Free chapter ยท Read without an account

Page 15

by Ramlat Abdulrahman Manga ยท NAZNEEN.....

*NAAZNEENโคโ€๐Ÿ”ฅ<15>*

EXQUISITELY BEAUTIFUL


#Mai_Dambu


'Top-Notch

Season 3

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…

Curewa wuri guda Hajiya Haulatu sukayi da yaranta, domin Nazneen ta zame musu abin tsoron, juyawa tayi ta nufi dakinsu. Duk yadda take sonsu haka take hakura da abin da suke mata, amma ba zata yarda su tab'a mata Nne ba.


Alhaji Adamu yana wurin aiki, Hajiya Haulatu ta kira shi tana kuka, balbaleta yayi da fada, ganin ba zata yi magana ba ya kashe wayar, can ya kuma kiranta shi ne ta ce mishi. "Yarinyar nan da ka kawo." Bai gama ji ba, ya kashe wayar. Tasan zai zo shi yasa ta shirya haka, aikuwa minti arba'in ya kawo shi gidan, lokacin da ya zo ya gansu a falon. "Me ya faru?" Fashewa sukayi da kuka, ta ce mishi "meyasa kasan yarinyar nan ba mutum ba ce, ka kawo mana ita?" Sharce hawaye tayi ta cigaba da cewa. "Saura kiris, ta kashe Baba karami." Kallon karin bayani yayi mata a rude. "Kamar ya?" Ya cilla mata tambayar, yana kallon Baba karami da yake nad'e cikin bargo, "ban san me tayi mishi ba."

"Papa...!" Ta kira sunan a shagwabe. Da dan sauri ya juyo yana kallonta har ta iso wurinshi, durkusawa yayi ya bude mata hannuwan shi. Shiga jikinshi tayi tana faษ—in. "Kasan Momma ta hanani shigar mata kitchen, shi ne ya zo ya kashe min tv. Ni bani na mishi kome ba, Angel of guardians ne yayi switch ษ—insa."

Sake rungumeta yayi yana shafa bayanta. Ya d'ago kai yayi yana faษ—in. "Daga yau kada wani ya kuma takura mata, idan haka ya faru zan dauki mataki."

Wannan abin ya b'ata musu rai, dama suna cike da haushin lokacin da aka kawota office din Alhaji Adamu an yi bikin kara mishi girma, kawai da ya tashi tafiya Nazneen ya dauka da Hajiya Haulatu, karshe Hajiya haulata ganin ba za a je da yaranta ba, tace ta fasa zuwa dole aka tafi tare dasu.

Abin da ya musu ciwo har suka ji kamar da basu biyo Daddy ษ—insu ba, yadda yayi ta gabatar da Nazneen a gaban kowa da nuna ita yarshi ce mai daraja. Ga kyau ga nutsuwa, Munayyah tana kallon wannan kayan bakincikin ta cewa Uwarta. "ina ji kamar na kasheta!" Rike ta uwar tayi tana girgiza mata kai. Ire-iren waษ—annan abin yasa suka tsaneta, gashi babu halin a tab'ata Aljanunta zasu dauki mataki akanka.

....... Kallonshi tayi sannan ta ce mishi.

"Ni ba zan koma Bauchi ba, i change my mind." Ware idanu yayi yana faษ—in. "Me?"

"Ba zanje bauchi ba!"

"Saboda me?"

"Allah bani zuwa bauchi, zan gayawa Malam." Ta faษ—a tana dariya, jan hancinta yayi yana faษ—in. "Zaki hada ni da kawarki."

"Ba zan koma Bauchi ba.".

"Ki koma na miki alqawarin kai ki London, idan kika gama primary school."

Murmushi tayi, tana faษ—in.

"Papa da gaske?"

"In sha Allah, da gaske."

Tsalle ta fara yi, tana jin wani irin dad'i.

"Zaki bauchi?"

"Eh zani."

Ya gama yanke hukuncin kaita can, domin yasan Innayo ba zata tab'a barin, yayi abin da ya dace ba, sannan idan tana nan abuja ba zai taba samun zaman lafiya ba, don haka ya saka a ranshi kafin ya tafi da ita bauchi, zai tattauna da Abdullahi domin ta haka zai nisanta Yarshi daga fitinar yan uwanshi da Matarshi da Mahaifiyarshi.

A duk lokacin da ya kalli yarinyar, sabon soyayyar mahaifiyarta yake kara cika mishi zuciya, yana ji kamar ya dauke yarshi ya boye ta. Bai auri Chioma domin yana sonta ba, abu biyu ya ja hankalinshi, kyanta da laluranta. Tunda ya mata jinya na tsawon kwanaki goma, shi kenan Yarinyar ta makale mishi.

A duk lokacin da ya tuna da haka, addu'a yake Allah ya tsare mishi Yarinyar shi kada ta faษ—a irin rayuwar da Uwarta tayi. Mikewa yayi ya nufi dakinshi.

Yana zaune Hajiya haulatu ta shigo, tana murmushi.

"Daddy ka dawo ne?"

"Eh na dawo."

Shiru tayi kafin ta ce mishi. "Batun zuwan mu Dubai da Yara baka ce kome ba." Kallonta yayi na wasu lokuta kafin ya ce mata. "Na soke zuwan ne, dama domin Nazneen zan biya. Yanzu kuwa na fasa."

"Amma!"

"Dakata min, kin san dai nace na fasa ko kuma bani da niyyar kuje. Tunda kin zabi haka. Ba damuwa ina ganin zaku koma Bauchi ke da yaran suyi karatun a can. "

"Bauchi!" Ta faษ—a tana mikewa, "eh bauchi, ko ba daga can kuka dawo nan ba?"

"Amma karatunsu fa?"

"Akwai makarantu a can."

Daga haka ya ajiye maganar bai kuma tanka mata ba, fita tayi fuuuu, ya kira Malam ya gaya mishi, shima dake yana bala'in tausayinta tare da soyayyarta, haka yasa ya bawa Adamun goyan bayan, sannan ya gaya masa cewa zuwa duk wata ya kama shi kenan. Sosa kai yayi yana faษ—in. "Eh malam, amma ina son na kara aure ne."

Shiru Malam yayi kafin ya ce masa. "Tow Allah ya tabbatar da alkhairi, amma kasan yana da kyau ka nime yar mutunci ko?"

"Eh malam, yar Dass ce tana aiki a nan bauchi babban asibiti. Yar gidan Alhaji Nuhu Dass ce." "Masha Allah, shi kenan."

Da haka suka ajiye maganar, za a tafi nima mishi auren, kanshi a sunkuye. Bai san zuwan ba, sai dai kamar kiftawa da Bismillah, ya ga kamar wani bakin mutum a kanshi, a dan tsorace ya D'ago kai yana fadin. "Kin bani tsoro."

"Papa! Kana son auren Dayyiba ko? Ita ai tafi Momma mugun nufi, gara ka hakura da ita. Kayi maneji da Momma. Amma Dayyiba shaidaniya ce fitinaniyar mace, idan ka aureta zaku sha wahala ne."

"Ya aka yi kika san sunanta?"

"Ina jin kana gayawa Baba Malam zaka kara aure, sannan a kaina kake son ka maida Momma bauchi ko? Kyaleta ta zauna da kai a nan, ita kuma wancan matar da kanta zata kiraka gobe ta ce ta fasa aurenka "

Daga haka ta saka kai ta fice daga cikin dakin, tana wakarta.

Dafe goshinsa yayi, dole ya hana Nazneen magana, domin aljanun da suke tare da ita, sun bude mata kunne da idanunta. Yana tsoron kada haka yasa ta rasa mijin aure.


Haka yayi ta shirin maida ta bauchi, yana ji kamar bai kyauta ba. Shi da gidanshi amma bai da ikon kawo kowa ฦ™arฦ™ashinsa, haka yasa bai kuma bin ta kan Haulatu da Yaranta ba.

Kamar yadda Nazneen din ta fada, haka ya faru Dayyiba da kanta, ta ce su hakura da juna. Bai yi mamaki ba sai ma godiyar da yayiwa Allah. Kwana biyu tsakanin ya dawo da Nazneen bauchi, bayan ya tsaya ya gama mata kome, shi da Tahir da yake son gani yarinyar ta cigaba. An sakata a Urban college, da drivern da zai na kaita. Duk wani abin bukata sai da ya ajiye mata.

Budar bakin Innayo ta ce mishi.

"Ban yarda ka sake kashe mata kudi haka ba, ai nima ina da hakki akanka."

Shiru yayi bai ce kome ba, Nazneen tana wurin Malam, amma tana jinsu kowa a gidan tana jin maganarshi. Murmushi tayi.

Haka tasha fura a wurin malam, tana gama sha ya ciro mata kunshin kilishi. Ta fara ci tana lumshe idanunta. "Baba Malam, wannan namar kullum ana ajiye min."

"In sha Allah, amaryata."

"Kace Innayo ta min wanka da ruwan barkono kenan."

"A'a waye ya gaya miki."

"Eh tana da mugun kishi, da son kanta tana son kowa ya zama."

"Shiiiii! Kul na kuma jin kin fadi haka. Ya kamata muyi wani abu akan aljanin da yake tare dake."

"Meye yayi maka?"

"Saboda ya bude miki, idanu da baki kina fadar magana."

"Ai har da kunne, daga nan ina jin goma tana zagin Innayo."

Maza yayi ya toshe mata baki.

"Bana ce ban da magana ba."

D'ago kai tayi tana faษ—in. "Kace Baba Malam"

Hawaye ne ya zubo mata, tana kallonshi sannan ta sunkuyar da kanta. "Maganar zata saka a tsaneki, dole na tsaya miki da rokon Allah, ya baฦ™i lafiya."

Gyada kai tayi, tana wasa da bakin rigarta. "Ba na miki faษ—a don bana sonki ba ne, a'a maganar ce bata da amfani kinji."

"Tow kuwa Baba Malam, Innayo tana ฦ™oฦ™arin raba ni da Papa, ni kuma ba zan yarda ba." Ta faษ—a idanunta suka fara juyawa.

"Kenan ba zaka rabu da yarinyar nan ba?" Malam ya daka mata tsawa, D'ago kai tayi tana dariya, idanunta yana wani irin juyawa ta ce.

"Muhammad Sani Malami, ce maka akayi zamu barta? Ai muna kan umarnin mu sauyin ฦ™addara ba zai rab'a mu ba."

"Kai wani irin mushuriki ne?" Dariya Nazneen ta saka tana kallon Malam. "Ba zamu rabu da ita ba."

"Zaku rabu da ita!" Inji Malam. Tabe baki tayi tana kauda kanta.

"Ku fita kafin na fara kona ku."

"Babu inda zamu je, domin muna tare da ita matuฦ™ar aka ce za a tab'ata sai mun bayyana, kuma ka ja kunnen matarka ko kuma daga yau mu fara takun saka da ita."

Shiru suka yi, ta fara hamma kafin ta kwanta a wurin.

Barci me nauyi yayi gaba da ita, shigowar Babanta Malam ya zuba mishi idanu, ganin yadda idanunshi suka kad'a jajjur.

A hankali ya zauna yana sakin murmushin yake, ya cewa Malam.

"Mamana tayi barci ne?"

"Me Uwarka ta kitsa maka?" Shiru yayi yana jin babu dad'i.

"Kasan ba zaka iya rike ta ba, ka saka ni baka ita? Kasan sai abin da Uwarka ta gaya maka na barka da yarinyar da ta nace zata zauna a wurinka akan mahaifiyarta?"

"Malam ya zan yi? Shi yasa naso da Uwarta tana nan, zata fi sakewa."

"Kasan Allah, wannan yarinyar akwai babban lamari akanta. Kada ka biyewa mahaifiyarka ku shiga hakkinta. Yanzu haka sun ce ba zasu kyale duk wanda ya tab'ata ba. Har yau na kasa gano bakin zaren dalilin samuwarsu a tare da ita ba. Abu daya na sani aljanin yana da alaka da irin aljanun da ake bautawa.

Na so, nayi dogon binciken akansu sai na fara sai abin ya lalace. Duk wanda ya rab'eta matukar mutumin kirki ne, Allah yana yalwata shi da kare shi, idan kuma ka nufe da sharrin zai koma kanka, zan gayawa mahaifiyarka da mutanen gidan nan, duk da nasan bai zama dole su yarda da ba. Amma idan suka ga wani abu a kan idanunsu zasu nutsu.

Ba fata nake ba, amma ban tab'a ganin aljani me mugun taurin kai irin Aljanin Nazneen ba."

"Malam ya zamuyi da ita? Bana son wannan laluran ya lalata mata gobenta." Ya faษ—a cike da damuwa. Murmushi Malam yayi sannan ya ce masa. "Idan aka yi hutu, kazo ka ษ—auketa."

Haka ya bar gidan bayan ya bawa Malam kome ya gaya mishi yadda suka yi da Innayo, sannan ya wuce Gombe.

Sai dare ta farka, Malam ya kalli yadda take mika ya ce mata.

"Lokacin sallah ya wuce, kiyi sallah kizo muyi karatu."

"Tow;" ta nufi cikin gidan, a bakin kofar dakin Innayo ta ga akwatin kayanta, kamar ta fashe da kuka ta ce. "A ina zan kwanta tow?" Ta shiga kokarin daukar akwatinta. Dauka aka yi cak sama, juyawa tayi ta ganshi sanye da farar shirt.

"Ina zaki iya dauka kayan nan." Ta shiga falon Innayo da kayan. A fusace ta sallame addu'ar da take yi. Ta ce mishi.

"Bana son munafunci, ku fice min a daki."

"Babu inda zata, kin isa ki hanata zama ne bayan kin rabata da ubanta." Inji Malam ya faษ—a yana shigowa cikin falon, haษ—e rai tayi tana hararanta.

"Shiga wancan dakin, ka ajiye kayan a dakin can, daga yau nan ne dakinta."

"Ban gane ba? Kana nufin daki za a bata?"

"Kiyi a hankali, shaidanun da suke kanta sai sun shayar dake mamaki zaki gane abin da nake nufi."

Daga nan ya fita tsakar gida, ya tara su yana musu nasiha tare da gaya musu muhimmanci azkar na safe da marece,

Ayatul kursiyyu

Suratul iqlas (kulhuwallahu)

Falaqi da nasi,,,, kafa uku uku,,,


Ko su kadai ka karanta sun isheka kariya,,, idan Kuma ka ita sauran addu'o'in da akeyi saika Kara dasu. Ga wasu daga ciki :

ุงูŽู…ู’ุณูŽูŠู’ู†ูŽุง ูˆูŽุงูŽู…ู’ุณูŽู‰ ุงู„ู’ู…ูู„ู’ูƒู ู„ูู„ู‘ูŽู‡ู ูˆูŽุงู„ู’ุญูŽู…ู’ุฏู ู„ูู„ู‘ูŽู‡ูุŒ ู„ูŽุง ุงูู•ู„ูŽู‡ูŽ ุงูู•ู„ูŽู‘ู‘ุง ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ูˆูŽุญู’ุฏูŽู‡ู ู„ูŽุง ุดูŽุฑููŠูƒูŽ ู„ูŽู‡ูุŒ ู„ูŽู‡ู ุงู„ู’ู…ูู„ู’ูƒู ูˆูŽู„ูŽู‡ู ุงู„ู’ุญูŽู…ู’ุฏู ูˆูŽู‡ููˆูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ูƒูู„ูู‘ ุดูŽูŠู’ุกู ู‚ูŽุฏููŠุฑูŒุŒ ุฑูŽุจูู‘ ุงูŽู”ุณู’ุงูŽู”ู„ููƒูŽ ุฎูŽูŠู’ุฑูŽ ู…ูŽุง ูููŠู’ ู‡ูŽุฐู‡ ุงู„ู„ูŽู‘ูŠู’ู„ูŽุฉู ูˆูŽุฎูŽูŠู’ุฑูŽ ู…ูŽุง ุจูŽุนู’ุฏูŽู‡ุงุŒ ูˆูŽุงูŽู”ุนููˆู’ุฐู ุจููƒูŽ ู…ูู†ู’ ุดูŽุฑูู‘ ู…ูŽุง ูููŠ ู‡ูŽุฐูŽู‡ ุงู„ู„ูŽู‘ูŠู’ู„ูŽุฉู ูˆูŽุดูŽุฑูู‘ ู…ูŽุง ุจูŽุนู’ุฏูŽู‡ุงุŒ ุฑูŽุจูู‘ ุงูŽู”ุนููˆู’ุฐู ุจููƒูŽ ู…ูู†ูŽ ุงู„ู’ูƒูŽุณูŽู„ูุŒ ูˆูŽุณููˆุกู ุงู„ู’ูƒูุจูŽุฑูุŒ ุฑูŽุจูู‘ ุงูŽู”ุนููˆู’ุฐู ุจููƒูŽ ู…ูู†ู’ ุนูŽุฐูŽุงุจู ูููŠู’ ุงู„ู†ูŽู‘ุงุฑู ูˆูŽุนูŽุฐูŽุงุจู ูููŠู’ ุงู„ู’ู‚ูŽุจู’ุฑู


Transliteration:'Amsaynaa wa'amsal-mulku lillaahi walhamdu lillaahi, laa 'ilaaha 'illallaahu wahdahu laa shareeka lahu, lahul-mulku wa lahul-hamdu wa Huwa 'alaa kulli shay'in Qadeer. Rabbi 'as'aluka khayra maa fee hatheehil-layla wa khayra maa ba'daha wa 'a'oothu bika min sharri maa fee hatheehil-layla wa sharri maa ba'daha, Rabbi 'a'oothu bika minal-kasali, wa soo'il-kibari, Rabbi 'a'oothu bika min 'athaabin fin-naari wa 'athaabin fil-qabri.



ุงู„ู„ูŽู‘ู‡ูู…ูŽู‘ ุจููƒูŽ ุงูŽู”ู…ู’ุณูŽู€ูŠู†ุง ุŒ ูˆูŽุจููƒูŽ ุงูŽู”ุตู’ุจูŽุญู’ู†ูŽุง ุŒ ูˆูŽุจููƒูŽ ู†ูŽุญู’ูŠูŽุงุŒ ูˆูŽุจููƒูŽ ู†ูŽู…ููˆุชูุŒ ูˆูŽุงูู•ู„ูŽูŠู’ูƒูŽ ุงู„ู…ุตูŠุฑ


Transliteration: Allaahumma bika 'amsaynaa, wa bika 'asbahnaa, wa bika nahyaa, wa bika namootu wa 'ilaykal-maseer


โ€จ


ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู…ู‘ูŽ ุฃูŽู†ู’ุชูŽ ุฑูŽุจู‘ููŠ ู„ู‘ูŽุง ุฅูู„ูŽู‡ูŽ ุฅูู„ู‘ูŽุง ุฃูŽู†ู’ุชูŽุŒ ุฎูŽู„ูŽู‚ู’ุชูŽู†ููŠ ูˆูŽุฃูŽู†ูŽุง ุนูŽุจู’ุฏููƒูŽุŒ ูˆูŽุฃูŽู†ูŽุง ุนูŽู„ูŽู‰ ุนูŽู‡ู’ุฏููƒูŽ ูˆูŽูˆูŽุนู’ุฏููƒูŽ ู…ูŽุง ุงุณู’ุชูŽุทูŽุนู’ุชูุŒ ุฃูŽุนููˆุฐู ุจููƒูŽ ู…ูู†ู’ ุดูŽุฑู‘ู ู…ูŽุง ุตูŽู†ูŽุนู’ุชูุŒ ุฃูŽุจููˆุกู ู„ูŽูƒูŽ ุจูู†ูุนู’ู…ูŽุชููƒูŽ ุนูŽู„ูŽูŠู‘ูŽุŒ ูˆูŽุฃูŽุจููˆุกู ุจูุฐูŽู†ู’ุจููŠ ููŽุงุบู’ููุฑ ู„ููŠ ููŽุฅูู†ู‘ูŽู‡ู ู„ูŽุง ูŠูŽุบู’ููุฑู ุงู„ุฐู‘ูู†ููˆุจูŽ ุฅูู„ู‘ูŽุง ุฃูŽู†

ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู…ู‘ูŽ ุนูŽุงููู€ู†ูŠ ูููŠ ุจูŽุฏูŽู†ููŠุŒ ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู…ู‘ูŽ ุนูŽุงููู€ู†ููŠ ูููŠ ุณูŽู…ู’ุนููŠุŒ ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู…ู‘ูŽ ุนูŽุงููู†ููŠ ูููŠ ุจูŽุตูŽุฑููŠุŒ ู„ูŽุง ุฅูู„ูŽู‡ูŽ ุฅู„ุงู‘ูŽ ุฃูŽู†ู’ุชูŽ. ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู…ู‘ูŽ ุฅูู†ู‘ููŠ ุฃูŽุนููˆุฐูุจููƒูŽ ู…ูู†ูŽ ุงู„ู’ูƒููู’ุฑุŒ ูˆูŽุงู„ููŽู‚ู’ุฑูุŒ ูˆูŽุฃูŽุนููˆุฐูุจููƒูŽ ู…ูู†ู’ ุนูŽุฐูŽุงุจู ุงู„ู’ู‚ูŽุจู’ุฑู ุŒ ู„ูŽุง ุฅู„ูŽู‡ูŽ ุฅู„ุงู‘ูŽ ุฃูŽู†ู’ุชูŽ3*


ุญูŽุณู’ุจููŠูŽ ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ู„ูŽุข ุฅูู„ูŽู‡ูŽ ุฅูู„ู‘ูŽุง ู‡ููˆูŽ ุนูŽู„ูŽูŠู’ู‡ู ุชูŽูˆูŽูƒู‘ูŽู„ู’ุชู ูˆูŽู‡ููˆูŽ ุฑูŽุจู‘ู ุงู„ู’ุนูŽุฑู’ุดู ุงู„ู’ุนูŽุธููŠู…ู7ร—


Transliteration: Hasbiyallaahu laa 'ilaaha 'illaa Huwa 'alayhi tawakkaltu wa Huwa Rabbul-'Arshil-'Adheem.ร—7


ุจูุณู’ู…ู ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ุงู„ู‘ูŽุฐููŠ ู„ูŽุง ูŠูŽุถูุฑู‘ู ู…ูŽุนูŽ ุงุณู’ู…ูู‡ู ุดูŽูŠู’ุกูŒ ูููŠ ุงู„ู’ูŽุฃุฑู’ุถู ูˆูŽู„ูŽุง ูููŠ ุงู„ุณู‘ูŽู…ูŽุงุกู ูˆูŽู‡ููˆูŽ ุงู„ุณู‘ูŽู…ููŠุนู ุงู„ู’ุนูŽู„ููŠู…ู3ร—


Transliteration: Bismillaahil-lathee laa yadhurru ma'as-mihi shay'un fil-'ardhi wa laa fis-samaa'i wa Huwas-Samee 'ul- 'Aleem.ร—3


ุฑูŽุถููŠุชู ุจุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ุฑูŽุจู‘ู‹ุงุŒ ูˆูŽุจูุงู„ู’ุฅูุณู’ู„ูŽุงู…ู ุฏููŠู†ุงู‹ุŒ ูˆูŽุจูู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏู ุตูŽู„ูŽู‰ ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ุนูŽู„ููŠู‡ู ูˆูŽุณูŽู„ู‘ูŽู…ูŽ ู†ูŽุจููŠู‘ูŽุงู‹3ร—



Transliteration: Radheetu billaahi Rabban, wa bil-'Islaami deenan, wa bi-Muhammadin (sallallaahu 'alayhi wa sallama) Nabiyyan.

ร—3

ุณูุจู’ุญูŽุงู†ูŽ ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ูˆูŽุจูุญูŽู…ู’ุฏูู‡ู


Transliteration: Subhaanallaahi wa bihamdihi.(100times)

โ€จ

ู„ูŽุง ุฅูู„ูŽู‡ูŽ ุฅูู„ู‘ูŽุง ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ูˆูŽุญู’ุฏูŽู‡ู ู„ูŽุง ุดูŽุฑููŠูƒูŽ ู„ูŽู‡ูุŒ ู„ูŽู‡ู ุงู„ู’ู…ูู„ู’ูƒู ูˆูŽู„ูŽู‡ู ุงู„ู’ุญูŽู…ู’ุฏูุŒ ูˆูŽู‡ููˆูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ูƒูู„ู‘ู ุดูŽูŠู’ุกู ู‚ูŽุฏููŠุฑ


ุฃูŽุนููˆุฐู ุจููƒูŽู„ูู…ูŽุงุชู ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ุงู„ุชู‘ูŽุงู…ู‘ูŽุงุชู ู…ูู†ู’ ุดูŽุฑู‘ู ู…ูŽุง ุฎูŽู„ูŽู‚ูŽ


Transliteration: 'A'oothu bikalimaatil-laahit-taammaati min sharri maa khalaqa. (3times)

ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู…ู‘ูŽ ุตูŽู„ู‘ู ูˆูŽุณูŽู„ู‘ูŽู…ู’ ุนูŽู„ูŽู‰ ู†ูŽุจููŠู‘ูู†ูŽุง ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏู


Transliteration: Allahumma salli wa sallim 'alaa nabiyyinaa Muhammadin (10 times)

"Kada ku sake kuyi wasa da addu'a. Domin kuwa shaidanun da suke jikin Nazneen, suna iya zame mana fitina. Idan kuna son zaman lafiya, kada wani ya nufi cutar da ita. Sannan Addu'a ya zame mana jiki kamar kullum.....

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.