Free chapter · Read without an account

#40

by Aunty Mamee · FANSA KO ƘIYAYYA

*FANSA KO ƘIYAYYA?* 💔


*©️AuntiMamee*





_Page 40 _


        WASHEGARI


Umma ce da amintattun maƙotanta da Naja datayi musu rakiya zaune a palon gidansu Binazir. Dukkansu sunyi shiru bamai magana bayanda suka gaisa da Mummy kowa ya ɗinke bakinsa yayi tsit.

Mummy ce ta kalli Naja dake zaune tsuru ta saki ajiyar zuciya da faɗin "Naja ki tafi wajan Auntyn taki mana, ai tana cikin ɗakinta" Mummy ta faɗa.

A kunyace Naja ta miƙa tareda nufar ɗakin Binazir da batasan mai akeyi a cikin palonba.

Maido da kanta Mummy tayi ga Umma tareda sakin ɓoyayyan ajiyar zuciya.

  "Mudai munzo bada haƙuri ne bisa laifin da muka aikata " Baba jumnai ta katse shirun.

   "Wanne irin laifi kuma?" Mummy ta tambaya cikin yaƙe

  "A'a karki nuna bikisan komaiba baiwar Allah, laifine anyishi da gangan kuma gaskiya ba'a kyauta ba ba kuma ayiwa yarinya adalciba amma dukda haka munzo neman alfarma ayi haƙuri a amashemu a yafe mana, kuskure dai munyishi amma Insha Allah hakan bazai sake faruwa ba" Hajiya Inna ta faɗa tareda zungurar Umma kan ta furta wani abin.

Ita dai Mummy batace komaiba dan ba azo gaɓarda zatace inba, so take Umman ta magantu da kanta sannan itama ta faɗi abinda ke cikin zuciyarta.

   "Banso bayan mutuwar maigidanki haɗuwata dake tabiyu ta kasance irin wannan haɗuwarba, naso haɗuwace wadda zamu kasance cikin farin ciki da ƙara fahimtar juna amma sai shaiɗan yayi tasiri a zuciyata bisa wani dalili nawa na daban, amma ina neman afuwa a yafemin bisa kuskurena insha Allah abu makamancin irin haka bazai sake faruwa ba" Umma ta faɗa cikin sanyin murya amma wani ɓarin zuciyarta yana tausayin Bishira tareda nuna mata bata kyauta mata ba, kuma tuhumar kanta take tunjiya mene abin rashin kyautawar da tayiwa Bishirar dan tazo ganin jikarta ? amma dukda haka batajin daɗin zuciyarta.

  Ajiyar zuciya Mummy ta sauke tareda kallon cikin idanun Umma bako ɗar tace "bazan ɓoye mikiba Ummansu Naja, har yau inajin zafin abinda kika aikata wa gudar jininki, dukda kin girmeni hakan bazai hana na gaya miki gaskiya da abinda ke cikin zuciyata ba" Mummy ta faɗa muryarta da sirkin ɓacin rai

  "Ban damu da rashin bibiyar dawowar Binazir gida da bikiyi ba, amma haka tana sauka na kiraki na faɗa miki amma sai kika nuna halin ko inkula, wanda ko kaza na kira na shaida miki ta ƙyanƙyashe ƙwai, ya dace ki kirani ki tayani murna amma sai kika banzatar da lamarin, yarinyar nan tana dawowa da rawar jiki ta shirya zata takai miki jikarki, bata riƙeki ba, bata ƙullaceki ba, amma sai kika tarbeta da wulaƙanci irin wanda ko baiwa ce ita bai cancanci kiyi mata hakaba ballantana tana da daraja, kuma fin ƙarfinta akayi wajan aura mata ɗanki, kusan tilasta mata akayi amma haka take zaune dake da Naja kamar ba komai a tsakanin su, shiyasa bazan ɓoyemiki ba, banajin zafin Samir kamar naki, dan akoda yaushe yana abinda zai faranta miki ne koda shi zai cuci kansa, da ace kinso yazo yaga jininsa nayi imani harga Allah bazaiyi sakan gudaba zai zo ga gudan jininsa amma kin hana hakan ke kuma biki zoba, ina amfanin irin hakan?" Mummy ta ƙarashe cikin ɗaci.

Numfashi Umma ta sauke tareda kallon Mummy "harga Allah naji daɗin zuwa nan da har kika samu damar fitarda abinda ke cikin zuciyarki, amma zancen gaskiya bansan Babban mutum baizo ba wallahi, nidai nasan ban taɓa yimasa maganar yazo ko baizoba ko maganar ansamu ƙaruwa ba, amma ko maine na ɗauka kuma ina nema a ƙarayin haƙuri" Umman ta faɗa cikin sallamawa.

 "Gaskiya laifi anyi laifi mai girma saidai ayi haƙuri a yafe mana a dubi girman Allah da zuri'a a yafe komai a fuskanci gaba" Baba Jummai ta faɗa cikin sigar ban haƙuri.

  "Kuma nasan haryau Biki san sunan yarinyar ba ko? Hmmmm Nafisanki akayiwa takwara ana kiranta da Nafi kamar yadda mahaifiyarta ta tsara hakan" Mummy ta faɗa tareda share ƙwallar takaicin da ta tarar mata a idanunta.

 Da sauri Umma ta zaro idanunta waje tareda dafe ƙirjinta, sai kuma tayi ƙasa da kanta idanunta cike taf da ƙwalla, wani irin rauni, dana sani da nadama ne ya shiga zuciyarta, gefe guda kuma wata soyayyar kaka da jika ne ke ratsa zuciyarta na ƙaunar jikarda bata taɓa gani ba.

 "Mudai ayi haƙuri dan Allah komai ya wuce Allah ya yafe mana baki ɗaya a taimaka a fito mana da jikar tamu muganta" Hajiya Inna ta faɗa cikin sigar bada haƙuri.

Ajiyar zuciya Mummy ta sauke tareda kallon yatsun hannunta, sai kuma ta ɗago idanunta akan Hajiya Inna da faɗin  "Ni abu idan ban faɗeshi bane yakecin zuciyata, amma idan na furta shi shikenan na gama dashi kuma, Allah ya yafe mana baki ɗaya" ta ƙarashe tareda miƙewa tsaye dan zuwa kiran Binazir.**

 Sanda Naja ta shiga ɗakin Binazir da sallama, shiru taji anyi, hakan yasa ta dan leƙo da kanta, anan ta samu Uwar da 'yar a kwance kan gado suna bacci. A hankula ta taka har wajan gadon tasa hannu ta ɗauki Nafi, firgigit Binazir ta farka a tsorace idanunta suka sauka kan Naja dake ɗauke da Nafi a hannu, tsaida idanunta tayi kaɗan akan Najar sai kuma ta saki Numfashi tareda miƙewa ta nufi toilet dan watsa ruwa, bayan ta fito ne ta kalli Naja dake goyeda Nafi a baya da faɗin "Ni dama zaki dinga zuwa kullum kina goyatan dan bason goyon nakeba dandai Mummy ta matsane" ta faɗa cikin mita.

  "Ai idan kika dawo gida kinsan dama nice 'yar raino" naja ta bata amsa kanta tsaye.

Dakatawa Binazir tayi da shafa manda takeyi tana kallon Naja, sai kuma ta saki huci tareda cigaba da shafa manta ba tareda tace komaiba.

 "Da gaske akwai sihiri jikin Umma kuma Alhamdulillah, yanzu ina ganin sauyi dan tunda na bawa malaminmu labarin halinda ake ciki ya bani wani ruwan addu'a yace na tabbatar Umma ta shanyesa, da yake Ba rubutu bane tofi ne haka nayita bata tsawon kwana uku a matsayin farin Ruwa kuma masha Allah, ina ganin Nasara Aunty tunda ga Umma cikin palon gidannan tazo bawa Mummy haƙuri tareda ganin jikarta Nafisa" sune kalamanda Suka dakatar da Binazir daga shirin da takeyi na fita daga ɗakin, dawowa tayi da baya zuciyarta na bugawa da sauri, waje ta samu a bakin gadon ta zauna idanunta akan Naja dake wasa da yatsun hannunta.

  "Kikace Umma na palon gidannan?" Kaɗa kai Naja tayi daidai sanda Mummy tayi sallama tareda shigowa cikin ɗakin.

Dubanta takai ga Naja dake goyeda Nafi da faɗin "agogo Sarkin aiki, to kikaita palon za'a ganta" Mummy ta faɗa tareda juyawa tabar ɗakin hakan yasa Naja tabi bayanta.

 Shiru tayi tareda lumshe Idanunta sannan ta buɗesu lokaci guda, wani irin sanyi jikinta yayi dan tanada tabbacin ba kawai dan Umma tasha ruwan rubutu ne tazo gidan ba, no tsarinsa ne hakan dan shekaran jiya da dare ta goranta masa kan abinda Umman tayi mata she knows tunda ta jishi jiya shiru ba kira ba sms tasan yanacan Yana planning wani abune amma bata taɓa tunanin Umman da kanta zai turo tazo gidansu ba.  "Ya Allah, ka mallakamin shi mallaki na har abada, Ubangiji kasa alkairi a zamantakewata dashi kasa ya kasance alkairi gareni Ya Rabbi!" ta faɗa a fili tareda share wata guntuwar ƙwallar da ta tarar mata a idanunta she knows she had totally Fall in Love with him.**

 Wata irin bugawa ƙirjin Umma tayi sanda ta ɗora idanunta akan Nafisa, dan sakk Nafinta sanda tana jinjina saidai shi yaro ba'a yanke masa hukuncin kamanni harsai ya girma. wata iriyar zazzafar ƙaunar yarinyar ne ke ratsa cikin ɓargo da zuciyarta, haka kawai taji ƙwalla ta tarar mata a idanunta ƙwalarda batasan kona mene ba, tabbas karamcin wannan ahalin ya wuce inda ake zato bata damu da sanin yadda sukasan labarin Nafin taba, tunda suka furta sunsanin ita yanzu karamcinsu kawai take gani.

  "Ina ita sirikar tamu ai Akira mana ita mu gaisa" Baba Jummai ta faɗa cikin sigar lallali kamar mai neman wani abu wanda yanayinda tayi maganan yasa Mummy murmushi da faɗin "aina ɗauka wajan jikar taku kawai kukazo" ta faɗa da tsokana.

  "Allah sarki, ni dama abu biyu ya kawoni jira nake a gama murnar Jikalle sannan naji yaushe 'yata zata dawo gidanta, dan dai Yakamata ace tana ɗakin nata tunda wanka ta tafiyi kuma ta dawo saita koma abune dai akayishi cikin huɗubar shaiɗan tareda son zuciya saidai fatan ALLAH ya yafe mana" Umma ta faɗa murya a sanyaye.

Mummy ce ta tsaida Naja dake shirin barin wajan da faɗin "ki turo Auntyn taki Naja" 

 Kusa da Mummy ta zauna tareda jam'in gaida su su duka, da kulawa suka amsa mata 

  "Umman su Naja ce keson magana dake" Mummy ta faɗa tareda barin waja.

Gyara zamanta tayi jiki a mace tareda kallon Umman dake rungume da Nafi.

  "Duk abinda zance miki ko zan miki ban isa na goge tabon abinda nayi mikiba, amma abu ɗaya nake nema a wajanki shine alfarma, wadda ita mukeci a duniyarmu, kiyimin ita ki yafemin abinda nayi miki bisa kuskure da son zuciya ni 'yar adamce kuma Ni Uwace, lokacin da kika tafi da ciki jikinki hakan ba ƙaramin tayarwa da Babban mutum hankali yayi ba wanda ya gaza samun kwanciyar hankali da nutsuwa kuma abinda ya ƙara sani a shakku da damuwa shine ba yadda banyiba kan ya sanar dani inda kike saiya yimin shiru hakan yasa nayi zargin akwai matsala a zamantakewar taku wanda shaiɗan yayi tasiri a zuciyata daidai wanna lokacin amma ni harga Allah bikiyimin komaiba, sannan ina kuma neman alfarma ta biyu Kidawo gidanki dan Allah kodan zuri'arda Allah ya haɗa bazan ɓoye mikiba kinsan zuciyar Babban mutum ko lokacinda ba zuri'a a tsakaninku kin fini sanin ra'ayinsa a kanki ballantana yanzu , wallahi sanda kikaje na ɓata mikinnan dukana ne kawai Babban mutum baiyiba amma a ranar har gori saida yayimin haka ya ɗau fushi dani" ta sauke numfashi "ban faɗa miki bane danwai zan miki daɗin baki, ina faɗa mikine kawai dan kisan martabar da kike dashi a idanun mijinki wanda mahaifiyarda ta kawosa duniya ma bata isa taci zarafinki ya ƙyale da sunan kawaiciba" Umman ta faɗa tareda sauke numfashi dan batada abin faɗa kuma da yarage.

Nan dai su Baba Jummai suma suka saka baki wajan bata haƙuri tareda neman biko, ita dai batace komaiba kanta na ƙasa, ajiyar zuciya ta sauke sanda kukan Nafi ya ƙwaceta.

Da sauri Umma ta miƙo mata Nafin da faɗin "maza a sallameta kada tayi fushi" hannu biyu tasa tareda karɓarta ta nufi ɗakin Mummy dan turo musu ita.

A haka sukayi sallama suka tafi cikin mutumta juna zuciyoyinku kuma fesa dan kowa ya amayar da abinda ke cikin zuciyarsa ba sauran ƙyllaci kunya ko fargaba, amma Umma ta tafi da ƙaunar jikarta a zuciyarta sai kuma tarabbabin ƙin cewar komai da Binazir tayi na gameda komawanta ɗakinta.*********************

   

 "Abba yau kaine a gidan....." Maganar ta maƙale sakamakon wanda tayi ido biyu dashi a zaune gefensa.

 Sun gama girki kenan itada su Asabe ta nufo ɗakinta tayi wanka, tana tsaka da saka kaya Mummy tazo ta shaida mata Barrister yazo yana nemanta a palo tareda ɗaukar Nafi dan kaiwa Barrister ita dan ita ya fara tambaya a gidan wanda da sauri Binazir ta zura doguwar rigarta ta fito cikin ƙamshi da taku.

  Ajiyar zuciya ta sauke tareda neman waje a ƙasa ta zauna tareda gaida Barrister jiki a sanyaye.

  "Wannan dai ba halinki bane ƙin gaida mutane Uwar Nafi, bani kaɗai bane a palon" ya faɗa cikin yiwa Nafi dake kan cinyarsa wasa.

Ɗago idanunta tayi ta kalli Barrister kaɗan sam hankalinsa ba akanta yakeba amma kuma ya iya zaro magana daga inda yake, murmushi tayi a zuciyarta tareda kallon gefenda yake.

 Karaf idanunsu suka sarƙe dana juna wanda ya haifarwa da kowanensu bugun zuciya lokaci guda, janye idanunta tayi tareda furta "Barka"

Kai Barrister ya girgiza tareda gyaran murya.

Hakan yasa duk suka maida hankalinsu garesa dai-dai nan Mummy ta shigo ɗauke da drinks ta samu waje ta zauna itama.

  "Hajiya Jamila" Barrister ya Kira Mummy 

 "ina jinka Barrister" ta faɗa itama tareda bashi dukkan attention inta.

"Nazo ne kan maganar Zaman Binazir a gida, kwanaki biyu da suka wuce mijinta ya sameni kan batun dawowarta nikuma na gaya masa 'yata bazata koma gidansa ba, ba tareda magabatansa sun shiga cikin lamarin ba, kuma Alhamdulillah yayi yadda nace shine yanzu na kawosa kamar yadda ya nema kuma koda bai nemaba nima idan kika ɗauke waccan matsalar, inada niyar zuwa naji zaman me yarinya takeyi alhali da aure a kanta. wanna matsalar da mahaifiyarsa tazo ta warware shi, shiya hanani korata ɗakinta, amma tunda yanzu komai ya daidaita inaso naji zaman me kuma takeyi a gida?" 

Ajiyar zuciya Mummy tayi cikin bashi girmansa ta furta "zaman jiran Umarninka take dan ban isa na shiga sha'anin aurenta kai tsaye batare da ka saniba" 

Murmushi yayi da faɗin "indai nine waliyinta Kuma wakilin mahaifinta, ina mai bata umarni ta koma ɗakinta nan da kwana biyu, Allah kuma ya jiƙan Alhaji ya rahamta masa Allah ya ida cika masa burinsa na yalwar arziƙin zuri'a a tsakaninku "

  "Ameen ya Allah, Ubangiji kuma ya kaimu" Mummy ta faɗa cikin sanyin murya dan itama burinta kenan tunda komai ya wuce 'yar tata ta koma gidanta bawai dan ta gaji da itaba, saidan hakan shine martabar kowacce 'ya mace kuma tasan shine burin mijinta na ƙarshe bayan neman yafiyar ubangijinsa. 

  "Allah yayi muku albarka ku duka ya kuma raya zuri'arku" Barrister ya faɗa tareda miƙewa ya ɗauki lemon kan tray ɗaya sannan ya miƙawa Samir Nafisa haɗida yiwa Mummy sign kan tabarsu a palon.

  Ajiyar zuciya ya sauke bayan fitar Barrister da kuma barin Mummy palon.

Tsam ya miƙe tareda komawa kusada ita kaɗan ya zauna yana kallonta Nafisa rungume a ƙirjinsa.

Ɗan ja da baya tayi kaɗan tareda ɓata fuska.

   "Ina taya Nafisa murnar komawa gidan mahaifinta saidai ba wanda kika sani bane, dan 'yata bazatayi maƙota da gidanda aka siyesa da kuɗin cultism ba"










*Contact me 👇

**** 

*Comment*

*Vote*

*Share*

*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.