Free chapter · Read without an account

36-37

by Fateema Zahra Musa · TRIPLETS (YAN UKU) BOOK 1 CMPLT

TRIPLET'Sđź’ž




đź’ž FATEEMA MUSAđź’ž

(đź’žSTAR LADYđź’ž)



*GargarÉ—i*


_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_





WhatsApp me for more information ***







Episode 38-39



Jehan na isowa wajen kai tsaye wajen Sadiq tanufa, yana sunkuye kamar yayi ruku'e ya sunkuyar da kan sa yana kallon kasa kamar mai yin kuka, tana zuwa ta fara tambayar sa abun dake faruwa, cike da damuwa da tashin hankali ya É—ago kai ya fara bata labarin abun da yake faru, baban sa ya tara musu jama'a wai basa jin maganar sa mijin Hanan zai fita da ita suje sayayya shi Sadiq É—in ya hana, É—agowa Jehan tayi ta kalli Alhajin.


Kara zaro ido tayi tana kallon sa tabbas tasan wannan fuskar amma ai na ta mance, shiru tayi tana tunanin ai na ta san wannan fuskar


Ganin ta zubawa Alhajin ido tana kallon sa tayi shiru ne yasa Sadiq yace "Jehan lafiya" dago da kallon ta kan Sadiq É—in tayi tana girgiza kai alamar babu komai, shesshekar kukan hakan yasa ta juyo ta kalle ta


A takaice tace "Hanan tashi ki shiga gida" ƙin tashi Hanan tayi dan tana tsoron baban ta, Jehan ta fahinci abun da Hanan ɗin ke nufi, dan haka sai ta dawo da kallon ta kan baban Sadiq wadda yayi shiru saboda zuwan Jehan, yana tsoron aljanun Jehan na dare shiyasa yayi shiru


"Kace mata ta shiga gida" Jehan ta faÉ—a tana kallon baban Sadiq É—in, ba musu baban Sadiq yace "Tashi ki shiga cikin gida Hanan" da gudu Hanan ta tashi ta shige cikin gida, dan dama kamar a kan kaya take zaune.


"Baba ya zaka ce ta shiga gida ban gane ba" cewar Alhajin, shiru Jehan tayi tana kallon su tana son taga ya zasu kare


Cikin girmamawa baban Sadiq yace "Kayi hakuri Alhajin wani lokaci zaku je yanzu dai ka kyale ta" da sauri Alhajin yace "A'a baba ni yau nake son muje, yau nayi niyya" satar kallon Jehan baban Sadiq yayi kafin yace "Dan Allah kayi hakuri Alhaji" girgiza kai Alhajin yayi yana faÉ—in "Ina ba zai yiwa ba gaskiya kawai ta fito mu tafi" sai hakuri baban Sadiq ke bashi amma Alhajin nan ya murje ido yace sam bai yarda ba dole Hanan ta fito su tafi.


Da dai Alhajin yaga da gaske baban Sadiq ba zai kira Hanan tazo su tafi ba, sai ya fara masifa yana faɗin baban Sadiq ya karɓe masa kuɗin sa akan ya bashi Auren Hanan, to wlh ba zai yarda ba dole yau Hanan ta fito su tafi,


Yadda zaka gane da wata manufa a ran sa game da Hanan É—in shiyasa ya dage a kan tazo su tafi.


"Hanan ba zata fito ba kuma daga yau ma karka sake zuwa wajen Hanan idan ba haka ba duk abun da muka maka kai ka ja ma kan ka" cewar DPO wato Jehan, tayi maganar cikin kwanciyar hankali, kallon tsab Alhajin ya mata kafin yace "Idan Hanan ba zata zo ba ke zaki zo kenan? Dan naga kin fi Hanan ɗin hankali zaki fita iya zaɓen kayan sai mu tafi dake kawai a bar hanan ɗin" karo na farko da Jehan ta saki murmushi a rayuwar ta na yanzu, dan ita ko lokacin da suke tare da daddy ba ta murmushi bare dariya haka face nata yake a ɗaure tamau.


Matsowa ta ɗan yi gaba kaɗan kasa kasa tace "Anya zaka iya fita da Jehan kuwa?" Tayi maganar tana murmushi, shiru Alhajin ya ɗan yi kafin yace "Amma ke kin san me kika faɗa kuwa" kashe masa ido ɗaya tayi kafin tace "Eh niko na san me nake faɗe cewa nayi mu tafi, idan zaka iya fita da ni, Jehan a shirye take" Tashin sense, shiru Alhajin yayi Jehan ta jefa sa cikin tunani, "anya wannan yarinya lafiyar ta kuwa, kai ina ga bata san me na shirya a tafiyar bane shiyasa amma bari na gwada ɗaukan ta muje in gani, idan bata san me na shirya ba, na samu ɓagas daman tafi Hanan komai da komai zan more tsuntsu daga sama gasashen" duk Wannan zancen a zuciyar sa yake sakawa.


Yana cikin zancen zucin nasa ne muryan Jehan ta katse shi da cewa "Ko dai ka manta baka kama hotel ɗin bane? Au sorry na manta fa ashe gidan ka zamu je ba hotel ba, amma ina son sani wani abu ɗaya kafin mu tafi, a gidan naka babu kowa ko, ma'ana iyayen ka ba a nan suke ba ko? Dan ban cika son hayani ya ba" tashin hankali, wani irin dukan uku uku gaban Alhajin nan yayi, tunani ya kara shiga "Anya wannan yarinyar mutunce kuwa? Ita da kan ta ta kawo kan ta, to gaskiya ba lafiya take ba, kila tana da wani ciwon dai, dan mace mai lafiya kuma cikakkiyar mace kamar wannan ba zata miƙa kan ta haka ba, gata da ka ganta kaga cikakkiyar mace mai addini to meke shirin faruwa ne"


Su Sadiq dai yau suna ganin ikon Allah


Ganin yayi shiru yasa Jehan ta kara matsowa kusa da shi, kasa kasa tace "Farooq Salahuddeen Abubakar, right?" Zaro ido waje yayi yana kallon ta da mamaki ai ina ta san shi


Bai gama tunanin sa ba muryan ta ta katse shi da cewa "Me yasa kayi shiru? Ka tsorata ne? To karkaji komai, amma dai ya kamata kasan wani abu guda, duk abubuwan da kayiwa Hanan jiya da daddare munyi audio recorded na voice naka, sannan duk wasu maganganu da kake mata a nan duk munyi recorded, dan kullun idan ka zo tana kunna karamar wayar ta tayi ta recording, so ina son ka sani idan ka sake dawowa cikin garin Katsina wlh sai na baza wannan recorded É—in wa duniya kowa yaji, kasan dai ba wanda bai san muryan ka ba ko? Dan kullun kuna hawa kaban mike kuyi ta shirgawa mutane karya, kowa ya sheda wannan É—an iskan muryan naka kamar na karuwar akuya, ka baro Abuja kana bin kauyuka kana lalata Ć´aĆ´an mutane, dan bakin iyaye na bin ka ko? To mu nan munfi karfin yaro sai dai baban yaro wato Salahuddeen Abubakar ina ga shine dai dai mu, wato yanzu kun dai na neman mata a manyan birane saboda gudun cututtuka, sai ku shiga kauye ku yau dari Ć´aĆ´an talakawa da sunan aure ku lalata musu rayuwa ku gudu ku barsu, wasu ma da ciki zaku gudu ku barsu, ayi ta haifan Ć´aĆ´an da basu da uba suna tashi cikin wahala da kuncin rayuwa, ba ilimin boko bare Arabic, da sun girma su zama yan shaye shaye dan ba ilimi, saboda ire iren ku zan zama yar sanda, duk sai naci Kutumar uban ku, na tarwatsa muku tunani yan iska banza" duk wannan magana tayi shine cikin harshen turanci


Tun da ta fara magana Farooq ya tsare ta da ido yake ta faman haɗiyar wahalallen yawu, sai zazzaro ido waje yake kamar wani ƙasurgumin munafuki, tunani yake wace ce Jehan, ai na kuma ta san shi farin sani haka, wayan nan tambayoyin duk ita ya dace yayiwa sai dai ba dama, dan cikin sa ya ɗuri ruwa, musamman da yaji sun yi recorded abubuwan da yayi ta faɗe a matsayin sa na kanin babban ɗan siyasa, idan wannan abun ya fita yake nan, gashi kuma ba wanda bai san voice na saba, wasu ma a media har tsokanar muryan nasa suke, saboda yana magana da sauri sauri kuma muryan tasa kamar na yar baby, irin munafukan muryoyin nan gare sa.


A ɓangaren su Sadiq da sauran yan anguwa kuwa, sun zubawa Jehan da Farooq ido, sun kasa kunne suna son jin me Jehan take faɗawa Farooq, sai dai basu samu damar ji ba, dan ƙasa ƙasa Jehan tayi maganar saboda ita da kan ta bata son fitina, bata son kowa ya gane wace ce ita, kuma da turanci tayi maganar.


A ruÉ—e Farooq ya shiga motar sa ya kunna, har lokacin yana kallon cikin idon Jehan yayin da itama take kallon cikin idon sa, sai dai Farooq ya kasa gane wace ce saboda fake face dake fiskar ta yasa bai gane wace ce ba, amma bashi da wani burin da ya wuce ya gane wace ce Jehan ai na kuma ta san shi, dan shi bai cika wani fitowa gidan Tv ba, sai dai ya taya yayan sa kanfen da muryan sa kawa, amma dai dayawan mutane sun san shi, sai dai ba kowa ya damu da fuskar tasa ba dan ba shi ne mai neman takarar ba yayan sane, tunani É—aya yake, ko ma wace ce Jehan makusanciya ce a gare shi dan wannan sanin da ta masa ba sanin wasa bane farin sani ta mi shi.


Ko uppan ya kasa cewa Jehan ya ja motar sa ya bar wajen yana tunanin ko dai kashe Jehan zai sa ayine, dan in wanna voice É—in nasa ta fita shikenan ya gama yawo yayan sa ma ba zai bar shi ba, da tuni fal ransa na ya zai yi da Jehan, ya zai yi ya kwace Audio sa dake hannun ta haka ya bar layin gaba É—aya tunani cike da ran sa, sai dai abun da bai sani ba ba wani recording da Jehan ta masa, kawai ta shirga masa karya ne dan ta ceci Hanan.


Bayan ya tafi ne Sadiq ya matso wajen Jehan, dan tana tsaye tana bin motar Alhajin da kallo har ya bar layin nasu.


"Jehan me kika ce masa haka, naga ya tafi da sauri kuma yana cikin tashin hankali har haka?" Cewar Sadiq, kamar jira Jehan take a mata magana ta juya da sauri ta wuce cikin gidan.


A zaure ta wuce su maman Sadiq sunyi cirko cirko suna leƙo abun dake faruwa, kai tsaye ɗakin maman Sadiq ta wuce, ta faɗa saman yar katifar maman Sadiq ta hau kuka kamar karamar yarinya.


Tashin hankali yau ga DPO Jehan tana kuka meke faruwa muje zuwa.


A tare Sadiq da maman sa suka biyo bayan ta, kusa da ita maman Sadiq ta zauna yayin da shi kuma Sadiq ya zauna ta bakin kofa, in da ya saba zama.


A hankali maman Sadiq ta shafa kan ta tana faɗin "Lafiya Jehan meke faruwa? Me ya saki kuka" ɗago wa tayi cikin kuka tace "Daddy na na tuna, Farooq ya tunamin da daddy na" ka san cewar su maman Sadiq sun san wace ce ita sai bata ɓoye musu waye Farooq ba da kuma abun da yake tsakanin su.


"Yayan Farooq yana ɗaya daga cikin abokan takarar daddy na, ya taɓa zuwa har gidan mu, sannan kuma akoi hotunan su a wayar daddy na sosai, na san Farooq nasan halin sa, duk yan gidan su na san su, da Farooq da yayan sa sun taɓa zuwa har gidan mu wajen daddy na" ta kai karshen maganar tare da sake fashe wa da kuka, sosai maman Sadiq da Sadiq suka shiga bata baki suna rarrashin ta, da kyar suka samu tayi shiru ta hakura.


Da sallama Hanan ta faɗo ɗakin da sauri taje ta rungumi Jehan, duk da zata girmi Jehan a shekaru amma sai tace "Aunty Nagode" shafa kan ta Jehan tayi murya a dashe tace "Ba komai Hanan" maman Sadiq ce ta tambaye su wai meke faruwa ne tsakanin Hanan da Alhajin nan, basu ɓoyewa maman Sadiq komai ba suka sanar da ita, sosai ta musu addu'ar kariya daga sharrin zina sai amsawa da amin suke.


Sannan Jehan da Sadiq suka fito suka nufi asibiti, dan maman Sadiq tace musu anyiwa mum aiki cikin nasara, amma har yanzu bata farfaÉ—o ba likitoci sunce zuwa gobe da safe zata farfaÉ—o, tun safe maman Sadiq na asibitin sai shabiyun rana ta dawo gida.


A tsakar gida suka wuce baban Sadiq da amarya, baban Sadiq yana zaune saman kujera yana tsinkewa amarya ganyen alayyaho zatayi musu miya, sosai Jehan ke jin haushin baban Sadiq kamar ta shake sa ya mutu kowa ya huta, wani kato da shi sai ya rinƙa biyewa yar amaryan nan tana sashi abubuwa kamar ƙaramin yaro.


Amarya da baban Sadiq É—in har suna haÉ—a baki wajen cewa "Sannun ku" ko kallon su Jehan bata yi ba ta wuce, shi kam Sadiq mamaki ne yake hana shi amsa sannun nasu, Allah sarki Sadiq bawan Allah bai saba ba, sai yaga abun kamar a mafarki.


Sunyi Sa'a suna fita suka sami taxin suka hau zuwa asibiti.


Mu koma muje mu leƙa su Umaisha wato gidan Abbi mu dawo sai muga ya jikin mum.


đź’žKADUNAđź’ž


Sai karfe 4 na yamma sannan su Umaisha suka dawo gidan, ba laifi Aunty ta samu sauki sosai da sosai, taji kwarin jikin ta saboda ruwan da aka kara mata


suna shiga Palo Umaisha ta wuce bedroom nasu, ita ma Aunty nata bedroom É—in ta wuce, tana mai godiya ga Allah sanan tana yiwa Umaisha addu'ar fatan alkhari da fatan Allah ya tsare ta da tsarewar sa.


Umaisha na shiga bedroom nasu wayar ta ya fara kara, dogon tsaki taja kafin ta kalli Aafia dake baje saman gado tayi ɗai ɗai tana barci, a ƙule ta ɗauki wayar kamar zata sa ihu dan haushi.


Shiru tayi bata yi magana ba, shima Akil É—in shiru yayi bai yi magana ba, almost 5mins suna manne da waya a kunne ba wanda yace da É—an uwan sa uppan, da dai taga bashi da niyar yin magana sai tace "Hello" shiru yayi kamar ba zai amasa ba "Hello ina jin ka, kayi maganar da zakayi pls" ta sake faÉ—a tana hararar É—akin nasu kamar Akil É—in take gani a zahiri


Cike da wannan izzar nasa yace "Lallai dole na koya miki hankali har ni zaki cewa kina jina nayi magana na ba, tom ki shirya gobe zan yiwa Nigeria diran mikiya, da safiya ina garin Kaduna, kuma ina sauka ki sani gidan mijin ki zaki wuce" shiru tayi kamar bata ji me yace ba, yana sane tana jin sa sarai amma taki yin magana, katse kiran yayi zuchiyar sa na tafasa ji yake tamkar ya ganshi a gaban ta yanzu, ya karya ta ya zauna kuma yayi jinyar kayan sa, yana bala'i kaunar ta sosai, sai dai baya É—aukan raini ko kaÉ—an, shiyasa duk wani maganar da zai mata da umarni yake maganar.


Ita kuwa yana katse kiran tayi wurgi da wayar saman gado tana faÉ—in "Dan wahala kawai, Allah ya kai mu goben in ga karshen rashin kunyar taka, yaro man kaza, gobe zan diro Nigeria ina zuwa zan É—auke ki, eyee to sannu Sulman dan ba zance Abbi ba sai dai ince sannu baban Abbi" ta kai karshen surutan rashin kunyar nata tare da wucewa toilet dan tayi wanka, tun safe bata yi wanka ba, tana fama da Aunty a asibiti ti.


A ɓangaren Abbi da daddyn Jelly kuwa, ko da Abbi yaje yaji abun dake faruwa, sosai hankalin sa yayi mugun tashi, ya shiga damuwa fiye da tunanin mai tunanin, bai yi kasa a gwiwa ba, ya ɗauko daddy dan su dawo Kaduna tare har sai angane in da Jelly take, idan ba haka ba barin daddy shi kaɗai babban haɗari, sannan Abbi ya sake hurawa jami'an tsaron Kano wuta akan su kara kokari wajen neman Jelly, shiyasa ma basu baro Kano da wuri ba sai karfe 4 na yamma, dan sunyi ta zarya tsakanin police station da gida, duk da daddy bai da lafiya amma sai da ya dage yayi ta bin Abbi, tare sukayi ta zarya, daga karshe suka kama hanyar Kd, Abbi yana jin kamar zai yi kuka, yaso faɗa wa su Imran amma daddy ya hana shi, yace ya bar su su rubuta Exam nasu cikin kwanciyar hankali da nitsuwa, to Abbi yace sannan ya hakura da zancen faɗa wa su Imran ɗin har sai sun dawo.


A ɓangaren Jelly kuwa, yau dai anyi Sa'a da kan ta tayi jika jikan ta wato wanka bata fita ba sam, duk jikin ta sabulu da kumpa, Hajiya Turai tana palon bata ma san Jelly ta shiga wanka ba, yau ra'ayin kanta kawai tayi, da kan ta tayi wankan.



Tana fitowa daga toilet É—aure da towel ta nufi gaban mirror kamar yadda taga hajiya na mata, ita da kan ta sai sosa jikin ta wajen bayan wuyar ta take, saboda ta lapka sabulu a wajen kuma bata wanke ba, sai sosa wajen tare.


Tana zuwa gaban mirror ta hau labta mai a kan sabulu da kumfa, gashi mai É—in ma har da na gashi ta tabka dayawa dayawa, a takaice dai duk wani mai dake Wajen mirror sai da ta labka a fiskar ta zuwa jikin ta, sai kwailin take, har wani kyalli fatar ta keyi, fuskar ta taji mai har yana É—iga


Akan mai É—in ta É—auko Foundation da beauty blending ta fara labkawa shima, bayan ta gama ta É—auki kwalli ta saka a kasan idon ta, kamar wata dodo haka ta zama, bata sa lipstick ba dan yau taji bata ra'ayi, fiskar nan nata yayi wani faw kamar jan kosai ko in ce kamar an É—aye fatar biri, ga wajen idon ta yayi bakin kirin da kwalli, baka ganin komai a fiskar ta sai idon ta farare tas, idan ka haÉ—u da ita da daddare sai ka suma saboda tsoro, ta labka mai a saman labkakken sabulu da kumfa ga Foundation abun ba'a cewa komai.


Bayan ta gama lafke lafken kwalliyar ta sai ta wuce wajen drawer kayan sawar Hajiya, dan duk wannan tsiya a bedroom É—in Hajiya akayi shi, sai faman haÉ—a zufa take saboda uban mai da ta labka wa jikin ta.


Tun bata karisa wajen drawer ba ta cire towel É—in jikin ta tayi wurgi da shi saman bed, taje ta buÉ—e drawer kayan Hajiya, abuna farko da ta fara cin karo da su shine breziya da pant, É—auko pant É—in Hajiya tayi, ta É—ago shi sama tana kallo, kara zaro ido tayi, a sukwane ta kalli waist nata wato kugun ta, taga pant É—in Hajiya wargajeje gari guda, irin ta biyar sai su shige cikin pant É—in, sai jujjuya pant É—in take wai ko zata samu wajen rage masa girma


Da dai taga ba wajen rage masa girma, sai ta dura shi haka nan, dukka kafofin ta a site É—aya ta haÉ—e su, wato a kafan pant É—aya, sauran jikin pant É—in da ya mata yawa kuma sai ta tattara ta É—aure kamar mai É—aure alale, ta cusa cikin ta saman kugun ta, sannan ta É—auko breast, tayi shiru tana tunanin ya ake sawa, dan tabbas tana ganin shi a jikin Hajiya, sai dai koko É—aya na breziyar Hajiya dai'dai yake da ya É—auke breast nata dukka biyu, tashin sense, haka ta saka abun ta, koko É—aya a breast nata É—ayan kuma a cikin ta, abun gwanin ban dariya, ga fuskar kamar an É—aye fatar biri sai turo baki take.


Sake sanya hannun ta tayi cikin drawer ta ɗauko wani shaddan Hajiya fari tas, yaji aiki sosai ɗinkin half gown da zani, rigar kawai ta sanya wadda yazo mata har idon sahu na kafar ta, dan Hajiya Turai irin hamshaƙan matan nan ne, ga tsawo ga kiɓa, ta ko ina masha Allah, a gefen faɗi kuwa, Jelly kamar tsinke ta zama cikin rigar Hajiya, abun gwanin ban dariya, kayi dariya har cikin ka yayi ciwo.


Bayan ta gama duk wannan shirye shiryen nata, ta fito ta nufi palo da zumuÉ—in ta zata je ta nunawa Hajiya yau tayi abun arziki da kan ta.


Hajiya na zaune a palo tana shan black tea É—in ta, Kamar daga sama Jelly ta faÉ—o mata babu ko sallama, duk kiba irin na Hajiya ganin Jelly bai hana ta tashi a É—ari kamar siririyar mace ba, idan ana zancen cetan rai wake ta wani zancen kiba, to wannan ma hakane domin a tunanin Hajiya aljana ce, sai faÉ—in innahu min sulaimanu wa innahu Bismillahirrahamanin rahim, a guje Hajiya fa ta zura tayi babban palon kasa tana ihu yau ga aljana a palon ta,


Ganin Hajiya ta zura a guje tayi waje ne yasa Jelly tayi tunanin kila wani abun tsoro Hajiya ta gani, ita ma ai sai ta kwasa a kuje tabi bayan Hajiya tana ihu dan kar abun tsoron da Hajiya ta gani ya kama ta, bata san itace abun tsoron ba


Hajiya kuma ganin Jelly na bin ta da gudu sai tayi tunanin Aljanar ke binta, dan haka sai ta kara karfin ihun ta dan jama'ar gidan su kawo mata ɗauki, ga firskar Jelly yasha daɓa daɓa da kayan make up sannan gashi ta sanya farar shadda, kuma burgujeje ya mata yawa, tana yawo a cikin kayan, ya kuke ganin abun zai kasance?.


Da gudun gaske Hajiya Turai ta faɗa ɓangaren su Afnan, tana gudu tana ihu, a palon part ɗin su ta isko Afnan da Maman ta suna zaune, ganin Hajiya Turai a guje yasa suka miƙe suna faɗin "Ke Hajiya Turai me hakan, zaki shigo mana ba sallama, bamu san... Basu kai ga karisa maganar ba Jelly ta faɗo cikin palon da gudu, Subhanallah zokaga yadda ake gudun cetar rai, Afnan uwar rashin kunya, tuni ta watsa a guje tayi cikin ɗakin ta ta banko kofa,


karo na farko a rayuwar Afnan da ta fara kiran sunan Allah data ga bone, ita kuwa maman Afnan É—in, tsabar tsorata rungume Hajiya Turai tayi tana faÉ—in "Na shiga uku na lalace ki taimake ni Hajiya Turai, karki bari Aljanar nan ta kama ni" ita kan ta Hajiya Turai neman tsira take maman Afnan zata wani ce ta taimake ta, ture maman Afnan tayi ta bi bayan Afnan da dugu ta shige É—aki, aiko itama maman Afnan bata yi kasa a gwiwa ba ta rufa musu baya, ita ma Jelly bin su da gudu tayi dan a tunanin ta wani abun tsoron suke gudun wa.


Jelly na shiga É—akin Afnan, suka fasa ihu a guje suka sake bazama waje, still itama Jelly tabi bayan su tana kuka.


A takaice dai yau Jelly tasa gaba É—aya familyn Abbo sun haÉ—u waje guda, wayan da basa shiri basa ko ga maciji yau sun haÉ—e waje guda saboda Jelly, dan ba wani part a cikin gidan dasu Hajiya turai basu faÉ—a da gudu suna ihu ba, duk kuma in da suka shiga sai yan part É—in sun rufa musu baya suyi ta gudun cetan rai tare.


Daga karshe dai tsakar gida suka koma suna yar tsere da Jelly, suna gudun ta, ita kuma tana gudun abun da suke gudu, domin a ɗaukan ta wani abun suke gudu, Allah sarki Hajiya Turai gata da ƙiba sosai haka Jelly tasa baiwar Allah nan ta rinƙa tikan gudu kamar mahauniya sai haki take tana mumfashi sama sama.


A wannan yanayin na yar tsere da suke da Jelly Nawid ya shigo cikin gidan same su, dan yana ta horn ba wanda ya buÉ—e masa gate, dan mai gadin ma dayake mara hankali ne irin kauyawan nane wai sai ya É—auko sanda yana bin Jelly zai make ta, idan kuma ta juyo ta kalle sa, sai ya fasa ihu ya shige bayan flowers.


Nawid dai yaga tashin hankali dan kuwa ya rasa me ma zai yi, tsayuwa kawai yayi yana kallon yadda iyayen nasa da kannen sa har ma da yayyun sa mata ke gudu suna ihu, tun shigowar sa kallo É—aya yayiwa Jelly ya gane ita É—in ce, abun da bai ganeba shine gudun me iyayen nasa keyi, dan shi bai ga abun da suke wa gudun ba, saboda yaga Jelly É—in na binsu ita ma tana gudun, gashi dukkan su sai ihu suke har da ita Jelly, shine abun ya kulle masa kai ya rasa me suke wa wannan gudu da ihun


Afnan uwar rashin kunya yau tayi gudu ne har ta godewa Allah, gashi kuma sai addu'a suke aljananan wato Jelly taki ɓace wa, sai gudu suke daga masu kiran, ya Allah ka kawo mana ɗauki sai masu faɗin, Ya Rahman bayin ka suna cikin halin a ula'e, addu'a kala kala yau sun zuba shi, wasu ma basu san me suke faɗe ba kwata kwata saboda tashin hankali, duk abun da yazo bakin su suke faɗe.


Shiru Nawid ya tsaya, sai da ya ga Hajiyar sa na kokarin zubewa kasa saboda gajiya sannan ya karisa wajen da sauri, cikin tsawa yace "Wai me hakan ne? Meke faruwa ne?" Ya kai karshen maganar tare da riƙo Hajiya Turai, sai faman nuna masa Jelly Hajiya Turai take da hannun ta ta kasa magana, kallo Jelly yayi kafin ya dawo da kallon sa kan Hajiya "Ummi me babyn kuma tayi yau kike gudun ta? Ko dan tayi wannan kwalliyar ne" sai lokacin Hajiya Turai ta waro idon ta da kyau ta kalli Jelly da kyau, daman su sauran yan gidan basu san Jelly ba bare su gane ta, dan bata taɓa zuwa part ɗin kowa ba, kullu tana tare da Hajiya


Ganin Jelly ce da gaske yasa Hajiya Turai ta sake jikin ta tana faɗin "Ruwa a taimaka min da Ruwa" ba ita ka ɗai ba masu bukatar ruwan suna dayawa a wajen, mafi yawancin su sun baje a kasa suna a basu ruwa, girgiza kai Nawid yayi ya riƙo hannun Hajiya, da kyar da kyar take ɗaga kafar ta, suka wuce ciki, har sun ɗan yi nisa, ya juyo ya kalli Jelly dake tsaye, da hannu ya mata alama da tazo su tafi, da yar gudun ta ta kariso wajen sa suka shige cikin palo tare, su kuwa sauran sun baje a kasa suna ta neman agajin ruwa, mai gadi ma ya fito daga maɓoyar sa wato bayan flowers ya koma bakin gate yana faɗin "Amma wannan abu bai min daɗi ba, naso na make shagiya ta mutu, amma ba komai akoi gobe ma ai sai na make ta ta mutu ɗin" sai surutan sa yake shi kaɗai kamar wani zararre.


Hajiya Turai suna shiga palon su, ta haye saman sofa mai zaman mutun 3 ta kwanta tana mai da numfashi, ruwa Nawid ya ɗauko mata mai sanyi a fridge ya bata tasha sannan ya wuce bedroom nasa, kusa da ita Jelly ta zauna tana kallo a Tv ko a jikin ta, Hajiya kuwa ta lumshe ido tana sauke mumfashi wahala, dan yau ta wahala fiye da tunain mai tunani, kun dai san yadda gudun mai ƙiba yake to hakane.


Kun dai ji halin da Jelly ke ciki na saka mutanen gida motsa jiki, yanzu dai muje mu leƙo Washington DC mu dawo kafin nan kila Hajiya tayi barci ta huta, sai ta tashi tayiwa Jelly ɗin ku wanka...



đź’žWASHINGTON DCđź’ž



James yana fita wajen Romeo kai tsaye word room ya nufa, zaune ya isko Musharraf, abun ku da na'urori na zamani sha yanzu magani yanzu, idan kana da kuÉ—i ba abubuwan da ba za'a maka ba, saboda kayan aiki na zamani da Dr William jacop yake da shi hakan yasa kafar Musharraf yayi saurin samun sauki, sai dai baya iya tafiya sosai kaÉ—an kaÉ—an yake É—ingisa kafar, amma yana iya tashi da kan sa ya zauna, kuma yana samu kulawa sosai a wajen dad da James, su kaÉ—ai ke kula shi a gidan, shima dad dan bai san Musharraf Musulmi bane da ba zai kula shi ba.


Gefen Musharraf ɗin James yazo ya zauna yana faɗin "Uncle are you feeling?" Murmushi Musharraf yayi kafin yace "My son I'm getting better" "what do you want to eat today uncle?" Sosai Musharraf yaji daɗi cike da matikar kaunar James yace "Gaskiya ina son cin miyar steew da akayi da kifi, da kuma shinkafa" okey James yace lafin ya miƙe ya ɗauko wa Musharraf kujeran tura mara sa lafiya wayan da ke da matsalar kafa


Kamar baby haka James ya É—aga Musharraf ya É—aura sa saman kujerar yana faÉ—in "Muje ka ga gida, yau dai ka É—an fita waje" sai murmushi Musharraf yake yaji daÉ—i sosai dan dama ya gaji da zama a É—akin.


James da kan sa ya turo Musharraf suka fito, kai tsaye palon kasa ya nufa, su dad gaba É—ayan su suna palon kasa suna zaune suna hira har da Michael mai barci ma ya taso yayi joined nasu.


Suna ganin Musharraf suka É—aure fuska, musamman uncle Herry da Tga da John, Jay ne yace "Kai James who is this man?" Dan su Jay kwata kwata basu san da zaman Musharraf a gidan ba, atakaice James ya faÉ—a musu waye Musharraf da kuma zaman me yake a gidan, nan fa suka ce basu yarda ba dole Musharraf ya bar gidan nan yau, a kai shi hospital ayi jinyar sa a can ba dai a gidan nan ba, kallo Michael James yayi kafin yace "Kana tare da su Michael? Kana son uncle ya bar gidan na?" James ya tambayi Michael ne dan yasan idan Michael yace baya son Musharraf ya zauna a gidan tofa ko zai mutu sai Musharraf ya bar gidan, dan lion ba zai yarda da zaman Musharraf ba muddin Michael baya so, amma idan Michael yana so to ya samu daman da zai tinkari Romeo ya neman wa Musharraf takardan izinin zama a gidan.


Romeo yana da wata ka ida, ko wani irin mutun ne yazo gidan zai zana to fa ba zai yiwu ya zauna ba sai da takarda izinin zama gidan, misali yanzu idan daddy ya kawo abokin sa yace to ga abokin sa zai ɗan zauna da su a gidan, tofa sai ya sa hannu a takarda dan gidan su tana da takardan zama a cikin ta, ma'anar takardan nan kuwa, shine, misali bari ayi gwari gwari, idan bako yazo zai zauna dasu, Romeo zai tambaye sa zaman shekara nawa zai yi, idan yace shekara ɗaya, to Romeo zai rubuta a takardan sa, shekara ɗaya mutunmin zai yi, sai ya baka ka sa hannu, kana sanya hannu to ka dawo karkashin kulawar Romeo ko fita zakayi sai da izinin sa, dan shi baya yarda da mutane shiyasa, ba zai bari ka rinƙa fita da shiga gidan ba, sannan kuma baka isa kace zaka tafi wannan shekara ɗayan bata cika ba, baka isa ba, kome zai faru sai wannan shekaran ta cika, amma babban abun daɗin shine in dai ka samu takardan zama a gidan tofa kana cikin tsaro, dan Romeo zai kula da rayuwar ka duk in da zaka je zai iya sanya sojiji su raka, dan ka sanya hannu a takarda kamar ka zama ɗan gida ne, sai dai fa samun takardan izinin zama a gidan nasu ne, babban tashin hankali dan basu ma son bako, bare har ya samu wannan takarda, amma in ka samu lafiya Lou.


Shiru palon yayi suna jiran amsar Michael, ya amince Musharraf ya zauna ne ko kuma bai amin ce ba, hannu Michael ya miƙa wa Musharraf yana faɗin "James is my blood, i love him more than everything in my life, duk abun da James yake so ina son shi dan haka uncle ɗin James kayi zaman ka tare da James ɗin ka" nan fa Tga ya bugi kirji yace uban kuturu yayi kaɗan bare na makawo, ba zai taɓa yarda ba dole Musharraf ya bar gidan.


Miƙa hannu Musharraf yayi sukayi shaking hand da Michael, shi kuma James ya wuce ya haura sama ya bar Michael da Musharraf suna hira, su kuma su Tga suna surfa bala'i dole Musharraf ya bar gidan, kamar gidan su.


Part É—in Romeo James ya nufa dan yaje ya nemawa Musharraf takardan izinin zama a gidan, ko da ya shiga bedroom É—in Romeo sai yaga kamar Romeo na barci, ganin haka yasa sai ya juya a hankali zai fita, kamar daga sama yaji sexy voice É—in Romeo yace "James" da sauri ya juyo still idon Romeo a lumshe sai dai ba barci take ba


Da sauri James ya koma kusa da shi ya zauna yana faɗin "Please my lion wata alfarma nazo nema" shiru Romeo ya masa kamar bai ji me yace ba, ci-gaba da magana James yayi dan yasan Romeo na jin sa sarai "Ina son ka bawa uncle na wadda na buge da mota takardan izinin zama a gidan nan dan su Uncle T da uncle Herry sun takura masa wai sai ya bargidan nan, ni kuma bana so ya tafi yanzu dan ya faɗa min bai da kowa" sai lokacin Romeo ya waro dara daran fararen idon sa tal kamar audiga masu ɗauke da kwayar ido blue, shiru ya ɗan yi kamar ba zai yi magana ba, sai kuma gently yace "Ba dai kai da Michael kuna son zaman shi a tare da ku ba?" Da sauri ya gyaɗa kai yana faɗin "Of course numa so" da hannu yayiwa James nuni da cikin drawer mirror sa, akan ya ɗauko takardan, cike da zumuɗi James yaje ya ɗauko takardun ya dawo ya miƙa masa, karɓa yayi ya ciri guda ɗaya ya miƙawa James ɗin yana faɗin "Ka kai masa ya karanta doka idan yayi agree fine ya sa hannu ka kawo min nima na sa hannu" da sauri James ya karɓa ya nufi waje.


Har lokacin sai surutu su Tga suke a kan lallai Musharraf ba zai zauna a gidan ba, ganin James ya dawo riƙe da takardan izinin zama a gida ne yasa sukayi tsit kamar babu kowa a palon, dan sun san lion ya amince kenan basu da wani bakin magana kuma, James kan ko a jikin sa yazo ya miƙawa Musharraf takardan yana faɗin "include we need your signature here" karɓan yar takardan Musharraf yayi ya fara karanta dokokin kamar haka, shekara nawa zaka zauna, hannu Musharraf ya miƙawa James a kan ya bashi bairo, ba musu James ya ciro bairo daga gaban rigan Tga ya miƙa masa, haushi kamar Tga ya shaƙe su daga James ɗin har Musharraf ɗin duk su mutu.


Wajen da aka rubuta shekara kawa zakayi, haka kawai Musharraf ya tsinci kan sa da rubuta 4 years bai yi tunain me zai je yazo ba, kawai ya damɓara shekara huɗu, doka ta biyu, idan ka sa hannun rayuwar ka ta zama a karkashin kulawar lion kuma sai abun da yace zakayi, Musharraf ya damɓara yes ba wani tunani, na uku, babu fita daga gidan nan babu zuwa ko ina sai da izinin lion, nan ma ya damɓara yes ya yarda kenan, na huɗu, baka isa kace zaka bar cikkin familyn William jacop ba har sai wannan shekaru da kace zakayi sun cika, nan ma ya damɓara yes, daga karshe ya sanya signature wato sa hannun sa, ya miƙa wa James, sai daɗi James yake ji ya wuce ya mayarwa Romeo takardan ya karɓa ya sa hannu sannan ya bawa James ɗin ya mayar in da ya ɗauko,


Su uncle ba karamin haushi sukaji ba wannan ma basu san cewa Musharraf musulmi bane wata kila idan sun sani sai kisa kawai zasu masa, dan haushi.


James na dawowa Palon ya wuce kitchen yaje ya sanar da sojojin dake musu girki a kan suyi miya da kifi yau, sun sha mamakin jin abun da James yace, amma basu da wani zaɓi abun da yan gida keso shi suke girka musu.


Sosai James yayi yawo da Musharraf a cikin gidan, nan yake sanar masa anjuma da daddare zai yi tafiya, amma baya son kowa ya sani, har lion shiyasa ma zai yi tafiyar dare, shima Musharraf É—in ya faÉ—a masa ne dan yasan ba zai faÉ—awa kowa ba, sosai Musharraf ya masa fatan alkhari da fatan nasara, haka suka ci-gaba da yawata cikin gidan suna hira.


After some hours


Gaba ɗaya family'n daddy sun haɗu a table dan cin abinci amma banda oga lion, sai kuma James da ya tafi kai wa Musharraf abincin sa, daga kaiwa Musharraf ɗin abinci sai ya zauna suka ɓige da hira, haka kawai yake bala'i kaunar Musharraf har cikin ran sa.


Bodyguards dake serving nasu abinci ne suka fara zuba musu abincin


Jin kalan kamshin da abincin keyi yasa gaba ɗayan su suka ɗago idon su a sukwane suna kallon kallo wa junan su, mamaki ya hana su magana, yau shinkafa da miyar steew kuma har da kifi da basa ci a gidan su, nan take ran kowannen su ya ɓaci, Michael yafi kowa shiga ɓacin rai dan saboda shine ma ba'a girka kifi a gidan, kwata kwata baya son kifi bai son ganin kifi, saboda shi Romeo ya kafa dokar kada a kuskura a girka kifi a gidan, ba'a taɓa girki da kifi ba, shiyasa sauran ma basu saba cin kifin ba, kuma suke kyamar kifin sosai, dan suna ganin kamar wani kazanta ne tun da lion ya hana girkawa, shi kuma James lokacin da yaje ya sanar da masu girkin su dafa miya da kifi, bawan Allah ya manta bai cewa sojojin iya abincin Musharraf kawai zasu girka da kifi ba, shi dai kawai yace suyi girki da kifi bai rabe musu ya zasu yi ba, shiyasa sukuma suka labta kifin wa gaba ɗaya jama'ar gidan.


Jin warin kifin yasa Michael miƙewa da gudu ya haura sama, ya shiga part nasa, yaje toilet ya rinƙa kwara amai kamar zai amayar da hanjin cikin sa, gaba ɗaya bodyguards dake wajen sai da hantar cikin su ya kaɗa, saboda tsoron hukuncin da zasu fiskanta duk da basu sukayi girkin ba.


A tare gaba É—aya family dake saman table É—in suka tashi da gudu sukabi bayan Michael dan sun san bawan Allah amai yake, tun yana yaro baya son ko kallon kifi da ido


Shi kuwa James yana can yana zuba hirar sa da Musharraf, Musharraf na ba shi labarin tarihin rayuwar sa, sai dariya James yake kamar ba shi ba, can kuma ga Michael na tikar amai kamar zai amayar da Ć´aĆ´an hanjin sa.


Sosai family suka tausayawa Michael dan yayi amai ne har ya galabaita kamar zai amayar da kayan cikin sa duka, da kyar da ma kyarkyata ya samu amai ɗin ya dakata, rai a matukar ɓace ya fito ba tare da yayiwa su daddy magana ba, kai tsaye ɗakin ajiye makaman su ya wuce, babu kalan makamin da babu a ɗakin sai na kare dangi


Wata iriyar wuƙa mai bala'i kaifin gaske wadda ke aiki da wata yar inji a jikin ta wadda akewa charji, idan aka kunna injin wannan wuka zata iya zaba ɗan adam gida biyu saboda kaifin balai da take da shi, wannan wukar Michael ya ɗauko ya nufi waje.


Kai tsaye palon kasa ya koma su daddy suna biye da shi, cikin tsawa ya kira sojojin dake musu girki, sai wani huci yake kamar É—an zaki, cikin sauri sojojin suka fito daga cikin Kitchen É—in, kallon sa dad yayi kafin yace "Michael what are you going to do with this AK" sunan wukar kenan AK, "that I want to cut their hand"


Tashin hankali kasa sojojin suka zube sunji Michael zai yanke musu hannu, ɗaya daga cikin su kam ma kuka ya fara yi dan yasan yaran William jacop basa maganan da ba zasu aikata ba, hakuri dad ya shiga bawa Michael yana lallaɓa sa akan ya kyale sojojin yayi hakuri ya tsaya suji dalilin da ya sa suka saka musu kifi a abinci, ina Michael yayi nisa baya jin kira ya dage sai ya yanke musu hannayen su, da sauri daddy yace da su jay su rike Michael kar su bari ya yanke wa sojojin nan hannu,


Kin rike Michael É—in su Jay sukayi dan mugunta sai ma kara ingiza shi suke, jikokin mugaye, su Jay akoi su da mugun ta zuciyar kafurci babu É—igon imani, shi kuwa James da ya haddasa wannan bala'i yana can suna hira da Musharraf hankali kwance sai dariya yake bai san meke fatuwa ba, sai dai shima yaki cin abinci ko da Musharraf yace yaci, sai yace a'a basa cin kifi, basu saba ba, shi a tunanin sa iya Musharraf kawai akayiwa girki da kifi.


Sojojin dake girkin kuwa sai kuka suke bayin Allah basu jiba basu gani ba za'a yanke musu hannun suna ji suna gani, ɗayan kam har da majina ya haɗe hawaye sharɓa sharɓa a fuskokin su, Tga har da cewa idan Michael ba zai yanke musu hannu ba ya bashi wukar bari shi ya yanke musu, mugun kafuri zuciya ba imani ba tawakkali, shekara wajen 8 sojojin nan suna yi musu girki ba'a taɓa samun matsala ba sai yau, yau ɗin ma matsalar daga wajen James aka samu shine bai musu bayani yadda ya kamata ba, amma su Tga sun murje ido sunce dole su yankewa sojojin nan hannun su, daga saman wajen hammatan su zasu yanke gaba ɗaya.


A ɓangaren Romeo kuwa, tsaye yake gaban mirror ɗaure da towel mai laushi fari tas a kugun sa, soft skin na sa kaɗai abun kallo ne, yaji hutu sosai yana kwance lif sai sheki yake ga tsantsi kamar fatar jariri, kasan cewar babu riga a jikin sa, hakan ya bayyanar da kakkarfar suran jikin sa, Romeo yana da tsawo sosai, dan ya fi su James tsawo dukkan su, daga shi sai James Michael ne ya ɗauko tsawon mum ɗin su ɗan dai'dai da shi, James kuma tsawon uncle Tga ya ɗauko, Romeo kuma tsawon daddyn su, har ma yafi daddyn su tsawo kaɗan, amma shima daddy ba baya ba a tsawo.


Romeo yana da buɗaɗen kirji sosai sannan gashi yana ɗaga karfe sosai wato gym kenan, hakan yasa kirjin nasa ya kara buɗe wa sosai kamar wani irin manya manyan zakunnan nan, wayan da suka riƙa, damtsen hannun sa kawai idan ka gani ya isa ya sa ka razana har kaji kamshin suma, breast nasa kuwa ba'a magana a cike suke bul bul gwanin burgewa, yana da korjinin bala'i wadda ganin sa yana cikin farinciki ma kawai yana sanya hantar manyan jaruman maza ta kaɗa, shiyasa mum nasu take cewa ganin lion yana cikin farinciki ma razana ta yake,

## Korjinin sa ya sanya idan yayiwa mutane tsawa suke iya mutuwa, gashi da bala'i farinjini kamar me, ba iya mace ka É—ai ba har maza idan suka ganshi kyasawa suke, maza ma bala'i san shi suke ina ga mata kuma ai ba'a magana, ko wani jinsi son shi suke kamar me, gashi kuma ko full face nasa basu sani ba, haka suke son shi, wasu da dama masoyan kyakkyawan kiran jikin sane, wasu kuma masoyan tarin dukiyar da Allah ya bashi, wasu masoyan matsayin sa a wajen aiki wato THE GENERAL OF THE ARMY, wasu kuma masoyan kuruciyar sa ne, da wuya a samu mai san shi dan Allah bacin iyayen sa da Triplets nasa, kullun fiskar sa a É—aure take tamau kamar hadari bai san menene dariya ba.


Sai faman shafawa kan sa tsadaddun hair cream nasa masu bala'i kamshi da kyau da tsada yake, ga gashin nasa sai kyalli yake yana wani curly gwanin ban sha'awa


Mai kala uku ya shafa a kan nasa, duk wannan fitinannen kamshi mayu kan dake tashi daga gashin nasa hakan bai hana shi É—aukan turaren gashin mai bala'i kamshi, ya sake fesawa curly hair na saba, dan shi ma'abocin kaunar kamshi ne sosai, kullun yana cikin zuba kamshi har kamshin turaren nasa ya kama jikin sa, ko bai sa turare ba kamshi yake zubawa, amma a haka sai ya saka.


Bayan ya gama ne ya É—auko almakashi ya rage tsawon wannan guntun gashin gaban goshin nasa, dan yanzu gashin ya É—an yi tsawo ya zo masa har wajen gemu shi kuma bai san haka ya fison na gaban goshin É—an guntu zuwa kyakkyawan dogon hancin sa, shiyasa duk bayan 1 week yake rage tsawon gashin gaban goshin ya bar na bayan da yake har tsakiyar bayan sa.


Dressing room nasa ya nufa bayan ya gama shafe jikin sa da gashin kan sa da tsadaddun mayukan sa, 10mins ya É—auka a dressing room É—in sannan ya fito, jikin sa na sanye da pajama launin sky blue mai kyau da tsada, ya É—aure gashin kan sa a baya, ya saki wannan É—an guntu na gaban goshin da ya datsen ya kara rage mata tsawo yanzu, sai tashin fitinannen kamshi perfume nasa yake.


Saman katafaren lallausan gadon sa ya haye tare da jawo laptop nasa dake saman bedside drawer ya kunna wutar gaban screen É—in tare da cire password ya shiga bincike a kan James


Kasan cewar ya saukar da idon sa kasa yana kallon screen na laptop ɗin hakan yasa idon nasa tayi kamar a rufe, zara zaran eyelashes nasa suka kara bayyana, dan shi da Michael irin eyelashes ɗin daddy gare su dogaye sosai kamar sun kara dana kanti, ga gashin geran su kiris ya rage su haɗe da juna dan cikan gashi dake wajen, sai dai duk cikan gashin gerar nasu a kwance yake lif yana ta shaƙi kamar wayan da akayiwa make up, duk cikin su lips na Romeo ne yayi red sosai kamar ya sanya jan baki, shi Micheal lips nasa dark purple ne, shi kuma James red ne irin na Romeo sai dai bai kai na Romeo yin red sosai ba.


Duk wannan badaƙala na yankewa sojoji masu yi musu girki hannaye da Michael ke shirin yi Romeo da James basu sani ba, suna nan suna aikin gaban su, Micheal na tsula tsiyar sa a palon kasa son ran sa...



Share fisabilillah 👏


To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪


đź’žStar Ladyđź’ž



Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.