Free chapter · Read without an account
Episode 7-8-9
*đź’žTRIPLET'Sđź’ž*
STAR 🌟 LADY..✍️
*đź’‹The beginningđź’‹*
Episode 7-8-9
đź’žđź’žđź’žđź’žđź’žđź’žđź’žđź’ž
*3 years back*
*Abuja*
*7:10 am*
Wata haÉ—aÉ—iyar Hajiya ce zaune saman sofa mai zaman mutun 2 cikin wani katafaren palo, palo ne mai girman gaske mai É—auke da sofa set manya manyan set biyu kowani set da kalan sa sai makekiyar Tv plasma dake manne a bango, daga gefe kusa da kyakkyawar staircase É—in haurawa sama table É—in cin abinci ne awajen mai bala'i kyau mai kujeru 8 daga wajen table É—in kofar kitchen mai girma gaske mai É—auke da duk wani abun da mace ke bukata a kitchen, ga manya manyan gas cooker guda biyu.
Sanye matar nan take cikin dan kareriyar Swiss lace pink color da ratsin baƙi, ɗin kin bubu gown ta sha kwalliya sosai, wuyar ta da hannun ta sanye da dankara dankaran gold tayi kyau sosai ta yi ɗaurin Zahra Buhari a kan ta da ganin ta kasan naira ta zauna mata sosai jikin ta jikin hutu yayi luwai luwai da shi gata fara tas kyakkyawa a jin farko, shiru ta zauna tana kallon News a makeken Tv plasma dake manne a bango, hankalin ta yayi nisa a kallon da take wani kyakkyawan Alajine ya sauko daga saman bene fari tas da shi kamar balarabe yana shirye cikin wata dakakkiyar shadda ash color kyakkyawa ne sosai yana da kwantatciyar saje da gemu bakin kirin ga gashin kan sa na fulani har wani curly yake yana nannaɗewa ya gangaro masa har gaban goshi ga wata kyakkyawar gashi da ta kewaye ɗan bakin sa tayi masa kamar raun ba karamin kyau hakan ta karawa face na shi ba, a hankali ya tako ya kariso cikin palon ya sanya hannu ta baya ya rufe idon hajiyar dake zaune sofa, cool murmushi ta sake har sai da fararen hakwaran ta suka bayyana ga wani siririyar wushirya a tsakanin hakwaran nata gwanin ban sha'awa cikin shagwaɓa tace "Barkama (sunan girmamawa ne na fulani) kayi latti ai to" murmushi ya saki wadda yasa dimple na shi lotsawa slowly ya zame hannun sa daga kan face nata tare da zagayowa ta gaban ta yana faɗin "bongel am (kyakkyawa ta) barka da tashi" murmushi tayi tana kokarin yin magana wata kyakkyawar yarinya chocolate color ta sauko daga saman benen da gudu, kyakkyawace ajin farko doguwa tana da dogon hanci har baka ga dara daran ido kamar ball farare tas kamar auduga idon nata design of fish ne san nan kuma sleeping eyes gare ta wadda idan ka ganta zakayi tunanin barci take ji amma ba barci bane gasu da girma idon kamar ball bakin ta ɗan karami launin pink lip nata na sama design of heart ne kanta ba ɗankwali curly hair ta ya nannaɗe kamar indomie ga gashin nata dark black sai kyalli yake kai kace an tsomashi cikin baby oil ne saboda curly da kyalli da yake gashin nata har gadon bayan ta duk da yana nannaɗe hakan bai hana shi kai mata tsaliyar bayan ta ba tana da dogayen gashin ido sosai kamar tasa eyelashes ga saje mai kyau dark black kwance a gefe da gefen kumatun ta tana sanye cikin wando skin tight baƙi da white T-shirt mai dauke da bajel ɗin makaranta kyakkyawan kafofin ta ba ta kalma, hannu ta na riƙe da wani katuwar teddy kamar jaririn mutun a shekaru ba zata wuce 10 years ba,
Da gudu ta sauko bene tana faɗin "Daddy kace wa Jehan ta kyaleni" tayi maganar cikin harshen shuwa arab ta kai karshen maganar tare da rungume sa, shafa curly hair ta yayi kafin yace "My Rimsha My siha where is your Abaya? Ko so kike muyi latti ne?" Girgiza masa kai tayi tana faɗin "Daddy this teddy is it not my own?" Tayi maganar sai da dimple nata irin na shi ta lotsa sosai, ta kai karshen maganar tare da ɗago masa teddy'n dake hannun ta tana nuna masa, yana kokarin yin magana Jehan ta sauko da gudu tana faɗin "I'm I playing with you? I'm I your mate?" A lokacin Jehan tana da 12 years, tana sanye cikin uniform riga me dogon hannu light blue se doguwar riga a saman ta dark blue mai hannu a kafada rigar ta tsaya a dai dai gwiwar ta se wandon uniform dark blue ƙafar ta sanye da Black socks ba takalmi a ƙafarta da gudu tayo kan daddy tana kokarin fisgo Rimsha, ihu Rimsha ta fasa tare da kanka me daddy tana faɗin "Daddy save me" fararen hannun sa yasa ya riƙo hannun Jehan yana faɗin "Haba Jehan yau fa Graduation ɗin My siha mai kuma ya haɗa ku faɗa a kan teddy kullun baku da aiki sai faɗa kan teddy ba kalan teddy da ban sawo na kawo gidan nan ba ni narasa meke damun ku" bai kai ga rufe baki ba mum ta miƙe ta amshe teddy tana faɗin "This teddy is for Rimsha whare is your own Jehan?" Turo baki Jehan tayi tana faɗin "Mum This is mine, is not for Rimsha" kallon mum daddy yayi san nan yace "bongel ɗauko min sauran kayan su yau ba ma zamu yi breakfast ba haka zamu wuce dan munyi latti, sayi breakfast ɗin a school ɗin na su ko idan mun dawo" ya kai karshen maganar tare da ruƙo hannun Rimsha ɗaya na Jehan ɗaya suka zauna saman sofa mai zaman mutun 3 yana kallon face na Rimsha, har cikin ransa yake bala'i son yaran nan nashi gashi Jehan ita ce mai kama da shi sai dai bata da dimple irin nashi ita kuma Rimsha da mum take kama sai kuma ta ɗauko dimple ɗin dad wushiryan mum, miƙewa mum tayi ta haye sama sauri sauri dan ɗauko musu sauran kayansu
Kallon daddy Rimsha tayi cikin harshen shuwa arab tace "Daddy ni zanzo first class In Sha Allah" murmushi daddy yayi ya sanya hannu yana tara mata curly hair ta da baya kitsuwa idan a ka mata kitso sai ya warware ga gashin nata da tsowo sosai a nannaÉ—e kamar indomie duk da naÉ—uwar sa kuma bai hana tsowon gashin nata bayyana ba dan a nannaÉ—en ma ya kai mata har tsakiyan baya "In Sha Allah my siha ke zaki zama first class" ya kai karshen maganar tare da É—aure mata gashin nata da kyar dan sai ya kamo sai su zame shi yasa ma bata cika É—aurewa ba dan ko ta sanya rebon fita yake shima daddy yanzu kulle mata yayi kamar igiya da gashin ya kullu, ita dai Jehan ko a jikin ta hankalin ta na kan Tv,
a tare mum da gwaggo suka sauko hannun mum riƙe da Abayar Rimsha Black colour da Hijab fari da takalmin ta da Black socks ita kuma Gwaggo na shirye cikin Abaya fari tas ta yafa gyalen abayar a kan ta idon ta sanye da glass ɗan siriri mai matukar kyau da tsada, hannun ta rike da Hijab ɗin Jehan light blue Dan Karami kalar T-shirt ɗin uniform ɗin, mum ta shirya Rimsha Gwaggo ta shirya Jehan
bayan mum ta gama shirya Rimsha ne ta ɗago ta kalli daddy tace "Yanzu Barkama da gaske kake ba zan biku ba?" Dogon hancin ta yaja yana faɗin "Duk abun da zai faru a School ɗin daga farkon har karshen zaki gani ki kunna TV kuma in muka dawo nayi alkawari zan biya" hararar wasa ta masa tana musu addu'a, riƙo hannun Rimsha yayi gwaggo kuma ta rinƙo hannun Jehan suka nufi hanyar fita daga palon "eyeeee My siha yau ba zuwa da jaka kenan" mum tafaɗa tana dariya, dariya ita ma Rimsha tayi kafin tace "Mum yau hutu za'ayi ai" komawa mum tayi ta zauna saman sofa tana faɗin "Allah ya bada Sa'a kuzo min da first class" a tare gwaggo da daddy suka amsa da Amin dai dai lokacin suka fice daga palon suka nufi parking space na gidan, da gudu wani ɗan sanda ya nufo su ya buɗe wa daddy da gwaggo kofar motar daddy kirar Roll-Royce boat Tail a tare suka shiga gidan baya daddy ya ɗaura Rimsha saman cinyar sa ita ma gwaggo ta ɗaura Jehan saman cinyar ta, ɗan sandan ya shiga ya tada motar yaja suka nufi gate, tun basu kariso wajen gate ɗin ba iliya mai gadi ya wangale musu tampatsetsen gate ɗin cikin kwarewa da iya tuki ɗan sandan nan ya danna hancin motar waje suka miƙi titi,
Cikin kankanin lokaci suka isa bakin katafaren gate É—in Great Heights Academy horn É—aya É—an sanda yayi mai gadin ya wangale musu gate É—in, É—an sandan ya kutsa motar sa cikin school É—in.
Makarantar cike take makil da jama'a ga manya manya baki da manya manyan yan siyasa da sarakuna sunzo taya yaran su murna masu kammala primary da jss 3 da ss 3 Rimsha na cikin wayan da za su kammala primary 6 na su tana cikin wayan da suka zana common entrance while Jehan na jss 2 yanzu, sai murna Rimsha take ita ma zata shiga secondary zata kamo Jehan.
Ɗan sanda na parking a parking space na school ɗin ya fito ya buɗewa daddy da gwaggo suka fito nan take manya manyan alhazawan dake tsaye a wajen suna jiran fitowar daddy suka kariso cikin murna da fara'a suka fara bashi hannu a kan su gaisa, kasan cewar shine babban bako a wajen hakan yasa director makarantar da sauran malamai suka kariso wajen da sauri dan tarban sa, cikin girmamawa director ya miƙawa daddy hannu yana faɗin "Barka da zuwa gaskiya munji daɗi da amsa gayyatar mu da kayi muna alfahari da hakan" murmushi daddy ya saki har sai da dimple na shi ta lotsa yace "Ai dole nazo ko dan siha ta" ya kai karshen maganar tare da shafa kan Rimsha cool murmushi ta saki har sai da dimple nata ya lotsa siririn open teeth dake tsakanin fafaren hakoran ta ya bayyana hakoranta fafare tas da su kamar gonan audiga, manya manyan Alhazawan dake wajen dukkan su Rimsha ta matikar burge su sosai. Malamar su Rimsha ce ta ƙaraso ta gaida daddy cikin girmamawa ta kama hannun Rimsha tana faɗin "let's go and get ready" a hankali ta lumshe sleeping eyes nata ta sake buɗe wa kafin tace "Bye daddy see you in the Hall" ta kai ƙarshe maganar tana yi masa bye bye da hannunta shima bye bye ɗin ya mata ita dai Jehan tun saukowar su ba ta jira kowa ba ta wuce wajen friends nata,
Director ne yace "sir please let's go in"
Kallon Gwaggo daddy yayi yace "Anty A'isha muje Koh"
a tare suka ranƙaya zuwa cikin katafaren hall ɗin dake cikin School ɗin a nan za'ayi taron ƴan jarida sunzo ɗaukar new gidan TV kala kala gaba ɗaya student na ciki kowa na zaune saman kujera an kawata hall ɗin sosai da kalar makarantar Dark blue da light blue an rubuta Sunan Makarantar da ballons dark blue da light blue idan nace zan tsaya zayyana muku haɗuwar da hall ɗin nan yayi to zamu kwana mu wuni bamu kammala ba kawai ku kawata shi a ran ku, hall ne mai girman gaske an cike sa da kujeru da student suka zazzauna, ta gaba kuma inda aka tanadar na ɗaliban da sukayi graduation ɗine, daga saman staircase wani ya opposite ɗin students ɗin, a ka shirya wasu haɗaɗu kujeru masu kyau sun kawatu iya kawatuwa ga wata doguwar table a gaban kujerun an jera drinks a sama da ruwan faro masu sanyi wadda daga ka gani kasan wajen baki na musamman ne daga tsakiyar kuren a kwai wata haɗaɗiyar kujera golden color an mata kwalliya sosai kamar kujerar sarauta daga gani kasan mutun na musamman a ka tana dawa,
manya manyan alhazawa da sarakuna ne zazzaune saman sauran kujerun da a ka jera layi sai wan nan ɗayan mai kama dana sarakuna shi da na kusa da shi ne babu kowa a kai, saman sa daddyn su Jehan yaje ya zauna ita kuma gwaggo ta zauna a kujerar kusa da na shi, nan take student suka miƙe suka fara kwasan gaisuwa daddy na amsa musu da fara'a a face na sa, duk school nan ba wanda bai san shi ba sai dai in new comer amma student ɗin school ɗin sun san shi dan mutun ne shi mai fara'a da kyauta gashi da son yara duk kuɗin da yake da shi, shi da kan sa yake kawo su Jehan school kuma ya dawo ya ɗauke su dan gani yake kamar idan ya bari driver ya kai su ba zai kula masa da su sosai ba, shi yasa ko abu suke so yake ɗaukan su suje shopping tare da shi komai aikin da yake zai ajiye yazo yayi attended nasu, yana bala'i kaunar su sosai,
Bayan sun gama kwasan gaisuwa ne suka koma suka zauna.
Mike director ya ɗauko ya sanya a saitin bakin sa ya fara magana cikin harshen turanci "Ina mai farincikin zuwan wan nan rana mai albarka Jehan Nawazudden Salman kizo ki buɗe mana taro da Addu'a" shiru hall ɗin yayi, gaba ɗaya manya manyan bakin da suka halakci taron sun zubawa Jehan ido wadda ta taso tana tafiya a nitse, a hankali ta tattaka saman staircase ɗin ta hauro sama taje ta tsaya kusa da director, miƙa mata mike ɗin director yayi ta ansa cikin kyakkyawa turancin ta da zazzakar voice nata mai sanyi da daɗi ta fara da yi musu sallama san nan ta fara jero addu'a "We take refuge with Allah, The Supreme and with His Noble Face, and His eternal authority from the accursed devil In the name of Allah, and prayers and peace be upon the Messenger of Allah O Allah, open the gates of Your mercy for us Amin" ta kai karshen Addu'ar tare da rufewa da Ayatul kursiyyu, sosai jama'a suka yi ta kabbara ciki hadda daddy da gwaggo sosai daddy yaji daɗi, ji yayi kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha,
bayan Jehan ta sauka ta koma mazaunin ta ne director yace a shigo da É—aliban da sukayi graduation É—in, a cikin layin suka shigo cikin tsarin suna sanye Cikin graduation gown kalar uniform É—in makarantar daga bayansu kuma malaman sune kowa fuskarsa cikin annashiwa da tsantsar farin ciki, kai tsaye inda aka tanadar domin su suka karasa sannan sukayi Anthem É—in makarantar aka basu iznin zama
Director ne fara kiran graduates É—in É—aya bayan É—aya sukazo su gabatar da kan su san nan suyi jawabi tare da nuna farincikin su sai suyi karatun al Qur'ani mai girma,
ba laifi yaran sun iya kira'a daddy ya kosa a kira Rimsha É—in sa haka ita ma gwaggo ta kosa taji karatun Rimsha, duk yarinyar da tazo a kace ta karanta Al Qur'ani mai girma bata wuce karanta sura daga nasi zuwa amma ko sabbi,
Rimsha itace yarinya ta goma da a ka kira cikin nitsuwa ta taso tana tafiya a nitse ta hauro saman wajen ta ansa mike ɗin da zazzakar voice nata ta fara da bilmillah san nan ta karanta suratul fatiha daddy yaji ba daɗi a tunanin sa a suratul fatiha zata tsaya sai yaji ta sake wata Bismillah ta fara karanta Suratul Baƙara,
shiru hall É—in yayi ba abun da ke tashi sai zazzakar voice É—in Rimsha dake tashi, gaba É—aya kowa ya nitsu tsit suna sauraron baiwar da Allah ya mata farincikin a wajen daddy da gwaggo ba'a magana,
hawaye Rimsha ta fara yi tana karatu ko da tazo In da Allah ke magana a kan itaciyar da ya hana Annabi Adam ci Annabi Adam yaci ta sanadiyar haka Allah ya fito da shi daga aljanna, sau uku tana mai mai ta ayoyin san nan ta ci gaba tana karatu tana kuka, tun muryan ta na fita sosai har ya fara sarkewa saboda kuka da take idan ta tuna girman Allah ta tuna mutuwa kwanciyar kabari gadar siraÉ—i hisabi sai ta kara fashe wa da kuka shi kan sa daddy sai da kwalla ta cika masa ido duk wani mai imani a wajen sai da idon sa ta kawo kwalla dan kukan da Rimsha ke yi tana rero kira'ar nan, masu saurin kuka kam ma tuni sun fara rera nasu kukan cikin harda Jehan,
da kyar Rimsha ta iya kai karshen suratul bakara tana kokarin durkushewa kasa a wajen daddy da ya kasa hakuri ya taso da sauri yazo ya rungume ta yana faɗin "It's okey my siha" cikin kuka tace "Daddy me mutun zaiyi a dunuyyar nan da ya wuce bautan Allah daddy mutuwa gaskiya ce kwanciyar kabari gaskiya ce gadar siraɗi gaskiya ce hisabi gaskiya ce haka zalika wuta da aljanna gaskiya ce daddy, duk wani rai sai ya ɗanɗani zafin mutuwa daddy, duk lokacin da na kalli kwayar idon ɗan Adam daddy ina kara jin tsoron Allah da ganin girman Allah a rayuwata dan idon ɗan adam ma kawai ya isa yasa bawa mai hankali ya kara jin tsoro Allah, duk lokacin da na tuna da mutuwa hisabi kwanciyar kabari gadar siraɗi wutar jahannama daddy ina shiga tashin hankali sai in ji gaba ɗaya duniya ta fitamin a rai na daddy, me ya rage bawa yake so bayan yayi bautar Allah dan ya samu ya tsira ranar gobe kiyama, daddy ban taɓa kwaciya barci na sawa rai na zan farka a duniya ba, ban taɓa lissafin me zai faru gobe na ba kullu lissafi na iya yau nake dan bana sawa rai na zan kai goben mutuwa gaskiya ce kuma tana ɗauka duk lokacin da kwanan mutun ya kare ba ruwan ta da abun da kake ko in da kake zata ɗauke kane kawai, daddy duk wani musulmi kamata yayi ya sawa ransa iya yau kaɗai garesa ba zai kai gobe ba dan ya samu damar aikata aikin Allah, daddy duk lokacin da na samu dama har tsawon kwana na ya kai nayi sallar issha, ji nake tamkar an sauke min wani katon dutse a kai na dan kullun ina cikin fargabar kada na mutu gab da wata sallar ko azahar ko la'asar kuma a ce ban samu damar yin wan nan sallar ba" ganin maganar da Rimsha take babban magana ne yasa director ya kawo mata mike ɗin sai tin bakin ta dan kowa yaji maganar nata, sosai hall ɗin gaba ɗaya suka ɗauka da kuka babban magana miƙewa manya manyan sarakuna irin su sarkin Zazzau Sarkin kano Gombe Bauci da dai sauransu suka yi, ba karamin tashin hankali magangun Rimsha ta jefasu ba yariya yar karama kamar wan nan amma tana da karfin imani har haka shi kan shi daddy yayi shocked da jin maganar Rimsha yasan dai tafi Jehan ilimin addini dan ita kullun tana tare da mum tana koya mata karatun addini ban da Jehan da a iya islamiyya kawai take ɗauka bai taɓa tunanin girman ilimin Rimsha ya kai haka ba, ba wanda bai yi mamaki da jinjinawa Rimsha ba ta girgiza gaba ɗaya hall ɗin ta karawa mutane da dama imani a ran su dayawa daga cikin wayan da suka halakci wajen sun kudurci niyar gyara ɗabiun su marasa kyau ta dalilin maganganun Rimsha, sosai suka shiga tashin hankali duk wanda ya manta da lahira yau sai da Rimsha ta tuna masa wani ma ji yayi kamar yaje ya sadakar da dukiyar sa dukka ya koma ga Allah yayi ta ibada,
da gudu Jehan ta miƙe ta hauro saman wajen ta rungumi Rimsha tana kuka tana faɗin "Kinyi gaskiya yar uwata duk abun da kika faɗa gaskiya ne amma jama'a da dama sun shagala da duniya sun manta da mutuwa da kwantatciyar kabari sun manta duhun kabari da siraɗi da hisabi idan ka dace ka shiga aljanna idan baka dace ba ka wuce wutar jahannama bayan ka gama ansan azabar kabari dana siraɗi ga tsayuwa kafin hisabi tsayuwar shekara ɗai ɗai har shekara dubu saba'in ga kuma rana a dai dai sai tin kan ku babu dare babu inuwa sai wan da yayi aikin Allah ne kaɗai zai shiga inuwar al'arshin Ubangiji Innalillahi wa inna ilaihir rajiun Allah mun tuba mun tuba ya Allah" sosai jama'a suka ciro wayoyin su suka rinƙa yi musu video ciki har da director.
Da kyar daddy ya iya rarrashin Rimsha sai da tayi shiru san nan ya riƙo hannun ta suka miƙe ya dubi director yace "Mu zamu wuce gida ba zamu iya jira a gama taro ba dan jikin siha ya fara zafi saboda kukan da tayi" ya kai karshen maganar tare da kallon gwaggo dake zaune saman nata kujerar tana goge kwallan dake idon ta yace "Aunty A'isha muje ko?" Da kyar gwaggo ta iya miƙewa dan gaba ɗaya Rimsha ta kashe mata jiki, gaba ɗaya manya manyan baki da sarakunan dake wajen suka miƙe dan raka su daddy zuwa wajen mota, sunyi sunyi a kan daddy ya bari suyi hoto da Rimsha amma yaki haka suka hakura ba dan sun so ba suka bar su Rimsha suka tafi ba tare da sun yi hoton ba, da haka taron ya watse dan dukkan su sun kasa gudanar da komai jikin su ya mutu da har da kayan kiɗa suka kawo amma jin zancen Rimsha yasa suka manta da wani kayan kiɗa da suka kawo, kowa ya wuce gida taro ya watse
đź’žđź’žđź’žđź’žđź’žđź’žđź’žđź’ž
KANO
Zaune jelly take saman mirror chair daddy na tsaye a kan ta yana ɗaure mata gashin kan ta da roba irin na kitson yara kasan cewar gashin nata yayi tsantsi sosai baya kitsowa sai dai a ɗadɗaure mata shi da roba, sai murmushi take fararen hakwaranta masu kyau suna jere kanana da su sai kyalli suke, shi ma daddy sai murmushi yake yace "My baby kinyi kyau over" kara murmushi tayi sosai a wan nan karon har fararen hakoran ta suka kara bayyana sosai "Daddy amma dai yaya Imran zai zo school na mu ko?" Tayi maganar cikin shagwaɓa "Eh my baby yace min zai zo In Sha Allah" tana kokarin sake yin magana daddy yace "Sauko na gama kuma surutun nan ya isa dan 07:00 am tayi yanzu taso na sanya miki uniform dan karmuyi late" make masa kafaɗa tayi cikin shagwaɓa tace "Daddy kai fa ka ɗaurani saman chair ɗin yanzu kuma kace na sauko da kai na ni ban iya ba" girgiza kai kawai yayi ya sanya hannu ya ɗagota cak suka nufi wajen gado dan bai son biye mata idan ya biye mata ba zasu wuce school da wuri ba,
saman gado ya É—aura ta san nan ya wuce ya É—auko mata uniform nata riga fari da wando blue sai É—an hijabi fari ya dawo ya sanya mata sharp sharp san nan ya É—auko perfume ya feshe ta da shi nan take ta fara zuba kamshi wuce wa yayi ya É—auki suit nasa da zai sanya ya shige toilet,
tana zaune har ya fito shirye cikin bakin suit da ya ɗauka ya dube ta yace "Let's go my baby" shiru ta masa kamar bata ji me yace ba, sake mai mai ta maganar yayi dai dai lokacin da yake ɗauko jakar computer sa nan ma sake masa shiru tayi kamar bata san da mutun a ɗakin ba, da sauri ya juyo dan yaga wai ko barci tayi ne ganin idon ta kar a kan sa ta turo baki kamar biro ne yasa ya dafe kan sa da hannun sa yana faɗin "Yanzu kuma menene? haba my baby zamu makarafa" kukan shagwaɓa ta sa masa tana faɗin "Ni daddy yanzu ka dai na sona baka ɗauka na sai kace na tafi da kafata" "Haba my baby yanzu fa 11 years kike da shi gaskiya kin min katuwa ba zan iya ɗaukan ki ba" sauka kasa tayi daga saman gadon ta kwanta a kasa ta fara birgima tana masa kuka girgiza kai yayi ya ratiyo jakar computer sa ya kariso wajen tare da sanya hannu ya ɗauke ta cak kamar yar baby suka nufi waje, ganin ya ɗauke ta yasa tayi shiru kamar an kashe gen.
Ko da suka fito palo su Zuwaira sun kammala shirya musu breakfast ga kuma basket na school É—in Jelly sun shirya mata abincin ta a ciki roban cool Yoghurt ne mai É—an girma da snacks a cikin wata kyakkyawar transparent roba sai pepper chicken a cikin foodflask, daddy bai tsaya yin breakfast ba dan time ya tafi basket na lunch nata kawai ya É—auka mata suka nufi waje lokacin 7:45 am yayi.
Suna fita harabar gidan wata dankareriyar mota kirar Mercedes-Benz ta danno hanci cikin gidan ihu jelly ta fasa mai rikita ƙwaƙwalwa tana faɗin "Daddy ka sauƙe Ni" ba musu ya sauƙe ta da gudu ta nufi motar zata runguma ba ruwan ta da tafi motar yake, saura kaɗan yabi ta kan ta dan irin shigar da tayiwa motar, a sukwane mamallakin motar ya taka birki, ba karamin tsorata daddy yayi ba ganin saura kaɗan motar ya take ta, ita ko, ko a jikin ta bata ma san me tayi ba da gudu ta karisa wajen marfin motar tana faɗin "Yaya Imran nayi kewar ka" gently a ka buɗe kofar motar a hankali ya zuro kyawawan kafafun sa dake sanye cikin cover shoe baƙi waje kafin ya fito gaba ɗaya, cikakken namiji ne chocolate color yana da dogon hanci da dara daran idon ga kyakkyawan saje kwance a face na shi kaman sa ɗaya da daddyn Jelly sai dai shi chocolate color ne sosai, yana sanye cikin dakakkiyar shadda fara tas da hula baki sai cover baki a kafar sa kyakkyawa ne a jin farko, da sauri Jelly ta faɗa jikin sa tare da sakin kukan shagwaɓa, ɗagata sama yayi yana faɗin "Rabin rai na nima ai nayi kewar ki yanzu dai a dai na min kukan haka ya isa kin san ban son kukan ki ko?" kwantar da kan ta tayi saman kafaɗar sa tana yar dariya kamar ba ita ke kuka yanzu ba, wucewa Imran yayi ɗauke da ita a jikin sa ya nufi daddy dake tsaye sai murmushi yake bakin sa yaki rufuwa yana bala'i kaunar Imran sosai,
Risinawa kasa Imran yayi ya gaida daddy, da fara'a daddy ya amsa yana murna "Daddy muje ko lokacin ya tafi" cewar Imran yayi maganar tare da ansan basket É—in Jelly dake hannun daddy,
a tare suka ranƙaya zuwa wajen motar Imran,
daddy ya shiga gidan gaba tare da ansan Jelly shi kuma Imran ya koma mazaunin driver ya zauna tare da yiwa motar key yana satar kallon face É—in Jelly yaja motar suka bar gidan suka nufi School É—in su Jelly
Share fisabilillah 👏
To masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai mu
đź’žStar Ladyđź’ž
*đź’žTRIPLET'đź’ž
*đź’žThe beginningđź’ž*
STAR 🌟 LADY..✍️
Episode 8
*KADUNA*
Zaune Abbi yake saman sofa a cikin palon sa ya buga uban tagumi yayi shiru, kallo É—aya zaka masa kasan yana cikin matsanancinyar damuwa, duk da sanyin Ac dake cikin palon hakan bai hana shi zufa ba, jikin sa sanye da jallabiya baki gaba É—aya a hargitse yake,
da sallama Irfan ya shigo cikin palon, Abbi yayi nisa cikin tunani bai ji sallamar da Irfan É—in yayi ba,
````Irfan````
Cikakken namiji ne yana da tsawo dai dai san nan yana da ɗan kiba kaɗan yana da faffaɗar kirjin ga hancin sa dogo har baka idon sa dai dai ne basu da girma sosai kuma ba kanana bane yana da ɗan karamin baki laɓɓan sa na sama brown color na kasa pink color kyakkyawa ne sosai fari tas da shi kamannin sa ɗaya da Umaisha sai dai shi fari ne a shekaru ba zai wuci 26 to 27 years ba sanye yake cikin shadda brown color ɗinkin half jomfa ba karamin kyau kayan suka masa ba kasan cewar fatar sa na da haske.
......Jiki ba kwari ya kariso cikin palon, ya shiga damuwa sosai ganin halin da Abbi ke ciki, kusa da shi Irfan yazo ya zauna ya ɗan taɓa shi yana faɗin "Abbi lafiya?" Yar firgigit Abbi yayi ya ɗago idon sa da suka sauya launi zuwa ja, dogon numfashi yaja tare da sauke wa a hankali,
"Abbi me yasa kake yawan sa kan ka cikin damuwa ne? Karfa wani ciwo ya kama mana kai" jinjina kai Abbi yayi murya a dashe yace "Irfan dole na shiga damuwa Alhaji Ma'azu ya cuce ni yaci amanar yarda" riƙo hannun sa Irfan yayi cike da tausayawa yace "Abbi ba komai Allah zai saka maka yanzu dai ina son ka dai na sawa ranka damuwa muyi hakuri muga me Allah zai yi" girgiza kai Abbi yayi kafin yace "A'a Irfan dole mu sai da Company nan, mu fara business da kuɗin dan kar muzo mu rasa na cin abinci" shiru Irfan yayi yana tunanin mugun ta da Aminin Abbin ya masa, duk wani abu mai amfani a company su na sarrafa shinkafa sai da ya kwashe cikin dabara, saboda yadda da shi da Abbi yayi yasa bai farga da wuri ba, har injuna da sauran kayan amfani bai bari ba Abbi yayi reported na shi a police station amma ba wani abun da ya samu sai ma kuɗin da ya rinƙa kashe wa kuma ba'a masa adalci ba saboda Alhaji mu'azu ya saye jami'an tsaron, Alhaji mu'azu ba abun da ya barwa Abbi a company sai kangon gini kawai duk wani abun da ya sace kuma sai da yaje ya musu takardun karya wadda zasu tabbatar da nashi ne,
"Irfan tashi muje muyi Sallah azahar lokaci yayi idan muka dawo sai kaje ka É—auko su Aafia a school" a lokacin Aafia na ss2 ta rubuta waec and neco yau suke graduation Abbi bai samu daman zuwa ba saboda damuwa da ta masa yawa shi kuma Irfan baya nan ya manta ya tafi wajen friend na shi a cikin Zaria City, Umaisha kuma tana ss1,
a lokacin Aafia na da 17 years Umaisha na da 15 years
"Amma Abbi me yasa ba zaka tambayi bappa Yaya ya baka kuɗi ba ko da bashi ne sai ka tayar da company namu" cewar Irfan yayi maganar yana kallon cikin idon Abbi "A'a Irfan ko na tambaye sa Hajiya Umaiya ba zata taɓa bari ya bani ba kasan halin ta shi kuma Abdul Malik yanzu haka yana cikin matsala ba zan iya tambanyar sa ba, na san idan na tambaye sa ko bai da shi zai nemomin bashi amma bana son sashi cikin damuwa in kara masa damuwa kan wadda yake ciki" waro ido waje Irfan yayi yana faɗin "Abbi Bappa maik ɗin ne yake cikin damuwa? To damuwar me kuma?" Gyara zama Abbi yayi san nan ya fara magana "Akoi wani abokin Takarar sa a fagen aiki su da ya sako sa a gaba a kan company sa *filman Nigeria limited* wai sai dai maik ya sai da masa da company kuma mutun ne mai haɗari sai barazana yake wa maik, kawai dan company maik yafi nasa sanuwa a duniya maik ya fisa farin jini shi yasa yake son dole dole sai ya tankwarar da maik yanzu haka a koi wani aiki da company maik dana abokin takarar nasa dana wasu su kayi applying, aikin gina wani katafaren asibiti ne a Villa to shi Alhaji Auwal ɗin yasan duk in da aiki ya fito kuma company maik ta nuna sha'awar sa a kan aiki to shi a ke bawa shine ya ɗaga masa hankali dan aikin babban aiki ne sosai duk company da tayi Sa'a ta samu aikin to zata samu makudan kuɗaɗe shiyasa ya sako maik a gaba da baraza a kan dole maik ya janye neman wan can aikin kuma ya sayar masa da company sa" kara waro ido waje Irfan yayi cike da damuwa yace "Abbi to me yasa daddyn jelly ɗin ba zai yi report na shi ba" girgiza kai Abbi yayi yana faɗin "No Irfan idan baka iya kama ɓarawo ba sai ɓarawo ya kama ka ai wan nan mutumi baka isa ka kai karan sa ba Alhaji Auwal ya wuce tunanin ka yana da wani ɗan iskan yaro mai suna Muneer wan nan yaron har gida yake zuwa yayi wa maik abun da yake so ba yadda maik zai yi da su, addu'a ita ce kaɗai zata raba su dan haka ka taya bappan ka da addu'a Allah ya raba shi da su, amma kuma Maik ɗin ya ce min ya turawa Nawazudden later a kan matsalar kuma na san in dai Nawazudden ya samu later nan to ba makawa zai taimaka wa Maik sosai dan shi ɗin mai yi ne yana da zuciya mai kyau kuma kaga yanzu sune gomnatin gaba ɗaya, In sha Allah zaɓe mai zuwa sai ya zama shugaban kasa dan yace tabbas zai tsaya takara ku tayasa da addu'a" dogon numfashi Irfan yaja tare da saukewa a hankali yace "Abbi duniyar yanzu mutane ba abun yarda bane yanzu dubi yadda kayiwa Alhaji mu'azu gata ka jawosa inuwa ya turaka rana ashe ba ma kai ka ɗai ba har da bappa maik ga kuma maman su Imran ta hana bappa Yaya taimakon ku ta raba zumunci ta rabamu da yan uwan mu gashi Bappa yaya yana da kuɗi na fitan hankali amma ta hana kowa yazo kusa da shi yanzu fa bappa yaya ma ina ga ya manta da ku gaba ɗaya a rayuwar sa nifa idan ba Imran ba ba wan da na sani a gidan shima Imran ɗin dan yana da son zumunci yana zuwa nan kuma muna waya da shi shiyasa amma ba dan hakan da shima ba zan san shi ba" ajiyar zuciya Abbi ya sauƙe san nan yace "Ba kai ka ɗai ba nima nan iya Imran kawai na sani ban san sauran yaran yaya ba amma naji daddy'n jalila yace ƴaƴan yaya uku ne bayan Imran a koi Akil da Akila amma ni ban san su ba ban taɓa ganin su ba ko shi maik ɗin ai sau ɗaya na taɓa kallon jalilan sa lokacin tana yar shekara biyu yanzu ko a hanya muka haɗu ba gane ta zan yi ba ni ma kuma bana jin maik ya san su Aafia kai kaɗai ya sani dan kai kaɗai ne mai zuwa wajen sa" cikin sauri Irfan yace "Ae, kuwa dole wan nan hutun na kai su Aafia wajen sa dan ya san su suma su san shi dan zumunci nima daga nan naga jelly dan rabon da na ganta tun tana da shekara 6 duk lokacin da zanje gidan tana School kuma ban taɓa kwana ba amma wan nan karon zan kira Imran ya zo mu haɗu a can gaba ɗaya muyiwa bappa koda 1 week ne muga juna su Aafia su ga jelly ita ma ta gansu nima kuma na ga su Akila ɗin dan zance Imran yasan yadda zai yi yazo da su" kakalo murmushi Abbi yayi kafin yace "Wallahi har kasa naji daɗi ba dan ina cikin wan nan matsalar ba ai da tare zamu tafi dan nima rabona da ganin maik wajen shekara 6 kenan yanzu sai dai muyi waya kawai" murmushi shi ma Irfan yayi yana faɗin "Abbi karka damu komai zai warware yanzu dai muje muyi Sallah gashi nan har an tada Kabbara"
A tare suka miƙe suka nufi waje suna yar hira suka nufi masallaci.
đź’žđź’žđź’žđź’žđź’žđź’žđź’žđź’ž
*ABUJA*
Da sallama É—auke a bakin daddy ya shigo palon da sauri Mum dake zaune tana kallon abun da ke faruwa a school É—in su Rimsha a Tv ta tashi ta nufo su tare da buÉ—e hannu ta rungumi Rimsha tana murmushi, rungumarta Rimsha tayi tana É—an murmushi ita ma "My Siha Allah ya miki albarka, Allah ya inganta min rayuwar ki Allah ya dafa muku gaba É—aya daga ke har babayn daddy" tayi maganar tare da jawo Jehan ta haÉ—e su ta rungume, sai murmushi daddy da gwaggo suke,
mum ta ɗan jima rungume da su tana zuba musu Addua'o'i daddy da gwaggo na amsawa kafin ta sake su ta riƙo hannun su suka haura saman bene dan taje tayi wa Rimsha wanka ita kuma Jehan tayiwa kan ta wanka, duk wan nan dukiya da Allah ya bawa daddy bai yarda da yar aiki ta kula masa da yara ba mum ɗin su ke musu komai dan gani yake ba wadda zata musu abun da ya dace kamar mum, ko itama mum ɗin wani lokaci idan tana musu wani abun zuwa yake ansa da kan sa ya musu sai yace bata musu yadda ya dace sai dai ta girgiza kai kawai tana masa dariya.
Wucewa shi ma daddy yayi ya haye sama dan yaje yayi wanka ya shirya yazo ya ci abinci ita ma gwaggo ta wuce nata bedroom É—in dan yin wanka ta huta.
After some hours
Mum na zaune saman sofa ita da daddy da gwaggo suna hira a palon, sai murmushi suke suna anna suwa da alama hiran na musu daÉ—i,
da gudu Jehan da Rimsha suka sauƙo suna rige rige zuba musu ido daddy yayi yana kallon ikon Allah ita kuwa mum da ta saba sai ta ɗaga ido ta kalli agogon dake manne a bangon palon ta saman Tv 2:30 pm dai dai girgiza kai kawai mum tayi tana faɗin "Bismillah" da sauri Rimsha ta ɗauke remote ɗin Tv ta canza tasha zuwa news, nan take murmushi ya bayyana a kan face nata ta koma saman sofa ta zauna tana faɗin "Allah na gode maka da kasa TGA ya yarda ya amsa wan nan gayyatar yauma dani za'a fara hira da shi kuma har a gama" tayi maganar cikin harshen larabci, bata gama rufe baki ba Jehan ta anshe remote ɗin ta canza tasha tana faɗin "Daga yau kin dai na kallon wan nan kafurin Krista a gidan nan" a kule Rimsha ta miƙe kamar zata yi kuka tace "Dan Allah Jehan ki bani remote nan wallahi yanzu fa TGA zai shigo kin hanani kallo a bedroom na hakura na dawo nan to dan Allah a nan karki hana ni ki bar ni na kalli jarumi na" kallon sama da kasa Jehan tayi mata kafin tace "eyee ina cewa ɗazun ba cimawa kika gama mana jawabi a school like good girl shine yanzu zaki zo ki fake da kallon wan nan kafurin da ma bai san da zaman ki a duniya ba, gaskiya ne wan nan magana do what I say don't do what what I do" su daddy dai sun zuba musu ido suna kallon ikon Allah "No Jehan wan nan abun da nake kallo ba hara mun bane a musulci kuma dan na faɗi magana a school hakan ba yana nufin ni bazan yi nishaɗi a rayuwa ta ba ko kuma wasu ba zasu yi nishaɗi a rayuwar su ba abun da nake nufi kar ku shagala da duniya ku manta da lahira kuma ai ni ban shagala da duniya ba kema sheda ce a kan hakan kiyiwa Allah ki bani remote ɗin nan" ta kai karshen maganar kamar zata yi kuka duk wan nan magana da suke cikin harshen larabci suke yin sa, a kule Jehan tace "Ba zaki sake kallon wan nan mummunar mutumin mai kama da zunubin a gidan nan ba" a fusace Rimsha ta wanke mata fuska da mari tare da sanya hannun ta ta fisge remote ɗin ta canza tasha ta mai da News, ta koma ta zauna saman sofa ta ci-gaba da kallon ta, cikin zafin nama da ɓacin rai Jehan tayi kanta da niyar dukan ta da sauri daddy ya miƙe ya ɗauki Jehan ɗin cak suka haura sama ihu ta fara yi masa tana wuntsilo kafofin ta,
Kallon Rinsha mum tayi cikin harshen shuwa arab da kakkausan murya ta fara magana "Daga yau idan kika sake marin sister ki Rimsha sai ranki ya ɓaci koma me ta miƙi ba muna zaune a wajen ba ai kin san ba zamu bari ta hana ki kallon ki ba zamu ansan miki, karki sake yin wan nan kuskure ko da sunan wasa kada ma ki sake tana magana kina bata amsa gaba take da ke, ki rinƙa mata biyayya kuma ki gama kallon idan daddyn ku ya rarrashe ta kije ki bata hakuri kina jina?" Cikin ladabi da biyayya tayi kasa da murya tace "Naji mum kiyi hakuri ba zan sake ba" har cikin ranta mum taji daɗi Rimsha yarinya mai biyayya ga hakuri kamar damo bata son yawan hayaniya,
A ɓangaren daddy kuwa kai tsaye bedroom na shi ya wuce da Jehan dake ta wuwwuntsilo masa kafofin ta sama tana masa ihu, saman katafaren gadon sa ya sauƙe ta san nan ya zauna gefen ta tare da ɗaure fuska ya fara magana cikin harshen turanci "Why Jehan you always look for troubles, amid you are a senior, you know Rimsha is patient, but you vividly push her to fight you at most?" Shiru tayi tana turo baki "As from Today kar na sake ganin kina neman Rimsha da faɗa kina ji na ko?" Gyaɗa masa kai tayi alamar eh ba tare da tayi magana ba.
Miƙewa Rimsha tayi zata bar palon mum tace "A'a Rimsha kin fasa kallon ne kuma?" Turo baki Rimsha tayi kamar za tayi kuka tace "Mum hankali na ya kasa kwanciya ne zanje na bawa Jehan hakuri sai na dawo na ci-gaba da kallon" "No my Rimsha zo kiyi zaman ki karki damu ki bari sai kun shiga ɗaki sai ki bata hakuri" ba musu Rimsha ta dawo ta zauna ta kafe Tv da dara daran sleeping eyes nata masu ɗaukan hankali,
sosai ta kafe Baturen dake magana a Tv da idon ta yana sanye da face mask a face na shi, farine tas yana sanye da kananan kaya sai jacket da ya ɗaura a saman kayan nasa kasan cewar sanyi dake wajen nasu, duk da rabin face nashi a rufe da face mask hakan ba zai hana ka gane kyakkyawa ne ajin farko ba yana da murɗaɗen jiki ga faffaɗar kirjin kamar wani zaki kirjin nasa a cike ɗamtsen hannun san nan kamar zasu fashe saboda training da yake, "Rimsha ni ko in da tambaya a kan wan nan boss ɗin naki" cewar gwaggo ɗago sleeping eyes nata tayi ta kalli gwaggo, calmly tace "To gwaggo Allah yasa na sani" "Jarumin nan naki mutun ɗaya ne ko biyu?" Cikin sauri Rimsha tace "Shi kaɗai ne wajen mum da daddyn sa dukka" shiru gwaggo ta ɗan yi kafin tace "Amma wani lokaci zaki gan shi da ido ligh ash wani lokaci kuma ligh blue shi yasa nace ko su biyu ne" girgiza kai Rimsha tayi tana faɗin "Eh gwaggo nima ina ganin hakan sai dai ina tunanin sanya kalar idon nasa yake dan shi kaɗai ne wajen mum da dad na sa bai da wani ɗan uwa i think yana using eye contact ne" mum ce ta ansa zancen da cewa "Ni ma tun da jimawa nake son mata wan nan tambaya ban samu dama ba amma fa dukka idon da light blue da light ash ɗin duk suna masa kyau sosai" da sauri Rimsha tace "A'a mum light blue nan yafi masa kyau idan ya sanya ta zaki ganshi idan ya ɗago idon nasa har wani kyalli take kamar madubi, tana ɗaukan hankali idan kikaga idon nasa zaki yi tunanin light ash ne amma kuma light blue ne ni kasa ganewa ma nake har sai ya ɗaga idon nasa ko yana kallon mutun ko yana kallon wani abu a nan ne nake iya gane light blue ne amma idan kika gan shi at the first time zaki yi tunanin light ash ne" ta kai karshen maganar tare da miƙa wa ta nufi bene tana faɗin "Mum an gama shirin dan shi baya wuce 15mins yake badawa a cikin time na sa, yace kowani second a rayuwar sa tana da matukar muhimmanci" girgiza kai kawai mum tayi tana mamaki irin kaunar wan nan Christan da Rimsha keyi, mutumin da bai san hanyar Nigeria ba ma amma ita tana nan tana fama da kaunar kallon face na shi da labarai a kan sa.
đź’žđź’žđź’žđź’žđź’žđź’žđź’žđź’ž
*UNITED STATES OF AMERICA*
*WASHINGTON DC*
*HARVARD UNIVERSITY*
*Allotment garden*
Babban filine mai girman plot 10 filli ne mai matikar kyau da kawatuwa, wajen cike yake da shuke shuke kanana kanana da manya manyan flowers masu bala'i kyau da ɗaukan hankali launin yellow da kore, wani wajen an yi design of heart da flowers wani wajen kuma an rubuta Harvard University, daga bakin katafaren gate ɗin shigowa an rubuta Welcome to *Allotment garden* da flowers kore da yellow an kawata wajen sosai da sosai gwanin ban sha'awa sai kamshin furanni ke tashi a wajen, gaba ɗaya garden ɗin shinfiɗe yake da wasu kanana ƙanana grass masu bala'i kyau kai kace grass carpet ne a shifiɗe a wajen ga wasu Gumaka da a ka kawata su suna zubar da ruwa, ƙatuwar Giwa a ka gina ta a tsakiyar wajen ta ɗaga hancin ta sama ruwa na zuba ta kofar hancin nata kasan ta kuma an kewaye shi kamar rujiya ruwan na taruwa a wajen daga gefen Giwa ga kuma maciji shima ya ɗaga kai yana fesa ruwa daga bakin sa, ko ta ina ka zaga a wajen fitullune masu haske gaske ke haske wajen ga wasu tamtsama tamtsaman kujeru na alfarma masu numfashi, launin Milk color cike a wajen, daga karshe karshen ginin dogayen bishiyoyi ne masu ganye ja da kuma yellow, Allotment garden ya kawatu iya kawatu wa,
duk girman wajen shiru babu mutane sai wani haɗaɗen Bature dake zaune saman sofa fari tas da shi jikin nan nasa ka rantse da Allah bai taɓa taka kasa ba saboda laushe da kyau gashi a kwance luwai luwai Kyakkyawan farin matashi ne mai jini a jika, sosai yake da hasken fata da kallo ɗaya zaka masa kasan asalin 𝑩𝒂𝒕𝒖𝒓𝒆 ne, dogone cikakken namiji, yana da faffaɗan kirji da yasa muscles ɗinsa Fito wa sosai cikin baƙar top din Salvatore ferragamo da ya Fito da kakkarfar farar surar jikinsa, kyakkyawan fuskarsa ɗauke take da dogon hancin da ya ƙara wa fuskarsa kyau, ɗan karamin bakinsa ɗauke yake da kyakkyawan laɓɓa dark purple da yayi wa karamin bakinsa kawanya , a hankali ya ɗago da dara daran eyes dinsa masu shegen kyau kamar yasa musu kwalli, kwayar idanuwansa da ta kasance light brown mai ɗaukar ido, idan kayiwa idon na shi kallo a fusge sai kaga kamar idon damisa (tiger) a hankali ya fara motsa idanuwansa dogayan eye Lashes dinsa suka kara fitowa sosai , daga saman idanunsa kuwa sosai girarsa take a cike da taso haɗewa sabida cikarta, gefe da gefen fuskar sa duk gargasar gashi ne da yasha gyara, kyakkyawar dark brown hair sa har gadon bayan sa ya kai masa sai curly gashin kan nasa keyi, zaune yake shiru fuskar nan tasa a ɗaure take tamau kamar bai san me dariya ba, daga gefen da gefen sa wasu mahaukatan karnuka ne jibga jibga guda uku masu gashi sosai a jiki, biyu daga cikin su farare ne kal ɗayan kuma ja gashin jikin su har ja yake a ƙasa saboda yawa manaya manya ne sosai karnukan sun samu kiwo nai kyau. Wan na shi ne *Michel*
wasu matasan Turawa ne su uku suka shigo wajen suna tafiya suna kwaɓe fuska kusa da Michel suka zauna, ɗaya daga cikin su yasa hannu yana shafa gashin jikin karen dake kusa da shi,
cikin harshen turanci Michel yace "Dest me ya tsayar da ku sai yanzu kuka zo?" Guntun tsaki Dest ya ja kafin yace "Wan nan ban zan uncle da a ka kawo sabon nan ne mana wai yaji labarin mune marasa ji a School nan dan haka zai sa mana ido kullun idan yazo mana lecture bai gammu a class ba sai ya hukun tamu" dogon tsaki Michel yaja ba tare da ya sake magana ba "Michel muje mu sha giya ko? Ina jin yinwa" Cewar ɗayan dake daune ta ɗayan ɓangaren Michel ɗin, ata kai ce Michel yace "As from Today na dai na shan wine" waro ido waje Dest yayi kafin yace "Michel kana jin me kace kuma? Ka dai na shan giya?" Shiru Michel yayi bai sake magana ba, a ƙule Johnson ya buɗe baki zai fara magana kenan wani Bature ya shigo wajen jikin sa sanye da suit kallo ɗaya zaka masa kasan lecturer ne, miƙewa tsaye gaba ɗaya guys ɗin suka yi amma ban da Michel dake zaune kamar bai da mutumin a wajen ba, kasa da murya Johnson yayi dai dai sai tin kunnen Michel yace "Wan nan shine sabon teacher'n shi bai san mu ba zai iya sanar da Romeo idan muka masa taurin kai" kallon sama da katsa Michel yayiwa Johnson kafin ya mai do da kallon sa kan uncle ɗin dake tsaye yana musu kallon tuhuma kasa kasa Michel yace "Romeo baya kasar nan tun jiya" bai karisa rufe baki ba uncle ɗin ya daka musu tsawa "Kai dest dana ce kuje ku zauna kuyi karatu shi ne kuka zo kuka zauna a nan kuna shirme ko? To yau zaku yi bayani, ba kunce ku baku ji ba tun da na shigo makarantar nan ko wani malami sai yace min kar na shiga har kan ku kuna da haɗari, ku gaku tantirai to nima tsohon ɗan daba ne kafin daga baya na ajiye dabanci na rungumi bairo da takarda, ku fara frog jump daga wajen da kuke, yau sai kun kewaye min garden ɗin nan sau hamsin" ya kai karshen maganar tare da dawo da kallon sa kan Michel yace "Kai ne ogan su ko to naka hukunci daban ne kukace ku yan iskan gari ba?, ba zaku yi karatu ba sai dai ku zauna kuna jagaliyanci ku addabi masu karatu parents naku na kashe makudan dukiya a banza, to ni zan gyara muku zama" duk wan nan magana da su cikin harshen turanci suke yin sa, ganin wan nan uncle ɗin ba zai dai na wan nan surfa uwar masifa da yake bane gashi ya toshe masa kunne yana da mun sa yasa Michel ɗin ya miƙe tsaye tare da shafa kan ɗaya daga cikin jibga jibgan karnukan sa kasa kasa a sai tin kunnen karen yace cikin harshen turanci "Lucky ko ya masa hankali" ya kai karshen maganar tare da komawa ya zauna saman sofa ɗin,
dirowa kasa lucky yayi tare da girgiza jikin sa wani jibgege da shi ya É—aga wuyan sa sama ya fara takowa a hankali hankali ya nufi uncle, baya baya uncle ya fara ja yana faÉ—in "Ku dakatar da karan nan" kamar jira lucky yake uncle yayi magana ya rufa masa, a guje uncle ya juya yana ihu, da É—an ma dai dai cin gudu lucky ya bi bayan sa ta yadda ba zai kama sa ba zai kuma hawalar da shi, kwashewa da dariya su Johnson suka yi suna faÉ—in "New uncle ma ya shiga layi" suka kai karshe maganar tare da tafa hannu shi dai Michel yana zaune shiru,
Shi kuwa uncle gudu yake kamar zai tashi sama yana ihu a kawo masa É—auki amma ina duk in da yazo wucewa sai student sun tashi sun gudu dan sun san halin lucky duk wan da ya kwana ya tashi a Harvard University to yasan da zaman Lucky da Winston Copper karnukan nan bala'i ne basu da mutunci gashi sun samu horo da kyau wajen Michel, duk abun da Michel É—in yace suyi shi suke idan yace su rikita mutun zasu bi mutun amma ba da gudu sosai yadda zasu kama mutumin ba sai su bishi da gudu kaÉ—an kaÉ—an dan su galabaitar da mutun san nan duk in da ka shiga sai sun bika ba wanda ya isa ya raba ka da su sai shi Michel É—in da ya haÉ—a ka da su,
Tsabar gudun da uncle yake har sai da wandon sa ta cire ya rage daga shi sai Short sai uban zufa yake yana ihu yana neman tai mako,
a guje ya shiga Harvard Community garden wajen cike yake da student, ganin uncle da gudu yana ihu ga kuma lucky na bin sa a baya ne yasa gaba É—aya student É—in suka fara gudun cetan kan su suma,
uncle dai yanzu karfin sa ta fara karewa ya rage gudu daker yake nishi girgiza jiki Lucky yayi tare da yin haushi mai firgita kwakwalwa nan take uncle ya ji sabon karfi yazo masa ya kara kwasawa a guje ya nufi wajen garden É—in yana ihu kamar mahaukaci,
a guje ya shiga wajen Harvard swimming pool dake kusa da goro place watermelon, manya manyan swimming pools ne a wajen wadda a kalla zasu kai 20 an kawata wajen sosai da sosai,
a sukwane uncle ya faɗa cikin pool ɗaya, a tunanin sa ya tsira sai nishi yake sama sama kamar zai mutu, lucky na shigowa wajen shi ma ya faɗa cikin ruwa ihu uncle ya fasa tare da fita a sukwane jikin sa duk ruwa tsantsin tiles ya kwashe shi ya faɗin ƙasa ya buga kai a tiles, rage gudu lucky yayi har sai da uncle ya miƙe ya ci gaba da gudu san nan shi ma lucky ya rufa masa baya.
Share fisabilillah 👏
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu shin ya uncle zai ƙare da *Lucky* wayyo ni *Princess Teema* Machel na sha'anin sa 🤣🤣🤣🤣🤣
đź’žStar Ladyđź’ž
*đź’žTRIPLET'đź’ž
*đź’žThe beginningđź’ž*
*Episode 9*
.....Idan uncle yayi kamar zai tsaya sai Lucky ya girgiza jikin sa yayi haushi mai rikita ƙwaƙwalwa, uncle kuma da yaji haka sai yayi tsammanin lucky ya kusa kama shi ne sai ya daure ya kara karfin gudun nasa, gaba ɗaya student da ke ganin halin da uncle ke ciki sun tausaya masa ba kaɗan ba dan ya fara manya ta a kalla zai kai 45 years ba yaro bane, ga abun dariya ga kuma abun tausayi,
Shi kuwa Michel yana zaune hankalin sa kwance,
kallon sa test yayi cikin muryan neman alfarma yace "Please Michel ku ɗauke ni aiki mana a gidan ku koda goge muku takalma ne idan zaku fita ina son in ganni dai na zauna a cikin gidan ku" shiru Michel ya ɗan yi kafin yace "Babu wan da ya isa ya kawo wani Mai aiki gidan mu idan ba Romeo ba shi kaɗai yake iya ɗaukan masu aikin da yake so, ko daddy bai isa yace ya ɗauko mai aiki ba kuma shi Romeo kafin ya ɗauki mai aiki yana da doka, dokar kuwa itace idan har yaga ka dace ya ɗauke ka aiki tofa zaku yi agreement da shi ne zai rubuta maka takarda kasa hannu misali idan zai ɗauke ka aiki zai faɗa maka aikin wata kaza ko Shekara kaza zaka masa idan ka amin ce to zai rubuta maka takarda kasa hannu, idan kuma kasa hannu tofa ka sani komai zai faru sai ka cika adadin shekarun da kukayi da shi ko da baban kane ya mutu a ranar sai kazo aiki baka da wani iko da kan ka sai abun da yace kayi kuma shi aikin sa bata da time ko wani lokaci yana iya saka aiki koda cikin dare ne, babu wan da ya isa ya tinkari Romeo yace ya ɗaga maka kafa, ko daddy ka sani tsoron sa yake, kuma mu ai kasani dukka gidan mu sojoji ne masu aiki har abinci sojoji su ke girkawa wan nan tsarin Romeo ne" "please Michel ka ɗan roƙe sa mana ya ɗauke ni ko da mai goge muku takalma ne" kallon sama da kasa Michel ya masa kafin yace "Ko daddy bai isa ya ce da Romeo ga abun da zai yi ba shifa abun da ya ga dama yake, kai mutun ma ya isa ya tinkare sa yace masa yayi wani abun hmmm ka tambayi Johnson ya faɗa maka, kai bama sai an faɗa maka ba ni zan baka 1 million $ idan ka iya tinkarar Romeo ka gaida shi ma kawai" ya kai karshen maganar tare da miƙa wa ya bar wajen cikin sauri dest da test da John ɗin suka rufa masa baya, da sauri karnukan sa biyu Winston da Copper suka diro kasa tare da girgiza jikin su wasu jibga jibga da su cikin takun ƙasaita suka rufa masa baya,
A ɓangaren uncle kuwa kasa cigaba da guduwa yayi ya zube kasa a dai dai Allston dake kusa da hanyar tafiya community garden, ya kasa ci gaba da numfashi, numfashi ta masa wahalar jawuwa hakan yasa numfashin sa ta ɗauke ya sume, da guduwa Lucky ya kariso kansa yana kokarin kai masa cizo a kafa Michel da ya iso wajen yanzu yace "Wait Lucky" ba musu lucky ya tsaya tare da juyawa da gudu ya koma wajen Michel ɗin shafa kan sa Michel yayi kafin ya juya ya bar wajen Lucky Winston Copper suka sufa masa baya san nan su dest suka rufawa su lucky baya,
Su Michel na tafiya sauran uncle's ɗin suka zo suka ɗauki uncle dake sume suna ta masifa "da ma ai mun faɗa maka karka shiga sabgar wayan nan kaƙi yanzu gashi kaji a jikin ka ai" haka sukayi ta surfa masifa har suka wuce da shi cikin *(HUHS) Harvard University Health Services*
Shi kuwa Michel kai tsaye ya wuce *Harvard Square Parking Garage* yaje ya shiga dankareriyar motar sa kirar *Aston Martin* a guje Winston Copper suka shiga gidan baya shi kuma Lucky ya shiga gidan gaba, Johnson ma wucewa yayi ya shiga motar sa, kuɗi Michel ya ɗebo dollars ya miƙawa su dest yana faɗin "Kai test zaka iya zuwa ka gaida Romeo ne gobe na zo maka da kuɗin ka cash 1 million dollars zan baka idan ma sun maka kaɗan zan karama" cikin sauri test yace "A'a ni nama fasa batun aikin ai" turɓune fuska Michel yayi kafin ya miƙa musu kuɗin hannun sa yana faɗin "See you next time guy's" ba musu dest da test suka ansa kuɗi, Michel ya kunna motar sa da gudun gaske ya figeta ya bar School ɗin dama shi Johnson tun isowar su parking space ɗin yaja motar sa bai tsaya wani magana ba, su ma dest da test kowa ya shiga motar sa ya wuce gida dan yau ba zama a School sun san sunyi tsiya kar aje a faɗa wa daddyn su gwara shi Machel shi da Johnson ba mai karfin gwiwar iya nufan hanyar gidan su ma bare ya kai karan su.
John wadda kuka fi sani da Johnson É—ane ga uncle É—in su Romeo, mai suna uncle herry a gidan su Michel É—in yake da zama da shi da É—an uwan sa jay.
Gudu sosai Machel ke shararawa a kan makekiyar titin *beach drive* duk motar da tazo sai dai ta kauce ta bashi hanya ba dai shi ya kauce ba, mutane na girmama shi saboda tambarin dake gaban bambam motar sa wadda a ka rubuta *William jacop Family* saboda wan nan suna yasa suke kaucewa su bashi hanya,
*Washington DC*
Birni ne mai matukar kyau da É—aukan hankali kuma shi ne babban birnin Usa gaba É—aya garine na manya manyan masu kuÉ—i ta duniya, garine mai cike da dogayen gine gine na alfarma ga wurare daban daban na wasanni da kayatar da É—an adam, duk ta in da ka juya irin wayen nan kyawawan jirgin kasa na masu shiga har cikin anguwa nan ne (Portland train) ma su kama da luckgerious bus, ko wani bakin titi zaka samu kyawawan kujerun zama wadda passenger zai zauna ya jira jirgin kasa ko Asalin Bus, kowani wajen da kujera yake an sanya masa runfa mai matukar kyau saboda ruwan sama kowa harkan gaban sa kawai yake ba ruwan wani da wani, *Washington DC* garin ya haÉ—u ta ko ina ya kayatar matuka, kawatuwar sa ba zai faÉ—u a baki ba,
Sosai Michael ya kunna kiÉ—ar sa ya kure volume yana sharara gudu yana kaÉ—a kai su lucky na tayasa,
cikin kankanin lokaci ya iso katafaren unguwar su mai suna *lot 33*, anguwa ce ta manya manyan masu kuÉ—i da masu mulki ma'ana yan siyasa da sarakuna, ko ta ina a anguwar the most billion dollars gidaje ne a wajen wata gidan ma idan ka ganta kace da gold a kayi ta, anguwar tsab tsab take babu alamar datti ko kaÉ—an kamar mutane basa rayuwa a waje saboda hasken da tsabtar unguwar tayi, har kan titi babu alamar datti ko kaÉ—an duk wani lungu da sako na anguwar titi ne mai matukar kyau shifiÉ—e har bakin kofar gidaje, gaba É—aya gidajen dake wajen babu hawa 2 daga uku yayi sama dogayen gini ne sosai a unguwar kai dagani ba tambaya kasan anguwar na masu shi ne.
Wata dankareriyar hanya Michel ya miƙa kai da ganin hanyar kasan ta musamman ce, kai tsaye wata aljannar duniya ya tinkara, dan wan nan gida itace aljannar duniya, tun daga nesa ya fara danna horn na motar sa,
a guje wasu jibga jibgan sojoji masu jini a jika lafiyayyu masu razana mai rai suka wangale masa tampatsetsen gate É—in wadda da ganin gate É—in kai kasan ba gidan wasa bane a wajen, dan haÉ—uwar gate É—in gidan kawai ma abun lallo ne,
yana kari sowa wajen ya danna hancin motar sa cikin gidan ya nufi second gate sai sara masa jibga jibgan sojojin suke, in da second gate É—in yake, kafin ka karisa wajen sai ka shiga ta wani waje kamar É—aki wadda a ka rubuta scanning a wajen, cikin wajen yana bada wuta launin purple, wajen bai da nisa da gate 2, wajen cike yake da na'urorin da a ka haÉ—a su da jikin bangon wajen, san nan wajen babu kofa zaka shiga ta nan idan wajen ya gama scanning naka sai ka fita ta can haka wajen yake
ko da Michel ya isa wajen, dai dai wajen da a ka rubuta scanning place ya tsaya, yana jira, sai da na'uran dake wajen tayi scanning na motar sa tsab dan tabbatar da ba wani mugun abu a motar tasa,
bayan na'uran ta gama scanning sai da ta É—auki 2mins san nan gate 2 yayi kara kiii kafin ya buÉ—e kansa da kan sa alamar motar Michel babu komai dan gate É—in an haÉ—ata da nauran ne idan a koi wani mugun abu a tattare da kai to gate É—in bazata buÉ—e ba zatayi kara kamar jiniyar motar yan sanda su kuma jibga jibgan sojojin dake bakin gate na farko suzo su kamaka su binciki me kazo da shi yasa nauran ke kara shiyasa a gate É—in farko a kasa sojoji na biyu kuma gate mai aiki da na'ura mai buÉ—e kan ta kuma ta rufe kanta.
Da gudun gaske Michel ya figi motar sa zuwa cikin gida
````Wow````
Gida ne mai girman Hectare 4 wato plot 24 kenan, gida ne gari guda, gaba ɗaya gidan har jikin bango da kasa, tiles da glass ne kai kace ginin tiles da glass ne kawai, hawa huɗu ne gidan, ginin ya tsaru iya tsaruwa ya fita iya fita ko gidan shugaban kasa albarka parking space na gidan kawai taci 3 palo san nan shi kan shi parking space ɗin a keɓe yake waje guda an sa masa katafaren gate da na'urorin da zasu wanke motar da a ka fita da ita idan an dawo, kamar ɗaki a ka gina parking space ɗin motocin ne kala kala jere a wajen,
a tsakiyar harabar gidan wani gini a kayi kamar rijiya a ka kewaye wajen san nan a kayi wanin gini a tsakiya kamar fai fai ruwa na zuba a wajen,
garden na gidan ya kai girman plot 2 cike yake da kana kanan flowers masu kamshi launin je da kore a dai dai kofar shiga garden ɗin daga ɗan gefe an rubuta *Romeo da flowers*, ga manya manyan kujeru masu numfashi na hutawa shirye a wajen, ga fitillu masu hasken gaske sun haske ko ina, gaba ɗaya garɗen ɗin kewaye yake da glass ƙasan sa kuma tiles ne wani gefen kuma grass carpet, tsayawa zayyana muku haɗuwar garden ɗin nan zai cimana lokacin sosai, wajen lambun daddy kawai yaci 2 plot, dan daddy mutun ne mai son lambu sosai, kowani ɗaki a gidan yana da balcony ta gaban sa an kawata wajen da furanni masu ɗaukan hankali, gaba ɗaya gidan kewaye yake da jibga jibgan sojojin masu jini a jika suna tsaye rike da manya manyan bindigu fuskar nan tasu kamar an aiko musu da sakon mutuwa, idan ba kana da dakakkiyar zuciya ba ka kalli face ɗin sojojin nan to zaka iya sumewa dan babu alamar annuri a face nasu ko kaɗan, kowani lungu da sako na gidan jibga jibgan sojoji ne riƙe da manya manyan bindigu kai kace wajen yaki zasu tafi, kai daganin hakan kasan ba gidan wasa kazo ba,
manya manyan swimming pools uku ne a gidan É—aya na Romeo ne shi kaÉ—ai ba mai zuwa wajen sai shi, biyun kuma na sauran yan gida, haÉ—uwar wan nan gida ba zai faÉ—u a baki ba dan gidan nan gari ne guda,
Kai tsaye parking space Michael ya nufa yana zuwa wajen, daga saman gate ɗin wata yar na'ura kamar yar baby ta fara karanto number motar sa daga farko har karshe san nan ta kira sunan wadda ya fita da motar, nan take gate ɗin ta buɗe kan ta, Michael ya shige, duk wani kofa na gidan sai da Romeo ya sai tata da nauran sa dan ya rinƙa samun information a kan waye ya fita waye ya shigo, ko mota zasu ɗauka sai yasan da wani mota suka fita kuma waye ya fita da motar, ko wani kofa a koi matakan tsaro a jikin ta, idan ba gate ɗin farko na shigowa gidan ba bawani waje dake da mai gadi shi ma gate ɗin farko ya bar shi ne dan criminal ya samu ya wuce gate ɗin farko ya shiga gidan, gate na biyu ya tonasa asiri, kuma ba halin guduwa sojojin dake gate na farko zasu yi ram sa shi wan nan shi ne dalilin da yasa ya bar jibga jibgan sojoji a wajen,
Michel na shigar da motar sa ya kashe ta ya fito tare da su lucky, ya danna wani waje kamar remote san nan ya fice daga wajen su lucky na biye da shi, nan take ruwa ya fara sauƙowa yana wanke masa motar tasa, a she ruwa ya danna dan ta wanke masa motar.
Yana fita ya wuce wajen É—akin su lucky dake kusa da garÉ—en, É—akin karnukan ma duniya guda ne har da katon gado a ka sanya musu kai kace ba kuÉ—i a ke sawa ake sayen abubuwan nan ba, yana kai su É—akin su ya rufe su ya fito
Kai tsaye katafaren kofar da zata sada shi da cikin gida ya nufa shi kan shi kofar ma abun kallo ne, yana zuwa wajen ya buɗe yatsun sa ya ɗaura saman finger scanner yana kwaɓe fuska yana jin haushin wan nan matakan tsaro irin na gidan, ba karamin fama ya shaba kafin Romeo ya yarda ya dai na haɗa shi da bodyguard suna raka shi School har rashin lafiyar karya yayi dan a barshi ya rinƙa fita shi kaɗai yana shanawar sa, bayan finger scanner ta gama scanning na hannun sa ne katafaren kofar mai girman ta wangale kan ta, guntun tsaki yaja tare da kutsa kan sa cikin,
wani aljannar duniya ne a wajen palone mai girman plot 1 da rabi shi kansa palon yayi girman gidan wani, palon ɗauke yake da tampatsa tampatsan kujeru na alfarma masu numfashi set huɗu ko wani set kuma yana da nisa da ɗan uwan sa kai kace ma kujerun ba a palo ɗaya suke ba saboda ratan dake tsakanin su zaka ce palo huɗu ne kusa da juna amma kuma ba haka bane dukka palo ɗaya ne girman palon ne yasa a kai wa kowani set da mazaunin sa, kowani set da kalar sa sky blue fari milk golden color shine colors ɗin kujerun, wajen table ɗin cin abincin su ma duniya ne guda, table ɗin yana da tsawon 2meter ga haɗanɗun kujerun sa launin golden color masu ɗaukan hankali da ɗaukan ido guda 24, gaba ɗaya curtains na falon farare ne kal kamar yanzu a ka fito da su daga kwalin su saboda haske, Makekiyar Tv ɗaya ne a palon mai bala'i girma wadda idan kana kallon mutun sai kaga kamar ka kira shi ya amsa saboda girman Tv, fentin palon gaba ɗaya golden color ne sai ɗaukan ido yake kamar gidan gold, daga kusa da sofa set milk color nan wata iriyar tampatsetsiyar staircase ne mai kamar indomie raun haka kamar maganain sauro haka staircase ɗin yake, daga farkon staircase ɗin a miƙe yake straight daya ɗan yi nisa kamar nisan tsawon mutun daga nan sai ya tafi sama a nannaɗe kamar maganin sauro, shi kan shi staircase ɗin abun kallon ne duniya ne guda fentin jikin sa golden color ne kamar gold san nan ga wasu kwayaye fitillilu a jikin sa dake haske stair ɗin da kyau sai walwali yake yana kwalli kamar gold, staircase ɗin nan ya haɗu iya haɗawa sosai, gashi tsab da shi kamar kafa bai taɓa taka kan shi ba,
a kasan iya palo da katafaren kitchen ne kawai a wajen sai wajen dining table wadda shima duniya guda ne wajen, kitchen ɗin kawai kusan 1 plot ne a wajen babu abun buƙata da babu a kitchen ɗin jibga jibgan sojoji ne ke musu girki da duk wani aiki na gidan gaba ɗaya gidan daga farkon ta har karshen ta babu alamar mace a cikin ta
gaba É—aya palon kasan kewaye yake da tsadaddun curtains masu bala'i kyau da É—aukan hankali farare tas ko ta ina hasken gaske ne a palon saboda kyawawan fitullin dake bada haske daga sama POP,
palon nan a gyare yake tsab kai kace ba a taɓa taɓa komai na palon nan ba saboda tsab ɗin da yake, sai wani fitinan ne kamshi ke tashi a palon kamar an yi ɓarim turare,
Wan nan gida dai sai dai muce Masha Allah dan ta ko ina yayi ne
Kai tsaye staircase ɗin Michel ya nufa sai kwaɓe fuska yaƙe, yana hawa wani kyakkyawan Bature ya sauko wadda kallo ɗaya zaka masa kasan daddyn su ne dan kammanin sa ɗaya da Michel sai dai shi kwayar idon sa blue ne, ko kallon in da yake Michel bai yi ba ya wuce, cikin sauri daddy yace "Welcome My tiger" da yake haka daddy ke kiran sa a cewar daddyn wai idon Michel ɗin na shining like Tiger eyes shi yasa yake ce masa tiger "Thank you dad" ya faɗa tare da wucewa ya karisa hawa saman, a mai makon ya shiga palon saman sai ya kauce hanya ya shari kwana ya nufi wajen wata kofa wadda daga bakin kofar kana iya leko palon kasa, kofar ya sanyawa fingerprint na shi na tsakiya, nan take kofar ta buɗe ya shige abun sa, shi kuma daddy ya wuce ya sauƙa palon kasa ya nufi wajen sofa sky blue ya zauna tare da kunna News a makeken Tv plasma su.
đź’žđź’žđź’žđź’žđź’žđź’žđź’žđź’ž
*KANO*
Sai 04:00 pm su jelly suka dawo gida a motar Imran, sauri sauri Imran ya sauƙe su a gida tare da yin sallama da daddy dan lokacin jelly tayi barci a jikin daddy sauri sauri ya juya kan motar sa ya bar gidan dan tsoron kar dare ta masa a hanya ba shi da amsan da zai bawa Ammie sa idan ta tuhume sa a kan ina yaje,
wucewa cikin gida daddy yayi kai tsaye bedroom na shi ya wuce su Zuwaira na gaida shi amma bai kula su ba saboda bai son amsa magana jelly ta tashi daga barcin da take, saman gadon ta dake bedroom na shi ya kwantar da ita a hankali dan karta tashi, sai bayan ya kwatar da ita ya tuna sun manta basket na ta a motar Imran, wucewa yayi ya ajiye jakar computer sa ya nufi toilet dan yin wanka.
đź’žđź’žđź’žđź’žđź’žđź’žđź’žđź’ž
*👹 DAULAR MUTUWA 👹*
Yan sanda mota biyu ne suka shiga wajen wan nan dajin dan sun samu labarin akoi gidan magicians a wajen, tun daga ɗan nesa suka kashe motocin su, suka sauka suna tafiya da kafa a hankali hankali kamar wasu ɓarayi sai sanɗa suke suna tafiya, suna addu'ar Allah yasa nan shine address ɗin da a ka basu kuma Allah ya basu Sa'a su samu su tarwatsa wan nan gidan dan an sanar da su waje ne mai haɗari ga kuma a saran rayuka da basu ji ba basu gani ba da ake a wajen, a na zaluntar bayin Allah a wajen,
Sunyi tafiya mai nisan gaske sunayi suna duba map har sun gaji wasu daga cikin su suka cire takalmin kafarsu suka ci-gaba da takawa da tafin kafar su,
Dai dai wasu bishiyoyin masu tsawo ga wajen da ɗan duhu saboda cikan ganyen bishiyoyin, suna shiga wajen sun ɗan fara tafiya kenan suka fara jin wata iriyar gigitatchiyar takun sahu dan duk in da a ka taka sai kasa ta bada dum dum, a guje suka nemi wajen ɓuya kowa yayi ta kansa suka laɓe suna ɗan leƙowa wasu sun laɓe wajen bayan bishiya wasu kuma sun shige cikin ciyayi, suna tsaye sunyi tsurutasu suna jiran su ga wanene zai bayyana,
ba karamin girgiza sukayi ba ganin barbushi basu taɓa ganin irin wan nan halitta mai girma da muni har haka ba nan take tsoro ya bayyana a face nasu wasu daga cikin su fitsarin tsoro suka saki a wandon su, wasu kuma sumewa sukayi a wajen dan halittar Barbushi sai mai karfin imani zai iya kallon sa kuma yasha lafiya, wani ɗan sandan ma har da kashi yayi a wando saboda tsoro, jikin su sai kerma yake ido ya rena fata sai zufa suke sun kasa riƙe bingun hannun su wasu daga cikin su sai kalmar shahada kawai suke furtawa a ran su, shima kalmar shahadar basu iya furtashi dai dai ba dan akoi masu ɗauko farkon kalmar shahada su karasa da wata sura ko nasi ko falaki saboda tsoro,
ɗaya daga cikin sune yayi ta maza ya saita Barbushi da bindiga, hannun sa sai rawa yake haka ya daure ya danna kunamar bindigar ya harbi Barbushi a sai tin hannun sa, abun da ya kara rikita ƙwaƙwalwa su shine da bullet ɗin yaje sai ya daki hannun Barbushi ya faɗi kasa kamar wadda ya daki karfe,
ihu ɗan sandan da yayi harbin ya saki saboda tsorata dan bai taɓa ganin in da aka harɓi mutun kuma bullet ɗin taje ta daki jikin sa kuma ta dawo kasa ta faɗi kamar ta daki karfe ba, jin ihun ɗan sandan yasa Barbushi juyo da idon sa masu kama da wuta dai dai sai tin in da yaji ihun, kasan cewar wajen da ɗan duhu baka gani sosai yasa nan taƙe idon Barbushi ta rikiɗe ta zama kamar torchlight mai hasken gaske kai tsaye sai kan ɗan sandan da ya harbe sa hasken idon nasa yaje, a guje ɗan sandan ya fita daga maɓoyar sa yana kokarin guduwa
Girgiza jiki barbushi yayi ya fasa ihu mai rikita ƙwaƙwalwa da wan nan katuwar muryan tasa san nan ya zuro harshen sa waje wata iriyar doguwa harshen nasa tayi kamar igiya, yana tsaye a wajen ya aika harshen nasa ta capko masa ɗan sandan nan, ya kawosa gaban sa ɗago katuwar mummunar hannayen sa yayi ya damki ɗan sandan nan ya murɗe masa wuya ya ji kake kakas kas wuyar ta karye nan take rai tayi halinta ɗan sandan ya mutu, buɗe mummunar bakin sa duk wari kamar shadda yayi ya jefa ɗan sandan a cikin ta ga hakoran san nan zabga zabga kamar block a ka jera masa gasu da tsini kaifi kamar wuƙa nan take ya fara tauna ɗan sandan da gabza ganzan hakoran sa, kan kace me jinin ɗan sandan ya fara gangarowa daga bakin Barbushi hancin sa har ta ido
ihu sauran yan sandan da suka rage suka fasa tare da fita a guje suka bazama, suna neman cetar ransu, girgiza jikin sa Barbushi yayi kafin ya durkusa a wajen nan take ya rikiÉ—e ya zama katuwar maciji mai katon kai kamar faranti, ihu yan sandan nan suke basu san in da suke takawa ba guduwa kawai suke masu kashi a wando suna yi masu fitsari suna yi, kwanciya Barbushi da ya rinkiÉ—e ya zama katuwar maciji yayi ya kutsa ta cikin grass dake wajen yabi bayan yan sandan, duk wanda ya kama haÉ—iye su yake kamar paracetamol, yan sanda Shabiyar ne suka shigo cikin dajin Barbushi ya cinye uku yanzu biyar sun sume a wajen da suka fara ganin barbushi bakwai kuma suna gudun cetar rai sai kalmar shahada suke shima kalmar shahadar ba dai dai suke faÉ—e ba saboda tsoro da suke ciki
Sai da Barbushi ya cinye yan sanda biyar daga cikin su san nan yaji ya É—an koshi sai ya fara kamasu yana murÉ—e musu wuya idan sun mutu sai ya goya su a bayan sa,
har ya gama kashe su dukka ba tare da ya lura da biyar É—in da suka sume a wajen bishiyoyin ba ya É—auki gawar wayan da ya kashe san nan ya rikiÉ—e ya koma asalin mummmunar halittar sa ya wuce ya koma in da ya fito
Su kuma biyar É—in suna sume a in da suke.
đź’žđź’žđź’žđź’žđź’žđź’žđź’žđź’ž
*WASHINGTON DC*
*Harvard University*
Kamar kullun zaune suke saman kyawawan fararen kujerun dake gore place, Michael yana latsa wayar sa Johnson na riƙe da drinks shi da test, dest kuma na shafa gashin jikin lucky, basu da aiki kullun in sunzo school sai su zauna suyi ta shaye shaye suna addabar ƴaƴan mutane,
School ɗin ma dan dole suke zuwa Michel bai isa yace ba zai zo school ba saboda Romeo zai ɓallasa duk wan nan iya shegen da suke Romeo bai sani ba kuma ba wan da ya isa a School ɗin ya tunkari Romeo yace zai sanar da shi dan bala'i tsoron sa suke ji, shi yasa Michel keyin abun da ya ga dama kuma dole a masa biyayya ko ana so ko ba'a so
Wani lecturer ne yazo wucewa ta in da suke zaune bai lura da su a wajen ba yazo zai wuce cike da iya shege John yace "Dr Simon kwana biyu baka watsa jini ba kenan da har zakazo ka wuce baka gaida mu ba" kafin Dr Simon yayi magana John yace "Copper punish him" ihu Dr ya fasa yana faɗin "I'm sorry I'm sorry Johnson please karku haɗani da wayan nan tashin hankali" ya kai karshen maganar tare da duƙawa kasa yana kuka, hannu kawai Michel ya ɗaga masa ala'mar ya tafi ya basu waje, a guje Dr Simon ya miƙe ya bar wajen shi kuma Copper yana zaune ko motsawa bai yi ba dan daman idan ba Michel bane ya basu umarnin basa taɓa yin abu umainin Michel kawai suke bi
To masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai
đź’žStar Ladyđź’ž
Share fisabilillah 👏