Free chapter · Read without an account

4

by salmeert sani salman · SHEIKH IMAM 🌹

🌹 SHEIKH IMAM🌹



By


YAR LELEN ROYAL STAR



Page....4



... Sheikh Muhammad Aleeyou Imam shi ne cikakken sunansa, Amma ana masa lakabi da (Sheikh Imam)....



SHEIKH IMAM D'a ne ga Aleeyou, wanda ya kasance hamshakin Dan kasuwa da duk fadin duniya babu kamarsa, yana simogarin kaya daga wata kasa zuwa wata kasa, a takaice dai shi babban dila ne na kaya kama daga kayan Abin ci kayan sawa da sauran ababen Amfani, haka yana siyan kayayyakinmu na gida Nigeria kamar su Auduga , zobo , fata d.s yana aikawa da su k'asashen waje domin a safartasu su koma wani abun amfanin, bugu da kari kuma yana da kamfani nasa ba kansa da ake buga takalman fata da kuma kamfanin robobi, sosai ya shahara yake kuma amsa sunansa.

Sun haifi SHEIKH cikin gata da kulawa, in da tun yana da shekara biyu Mahaifinsa ya daukesa ya kai sa chan wata makaranta da take Madina wadda ake kai yara tun kafin su fara magana domin su tashi da larabci da kuma karatun Al-qur'ani a bakinsu...



Bai dawo k'asar haihuwarsa ba sai bayan da ya cika shekara Ashirin da biyar cib, shima a sanadiyar rasuwar mahaifinsa, mutuwar nan ta girgiza dubbsn mutane musamman ma na jikinsa sosai, sanan mutuwar tazo da abubuwa daban² na abun mamaki wanda har mutane da yawa suke zargi da tunanin cewar ba mutuwar Allah yay ba akwai sa hannun Yan uwa ko wasu na jikinsa, haka aka zo rabon gado, duk da Yana da Yara har biyu ga mata, amma hakan bai yan uwansa wawure dukiyarsa ba, dan abun da aka bar musu ba wani abun azo gani bane.




Babu wanda yay wa dangin mahaifinsu magana don su ko da aka ce su kai kara kotu sun wawurewa Yara arzikinsu, sai cewa su kai Arzikin bawa ai na jikinsa, in Allah yawa bawa arziki to bb wanda ya isa ya karbesa, idan kuma yay ka wanda bashi da shi to fa tabbas ko duniya zasu taru don su azurtaka, ba zaka tashi daga abun da ya tsaga na arzikinka ba , da haka ta ci gaba da kula da Ahlinta, tana kokarin ganin ta zauna da su don debe musu kewar mahaifinsu, amma IMAM ko da na second daya mutuwar mahaifinsu bai tab'a fita a ransa ba, ya kara wani irin shiru², bb ruwansa da kowa, harkokin da yasa gaba kawai yake yi, da haka ya koma gurin karatunsa, wanda daga wannan zuwan ne bai kara zuwa ba sai da yana da shekara 30 cif, lokacin ya gama karatunsa tsaf, sai dai fa jami'atul Madina ta rik'esa domin ya yi musu aiki, domin shi din babban likitan kwakwalwa ne bangaren daya kuma yana koyarwa a jami'a, kyautar 'Ya sukutukun Baba Hameed da ya kasance Yaya wa Babansu Imam, ya bawa Ummie kasantuwar tana matukar son 'ya mace saboda bata da ita, sai ta karb'a da hannu bibbiyu.




Wanda dalilin yasa bai fiye samun zama ba sosai, amma duk da haka yakan yi kokarin ziyarta mahaifiyarsa a ko wane karshen wata daya ko biyu, domin duba halin da take ciki da kuma kaninsa, daga nan ya bada karatu a masallatai da aka gayyacesa, sannan Kuma baya kasa a guiwa gurin amsa gayyatar k'asashen duniya da yake samu, ya iya karantar da Mutane da natsar da zuciyoyinsu, zai yi wuya ya je jami'o'i bayar da lectures ba'a samu wanda ya musulumta ba, hakan yasa ake matukar Alfahari da shi domin yana matukar kawowa Musulumci ci gaba.



A cikin lokaci kadan yay kudi na ban mamaki, wanda ki a iya aikin zuwa jami'o'i ya tsaya to ya taka babbar nasara balle kuma har da aikin Asibiti a sashen mafi daukaka da ba kowa ne kan iya jurar karatu a sashen ba sai wanda ya mayar da hankali , sannan yake da natsuwa....




Wacece Aizza....


Cikakken sunanta shine Khadija Ahmed, kuma ita haifaffiyar garin Katsina ce , mahaifinta shahararren mai kudi ne sannan dan siyasar da ake ji da shi, ta wani fannin kuma Yana dan tab'a black market, Mahaifiyarta bafulatanar Adamawa ce , sun hadu da mahaifinta a wani taron karawa juna sani (Samina) ita ma Mahaifinta Mai kudi ne sosai a Adamawa , basu jima da haduwa ba su kai gaggarumin biki sosai aka hada, kasantuwar kudi da kud'i an hadu, sun jima sosai kafin Allah ya basa haihuwa, mahaifiyar tana haihuwa bata ko juya ta ga abun da ta haifa ba Allah y karb'i abun sa, hakan yasa mahaifinta ya dauki son duniya ya daura mata ya nuna mata gata da wata soyayya na ta tab'a kowa ba komai , tayi duk abun da take so ba tare da sha yi ko Jin dar ba, tun tana karama ta tashi da wannan izzar da kuma karfin da mahaifinta ya bata, ta sha raina manya a gabansa sai dai yay dariya, duk abun da zatai baya daukarsa a matsayin laifi, shi koma mai tai dai² ne ko da kuwa ba dai² bane, hakan yasa suka ringa samun sab'ani da mutane a kanta, hatta da makaranta kusan a gida tayi ta, don kar a b'ata mata, sannan kuma kar a doketa, don haka special teacher ya daukar mata, don ta samu ingantaccen ilimi, ya ginata sosai akan boko, bb Addini sam a cikin rayuwata, sunan Allah ma tana ji dai ana fada ita ma take fada, amma bata san komai ba, hatta da Sallah yinta kawai take ba don tasan sharadodi da ka'idojinta ba , ba ma ki yaushe take yi ba,mahaifinta y kara aure, inda matar take tsananin kula da ita,sai dai duk da haka bai mata ba, hakan yasa bata ko shiga harkar matar, tai mata rashin kunya a gaban Baban amma baya cewa komai, in kuma matar tai mishi mgnr sai ya hau ta da masifa ita bata son yarsa, ita bata me ne ne haka zai ta mata mita.





Mafarin kara lalacewarta lokacin da ta shiga higher level ne ta hadu da Layleerh da Beerbah, wanda anan abubuwan suka kara ta6ar6arewa, suma yaran masu kudi ne sosai, wanda aka nuna musu gata makamanciyar tata, an rainesu akan suyi komai ba komai, su tab'a kowa bb abun da zai faru domin sune masu k'asa.



Fadawa harkar shaye² shine babban abun da suka fara jefa kansu a ciki, dagan an kuma sai lesbian, bayan kuma mugayen aiyuka suke aikatawa a b'oye....





Tafiya yake a hankali yana tasbihi da yatsunsa har ya karasa masallacin, cikin natsuwa ya kwada kiran Sallah a babbar masallacin Anguwar, Kai tsaye ya sauka a kunnuwan Al'umma da dama. Cikin sauri mutane suke ta zuwa ga Sallah , Cikin kasalar da yaji ya saukar masa suka gabatar da Sallah, ko da suka idar, zama ya yi yay karatu sosai sai guraren 6 ya tashi zuwa gida.



A parlour ya tarar da Ummie zaune kan Sallayarta tana jan chasbaha, zama ya yi kusa da Ummie, cikin natsuwa da girmamawa yace "Barka da safiyya Ummie", ya fada cikin sanyin harshe , hannunta ta sa a kansa cikin Jin sanyi a ranta tace "barka dai Muhammad", cikin sanyi ya kara yin k'asa da kansa, yana mai jin matukar dadi idan ta kirasa da sunansa na gaskiya, har ya kan ji kamar ta fi kowa iya fad'ar sunan saboda yarda take fitar da ko wacce kalma , "Allah ya maka Albarka Muhammad, ubangiji y kareka daga sharrin mutum da Aljan, Allah ya tsare gabanka da bayanka, ubangiji ya rabaka duk wani abun cutarwa ya azurta min Kai da mace ta gari da zata tarairaya min kai, ta adana min kai , ta tallafi maraicinka", wani rauni ya ji ya zo masa a ransa, cikin kara yin kasa Kai da wani sanyi da ya mamayesa yace "Ameeen yah Ummie", daga haka ya tsuke bakinsa ba tare da ya kara cewa komai ba, sai wasa da hannunsa da yake, magana yake son yi, ko wani abu yake so, amma kuma bakinsa yay nauyi ya kasa fada.




Cikin so da kauna ta ce "Coffee ?", Bai yi magana ba sai zuba mata idanu da yay, hakan kuma ne ya alkalanta mata cewar lallai fa coffee yake so, mikewa tai don had'o masa, tana kara jinjina miskilanci da rashin son magana irin nasa, tunani tai sai kuma ta ga da yawan surutu marar amfani gwara shiru mai amfani .



Don shi mutum ne da bazai tab'a bude bakinsa yay magana ba tare da ka dauki wani darasin rayuwa, ko na zamantakewa ba, sau da dama wani Abokinsa da shine kawai Abokinsa a duk duniya ya sha ce masa "kai din Allon duba ne, sannan Kuma baka maganar banza, dukkan maganar da zaka yi tana da amfani, ko ba'aga amfaninta yanzu ba, gaba za'a gani, Ina matukar Jin dadin tarayya da kai", sai dai ya d'aga kai ya kallesa kawai.



Bata jima sosai ba ta dawo da wani madaidaicin flask sai wani tray da aka jera masa cups masu kyan gaske, a gabansa ta ajiye masa, duk'awa tayi da niyyar zuba masa, cikin sauri ya riketa, jujjuya mata kai yay, kafin chan kasan mak'oshi yace "Ummie zan zuba", ya fada dak'yar kamar an masa dole.



Zubawa yay cikin cup ya fara sha a hankali yana dan lumshe idanunsa, da taune lips nasa, wanda zafin coffee din ke ratsawa, "ko zaka kawo na hutar ma da shi ?", Ta fada tana kallon yarda yake dan yatsina fuska da taune bakinsa, jijjiga Kai yay a'lamar aa.



Amaya ce ta fito daga bedroom nata da kayan barci masu santsi, kanta ba hula gashinta da aka mata kalaba ya zubo, zama tai gefen SHIEKH, tana gaishesa, Yarinya ce da ha zata wuce shekara biyar ba, sun dan saba da Sheikh duk da ba wani sake mata yake ba, sannan ba wata magana, don duk duniya da mutum daya wato Ummie ya juri yin magana shima ba wata mai tsawon ba, duk maganarsa bata wuce kalma biyu, ukku biyar, Ummie kawai yake iya yin maganar da ta kai kalma goma da ita.




Sai da ya gama shan Coffee, ya kalli Ummie, a hankali kamar mai koyon magana yace "Ummie Asrat ya shirya by 8Am ", yana gama fad'ar haka ya shige ciki......




YOUR ƳAR GABAN GOSHI 😂.



YAR LELEN ROYAL STAR........

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.