Free chapter 路 Read without an account

Episode 36

by Fateema Zahra Musa 路 DUK KARFIN IZZATA

*馃挮STAR LADY馃挮*34


馃挅The Talent Troupe Writer's 馃挅



*DUK 茦ARFIN IZZATA*


馃挅Story And Written馃挅

猬囷笍

*Star lady*



Duk mai bu茩atar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har 茩arshe to yamin magana ta wan nan num 蓷in *** ban da kira iya whatSapp kawai




*Episode 3锔忊儯6锔忊儯*



A fusace Bgs ya juya yama fasa shiga wajen Ammin taku yake irin na jaruman maza, ya fice daga part 蓷in gaba 蓷aya, part 蓷in Aryan ya nufa a dai dai wajen part 蓷in Ummi yachi karo da Yusuf da lamrat suna sunfito daga part 蓷in Ummi sun nufi part 蓷in Ammi sai murnushi suke suna hira kamar wasu kawaye, mamaki da al ajabine ya hana Bgs magana tunani ya shigayi wai yaushe yaran nan suka dawo hakan, yayi nisa chikin tunani sai jin Yusufu yayi ya 蓷an ta蓳a kafa蓷arta yana fa蓷in


"Big bro me kuma ka keyi a nan? Wani mugun kallo ya wurgawa Yusuf wadda sai da yasa Yusuf 蓷in ha蓷iyar wata yawu mai kuyar wuche makoshi, da kyar Yusuf ya iya bu蓷e baki ya sake chewa "my bro lfy kake kallona haka"? A fusache Bgs ya wuche ya nufi part 蓷in Aryan, batare da ya chewa Yusuf komai ba


Juyowa Yusuf yayi yana kallon lamrat dake tsaye,ta har蓷e hannu a kirji tana kallon sa "my baby ke kam ba kya tsoron yaya prince 蓷in ne? Murmushi lamrat ta yi kafin tace "to ni yaya Yusuf in ban da kaima da neman magana ina ruwana dashi, mutumin da ko magana bai ta蓳a yi ba, nifa ban ta蓳ajin voice nashi ba kwata kwata, to ai kaga ba ruwana dashi


Murmushi kawai Yusuf yayi san nan ya jawo hannunta yana fa蓷in zo muje mu gai da Abba tun da kin gai da Ummi, yau so nake na gabatar dake wa kowa na gidan nan, shima yaya prince 蓷in naso gabatar masa dake amma sai yayi tafiyar sa sunkuyar da kai kasa kawai lamrat tayi bata che komai ba


Jan hannunta yayi har chikin fada, lamrat sai kokarin kwache hannun ta take dan kunyar Abba takeji amma yaya Yusuf ya ri茩e ta sosai kuma yana jin, yadda take ta mutsu mutsu da hannun tana son kwache wa, amma yaki sakinta saima kara riketa da yayi sosai sai da suka isa gaban Abba san nan ya saketa ya samu waje saman sofa mai zaman mutun 1 ya zauna yana fa蓷in


"Sannu da hutawa Abba" da fara'a Abba ya amsa lamrat kuwa tsugunnawa tayi har kasa ta gai da Abba, sai murnushi yake ya amsa mata san nan ya 蓷ora da chewa "amarya tashi ki zauna saman kujera, sunkuyar da kai kasa Yusuf yayi wai irin kunyar nan, hararar wasa Abba ya wurga masa yana fa蓷in "au sai yanzu kasan da wani abu wai shi kunya ko"? Bari na samu Ammin ku anjima zan sanar da ita da kai da Khalid duk kar ta kara barin kushiga part nata sai ranar da aka shafa fathiha"


waro green eyes nashi waje Yusuf yayi sosai, chikin voice irin na masu shago蓳a ya fara magana "haba Abba so kake muyi chiwo ne, Allah ko kwana 蓷aya ba zan iya jurewa ban ga my baby ba, da gudu lamrat ta tashi ta fice daga fadan dan ta lura shifa yaya Yusuf 蓷in nan bai san kunya ba


Zuba masa ido Abba yayi yana kallon ikon Allah

"Abba kasan me wlh ina son kafin mu koma London an shafa fathihan nan sai kowa ya wuche da matar sa" "Yusuf tashi ka bani waje kuma ni ba zan yiwa lamrat Aure a yan shekarun tan nan ba kwata kwata fa she is 14 years tayi kan kanta da yawa" waro ido waje yaya Yusuf yayi kafin yace "haba Abba na pls ai zata karisa girman ta a gida na, nifa Abba banso ma a che Auren mun nan ya wuche nan da 1 week ba"


Kwafa Abba yayi yace "to ka fa蓷awa babban yayan kune? dan kasan ni dai ba zan maka maliyi ba shine zai maka waliyi ni kuma waliyin lamrat" a sukwane Yaya Yusuf ya mi茩e ya nufi hanyar fita yana fa蓷in "lallai Abba baso kake nayi aure ba a wannan rayuwar, in dai sai na fadawa Bgs ya zamo waliyina to wlh nama hakura da Aure har abada ya kai karshen maganar tare da ficewa daga fadan


Dariya sosai Abba yayi kafin yace "dukkan ku nasan maganin ku ai tun 蓷azun nake chewa ka tafi kabani waje kaki ka zauna kanamin surutai ba gashi yanzu chikin ruwan sanyi ka tafi ba"


A蓳angaren Bgs kuwa


Kwanche ya samu Aryan saman katafaren gadon sa, idon sa biyu yana kallon sama da alama yayi nisa chikin tunanin da yake, dan ko sallamar da Bgs yayi bai jiba.


Hayewa samab gadon Bgs yayi ya kwanto da fuskarsa dai dai face 蓷in Aryan 蓷in, ya kwaro green eyes nashi sosai, a chikin idon Aryan, a sukwane Aryan ya yunkura zai tashi tamke wuyar sa Bgs yayi ya mai dashi ya kwantar, yana fa蓷in "yan zu kuma tunanin me ka keyi?


Chikin fushi ta jin haushin tadda Bgs ya tsoratashi yace "wai dan Allah Bgs me na maka ne, bazaka kyaleni naji da damuwa taba sai ka karamin naka, komawa gefe Bgs yayi ya zauna kamar bai ji me Aryan ya fa蓷a ba, shiru suka zauna Almost 10mnt kafin Bgs ya juyo da kallon sa kan Aryan ya fara magana


"Ina kaunar ka Aryan duk duniya idan ka chire iyaye na ba wanda nake so kamar kai ba zan iya ganin ka a chikin damuwa ba, duk lokachin da ranka ya 蓳achi ko kashiga damuwa tofa nafi kowa shiga tashin hankali, dolene na rin茩a yawan tambayar ka meke damunka, dan kai ne mutun na farko da nake kauna bayan iyaye na, daga kai sai Fahad sai Zahra Aunty Farida da kuma Khalid Yusuf Ahmad, ba zan iya ganin damuwar ku ba, na yi shiru ba"


Da mamaki Aryan ke kallon Bgs "wai wace Zahra kake nufi" Aryan ya jefo masa tambaya, guntun tsaki yaja kafin yace "daman muna da wata Zahra ne a wan nan gidan bayan Auta "amma lallai Bgs ka iya iskanchin kala kala yanzu daman kasan ana kuran Zahra da sunan Auta, eyee wato duk abun da ake a gidan nan kana sane, amma sai kayi kamar baka san komai ba ko?


"Kaga Aryan ni yanzu ka fa蓷amin tunanin me kakeyi ban che kamin wasu tambayoyin ba" "yanzu idan nache maka tunanin mace nake me zakache? Dogon tsaki yaja kafin yace "ka hauka che mana me kuma zan che sai na tashi na kama kai na dan ba amfanin na zauna ina magana da wanda bai da hankali, tsaki Aryan ma yaja san nan yace "hmmmm Ni bari naje nayi wanka kana nan ne ko dai in same ka a part naka? Shiru Bgs yayi kamar bai ji abun da Aryan 蓷in yace ba, ganin bai da niyar magana yasa Aryan ya mi茩e ya nufi toilet ya barshi awajen, Shiru yayi kamar mai tunani jim kadan ya fara magana


"Khalid yana son Auta wow nayi farin chiki da hakan gaskiya domin ko ba komai zata samu farinchiki, amma dai dole Khalid ya chanza kasa dan ba zai zauna damu waje 蓷aya ba, shi ma Yusuf transfer zan masa ya koma, Us ko India duk kansu bazasu zauna kusa damu da mata a gefen suba"


"Gaskiya ko ni nayiwa Auta murna da samun Khalid a matsayin miji, chewar Aryan dake tsaye a bakin kofar toilet 蓷aure da towel a 茩ugun sa. Wani hararar Bgs ya wurga masa san nan ya mi茩a yace "idan ka gama shiri ka same ni awajen Ahmad, yana gama fa蓷in hakan yayi waje Aryan kuma ya juya ya koma chikin toilet


AUNTY AMARYA


Zaune take saman sofa mai zama mutun biyu tana waya da Aunty Maryam, yaya Umar da yaya Haidar suna zaune a gefen ta saman sofa mai zaman mutun 3, da gudu wata bigaggiyar budurwa ta shigo ko sallama babu tana sanye chikin wasu shaggun riga da wando, wadda kana iya ganin komai na tsurar jikinta, ta zuba gashin doki akai kamar wata aljana, ga wani dogayen gashin ido da ta sanya yarinyar tana da kyau ba laifi farache sosai amma farin mai ne, a shekara bazata wuche 21 year's ba


....... Da gudu ta tafi ta fa蓷a jikin Aunty amarya tana dariya "ke zulaihat menen hakan karyani kike so ki ke yi koh"? Chewar Aunty amarya "haba momy yanzu ni 蓷in che zan karyaki ki ganni fa ko kiba bani dashi" "eh to naji yanzu dai 蓷aga ni" "gaskiya aa mommy ni wlh a jikin ki nake son kwanchiya wani tsawa Umar ya daka mata wadda yasa sai da ta mi茩e ba shiri "ke!! bazaki tashi ba"

"Haba Umar baka ganin yarinya che wan nan irin tsawa haka ai ba ita ka蓷ai ka tsorata ba har dani" chewar Aunty amarya, mi茩ewa Umar yayi a fusache ya nufi waje da sauri haudar ma ya mi茩e ya bi bayan sa


"Maryan ki bari zamuyi waya anjima" chewar Aunty amarya batare da tajira amsar Aunty Maryam ba ta katse kiran ta ajiye wayar a gefe, san nan ta dawo da kallonta kan zulaihat dake tsaye tana taunan chingum.


"Dawo kiyi zaman ki my zulee kyale su Umar 蓷in nan" "Allah mommy wan nan Umar 蓷in bai da kirki ai naso na che masa bazan tashi ba, sai kuma na kyalesa" "kai zulaihat yayan naki zakiwa rashin kunya? "Aa mommy wlh Umar ba yaya na bane dan fa bai girme min ba, mommy na tace tare aka haife mu"

"Kai zulaihat aiko Umar ya baki shekara 4 dan yanzu wata uku ya rage masa ya chika 25 years" "to nidai mommy koma me gaskiya ba zan bari awani a chikin gidan nan ya takani ba, Ni mommy ina mijin nawa ma yake? Inane 蓷akin sa naje na ganshi?


"A lallai zulaihat na yarda baki da hankalin kin san wanene muke son ha蓷a ku kuwa Bgs Brigadier General Safras, kuma prince yarima mai jiran gado shine zai rike da babban mukami na soja gaba 蓷aya bayan mukamin sa ba wani duk wani soja dakike gani a karkarshin sa yake, ke bama shiba wlh ina rabaki da matasan gidan nan kibi kowa a sannu idan ba haka ba wlh inaga gawar kima zatayi wuyar ganewa kin dai ji na fa蓷a miki, yanzu ki wuche 蓷akin tsakiyar nan kije kiyi wanka dan lokachin chin abin chin rana ya kusa, kiyi sauri inason in gaba tar dake wa kowa"


Shiru zulaihat tayi tana tunani "hhhhhh lallai su wato masu girman kai ko to wlh nine nan zan gyara musu zama, ba Brigadier General Safras ba koma ta蓳a samane zanyi maganin sa, ni da na juya manyan manyan maza masu fa蓷a aji a kasar nan ma bare shi 蓷an karami kwaro, ni wlh ba dan ma yana da kyau ba me zanyi dashi, kyau nashi ne ka蓷ai ke burgeni da kuma kirar jikin sa irin na jaruman maza ko inche sadaukin yaki amma ba komai zan dawo dasu kan saiti" ganin zulaihat tayi shirune yasa Aunty amarya ta mi茩e ta dafa kafa蓷ar ta tace


"Zulaihat kar kiji tsoro fa dan nache maki shi Brigadier General, ne na sojoji mubi komai a sannu In Sha Allah zai soki kuma zai Aure ki, kinji" dawo da kallonta zulaihat tayi kan Aunty amarya san nan ta sheke da wani shu umin dariya tana fa蓷in "haba mommy karki damu nifa ba wani tsoron da naji yanzu dai bari naje nayi wankan" tana gama fa蓷in hakan ta 蓷auki jakar ta ta wuche 蓷aki, binta da kallo Aunty Amarya tayi har ta shiga 蓷akin, wani nauyayyar ajiyar zuchiya ta sauke kafin tace "lallai zulaihat idan bakiyi hankali ba zaki koma da karyayyen kafa koma daga nan ki wuche gadon asibiti dan na lura kan ki na rawa sosai, kuma kan naki ma ya rasa aina zai yi rawa sai a gidan Alhaji Abubakar Saraki gidan da yake da tarin matasa har rai 9 chikin su akoi manya manyan sojoji ga manyan likitoci, lauya engineer saurauta, hmmmm gaskiya rawan kan nan naki bai miki adalci ba, to Allah dai yasa ki wanye da kowa lfy, tana kai karshen maganar ta mi茩e ta nufi 蓷akin ta


Washe gari


Maiduguri


Zaune take a chikin Class nasu tayi shiru tana kamar mai tunani sauran students sai surutu suke, buga belt 蓷in fita breakfast da akayi ne yasa students 蓷in su kayi ihu da karfi suka fara tururuwan fita waje, gama 蓷aya kowa ya fice daga class 蓷in sunyi waje dan zuwa yin breakfast saura diyana da wata yarinya dake zaune a kujerar bayan ta, chikin nutsuwa diyana ta mi茩e tanufi hanyar fita har ta kai bakin kofar fita sai kuma ta dakata ta juyo tana kallon tarinyar dake zaune chikin Class 蓷in, kallo 蓷aya tayiwa yarinyar ta gane akoi damuwa atattare da yarinyar sosai, juyowa tayi ta dawo chikin Class 蓷in kusa da yarinyar taje ta zauna chikin sanyin murya ta fara magana


"Sannun ki sunana diyana kefa" chikin sanyin murya itama yarinyar tace "Sunana Zainab" "wow amma Zainab me yasa ko da yaushe idan muka fita breakfast ke kike zama a class baki fita ko ina? "Babu komai Aunty diyana kawai Ni ban san me zan fita naje nayi awajen bane saboda ni bana zuwa da abinchi kuma ba'a bani ku蓷in break"

"To Zainab me yasa baa baki ku蓷in break 蓷in? ko me yasa ba'a baki abin chi a gidan basu ganin har karfe 3 muke tashine?da baza su rin茩a baki abinchi ba, basa tunanin zaki ji yinwa? "Aunty diyana Ni fa bani da mama awajen matar babana nake shiyasa ita kuma bata bani abin chi kuma koda daddy ya bani ku蓷in break tache idan na sayi wani abu da shi sai ta kasheni sai dai na ajiye ku蓷in na mai da mata" wani dogon tsaki diyana taja kafin tace "zanchen banza ke bazaki sanar da daddyn na kuba, to ina mamaki take ko ta rasune? "Aa bata rasu ba tana raye sabuwa kawai sukayi da daddy na"

"Eyya to shike nan yanzu dai muje muyi break tare kuma daga yau tare zamuna chin abinchi na, kin zama friend 蓷ina kinji, ta karisa maganar tana mi茩awa Zainab 蓷in hannu, hannu Zainab ta bata suka gaisa san nan suka mi茩e atare sukayi waje


Da mamaki yan class nasu ke bin su diyana da ido mamaki suke yanzu duk jan aji da iyayi irin na diyana bata kula kowa a school shine zata kula wanchan kazamar Zainab 蓷in, ita kuwa diyana bata ma san sunayi ba dan basa gaban ta daman ba ta yiwa kowa magana a school 蓷in rike da hannun juna suke har suka isa wajen chin abinchin school 蓷in.


KANO



Aban garen su hiyana kuwa


Kamar kullun ta fito daga class nasu kan ta na mata matsanan chin chiwo, ta nufi class nasu Zahra a hankali take tafiya kamar kamar bata son taka kasa "ke ina zakije zo nan, chewar jabir dake tsaye a bakin kofar Class nasu" chikin sanyin murya hiyana tace "kayi hakuri jabir wlh yau kai na namin chiwo sosai bana son jin surutu ko ka蓷an yanzu ma zanje na kira Zahra ne tazo ta rakani office na Hm, saboda ya saka a mai dani gida" chikin tsawa jabir yace "ke ni kike chewa baki son surutu na wato ma surutu kika 蓷auki magana ta ko? Shiru hiyana tayi bata chi komai ba "to ki wuche mutafi yau wlh har atashi muna tare kuma ke zakimin hara yau ni kuma in zauna shiru ina sau raron ki "gaskiya jabir ba zanje ba saboda bazan iya magana ba koma ko ina da lfy ni ban iya surutu ba bare kuma yanzu da baki da lfy" a fusache jabir ya damko hannun ta ya fara jan ta da nufin sutafi


A zuchiye hiyana ta 蓷aga hannu ta sharara masa mari chikin tsawa tace "idan ka sake ta蓳a jikina wlh duk abun da namaka kai kaja" a zafafe jabir ya 蓷aga hannu zai zabga bama mari charab yani daga baya an ruke hannun sa, a fusache ya juyo da karfi ganin.....鉁嶏笍



Amin afuwa bana update ranar Sunday amma na muku yau ba yawa dai, ina busy sosai ne sai mun ha蓷u gobe idan mai dukka ya kaimu akoi fa chakwakiya

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.