Free chapter · Read without an account

Chapter 8

by Ikilima Adam · Makauniyar sharia

*Makauniyar Shari'a*

_Sai a Lahira_


*NA*


_*IKILIMA ADAM*_

_( kyauta daga Allah)_




SHAFI NA TAKWAS



Bayan rigarsa suke kallo , inda yaga an rubuta *MASTER* da babban baki , nan da nan hantar cikinsa ya kada wani irin gumi mai dumi ya ringa sassarfo masa dukan ilahirin jikinsa , ji kake gab!! gab!! da karfi .


Ahankali mutumin da ya basu baya ya waigo yana busan sigari da tashin hayaki , cikin isa da kasaita ya ke taku irin na yan daba hannunsa daya sanye cikin Aljihun rigarsa . Cikin razana Amatullah ke kallon fuskarsa a rikice da tsoro , ta fara ja da baya baya , bakinta na rawa ta ce , " kaine ?".

Be bata amsa ba illah cigaba da takunsa ya yi yana nufo inda suke yaransa suna cigaba da bashi hanya har ya karaso daf dasu , cikin tsananin bacin rai da ya bayyana a fuskarsa ya ce , " Ina zaku tafi da sanyin asubahin nan ? baku san tun lokacin da nasan kuna zaune anan wurin na fara gadin ku ba ? saboda bana son abin da ze taba min Yarinyar nan , akanta zan iya yin komai ." Yakai karshen zancen yana kallon Papy da ya dukar da kansa idanunsa a kasa. Kara zuko sigarin ya yi tare da turnuke su da hayaki , silan haka yasa Amatullah kwarewa har numfashin ta na tsarkewa , nan da nan ta fara tari tana yi tana bubbuga kafafunta sosai hayakin ya shiga hudar hancinta ya hau kanta tare da haddasa mata ciwon kai lokaci daya . Papy lura da yanayin da Amatullah take ciki hakan yasa ya ajiye kayan hannunsa , hanzarta karban kayan dake hannunta ya yi tare da ajiye su akasa. Kana janyo ta tare da kai mata wawan runguma dake nuna tausayi da jin kai na Mahaifi , hannayensa yasa yana mai dan bubbuga bayanta . Duk abin da suke Karfin Iko na kallon su shi da mabiya bayansa da suke sanye cikin face mask .


"Zan canza muku wajen zama in kama muku haya acikin gari". Cewar Karfin Iko yana cigaba da tashin hayakin sa.


" Babu inda zamu bi ka , ka barmu inda ka ganmu , bana bukatar taimakon ka ". Cewar Amatullah cikin kuka mai gunji , ba tare da ta dago kanta daga jikin Papy ba . Karfin Iko cak kalamanta suka cika zuciyarshi da zunzurutun mamaki dan ba zato ba tsammani ya ji amon muryanta cikin kuka wanda ya kara sanya dukan gabobin jikinsa yin sanyi kamar kankara , kana yana mai kara kallon yanda take kara shigewa jikin Papynta dake rungume da ita yanda kasan sace ta za'a ko raba su. Sanyayyar iska mai kadawa da yanayin sanyin asubahi ya buso su hade da ni'imattacen shaka. Nan da nan Amatullah ta kara matse Papy ajikinta dan sam bata son sanyi.


Karfin Iko jefar da Sigarin hannunsa ya yi , ya take da kafafunsa kana , ya juyo da fuskarsa , yana mai kara kallon su karo na barkatai , cikin babban muryansa ya ce , " Haba Yarinya kul kada na kara jin kina fadin in fita daga tsabgarku , hakan babban zunubi ne , maganar bakyason na canza muku muhalli , to ku zabi in da kuke son zama zan biya kudin haya ". Yana kai karshen zancen ya fara kokarin daukar kayan nasu . Papy da sai yanzu yaji ze iya magantuwa ya ce , " na amince ka samar muna wajen zama amma don Allah karka kama muna daki da kudin haram." Ya kai karshen zancen yana mai kallon Karfin Iko cikin idanu.


Gabakidaya wajen sosai har yaran nasa suke juya kalaman Papy , hatta Amatullah ita ma kam kalamansa ta daura a ma'auni tana tankade da rairaya amma sam ta kasa gane inda Papy ya dosa . Karfin Iko murmushi ya yi na gefen baki , kana cikin muryansa na dabi'a ya ce , " na muku Alkawarin da kudin gadona zan kama muku haya , dan ma garin mu ba Abuja bane da Gida zan baku ku zauna har iya adadin lokacin da kuka bukaci komawa muhallinku ko in ce Garin ku." Papy sosai ya ji ya gamsu da Karfin Iko ,kallo daya ya masa ya tabbatar da gaskiya yake fadi har kasan ransa . Kafin su bar wajen saida ya basu dubu ashirin kudin cefane , kana ya basu kwana uku su zauna ciki shiri zasu canza muhalli.

Papy komawa suka yi bukkansu suna juya kudaden dake hannunsu , lissafin rayuwa yake hakan yasa cikin karfin hali ya ce , " Amatullah ". dago kai tayi tana kallonsa da idanunta masu tarin barci , kana ta lumshe su tana mai sauraren me ze fadi . " Ina son ki sani duk duniya banda kamarki , kuma ba zan so ganinki cikin damuwa ba , ina son ki sani rayuwa aduk yanda ka tsinci kanka hakuri ka ke yi , dan haka ina mai rokon ki Please ko babu ni karki jefa kanki cikin halaka ".


Kamar an tsinkaye da Allura , afirgice ta bude idanunta, tare da dan murzasu tana son tabbatar da abinda take ji daga bakin Papy.

Nan da nan ta nemi barcin da take ji ta rasa , tattaro kuzarinta ta yi tare da zama tana face dinsa dakyau , damshin hawayene suka cika kwarmin idanunta , cikin rawar murya da tsoro da fargaba ta ce , " Papy bangane me kake nufi ba ? Karka ce zaka guje ni dan Allah bansan kowa ba sai kai ban taso da uwa ba , ban taso da uba ba , Papy in ka guje min waze jibinci lamurana ?." Takai karshen zancen tana sheshekar kuka.


Dubanta yake cikin sanyin murya da tausayawa da jin kai ya ce ," Amatullah nasha gayamiki akwai mutuwa kin san mutuwa bata sallama Amatullah banason ki sawa kanki damuwa aduk lokacin da mutuwa tayi awon gaba dani pls my Friday ". ya karashe zancen domin kwantar mata da hankali. Duk da hakan sam bata ji sassauci ba , bakinta na rawa da tsoro ta ce , " mu bamu da dangi ne ? ina mahaifiyata Papy? bamu da yan uwane , mu kadai muke rayuwa ne , kuma kana ta yawan ambato mun zancen mutuwa shin ya kake son na kasance in babu kai ? ." Ta jera masa tambayoyi cikin muryan kuka.


Cak wutar lantarki jikinsa ya dauke, nan da nan ya ji zufa ya keto masa , cikin kasa da murya ya ce , " Amatullah zan miki takarda full na address din Gidanmu in har kin samu zuwa kawai kice kina son ganin dan Gidan kawai , kuna tozali da shi kawai ki mika mishi papper , amma sai bayan raina ko wani abu ya gifta za kiyi hakan , anan in sha Allah zaki san tarihinki hatta Mahaifiyarki , batun mutuwa Amatullah ko muna so ko bamu so tabbas sai ta raba mu ". Ya karashe zancen yana maganar zuci inda yake fadin " Amatullah mun kusa rabuwa daman nasan wannan ranar zata zo , Allah yasa kije gida lafiya , Amatullah banson barinki adaidai wannan lokacin ba amma tun da na fahimci kin fara hankali babu sauran zama ni dake Diyata ". yakai karshen zancen yana mai kuka mai cin rai , shi da ita babu mai rarrashin wani domin kukan yaci karfinsu.



Benin Cotonou


Alhaji Isah Sharifai , cikin tsadaddan shaddarsa ya fito compund din Gidansa , hannunsa rike da bakar jaka, ba karamin haduwa ya yi ba cikin shigar hash color , hular kansa ya tsaya gyarawa yana mai kallon , Meenat dake kusanto inda yake murmushi a kyakkyawan fuskarsa . Ahanzarce ta karaso tana mai rike hannunsa mara dauke da jakar , Yarinya ce wacce bazata wuce shekaru sha bakwai ba , sanye cikin red habaya mai adon stone hannun riga da tsakiyar riga ,tayi rollin din kanta da dankwalin rigarta ,doguwa ce fara sol dan tana mugun kamannin da mahaifiyarta Hajiya Basma. Nan da nan ta karya murya cikin cool voice dinta ta ce , " Daddy ni fa yau so nake naje bikin kawata kuma kudin da kabani , naira million biyar satin da ya wuce sun kare , pls ka karamun biyar din dan zanyi bajinta awajen taron". Ta karshe zancen cikin shagwaba. Alhaji fuskarsa dauke da Annuri ya ce , " Haba daughter in kina son kudi , kawai ki ce na tura miki , kin ga Zahra'u tana Dubai tana karatu , zanso kema kije...... ". sauran kalamansa makalewa su kayi sakamakon ganin , Yasmin cikin shigar makaranta ta fito daga sashinsu , sanye cikin tsohuwar uniforme mai kalan bleu da fari da jakarta da ta rungume , kafarta sanye take da da safa cikin takalmin makaranta mai igiya , Yarinya ce me kimanin shekaru 16 aduniya farace sol zubin larabawa , duk da dushewan fata da tayi hakan be hana nunawa ita din fara ce sosai ba . Dauke ganinsa a kanta ya yi yana kallon yanda Meenat ke binta da kallon mamakin ganinta , shi kuwa kauda kansa ya yi yafara kokarin shigewa daya daga cikin jerun motocinsa , da mamakinsa sai gani ya yi Yasmin ta bi kusa dashi har sun kalli juna ta dauke idanu bata gaishe shi , bakaramin shock ya shiga ba duk da yasan duk tsawon shekaru ko baze amsa ba zata gaishe shi , cikin hanzari ya kara kai dubansa akanta , hangota ya yi cike da girmamawa take gaishe da Tanimu me Gadi . Meenat dake kallonsa tabe baki tayi cikin siririyar muryanta ta ce , Daddy pls ina jiran kudin, ka tabbatar ka tura su kafun kafita ". takai karshen zancen tare da barinsa tayi cikin gida cikin hanzarinta domin kaiwa mominta labari da dumi duminsa, shi kuwa sai da ya share minti biyar ya tunanin sabon halin Yasmin , barin tunanin ya yi tare da yin transfert din kudin a account din Meenat . Ahanzarce ya tada motarsa . Tanimu mai Gadi cikin hanzarinsa ya bude masa gate , Alhaji na kokarin fita daga Gidan ya fara jero masa gaisuwa har kasa , amsa masa ya yi yana mai kokarin danna hancin motar wajen Gidan , yana fita da hancin motarsa daga gidan ya hango Yasmin bakin titi alamun napep take nema , tsaida tukin motarsa ya yi yana kallon yanda take daga hannu wajen tsayar da mashin , tana yi tana kallon agogon hannunta da dukan alamun hankalinta a tashe yake ganin za tayi latti , wata bakar mota ta faka gabanta kallon daya tayi wa motar ta fara yunkurin barin wajen , wanda ke cikin motar kyakkyawan matashine ajin farko , kallon daya zaka masa kasan dan hutune , domin agogon dake hannunsa na diamon ne , kara binta da motar yayi yana mai fadin " Baiwar Allah dan , dan Allah bari na sauke ki makaranta da dukan alamu kin rasa abun hawa ". Yakai karshen zancen yana mai kokarin bude murfin motarsa , ita kuwa kin tanka masa tayi , tare da samun mashin a daidai lokacin , ba ta jira sunyi ciniki ba ta fada masa makarantarsu , hawa mashin din tayi inda suka bar wajen , shi kuwa matashin murmushi ya yi jin sunan makarantar da zataje, daga haka yaja motarsa ya yi gaba .


Alhaji Isah Sharifai shi ma tada motarsa ya yi tare da fara bin sahun Yasmin, har ta iso makarantarsu , tana kokarin shiga ya yi daidai da isowarsa makaranta , kallon skul din yake da kyau ganin ansa *Raudat school* nan dai ya shiga bin dalibai masu shige da fice a makarantar . Wani dalibi ya gani , samun kansa ya yi da tsayar dashi ta hanyar kira , tambaya ya fara masa domin son sanin ajin da Yasmin Isah Sharifai take Cikin zazzare idanu dalibin ya ce , " Tabb wai Yasmin Sharifai , ai yanzu ta ce adaina kiranta da Isah sharifai ".


Zazzare idanu Alhaji ya yi bakinsa na rawa ya ce ,"

Wani suna take son a dinga kiranta da shi? ". Ya jefo masa tambaya.


" Yasmin Umar , shine sunan da tace mu ringa kiranta da shi kuma mu kanmu banda malaman mu , har mun fara manta asalin Isah Sharifai din ". Ya kai karshen zancen yana mai bin hanya domin yin uzurinsa . Shi kuwa Alhaji Isah kamar an datsa shi a wajen ya dade yana juya kalaman yaron , cikin rashin kuzari ya tada motarsa tare da barin wurin.



Meenat tana isa sashinsu labari taba hajiya Basma akan Yasmin ta fito farfajiyar Gidan bayan tasan suna nan ita da Daddy. Hajiya Basma cikin tsoron kada shirinta ya lalace ta ce " Meenat kyaleta dan uwarta zata gane shayi ruwa ne sai nayi sanadin da zasu bar gidan nan daga ita har shegun ya'yanta , da kuma Mariya dake zaune a gidan mu , dan kawai ta haife shi sai ta tare mana a Gida taci zamaninta , tazo kuma tace zataci da surukai haba wannan zancen karya ne wallahi ". Tana kai karshen zancen ta fara kokarin lalubo wayarta , dayan hannunta na kan Diyar Asma'u dake kwance saman cinyarta yar kimanin shekaru goma a duniya . Waya take yi da kawarta, nan da ta shiga bata labarin abinda ke faruwa, daga cen bangaren sosai ta nuna jijjiga da batun nata inda har ta nuna mata ya kamata , ayi sabon shirin domin gudun bacin rana.

Duk hirar da suke Meenat da Asma'u sai murmushi suke , cikin yaukin murya Asma'u ke fadin " ni wlh na tsani ganin su Yasmin cikin Gidan ubanmu , Daddy yace ba ya'yanshi bane to akan me zasu zauna mana Gida". takai karshen zancen tana kara matsewa jikin Mamarta. Hajiya Basma murmushi da ita kaɗai ta baiwa kanta sani take yi .


ABUJA CITY


Bayan kwana uku


Safiyar Litinin da misalin karfe goma


Ridwan yan jaridu makil a kofar Gidansa , yana daga cikin dakinsa sai tashin hayaniyarsu yake ji , duk da asaman bene yake , ahankali ya fara yunkurin sauka daga kan lallausan gadon barcinsa , idanunsa basu gama wartsakewa , sanye yake cikin tsadaddan kayan barcinsa mai kalan ruwan toka , ahankali yakai dubansa akan agogon dake makale a bangon dakinsa inda yaga karfe goma da kwata , jin tashin hayaniyar na karuwa yasa shi tattaro kuzarinsa tare da yin wajen window din dakinsa. Lallausan hannunsa yasa domin janye window glass din Dakinsa , tare da zura kansa domin ganin me ke faruwa , cikin zallan mamaki da rudewar tunani yaga.................




Makauniyar Shari'a taku ce


Comment and sharhi pls

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.