Free chapter · Read without an account

4

by Asmy b Aliyu · ALBI (zuciyata)



Hawaye kawai ke rolling akan face ɗinta, ta kasa baiwa Ummi amsar da take buƙata, maganar auren da Abbanta ya faɗa zai yi mata yafi komai tsaya mata a rai. Tabbas bata shirya yin aure yanzu ba, tana son tayi karatu mai zurfi da shine babban mafarkinta a duniya ta ganta a cikin jami'ar Ado Bayero. Da ace da Imran zai haɗa auren da sauƙi. Ƙara rushewa tayi da wani irin kuka mai cin rai da sauri ta rarrafa gaban Ummi ta rike hannunta still hawaye na zubar mata take faɗin. "Ummi kina jin aure Abba zaiyi min? Aure fa Ummi ni ina na isa aure Ummi? Da kananun shekaru irin nawa. Wallahi Ummi ina son na zama likita tamkar keda Imran. Karatun likitanci fa yayi shima Ummi, ki taimakeni Ummi wallahi ban isa aure ba, kuma kin san Abba zai iya Ummi." Rahama ta faɗa a haukace. 

Da sauri Ummi ta fisge kanta daga riƙon da Rahama tayi mata tana yi mata wani irin kallo take faɗin. "Bakison aure Rahama meya kaiki gidan su har cikin ɗakin barcinsa? shin bakiji yarda mutanen unguwar nan ke tsinewa hallayar Imran matawalle ba.? Ai wallahi da kije ki kwaso mana abun kunya ƙara ayi maki auren kowa ya huta, tunda ke magana ɗaya bata shiga kunnen ki. Nayi faɗa, nayi nasihar, nayi addu'ar amman duk a banza. Wallahi Rahama kafiyarki tayi yawa akan wannan tsinannen yaron, ko mahaifinki ya yarda da auren Imran Matawalle, ni bazan yarda ba wallahi koda bayan numfashina ban yarje maki auren wannan tsinannen ba." A fusace Ummi ta nufi stairs ba takarabi takan Rahama ba, wacce tsabar shock zama tayi akan marbles tana jin zuciyarta tamkar zata fito saboda tashin hankali. Duk yarda taso ta farantawa iyayenta akan dena zuwa wajen Imran kasawa takeyi, zuciyarta ta hanata hutawa daga bugawa duk akan ƙaunar da take yi wa Imran Matawalle. Tana ƙaunar Imran Matawalle tun kafin ta ma san meye so, ko yanzu bawai tana banbance soyayyarsa bane acikin zuciyarta, tasan dai kawai ganin Imran Matawalle a idanunta yana sakata wani irin farin ciki. Murmushinsa a gareta, tafiyar sa , komai dai na Imran Matawalle tana sonsa tana kuma girmamasa. Komai zai faru bazata yarda da wannan auren da Abbanta ke son yayi mata ba. Bazata karɓesa ba ko hakan zaisa iyayenta su juya mata baya, dan indai akan Imran Matawalle ne kowa zai ɓata da ita. Ta share hawayen idonta ta nufi stairs tana jin wani ciwon kai na damunta ga tafiar da taji Matawalle na faɗar zasuyi da Imran a yau, wanda Imran ɗin bai sanar da ita hakan ba. Ra'is na kallanta har ta haye, ya girgiza kai, ita dai Yaya Rahama kullum sai taja an doketa akan wancen guy ɗin. Ya juya shima ya nufi wajan tv. 


*****

Ya daɗe cikin bad mood saboda rashin shan beer, ya rarrafa da kyar ya janyo wayarsa. Al-Amin ya shiga kira ana ce masa wayar a kashe take. A ranar jirginsu Imran ya ɗaga zuwa ƙasar Russia. Matawalle yana kula da yanayin sa, sai dai ya sharesa ko acikin jirgin ana bada abinci amman Imran babu abunda yaci. Gaba ɗaya hankalinsa yana kan Rahama dan ya san yanzu tana can mahaifinta ya mata duka duk sabida kulawarta a garesa, dan yanaji a jikinsa duk inda take a halin yanzu bata cikin yanayi mai daɗi, kuma duk ta sanadiyarsa. Tabbas da zai iya durkusawa Abubakar Galadanci, da yaje ya duƙa yace ya basa auren Rahama. Amman bazai iya wannan kasadar ba, dan yasan ko ya durkusa masa akin banza ne, yarda yake da zuciyar arnaye. Kwana biyu da tafiyar Imran bai samu ya kira Rahama a waya ba, dan dama landline ce suke yi a ciki. Basu san duk yarda za'a haɗu Rahama da Imran ta kowace ƙofa Abubakar Galadanci ya toshe ta, kuma shi da kansa yake kai Rahama makaranta, haka zalika shi yake zuwa ɗaukar ta. 

Kamar kullum dawowar su kenan daga makaranta a bakin gate mahaifinsu ya aje su sai da ya tabbatar da shigar su ya juya motarsa zuwa office. Haka su Rahama suka shigo parlorn fuskarta tamkar hadari sai dai ganin Hajja zaune a parlorn yasa ta wani ruga da gudu gameda buɗe hannayenta duka biyu tana jin hawaye na cika idonta lokaci ɗaya ta fashe da kuka tana ƙanƙame Hajja.


"I'm so much happy to see you my Hajja, nayi kewarki sosai." Hajja ta shiga bubbuga mata baya. "Meye na kukan kuma bayan gani nazo? Ke tsiyata dake kenan wallahi Rahama saurin kuka gareki." Bayan hannu tasa tana share fuskarta da hawaye ya ɓata tace. "Hajja zaki daɗe a nan gidan? Dan Allah karkice zaki tafi da wuri, kiyi zamanki muna san ganinki." Hajja ta kamo hannunta ta zaunar da ita gefenta tana faɗin. "Zan ɗan kwana biyu kafin na koma, ke meye damuwarki ne da dole sai nabaro ko'ina na dawo gidan nan?" Ummi ce tayi saurin cewa. "Rabu da ita Hajja shegiyar rigima ce kawai irin ta Rahama. Kutashi kuje ku cire uniform kuyi wanka kuzo ga lunch yana jiranku." Rahama ta kalli Hajja tana da maganganun da takeson yi mata, tashi tayi suka wuce stairs, jiki na rawa ta cire kayan ta shiga bathroom. Mai aiki tazo ta kwashe uniform ɗin ta shiga ɗakin Ra'is shima ta kwaso nashi taje tasa a washing machine ta wanke su tas. Rahama bata daɗe ba ta fito, riga da wando tasa kanta babu hula, tare suka taho da Ra'isa Hajja ta kallesu. "Kai yaran nan har kunyi wanka?" Rahama taje wajanta, gefen dama ta kwantar da kanta tana faɗin. "Hajja muje muci abinci dake." Hajja ta ɗan shiga tureta tana daga jikinta tana faɗin. "Kai yarinyar nan akwai san jiki, ɗagani ni kije kici abinki, ina zuwa aka bani nawa naci." Sai kawai Rahma ta turo baki, duk da yunwar da takeji bazataci ba indai Hajja bataci ba dan gabaki ɗaya zuciyarta rawa takeyi ta kuma san rashin ganin Imran ne kwana har biyu. Ummi kam tashi tayi tabar parlorn, Rahama da sauri ta kalli Hajja. "Ina wayarki Hajja?" Hajja tasa hannu cikin lalitarta ta zaro wayar, Rahama ta karbe. "Me zaki?" Hannunta yana rawa lambar Imran take sawa a ciki wacca daman can Rahama ta tilastawa kanta haddaceta. "Hajja Imran zata kirawo, kuma Abbah da Ummi sun hanata." Shaye da toka Rahama ke kallan Ra'is tace. "Kai kuma yaushe ka zama munafuki? Ina ruwanka dani da zaka shiga rayuwata, ko kai ina samaka baki a lamurranka?" Ra'is ya wuce wajan dining yana murguɗa baki. Wayar bata shiga, Rahama ta buga wayar hannunta akan kujera, Hajja ta zaro ido ta kwace abarta tana faɗin." Sai kin fasa min ke kuma? Ki tashi kije kuci abinci aka ce." Farooq ne ya shigo tare suka zo da Hajja yana can b-q yana ɗan hutawa shine yanzu yace bari ya shigo. Kallan juna sukai shida Rahama. "Lallai ma, wai wannan Hajja take cewa za'a aura min." Cewar Rahama tana ɗauke kai daga Farooq dake shigowa parlorn. Sanye cikin riga da wando jeans light blue, ba karya Farooq akawai kyau, amman Rahama ganinsa take tamkar yafi kowa muni da bakin jini a duniya. Kusa da Hajja shima ya ya isa yana faɗin. 

"Hey my sweet Hajjana." Farooq ya faɗa yana zama a soofa idanunsa kyar akan Rahama. "Kai ni ba wani hey, tunda ka dawo daga ƙasar can kabi ka ishe mu da turancin banza." Murmushi sosai a fuskarsa saboda ganin Rahama kaɗai a yanzu ya mugun faranta masa rai. Ashe haka yarinyar ta sake zama? kyawunta ya sake fitowa? Lallai Abbie ya zaɓa masa mata dan tayi masa ɗari bisa ɗari. Yaji idan ba ita ya aura ba zai samu matsala a rayuwarsa. Rahama taci gaba da trying numbern Imran bata ko kalli inda Farooq yake ba. Shiru wayar bata zuwa har lokacin, cikin takaici ta sake buga wayar akan soofa tana rintsa ido tace. "Ahhhhh! Hajja wayar taki shiga, na shiga uku wayyo Allah na."

"Ke tafi can, ba yanzu Ra'is yace an hanaki neman waye yake da suna nema?" Daga can wajan dining Ra'is ɗin yake faɗin. "Hajja sunan shi Imran Matawalle." Farooq ya kallesu gabaki ɗaya a cikin wani irin yanayi. "Banda shirmenki Rahama ina ke ina jinin Matawalle? Mutumin da kiri-kiri ya nuna baya san mahaifinki, yayi yadda zai yi wajan ganin ya karɓe kujerar da Abbanku yake nema, shine ke kika damuwa dashi?" Rolling idanunta tayi ta taɓe baki. "Ni ba ruwa na Hajja, gabar da su Abba keyi bata shafi zumuncin mu da, Imran ba."

"Who is he Hajja?" Farooq ya tambaya shaye da toka. "Ga gidan Matawalle nan, wannan makocin nasu fa da yai karfa-karfa wajan zaɓe, shine wai banda shirmen Rahama har take mu'amala dasu." Ganin ana shirin ciwa su Imran mutunci yasa Rahama tashi ta haye stairs ranta a mugun ɓace. Da kallo Farooq ya bita harta shige ɗaki, ya miƙe da sauri yabi bayanta. "Wayyo Allah Imran where are you hhh? Kasa zuciya ta cikin ruɗani, ina ka tafi Imran?" Farooq tsaye yayi yana kallan yadda take birgima akan gadonta, gashin kanta duk ya barbaje, ribbon ɗin ya fice daga tufkar da tayi masa. Zama yayi gefen bed, turaran da ta shaƙa ne ya tabbatar mata da cewa ba Hajja bace haka zalika ba Ummi bace ba. Waigowa tayi a fusace, Farooq ne zaune a gefenta yana bin ta da wani kallo. Ta haɗe rai sosai ganin Farooq galadanci a ɗakin barcin ta. Tayi saurin matsawa daga gefe, hannu ya miƙa zai  kamo nata da sauri Rahama ta janye cikin tsiwa tace.

"Ni bana san kana taɓani idan ba haka ba zan gayawa Ummi." Murmushi Farooq yai dan yanayinta yanzu ya sake jefa wutar soyayyarta a zuciyarsa. "Abbie da Abba sun mana tunani mai kyau Rahama, auren mu zai daɗa ƙara zumuncin mu." shaye da toka Rahama ta zabura tana faɗin. "Wallahi I will never married you Farooq Galadanci, kana mafarki ne kawai." Taja uban tsaki. "Kaga nayi kalar aure a kananun shekaruna ? In fact ni bana sonka haka bazan aure ka ba wallahi ko sama da kasa zata haɗe." Da sauri Farooq Galadanci ya juya, hayewa gadon yai ya dafa kafaɗunta, a fusace ta shiga tureshi Farooq yai mata rikon da ba zata iya kwacewa ba. "I love you Rahama for the first time dana ganki. Zanyi taking care for everything naki Rahama, ki yarda ki amince min, meye na rasa da baki so a gurina?" Ta shiga turesa "Bana sanka, bazan aureka ba Yaya Farooq leave me alone."

Sakinta Farooq Galadanci yayi yana jin maganganunta na huting ɗinsa, bai taɓa tunanin zai faɗa matsanaciyar soyayyar Rahama Galadanci lokaci ɗaya ba, saboda koda Abbie yayi masa maganar bai ɗauki maganar nasa da muhimmanci ba. Duk a ganinsa Rahama kamar tayi masa kan kanta, sai da yayi karo da ita yau a cikin gidansu. Zuciyarsa ta rikiɗe da wata irin muguwar soyayyar ta. Gashi komai na yarinyya tana dashi yarda yakeso a jikin matar auren sa. 

Ƙananun shekaru kurum take dashi, amma tana da wani irin diri wanda duk namijin da yayi tozali da ita bai isa ya ɗauke kallonsa akanta ba lokaci ɗaya. miƙewa yai yana kallonta da kyawawan idanunsa yana faɗin. "Zamuyi aure dake Rahama, you are my choice, daɗin abin ma iyayen mu suna so no need to stress yourself." Wani ihu da tayi ne yasa Farooq saurin ficewa daga cikin ɗakin. Rahama ta ɗora hannu aka ta wani fashe da kuka mai cike da ban tausayi....






#Asmy B Aliyu

#Hajja ce


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.