Free chapter · Read without an account

Page 5

by Ramlat Abdulrahman Manga · NAZNEEN.....

*NAAZNEEN❤‍🔥 <5>*

EXQUISITELY BEAUTIFUL


#Mai_Dambu


'Top-Notch

Season 3

بسم الله الرحمن الرحيم

Yayi kokarin kula da Yaranshi, amma Wasube sai da ta shiga ta fita ta raba shi da Yaranshi sannan hankalinta ya kwanta. Sannan ta cigaba da baza mulkinta daga ita sai Yarta. Wasube sunan ta musulunta ne amma muguwar mace ce da bata yarda da kowa ba sai kanta da Yarta, wacce Allah ya yanka mata ita da arha, Gimbi tana da kyau domin bakar mace ce me kyau da haiba, tana da wani irin nutsuwa da mugun naci, duk abinda take so tana nimanshi ne idanu a rufe, tun tana shekara goma a duniya ta fahimci Uwarta Mayya ce, amma bata taɓa sha'awar zama mayya ba.

Gashi sai Allah ya daurawa Uwar sonta da bin duk abinda takeso kamar me, domin duk abinda take so uwar na mata. Duk da aikin Malam Yusuf Bogoro, amma zaka sha mamaki yadda Wasube take juya kudi kamar wata matar Attajiri. Ga wata bakar dabi'a ta ta na zuwa kasuwar kauye sayan dawar kunun zak'i. Duk da kuwa an san dawa take sayowa amma ita fa ba dawar bace, kurwan mutane take kamawa ta kai a juye mata dawa, kuma abin mamaki yadda kununta yake karewa duk sati. Musamman ranar Laraba da Alhamis ranar kasuwar mararaba da kasuwar Dass, babban j5 ake cikawa da manyan kuloli ana kaiwa kasuwar, ta sayo dawa ta kai musu kunun zak'in.


Ranar juma'a kuwa, kasuwar cikin garin Bauchi da ake ci na C&C, shima anan tattara kurwan mutane take tana sayar musu da kunun, ranar lahadi kasuwar durum, duk yadda kake tsammanin Wasube ta wuce tunanin me tunani, lokacin da Gimbi take aji uku na secondry school, wani yaro ya kamata yayi mata duka, domin tayi rashin kunya, abin da ya janyo haka shi ne tayi kwalliya kuma ta makara, ya ce ta goge taki, shine fa ya zane ta sosai. Ai juyawa tayi ta koma gida tana kuka, koda uwar ta ganta ta ga bulalar yadda ya mata burtutu. Sai da ranta ya b'aci. Don haka ranar juma'a taje makarantar da Gimbi don sai da tayi kwana uku a gida babu lafiya, daga nesa uwar ta tambaye ta Yaron. Nuna mata shi tayi.

Murmushi tayi sannan ta juya, tana me cire kurwanshi a jikinshi. Sannan ta juya tana faɗin. "Dan iska, gaka da nauyi kamar buhun sumiti!" Dama ba ta kama shi don ta bada shi ba, ta kama shine don ta rama abin da yayiwa Yarta. Aikuwa ta nufi kitchen ɗinta, ta daure shi a gefen murhu ta ajiye shi.

Yaron yana ganin Gimbi ya dauke kai, sakamakon sarawa da kanshi yayi, dakyar aka gama tsaron lattin da shi, ya koma aji ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. Jikinshi a matukar gajiye. Yaron nan ya takura har aka tashi break. Bai fita ba, sai dai abokansa da suka kawo miishi abin break. Domin saurayi ne, lokacin da aka tashi yaron nan da kyar yaƙe takawa, har ya isa gida, tunda ya zube a kofar dakin Mamarsu bai kuma farkawa ba, sai la'asar.


---- lokacin da Gimbi ta dawo ta samu uwar ta gyara nama, dama tasan matukar taga Uwarta a gida kuma tana gyara nama, tasan ba ordinary nama ba ne, don haka da sauri ta isa gabanta ta ce mata. "Mamana ina cewa ba Namar sagir ba ne?" Dariya uwar tayi tana faɗin. "Ga dan banza can, na daure shi ai ba zai kuma damunki ba, sai ya shekara uku anan kafin na sake shi."

"A'a ni ba haka nake so ba, zaa ce don ya dake ni aka mishi haka, sannan idan aka gano ke mayya ce babu me ƙawance da ni, yayi kwanaki ki sake shi. Domin bana son ko fata tab'a mutane a kaina!'

Washe bakin Wasube tayi tana faɗin. "Chab! Kunga zuciyar Muslunci, shi kenan zan sake shi amma sai na wahalar da dan banza domin ba karamin wahala na sha wurin dauko shi ba." Ta faɗa tana hararan sagir da yake takure wuri guda, abin tausayi.

Haka don mugunta Wasube ta wura wuta, kurwanshi yayi ta azabtuwa da zafin wuta sai da ta ga ya kwanta a wurin baya numfashi, ta dauke shi zuwa wurin tukwanen kunun zak'inta, tayi ta kwana mishi ruwan randan kasa, me sanyi kalau.

Sannan ta daure shi, a wurin ta barshi. A can gidansu Sagir, ganin yadda yake suma iyayenshi suka nufi asibiti da shi, inda aka yi ta mishi karin ruwa da allurai, amma babu canji. Sai jikin shi ya dauki zafi na wasu awanin kafin kuma ya dauki sanyi kalau.

Haka Wasube tayi ta wahalar da Yaron nan, a makaranta Gimbi taji labarin halin da yake ciki, tana dawowa uwar zata fita, tsare mata hanya tayi, fuska babu wasa ta ce mata. "Muje ki sake mishi kurwanshi!" Yadda tayi maganar da karfi, yasa Wasube rufe mata baki, ta ce mata. "Bafa kashe shi zanyi ba, dukar da ya miki nake rama miki." Cikin kuka da hargagi ta ce mata. "Bana so! Ina da rayuwa da farinciki, idan aka san cewa nice silar kome, ya kike so nayi? Don Allah ki sake shi." Juyawa uwar tayi ta nufi gindin randar sanyi ta kunce shi.

Sannan ta ce mata. "Shi kenan, na kunce shi." "Muje ki nuna min!" Haka suka nufi wurin, ta ga wani karamin tsuntsu, ya kasa tashi. Daukarshi tayi tana faɗin. "Don Allah dame haka yayi kama? Mamana mutum ne fa, kika mishi haka? Ya za ayi ta tashi."

"Ki cilla shi sama!" Kallon tsuntsun tayi tana kuka, domin duk rashin mutuncinta bata kai Uwarta ba, saima dai uwar da Allah ya daura mata soyayyar yar yasa take biye mata, sannan take kaunar yar kamar me, domin bata jin akwai abin da take so bayan Gimbi. Sai rayuwarta shi yasa take bin umarnin Yar, tunda ta sake Sagir yaron ya sha jinya sosai kafin yayi lafiya domin daga baya aka ji labarin ai mayyu suka kama shi..

Tun daga lokacin Gimbi bata kuma yin abin da zai saka wani a hatsari ba, domin tasan ko kuka tayi uwar sai ta bi diddigin kukan, balle kuma faɗa shi ne ta daina yarda tayi rigima da kowa asalima taki ƙawance da kowa don kada ta saka su cikin matsala. Shekaru sun ja ta gama secondry, kai tsaye ta samu Federal polytechnic Bauchi, inda take karantar Business Admistration, a wannan lokacin suka hadu da Siyamah da Linah yasaka Gimbi sake jin ita wata ce, domin suma Yan mata ne, na gararin rayuwa gashi basu jin magana domin ita dai Gimbi tana da kokarin yin abin da ya kawo ta , banbancinta dasu kenan, su kuma basa karatu sai bin maza da yawon shashanci.


Duk wannan abin da suke, ita kan bata taɓa yarda ta bawa namiji kanta, domin tun bata kai haka ba, Uwar ke gaya mata advantage na virgin ɗinta, shine sword din da zata yi Amfani da shi wurin mallakar abin da take so.

Haka yasa Gimbi ta ajiye aranta, ba zata bawa Kowa kanta ba, sai wanda take ganin ya dace da ita. Haka yasa baki daya take da mugun kamun kai da nutsuwa, idan ka cire kawayenta masu shegen rawan kai da niman suna.


Bayan ta gama diploma na farko, sannan ta shiga yin na biyu, shima ta gama ckin nasara, har ta tafi bautar ƙasa. Tana dawowa ta hadu da wani dan majalisar karamar hukumar Bogoro, sosai yake kashe mata kudi, har an fara maganar aure. Manyan sun shiga cikin maganar, Linah ta gayyace ta wani biki, a nan suka hadu da Saifullahi-Khalid Mansur Katagum, D'a ga Ambassador Mansur Saifullah katagum.


WAYE SHI...?

Kafin mahaifinshi ya zama jakadan Nigeria a masar, Tsohon shugaban Jami'ar Alkahira ne, sannan ya jagoranci wasu zabubbukan da aka yi a Nigeria, sannan wani abin mamaki, shine Ambassador Mansur Saifullah katagum ya auri yar kasar Egpyt Samiha Onsi Sawiri, wacce suke zaune a garin Abuja ita da Yaranta. Haka ya faru ne sakamakon can Alhaji Mansur Katagum yayi karatun degree dinshi na farko.

Sannan suka hadu, ita kuma ta fito Babban gida ne domin babu wanda bai san gidansu ba, Attajiran larabawan Egpyt ne masu tarin arzikin gado, Yayanta Omar Onsi Sawiris da kaninta Naguib Sawiris.

Familyn suna da karfi sosai, sannan sun bawa Alhaji Mansur Katagum auren yarsu ce, domin tana sonshi don suna da dabi'ar idan kana son abu ba zamu hanaka ba.

Anyi bikin aure tare da wanta Omar Onsi Sawiris, wani ikon Allah kusan a tare suka haifi Yaransu lokaci guda. d'an Samiha ya ci sunan kakansa. Saifullahi-Khalid haka kakansa ta wurin Uwa tace a kira shi da sunayen biyu. Shi kuma ɗan Omar aka saka miishi Nassef Omer Sewiris, a tare suka taso kome nasu ɗaya.

Don haka duk inda daya ya wurga kafa daya yana wurin, Saifullahi-Khalid yana aiki a lagos, a jami'ar Lagos, inda yake koyar da Islamic Science, kuma yana kasuwancin tsakanin kasashen turai. Da nan Egpyt ɗin. Kuma har lokacin bai yi aure ba, Saifullahi-Khalid yana da kanne mata biyu da namiji ɗaya, sannan kafin Mahaifiyarshi Mahaifinsu yayi aure matar ta rasu, ta bar Yara mata biyu.

Suma kuma suna auren manyan mutane, Saifullahi-Khalid dan shekaru talatin da takwas a duniya, yana cikin manyan Malaman Addinin musulunci sosai, domin yana jagorantar tafsir duk shekara a nan Azare central Mosqus.

Ya biyo mata biyu,

Aunty Mariya, Shamsiyah, sai kanenshi, Jasrah da Basmah, sai karaminsu Autansu Hashim.

A duniya family nan, suna son junansu. Domin Samiha ta koya musu tausayin juna.

Aunty Mariya tana auren Sarkin Fulanin Gombe, Dr Bashir Buba Yero da Yaranta guda uku, maza biyu mace daya. Afif da Arif, sai Sharifah. Tana da kishiyoyi itama.

Sai Shamsiyah tana auren Babban accountant general Alhaji Musa Muhmud Shira, na shugaban kasa domin mahaifinsa sune manyan mukararaban gwamnatin Nijeriya, suna can Abuja da Yaranta hudu, namiji ɗaya Mata uku, Ummu Kulsum, Aymanah, Amatullah. Sai Muhmud.

Jasrah tana auren Dan Sarkin Adamawa, babban sojan ruwa, suna zaune a lagos Yarta daya, Basmah tana bautar ƙasa domin basu aure sai sun kammala bautar kasarsu, amma an kai tambayar aurenta da kome bikin ya rage, zata auri Dan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Dr Hassan yame, yan Bauchi ne fulanin Yame ne.

Rayuwarsu kafin haduwar Gimbi da Saifullahi-Khalid, yana zaune cikin yanci da salama.

A dawo labari.


Tunda Gimbi ta ganshi, ta kuma ji yadda MC yake fadar matsayinshi yasa kara kwadaita mata sai ta nime shi, sai da aka bashi damar bude taro da addu'a, ya mike Nassef ya mike zai bishi. Juyawa yayi ya ce mishi. "Koma ka zauna!" Tab'e baki yayi ya koma ya zauna yana kallon shi. Koda ya isa wurin da zai bude taron da addu'a. Sai da yayi addu'a, jin muryanshi kawai Gimbi ta ji baki daya hankalinta ya bar jikinta. Kamar tayi hakuri, karshe tashi tayi ta bar hall ɗin, zuciyarta tana wani bugawa kamar zata faso kirjinta. Tana tsaye har suka gama abin da za su suka fito, tana kallonshi, wani irin azazzalar tsiya zuciyarta take mata, bata san lokacin da ta fito ba, daga inda take tsaye ta iso har inda suke. "Please ko zaku rage min hanya?" Dake a zaranda hotel aka yi taron, babu wanda ya kalli inda take balle ta saka ran zata samu damar shiga motarsu. Haka suka shiga zasu tashi motar, Saifullahi-Khalid din ya sauke glass zai magana Nassef da bai ɗaukar renin hankalin ya ce mata.

"Maybe fitowa zamu yi mu dauke ki ko?" Jin haka yasa ta nufi motar da sauri ta shiga, tana sauke ajiyar zuciya cikin harshen larabci ya ce mishi.

"Me yasa baka da hakuri? " "Mtsew! Kada ka min magana, kuma wallahi ba zan kuma hawa motar nan ba."

Shiru Saifullahi-Khalid yayi domin yasan matuƙar ya biye mishi, abin kunya zasu yi. A zafaffe ya juya yana kallonta. "Kin ja baki kinyi shiru a ina za a ajiye ki?" Kamar tayi kuka, domin Nassef akwai daukar dumi. "Hey ka mata a hankali, mace ce fa sai ka razana ta ai tayi kuka?"

"Zan zage ka, mara mutunci uban me na mata? Ta jima bata yi kuka ba!" Ai kuwa kamar jira take ya kai aya ta fashe da shashekar kuka, "Ya isa haka! Meye sunan unguwarku?"

"Kasan Allah ba zan bika ba, ajiye ni idan kaso ku je duk inda yayi muku."

Haka kuwa yaje y ajiye shi, a gidansu Saifullahi-Khalid din da yake Sir kashim g.r.a dake bikin class mate dinsu ne, yasa suka tawo tare. Sannan ya ciro hanky ya mika mata, ta amsa. Saifullahi-Khalid yana da matukar tausayi da kirki sosai. Mutum ne sa yasan darajar mutane, duk da Naseef ma haka, amma akwai abubuwan da ya banbantasu...

"Sunan unguwarku?"

"Idan ka isa winti ka ajiye ni, domin muna da nisa!" Ta faɗa tana shashekar kuka.

"Ok!" Ya fada yana cigaba da da tuki, a tunaninta zai ce a'a ya kaita gida ne, sai taji akasin haka. Haushi ya kamata kamar ta ce ya wuce da ita gida, amma ganin dare yana yi, yasa ta hakura ta kuma san bai zama dole su kuma haduwa ba....

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.