Free chapter 路 Read without an account

Episode 30-31

by Fateema Zahra Musa 路 TRIPLETS (YAN UKU) BOOK 1 CMPLT

TRIPLET'S馃挒




馃挒 FATEEMA MUSA馃挒

(馃挒STAR LADY馃挒)



*Gargar蓷i*


_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book 蓷in nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a ha蓷amun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun ha茩茩ina_





WhatsApp me for more information ***







Episode 30-31


馃挒WASHINGTON DC馃挒



Shi kuwa Romeo kamar bai san James na tari ba, aikin sa kawai yake, yana cizan laullausan la蓳a蓳蓳an sa


sai bayan tarin nasa ya tsaya ne, ya ajiye fruit 蓷in hannun sa, ya mi茩e zai bar wajen, gently in a cool Romeo yace "Come here" ba musu ya je ya zauna, yana fa蓷in "here I am" shiru Romeo ya masa kamar bai ji me James 蓷in yace ba, shima James shiru ya zauna yana tunanin me yasa Romeo ya kiransa.


After 45mims


A hankali Romeo ya 蓷an ture system 蓷in gefe, yana ture system 蓷in bodyguard sukayi sauri matso masa da plates 蓷in abinci gaban sa, tsalleke abincin yayi ya 蓷auko fruits ya fara ci a nutse kamar bai son tauna, hannu James yasa suka fara ci a tare, sai satar kallon Romeo yake dan ya fahimci ko akoi wani sauyi a face 蓷in Romeo.


"Why are you looking at me like this?" Kamar saukar aradu haka James yaji wanna tambaya ta Romeo, ko taya akayi Romeo yasan yana kallon shi oho, sai ta nitsuwar sa yayi yace "Because your my blood, I like to watch my blood face like film" shiru Romeo ya masa bai sake magana ba.


Yau dai fruits kawai Romeo ya ci, gently ya mi茩e ya nufi hanyar haurawa sama, binshi da ido James yayi yana mamakin, to akan me Romeo zai kirasa kuma bai yi masa wata magana ba, a ransa yace "Lion mur蓷a蓷en mutun baka ta蓳a gane gaban sa bare bayan sa, kullun cikin gindayar da mutane yake, sai ka rasa ina ya dosa kwata kwata, Allah ya kawo masa sauki, yanzu kawai ya wani kirani kuma ya tashi ya barni zaune, ni ya 蓷aga min hankali ma" ta kai karshen zancen zucin na sa tare da mi茩a wa ya wuce word room.


Ido biyu ya isko Musharraf, bawan Allah ya jima da tashi babu mai masa alwala shiyasa ya kwanta shiru kamar wani maraya, hakuri James ya bashi sanna ya 蓷auko ruwa da niyar yi masa alwala.


"No James just leave it, yau bana jin da蓷in jikina, sai zuwa gobe zan yi sallar daren" kamar James zai yi magana sai kuma ya fasa, ya ajiye ruwar ya dawo gefen Musharraf 蓷in ya zauna yana fa蓷in "Okey let's chatting" murmushi Musharraf yayi, zai yi magana wayar James ta fara kara, cikin sauri ya fito da wayar daga aljihun wandon barcin jikin sa.


Josephine shine sunan da ya bayyana a saman screen 蓷in, guntun tsaki yaja kafin yace "Not know" yana kai karshen maganar ya katse kiran tare da sanya number a blacklist ya mai da wayar aljihun sa


Cike da karanbani Musharraf yace "who called at this time 1:20am?" (Waye ya kira ka a wanna lokacin) 茒aure fuska James yayi kafin yace Josephine, "Who is Josephine?" Musharraf ya sake tambaya, a kule James yace "Our mum" ya bashi amsa a takaice, zaro ido waje Musharraf yayi kafin yace "gaskiya ina son sanin me mum 蓷in nan taku ta muku, da har kuka mata wanna tsana haka" shiru James ya 蓷anyi kamar mai tunani, kasan cewar su turawa ba ruwan su, kusan yaruwar su rabi dukka a faranti suke basu san kunya ba, bare rufawa wani asiri, sai James ya fara bawa Musharraf labarin abun da ya ha蓷a su da mum nasu, abubuwan da ta musu a baya in short dai ya bashi labarin "daddy tell us, lokacin da muke jaririrai, mum 蓷in mu ta ha蓷u da wata friend 蓷in ta yar kasar India kuma musulma ce, sun zama friend sosai, shi ne wan can 蓷in tace wa mum ta kai mu wajen magicians, ta bada jinin mu su mata ku蓷i da shi, lokacin dad bai da ku蓷i, mum kuma sai ta biyewa wan can musulman ta kai mu wajen Magicians, thank God, muna da sauran kwana dad yaje ya kar蓳o mu ba'a riga an yanka mu ba, shine fa mum tace ba zatayi feeding namu breast nata ba, kuma ba zata zauna da dad ba dan bai da ku蓷i, ta tafi ta bar daddy, haka ya rin茩a shan wahalar renon mu har muka girma, that is why bamu son ta, shiyasa su dad basa son Musulmai wai Musulmai mugaye ne, sannan yana 蓷aya daga cikin abun da yasa bama son girl a area da muke, dan mata duk haka suke basu da gaskiya, shi yasa nace kada ka fa蓷a wa su daddy you are a Muslim, ba zasu yarda ka zauna a nan ba" girgiza kai Musharraf yayi kafin yace "Amma kana ganin gaskiya dad ya fa蓷a muku a kan mum ta kai ku wajen Magicians?" Da sauri James ya gya蓷a kai yana fa蓷in "Yes ita da bakin ta ma ta fa蓷a, she accepted her mistake, before now har kasa ta du茩a ta bawa dad da lion hakuri tana kuka, dad da lion sun ce ba zasu yafe mata ba because haka mata suke in sun yi abu zasu ce Sorry later kuma zasu sake repeating na the same wannan mistake 蓷in, kuma this is the reason why kawai ba su yafe mata ba, dan ko sun yafe mata zata sake wani mistake 蓷in, kuma ai kaga muna da gaskiya, tun muna yara bata son mu sai yanzu da muka girma, she saw we have plenty money now, shine kuma zata dawo tace tana som mu no we can't except her" jinjina kai Musharraf yayi yana fa蓷in "Eh haka ne kuna da gaskiya, kuma kunyi dai dai, amma in dai ita da kan ta ta yarda da kuskuren ta kuma ta baku hakuri, to please ku yafe mata mana" mi茩ewa James yayi yace "Good light uncle, and please don't talk about mum to me again" zuba masa ido Musharraf yayi a ransa yana fa蓷in "Tabbas she蓷an ya ru蓷i Mahaifiyar ku tayi kuskure to amma bata cancanci hukuci mai tsauri haka ba, tun da har ta baku hakuri, kamata yayi ku hakura, domin uwa da 拼a拼an ta sai Allah, yanzu Allah ne ka蓷ai yasan irin ra蓷a蓷in da take ji a zuciyar ta na rashin amincewa da ita da kuka yi, amma ina da tabbacin In Sha Allah kuka musulta, imani ya ratsa ku, kuka san darajan iyaye da amfanin su, da izinin Allah zaku nemeta da kan ku" shi kuwa James tuni ya wuce bedroom nasa ya bar Musharraf da zancen zuci, gyara kwanciya shima Musharraf yayi tare da tuntse idon sa yana son yin bacci.


James dai ko da ya kwanta sai yaji ya shiga damuwa kala biyu, bacci yaki zuwa masa, abu na farko, yana jin like bai kyautatawa Musharraf ba, na biyu kuma damuwa a kan gobe zasu yi taron su na yan ta'adda, kuma tabbas yaga Romeo ya shirya yadda za'a farmaki taron a system na sa, amma ba yadda zai yi dole yaje taron nan in ma ya mutu ko yayi rai, abun da ya fi sawa ran sa shi ne mutuwa zai yi, dan mawuyacin abu ne yaran Romeo su farmaki waje kuma basu yi nasara a kan aikin ba da kamar wuya, yasan tsab sai sun kashe kowa da kowa, a ransa yake jin shike nan zai rabu da yan uwan sa kenan.


Ya kasa bacci sai tunani yake, kamar yadda yaga rana haka yaga dare, sai kusan karfe 6 na safe sannan ya samu bacci wahala ta 蓷auke sa.


A fannin shima Romeo bai yi baccin ba, ya kwanta yana ta tunanin yadda aikin zai kasan ce, sai yiwa yaran sa fatan nasara yake, duk da yana da kwarin gwiwa a kan su, Yasan sun samu horo, bai ta蓳a turasu aiki basu yi nasara ba, sai dai babban damuwar sa 蓷aya ba tare da Tga zasu tafi ba, kasan cewar Tga na kwance a gadon masu jinya, daddy na dubasa, wajen da kwarin nan suka harbesa ya kumbura sosai, abun dai sai addu'a dan kuwa ko wando baya iya sawa, yana kwance yana baje yana shan iska, gashi yaki tsayawa a wani duba shi ma saboda ra蓷a蓷in azaba, duk wannan Romeo bai sani ba, bai san cewa Tga yaki tsayawa a bashi kulawar da ya dace ba, da tuni yaje da kan sa ya danne sa ya bashi kulawa da kan sa, sai dai bai sani ba, kuma duk suna tsoron fa蓷a masa shi yasa, shi kuma bai cika shiga harkan yan gidan ba kullun yana 蓷aki, in dai ba kai ka nemo sa ba, to shi baya neman kowa, 蓷an gara Triplets na sa da kuma daddy, idan ya wuni bai ji motsin su ba yana kiran su a waya yaji lafiya.


Haka dai shi ma ya kwana ido biyu ba bacci, yana ta tunanin yadda tafiyan yaran nasa zai kasan ce ba Tga ,wannan ne dalilin da yasa jiya da daddare ya kira James dan ya duba masa jikin Tga 蓷in sai kuma ya mance da me yasa ma ya kira James 蓷in, shiyasa ya mi茩e ya bar james zaune a wajen.


Asuba ta gari



Wannan kenan bari mu le茩o su Jelly mu dawo muga cakwakiyar familyn William jacop.


馃挒NIGERIA馃挒


JELLY


Yanzu ta 蓷an fara sakewa da gidan tana iya zama ita ka蓷ai, inma a bedroom ko a palo, sai dai fa har yanzu bata wanka da kan ta kuma bata cin abinci da kan ta, sai dai Hajiya ta mata wanna dukka.


Yauma kamar kullun tana zaune a palo ita ka蓷ai tayi shiru tana kallon Tv ana labarai, duk da ba gane abun da ake fa蓷e take ba, ta zuba musu ido kamar ta san me ake cewa, yayin da news 蓷in ke magana a kan 蓳atar ta, dan daddyn ta ya shiga damuwa over, shiyasa har gidan Tv a ka kai zancen, ana cab da sanya hoton daddyn ta, wannan tantiriyar budurwan ta shigo palon babu ko sallama, hakan yasa hankalin Jelly ya kau daga kan Tv ta koma kallon yarinyar, while a Tv kuma an sako hoton ta dana daddyn ta


zubawa attachment 蓷in kan yarinyar ido Jelly tayi tana mamaki, ganin babu kowa a palon yasa yarinyar tace da Jelly "Ke zonan" turo baki Jelly tayin kafin ta make kafa蓷a tace "A'a ni ba zam zo ba" shiru yarinyar ta 蓷an yi tana tunanin yadda zata yi da Jelly ta fara bin ta 蓷aki, can wata dabara ta fa蓷o mata, hannu tasa cikin Jakarta ta fito da chewing gum da take yawan ci, ta mi茩awa Jelly, ba musu Jelly ta mi茩e ta karisa wajen ta, ta sanya hannu ta kar蓳a chewing gum 蓷in tana dariya, dariya irin na yan duniya yarinyar tayi kafin tace "Yauwa ki saki jikin ki dani ko? Ni auntyn kice, daga yau in nace kiyi abu, ki rin茩a yi zan saya miki sweet kala kala kinyi?" Tayi maganar tana shafa kan Jelly zuwa wuyar ta, Gya蓷a mata kai kawai Jelly tayi tana faman tura chewing gum a baki, murmushi shakiyanci yarikyar tayi kafin ta 蓷an du茩o da kan ta, dai dai saitin goshin Jelly kasan cewar ta fi Jelly tsawo, ta mannawa Jelly kiss a goshi tana shafa wuyar ta, ta wuce part nasu, wucewa itama Jelly tayi ta koma cikin bedroom na Hajiya.


Hajiya na kwance Jelly ta fa蓷o mata 蓷akin babu ko sallama, Hajiya bata damu ba dan ta 蓷auki hakan a matsayin dan Jelly bata da lafiya ne, bata san Jellyn daddy ba already haka take daman.


Hayewa saman gadon Hajiya tayi ta fara gaya mata yadda suka yi da wancan yarinyar, zubur Hajiya ta mi茩e zaune tana kallon ta dan tasan halin afnan sarai, ta santa yar lesbian ce dan kuwa har ita kan ta Hajiya sai da afnan tayi mata tayin lesbian a baya, Hajiya batayi kasa a gwiwa ba taci mata mutunci fes shi ne yasa yanzu Afnan bata mata magana a gidan.


Mi茩ewa tsaye Hajiya tayi, ta diro kasa daga saman gadon rai a matukar 蓳ace ta fice daga 蓷akin ta nufi part 蓷in su Afnan, da sauri Jelly ta sauko kasa ita ma tabi bayan Hajiya.


A palon part na su Afnan Hajiya ta tsaya, ta fara kwalawa Afnan kira, da sauri mahaifiyar Afnan da yaya ta da ita kan ta Afnan 蓷in suka fito suna tambayar ko lafiya Hajiya ta shigo tana ihu hakan, rai a matukar 蓳ace Hajiya tace "Ke Afnan wlh summa wlh ki fita harkan baby, babu ruwan ki da ita, na rantse miki da Allah idan kikayi gigin ta蓳a hannun yarinyar nan zan nuna miki yadda ake bariki, karkiga kina yin duk abun da kikaga dama a gidan nan muna zuba kiki ido, wlh ba wai kinfi karfi na bane, dan dai kawai bani da lokacin kine, amma a kan baby ina da lokacin ki daga nan har illah masha Allah, ke in takaice miki zance wlh zan iya komai a kan baby" kallon sama da kasa Afnan tayiwa Hajiya zatayi magana mahaifiyar ta ta rigata da cewa "Ke Hajiya Turai bafa tsoron ki muke ji ba zaki zo ki wani tayar mana da hankali a kan wancan shegiya tsintaciyar magen, daman ina cike dake a kan yarinyar, dan Alhaji yazo jiya yana wani ce mana kin kawo yarinya dan Allah kar yan gidan nan su takura mata, to yarinyar yar kanwar uwar ki ce? Ko ma yar kanwar uwar ki ce idan bata mana ba sai munci uban ta a gidan nan bare kuma naji Alhaji yace wai tsintar ta kikayi, to wlh tsintaciyar mage bata isa ta zo tace zata takurawa yan gida ta hana su jin da蓷i ba kinji na fa蓷a mi茩i, Afnan kuma koma me tayiwa yarinyar dedene, Afnan ki ci uban ta dan ba gidan uban ta bane, na uban kine" ita maman Afnan a tunanin ta rigima ake dan Afnan ta daki Jelly bata san kan magana ba


Aliyu yayan Afnan ne yace "Ummi kiyi hakuri kije, dan Allah komai ta wuce haka kinji?" Ita kuwa Hajiya jin abun da maman Afnan tace yasa tayi tunanin kenan da sanin maman Afnan, Afnan ke yin lesbian? Ta tambayi kan ta tambayar da babu amsa, amma a zahirin gaskiya maman Afnan bata san Afnan na wanna aika aikan ba, shikan shi yayan nata bai sani ba, su suna tunanin duk wannan masifar da Hajiya keyi tanayi ne dan Afnan ta daki Jelly, basu san dawar garin ba, shi yasa maman Afnan ta zage dantse dan tarewa yarta fa蓷a, shi kuma yaya Afnan kasan cewar baya son hayani sai yayi ta basu hakuri.


Da kyar ya samu Hajiya ta hakura ta wuce ta koma part nata, tana shiga palon ta ta samu Jelly zaune tana kallon Tv, da Jelly ta fito ne zata bi Hajiya, sai taga ana nuna cartoon a Tv sai ta zauna kallo.


Hannun ta Hajiya ta ja suka bar palon zuwa nasu part 蓷in. A palon part nasu Hajiya ta zauna ta zaunar da Jelly gefen ta, cikin nitsuwa tace "Baby daga yau karki sake fita babban palo bana so, kiyi zaman ki a nan, ga Tv nan zan rin茩a kunna miki, kuma idan wani ya sake cewa ki zo a gidan nan karki yarda ki je, ba ruwan ki da kowa karki sake yiwa kowa magana daga ni sai Abbo sai yaya Nawid, mu ka蓷ai zaki rin茩a yiwa magana, kuma mu ka蓷ai ne idan munce kiyi abu zaki yi kin ji ko?" Kai Jelly ta gya蓷awa Hajiya alamar taji.


Cab lalai Hajiya kin kashe maciji baki sare kai ba, dake da Abbo da Nawid ne kawai zaku mata magana tayi abun hmmm, muje zuwa.


Wunin ranar dai Jelly bata sake le茩a babban palon ba tun safe da abun ya faru, a nan tayi zaman ta har dare, idan ta gaji da zama ta kwanta, idan ta gaji da kwanciya ta shiga bedroom 蓷in Hajiya su 蓷an yi hira, Hajiya na koya mata karatu, amma fa ba abun da take gane wa.


Da daddare suna cin abinci ne Nawid ke sanar da Ummi zai yi tafiya zuwa Katsina next week, kasan cewar Hajiya Turai ya ce ga sarkin matsina, Nawid jikane ka sarkin, hakan yasa yake yawan kaiwa kakan nin sa ziyara


Da fara'a Hajiya ta amsa masa da to dan tana son daman zumuncin ta da yan uwan ta maza da 拼a拼an su ya kara karfi sosai yafi haka,


Yanzu Nawid na daina hantarar Jelly dan ya fahimci haka take, kuma abun ya ha蓷u mata da ciwo, shi yasa baya damuwa idan tana wani shagwa蓳ar nata, yanzu in tace masa yaya yana amsawa har ya biye mata, dan Hajiya ta masa kanwar dole, kuma haka ya kar蓳a ba yadda zai yi, wani lokaci ma idan Jelly ta tayar da ballin ba zata ci abinci da hannun ta ba, shi yake bata a baki da kan sa, ko Abbo.


Bayan sun kammala cin abin ne kowa ya mi茩e ya nufi bedroom nasa, ita kuma Hajiya ta ri茩o hannun Jelly suka tafi bedroom nata, dan sun saba sai Jelly tayi barci Ummi ke mai data bedroom nata, dan bata yarda tayi barci ita ka 蓷ai, wani lokaci kuma a bedroom 蓷in nata suke zuwa su kwanta har sai tayi barci, sai su salalla蓳a su fice su koma nasu bedroom 蓷in.


Yau Hajiya ta gaji sosai, suna kwanciya ba jimawa barci ya 蓷auke ta, saura Abbo da Jelly, daman Jelly na ta gefen Hajiya, ma'ana Hajiya ce a tsakiyar su.


Mi茩ewa Abbo yayi, yayi kwanciyar rigingine yana fiskantar Jelly, ya zuba mata ido yana ta kallon ta daga sama har kasa, yana son ta蓳a ta yana kuma tsoron kada ta masa ihu ko ta tashi Hajiya daga bacci, dan yasan halin Jelly sarai ba'a mata abu tayi shiru, kana mata abu da 蓷umi 蓷umin sa zata fa蓷a wa Hajiya ba 蓳ata lokaci, tunani ya fara yi ya zai yi, dan shi gaskiya yana matikar son Jelly, sai kallon ta yake ita kuma tana kwance ta rintse ido amma ba tayi barci ba, dan ga idon nata nan sai motsi suke, wutar 蓷akin a kunne yake dan Jelly bata zama a 蓷aki sai da wuta a kunne, tana tsoron duhu, wani lokaci sai tayi barci hajiya ke zuwa ta kashe mata wutar, amma fa idan ta tashi cikin dare, to akoi dirama dan ihu take kamar zatai hauka, da kyar ake lalla蓳a ta ta mai da barci, ta hanyar kunna mata wutar 蓷akin.


Ahankali ya kai hannun sa zai ta蓳a ta, sai kerma hannun nasa keyi kamar mazari, ya kasa ta蓳a ta, yana son ta蓳a kuma yana tsoron tsiwarta, sai dai abun da bai sani ba, yanzu Hajiya tace duk abun da Abbo da Nawid suka ce mata tayi to tayi shi, kuma ita Jelly duk abun da Hajiya tace tana yin sa ba 蓳ata lokaci, sannan in dai Hajiya tace tayiwa wani biyayya tofa kome zai mata ba lallai ta fa蓷a wa Hajiya ba, tun da Hajiyar ce tace tayi.


Haka Abbo yayi ta kokarin ta蓳a Jelly yana tsoro, har barci ya 蓷auke Jelly, haka ya zauna ya zuba mata ido yana ta kallon ta, yana kara jin haunar ta a ransa.


Sai wajen 1 na dare sannan barci ya 蓷auke sa, yau kasan cewar Hajiya ta rigasu yin barci, sai Abbo bai ce ta tashi ta kai Jelly bedroom nata ba, dan shima hakan yake so Jelly ta rin茩a kwanciya kusa da su, shi yasa ma baya wani damuwa wajen sa Hajiya ta koya mata kwana ita ka蓷ai a 蓷aki, shine ma mai kara injiza abun, da Jelly ta fara cewa bata so, sai ya wani ce a'a a barta tun da bata so kar a wani takura mata, shi ya fara kawo shawarar tun da tana tsoron kwanciya ita ka蓷ai to su rin茩a kwanciya da ita sai tayi barci su 蓷auke ta su mai da ta bedroom nata, insert of ya sanya Hajiya ta koya mata kwana ita 蓷aya, sai ya kara dagula komai dan shima yana ra'ayin hakan. A ranar dai a 蓷akin su Jelly ta kwana.


Mu le茩o Rimsha mu dawo


馃懝DAULAR MUTUWA馃懝


Yanzu dai ba laifi shakuwa ta shiga tsakanin Rimsha da duna, sai dai ita Rimsha tana biye masa ne kawai bisa umarnin baba na cewa ta biye masa har Allah yasa ya musulunta imani ya ratsa shi ya daina shan jini da sauran su, wannan dalilin yasa take biye masa, yanzu har zama take suyi ta hira, yana mata tambayoyi a kan addinin Musulunci tana bashi amma with her confidence, dan ita ma tana burin ya shiryu ya musulunta ya dai na duk wani abun da yake ya koma ga Allah, sai dai kullun in zata bashi amsa a kan addini, sai Queen ta sha茩e ta, tayi ta fama har sai duna ya taimaka mata, kasan cewar shi ma irin sune, da jikin sa ya ha蓷u da nata ka蓷an, tofa dole su sake ta.


Yauma kamar kullun suna zaune saman bencin duna suna hira, shi kuma yana zaune daga 蓷an gefe da su, saman wata kujera da ya bayyanar da ita da tsafin sa, yanzu baya zama kusa da su sosai a 蓷an gefe yake zama, saboda sun fa蓷a masa a addinin musulunci ba'a yin haka, saboda son da yake wa Rimsha yasa yake girmama addinin ta da kuma dokokin addinin nata.


Sai hira suke ita da su Ayla cikin nisha蓷i, yau basu je wajen baba ba, sun zauna wajen, zuba musu ido kawai duna yayi yana kallon yadda Rimsha ke ta murmushi kyakkyawan dimple nata yana lotsawa gwanin ban sha'awa hakan ba karamin kyau yake karawa face nata ba, daman abu hu蓷u zuwa biyar ne a face 蓷in Rimsha da yafi 蓷aukan hankali duk wanda yayi ido hu蓷u da ita, na farko wayan nan kyawawan dara daran sleeping eyes 蓷in nata farare kal kamar audiga, ba karamin tafiya da imanin 蓷an adam suke ba, kasan cewar idon nata yayi daban, sai ka tara mutane sama da dubu baka samu biyu masu irin wanna idon ba, shine babban abun da yafi jan hankali mutane a face nata, na biyu kyakkyawan dimple nata, idan tana murmushi ko tana magana, ko baka son ta sai ka tsaya ka kalleta, saboda dimple 蓷in nan, ba karamin kyau yake kara mata ba, 蓷an siririn open teeth, dake tsakanin hakwaran ta da suke farare kal a baya amma yanzu saboda da hannu take brush babu brush hakan yasa hakwaran nata suka rage haske, amma still suna da hasken sai dai ba kamar lokacin da suke tare da daddyn su ba, abu na hu蓷u 蓷an bakin ta, wow idan tana magana abun sai wanda ya gani, la蓳蓳an ta na sama design of heart ne ga bakin nata 蓷an karamin dashi launin pink color kamar wadda ta sanya lipstick, hancin nan nata har baka 蓷an siriri kamar karas Masha Allah, ga bakin saje kwance a gefen kumatun ta.


Sai hiran su suke duna ya tsare su da ido, can kome ya tunan ya mi茩e yazo ya tsugunna a gaban ta, tare da zuba mata ido a hankali yace "Me yasa idan kuna magana kuke yawan sanya Annabi Muhammad? Waye shi?" Dawo da kallon ta kan face nashi tayi cikin nitsuwa tace "Shi ne Babban abun soyuwa a gare mu, kuma shine annabin karshen da baba ya fa蓷a maka ranar, duk wani cikakken musulmi yana son Annabi Muhammad" "eh nasan kuna son shi kam dan baku magana 蓷aya biyu baku kira shi ba" yar murmushi Rimsha tayi kafin tace "Saboda son da muke masa ne yasa har a zamanin baya kafin yazo duniya ya samu takwara dayawa, sosai jama'ar zamanin da kafin yazo suka masa takwara" zaro ido duna yayi kafin yace "To bai zo ba kuma ya akayi suka san shi har suka masa ta kwara? Waye ya fa蓷a musu sunan shi da har zasu masa takwara? Bayan ni nasan sai an haifi yaro ake sanin sunan da za'a sa masa" 蓷an kawar da idon ta tayi daga kallon sa kafin tace "Annabi Muhammad (SAW) an san shi ne tun kafin a ganshi, kuma an sanshi ne tun kafin a haife sa, domin yazo a littafai da dama, sunan sa ya bayyana a littafai irin su attaura, injila, zabura, so already wayan nan littafai sun bayyana zuwan sa da sunan sa da yanayin da zai zo, da kuma in da zai bayyana, waye shi da sauran su, shi yasa jama'a suka rin茩a masa takwara saboda son da suke masa, muma yan zamanin yanzu muna kaunar sa fiye da rayuwar mu, ni kullun cewa ma nake da azamanin sa a ka haifeni dana more" shiru duna ya 蓷an yi kafin yace "Kwarai kuwa na san kuna son shi, nima shaidane dan kuwa akoi wata mata dana ta蓳a shanyewa jini a kasuwa, lokacin na ri茩e蓷e na dawo kamar yadda kika ganni yanzun nan, na shiga cikin mutane, a kasuwa na ga matar tana sai da kaya, kawai naji ina son shanye jinin ta, to lokacin akoi wata wa茩a da ta kunna suna fa蓷in annabi kwarai kasan gaibu, na kasa manta wannan wakar ita kan ta matar na kasa mantawa da ita, ban san ya akayi ba ita ce mutun na farko dana ta蓳a shan jinin ta dana kasa mantawa, bayan na sha jinin nata sai naji ban ji da蓷i ba, har yanzu na kasa mance ta" jinjina kai Rimsha tayi har idon ta ya kawo ruwa saboda tausayin matar a hankali tace "Baka kyau ta ba, amma dai karka 蓷auka abun da suke fa蓷e a wakar gaskiya ce, domin Annabi bai san gaibu ba, dalili kuwa shi da bakin sa yace bai san gaibu ba, a lokacin da sayyidina Abubakar ya tambaye sa yaushe za'a tashi kiyama, sai yace wa sayyidina Abubakar sanin gaibu sai lillahi shi bai sani ba, Allah ne ka蓷ai ya san ranar tashin Al kiyama, kaga kenan idan da annabi yasan gaibu da muma mun san lokacin da za'a tashi kiyama dan da zai fa蓷a wa sayyidina Abubakar, shi kuma zai ruwaito mana hadisai, abu 蓷aya ne yasa mutane ke ganin kamar annabi yasan gaibu, shine mafi yawancin lokaci Allah yana masa wahayi mala'ika Jibril yazo ya fa蓷a masa Allah ya bawa wanna sahabi aljanna, ko kuma Allah ya saukarwa wannan sahabi wata ni'imar, to idan mala'ika ya isar masa da wanna wahayi, shi kuma sai ya sanar da Sahabban sa, hakan yasa mutanen mu na yanzu suke ganin kamar annabi yasan gaibu tun da yana fa蓷in abubuwan da basu kai ga faruwa ba, kamar dai yadda ya bayyana Allah ya baiwa su sayyidina Abubakar aljannan tun suna raye, shi yasa rashin fahimter ce kawai da mutane ke samu, mafi yawancin mutane suna kan dai dai bisa nasu fahimter, basu kauce hanya ba kawai basu fahinci abun dai dai bane"


hannu ya kai zai shafi kumatun ta, sai kuma ya fasa, cike da kaunar ta yace "To ni dai gaskiya addinin ku yana burgeni, ta in da kuma yake burgeni in da akace matar ka kai ka蓷ai zaka ta蓳a ta ba wanda zai ta蓳a maka ita, wannan abun yamin da蓷i sosai, addinin akoi tsabta sosai, kinga a baya zamu kwanta da duk macen da muke so, kuma ina da tabbacin kafin mu wasu sun kwanta da ita, hakan tsam ba tsari, ace mace 蓷aya maza dayawa suyi ta kwanciya da ita abun ba 蓷a蓷i, amma addinin ku yayi hani da wanna gaskiya naji da蓷i kuma na jinjinawa addnin nan naku" cool murmushi ta saki taji da蓷i duna ya fara yaba addinin musulunci, da alama ya fara hawa kan hanya ma dai'dai ciya hakan ba karamin farinciki ya sanya su ba, dukkan su har da su Ayla.


A wanna yanayi Mustapha yazo ya same su, dan yanzu yana zuwa suyi ta hira da duna sun zama kamar friend, yana zama Rimsha ta mi茩e tana fa蓷in "Ina zuwa Ayla bari na je 蓷aki na 蓷auko apple na najiya" to kawai suka amsa mata da shi, sannan ta wuce ta bar wajen, su kuma suka ci-gaba da hiran su.


Tazo zata shiga 蓷akin nasu, sai taga yar siririyar hanya daga 蓷an gefen 蓷akin nasu, Rimsha da karambani tace bari ta le茩o taga menene a wajen, 蓷an karamin hanya ne, ga wani fitinanniyar wari bala'i dake fitowa daga wajen, haka ta kutsa ta wajen tare da toshe hanci ta tana lalla蓳awa sa蓷af sa蓷af kamar wata 蓳arauniya har ta kai karshen hanyar, ba tare da su duna sun ankara da ita ba, suna ta hiran su


ko da taje karshen hanyar sai taga ba wani abu a wajen sai wani katanga mai 蓷an tsawo daya musu katanga, ma'ana ya raba su da wan can part 蓷in.


Kamar a kafarki taji kafar ta ya tsunduma cikin wani abun, cikin tsoro a hankali ta kai kallonta kasa, nan taga wani irin jini mai bala'i kauri da yauki, cikin jinin duk guda gudan naman jikin mutun, ta wani gefen ma har da kashi 蓷an adam, 蓷ago idon ta tayi a razane ta kalli gefe gefen wajen da kyau, gaba 蓷aya kashin kwarangal na mutane ne, ga kuma naman jikin mutun wadda bai gama murmushe wa ba, kasan wajen wani daskararren jini ne mai balai wari, ga kuma wani sabon jini na malala a saman wannan daskararren, da alama yanzu ake zubar da wannan jinin, wani mugun tsoro ne ya dira mata a ranta lokaci guda, nan take jikin ta ya fara 蓳ari, wani irin wahalallan yawu ta ha蓷iye da kyar, nan take idon ta ya rena fata, wani gumin wahala ya fara karyo mata.


Amma saboda fitina irin na Rimsha sai da ta kama katangar nan har da yar tsallen ta, ta le茩o, dan ta dage sai taga daga ina jinin nan ke fitowa.

Nan fa idon ta suka gane mata abun da kwakwalwa ba zai 蓷auka ba, wani mahaukacin ihu ta fasa tare da sakin katangar, kamar zararriya haka ta bazama ta fito daga wajen, a guje su duna sokayo kan ta, saboda ihun ta da sukaji


Tun da yaga ta in da ta fito yace shikenan kuma mawuyacin abune yau Rimsha ta rayu a gidan nan, ita kuwa sai ihu take kamar wata zararriya, tunani duna ya shigayi ya zai yi ya ku蓳utar da Rimsha daga sharrin su Gujungu, dan yasan definitely wayan nan magicians dake wajen zasu biyo bayan ta dan sun jiyo ihun ta, kuma tabbas bazasu barta da rai ba, dan ba'a ganin sirrin su a rayu.


Sai ihu Rimsha take da alama ta fita hayyacin ta, dan ta razana sosai da abun da ta gani, jin takun sahun jiga jigan magicians 蓷in ne yasa duna kara tsorata dan yana ji a ransa sai dai yau ya mutu amma ba zai iya bari su 蓷auki Rimsha ba, takun magicians 蓷in sai kara kusan tosu yake, duk in sukayi taku 蓷aya, sai kasa da katanga sun girgiza saboda girman su da larfin bala'i irin nasu.


Sai zaro ido duna yake, kasan cewar yasan duk bala'i sa su Gujungu wato masu gadin fadar Queen sun fisa bala'i, ko su Barbushi basu isa su tinkare su ba bare kuma shi, banda Queen ba mai iya ja da su Gujungu a gidan, manya manyan jiga jigan magicians ne masu ji da larfin 蓷aga mota kamar yar baby da hannu 蓷aya, tsabar girman jikin su da karfin su, idan suka taka kasa, sai katangar dake wajen ta girgiza, hakan yasa mafiyawancin 蓷akunan gidan da dafaffun karafuna a kayi su katanga 蓷ai 蓷ai ne a gidan, dan katanga ba zai iya 蓷aukan karfin takun su Gujungu ba rushewa yake.


Jin sun kusa isowa in da suke ne, dan ga alamar sautin takun kafar su da kuma amshin kasa nan ya kara karuwa, tsabar tsorata duna bai san lokacin daya batar da Rimsha da tsafin saba, a baya yayi al茩awarin ba zai sake amfani da tsafin ba, saboda Rimsha ta nuna masa tana tsoro kuma bata son hakan, idan har zai ci-gaba da amfani da tsafin to gaskiya ba zata ci-gaba da yi masa magana ba, shiyasa yace mata ya dai na ba zai sake ba, amma yau bashi da za蓳i dan Rimsha ta ta蓳o gidan rina ta tsokalo gindin dodo bala'i da yafi karfin su, shiyasa ya 蓳atar da ita gaba 蓷aya daga wajen


Bayyanar su Gujungu a wajen ba karamin haukata kwakwalwan yan gidan gaba 蓷aya yayi ba, banda duna da ya saba ganin su, ba wanda kwakwalwan sa bai haukace ba a gidan sai Mustapha, saboda su Gujungu sun fi su Barbushi a muni uban ni su Barbushi ne, sanna a girman jiki sunyi biyun su Barbushi, sai dai basu da tsawo, gajeru ne, sai bala'i fa蓷i shiyasa kofar shiga wanna wajen nasu ma fa蓷in sa ya kai 2 miter dan su iya shiga da fita, amma duk da haka a takure suke, saboda girman jikin su, hancin su kawai ya kai girman kan bil adama, idon nan nasu bazai ganun wa 蓷an Adam ba, ka fafun sunan ya kusa fa蓷in fridge, munin su kawai zai iya sanya 蓷an adam zuciyar sa ta buga ya mutu, babu ko 蓷igon imani a tattare da fuskokin su bare tausayi, basu fitowa kullun suna wanna part din nasu suna aikin sarrafa wa Queen ganganjikkin 蓷an Adam da sauran ayyuka.


Tun kafin su iso daman duna ya koma asalin halittar sa na Magicians, Ayla da kausar tuni sun sume a wajen, shikuwa Mustapha, kamar mahaukaci haka ya bazama yayi 蓷akin da ya samu a bu蓷e ya shege, haka sauran yan gidan da basu suma ba, suma duk 蓷akin da suka samu kawai shiga sukayi dan cetan ransu, kuma basa hayyacin su.


Duna na tsaye har suka 茩ariso wajen, Gujungu ne ya fara tambayar ina wadda ta le茩a su take, cikin yaren su na matsafa, da muryan sa mai do蓷e kunnen 蓷an adam ya daina ji gaba 蓷aya, nan fa duna ya fara musu kame kame na cewar bai ganta ba, wani mahaukacin kururuwa Gujungu ya sa wadda yayi sanadiyar tada guguwa mai karfi gaske bakin kirin kamar bakin hayaki na itacen damuna, jijjiga jikin sa yayi tare da 蓷aga kofatan kafa 蓷aya zai sau茩e a kan Ayla, duna yayi saurin kwanciya kasa ya shiga tsakanin su, kafar Gujungu ya sauka ma shi a cinyoyin sa ta baya


razanannen ihu mai bala'i sauti duna ya sake mai razana kwakwalwar duk wani halitta mai rai, kan kace me cinyoyin duna sun rugurguje har kashin sa sai da suka rugurguje saboda takun kafar Gujungu fa ba wasa ba.


Wucewa su Gujungu sukayi suka nufi cikin gidan dan neman Rimsha, shi kuwa duna sai ihu azaba yake na cinyar sa da ta daddage, haka suka wuce zuwa tsakar gidan dukkan wadda suka samu a kan hanya ya suma bi ta kan sa suke su wuce, duk kuma wanda suka sau茩ewa wanna gofaton kafar nan tasu, tofa namar sa daga'daga yake ya daddage, wasu ma har lumewa cikin kasa suke idan suka take shi, banda jini ba wani abun dake malala a tsakar gidan, sai fantsala musu a fuska da jikin jinin yake, amma da yake yan datti ne ko ajikin su basu damu ba.


Bayan sun tsaya a tsakiyar gidan ne suka fara jawo duk wata halitta dake cikin gidan suna fito da su, da tsafin su, sai dai kagan su fiw sun jawo mutun waje ya fito, haka suka jawo Mustapha ma fiw ya fito kamar iska, har da baba suka fito da shi, duk a tsakar gidan suka tara kowa, kafin su juya idon su ya koma kalar na tsafin su, wato light green, da tsafin nasu suka fara neman in da Rimsha take a cikin gidan, domin kuwa madubin Queen ya nuna musu babu Rimsha cikin wayan da suka tara a wajen, sai zazzaro ido suke suna jujjuya idon nasu gwanin ban tsoro da tashin hankali


Bayan Mustapha da duna da baba ba wata halitta mai rai da ta rage tana cikin hayyacin ta a gidan, har ita Rimsha 蓷in da duna ya 蓳oyeta bata cikin hayyacin ta, mai iya kallon su Gujungu ido hu蓷u kuma ya iya rayu bai mutu ba, tofa sai mai tsawon kwana kuma mai karfin imani, irin dai mutanen part 蓷in su Rimsha, dan sune masu imanin gidan, tun da har suka iya wace part 1 suka wuce part 2 suka zo nan to tabbas sune jiga jigan masu imani, dan mai raunin imani baya iya tsallake wa su Barbushi.


Can cikin duhu 蓷akin duna idon tsafin su ya hango musu Rimsha tana kwance tana ihu, da karfi, Gujungu ya fisgota, da tsafin sa zuwa tsakar gidan


Sa茩abo ne ya wage wanna gabjejen bakin nasa ya fara 蓳a蓳蓳aga dariya irin nasu na gunguma gunguman matsafa, nan take gidan ya 蓷auka da karfin sautin dariyar tasa, juyawa sukayi, suka nufi hanyar da sukabi suka zo, da tsafi suka fara jan Rimsha tana bin su a baya daga kwance, Allah sarki jikin ta sai kukkujewa yake a kasa tana ihu kamar ranta zai fita....



Share fisabilillah 馃憦


To masu karatu sai mun ha蓷u gobe idan mai dukka ya kai馃お


馃挒Star Lady馃挒

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.