Free chapter · Read without an account
Page 1
*NAAZNEEN❤🔥 <1>*
EXQUISITELY BEAUTIFUL
D'an Kuka.........!
Top-Notch
Season 3
بسم الله الرحمن الرحيم
This article is a fictional story, it is not made to insult anyone or any other, it is not made to abuse a community or religion, it is written under the guidance of research and the author's guess, it is wrong to turn the story in any way without asking permission, not a writer, this is against the law of self-ownership, in the law section, it can face a severe punishment or the option of paying a fine.
Exorcist
Catholic church Enugu.
"In the name of father, the son, the holy spirit and virgin Mary lead us to not into temptation, but deliver us. From evil"
"Hhhhhhh! Father Christopher."
Ta kalle shi tana dariya me d'aga hankalin da wani irin bala'in iska, baki daya church din ya kaure da mugun duhu wanda ko tafi hannunka baka iya gani, wani tsoro ne ya kama wasu daga cikin malaman Catholic church din musamman masu aikin cire evil spirits, kafin su fahimci wani abu, an shiga buga su da kasa, suna wani irin azababben ihu.
"In the name of Jesus Christ, I command you." Dariya ta kuma kyalkyalawa ta ce mishi.
"Ba zaka iya kome ba, ba zaka tab'a rabani da jikin Amanda ba, ba zan tafi ko ina ba. Am the only angel of guardians, she can't live without me! I'm like breathing in her body. Ba zan taba fita ba, amma zan muku abin da. Ba zaku manta ba."
Aka faɗa ana tsinke chain din da aka daurawa me maganar.
"Saint Michael the archangel defend us in battle. May you cast out Satan and evil spirits who roam the world to curse souls!" Kusan abin da suke nanawata kenan, amma ina watsar da chain din aka yi,. Gaba daya dakin Ibadar yayi duhu.
"Ka gama ihunka, ba zan fita ba, amma zan gaya maka wani abu ko garin nan zaku hada ba xan tab'a barin jikin Amanda ba. Sun yi laifi wanda ita zata dauki zunubansu. " Ɗif aka yi shiru, haske church din yayi, malaman Catholic din suna gefe cure da juna, wani dattijo tsaye rike da bible Idanunshi rufe yana jan crossing. Yarinya ce a gabansu wacce bata wuce shekaru tara ba, rike da chain ta murde shi a hannunta. Kafin su ankara ta shiga zane su da chain din tana faɗin. "Kunyi karya, ba zaku iya min kome ba!"
"Wayyo Father Matthew ka taimaka mana zasu kashe mu." Inji Malaman.
Bude idanu yarinyar ta juya kanshi, a fusace tare da kai mishi bulala, wani azzababen ihu da rawa jikinshi yake. Ta kuwa cigaba da zanesu. Bude kofar shiga church din, wata mata tayi kanta daure da dankwali, "No....no Amanda don do this for me!" Ta fada tana diba a guje, taje tasha gabanta, lokacin Father Matthew yana cin uban duka, domin ya hadu da jagwal. Zubewa tayi a gabanta. Ta fashe da kuka,
"Please don do please, I beg you for the sake of son of God!" Ta faɗa tana hada hannunta wuri guda. Sake chain din tayi tana fadin.
"Nne!" Ta taka jikinta, da sauri ta bude mata hannun. "Don let her hug she is evil demon!" Da sauri yarinyar ta fada jikin Uwar, tana me bude idanunta, ta kalli father Matthew. "You can't change the destiny!" Ta faɗa tare da kura mishi idanunta. Wanda suke kore me had'e da wuta wuta, fasa ihu yayi yana burgima shi yasan azabar da yake ciki, "Mu dai ki fita mana da yarinyarki a church!" Ya faɗa yana kallon yadda baki daya cross na cikin church din ya juyasu upside down.
Bai san lokacin da ya zube a gaban babban gunkin virgin Mary ya fara addu'a ba.
" I cut the ties between your inner demon and outer demon. May the holy spirit cast you into the abyss, let all evil spirits be cast into hell"
Samun tsakiyar bayanshi aka yi, aka sakar mishi dundu, tare da kara make kanshi. Ya tintsira can, ba shi daya ba, hatta sauran malaman binsu aka yi da mugun rankwashe sai da Father Andrew ya saki fitsari, tare da fashewa da kuka.
"Nne take me out zasu kashe ni." Ta faɗa a daidai kunnen Uwar, cikin matuƙar gajiya, da son lallai ta kawo karshen matsalar diyarta ta juya a hankali, ta goyata. Suka fita daga church ɗin. Kamar dama jira ake su fita. A cigaba da zane malaman tare da basu wahala, musamman father Christopher da yake finsu zakewa, mari kawai ake sake musu.
★★★
Garin Bauchi.
Unguwar Jajja, daddaden unguwa ce a cikin garin Bauchi, domin tana cikin gari, bata yi waje da garu ba, sannan akwai manyan mutane a unguwar, masu karfi da ma'aikatan gwamnati, sannan yan kasuwa tare da babban gidan Malami Alhaji Sani Jajja, wanda ake kira Malam Malami Jajja.
Dattijon da yayi kaurin suna a koyarwa da tafsirin Alkur'ani mai girma, babban Malamin da yake da tarin almajirai kamar me a cikin unguwar domin manyan gidaje hudu gare shi na kwanan almajirai.
Banda taimako da yake bawa mutane, hatta yan siyasa ba karamin cin gajiyarshi suke ba.
Babban gidanshi me dauke da mata hudu rus, kuma kowacce ta zuba Yara kamar meye. Sannan wanin abin burgewa Malam Malami Jajja Yaranshi maza da mata suna karatun Alqur'ani da na boko, kowacce yarinya zata gama secondry school, kafin ayi aurenta. Mazan kuma har jami'a suke yi, ya danganta da abinda kake so ne, idan baka son karatu zaka kama kasuwanci ko gona. Domin ya yarda da in baka nemi ilimi ba, ba makawa zaka yi kasuwanci.
Matan gidan Malam Malami Jajja, har yau da girma ya kama su, suna da mugun kishi, da kafkaf da Yaransu. Domin Allah ya bashi ikon gargad'an su, bai yarda wata mace ta sauka akan Hanyar da ya dace ba, ba zai hanasu kishi ba, amma ya zama dole a garesu. Kada yaji kada ya gani wata ta tab'a mishi yara da asiri domin zai iya mata abinda ba zata iya kwatar kanta ba. Haka ya haifar masu da zafin kishin juna.
Don haka suka rufawa kansu, asiri kada wani yasan meye yar wancan take ciki. Hajiya Innayo, ita ce uwargidan Malam, tun auren fari. Tana da yara biyar domin tana yin wabi ne.
*Dr Adamu Malami Jajja
Shine babban danta, kuma yana zaune a garin Abuja, yana aiki da iyalanshi.
*Ahmad Rufa'i Malami Jajja
Babban lecturer ne, a federal polytechnic Bauchi. Yana zama a tambari housing estate da iyalinsa.
*Nurse Uwani Malami Jajja
Tana aiki da asibitin specialize Bauchi wato bakas tana da Yaranta, suna sabon unguwar railway da Yaranta.
*Nura Malami Jajja
Soja ne yana nasarawa state da Matarshi da Yaranshi,
*Hawwa'u Malami Jajja
Suna kiranta da Yar Bauchi, domin ta kware a masa, kasancewar tana aikin girke-girke a government house Bauchi, sannan tana da babban gidan cin Abinci na ta na kanta, tana zaune a tudun salmanu da Yaranta.
Hajiya Umma matar da take bin Hajiya Innayo, mace me matukar mutuncin da hakuri sanin ya kamata, kawaici da dattako, babu ruwanta, da hayaniyar matan Malam, su suka sani tana da Yara uku.
*Abdullahi Malami Jajja.
Dan jarida ne, da yake aiki da babban gidan Radio BBC, yana can London da zama, da iyalanshi, tsakaninshi da Dr Adam wata shida, kusan sa'io'in juna ne, shi kan ya riga su aure, domin yana da shekaru goma sha tara aka mishi auren zumunta, kuma shi ne me Babban D'a a gidan.
*Usmanu Malami Jajja
Yana aiki a ministry of health, yana nan a Bauchi a nan jajjan, da matanshi da Yaranshi shima.
*Fatimah Malami Jajja
Tana koyarwa a FGGC Bauchi, tana zaune a Ibrahim bako, tana da Yaranta. Kusan sun dauko halin uwarsu.
Hajiya Goma, kai jama'a Hajiya Goma Allah ya daura mata munafunci, idan kana niman munafuka ka samu Hajiya Goma, a shafa fatiha a rufe da addu'a kana a kara da salatin Annabi, domin yadda Al'amarin zai wuce. Duk da ta tsufa, amma munafika ce na bugawa a jarida, ga hada husuma ta koma gefe tayi shiru. Tana da Yara bakwai da a gidan, uku sun mutu saura huɗu.
*Habibu Malami Jajja
Shine babban dahta, shi ne sa'an Usman, yana kasuwancin shi, a central market. Yana zaune a dutsen tanshi da matanshi.
*Hadiza Malami Jajja
Tana koyarwa a primary school din sale manga, tana da Yaranta, anan jajja take da zama.
*Aminu malami Jajja.
Dan union ne a tashar mass, yana zaune a cikin jajjan gidan Malam sannan yana noma, masanin sirrin noma ne. Allah ya bashi wannan baiwar.
*Jamilah Malami Jajja.
Ance kamar kumbo kamar kure, tana nan Allah bai bata haihuwa ba, tana sayar da abinci a cikin gidansu, domin kuwa halinta da ta gada a wurin Uwarta shi ya hanata zama a gidan aurenta, har kotu sai da aka kaita saboda munafunci da hada husuma.
Hajiya Lami.
Tana da zafi da fada, da kuma faɗar gaskiya ko zaka mutum, sannan itama Malama ce, tana aikin wa'azi idan za ayi suna ko biki, walima da sauransu Yaranta ne kananu, kuma Amaryan Malam Malami Jajja, wacce tayi nasarar sace zuciyar dan dattijo. Tana da Yara uku,
*Jamal Malami Jajja
Yana karatun master a Atbu, kwanan nan yayi aure
*Aisha Malami Jajja
Tana aure a jama'are, tana aure a gidan Sarkin jama'are, tana kasuwanci na fitar hankali, domin mijinta yana da rufin asirinshi, don ma Mahaifiyarshi ta hana shi tafiya da A'ishan ne.
*Balkisu Malami Jajja
Autar malam, kenan ga kyau ga ilimi kaf gidan ita ce ta dauko Malam a kyau da tsawo. Tana aure a Abuja, kuma tana karantar medicine,
Malam yayi kokari da koda ya baka auren Yarshi, sai ya gaya maka yarshi zata yi karatu, a cikin Yaranshi. Jamilah ce taki boko kamar me, shi yasa ya duba inda Allah ya dafa mata, ya bata kudi ta fara sana'ar abinci.
Hajiya Innayo da Hajiya Goma tafiyarsu daya, Hajiya Umma da Hajiya Lami, tafiyarsu daya. Idan ka cire Hajiya Lami da Hajiya Umma, Goma da Innayo kamar su kashe kansu don kishi. Wani irin azzababen kishi ake kowa boye na shi laifin yake..
Duk da wannan nasarar da suka samu, Malami bai tab'a yarda a saya mishi kome a cikin gidan shi ba. Hatta namar miya yana da dabbobinshi a cikin ɗaya gidanshi da yake kiwo. Malami ya yarda da kanshi, shi yasa duk wata buƙatarshi yake miƙawa Allah tare da tsayawa akan kome.
Idan akwai mutumin da yasan darajar rayuwa da mutane, Malam Malami Jajja ne. Bafulatani ne daga kasar Kamaru, yawon almajiranci da kasuwanci ya kawo shi Bauchi shi da danginshi da suke Rijiyar Malam. Kyakkyawan mutum ne wanda har yau kana ganinshi ka ga wanda zamanin samartakarshi an buga kyau. Wani abun da yake kara ja mishi kima a idanun mutane, mutum ne mai yawan sadaka, duk ranar juma'a ana sadaka a gidanshi.
Kuma wani abin da ba a cika samu a wurin Malaman tsangaya ba shine, yana daga cikin wadanda suke bawa almajirai damar karatun boko da na addini. Tun da ya zo Jajja ya kafa unguwa aka mishi lakabi da malami Jajja. Wato unguwar Jajja samanta kadan akwai wani unguwa da ake kiranta Unguwar Borno, dayawan mutane da tarihi suna faɗan cewa mutanen borno sun zauna kafin suka bar wurin, amma a asalin labarin unguwa yana cikin unguwar da Aljanu suka zauna.
Izuwa yanzu babu wani wanda zai baka labarin unguwar, ta can yamma da unguwa katon gulbi ne da ruwa yake taruwa, haka yasa dole unguwar ta zama matattarar Aljanu da miyagu.
Zuwan Malami Jajja, ya fatattake su aka kafa makarantar allo ana koyarwar ba dare ba rana, Malami Jajja. Mutane dayawa suna cewa yana tarayya da aljanu, mutanen boye shi yasa wani lokaci yake yawan sadaka da yanka, bayan nan duk inda aka samu matsalar Aljanu wurinshi ake zuwa. Domin aikinshi ne.
Koda yake ba iya aikin Aljanu yake ba, hatta matsalar maita, asiri, da tsafi..yana bada taimakonshi daidai yadda Allah ya sanar da shi, shi yasa gidanshi baya rabuwa da masu zuwa amsar addu'a da Magani. Har kwanan gobe yana bada magani da addu'a, sanna sadakar da zaka bada ƙalilan.
Sannan Yaranshi idan mazan, suna bada taimako na fitar hankali. Wani abu da mai karatu zai sani, Yaran Malami suna da dabi'ar son mata, mazansu basu zina amma fa duk inda suka ga mace matukar suna da interest akanta, sai sun nime ta. Haka Malam Malami shima yana son aure aure, kafin ya cike mata hudu yayi aure aure, sai dai matan basu zama ne domin mutum ne me tsananin bukatar gaske.
Sannan Yaranshi ma haka suke, har kowa yasan cewa haka halinsu yake na shegen son mata, matukar zasu ganki magana ya ƙare.
Kaf zuri'ar Malami jajja babu wanda ya dauke shi a kyau, da tsawo da haske. Har girmanshi, yellow ne shi, domin tsananin haskenshi dayawan mutane cewa suke ya haɗa iri da larabawa, murmushi kawai yake domin shi yasan shi me kyau ne, ko a gidansu na Kamaru ana kiran gidansu da Gidan kyawawa.
Basu da arziki fa, amma kuma akwai ilimi kamar me, amma kuma babu arzikin da za a bude baki ace shahararrun masu kudi ne, sai da akwai na rufin asirin da biyan buƙatar rayuwa, noma da kiwo ya rike shi gam. Sannan yana kara saka Yaranshi a kan lallai su nime ilimi. Bayan haka ya kara musu wani irin kusanci da junansu, suna son juna suna tausayin junansu. Kishin iyayensu bai shafe su ba. Domin har yau da yake da shekaru Tamanin da biyu, yana tsaye ne a kan kafarshi. Don tsabar tsawonshi har sai da yayi doro.
Idan ka cire Dr Adamu Malami wanda ya dauko tsawonshi. Amma kyau da farar fatar Malami, sauran yaran fatar iyayensu mata ne.
#Alhamdulillah, gabatarwar mu, kenan acikin labarin nazneen ban san me gobe zata haifar ba..... Amma... Labari ne me tab'a zuciya. Labari ne me cike da alhini da ban tausayi. Soyayya da sadaukarwa, ƙaddara me cike da kalubalen rayuwa.
Kudai kubiyoni acikin rikitattacen labarin Domin ganin salon da na ke dauke dashi🥰..... Ina fatar zakuzo ayi tafiyar nan tare da ku💃💃💃💃💃💃
Mai_Dambun
Marubuta🥰❤🔥