Free chapter · Read without an account

3

by Aishatu Abdullahi Idris · Sawun Giwa

*SAWUN GIWA*

_Ya take na Raƙumi_


             



_By_

*Aishatu Abdullahi Idris*

_REAL ESHAA_



_In ana dara Uwa kan zaɓi💃🏻 Kamar yanda Fuskarta ya kasance fari haka zalika zuciyarta ya kasance fari ƙalll tana da wankekkiyar zuciya da batasan menene baƙin ciki,Hassada,ko ƙyashi ba alkhairin Allah ya cigaba da bibiyar rayuwarki Aunty Aysha Aliyu Garkuwa🥰 tabbas ke ɗin ta musamman ce..._



*F-R-PG 3*

Cikin ƙanƙance Ido Indu ta watsa musu kallon banza kana tace.

“Mtsss Sannu Matar gida da ace kin cika cikakkiyar mara mutunci da kunya zuwa zakiyi kai tsaye kice Indu ɗauki jakar ki kibar gidan nan bana son ganin ki tunda naga da Mai dattin hula aka haɗa kuɗi aka sai gidan kinga dole ki tsara yanda za'ayi”.


Ta gyara tsayuwar tare da kallon Lateefa data tsirawa TV Idanu tamkar bata san me akeyi ba tsaki taja aranta kana ta maida kallonta kan Meenah dake huci dogon tsaki taja kana ta cigaba da cewa.

“Ke wacece da har zaki zo gidan Yayana kice zaki tsara masa yanda zaiyi da rayuwarsa da Ahalinsa!?,Toh tun kafin na fitar dake ki tattara ƙazaman ƙafafunki da kuturun munafurcinki ki koma inda kika fito dashi domin idan haƙuri na ya ƙare zan iya cire kunya da mutunci na miki shegen duka”.

Afusace Meenah ke kallonta tana girgiza ƙafa yayin da zuciyarta ke ƙuna baki ɗaya bakinta ya mutu!jira take Lateefa tace wani abu amma sai taga ta ƙurawa TV ido.

Cike da isa Indu ta cigaba da cewa.

“Zama agidan nan yanzu na fara tunda dai gida gidan Yayana ne ba gidan tsohon wani ba koda yake ma wasu Uban nasu bashi da gida Albarkanci gidan miji akeci dan masu dattin hula nacan gidan haya duk ƙarshen shekara ana yawon maula da Allah baku mu samu”.

Ta yamutse fuska kana tace.

“Ana cin Albarkanci gidan miji amma sai feleƙen banza da ɗagawa wanda ba zai amfanar da mutum da komai ba kai Allah karabamu da zuciyar munafurci da Annamimanci tirrr! da masu irin wannan halayyar”.


A zuciye Meenah ta miƙe tana wani irin huci tace.

“Keee Indu,ko Hindatu kike da suna to wallahi hawainiyarki ta kiyayi ramata zan ɓaɓɓalla ki inga uban daya tsaya miki ni ba Lateefa dake ki keyiwa cin kashin da ranki ke so bane take ɗauka?”.

Tsayuwa Indu ta gyara tare da harɗe hannunta aƙirji kana sai kuma ta taɓe baki kallon sama da ƙasa tayi mata cike da cusa ta kaici tace.

“Me na sama yaci bare ya bawa na ƙasa!?,Ance da kare ana biki agidanku yace mu gani aƙasa to bari kiji

Idan ma turo ki akayi to ina dai-dai da zamin ko wani Gafalalle zancen ke ba Lateefa ba ce kuwa toh ki zama Lateefan kiga ikon Allah”.

Da sauri Lateefa ta kalleta jin yanda ta kira sunanta kai tsaye amma bata ce komai ba.

Wani Miskilin murmushi Indu ta saki kana tace.

“Tabbas ke ba Lateefa bace, Sannan ba zaki taɓawa kasancewa Lateefa ba dan wallahi idan kece amazaunin ta saina karairaiyaki,In ma turo ki akayi domin ki tun kareni toni wandon roba ce dai-dai da ƙugun ko wacce shegiya”.

Ta ida maganar tare da juyawa tashiga kichen zuciyarta ba daɗi.


Masha Allah Sosai kichen ɗin ya tsaru komai Akimtse tsaf-tsaf Cike da ɓacin rai ta ɗauki Plate ta buɗe Babban Warmers dake wajen ta ɗibi White rice ta zuba kana ta ɗibi sterw da yaji naman rago tasa wani roba ta buɗe tasa cokali mai ɗan faɗi ta ɗibi hadin Coslow ta zuba agefen shinkafar.

 jingina bayanta da jikin sink tayi tare da ɗibar cokali ɗaya ta kai bakinta da ƙyar ta haɗiye bawai Dan babu daɗi ba sai dan ɓacin rai dake ɗawainiya da ita kasa ci tayi hakan yasa ta ɗauki wani empty plate ta rufe Anutse ta juya ta fito karo suka kusa bugawa da Lateefa dake ƙoƙarin shiga.

Anutse Indu ta ɗauke kanta daga kallon Lateefa ta ratsa gefenta zata wuce.

Lateefa kuwa ganin tana ƙoƙarin ratsata ta wuce yasa tayi saurin riƙo tsintsiyar hannunta babu walwala atare da ita tace.

“Hindatu ashe baki da kunya da mutunci ban sani ba?,Ƙawar tawa zaki ciwa mutunci ko bataci daraja taba ai zataci darajar Mijinta, Amma saboda baƙin rashin kunya dake ɗawainiya dake har kina jefa min magana kamar sa'arki!?”.

Ta sake ɗaure fuskarta tare da cigaba da faɗin.

“Agaskiya kin bani kunya wannan abinda kika yi ba waye bane face rashin hankali da zubar da mutunci ina kallonki kamar wayayya mai hankali ashe dai kuskuren fahimta nayi”.

Cikin rashin walwala Indu ta kalleta tare da cewa.

“Ok Good ina fatan yanzu kin fahimci hakan sannan wani abune nayi na rashin kunya da rashin mutunci ita ya kamata ki faɗawa haka bani ba ko bakiji abinda ta faɗa bane?da zaki tsareni da tambaya kinga ki riƙe kanki!?”.

Ta wani ɗaure fuska tare da cigaba da faɗin.

“Kada ki manta Hausawa sunce idan tsoho baiji kunyar hawa jaki ba,to jaki ba zaiji kunyar kada tsoho ba dan haka shi mutunci madara ne idan ya zube ba zai kwasu ba ita kuma ƙawar ki idan bata fita sabgata ba saina tsula mata madaran rashin mutunci wanda sai tayi dana sanin sanina rayuwarta”.

Afusace Lateefa ta dakatar da ita ta hanyar cewa.

“Dakata Hindatu bana son rashin kunya shin Meenah sa'ar kice!?,Da zaki ce dan ta faɗa miki magana zaki mayar mata ko kuma so kike ki nunawa duniya cewa baki da tarbiyya!?”.


Da sauri Indu ta ɗaga mata hannu cikin ɓacin rai tace.

“A'a Aunty Lateefa ki tsaya iya matsayinki rashin tarbiyya kuwa kinsan dai wanda basu da tarbiya amma bani ba dan banga shegen da zai faɗa min magana ban mayar masa ba”.

Ta gyara jakar dake kafaɗar tace.

“Wallahi babu wani alaƙa dake tsakanina da ita ina ɗaga mata ƙafa saboda darajar mijinta ne dan haka ki faɗa mata ta kama girmanta idan kuma ba haka ba ina mai tabbatar miki zan sa ƙafa in Shure sauran mutunci da nake ganinta dashi”.

Baki Lateefa ta saki cike da mamaki cikin rawan Murya tace.

“Hindatu Ni kike faɗa wa magana son ranki kamar wata sa'arki mena miki da zaki min irin wannan sakayyar tun kina ƙarama na renaki naci kashinki da fitsarin amma yau Ni kike yiwa rashin kunya!?”

Kafaɗa Indu ta ɗaga cikin ko in kula tace.

“A'a kinsan dai ita gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata idan maganata ta ɓata miki rai kiyi haƙuri Mom Lateefa kada ki la'anceni”.

Ta ida maganar tare da ficewa batare data sake kallon inda take ba.


Tana fita ta samu Neenah jingine da gate ɗinsu da alamar fitowarta take jira.

Ajiyar zuciya Neenah ta sauƙe tare da kallon Indu da tayi kicin-kicin da fuska cikin sanyin murya tace.

“Me kika tsaya yi Indu na kai minti goma atsaye ina jiranki har na yanke shawarar shiga saboda munyi letti sai kuma naga fitowarki”.

Siririn tsaki Indu taja tare da sakin Ajiyar zuciya kana ta fesar da numfashi tare da cewa.

“Kiyi haƙuri amma Meyesa baki shiga ba tun da kika ga ban fito ba?, dan Allah Blue eyes ki daina biyewa wannan matar ko kuma kina nufin saboda ita zaki daina shiga gidan ne?”.

Cikin sanyi Neenah ta girgiza kai tare da fesar da numfashi kana tace.

“Haba dai Indu babu abinda zaisa in daina zuwa wajenki kuma yanzu ma Ina da niyyar shiga kenan kika fito”.

Kai Indu ta girgiza kana tace.

“Hmmm Blue eyes kenan nasan ko da zan kai awa ɗaya ban fito baza kishiga ba kin dai faɗa ne amma bakomai zan sanarwa Yah Imraan komai”.

Ta ƙarashe Cike da ƙunan zuciya da takaici.


Zare ido Neenah tayi tare da juyasa ta kalleta ganin yanda Indu tayi kicin-kicin da fuska yasa ta sassauta murya tare da faɗin.

“Dan Allah kada ki faɗa masa komai na faɗa miki inada niyyar shiga sannan babu wacce ta isa tashiga tsakanin mu”.

Ƙwaffa kawai Indu tayi tabbas zata sai tawa Meenah da Lateefa tunanin su musamman Meenah...


Cike da kulawa Neenah tace.

“Ya dai Indu meye faru dake naga kamar ranki aɓace ko dai nice na ɓata miki rai!?”.

Cike da takaici Indu ta girgiza kai tare da faɗin.

“Mtsssyy ko ɗaya nida Aunty Lateefa ce da Ƙawarta wallahi saina buɗa musu kansu zan nuna musu ƙaryar Iskanci suke wallahi albarkacin mijinta kawai take ci amma da saina ci zarafin ta! Ina mamakin wauta da rashin tunanin wasu matan da suke ɗaukar dangin miji ba abakin komai ba”.

Cikin sanyin murya Neenah ta sauƙe ajiyar zuciya tare da faɗin.

“Ayyah Indu am rayuwar ma nawa take duk abinda mutum zaiyi ka tura masa aniyarsa ko kare baya haushi shi kaɗai duk abinda mutum zaiyi kansa yayi wa dan Allah kifita sabgar su kawai tunda kece ƙasa dasu”.

Kai Indu ta girgiza kana tace.

“Hmmm Blue eyes kenan har yanzu baki san wacece Aunty Lateefa ba lumbu-lumbu ce wutar ƙaiƙayi na tabbata duk ita take kitsa wa ƴan uwanta da ƙawayenta magana akan mu idan ba haka ba taya zasu san wani abu agame da rayuwar gidan Aurenta?”.

Ajiyar zuciya Neenah ta sauƙe tare da gyara jakar hannunta kana tace.

“Ki tuna da Hadisin dake cewa akace _Iyyakum Wazannah Fa'innah Zhanna Akhzabul Hadith”_.

Numfashi Indu ta fesar da faɗin.

“Na sani Hadisin cewa Na hore ku da yin zato domin zato mafi ƙaryan zancene”.


  Cikin lumshe idanu Neenah tace.

“Toh kada ki zargi Aunty Lateefa akan abinda baki da tabbacin ita ta aikata! taya kike tunanin mace zata fitar da sirrin Mijinta?”.

Murmushin takaici kawai Indu tayi tasan babu wanda zai fahimci wacece Aunty Lateefa har sai ya zauna da ita amma ita Neenah ya kamata tasan halayyar ta sai dai taƙi faɗa saboda wani dalili nata...


Acan Falon Lateefa kuwa cike da ɓacin rai Meenah ta kalleta yayin da take jijjiga ƙafarta tana huci tace.

“Lallai wannan yarinyar ta cika tantiriyar mara mutunci to wallahi zan saita mata hankalin ta awannan gidan duk da cewa gidan Yayanta saina tattaka ta inga Uban daya tsaya mata!”.

Murmushi kawai Lateefa tayi tare da gyara zaman ta kana ta fuskanci Meenah da kyau tace.

“Ke dai ba nace ki kwantar da hankalin kiba just Calm down kiga mai zanyi da sannu zata gane kurenta,da sannu zata san wacece ni,da sannu zata tattara inata inata ta samu tsohuwarta a inda take”.

Tsaki Meenah taja cike da takaicin abinda ta mata ta jingina bayanta da jikin Kujeran tare da cewa.

“Toh wallahi idan ba tayi wasa ba saina karairaiya ta muddin bata iye bakinta ba shegiyar yarinya mai kama da sadaka yallah mai za'a yi da dangin miji”.

Lateefa dake girgiza ƙafa tace.

“Ke dai ki kwantar da hankalin ki ba nace zan ɗau mataki ba kada fa ki manta wacece Ni tunda nace zan ɗau mataki kinsan zan ɗauka kawai ki bani lokaci! nayi alƙawari saina rabasa da duk danginsa”.


Ajiyar zuciya Meenah ta sauke tare da ɗaga hannunta biyu sama alamar jinjina kana tace.

“Alafiya dai Lateefa Virus!Alafiya dai Lateefa ƙadangaren bakin tulu akarki akar tulu abarki ki ɓata ruwan Tulu!,Da girman kujeranki Virus kinfi ƙarfin kishiya ke kaɗai ce daga ke akulle ƙofa”.

Lateefa kuwa wani Miskilin murmushi ta saki kana ta ɗaga hannunta tare da cewa.

“Ya isa haka Meenah kada kisa tsohon tsimina ya tashi,Yo Imraan da Mahaifiyarsa ma ba abakin komai suke awajena ba bare kuma wata shegiya Indu?”.

Ta fesar da numfashi mai zafi kana tace.

“Wallahi yanda kika san akan ƙaya nake haka nake zaune da wannan yarinyar ina so in mata illar da sai taji ta tsani zaman wannan gida tsana na har abada!”.

Dariya mai sauti Meenah tayi kana tace.

“Haka nake son ji Lateefa idan ba ki nunawa dangi miji ke Shegiyar kanki bace tofa baza ku zauna lafiya ba tun da nake kin taɓa ganin wata shegiyar ƙanwar miji taje min gida ta kwana? Koda yake ma bashi da dangi sai dangin dan garere”.

Kai Lateefa ta girgiza murmushi Meenah tayi tare da cewa.

“Toh Wallahi sai dai ƙannena amma bawai ƙanwar miji ba kema kuma ke kika so da har kika bari ta zauna miki agida tsawon shekaru baki ƙarawa shegiya mai ba”.

Ƙwaffa Lateefa tayi kana tace.

“Ke dai Bari akwai shirin na musamman da nake wanda Wallahi ko sunan unguwar nan Indu taji sai zuciyarta ya tsinke bare wannan gidan sai dai hange daga nesa”.

Hannu Meenah ta miƙa mata suka tafa kana suka fashe da dariya atare.

Zama Meenah ta gyara kana tace.

“Wai ya batun auren Sojanki ne kusan shekara naji maganar ya mutu”.

Wani miskilin murmushi Lateefa tayi kana tace.

“Hmmm Meenah kenan idan fitsari banza ne kaza tayi mana?”.

Dariya Meenah tayi tare da cewa.

“Ban fahimce kiba kin san ba wani Hausa nake ji sosai ba”.

Jingina da jikin kujera Lateefa tayi kana tace.

“Labarin yana da tsayi da dogon sharhi amma dai ki sani kamar ayi ruwa a ɗauke kuma shida Aure har abada”.

Tuni Meenah ta dau haske dariya tayi tare da bata hannu suka tafa.

Daga nan suka cigaba da hira da kuma tsanar dangin miji...


****

Acan ɓangaren Indu da Neenah kuwa sai misalin uku da kwata suka isa Islamiyya direct ajinsu suka wuce kana suka fara Muraja'a acikin Suratul An'am الاء نعام.

Sunyi Rubu'i biyu acikin Muraja' an ɗaya daga cikin Malaman su ya shigo. 

Sai da suka kai ƙarshen aya kana suka tsaya tare da gaishesa cike da kamala ya amsa kana yace.

“Malamin Kur'anin ku ba zai samu zuwa da wuri ba yana da uzuri dan haka zamuyi Fiƙhu kafin yazo idan kuma bai zoba sai muyi darasin mu”.

Kai suka gyaɗa ko wacce ta buɗe jaka tare da ciro littafin Fiƙhunta ahankali Neenah ta saci kallonsa cikin rashin sa'a Idanunta suka sauƙa acikin nasa.

Kallon second huɗu zuwa biyar ya mata kana ya lumshe Idanunsa kasa janye Idanunta acikin nasa tayi da ido ya mata alamar ta bashi littafinta.


Numfashi ta fesar tare da janye Idanunta daga cikin nasa kana ta miƙe ahankali ta isa gabansa tare da durƙusawa ta miƙa masa littafin karɓa yayi yana dubawa.

Anutse ta juya ta koma mazaunin ta satan kallonsa tayi taga baki ɗaya hankalinsa nakan littafin Ajiyar zuciya ta sauƙe cikin ƙasa da murya ta furta.

“Indu zan koma baya”.

Ahankali Indu dake ciro Pencil cikin jaka ta kalleta tare da faɗin.

“Baya kuma? amma meyesa?keda bakison Zaman baya?”.

Kai Neenah ta girgiza kana tace.

“Haka nan bana son gaban yau”.

Cike da Mamaki Indu ta ware ido kana tace.

“Iyeee wata sabuwa yau kuma zaman baya kike so ke dai ki faɗi gaskiya?”.

Ta ƙarashe tana murmushi

Harara Neenah ta watsa mata kana tace.

“Eh haka dai naga dama yau bana son zaman gaban”.

Bata jira cewarta ba ta miƙe da niyyar komawa baya Dai-dai lokacin Malamin Fiƙhu ya ɗago kansa daga kallon littafin.


Cikin sanyin murya mai cike da nutsuwa da kamala ya furta.

“خديجة ina zaki je?”.

Da sauri ta juya ta fuskanci Allon tare da sunkuyar da kanta ƙasa kana ta shiga wasa da zara-zaran yatsun hannunta ahankali tace.

“Zan samu wajen zama ne Ya sayyadi”.

Kai ya gyaɗa tare da kallon inda tashi su biyu ne akan bencin tsayuwar sa ya gyara tare da faɗin.

“Nan ɗin fa ko ya miki kaɗan ne?”.

Saurin girgiza masa kai tayi kana tayi rau-rau da Idanunta.

Numfashi ya fesar tare da faɗin.

“Bi ma'ana dai wajen bai miki kaɗan ba?”.

Ba tare da tace Uffan ba ta koma inda ta tashi Indu tayi murmushi aranta tace maganin ki kenan.


Anutse Malam Hisham ya kallesu kana yace.

“Adaidai ina muka tsaya acikin darasin mu na baya?”.

 Indu da sauran ɗalibai da suka tattara nutsuwarsu akan sa kana suka haɗa baki wajen cewa.

“Faslu Fii Hayd(Haila)”. Saɓanin Neenah data sunkuyar da kanta ƙasan deks.


Kai ya gyaɗa tare da faɗin.

“Na'am akwai mai tambaya?, ko kuma Ƙarin bayani akan abinda mukayi,Bi Ma'ana kafin mu wuce Darasin?”.

Duk shiru sukayi domin sun matsu awuce wajen saboda kunya,sake tambayarsu yayi babu wani mai tambaya still Kai suka gyaɗa masa alamar eh.

Kai ya Jinjina kana ya gyara tsayuwar sa tare da cewa.

“Toni ina da tambaya kuma duk wacce na tambaya bata bani amsaba ko kuma ta tsaya shirme,Bi Ma'ana zan mata hukunci dai dai da laifinta”.

Kai suka gyaɗa zuciyarsu na tsinkewa da sun sani da sunyi masa tambayar kafin ya jefo musu tambayar.


Cikin sauri suka kallesa amma banda Neenah data ƙi ɗago kanta akan deks ɗin.

Adake ya kalli Indu data tsirawa littafin ido kana yace.

“Masu Haila?,Kashi nawa suka rabu?,Bi ma'ana rabe raben Mata masu jinin haila?”.

Ɗago kai Indu tayi ba tare data yarda ta kallesa ba tace.

“Kashi Uku suka rabu Ya Sayyadi”.

Kai ya gyaɗa tare da cewa.

“Na'am yanzu idan ƙanwarki tace Aunty Hindatu masu Haila kashi nawa suka rabu haka zaki bata amsa kai tsaye,Bi Ma'ana ba tare da kin warware mata ƙullin dake ciki ba?”.

Kai ta girgiza cikin sanyin murya da kunya tace.

“A'a Ya Sayyadi zan warware mata”.

Kai ya gyaɗa tare da gyara tsayuwar sa yace.

“Na'am toh ya zaki faɗa mata?,Bi ma'ana ki warware mana yanda zamu fahimta”.


Ajiyar zuciya ta sauƙe cikin sanyi da kunya tace.

“Na farko Itace Wacce ta fara,sai kuma na biyu wacce ta Saba,sannan na ƙarshe wacce ta daina”.

Kai ya gyaɗa tare da cewa.

“Jayyeed Barakallahu Fiki”.

Kallon Abeedah dake bayan bencin su Indu yayi kana yace.

“Kinji bayanin da Malamar nan tayi shin Wacce ta fara kwanaki nawa take yi ko kuma kwanakinta dai dai ne da wacce ta saba?Bi ma'ana menene banbancin su?”.


Anutse Abeeda ta kallesa tare da cewa.

“Wacce ta fara daga ranan da jini ya fara zuwan mata zata fara irga adadin kwanakin ta har zuwa ranan da zai tsaya sun zama kwanakin ta, wacce ta saba kuma Already tasan adadin kwanakin ta wasu daga ciki kuma har sukan san ranan da zai zo sannan ya ɗauke”.

Ta sauƙe ajiyar zuciya kana ta cigaba da faɗin.

“Sai kuma wacce ta daina ma'ana wacce shekarunta sun zarce yin Al'ada kamar misalin wacce takai Shekara Hamsin da biyar zuwa sama”.


Jinjina kai yayi tare da shafa sajensa kana ya furta.

”Barakallahu fiki”.

Kallonsa ya mayar kan Wacce ke gefen daman Abeedah kana yace.

“Misali idan duk wata jini yana zuwa miki kwana uku idan wani wata yazo ya ƙaru ya zakiyi?,Bi ma'ana idan ya wuce kwana ki Ukun da kika saba?”.

Cikin sauri Neenah ta runtse Idanunta kana ta damƙe hijabinta da ƙarfi tare da cije lips ɗinta Cike da kunya baki ɗaya ilahirin jikinta rawa yake ta lura sam baya jin kunya duk abinda yazo bakinsa kawai yake faɗa🤔.


Batare da shakka ko tsoro ba Sadiya ta gyara zamanta kana tace.

“Malam Idan misali jini yana zuwa min kwana Uku sai wannan watan yazo ya ƙaru to zan ƙara kwanaki Uku aciki sauran kwana kin kuma zan cigaba da sallah”.


Jinjina kai yayi kana ya kalli sauran ɗaliban tare da cewa.

“Kun fahimta?”.

Alokaci ɗaya suka gyaɗa masa kai alamar eh.

Kai ya girgiza tare da kallon Sadiya still fuskarsa adake yace.

“Ni ban fahimta ba kenan aduk lokacin da yazo zaki cigaba da ƙara kwanaki uku ne har sai sanda ya daina zuwa ko kuma yaza kiyi?”.


Zama Sadiya ta gyara tare da fuskantar Allo da kyau kana tace.

“A'a Malam yanzu misali Idan jini yana zuwa yayi maka kwana uku awata”.

Cikin sauri ya katseta da cewa.

“Idan yazo miki dai ni kuma mai zesa jini yazo min?”🙈.

Kai ta gyaɗa tare da sunkuyar da kanta cike da kunya sai kuma ta dake tace.

“Misali idan na saba ko wani wata Ina yin kwana Uku sai Watan gaba kuma yazo ya ƙaru akan kwana uku to zan ƙara kwanaki Uku akan ukun da nakeyi sai ya zama kwanaki shida daga nan sai nayi wanka nayi Sallah har zuwa lokacin da zai ɗauke”.

Wani irin kunya ne ya lulluɓe Neenah har zufa take haɗawa duk da kuwa Iskar dake kaɗawa da kuma fanka dake aiki acikin ajin..

Anutse Sadiya ta cigaba da cewa.

“Sannan idan wani wata yazo kwanakin suka ƙaru akan shidan shima zan ƙara kwana uku ya zama tara har zuwa lokacin da zai cika kwana 15 domin kwanakin mai Haila basa wuce shabiyar,Idan kuma har sun wuce daga nan sai mutum yanemi magani domin ya zama jinin Istihada wato na cuta”.

Jinjina kai yayi tare da cewa.

“Masha Allah Barakallahu fiki amma da jinin za tayi sallah ko yaya?Bi ma'ana ban fahimceki ba”.

Ɗan murmushi tayi mai cike da kunya tace.

Eh Malam idan har jinin bai tsaya ba zata yi wanka tayi sallah da jinin daga nan sai ta nemi magani domin ya zama jinin Istihada ma'ana jinin cuta kamar yanda na faɗa”.

Cike da gamsuwa ya furta.

“Jayyed!Jayyed!!”.

Anutse ya maida kallonsa kan Neenah da har zuwa lokacin kanta ke durƙushe aƙasa gyara tsayuwar sa yayi tare da harɗe hannunsa aƙirji kana yace.

“خدىجة”.

Cikin sauri Neenah ta ɗago kanta kana cikin sanyin murya da kunya tace.

“Na'am Ya Sayyadi”.

Fuska ya ɗaure kana ya tsira mata Idanu tare da cewa.

“Rabe-Raben wanka kashi nawa ne?”.

(🤣🙆🏻‍♀️ Daughter Amna el Yaƙub dake tsaye gefen window saura kaɗan wayarta ya zame jin tambayar ya Sayyadi tayi gaggawan tarewa).

Atsorace Neenah ta kallesa tare da Ware manyan Idanunta tana jujjuya ƙwayar acikin nasa cike da tsoron tambayarsa.

Duk yanda Indu taso ɓoye dariyar ta kasawa tayi jin tambayar da ya jefowa Neenah da kuma yanda ta zare Idanunta toshe bakinta tayi amma duk da haka sai da sautin ya fito.

 

Kallonta Malam Hisham yayi tare da galla mata Harara cikin sauri tayi ƙasa da kanta tana ƙunshe dariyar ta duk da cewa tana hana kanta amma ta gagara.

Anutse Malam Hisham ya gyara tsayuwar sa tare da kallon Neenah da har zuwa lokacin Idanunta na kansa kana jikinta na ɓari.

Cikin rashin walwala yace.

“جديخة ke muke sauraro”.

Da sauri Neenah tayi ƙasa da kanta kana ta lumshe Idanunta cikin rawan murya ta damƙe hijabinta da ƙarfi kana tace.

“Ya Sayyadi am-an-ce wan..kaaa..ku..kama dama kamar bakwai”.

 Ya fuskanceta da kyau cikin tsira mata Idanu yace.

“Ki zauna me kyau ki fuskanci Allo sannan ki faɗa min Wanne da wanne bawai ki barsu adunƙule ba Bi ma'ana ya akayi suka zama bakwai?”.

Da ƙyar ta iya ɗago Idanunta jin yanda yayi magana kana cikin tura baki tace.

_“1-Guslul Janabati 2-Guslul Hayd 3-Guslul Nifasi 4-Guslul Lidahalul Makkati 5-Guslul Istintanatu 6-Guslul Salatul Idaini, 7- Guslul Istihada”_

Jinjina kai yayi kana ya tsirawa littafin dake hannunsa ido yace.

“Masha Allah mennene banbanci tsakanin wankan Haila da wankan Janaba!?”.

Cikin sanyin Murya da kunya tace.

“Niyyah”.

Kai ya gyaɗa kana yace.

“Jayyid da wani alama ne mace ke gane ɗaukewar jini”.

Cikin sauri Neenah ta ɗago kanta akuma dai-dai lokacin shima ya ɗago kansa atake idanunsu suka sarƙafe cikin sauri ta janye Idanunta tare da yin ƙasa da kanta muryan ta na rawa tace.

“Ta hanyar bushewar gaba ko kuma ganin farin ruwa”.

Kai ya gyaɗa tare da cewa.

“Jayyid,ki gwada mana yanda ake wankan mugani”.

A wannan karon hannunta ta dafe aƙirji tare da zaro idanunta waje.

Dariya ce taso kamashi ganin yanda tayi amma sai ya kuma ɗaure fuskarsa yace.

“Muna sauraronki”.

Ruwan hawayen daya cika ƙwayar idanunta har ya gangaro kuncinta ta goge kana tace.

“Da farko mutum mai najasa zai samu tsarkaken ruwa a buta kamar yanda a al'adan Hausa Fulani suke yi da buta amma basai lallai da buta ba idan mutum ya samu tsarkakekkene mazubi sai ya zuba ruwansa”.

Ta kuma lumshe idanunta tare da cewa.

“Da farko zaka fara tsarkake inda yake da najasar kafin sai ka ɗaura alwala amma bazaka wanke daga idon sau zuwa faratun kaba,Daga nan saika wanke daga cibiyar ka zuwa ƙasa sai kuma ka sake wanke gefen dama kafin na hagu”.

Indu kam murmushi kawai take yau kam Malam Hisham yayi maganin Neenah.


Neenah kuwa cikin sanyi da tarin kunya ta cigaba da faɗin.

“Irin wannan wankan mutum zai iya yin Sallah dashi batare daya sake wani alwalan ba,Sannan kuma akwai wanda mutum zai iya yi ko acikin swimming pool, rafi,ko kuma kogi da niyyar aransa.


Lumshe idanunsa yayi tare da buɗe akanta kana yace.

“Barakallahu fiki,Shin akwai wani mai tambaya,Bi ma'ana kun gane ko kuma mu wuce darasin?”.

Kai Sadiya ta gyaɗa cike da kunya ta sunkuyar da kanta kana tace.

“Ya Sayyadi Ina da tambaya”.

Hankalinsa na kan littafin da yake buɗewa yace.

“Na'am muna sauraronki”.


Zamanta ya gyara kana tace.

“Misali idan jini ya zo min bayan ya gama kwanakin sa ya ɗauke nayi wanka nayi Sallah sai kuma kamar da yamma ko washe gari na sake ganin digon jini ya zanyi!?”.

Ahankali yake jinjina kansa har ta gama Kafin yace.

“Idan Misali jini ne kamar yanda kika faɗa kuma yana zuba to babu shakka zaki sake wanka kafin kiyi sallah idan kuma fatsi-fatsi ne kamar ruwan goro zaki wanke sai ki cigaba da Sallah Bi ma'ana ba sai kinyi wanka ba kin fahimta”.

Kai ta gyaɗa masa tare da cewa.

“Eh”.

Ahankali ya ɗaura musu darasi suka cigaba da karatu bayan ya gama ya miƙawa Neenah littafin karɓa tayi cikin sassauta murya yace.

“Ki duba ciki akwai saƙo”.

Kai ta gyaɗa masa batare da tace Uffan ba bayan fitarsa Malamin Tauheed ya shiga ya ƙara musu.


ƙarfe Biyar dai-dai akatashi Atare Neenah da Indu suka fita kallon Neenah da duk tayi zuru-zuru Indu tayi tare da fashewa da matsanancin dariya hadda riƙe ciki.

Fuska Neenah ta ɓata Muryanta na rawa tace.

“Kinga bana son wulaƙanci ya Zaki sani gaba kina Min dariya dan Allah ki bani Mi'atu Hadith ɗina in tafi banason wulaƙanci”.

Da ƙyar Indu ta tsaida dariyar ta ganin yanda tayi kicin-kicin da fuska still da murmushi afuskarta tace.

“Kece Dramer ki da Ya Sayyadi baya ƙarewa wai ma Meya faɗa miki?”.

Harara Indu ta galla mata sai kuma ta taɓe baki ta miƙa mata littafin Fiqhu.

Karɓa Indu tayi ta buɗe ware ido tayi kana tace.

“Iyeee kice yau muna da babban baƙo mu shirya tarbansa”.

Wani kallo Neenah ta watsa mata still Muryanta Asanyaye tace.

“Lallai dai kam sai kije ki tarbesa amma Ni wallahi koda yazo bazai ganni ba toma da wani idon zai iya kallona bayan wannan tambayar daya gama yimin?”.

Duk yanda Indu taso ɓoye dariyar ta ka sawa tayi saida tayi mai isarta kana tace.

“Wallahi Blue eyes akwai ki da abin dariya dama da da wani idon yake kallonki idan yazo ke dai kishirya tarbansa?”.

Baki Neenah ta taɓe kana tace.

“Ni dai kiban littafina zanyi hadda idan na koma kuma kinga hadari ya taso”.

Murmushi Indu tayi kana tace.

“Hmm gwanda ki rage wannan kunyar taki dan Ya Sayyadi baya so ɗan love ne littafin ki kuma muje gida in dauƙa Miki na manta”.

Kai ta girgiza kana tace.

“Ki barshi kawai gobe ki fito min dashi”.

Fuska Indu ta marairaice kana tace.

“Dan Allah muje in dauƙa Miki Kinga wallahi fitsari nakeji muyi sauri”.

Shiru Neenah tayi tare da binta badan ranta yaso ba sai dan babu yanda za tayi...


***

Acan ɓangaren Sir Abdallah kuwa ayanda ya kwanta rigingine ahaka bacci ya ɗaukesa batare daya shirya ba duk da cewa bacci yake amma kallo ɗaya zaka masa kasancewar baya jin daɗin baccin ƙaran wayarsa dake gefen Pillow ne ya karaɗe dodon kunnensa ahankali yayi miƙe tare da buɗe Idanunsa kana ya shafa sajensa tare da furta.

_“Alhamdulillahil lazi ahyana bada amatana wa'ilaihin nushur Astagfirullah wa'atubu ilaik100”_.

Ahankali ya miƙe tare da shiga haɗeɗɗen toilet dake maƙale da Bedroom ɗin babban toilet ne dake ɗauke da Bathtub aciki da kuma katon madubi kana da TV plasma madaidaici aciki Komai na cikin toilet din Fari ƙal ne yana fitar da wani sihirtaccen ƙamshi mai daɗin shaƙa cike da nutsuwa ya ɗaura alwala kana ya fito sallaya ya shimfida ya tada Sallah kasancewar lokacin biyar ta gauta bayan ya idar ya gyara zamansa counter dake maƙale ayatsar sa yashiga matsawa yana hailala da tasbihi bayan ya gama yayi Azkharul Masah karfe biyar da rabi ya miƙe ya fita kai tsaye ya nufi ainihin cikin gidan fadawa sai gaishesa suke yi hannu kai wai ya ɗaga musu yayin da sanyayyar iska ke kaɗa sa yana ratsa duk wani lungu da saƙo dake jikinsa lumshe Idanunsa yayi jin yanda iskar ke kaɗawa ya tabbatar masa ya kusa bada ruwa..


Kai tsaye wani ƙayatacce Sashen ya nufa sashe ne me kyau da tsari wanda akayi masa gini irin na Sarakunan Gargajiya masu riƙe da al'ada daga jikin bangon ko wani sashe akwai zanen ƙaton Kada da akayi masa ado na ƙawa wanda ke nuni da Al'adan Masarautar ce

Bakinsa ɗauke da Sallama ya shiga tsarerren falon dake cike da jerin kayan Sarakunan Gargajiya jikin bangon dakin manne yake da abubuwan gargajiya masu tarin yawa amma duk da haka bai sa falon yayi tarkace ba kana ƙasan ɗakin wasu manyan tuntunne Pinch da fari masu masifar kyau.

Ahankali Sir Abdallah ya maida Idanunsa kan Dattijuwar Matar dake hakimce akan kushin 2sitter cikin shiga ta alfarma haɗaddiyar Less Seygreen anyi Masa ɗinkin buba yayin da bayi biyu ke durƙushe ƙasan ƙafarta suna mata Massage gabanta cike yake da kayan marmari acikin wani ɗan kwando mai ƙayatarwa kama daga Inabi, Abarba, Ayaba,Tuffa Mangoro,Forien Pia da sauransu.


Wani irin lallausan murmushi matar ta sakar mishi tare da miƙa masa hannunta.

Cike da nutsuwa da kuma ƙasaita ya nufeta tare da zama aƙasan haɗeɗɗen Capet dake shimfiɗe Atsakiyar ɗakin kana ya ɗaura kansa akan cinyarta ya lumshe Cat eyes ɗinsa yana jin wani irin sanyi da nutsuwa na ratsasa cikin sanyi murya me cike da Shagwaɓa yace.

“Ammie naaa”.

Cikin sauri bayi biyun dake zaune suka miƙe suka fita bayan sun kwashi gaisuwa awajensa.

Ammie kuwa murmushi ta sakar masa tare da sanya Lallausan tafin hannunta tashafa yalwataccen sumar kansa Irin na asalin Shuwa Arab cike da so mai tarin yawa irin na Uwa da ɗa tace.

“Autana ya akayi me kake buƙata?”.

Ashagwaɓe ya tura ƙaramin bakinsa tare da ɗago kansa ya kalleta kana yace.

“Ammie ni dai bana son wannan sunan da girmana Please ki daina faɗa min”.

Lakace masa hanci Ammie tayi tare da faɗin.

“Uhm wani girma kake dashi Autana?,Duka duka shekarun ka nawa ne?”.

Da sauri ya ware Cat eyes ɗin sa tare da cewa.

“Ammie nan da wasu kwanaki zan cika 33 years gaskiya ni ba yaro bane!?”.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da jinjina kai ta fuskancesa da kyau kana tace.

“Toh tunda kasan haka Why not ka fito da mata kayi Aure shekaru na tafiya kwanaki na ƙarewa wannan rayuwar bata da tabbas idan mutum ya samu dama yayi amfani dashi ko dai baka so inga ƴaƴan kane?”.

Cikin sauri ya kalleta jin abinda tace kai ya Girgiza kana yace.

“Ina so mana Ammie har yanzu dai ban samu matar aure bace amma ki cigaba da tayani da addu'a?”.

Cikin sauri ta kallesa tare da cewa.

“Autah me kace?Baka samu matar Aure bafa naji kamar Kace ita kuma Meerah fa da tarin ƴan matan da ake kawo maka?da kuma wanda suke bibiyar ka”.

 Atake yaji zuciyarsa ya buga da ƙarfi ganin yanda ta tsaresa da ido yasa ya motsa laɓaɓansa da niyyar magana akuma dai-dai lokacin wayarsa ya karaɗe wajen da ruri kallon Ammie data tsaresa da ido yayi kana yace.

“Ammie bari nayi picking call Ina zuwa”.

Daga haka ya miƙe ya fita tare da sauƙe ɓoyeyyar ajiyar zuciya.

Kallon miss call ɗin Sir Auwal yayi wanda ya katse.

Da kallo Ammie ta bisa sai kuma ta girgiza kai kana ta ɗauki Inabi ta kai bakinta tana burin taga tilon ɗan nata ya samu matar Abokiyar rayuwa domin ya samu nutsuwa amma ta lura sam hankalin sa baya kan Aure.


****

Atare Neenah da Indu sukayi sallama tare da shiga falon kallo ɗaya Indu ta yiwa Lateefa da Meenah da har zuwa lokacin suke zaune ta ɗauke kanta wani Miskilin murmushi Lateefa ta saki tare da kallon Indu data kusa shiga Bedroom tace.

“A'a Ƴan mata na an dawo ne da alama dai yunwa kike ji naga duk kinyi zuru-zuru dake!?”.

Kallon mamaki Indu tayi mata kana ataƙaice tace.

“Uhm”.

 Tare da shigewa Bedroom saboda fitsarin daya matseta.

Neenah kuwa durƙusawa tayi cikin sanyin murya da ladabi tace.

“Aunty Lateefa ina yinin ku ya gida ya yara?”.

Wani shegen kallo Lateefa ta watsa mata kana tace.

“Auzubillahi Minal Shayɗanirrajim ya Allah karabamu da masifa da Annoba wai ke dan Allah Fatiha wace irin jarababbiya ce acikin jarababbu?,meyesa baki da zuciya ne ke baki da aiki sai bin ƴaƴan masu hannu da shuni?”.


Cikin sauri Neenah ta runtse Idanunta tare da cije Lips ɗinta na ƙasa zuciyarta na bugawa.

Meenah kuwa ya mutse fuska tayi tare da watsa mata kallon banza kana tace.

“Lateefa wai meyesa kike barin irin wa'annan mabaratan na shiga miki falo idan ma wani kyautar zaki bata sai ki bari ta jiraki afalon farko”.


Ta ƙarashe cike da Isgilanci tana yamutse fuska.

Siririn tsaki Lateefa taja tare da watsawa Neenah kallon tsana kana tace.

“Waya faɗa miki Mabaraciya ce?,Ina wannan Gafalalliyar yarin da nake baki labari wacce Sojana ke ɗawainiya da ita”.

Cikin sauri da matsanancin mamaki Meenah ta gyaɗa kai.

Lateefa ta gyara zamanta tare da cewa.

“Toh wannan itace tunda Indu ta jajuɓo mana ita shikenan ta zeme mana alaƙaƙai acikin rayuwarmu komai na Rayuwa Sojana ke yimata hatta makaranta ma iri ɗaya sukeyi”.

Zare ido Meenah tayi tace.

“Lallai inda ranka kasha kallo to waima ke Lateefa me kika tsaya kallo da har kika bari irin wannan abin na faruwa ko dai ƴar uwar suce?”.


Ya mutse fuska Lateefa tayi tare da kallon Neenah dake durƙushe hawaye na kwaranya daga idanunta tace.

“Ina fa ƴar Uwarsu!,Meye gamin Kashi da fura banda ƙazamin damu ai duk dangin su Sojana babu matsiyata irin wannan duk da dai suma ba wani arziƙi bane dasu,Amma nafi tunanin asiri ta masa wai fa cewa yake hakkin maƙoftaka tun tana ƙarama yake ɗawainiya da ita”.


Cikin sauri Neenah ta ɗago kanta cikin muryan kuka tace.

“Wallahi Ni ba asiri na masa na ban taɓa aikata shirka ba”.

Atsawace Lateefa tace.

“Rufe min baki baƙar munafuka algunguma wannan karatun da kike taƙama dashi ana biya miki saina salwantar sannan inɓatar dake adoron duniya baki san waye Ubana ba!?.

Toh shine na hannun daman Gwamna”.

Kai Meenah ta girgiza tare da kallon Lateefa tace.

“Dan Allah ki rabu da wannan gaular yarinya domin magana da ita ma bashi da wani amfani banda zubar da Value”.

Kallon Meenah Lateefa tayi cike da takaici tace.

“Ba abinda yake ɓata min rai Meenah kamar duk wani ɗawainiyar karatun ta na boko da Islamiyya Sojana ke ɗauka bayan ya maida ƙanwarsa Tamkar kishiyata bai ishesa ba sai daya gayyato min wata Gaula cikin rayuwarmu”.

Tafe hannu Meenah tayi Idanunta akan Neenah tace.

“Kar ki faɗa min Lateefa kina nufin wannan islamiyya da boko me tsadan Conoral Imraan ke biya mata to adalilin me ke kuma me kika tsaya kallo ba kici kutumar Ubanta kin cire mata ƙafar baya ba”.

Cikin sauri Neenah ta kalleta hawaye masu masifar zafi suka zubo akuncinta cikin rauni ta riƙa Kallonsu tana motsa laɓɓanta amma ta gaza furta komai.


Harara Lateefa ta zabga mata kana tace.

“Ƴar matsiyata anci na yau ana tunanin na gobe amma kinbi kin liƙewa ƴar masu shi yo inbada naci irin na ɗan talaka ina ke ina ƙawance da Indu ai ruwa ba sa'an kwando bane”.

Kallon Lateefa Meenah tayi cikin sigar Isgilanci tace.

“Aini nama rasa abin cewa amma duk ba wannan ba naji kince Fatiha ko kuwa duk ɗimuwar talauci ne yasa iyayen ta zaɓa mata wannan suna dan na lura talauci na ɗawai niya dasu?”.

Dariya Lateefa ta fashe dashi duk da kuwa yanda take cike da takaici amma tambayar Meenah ya bata dariya kai ta girgiza kana tace.

“Yo ai gwanda ma wasu talakawan da wa'annan dan su dai faƙiraine idan kinji ance talaka tofa da mutinci Fatiha kuwa shine sunan daya dace da ita”.

Gyara zama Meenah tayi tare da cewa.

“Ban fahimceki ba kamar ya shi ya dace da ita ko dai tana da wani ɓoyeyyen sirrine?”.

Dariya Lateefa tayi cikin ya mutse fuska tace.

“Yo ai dole kiji na ƙirata da Fatiha tun da bata da asali akwaroro fa aka tsintota Atsakiyar dare acikin wani Jememmen tsumma da alama abin kunya Uwarta ta aikata shiyasa tabi dare ta Jefar da ita agefen Juji shine Wannan fakirin ya mata gata”.

Zare ido Meenah tayi tare da fashewa da dariya sai kuma ta zabga salati tace.

“Ikon Allah yau naga abinda ya ishe ni Meenah ashe dai Gantalalliya ce haba wannan naci da maita ba abanza ba to dai Allah ya gyara ba mamaki tana da alaƙa da aljanu duba da wannan idanunta Ni wallahi tsoro ma take bani”.

Neenah kuwa cikin sauri ta dafe ƙahon zuciyarta dake wani irin bugawa da Masifaffen ƙarfi kana ta ɗago Idanunta da suka sauya launi lokaci ɗaya ta kallesu cikin wani irin yanayi na tsananin tashin hankali da ruɗu take kallon Lateefa yayin da numfashinta ke fusga Idanunta na juyewa kalmar Lateefa na ƙarshe nayi mata yawo acikin dodon kunne wani irin juyewa idanunta sukayi...


_@Follow me on Arewabooks realeshaa_


_@Follow me on Wattpad Realeshaa_


_Ya Allah Ubangijin kajiƙan mahaifina ya Allah kagafarta masa zunubansu ya Allah ka kai haske kabarinsa ya Allah kajiƙan duk kan musulman da suka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mu cika da imani._



_Ayi shearing saboda Allah Ƴan Uwa masoya da abokan arziki_



   *ESHAA CE*🤙🏻

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.