace "Wai ina zumu je ne?" Ta faɗa tana shafa mai a hannun ta.

"Club zamu je"

Waro idanu Zainab tayi ta ma bar shafa mai da take ɗin tace "Club kuma dai? Me kuma Zamuyi a club gaskiya ba zani ba"

"Mtsww kina da matsala zee, nayi tunanin kin wuce nan duba ga yadda yanzu kin zama ƴar gari babbar yarinya amma kina abu kamar wacce bata waye ba haba dan Allah, ashe da sauran ki"

"Ban gane da sauran ba?Club fa kikace inda ake rawa ana Shaye Shaye a bugu ke kanki kinsan ba na yin ɗaya daga ciki"

" Ni fa ba cewa nayi ki ce kiyi rawa ko kiyi Shaye Shaye ba , bana son zuwa ni ɗayane ,besides haka zaki zauna ne daga gida sai Alhaji Yusuf ya nemi ki?"


"Ki bari Nussy nifa na ma fara gajiya da mutumin nan,mutum kamar maye jiya jiyan nan fa muka dawo daga Lagos kar kiso kiga yanda yayi min pata pata, bai bar Ni na rintsa ba ƙasa na zafi yake min sabida nacin sa tun da na dawo nake ta barci kamar wata jaka"


Dariya Nussy tayi tace "Sannu don baki samu sabon jini bane da wallahi babu wahalar da zaki sha sai daɗi, kinga abinda baki sani ba ina fa sane na haɗa ki dashi sabida nasan zai sake miki chamama kiyi clean ki wanku Kinga ma sai ya shammace Ni ya sayi miki gida da mota, abu ɗaya ne ya rage miki yanzu dole ki samu saurayi ko ince samari masu sabon jini, suna kashe miki kuɗi suna kuma kashe miki sha'awar ki Alhaji Yusuf kuma na daga gefe yana cika miki account"


   Murmushi Zee tayi "Allah ƙawata?"

"Allah kuwa Ni ɗin wasa ne aka gaya miki?"

 Mikewa Zee tayi ta nufi inda take suka tafa suna shewa, walldrope ɗinta ta nufa ta zaro wata abaya Sky blue an masa ado da red stones ba ƙaramin kyau yayi ba ,Nussy tace "Me wannan a hannun ki?"

"Kamar ya? Kayan da zan saka mana ko tsirara ake zuwa ne?"

"Club fa nace miki zamu ba walima ba da zaki wani ɗauko wannan rigar kice zaki sa" fizge rigar tayi haɗe da wugarwa a ƙasa , walldrope ɗin ta buɗe daga gefe ta hango jerin ƙananun ƙaya, hannu tasa ta na duba wa ɗaya bayan ɗaya, nan ta zaro wata arniyar riga da wandon, jeans ne wanda ake ƙira da crazy an yayyaga jikin sa ta gaba kamar tsumma baki ,rigar kuma wata shegiyar rigace pink sai sheki take tana kyalli gaban dai da mutunci bayan kuma babu komai sai ƴar igiya guda uku da aka ɗan ɗaure shi da igiyar.

Miƙa mata tayi "Wannan zaki sa" kallon ta take cike da mamaki

"Bana son iskanci Nussy ki saka hijab har ƙasa Ni ki bani ɗan iskan kayan na nasa baki? Ba ki da hankali"

Tana hararar ta.


Cire hijabin Nussy tayi baki a buɗe Zee ke kallon kayan jikin nata, wando da riga ce a jikin ta wandon Royal blue shi ba guntu ba ,ba dogo ba kuma ba 3 Quarter ba gashi nan dai, sai kuma riga Yellow an ɗan tsaga hanun hakan nan bai rufe mata cibiya ba, kan nan nata ya sha gyara sai ƙamshi yake baki ƙirin ta kama shi da ribbon shima yellow tayi kyau sosai kamar ƴar baby.


"Shegiya ƙawata..."faɗin Zee "duk yadda nake tunani kin wuce nan, kan uba amma ya akayi ki ka fito a haka? Umma bata ganki bane? Sannan maganar da kike cewar sai magriba zamu fita ya zakiyi da Umma daa Yaya Ahmad? Yaushe zaki koma gida?"

"Wani gida kuma ana zaune ƙalau ? Idan fa abin yayi yanda nake so ƙila a chan zamu kwana, Umma kuma na sata a kwana ce mata nayi baba ba lafiya kuna asibiti, sannan ma tace na haɗa ta da mama su gaisa."

 "A gaishe ki Nussy, sai ki hanzarta ki sami maman ki haɗa su."

 "Yanzu kuwa" ta faɗa ta miƙa mata kayan, sai da ta mayar da hijab ɗinta kana ta fice daga ɗakin, kofar ɗakin ta nufa bata kai ga karasa wa ba tsinkayi Muryar mama na faɗin "A a Su Nusaiba ne a gidan namu?" Mama ta faɗa da fitowar ta kenan daga kicin hannun ta rike yake da plate,Waigowa Nussy tayi ta fara takowa ta dawo parlon "Eh wallahi mama Ni ce"

"Yaushe kika shigo banji shigowar ki ba?" Ta zauna haɗe da ajiye plate ɗin pepper soup na Kaji da ta riko hannun ta

"Na shigo ba kowa a parlor shine na shige ciki"

Ta faɗa tana mai zama akan sofa dake kusa da mama.

"Ina wuni mama?"

"Lafiya lau Nusaiba ya cikin gidan naku?"

"Lafiya lau ta ma ce na gaishe ki"

"Ina amsawa" ta faɗa haɗe da kai cinyar kaza bakin ta tana yaga.

 Ɗan muskutawa Nussy ta yi tace "Mama da ma wata alfarma nake nema a wurin ki"

Baki nan a cike ta kuma kai wani loman "ina sauraron ki" da ƙyar take maganar.


 Sosa kai ta shiga yi cike da fargaba ta soma faɗin "Da ma so nake na haɗa ki da umma ta kuyi Magana na mata ƙaryar cewar baba bayi da lafiya kuma fita Zamuyi da Zainab kuma baza mu dawo da wuri ba, ta kuma ce na haɗa ku shine nake so ki tare min dan Allah in ba damuwa" tunda ta fara maganar mama ke kallon bakin ta har ta dire..


*🆕RELEASE🔰*




  ```FT5```


    2️⃣0️⃣2️⃣3️⃣






💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼 *hohoho Allah ya kawo mu qarshen shekara tazo😍, masu iya magana suka ce mai laya kiyayi mai zamani🤸🏼‍♀️, wani kaya sai amale🏇🏼, in kaji ana a marmatsa to giwa ce ta iso🥳,haka in kaji kira ba banza ba🤩...Ina ku ke masoya, ma'abota karatun littafan hausa, kuma masoya littafanmu🥰, Hajiyoyi kun karanta waɗannan littafan ba?, LULLUƁIN BIRI, MUGUN NUFI, CAPTAIN FAWZAN, MATAR UBA, SUNE SILA....To ya ku ka ji salon dukka labaran?😍, sun ƙayatar ba?, sun tafi da ruhika ba😅?, to fa ai su ɗin duk ba komai ba ne, somun taɓi ne cikin shirin da muka yi na nishaɗatar da ku a sabbin labarai masu jan hankali🥰ku shirya kawai ku biyo mu cikin tafiyar TEAM FITATTU BIYAR, salon labaran da suke daban da saura, labarai masu tarin darasi, ma'ana da kuma tsuma zuciyar me karantawa da sauraro😍...LITTAFAI BIYAR A ALƘALUMA BIYAR CIKIN MAFARKI ƊAYA😍...Hajjiyoyi da Alhazawa da kuɗi ƙalilan za ku mallaki littafan da baza kuyi danasani da nadamar siya da karantawa ba💃🏼, akwai tarin ilimi aciki🫶🏼, akwai nishaɗi😹, wa'azantarwa🌝ga uwa uba ƙayatacciyar soyayya mai saka jiki kyarma saboda tsantsar shauqi😍...*






*LITTAFAN SUNE KAMAN HAKA👇🏻*




1- *ƘAYAR RUWA na Halimahz*


2- *FARGAR JAJI na Aisha Abdullahi Yabo*


3- *WASA DA RAI na Fadeela Yakubu Milhat*


4- *LOKACI NE na Fatima Oum Mumtaz*


5- *KWANTAN ƁAUNA na Nana Haleema*




_LITTAFI ƊAYA:- ₦500_


_LITTAFI BIYU:- ₦800_


_LITTAFI UKU:- ₦900_


_LITTAFI HUDU:- ₦1000_


_LITTAFI BIYAR:- ₦1200_


_VIP 2k._




Za ku biya kuɗi ta wannan account...


*6314170140*


*FIDELITY BANK*


*SA'ADIYYA ZAKARIYYA HARUNA*




sai ku tura da shaidar biya tare da sunan littafin da kuke biɗa a wannan number....*Oum Mumtaz(***)*




katin waya zaku tura hoton MTN da sunan littafin ta wannan number...*Milhat(***)*






*ƳAN NIGER KU TURA DA KUƊINKU TA Mkoudi 89356025 airtel, SANNAN KU TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBA...Aisha Yabo(***).*




_LITTAFI ƊAYA:- 350f_


_LITTAFI BIYU:- 600f_


_LITTAFI UKU:- 650f_


_LITTAFI HUƊU:- 750f_


_LITTAFI BIYAR:- 850f_






```ƳAN KASUWAN DA ZA'A TALLATA MAKU HAJOJINKU DOMIN KASUWANCINKU YA ZAGA IN DA BAKU YI ZATO BA, TALLAN YA KASU KASHI-KASHI:-```




*_TALLA A KOWANNE PAGE NA BOOK 500, 5pages2k, Complete Book 10k._*


*_•TALLA A VEDIO NA YOUTUBE 1500_*


*_•TICTOK 1500_*


*_•INSTGRAM 1500_*


*_•FACEBOOK 1500_*


*_•WHATSAPP STATUS; 24hrs500, 48hrs1k, 72hrs1500, 168hrs3500._*




```ku tura da kuɗin ta account numbern da ke sama sannan ku tura da shaidar biya haɗe da details na abin da kuke so a muku talla akai ta wannan lambar...NanaHaleema(***.)```




*Youtubers da suke son mallakar littafanmu domin ɗorawa a channel sai kuyi magana a wannan lamba...Halimahz(***).*






MUNA MARHABAN DA KOWA CIKIN MUTUNTAWA, A ISO LAFIYA🤩




*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga duk wanda ya siya littafin Fitattu Biyar...son so fisabilillah😍*


__________

Milhart ce 

Yar Terawa


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.