Free chapter · Read without an account

Page 2

by Fatima Adamu Fate · LOKACI NE

*LOKACI NE...!*

_Fitattu Biyar_


©️ *OUM MUMTAZ.*


  _No: 2_

_Free Page_


Ƙarfe goma da rabi na daren ranar Lawal ya shigo gidan bakin sa ɗauke da sallama, Umaima da take zaune tana kallon wani film da ake haskawa a tashar MBC2 sabida akwai nepa lokacin, ta ansa masa fuska sake tana masa sannu da zuwa, zama yayi a gefen ta ya ansa mata sannu da ta masa yace, "Kallo kike ba kiyi bacci ba?" 

"Eh wallahi, film ɗinnan nake son a ƙarasar, gashi kuma na jika shiru baka shigo ba nace Allah yasa lafiya." 

"Ina kofar gida tare da Yusuf shiyasa ban shigo da wuri ba,Babana yayi bacci kenan?" 

Ya tambaya yana leƙen fuskar Amir da yake bacci cikin gidan sauron sa na yara fankar ƙasa tana kai masa iska. 

"Yayi bacci amma fa sai da nasha rigima kasan halin mutumin naka ai."

"Gaskiya kam Amir akwai rigima, sai ke za ki iya da kayan ki."

Ya faɗa a sanda ya tashi ya shiga ɗaki hannun sa riƙe da wata bakar leda da Umaima bata san miye a ciki ba taci gaba da kallon ta. 

Tsawon mintuna ya ɗauka kamin ya fito, wanda fitowar tasa yayi dai-dai da sanda aka dauke wuta, yayi amfani da wayar dake hannun sa ya kunna torchi yana cema Umaima ta kashe sucket din TV, shi kuma ya shiga gidan sauro yabar mata tocilar wayar tasa kunne, sai da ta kashe sannan ta fita taje tayi wanka, ɗaki ta shiga ta shafe dik wani lungu da saƙon dake jikinta da wani daddadan khumra da Maimuna ta aiko mata jiya da bata taɓa amfani dashi ba. 

Riga da wando masu laushi da suka kasance na baccinta ta saka tare da hula mara nauyi ta fito da mahuci a hannu ta shiga gidan sauron ta danne musu. 

Kwanciya tsakiyar Lawal da Ameer tayi tana kallon Lawal da ya ke danna wayarsa yana game din maciji, wanda a lokacin wayar android bata shigo hannun mutane ba sai kananun waya,wanda shima sai an tona. Ƙamshin da Umaima yaji tana yi ne ya sa shi kallon inda take a hankali yace, "Wannan Kamshin turaren yayi min dadi sosai Umaima ta."

Yayi maganar a sanda yake janyo ta jikinsa yana shakar ƙamshin sabida ba ƙaramin daɗi yayi masa ba. 

Cikin kunnensa itama tace,  "Thank you Sweetie." A salon yadda yayi mata maganar. 

Hirar suka fara na soyayya dake cike da shauƙi, wanda Umaima tayi amfani da wannan damar wajen shigo masa da buƙatar ta. 

"Auren Hamidar yaushe ne?" Ya wurga mata tambaya a sanda fuskar sa ta fara ɗinkewa daga fara'a zuwa akasin ta, sabida shi fa yana ɗaya daga cikin mazan da wallahi ko da wasa basu da hannun kyautar kuɗi wa matan su ballantana kuma wasu yan gama gari, saboda yanda yake son ya zama cikakken mai kudi a rayuwarsa. 

A hankali tace, "Saura satu uku, bayan salla da sati biyu kenan." A ranta tana addu'ar Allah da daura ta akan sa ko da bazai bata duka ba. 

"To kinsan dai nima din ba wani kuɗi ne da ni ba, talaka ne dake fafutuka wajen ganin na samu na kaiwa bakin salati, dan haka magana ta Allah bazan iya baki naira dubu goma sha biyar kiyi kyauta dashi ba ni ina nan baki buɗe,amma gobe da safe idan Allah ya kaimu zan baki dubu biyar ki bayar Allah yasa mata albarka tinda dai kinsan,baki da gashin wane ba lallai ne kice sai kinyi irin kitson wace ba, suma kuma sun san baki dashi tinda ba sana'a kike ba."

Kallon sa tayi cikin duhun tana jin wani bakin ciki da takaicin maganar sa ta karshe, wai ita ba sana'a ba? Ko ya manta cewa shine ya hana ta sana'ar kan dalilin sa mara kan gado wai don kar mutane suyi tunanin ya gaza kula da iyalinsa har sai ta hada da sana'a? Sannan kuma idan shi ya manta ai ita bata manta ba, yanda ya kasa ya tsare a lokacin da ta fara sana'ar saida murhun gawayi da su kayan miya tana samun taron ta da kwabo yake bin dare yana kwashe mata su har sai da ta gaji tayi masa magana, shine ya fara borin kunya kan baza ta sake masa sana'ar kaskanci ba a gida tazo tana daura masa cewa ya daukar mata kuɗi, tin daga ranar yace wallahi koda bai sani ba idan ta sake ta kara yi masa wani abu da sunan sana'a cikin gidan nan a bakin auren ta, amma shine yanzu tsabagen ya raina mata wayo zai wani ce mata ita da ba sana'a take yi ba? 

Danne zuciyar ta tayi wajen ganin bata faɗa masa bakar magana ba gudun samun sabani da wannan daren da dik al'ummar gidan suke bacci tace, "Hakan ma na gode Allah amfana."

Jin abinda ta fada ne yasa shi sakin fuskarsa dake hade tinda aka fara maganar kuɗi da yayi tunanin zata matsa masa sai ya bata yace, "Amin-amin Umaima ta, shiyasa nake kaunar ki dayawa kina da saurin fahimta ta."

Bata ce masa ci kanka ba tayi addu'ar kwanciya bacci ta shafa tare da rufe idanunta, wanda hakan yasa shi shima yin addu'ar ba tare da ya damu da rashin amsawar ta a gare sa ba. 


****


Naira dubu biyar ya kirga ya bata, tare da naira dari biyu yace tayi kudin mashin zuwa da dawowa wajen kai kudin, bata nuna masa komai ba tasa hannu biyu ta karba tare da godiya sabida ita ai ko dubu biyar ɗin ba tayi tunanin zata samu daga gare sa ba sabida sanin hali. 

Wanka tayi bayan fitarsa ta ta shirya kanta da Amir ta rufe ƙofar kewayen nasu da kwaɗo a. 

Kaman yanda tayi tsammani zaune ta tarda Hauwa'u da Zainab matan Yayun Lawal suna zaune karkashin bishiyar da suke shan iska tsakar gidan har da ita idan bata da abin yi, ta tsaya suka gaisa tana tambayar yara suka tabbatar mata da sun tafi makaranta, sallama ta musu kan zata fita unguwa baza ta jima ba suka mata a dawo lafiya. 


****


"Yanzu ga 5k ya bani, bari ki gama aiki sai mu karasa gidan Aunty Halimar na bata sabida kinsan sha'anin kudi kar naje na kashe su nazo ina zare ido nasha caccaka a wajen Ammah."

Dariya Maimuna da take yankan cabbage tayi tace, "Wallahi fa da gaskiyarki ko ni kinsan idan naga idon kuɗi hannu na har ƙaiƙayin kashe su yake, idan banda su kuma nafi kowa shiga damuwa, zaki ga har wani ramar dole nake a tsaye." 

Dariya Umaima ta kyalkyale dashi jin abinda yar uwar tata ta fada, tace, "Kedai bari kawai amma fa kuɗi sunyi a rayuwa, inda ace kana da kudin ka yaushe zaka tsaya kana wani labe-labe kan a baka su ana daga maka hanci da baki dan kana auren mutum?" 

Maimuna da ta gama yanka cabbage din tana bude jikar ta karama dake ajiye kan kujerar parlon ta ba tare da ta baiwa Umaima amsar maganar da ta faɗa ba tace, "Ina da 20k a waje na, wanda Baban Kamila ya bani na bada nawa contribution ɗin, amma yanzu tinda 15k suka ce kowa zai bada ga wannan dubu biyar din, ki hada da dubu biyar ɗin da Baban Amir ya baki, kinga ya zama 10k kenan, sai ki bayar nima na mika nawa." Ta kare maganar a sanda take sanya mata dubu biyar din cikin hannun ta. 

Umaima dake jin zuciyarta cike da kaunar yar uwar tata dikda kowa uwarsa daban ne, amma ta tabbata ko cikin yan uwanta da suke daki daya babu wacce take mata ko kwatan abinda Maimunan take mata ta buɗi baki da niyyar godiya, amma sai Maimunan ta tari numfashin ta da sauri tace, "Dan Allah dan Annabi Umaima kar kimin godiya, nasha faɗa miki ba sau daya ba, ba sau biyu ba, idan kina min godiyar nan ji nake kaman wani bare can na tafi naje nayi ma alheri ba Ƴar uwata ta jini ba, wanda na tabbata idan da ace kece a matsayin inda nake za ki min abinda nake miki linkin ba linki, dan Allah idan dai godiya zakimin ki rike kayarki bana buƙata."

Da sauri Umaima ta rungume Maimuna hawaye na sauka a idon ta, zuciyarta ta cika da kaunarta da kuma fatan Allah ya bata abinda zata saka mata a rayuwa na irin halaccin ta a gareta tace, "Ina matuƙar ƙaunarki Ƴar uwata Allah ya barmin ke." 

"Nima ina kaunar ki sosai ƙanwata Allah ya barmu tare." 

Da sauri Umaima ta dago tana dariya a sanda take goge hawayen ta fuskar ta da murmushin tuno baya na yanda suke faɗa da Maimuna idan ta budi baki tace itace yayarta tace, "Wallahi nidai ban yadda ba ni ki daina cewa ke yayata ce, ai idan wani yaji kina fada sai yayi tunanin irin kin bani shekaru dinnan ne, nan kuwa ba a san kwata-kwata wata shida kika bani ba." 

Itama Maimunan dariya tayi, wanda da gangan dama ta kirata da ƙanwarta, sabida tasan sai ta tanka kasancewar ta mace mai tsananin son shekaru tin suna kanana ba su kai haka ba,k tace, "Amman dai kinsan ko kwana ɗaya na baki na girmeki ballantana har wata shida ko mata?"

Hira suka ci gaba da yi har Maimuna ta ƙarasa shiryawa, Umaima ta goyi Amir da tin fitowar su a gida bacci yake suka fita daga gidan bayan Maimuna ta bar ma yar aikin ta sallahun idan Kamila ta dawo daga makaranta taci abinci ta kai mata ita gidan yayarta Aunty Halima da ke gaba kadan da gidan Maimunan. 

Baifi tafiyar 6mins suka yi ba suka iso gidan, knocking suka yi mai gadi da buɗe ƙofar ya fito ganin wayanda ke knocking ya gaisar dasu sabida fahimtar da yayi kannen matar gidan ne ya basu hanya suka wuce bayan ya tabbatar musu da cewa tana nan a sanda suka tambaye sa. 

Babban gida ne mai kyau da tsari gidan Aunty Halima, wacce take auren wani attajiri mai kuɗi da za'a iya saka sa cikin layin masu kudin garin a sahu na huɗu cikin biyar,wanda yayi amfani da wannan damar ya sama mata aikin gwamnati bayan tayi degree ɗin ta, tana kuma daukan albashin ta mai kyau. Wanda take amfani da wannan damar wajen son ganin ta ƙasƙantar da na ƙasa da ita idan bai kaita arziki ba, bama kamar Umaima da kowa a gidan nasu yake jin haushin ta idan aka cire Maimuna, wanda kuma ba komai ne dalilin nasu ba sai dan ya kasance ita kaɗai ce a kaf yan matan gidan da ta auri miji mai ƙaramin ƙarfi, sai kuma tayi rashin dace da shi mijin da bai iya kashe ma mace kuɗi ba sai dan bazan nuna isa da iko.

Zaune suka same ta ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, hannun ta rike da remot tana baima yar aikin ta da take durkushe wajen ƙafafun ta umarnin abinda zata girka musu matsayin abincin rana kamin yaran ta su dawo daga makaranta. 

Fuska ta dan sake tana musu maraba, cike da girmama wa suka gaida ta da yake itace babbar yayar su a gidan da danta na farko ma Umaima wata biyu kawai ta basa. Kukan da Amir ya fara ne alamun ya farka yasa ta kun to shi a bayan ta tare da basa ruwan Faro da mai aikin Aunty Halimar ta kawo musu kamin yayi shiru. 

"Shi dai wannan dan bansan kukan banzan uban waye ya dauko ba, tinda mudai kaf gidan mu da zuri'armu babu rigimamme da yayi irin kukan sa, banki ma ace muna da masu taurin kai da suka fifita farin cikin su sama da na iyayensu." 

Umaima da ta fahimci inda maganar ta dosa ganin yanda Aunty Halimar take kallon ta a ɗaɗɗage sai ta dauke kai ba tare da tace mata ƙala ba, a ranta tana mamakin irin ƙiyayyar da Aunty Haliman ke mata sai kace ba uwarsu ɗaya ubansu ɗaya ba. Maimuna ce ta katse shirun da gurin ya dauka ta hanyar mika ma Aunty Halima dubu goma sha biyar tace, "Aunty ni ga nawa contribution din dama shi muka kawo miki." Ta kare maganar a ranta tana addu'ar Allah yasa kar tayi wata maganar kuma da zai bata ran Umaima idan taga nata kuɗin bai kai kaman yanda aka fada ba. 

Sakin fuska Aunty Halima tayi tana ƙirga kudin tace, "Kinga inda ake abin arziki ƙanwata, Allah dai ya raba mana zama da matsiya ta, ya kuma hada mu da waƴanda basu kadai ne zasu ke morar mu ba, idan kin koma gida kice ina gaida Baban Kamila sabida ni nasan wannan alherin daga gare sa ya ɓullo."

Sunkuyar da kai Maimuna tayi tana jin babu daɗi a ranta na ganin yanda yayar tasu take kokarin saka girmanta ta take a wajen su da zata iya haifar su. 

Umaima dake kokarin hadiye fushin ta wajen ganin ba ta maida ma Auntyn tasu magana ba tace, "Nima ga nawa nan iya abinda naga zan iya bayarwa kenan." 

Ba tare da ta jira jin abinda Aunty Halima zata sake fada ba ta saɓa Amir a kafaɗar ta, tana kallon Maimuna da itama take kallon ta tace, "To ni na wuce gida sai munyi waya" Sannan ta kalli Aunty Halima dake kirga kudin da ta bata tace, "Aunty sai anjima." Daga haka ta juya ta fice daga parlon ba tare da ta waiwaye su ba dik da kiran sunan ta Maimuna take yi ta jira tazo su tafi. 

A sanda take gama ficewa daga parlon ta tsinci muryar Aunty Halima na faɗin, "Harka dai da matsiyacin mutum bayyi ba a rayuwa, ni dama da gan-gan na yanke 15k dinnan sabida naga kamun ludayin ko wani dan iska, ni dama nasan babu wajen wacce za'a samu gibi a kuɗin nan sai wajen Um......" 

Da sauri ta fice daga parlon ba tare da ta tsaya jin karashen maganar ba idanun ta na cikowa da hawayen har ma bata ganin gaban ta mai kyau, wanda kamin ta karasa bakin kwalta ta tari mashin ta share hawayen dake mata sintiri a fuska yafi a kirga, a ranta take raya cewa da izinin Allah ita da sake zuwa gidan Aunty Halima insha Allahu tayi hannun riga kaman yanda ta yaye ma kanta zuwa gidan Aunty Asma'u.


*FITATTU BIYAR 2023 paid books:-*


1- *ƘAYAR RUWA na Halimahz*

2- *FARGAR JAJI na Aisha Abdullahi Yabo*

3- *WASA DA RAI na Fadeela Yakubu Milhat*

4- *LOKACI NE na Fatima Oum Mumtaz*

5- *KWANTAN ƁAUNA na Nana Haleema*


_LITTAFI ƊAYA:- ₦500_

_LITTAFI BIYU:- ₦800_

_LITTAFI UKU:- ₦900_

_LITTAFI HUDU:- ₦1000_

_LITTAFI BIYAR:- ₦1200_

_VIP 2k._


Za ku biya kuɗi ta wannan account...

*6314170140*

*FIDELITY BANK*

*SA'ADIYYA ZAKARIYYA HARUNA*


sai ku tura da shaidar biya tare da sunan littafin da kuke biɗa a wannan number....*Oum Mumtaz(***)*


katin waya zaku tura hoton MTN da sunan littafin ta wannan number...*Milhat(***)*



*ƳAN NIGER KU TURA DA KUƊINKU TA Mkoudi 89356025 airtel, SANNAN KU TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBA...Aisha Yabo(***).*


_LITTAFI ƊAYA:- 350f_

_LITTAFI BIYU:- 600f_

_LITTAFI UKU:- 650f_

_LITTAFI HUƊU:- 750f_

_LITTAFI BIYAR:- 850f_


```ƳAN KASUWAN DA ZA'A TALLATA MAKU HAJOJINKU DOMIN KASUWANCINKU YA ZAGA IN DA BAKU YI ZATO BA, TALLAN YA KASU KASHI-KASHI:-```


*_TALLA A KOWANNE PAGE NA BOOK 500, 5pages2k, Complete Book 10k._*

*_•TALLA A VEDIO NA YOUTUBE 1500_*

*_•TICTOK 1500_*

*_•INSTGRAM 1500_*

*_•FACEBOOK 1500_*

*_•WHATSAPP STATUS; 24hrs500, 48hrs1k, 72hrs1500, 168hrs3500._*


```ku tura da kuɗin ta account numbern da ke sama sannan ku tura da shaidar biya haɗe da details na abin da kuke so a muku talla akai ta wannan lambar...NanaHaleema(***.)```


*Youtubers da suke son mallakar littafanmu domin ɗorawa a channel sai kuyi magana a wannan lamba...Halimahz(***).*



MUNA MARHABAN DA KOWA CIKIN MUTUNTAWA, A ISO LAFIYA🤩


*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga duk wanda ya siya littafin Fitattu Biyar...son so fisabilillah😍*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.