Free chapter · Read without an account

#34

by Aunty Mamee · FANSA KO ƘIYAYYA

*FANSA KO ƘIYAYYA?* 💔


*©️AuntiMamee*





_Page34 _


   Tun daga wannan ranar bata sake kunna wayarta ba a haka har tayi kwana shida da haihuwa a ranar ne kuma dangin Mummy sukazo Banda Mummy dake zaman takaba.

Kowa na iya ƙoƙarinsa a kanta, Walida dama idan ta dawo daga school ita ke lura da komai na babay dan ta zage ta koya har cewa takeyi idan ta samu hutun school zatazo Kano dan tasan suna komawa wai Naja zata ƙwace mata fadarta a wajan baby.  "Hmm" kawai shine abinda Binazir ke faɗa a duk lokacinda Walida tayi irin wannan zancen..

Duk ƙoƙarin da dangi keyi akanta,hakan bai ɓoye halinda zuciyarta ke ciki ba, dan kallo guda zakayi mata ka tabbatar da tarin damuwar da ke shimfiɗe a fuskarta amma sai suka alaƙanta hakan da mutuwar Dady da kuma mutuwar aurenta da yazo lokaci guda, wanda da gaske hakan takeji amma tarin nadamar abinda ta aikata masa a baya ya danne zafin mutuwar auren nata dukda shima tanajinsa sosai a ranta.

Bisa ra'ayinta da kuma zaɓinta, ranar suna yarinya taci sunan NAFISA, sunan da tun randa ta haihu ta ayyana shi a ranta da daddare, cikin dare kuma bayan bacci ya gagareta ta tashi zaune tayiwa 'yar tata huɗuba da sunan.

Mummy na gida tana jiran Umma ta kira danjin labarin haihuwar amma shiru, sosai lamarin ya ɗaure mata kai amma dan karta sawa kanta damuwa ta ajiye batun a gefe dukda hakan na damunta.

Ranar suna VC suka haɗa duk abinda ke faruwa sai an hasko mata, a haka akaci suna aka watse washegari dangin Mummy da sukazo suka ɗau hanya.

 Barrister ma ya kirata a wayar Aunty Lubabatu da Mummy ta tura masa nomban yayi mata Barka. ranar suna haka ya aiko matarsa tun daga Kano tazo har Katsina ta hanyar kwatance da sukayi bayan ya haɗata da Aunty Lubabatu. ***************************

Ƙasa jurewa yayi daya tabbatar har anyi suna amma ba'a kirasa an shaida masa sunan abinda ya kasance mallakinsa ba, cikin ɓacin rai ya kira nombanta amma abin takaicin a kashe yake wani irin tafasa zuciyarsa keyi. ɗaga wayar yayi zai kwaɗata da ƙasa amma sai ya fasa hakan yasa ya kira Umma cikin fushi, yana kira ta ɗauka.

  "Yanzu dan Allah Umma menene amfanin a kiraki a martabaki a baki girmanda koni da nake matsayin mahaifi ba abaniba amma ki kasa tambayar abinda aka haifa da lafiyar babyn?" Shine abinda ya sauka cikin kunnan Umman wanda ya sata buɗe baki haɗida zaro idanu tun sanda ya fara maganar

  "Tooo kai kuma yau abinda ke daminka kenan? to bazan tambaya ba Babban mutum kuma idan ɗa kakeso insha Allah nanda shekara guda zaka riƙe naka a hannu tunda ita Bishirar tace ita ba ruwanta da bidi'a ko lefe sadakinta kawai takeso" Itama Umman ta mayar masa in a serious tone.

Ajiyar zuciya ya sauke tareda sosa gashin girarsa, yana saisaita zuciyarsa.

  "Umma wai dan Allah me kika gani tattare da wannan yarinyar da kikabi kika takura kanki kan saina aureta?"

  "Alkairi Babban mutum, shina gani"

Ajiyar zuciya ya sauke yana wani tunani, kodan ya huta da mitar Umman badai aurene kawai akeso yayi ba? adai ɗaura ace wance matar wane ce? Zai amince kodan ya samu ya rabu da wata damuwar ta Umman da a yanzu baida ikon zuwa Sabon titi dan tsoron maganar auransa da yaje da zancen zata fara tarar sa.

 "Shikenan naji" abinda ya faɗa tareda kashe wayar ya jefata kan gado haɗida riƙe kansa da yaji yana sara masa.

Umma kam kallon wayar tayi sai kuma ta saki murmushi da furta ALHAMDULILLA.

Naja bata gidan ta tafi gidan ƙawarta ƙunshi da kitso, hakan yasa ta fita dan tasan har taje ta dawo bai zama lallai zata dawo ba.

Kai tsaye gidan Baba Garba taje Bata samesa a gida ba sai iyalansa.

Bishira sai rawar jiki ake wajan tarbarta, haka Mamanta dan Bishira na bata labarin sauyin da aka samu daga Umman.

Sosai suka sauketa cikin mutumci, umma bata ja wani dogon lokaci ba ta sanar musu da abinda ya kawota na amincewar Babban mutum. Kaɗan yarage Bishira bata rungume Umman ba, kawai saita dake ta shige ɗaki da gudu dan gudanar da farin cikin ta, wai ta kusa tayi aure? aurenma Samir inta wanda tun tana secondary School Allah ya jarabeta da ƙaunarsa.

Maman Bishira kam cikin farin ciki take faɗin "kenan sabon gidansa da Bishira tacemin kin faɗa mata zai ajiyeta?"

 "Kwarai kuwa da aniya tunda har yanzu tsoronta yakeji ya kasa faɗawa iyayenta azo a kwashe kayanta ai rabon Bishirar ne wannan sabon gidan shiyasa waccen bata shiga gidanba kuma fa har mota yana nan da ita a ajiye"

 "Karma ki sake ki sashi yace azo a kwashe kayanta a barsu harsai bayan bikinsa da Bishiran, ai gaggawa naga sheɗan" Maman Bishira tayi saurin faɗa dan tasan wane Samir, muddin aka kwashe kayan Binazir tasan wannan danƙareren sabon gidan ya haramta ga 'yarta tsaf zai iya cewa idan bazata zauna a tsohon gidanba tayi gaba.

 "Yo ni dama meya shafeni aini ko zancensu ma bana tunowa, gida kuma dama tunda da wani harda Mota a ciki ai dole a saka mace a ciki."

Sosai Maman Bishira ta ninka farin cikinta sanda Umman ta tashi tafiya shatara ta arziƙi suka haɗa mata, Maman Bishira na shaida mata da zarar baban Bishira ya dawo zata faɗa masa wannan daddaɗan labarin.

************************************

Abu kamar wasa saiga zancen biki ya fara tafiya dan sosai Umma da iyayen Bishira suka riƙe wuta dan biki duka wata Uku aka saka, idan Umma ta tambayesa kuɗin wani abin in yaga dama bada idan baiga dama ba kuma kai tsaye zaice kuɗinsa bana hakan bane idan Umman ta fusata ta masa faɗa "a fasa bikin mana tunda da matsala" shine amsarda yake faɗa wa Umman wanda ke sata barin maganar tambayar kuɗin saidai ta koma naɗe tabarmar kunya da faɗin "duk abinda nakeyi dan kai nakeyinsa Babban mutum ita waccan da bata damu da kaiba mene bakayi mataba a nata auran sai kuma da abin yazo kan wacce ta san mutumcinka zaka ringa noƙe aljihu? wannan dai ba hali bane" hakan take cewa ta ƙara gaba ta barshi da ciwo a zuciyarsa.

Naja idan ranta yayi dubu ya ɓaci dan duk abinda ake kawai dan anfi ƙarfinta ne ta kira nomban Auntynta yafi sau adadi amma layin baya shiga gaba ɗaya, a gefe kuma ga tausayin Yayan nata dan ta fahimci shima fin ƙarfinsa akayi, dan akwai lokacinda ta taɓa gwadasa bayan yazo gidan tace  "Yaya yanzu kishiya zakayiwa Aunty Bishira?  daga tafiya yin wanka? Cabbb!". ta faɗa tareda jinjina lamarin dan tasan Auntyn tata akwai zafi.

a lokacin kallonta kawai yayi ya lumshe idanunsa tareda sosa gashin girar sa haɗida sakin ajiyar zuciya, sai kuma ya miƙe ya nufi hanyar fita daga ɗakin, abinda ya bata mamaki shine ƙwallarda taga ya share da handkachif inda ya zaro a wandonsa sanda ya isa bakin ƙofar ɗakin sannan ya ƙarasa ficewa.  

Har yau idan ta tuna wannan abin yakan tsaya mata kuma takanji inama tayi tsuntsuwa ta isa ga Binazir ta jawota ta dawo gidanta, amma tasan indai da rabo ba abinda zai gagari ubangiji.

************************************Binazir kam saidai muce Allah ya shiga lamarin dan gaba ɗaya ta zama wata iriya sakamakon nadama da tunani da tasawa ranta, abu ɗaya ne ke iya sanyaya mata zuciya shine fuskar Nafisa da ta mayar mata da suna NAFI. Fuskar yarinyar da take ganin kamanninta ya koma sak na mahaifinta shine abinda kesa zuciyarta ta sanyaya ta wani ɓarin kuma zuciyarta kan ƙara shiga damuwa a duk sanda taga fuskar Nafin, dan hakan na tuna mata da nisan tazarar dake tsakaninsu a yanzu. 

A Yaune zata koma Kano sakamakon kwana arba'in cur da tayi, komai takeyi jiki a mace takeyinsa dan saida Aunty Lubabatu ta tambayeta damuwarta amma saitace mata ba komai hakan yasa Aunty Lubabatu tayi zaton sabone da ake cewa turken wawa.

Saida Aunty Lubabatu ta sata ta shiga har gidanda takai ajiyar motarta danyi musu sallama da Godiya, haka sauran mutanan da sukayi mata kara wajan haihuwa da suna.

Awa biyu da wasu 'yan mintuna ne suka kawosu har GANDUN SARKI.

Zo kaga Mummy baki yaƙi rufuwa gata ga jikallanta.

Aunty Lubabatu na gama Hutawa tace hanya zatabi ba yadda Mummy batayi da itaba kan ta bari ta kwana taƙi amincewa badan Mummy tasoba, haka ta barta ta tafi da tarin kewa mutumci da ƙimar matar a Zuciyarta, ko Binazir saida ta matse ƙwalla sanda sukeyin sallama da Aunty Lubabatn.

Yamma nayi kasancewar Mummy kwananta biyu da fita takaba, ta shirya Nafi sai wajan siyayya. Sosai ta kashewa yarinyar kuɗi, dan wasu kayan ma irin na wasa data siya mata sai ta kusan fara tafiya amma saboda zumuɗi har an tanadesu.

  Bayan fitar Umma ne taji gidan yayi mata shiru hakan yasa ta janyo jakunkunan kayanta da ta dawo dasu don shiryasu cikin wardrobe, handbag inta data jefa ciki washegarin sadakar bakwan Dady ranarda zasu tafi KT ta gani, da sauri ta janyo jakar tana jujjuyata tana kallonta kamar maison gano wani abun a jikin jakar, sai kuma ta zugeta da sauri dan zaro takaddar da takeda tabbacin ciki ta sata.

Kuma zatonta ya kasance gaskiya dan takaddar na ciki kamar yadda ta sata. 

Jujjuya takardar ta farayi a hankula, sai kuma ta nufi ƙarƙashin pilo ta ajiyeta tareda sakin ajiyar zuciya.

sukuku ta gama gyaran ɗakin nata sannan ta shiga toilet danyin wanka, tana fitowa aka kira sallar magrib kuma alokacin ne su Mummy suka dawo. Yaƙe kawai tayi ganin irin tarin siyayyarda Mummy tayiwa Nafin "ni dama yanzu nasan na zama bare a gidannan an samu wadda ta fini"

"Sosaima kuwa" Mummy ta faɗa cikin tabbatarwa tareda karɓar Nafisa da aka gama bawa mama.

Murmushi kawai tayi ta saka hijabi dan tada Sallah.*******************


Wajan sha biyu na dare bacci ya ƙaitewa idanunta, tunda magrib ta ke so ta karanta takaddar sakinta amma tana tsoron abinda zata tarar dan ta fahimci ba iya sakin ya rubuta ba, harda wani dogon bayani dayayi wanda take zaton kan munanan ɗabi'unda tai tayi masa ne ya rubuta.

Ajiyar zuciya ta sauke tareda kallon ɓarinda Nafi take a kwance tana baccinta hankali kwance.  

Tashi tayi zaune cikin fargaba ta ɗaga pilonta tareda zaro takaddar da ke ƙarƙashi.

Kallon takaddar kawai takeyi cikin fargaba, jiki a mace ta maidata ƙarƙashin pilon ta gyara kwanciyarta.

a ƙalla ta ƙara shafe awa guda amma sam idanunta da zuciyarta sun ƙeƙashe ba abinda zuciyarta ke muradi samada tasan irin matakin hukuncinda ya yanke mata a cikin takaddar. 

Runtse idanunta tayi da ƙarfi har saida idanunta suka amsa mata sannan ta buɗesu tareda sauke su akan Nafisa, wani irin ƙarfin zuciya ne ya shigeta, hakan yasa ta ƙara tashi zaune a karo na biyu ta ɗakko takaddar, bata bari ɓarin raunanniyar zuciyarta tayi mata huɗuba ba, ta buɗe takaddar dukda bugawarda ƙirjinta keyi mata.

  "(Ga takaddarki nan na baki amma ba da manufar da kike nufiba, na bakine kawai dan kinnemi hakan, koda ace takadda ɗari kika nema zan baki indai zaki tsira da lafiyarki keda abinda ke cikinki.   

  Bansan laifin me nayi mikiba BINAZIR bayan abinda nayiwa Dady wanda hakan aikinane, kin tsaneni, ba kya ƙaunar kwanciyar hankalina. Biki damu da halinda zan shiga ciki ba nida zuciyata.  

Banida lafiya Binazir amma saboda ƙiyayyarda kikayimin kin kasa gane halinda mijinki ke ciki.  Kece sila zuciyata nayimin ƙuna da zafi kin min laifi da aurena ki keɓe da wani wanda ba muharraminki ba? har kina amsan abin hannunsa sannan kuma kiyi masa murmushinda ban taɓa samun irinsa daga gareki ba? ya kike tunanin zuciyata zata kasance? da bakinki fa kike faɗamin Samir ba saurayinki bane mijinda zaki aurane nan gaba. Kinsan munin kalmar kuwa? ba a wajena kaɗaiba har ga Ubangijin mu ni dake . zan rantse miki Binazir tun lokacin ban ƙara samun lafiya da sukuni a zuciyata ba, it hurts! ba abinda kemin yawo sai kalamanki da yadda na ganku tare jiya, but ba yadda zanyi.

ga takaddar na baki Ni SAMIR ABDYLLAHI na amince miki da kuma yardata kitafi gidanku har zuwa lokacin da zuciyarki zatayi sanyi ta huce ta karɓeni a matsayin miji ko nanda shekara nawa ne BINAZIR ina jiranki, keɗin tawace nini kaɗai kuma danni akayiki.

Ina kuma yi miki ta'aziyar rashin Dady, Allah ya gafarta masa, Allah ya amshi ibadunsa, Allah ya kyautata masa makwanci ina kuma fatan UBANGIJI ya yafemasa dukkan wani kurakuransa daya aikata na fili dana ɓoye.

ina roƙon a kowanne dare kafin kwanciya da ɓullowar alfijir da dukkan wata salla da zakiyi, ki dinga samin kanku a addu'a keda unborn child ina, Allah ya saukeki lafiya BINAHH)"

wani irin kuka ta saki mai sauti tareda rungume takaddar a ƙirjinta. Kuka takeyi ba ƙaƙautawa dan harta manta da babynta dake kwance kusa da ita.

sautin kukar yarinyar ne yasa ta tsagaita da kukan tareda maida idanunta kan yarinyar har lokacin tana kuka tana kallonta ba tareda ta ɗauketa ba.

Mummy ce ta shigo ɗakin jin kukan yarinya bayanda ta tashi yin nafila. 

Turus tayi tana kallon Binazir dake kuka ta tasa yarinya gaba tana kallo, tunanin kar azama ɗaya yasa tayi sauri ta nufi Nafi ta ɗauketa tareda jijjigata amman yarinya taƙiyin shiru, waigowa Mummy tayi ga Binazir dake binsu da ido, bata bi takanta ba, ta nufeta tareda zaro mama ta sawa Nafi a baki.

Tsitt yarinya tayi shiru, ba ajin komai sai sautin tsotsonta da sheshsheƙar kukan Binazir.

saida Mummy ta tabbatar da Nafisa ta ƙoshi ta koma bacci sannan ta zareta ta kwantar. 

bata ƙara bi takan iskancin Binazir data bata haushiba ta nufi fita don gabatar da sallarta.

  "Yanzu Mummy ashe kunsan Dadyn Nafi bai sakeniba kuka ha'inceni?"

  











*Contact me 👇

**** 

*Comment*

*Vote*

*Share*

*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.