Free chapter 路 Read without an account

Episode 32-33

by Fateema Zahra Musa 路 TRIPLETS (YAN UKU) BOOK 1 CMPLT

TRIPLET'S馃挒



***



馃挒 FATEEMA MUSA馃挒

(馃挒STAR LADY馃挒)




*Gargar蓷i*


_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book 蓷in nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a ha蓷amun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun ha茩茩ina_





WhatsApp me for more information ***







Episode 32-33




Sa茩abo ne ya wage wanna gabjejen bakin nasa ya fara 蓳a蓳蓳aga dariya irin nasu na gunguma gunguman matsafa, nan take gidan ya 蓷auka da karfin sautin dariyar tasa, juyawa sukayi, suka nufi hanyar da sukabi suka zo, da tsafi suka fara jan Rimsha tana bin su a baya daga kwance, Allah sarki jikin ta sai kukkujewa yake a kasa tana ihu kamar ranta zai fita.


Haka suka wuce da ita, duna yana ji yana gani dan kuwa babu abun da zai iya shima neman a kawo masa 蓷auki yake.


A wanna yanayi su Barbushi suka shigo part 蓷in suka same sa, kasan cewar mutumin sune kuma dole su taimaka masa saboda aikin da yake musu, cikin sauri suka 蓷auke sa suka wuce da shi, dan suje su nema masa ruwan tsafi wajen Queen ko kafafun nasa zasu gyaru.


Su Ayla kuwa bayan tafiyar su Barbushi Mustapha ne ya taso yazo ya taimaka musu ya jasu zuwa 蓷akin su, sanna ya mai da baba ma 蓷akin sa, ya dawo ya zauna shiru ya buga uban tagumi sai ha蓷a zufar wahala yake, yau yaga abun daya kwance masa notikan kansa, duk sai yaji duniya ta isshe sa, ban da addu'a a ransa babu abun da yakewa Rimsha, shi kan shi baba addu'a kawai yake mata tare da tausaya mata da kuma su Ayla idan suka tashi ya zasu ji a ransu ace musu an kashe Rimsha.


Haka baba da Mustapha suka zauna jugum jugum suka buga uban tagumi kamar wasu marayu, suna yiwa Rimsha addu'a.


Wanna kenan mu le茩o Washington DC mu dawo



馃挒WASHINGTON DC馃挒


9:20am


Sai sauri James yake ya sauko kasa daga saman bene, kamar wani mara gaskiya yana tafiya yana waigen bayan sa yana waya kasa kasa, jikin sa na sanye da suit ashe colar mai shegen kyau da tsada, kayan sun kara masa kyau sosai.


Dai dai tsakiyar palon yana waigen bayan sa bai ankara ba sukayi karo da wani bodyguard wadda ya 蓷auko tray mai 蓷auke da kyawawan glass cup wadda a ka cike su da drinks.


Gaba 蓷aya drinks dake cikin cups 蓷in nan suka kware a jikin James, zaro ido bodyguard nan yayi Allah sarki nan take jikin sa ya fara kerma, ya kasa magana saboda tsoro, James kuwa ransa ya 蓳aci iya 蓳aci, a fusace ya wanke wa bodyguard nan fuskar sa da wata mahaukaciyar mari, ji kake tass, dai dai lokacin Romeo ya sako kafar sa saman benen yana kokarin saukowa


Cikin jin haushi abun da James 蓷in yayi rai a 蓳ace ya dakawa James tsawa "Are you mad James!!? Tsabar tsorata da bodyguard nan yayi na tsawar da Romeo ya daka sai da zuciyar sa ta buga a wajen ya yanke jiki ya fa蓷i kasa gawa, Allah sarki ya 蓷auka shi Romeo ya dakawa wanna tsawar shiyasa ya tsorata haka har zuciyar sa ta buga ya mutu, dan dukka gidan idan Romeo yayi magana a hankali ma firgita su yake jikin su yayi ta kerma bare kuma tsawa ai sai mutuwa, criminals da dama tsawa Romeo ke daka musu zuciyar su ke bugawa saboda tsoro su mutu, dan duk wanda ya kwana ya tashi a Washington DC tofa yasan hukuncin GAR babu kyau, yasan GAR baya hukunci mai da蓷i, mutuwar tsoron sa jama'a keyi, ganin face nashi yana cikin farinciki ma razanar da hantar manyan maza yake bare kuma in ya 蓳ata rai, Subhanallah ba sai ya kai ga hukunta mutun ba tsawa kawai ya wada wa mutun zuciyar sa zata iya bugawa ya mutu, sai dai in mai sauran tsawon kwana.


Ganin bodyguard 蓷in ya fa蓷i kasa yasa James yayi saurin tsugunnawa yana ta蓳a shi, ina rai yayi halin sa, 蓷ago ido James yayi a tsorace ya kalli Romeo dake tinkaro su "He died" ya fa蓷a a razane, har cikin ransa Romeo bai ji da蓷in mutuwar bodyguard 蓷in ba, yasan dai jama'a da yawa a wajen suna tsoron tsawan sa, a wajen aikin su ma, wasu idan ya waro musu dara daran blue eyes na sa ya kalle su ma kawai suma suke, wasu criminals 蓷in ma da ance musu GAR ne zan yanke musu irin hukuncin da ya dace da su, a wajen suke mur蓷e wuyar su su kashe kan su, dan a cewar su, da hukuncin GAR gwara mutuwa, da GAR ya kalleka da fusatacciyar fuskar sa kamar wani lion 蓷in nan gara su mutu, bai ta蓳a tunanin bodyguard nasu na gida suna tsoron tsawar sa har haka ba, kasan cewar su bodyguard 蓷in wajen dining table ba sojoji bane, su kawai an ajiye sune dan mi茩a musu tissue paper da kuma ruwa da drinks sai serving nasu abinci.


Abun bai ma Romeo da蓷i ba, wuce wa kawai yayi ya nufi hanyar fita daga palon ba tare da ya kara tanka James 蓷in ba, yana fita ya turo jibga jibgan sojojin sa a kan suzo su 蓷auki bodyguard 蓷in su fitar da shi, aje a shirya sa zuwa mutuware,


Wanna ma ba cikin 蓳acin rai Lion yayi wanna tsawar ba, da ransa a 蓳ace yayi ta ina ga da har shi kan shi James 蓷in sai zuciyar sa ta buga.


Haka sojojin suka zo suka 蓷auki gawar bodyguard 蓷in suka fice da shi


Gaba 蓷aya James yaji ba da蓷i kuma ya 蓷aura alhakin mutuwar bodyguard 蓷in a kan sa, a cewar sa komai ya faru shine sila, da yayi hakuri bai mari bodyguard 蓷in ba da Romeo ba zai yi wanna tsawar ba, zai zo ne kawai ya wuce su ya fice daga palon, amma gashi yanzu saboda nuna masa kuskuren sa da Romeo ke kokarin yi yasa zuciyar bodyguard ya buga.


Jiki ba kwari James ya wuce ya koma bedroom na sa dan sake wanka ya canza kayan jikin nasa.


After some hours


Shirye cikin wando jeans baki three quarter James ya fito da riga Turtle high blue, kai tsaye wannan fili na Romeo ya nufa, dan yana da tabbacin suna can.


Da excuse 蓷auke a bakin sa, ya iso wajen, Romeo na zaune saman sofa daya saba zama yana latsa waya, while shi kuma Michael yana tsaye ya 蓷aure wasu kwala蓳e wadda Romeo ke 蓷aurewa sojojin sa idan suka masa laifi, sai ya 蓷aure musu wayan nan kwalabe suna lilo ya ce su ja baya sosai su saita kwalaben da bindiga su harbe su dukka su fashe su, kuma kwalaben ba tsaye suke waje guda ba ka蓷awa suke sosai suna lilo idan kayi missing na bullet 蓷aya baka fasa kwalbar nan ba, to horo mai tsanani Romeo zai baka, a koi wani ruwa mai kankara, gaba 蓷aya ruwan waje ice ne haka Romeo zai jefa ka ciki, ta kofar da yasa aka yiwa ice 蓷in, ka zauna cikin ice nan tsawon 3 hours kafin ya sa a fitar da kai ya sanya wasu sojojin su zane ka, kana rawan sanyi suna zane ka, idan suka maka kamar bulala hamsin sai a sake mai daka cikin ice 蓷in na 3 hours again, duk wanna hukuncin na missing bullet 蓷aya da kayi ne ba'a kai ga na laifin da kayi a ka kawo ka wajen harbin kwalaben bama tukun nan, wanna dalili yasa criminal da dama suke kashe kan su in dai suka san lion ne zai yanke musu irin hukuncin da za a musu, wanna ma idan yana farincikin kenan, duk wata kalar hukuncin mugun ta Romeo ya iya shi, gashi da zuciyar bala'i, ga kafiyar masifa idan yayi magana yayi ne ba wanda ya isa ya sanya shi ya sauya, baya mai mai ta magana idan yayi yayi ne, koda bakaji me yace ba to yazama dole kayi abun da yace dan ba zai mai mai ta maka ba idan kuma ba ka aikata abun da yace 蓷in ba hukun taka zai yi, ga bala'i zafin rai kamar wuta, ga zafin kai, ba mai iya tankwara shi ya canza masa abun da yayi niyar yi, babu wanna mahalukin dan shi kaifi 蓷aya ne, sannan miskiline na karshe, dan baya son magana, magana wahalan yi take masa, ga izzan bala'i idan ka masa magana sai ya dauki mintoci kafin ya amsa maka, bai son hayani, baya shiga tsabgar kowa, sannan bai yarda da kowa ba, sai Triplets na sa, da dad, su Uncle Herry, bayan su bai yarda da kowa ba, imma mace ko namiji.


茒aure kwalaben Michael yayi, sai famar harbin su yake da irin silent pistol gun 蓷in nan, wayan nan kananan bindigun marasa karan nan.


Michael ya karan da bullet sau uku, yana kare wa yana kara wani amma ko kwalba 蓷aya bai samu ya iya harba ba, saboda harbin wayan nan kwalabe ba wasa ba, sai wanda yaji training ya koshi, sai manyan jiga jigan sojoji masu saiti da kyau, Romeo na zaune yana ganin sa ta wutsiyar ido.


Wucewa James yayi har zai zauna kusa da Romeo, sai kuma ya fasa, ya nufi Michael tare da amsan gun 蓷in, kwata kwata ya manta sai abun ya masa kamar wajen ta'addancin su yake, sai ta kwalaben yayi ya fara har蓳i, tsabar iya saiti irin na James, kan kace me, ya fashe kwalaben nan dukkan, ba tare da yayi missing na bullet ko 蓷aya ba, ba wani bullet da ya fa蓷i kasa ba tare da ya fasa kwalbar ba, sosai abun ya bawa Romeo mamaki, dan kuwa wanna abun da James yayi kananan sojoji basu iya yin sa, horo ne mai wahala, dan ko Tga bai jima sosai da gama iya ire-iren wayan nan horon ba, abun ya 蓷an bawa Romeo mamaki, kallon tsab yayiwa James yana tunanin, a iya sanin sa dai James ko yadda ake ri茩e bindiga bai iya ba, dan bai koya musu ba, gara Michael ma daman shine mai karanbanin 蓷aukan kananan bindiga yace zai koyi har蓳i, amma James bai ta蓳a 蓷aukan gun ba ko da sunan wasa to tayaya ya iya harbin wayan abubuwan, kuma yayi harbin ne cike da kwarewa da kwarin gwiwa, kamar wadda ya 蓷auki 10 years yana kar蓳an horo.


Shi kuwa Michael rungume James yayi yana turo baki a shagwa蓳e yace "Why to ni na kasa harbin ko 蓷aya" raba jikin su James yayi yana fa蓷in "Baka mai da hankali ka sanya kan ka bane amma da zaka iya ai dan ba wahala" ya kai karshen maganar tare da wucewa zai zauna kusa da Romeo, sai lokacin idon sa ya sauka kan Romeo da ya tsare sa da dara daran blue eyes nasa yana kallon su da mamaki


Nan take James ya sha jinin jikin sa, dan kuwa yasan me Romeo ke wa mamaki, kwata kwata ya macen da ina yake shiyasa ya harbe kwalaben, kuma yasan wanna horo ne mai wahala, dan sai da yayi wata biyu yana koya kafin ya iya, dan ma yana da 茩wa茩walwa da basira shiyasa yayi saurin iyawa.


Cikin sauri ya kawar da kan sa daga kallon Romeo ya fasa zaman da zai yi ma, dan dama yazo ne ya sanar da Romeo zai je party a New York kuma ba zai dawo ba sai gobe karsu neme sa, a zahirin gaskiya kuwa Meeting na su na criminals zai je.


A nitse ya sanar da Romeo zai je party, shiru Romeo ya masa har lokacin bai 蓷auke blue eyes nasa daga kan James 蓷in ba, ganin haka yasa James ya sauka daga wajen ya nufi hanyar fita daga wajen yana fa蓷in sai ya dawo, cikin sauri Michael yace "wait for me I want to go to White House so mu fita tare kawai" shi dai Romeo ido kawai ya zuba wa James yana kokarin fahimter wani abu, tunani yake ai na James ya iya wanan harbi haka


Kasan cewar baya yi musu tambayoyi a kan abun da ya shafe su, sai yayi shiru bai tambayi James 蓷in ai na ya koyi har bi ba, idan ya ga wani abun da bai masa ba a tattare dasu bincike kawai yake da kan sa gani, baya tambayar su, har suka fice daga wajen bai dai na kallon suba.


Sai bayan sun tafi da jimawa sannan ya mi茩e ya bar wajen shi ma, ya koma cikin gida.


Michael kuwa, suna fita kai tsaye white house ya wuce, dan yau yace bari ya kaiwa president ziyara, tun daga bakin gate bodyguard da sojojin dake tsaron white house suka fara sara masa, ko kallon in da suke bai yi ba, da wata Winter Sports Hat nasa da yansa a kan sa, saboda yawan gashin kan sa, sai hat 蓷in tayi masa katuwa a kai.


Kai tsaye cikin ya wuce bai bi ta kan kowa ba, da fara'a President ya tare sa, sai tur蓳une fuska Micheal keyi kamar wadda aka sa shi zuwa dole, shiko president sai da蓷i yake ji, saboda murna ya rasa ina zai sa Michael, saboda kaunar da yakewa GAR ne ya shafi su Michael, yana son family William jacop sosai, kasan cewar kakan su Romeo jacop Roshan babban 蓷an siyasa ne kafin ya mutu, shiyasa suke da damar shiga ko ina a kasar ba wata shamaki sai ma girmamawa da suke samu daga manya manyan yan siyasa masu tasowa yanzu.


Wata dankareriyar diamond watch mai bala'i kyau da tsada president ya 蓷auko ya bawa Michael kyauta, first time da Michael ya cire diamond watch na su na Triplets ba barci zai yi ko wanka ba, kuma ya cire ne dan ya sanya wanda president ya bashi, saboda ya nunawa president yaji da蓷i.


Sosai president yaji da蓷in abun da Michael 蓷in ya masa, na cire diamond watch na su na Triplets da yayi ya sanya wadda ya ba shi, sosai agogon tayiwa Michael kyau kamar dan hannun sa a kayi ta, sanya diamond watch nasu na Triplets yayi a aljihun jacket nasa ya bar na president 蓷aure a hannun sa, suka ci-gaba da hira kamar wasu friend, bayan kuma president ya kusa jika da Michael, amma saboda son da yake musu, sai ya zama kaman friend nasu idan suka zo wajen sa.


Shi kuwa James kai tsaye wajen taron su ya nufa, a in da zasu gudanar da taro cikin dajin palace, a nan zasuyi taron, manya manyan criminals uban nin gidan su James sun hallara, sun zauna sai hira suke suna jiran saukowar sauran jiga jigan ogannin nasu, sai a fara taron.


Shi kuwa Romeo yana kwance saman lallausan katafaren gadon sa, yayi kwanciyar rigingine ya tasa system a gaba yana bawa yaran sa dake shirin tafiya yaki umarni, sai faman lumshe dara daran blue eyes nasa yake kamar mai jin barci, ga dadda蓷ar kamshin air freshener da sanyin Ac dake ta faman tashi a bedroom 蓷in nasa, gaba 蓷aya wutar 蓷akin nasa ya kashe farin wutar ya kunna sky blue, sky blue light 蓷in ba karamin karawa 蓷akin nasa kyau yayi ba, abun gwanin ban sha'awa da 蓷aukar hankali.


A 蓳angaren TGA kuwa, sosai wayan nan kwari suka masa illa, dan kuwa a kan gaban sa suka matsa wanna tsiyar, wajen ya kunbura sosai yayi jawur kamar jini ne a ciki, duk jarunta irin na soja sai da TGA yayi kuka, saboda ciwo a irin wanna waje ba karamin abu bane, yana da zafi sosai over, Allah sarki bawan Allah ko wando baya iya sawa saboda azaba, ga sanyi Ac amma duk da haka sai daddy ya kunna rechargeable fan ya kawo masa sai tin gaban nasa yana shan iska saboda azaba, shi ka蓷ai kwarin suka yiwa irin wanna lahani mai muni sosai haka, duk wannan hali da TGA ke ciki Romeo bashi da matsani dan yana can ya nitsa cikin aikin da yake.


Mu le茩a Jehan mu dawo


馃挒KATSINA馃挒


Yau ya kama Monday, tun 8 na safe a ka shiga da mum 蓷akin da za'a mata aiki, while ita kuma Jehan ta shirya tsab cikin wata dakakkiyar atamfan ta super wax mai bala'i kyau 蓷inkin riga da skit, kayan sun zauna a jikin ta sosai, sunbi shape 蓷in coca colan ta sun mata 蓷as, kasan cewar bata son 蓷ankwali ma bare hijabi hakan yasa ta 蓷auki 蓷an karamin Malaysian hijab 蓷in ta pink color tare da takalmi pink color, ta 蓷auko jakar ta suwaga shi ma pink color ta fito tsakar gida, ba karya duk da cewa fake face ne a fuskarta ba 茩aramin kyau tayi ba sai kamshin sauran perfume da ya rage mata take.


Kai tsaye kitchen ta nufa wajen maman Sadiq, suka gaisa sanna maman Sadiq ta mata addu'ar fatan fara aiki a Sa'a, yar murmushi tayi ta amsa da amin sanna ta fito daga kitchen 蓷in da sauri saboda hayaki.


Tana fitowa sukayi karo da Sadiq yana kokarin shiga kitchen 蓷in, 蓷an baya ka蓷an tayi tana fa蓷in "Good morning" zuba mata ido yayi yana kallon ta yana mai kara jin kaunar ta a ransa, tab lallai ita kuwa Jehan babu wani abu wai shi soyayya a ranta, bata san shi ba, kuma bata da wani ra'ayi a kan soyayya, ita da namiji da mace duk kallon abu guda take musu, namiji baya gaban ta, maza basu isshe ta kallo ba, kai har matan ma ita a wajen ta basu isshe ta kallo ba, bata ta蓳a kawo wani abu wai shi tunanin aure ma a rayuwar ta ba, a nata wautan har ta mutu dasu mum 蓷in ta kawai zata yi rayuwa.


Ganin Sadiq ya zuba mata ido ne yasa ta ra蓳a gefen sa zata wuce, cikin sauri yace "Jehan dan Allah ki koma ki cire kayan nan ki sanya uniform da suka baki karki ja su hana ki aikin nan, kuma kinga dai akoi bashin ku蓷in aikin mum a kanki ta wanna aikin ne kawai zaki iya biyan bashin da ake binku, to dan Allah karkiyi sanadin rabuwar ki da aikin nan kar kiyi wani kuskuren da zasu kore ki daga wanna aiki" ba tare da ta kalle sa ba, a takaice tace "I can't wear this uniform" girgiza kai Sadiq yayi kafin yace "Kiyi hakuri ki sanya jehan" cike da izza tace "Babu wanda ya isa ya za蓳a min abun da zan yi a rayuwa ta, ba zan sanya wani banza uniform nasu ba, ai ba sayata sukayi ba da zasu ce abun da suke so zanyi, ni Jehan babu wani da ya isa ya min iko da rayuwa ta bayan dad and mum, ko gwaggo lalla蓳ani take in tana son nayi abu, so kayan nan nayi niyar sawa babu kuma wadda ya isa ya sanya na canza" ta kai karshen maganar tare da sa kai ta nufi hanyar fita daga gidan.


Dawo da kallon sa Sadiq yayi kan maman sa dake tsaye a cikin kitchen ta zuba musu ido tana kallon ikon Allah "Ina kwana mama?" Ya fa蓷a yana sunkuyar da kai, dan yaji kunya ashe mama na tsaye tana kallon sa yadda ya zubawa Jehan ido, da fara'a maman sa ta amsa masa.


Bayan sun gaisa ne ya mata sallama ya wuce yabi bayan Jehan, sai addu'a mama ke musu da fatan alkhari, yana amsawa da amin amin ya wuce.


A 蓳angaren Jehan kuwa tana fitowa wajen gidan tayi karo da baban Sadiq yana shigowa, ko kallon in da yake ba tayi ba ta wuce, zata wuce shi ne yace "Sannun ki yarinya" yauwa kawai tace masa ta wuce tana 蓷aure fuska kamar wadda a ka aikowa da sakon mutuwa, dan haka kawai taji ta tsani baban Sadiq 蓷in nan bata son shi, kawai tana masa karane saboda Sadiq.


Jehan uwar dirama ta koyawa baban Sadiq da amarya hankali, yanzu amarya har gaishe da su Maman Sadiq take da safe, kuma yanzu sun 蓷an samu zaman lafiya da fitinar amarya, ta daina takurawa kowa dake gidan, ta shiga hankalin ta da kyau saboda tsoron aljanu, wanna shine idan baka yi sharan masallaci ba kayi na kasuwa, duk iskancin ka akoi baban ka.


Jehan zata wuce ta nufi bakin hanya ne, sai taga Hanan zaune gaban murhun gawayin ta na tuyar awara ta kifa kai da gwiwa tana kuka, da kamar ba zata kula taba zata wuce dan ita ba mai shiga harkan mutane bane, idan kuma ka kuskuren shiga nata harkan sunan ka sorry, dan Jehan ba sauki.


Kasan cewar Hanan yarinya ce so silent bata da hayaniya kuma bata neman magana hakan yasa Jehan ta matso kusa da ita tare da dafa kafa蓷ar ta tana fa蓷in "Ke lafiya kike kuka haka?" Yar firgigit Hanan tayi tare da 蓷ago kan ta idon ta sunyi jawur kamar jini saboda kukan da tasha, "Subhanallah lafiya kikayi irin wannan kuka haka?" Cewar Jehan tayi maganar tana tsugunnawa kusa da Hanan 蓷in, dai dai lokacin Sadiq ya fito.


Da sauri ya kariso wajen su yana fa蓷in "Lafiya Hanan me ya same ki?" Cikin kuka Hanan ta fara yi musu bayani "Wani Alhaji ne dake yawan zuwa wajen nan sayan awara, yaya Sadiq ba ka san shi ba? Wannan mai farar 茩atuwar motar nan?" Gya蓷a mata kai Sadiq yayi yana fa蓷in "Eh na san shi me ya faru? Wani abun ya mi茩i ne?" Ci-gaba da magana tayi tana kuka "To daman yace yana sona kuma ni bana son shi, kullun idan yazo nan ba sayan awara yake ba, kune kuke ganin kamar awara yake saya, hira kawai yake zuwa sai in ya tashi tafiya ya bani ku蓷i, to ni bana kar蓳an ku蓷in sa, ce masa nake bana so, yayi ta ha蓷ani da Allah naki kar蓳a dan ni tsoron masu ku蓷in nan nake, watarana baba yazo wucewa sai yaga Alhajin yana bani ku蓷i naki kar蓳a yana ro茩ana na kar蓳a, shine da baba ya ga haka sai yayi sauri yazo shi ya kar蓳e ku蓷i daga hannun Alhajin ba tare da an bashi ba, ya fara washe baki yana zubawa Alhajin godiya, Alhajin ya fito zai masa fa蓷a akan me yana bani ku蓷i shi kuma zai wani sanya hannu ya kar蓳a, sai nayi saurin cewa Alhajin baba nane, shine Alhajin ya kyale sa ya kara masa wani ku蓷in ma har da wani cewa baban ki kam ai baban nane, tun daga lokacin da baba yaga motar Alhajin yazo zai zo ya zauna a zaure yana jiran Alhajin ya bani ku蓷i ya tafi shi kuma yazo ya kar蓳e ku蓷in, ni wanna dukka bashi ne damuwa ta ba, damuwata shine kullun idan Alhajin yazo sai ya rin茩a yimin maganar banza, wai in munyi aure a ranar farko zai bani ciki, idan na nuna masa bana son maganar sai yace ai yana son ya koyamin yadda akayi ne tun yanzu dan na iya kar sai munyi aure naje na kasa yi masa abun da yake so, kuma sai ya rin茩a cemin ya kamata na rin茩a binshi muna fita zuwa hotel, ko gidan sa, bashi da wata magana sai na banza, idan nace bana so sai yace zai fa蓷a wa babana ina zagin sa, kuma kasan halin baba tun da Alhaji na basa ku蓷i duk abun da Alhajin ya fa蓷a masa yarda zai yi ya haukai ya zauna ya kamani ya min duka, saboda tsoron hakan yasa kawai nayi shiru ina sauraron maganganun banzan da Alhajin yake fa蓷amin, jiya da daddare Alhajin yazo lokacin kuna cikin 蓷akin mama kuna hira, baba yasa na fito dan muyi hira da Alhajin, dana fito Alhajin yace na shiga motar sa muyi hira naki, yace dole na shiga ai shi mijina ne tun da baba ya bashi aure na, kuma idan ban shiga ba sai ya fa蓷awa baba, ina tsoron ya fa蓷a wa baba shine na shiga na zauna, haka ya rin茩a ta蓳a min kirjina yana wasa da su har da gaba na ya rin茩a sa hannun sa yana wasa da shi, har yanzu sai zafi suke min, da kyar ya barni na dawo cikin gida bayan ya gama wasa dani, na rasa wazan fa蓷a wa, tunjiya da daddare nake kuka yau da zazza蓳i na tashi, babban abun da ya sake sani kuka yanzu, shine ina fitar da wanna murhun zan fara tuya, sai ga Alhajin yazo, wai jiya yaji da蓷i kuma ya kasa barci na tayar masa da hankali dan haka na shirya anjima zaizo ya 蓷auke ni, muje gidan sa mu 蓷an huta, ina cikin fa蓷a masa ba zanje ba sai ga baba yazo zai shiga gida, da yaga Alhajin shine yazo suka gaisa, nan fa Alhajin yace masa wai yace zaizo ya 蓷auke ni muje shopping ya sai min kayan arziki nace bana so, shine baba ya mare ni, ya rin茩a fa蓷a wai dole nabi Alhajin ko kwana ma yace zamuyi ba sai maje mayi ba, bare kuma kaya kawai zai saya min mu dawo, dan munafurci irin na Alhajin nan sai bawa baba hakuri yake wai baba ya dai na yimin fa蓷a baya so ana yiwa matar sa haka, sanna ya ciro ku蓷i dayawa ya bawa baba ya shiga Motar sa ya tafi yana fa蓷in karfe 蓷aya na rana zaizo ya 蓷auke ni, baba kuma ku蓷in ne kawai damuwar sa, yana kar蓳an ku蓷i ya wuce cikin gida yana fa蓷in dole ma ta bika ai shegiya mai kashin tsiya arziki na bin ta tana gudu, abun yamin ciwo shiyasa nake kuka dan nasan idan nabi Alhajin nan wlh shikenan zai rabani da mutunci na" ta kai karshen maganar tare sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.


Ba laifi Jehan ta fahimci abun da ta fahimta a zancen Hanan 蓷in, ta gane in da zancen nata ya dosa, duk da cewa wasu abubuwan bata gane su ba, 蓷ago ido Jehan tayi ta kalli Sadiq.


Kara zaro ido tayi tana kallon Sadiq 蓷in, lokaci guda kamannin sa sun sauya, idon nan nasa sunyi jawur zuciyar sa na tafasa ji yake kamar yaje ya sha茩e baban sa ya kashe sa dan haushi, tunani yake a ransa yanzu yana cikin gidan nan jiya wani katon banza yazo yana matse masa kanwa, wani ihu yayi kamar mahaukaci cikin fushi yace "Aina Alhajin yake?" Ita ma Hanan ba karamin tsorata da ganin Sadiq a haka tayi ba, dan tasan Sadiq mutun ne mai hakuri ga murmushi ba zaka ta蓳a ganin fuskar sa a 蓷aure ba, duk damuwa da matsalar da gidan su ke ciki, kullun cikin murmushi yake.


Murya a dashe saboda kuka da tayi Hanan tace "Nima ban san in da Alhajin yake ba" a fusace Sadiq yace "Jehan tun da kin san hanya kije wajen aikin kawai, idan kin taso ki wuce asibiti, ni zan tsaya a nan ba yace karfe 蓷aya zaizo ya 蓷auke taba, to zan jirashi, idan kinje hospital ki gaishe min da gwaggo da jikin mum sai da yamma zan zo in 蓷auke ki mu dawo" mi茩ewa tsaye Jehan tayi kafin tace "Yaushe ake tashi daga restaurant 蓷in?" Shiru ya 蓷an yi kafin yace "Inaga ku yan safe karfe 蓷aya zaku tashi, sai yan yamma su kar蓳e ku, amma dai in kinje ki kara tambayar Ibraheem" jinjina kai Jehan tayi kafin tace "Okey koma karfe nawa ake sallamar mu, ni dai by 1 dole zan dawo, dan inason in bawa Alhajin nan capital warning" tsabar bakin ciki da 蓳aci rai sun hana Sadiq bawa Jehan amsa, dan ji yake kamar zuciyar sa zata buga saboda haushin abun da Alhajin nan yayiwa Hanan.


Komawa Jehan tayi ta tsuguna ta gogewa Hanan hawaye, tana bata hakuri tare da mata alkawarin ba zasu bar Alhajin ya 蓷auke taba.


Sai da ta tabbatar Hanan tayi shiru sanna ta yiwa Sadiq sallama ta wuce bakin hanya dan tarar abun hawa ta wuce restaurant, yau asibiti ma sai ta taso daga restaurant zata biya ta can, gashi sai tunanin mum take, dan an shiga da ita 蓷akin da za'a mata aiki.


馃挒SUPER RESTAURANT馃挒


Tana shigowa kai tsaye reception wajen Ibraheem ta nufa, tun daga nesa Ibraheem 蓷in ya hangota, ganin bata sanya uniform nasu ba yasa ya 蓷aure fuska ya 蓳ata rai sosai, dan yasan ogan su ba zai yarda da rashin sanya uniform 蓷in ba.


Tana karisowa wajen sa tun bata yi masa magana ba yace "Ina uniform naki? Me yasa baki saka ba?" 茒aure fuska sosai ita ma tayi kafin tace "Ai tun jiya na fa蓷a maka ba zan sanka uniform 蓷in ba, au kai daman ka 蓷auka wasa nake maka, to idan ma baka sani ba ka sani ni Jehan bana fa蓷an abun da nasan ba zan aikata ba, garama kasani tun yanzu idan nace ba zanyi abuba tofa da gaske nake ba zan yi shi bane" tsabar haushi Ibraheem bai san lokacin da ya 蓷aga hannu kamar zai mare ta, sai kuma ya dakata yana wani huci, yariya yar karama kamar wanna ta tsaya tana fa蓷a masa magana, gently tace "Ya ka dakata? Ai da ka marenin ina ga zai fi" shiru Ibraheem yayi yana mai dana sanin taimaka mata da yayi.


Ganin yayi shiru ne yasa tace "Menene aiki na? Ka fa蓷a min naje na fara yi dan ina son tafiya gida karfe 蓷aya dai dai" zaro ido yayi yana kallon ta da mamaki, wato ita ma zata yanke wa kan ta hukunci ga lokacin da zata tafi cab lallai aiko aiki dole na koyawa yarinyar nan hankali.


A fusace ya bu蓷e baki zai yi magana, wayan dake gaban sa saman table ta fara kara, dogon tsaki yaja tare da sa hannu ya 蓷auki wayar, irin wayar nan ne da ake ajiyewa saman table wadda costumers ke kira dan bukatar abu. Picking na call 蓷in yayi tare da kara wayar a kunnen sa.


Jim ka蓷an ya ajiye wayar ya 蓷ago ya kalli Jehan yace "Kije room 22 akoi wani costumer da yake bukatar ma aikaci 蓷aya" rai a 蓳ace tace "to me zan masa" mai da wayar yayi ya ajiye yana fa蓷in "Idan kinje ai koma menene zakiji" guntun tsaki taja ta wuce ta tafi ta bar Ibraheem da binta da ido yana mamaki.


Ko da taje bakin kofar Room 22 蓷in sai da taja dogon tsaki kafin tayi knocking na kofar, bugu 蓷aya tayi aka bu蓷e kamar daman jira ake.


Wani Alhaji ne kato bakin kirin da shi gashi da katon ciki, yana sanye da gajeren wando, kaya ya mi茩o mata yana fa蓷in "Wanki ne zaki min" zaro ido tayi ta kalle sa kafin ta kalli kayan dake hannun sa yake miko mata, singlet and boxers ne, dawo da kallon ta kan face nasa tayi a kule tace "Yanzu saboda baka da hankali nice zan wanke maka shot naka? Ko kunya baka ji ba kato da kai, hauka nake zan wanke wandon kato kamar ka, tab lalai to Jehan dai ba za tayi wanna kazantar ba sai dai wata, daman wanna aikin shine aka kawo ni nayi, to wlh ba zata saku ba, ba zan iya ba"


Tashin hankali zaro idon mutumin yayi kafin ma yayi magana, Jehan ta sa kai ta wuce ta bar wajen, da sauri mutumin ya le茩o da kan sa waje yana kallon ta, mamaki ya sa ya kasa komawa cikin 蓷aki, a ransa yana fa蓷in "wannan yar yarinyar dai a shekaru da wuya ta wuce sha bakwai tsawo ne kawai gare ta, shine zata cemin katon banza, anya wannan a gaban iyayen ta ta taso kuwa, anya ta samu tarbiya, to wlh ba zan zauna a hotel 蓷in nan ba, basu san darajar costumer ba, har ma'aikaciya tana da bakin cewa costumer ba zata yi masa abun da yake so ba, tab lalai da sake" da wannan tunani ya koma cikin 蓷aki ya 蓷auki waya ya sake kiran Ibraheem,


Ita kuwa Jehan kai tsaye wajan sauran ma'aikatan tan restaurant 蓷in ta nufa dan ta tambaye su ko shine aikin da suka zo yi kenan wato wankin kayan costumers.


Da sallama 蓷auke a bakin ta ta karisa wajen da sauran ma'aikatan ke zaune, har suna rige rigen amsa mata sallamar nata, sunga kyakyawa, dan Jehan akoi farinjini na fitar hankali, duk in da taje sai an so ta, haka itama Rimsha


Sai wani washe baki ma'aikatan suke suna 蓷aga mata gaisuwa, ita kuwa kara 蓷aure fuska tayi kafin tace "dan Allah zaku iya fa蓷a min aikin me muka zo yi a nan?" Kallon kallo suka fara yiwa junan su, lallai wato wanna ma bata san aikin da ya kawo ta nan ba tab akoi cakwakiya.


茒aya daga cikin sune ta mi茩e ta dafa kafa蓷ar Jehan ta fara yi mata bayanin irin aikin da ya kawo su nan "Wanke wanke, shara, mopping, kai wa mutane abinci idan suka zo ci, sanna kaiwa yan 蓳angaren hotel abinci room nasu idan suka bu茩ata, wasu costumers 蓷in zasu bu茩aci mu musu wanki su biya mu, wanna ma yana daga cikin aikin mu, sanna dole ki san ta yadda zakiyi wajen kontarwa da costumers hankali har suji da蓷in wanna restaurant 蓷in gobema su dawo cin abinci, dole ki koyi sakin fuska da murmushi dan jawo ra'ayin costumers su sake dawowa cin abinci, danna dol.... Bata kai karshen maganar ba Jehan ta dakatar da ita ta hanyar cewa "Ya isa haka, da yake sayata sukayi ba ai dole su ce nayi kaza nayi kaza, to wlh ni idan ba kaiwa costumers abinci ba, ba wani aiki da zanyi a nan, dan ni Ibraheem bai cemin da Hotel ba iya restaurant yace min, kuma a restaurant 蓷in ma iya serving abinci kawai ya cewa iyaye na, dan haka iya shi kawai zan yi" ta kai karshen maganar tare da juyawa ta bar wajen ta nufi wajen girkin restaurant 蓷in. Mamaki ya hana sauran ma'aikatan magana, yau sun ha蓷u da abun da yafi karfin su.


A hanyar ta na zuwa wajen girkin restaurant 蓷in ne suka ha蓷u da Ibraheem, rai sa a matu茩ar 蓳ace, cikin tsawa yace "Ke zonan!!" Ba musu taje "Ke dan uban ki baki da mutunci ko? Baki da albarka ko? Mu rufa miki asiri mu 蓷auko ki mu kawo ki nan dan ki samu abun da zaki rufawa kan ki da iyayen ki asiri, shine bai miki bako? Yanzu dan baki da kirki baki da albarka costumer kikaje kikayiwa 蓷iban albarka haka eh? Keda muka kawoki dan ki jawo mana costumers shi ne zaki kora mana wayan da muke dasu ko? To wlh baki isa ba dan uban ki, tun wuri kije ki bawa mutumin nan hakuri ki kar蓳o kayan sa kizo ki wanke idan kina son zaman lafiya kinji na fa蓷a mi茩i!!!"


Tsare sa da wayan nan dara daran idon nata tayi babu ko kyap tawa, har sai da ya kai aya a maganar tasa, sannan gently tace "Ba zan yiwa wani katon banza wanki ba, dan ba wanna aikin mukayi da kai ba, masu sayan abinci kawai zan kaiwa abinci idan sun zo saya, bayan su ba wani aikin da zanyi, sai kuma maganar uniform karka sake min maganar sa dan ba zan saka ba" ta kai karshen maganar tare da wucewa ta nufi in da take da niyar zuwa wato wajen girkin su.


A fusace Ibraheem ya bi ta ya je ya sha gaban ta, dan yana takamar ya ranta mata 500k ne yasa ya 蓷aga hannu a fusace zai mare ta, cak ta rike hannun sa, cikin fushi ta 蓷aga hannu zata mare sa, sai kuma ta fasa saboda ta tuna da cewa ko ba komai ya taimaka musu ya basu aron ku蓷i gashi yau ana yiwa mum aiki saboda shi, dan haka bai kamata ta masa irin wannan rashin kunya ba.


A hankali ta sake masa hannu sa tare da sauke nata hannun cike da 蓳acin rai tace "Ina ganin mutuncin ka amma kana neman ka kaini bango, ka kiramin ogan naka zanyi magana da shi, domin kuwa bashi da iko dani, daga yanzu ba zan sake yin magana da kai ba, da ogan ka zanyi magana, dan na lura duk wanna hargagan da kake kana yin sane dan tsoron kar ogan ka ya maka fa蓷a a kan ban sanya uniform ba dan sauran su, to ni ka kiramin shi bari na masa bayani da baki na, a kan cewa ba zan saka uniform 蓷in ba, kuma iya kai abinci zanyi, sanna shawara da zan baka shine, ka daina jin tsoron wani 蓷an adam kamar kai, kaji tsoron Allah ka蓷ai, idan kana jin tsoron Allah tofa babu wani 蓷an adam da zai baka tsoro ko ya maka wani abun da Allah bai kaddara maka ba, bana son hayaniya amma kana son sani cikin ta, bana son yawan magana shima kana sani yi, please ina ganin girman saboda taimakon da ka mana, dan Allah ka fita harka ta!!!" Tana kai karshen maganar ta wuce ta bar Ibraheem yayi mutuwar tsaye a wajen, yau ya 蓷auko wadda ta fi karfin sa



Share fisabilillah 馃憦


To masu karatu sai mun ha蓷u gobe idan mai dukka ya kai馃お


馃挒Star Lady馃挒

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.