Free chapter · Read without an account
23
*MUTUM.....Mugu ne*
23
..... KADUNA....
Sai da suka fita daga haraban gidansu sannan ta gaishe shi cike da farin ciki. Hanyar Kano suka kama suna tafiya suna tad'i, har suka isa, gidan Malam Musa suka je Kawun Mom kenan. Dattijo mai karamci tarba mai kyau AY ya samu a wajenshi bayan an kawo masa abinci ya ci sannan suka samu daman magana.
Malam Musa yace " Layla ta gaya min kunason yin aure ba tareda sanin iyayenta ba saboda mahaifinta ba zai amince da kai ba, sai dai ina son jin dalilinka na auren Layla dan zuciyana na bani cewa akwai babban dalili"
Layla ta riga ta sanar da AY cewa Malam Musa babban malami ne kuma shi ya taimaka mata da addu'o'i lokacin da take jinya.
AY ya nisa ya bashi labarinsa a tak'aice sannan ya gaya masa babban dalilin da yasa yake son auren Layla.
Malam Musa dattijon arzik'i, a k'alla yayi 80 years. yai shiru yana nazari kafin daga bisani ya fara masa bayani kamar haka
" tabbas ina da kokwanto akan dukiyar Alhaji Kadi tun da dad'ewa sai dai ban ta'ba kawowa abin nashi har da tsafi ba. Ni dai kamar yadda Layla ta gaya maka ni Kawun mamanta ne, Ina matsayin k'anin kakar Layla ta wajen uwa, asalinmu 'yan k'aramar hukumar Had'eja ne a jigawa, Fatima mahaifiyar Layla 'yar dangi ce ciki da waje sai dai Alhaji Kadi da kake gani bamu da masaniyar asalinsu, sai dai kasan da yake abinda Allah ya riga ya had'a babu yadda aka iya.
Mahaifin Kadi, Abubakar cirani ya zo tun daga ƙasar Niger yayi yawo sosai anan k'asar kafin Allah yasa ya zauna a Had'eja. Tareda matarsa ya iso Had'eja, shekararsu d'aya da zuwa ta haifi Ishaq suna ce masa Kadi a haka suna Ishaq ya 'bace sai Kadi d'in, sai dai Kadi bai shekara uku ba mahaifiyarsa ta rasu. Nan Abubakar ya auri wata bazawara Saude 'yar asalin cikin Had'eja, Kadi ya taso a cikin walak'anci domin Saude irin mugayen matan nan ne da basu da tausayi. Yana shekara bakwai aka turashi almajiranci chan wajajen Zamfara, sai da yayi shekara shida Bai zo gida ba, da yazo ma ba abinda ya chanja agidansu domin daga Saude sai agolan da ta zo dasu gidan suke sha'aninsu. Kadi ya koma makarantarsu cike da fushin mahaifinsa, saboda yana gani Saude take muzguna masa amma baya iya cewa komai.
Kadi na shekara goma sha shida Abubakar ya rasu. Lokacin da yazo gida Saude da yaranta sun riga sun wawure dukiyar da mahaifinsa ya tara. Sai ya k'i komawa makaranta ya fara 'yan buge-buge a cikin Hadeja, daga baya ya koma yana bin babban mota daga Kano zuwa Lagos a haka soyayya ta shiga tsakaninsa da Fatima, Ina d'aya daga cikin wanɗanda suka nuna k'in amincewa da auren amma ba yadda na iya tunda mahaifanta sun amince. A haka suka yi aure da dad'i ba dad'i suna zaune, shekararsu biyar da aure kwatsam Kadi ya samu kud'i daga sama, ya bud'e shaguna a Kano yana kasuwanci, kafin shekara ta zago ya koma Kaduna nan ma ya fara harkokinsa daga nan ya bud'e kamfani acan.
A labarin da ya ke bawa mutane cewa yayi wani uban gidansa ne a Lagos ya bashi jari shine Allah ya sa masa albarka. Har yau Kadi bai san inda 'yan uwan mahaifinshi dana mahaifiyarsa suke ba, bana tunaninma ya damu da ya sansu. Kaji labarin mahaifin Layla.
Kuma tabbas maganarka zai iya zama gaskiya domin na jima ina zargin arzik'in Kadi"
AY yai ajiyar zuciya sannan yace "nagode Malam, Insha Allah zan kula da amanar Layla"
Daf da Azahar wakilan AY suka iso daga Zaria, k'anin Babansa ne sai cousin d'inshi da Kawunshi mahaifin Aisha matarsa ta farko.
Bayan anyi sallah aka gabatar da juna, suka nemi auren Layla Malam Musa ya basu. Bayan sallar la'asar za'a d'aura aure kafin nan suna sa ran k'arasowar Shabbir da ya ke hanya.
Cikin gida kuma, Mama uwargidar Malam Musa ta tasa Layla a gaba tana shiryata duk da babu lokaci, k'ananun kitso wata 'yar mak'ociyar su take mata, sannan Harira d'aya daga cikin yaran Malam d'in ta mata jan lalle. Sai da aka gama mata tayi sallah taci abinci sannan Mama ta had'a mata ruwan wanka. Layla ta kalla ruwan ta ga ya wani yi brown ne ko jaa nema ta rasa ganewa,
"yar tsohuwa mi kuma kika jik'amin a ruwa?"
"Yalle ta shaka da washu gari a ciki" wata k'aramar yarinya jikar Mama dake wajen ta fad'a
"Lalle Kuma?"
Mama tace "maza ki je kiyi wanka kafin ruwan ya huce, ki tabbatar kin cud'a jikinki sosai, idan ba haka ba zan shigo na miki da kaina"
Layla ta ta'be baki tace " yau na ji tsohuwar nan wai ki shigo ki min wanka, o'o"
Ta ji dad'in ruwan wankan dan k'anshi ruwan ke yi sosai. Tana wanka zuciyarta na tunani, daga yau fa zata zama mallakin AY, sai yadda yayi da ita. Mamakin yadda aka yi ta kamu da son AY take yi. Tabbas soyayyarshi ya mata kamu mai k'arfi.
Suna alwalar Sallar la'asar SY ya iso kano, bai gane kwatancen gidan bama sai da AY ya je ya taho da shi.
Bayan an idar da sallah aka d'aura auren *Alyasa'a Ahmad* da amaryarsa *Layla Kadi Maikud'i* bisa sadaki dubu ishirin.
Mutanen Zaria suka wuce abinsu dan dama ba kwana zasu yi ba ya rage saura SY.
Shabbir yana zaune gefen AY ya bashi labarin gamo da yayi ranar da zai je Minna.
"Oga, Allah ina ji ajikina akwai wani abu dake jirana a Kaduna like something super natural, kasan saboda ina son zuwa Kaduna yasa nake ta speeding investigation da nake yi a Minna yanzu haka zan bada report next week, I just hope this time a bani case d'in sirikinka" ya k'arasa maganar yana dariya.
AY ya dundi bayanshi shima yai dariyan.
"Just be careful Shabbir, kasan kai kad'ai ne namiji a gidanku, gashi ka k'i aure balle ka ajiye iri"
SY yai dariya yace "karka damu tunda kaima kayi aure nima zan k'ok'arta na yi"
Malam Musa ya shigo bayan an d'aura aure ya bawa Layla sadakinta a hannu, nasiha ya mata sosai sannan yace mata kamar yadda ta buk'aci kada ya sanarwa Mom d'inta gameda auren, ba zai gaya mata ba saidai, da zaran wa'adin da Alhaji Kadi ya bata ya cika zata sanar dasu cewa ta riga ta yi aure.
"Ba kya tunanin idan Alhaji Kadi ya ji zancen auren nan, ba zai tirsasa Alyasa'a ya sakeki ba?"
Layla cikin zuciyarta tace "kafin nan ma ai na samu ciki in Allah ya yarda ba halin rabani da AY"
A fili Kuma tace "Malam Insha Allah Daddy zai hak'ura ya bar mu, musamman tunda kai ka d'aura mana auren kasan duk cikin familyn Mom kai kad'ai yake shakka"
"Allah ya baku zaman lafiya" ta amsa da Amin.
D'akin Mama ta kwana, bayan ta gama d'irka mata abubuwa tasha. Text d'in AY ya shigo mata yana mata sai da safe a k'arshe har da rubuta amaryata. Ta yi fari da idonta cikin zuciyarta tana jin dad'i, finally AY ya zama nata. A haka tayi bacci zuciyarta fes.
Washe gari da sassafe Shabbir zai wuce Minna. Malam ne ya lek'o yace ta je zaure su gaisa da Shabbir dan yana d'aya daga cikin wakilan Alyasa'a.
Dogon hijab d'in Mama ta saka wanda har k'asa ya kai mata sannan ta fito. d'akin dake zauren ta nufa inda nan AY da Sy suka kwana.
Sallama tayi a hankali ta tsaya bakin k'ofa.
"Wa'alaikissalam Amarya, Bismillah ki shigo"
Kanta k'asa ta shigo d'akin d'an gefe guda ta samu ta zauna ta d'an d'aga ido ta kalli SY ta gaidashi sai alokacin ta lura AY kwance yake kan katifa da alama ma bacci yake yi.
"Amarya Layla barka da zuwa"
Murmushi ta yi, sannan ya cigaba " ga Aminina nan, Yayana kuma Oga na Dan Allah a rik'e mana shi amana, Kuma sai kin yi hak'uri da shi sosai dan Oga na akwai zafin rai, lokacin da muke aiki tare naji jiki a hannunsa"
Dariya ne ya k'wace mata musamman data tuna farkon had'uwarta da AY, shima Shabbir d'in ya d'an dara kad'an.
ya mik'a mata wata leda yace " ayi mana hak'uri bikin naku ne yazo bazata" ta amsa ledar ta masa godiya.
Ya d'au jakarsa ya rataya yace "Oga ni zan wuce" sai alokacin AY ya bud'e ido ashe dama ba bacci yake ba kallon inda Layla ke zaune yayi itama d'in shi take kallo suna had'a ido ya harareta tayi saurin sunkuyar da kai.
Ya tashi ya raka Shabbir wajen motarsa.
Kasa tashi tayi dan batasan ma'anar hararan da AY ya mata ba, dole ta jira ya dawo ta tambayeshi.
Minti biyar da fitarsa ya shigo d'akin, "Ina kwana Yaya AY" tace dashi
Maimakon ya amsa mata sai ya fara fad'a " wannan wani irin shirme ne da safiyar Allah kinzo kina yiwa mutane dariya, miye abin dariya acikin maganar da Shabbir yayi yanzu, inba shirme irin naki ba"
Lallai namiji daga d'aura aure jiya har ya fara kishi irin haka.
Ta tashi daga inda take zaune ta zo ta zauna gefenshi ta kwantar da kanta a k'irjinsa tana d'an shafa shi a hankali tace "Ango na san nayi laifi amma kayi min hak'uri"
Yadda take shafa masa kirjinsa yasa shi had'iye maganar da ya keson yi.
Ta sake narke muryarta tace "Dear ka tashi lafiya?"
Juyo da ita yayi yasa hannunsa yana shafa fiskarta before she knew it ya had'e bakinsu.
K'ok'arin cire hijabin jikinta yake yi tayi saurin rik'eshi "dear ban fa yi wanka ba..."
"And so" yace mata yana d'aga mata gira
"Allah Mama tace na dawo da wuri"
Ya mata peck a goshi yace "shikenan 'yar Mama zan biki bashi"
........ Bayan tayi wanka ta shirya cikin wata lace jaa mai flowers bak'i d'inkin riga da zani, Kunu da k'osai aka kawo mata, ta sha kunu kawai dan ba wai ta damu da cin k'osai bane sai ta fi shekara bata ci ba.
Mama ta sata gaba ta mata nasiha mai ratsa jiki game da zamantakewar aure da hak'k'ok'in miji akan matarsa. Sosai jikin Layla yai sanyi dan sai ta ga ashe dai a duhu take bata san minene aure ba sai yanzu.
K'arfe goma AY ya shigo suka yi sallama da iyalen Malam Musa, shi ya fara fita ya je ya jirata cikin mota, kusan minti sha biyar ta 'bata kafin ta fito. Harira tana rik'e da ita dan ta rufe fiskarta da gyalen da ta yafa irin dai yadda amare suke yi d'in nan. Wasu jikokin gidan maza da mata sunata ihu"ga Amarya, ga Amarya"
AY ya fitar da sababbin kud'i 'yan d'ari biyu na dubu biyar ya mik'awa wani babba a cikinsu yace su je su raba, suka kwasa a guje sai cikin gida suna ihu.
Maimakon Zaria da zasu wuce gidansu AY sai taga sun nufi wani Hotel. Ta d'an janye gyalenta ta kalleshi tace "Dear ba Zaria zamu je ba?"
"Ban ce miki ba"
Ta d'an langwa'be kai " amma fa yadda muka tsara daga Kano sai Zaria"
Yai murmushi yace "kwantar da hankalinki amaryata har yanzu ma daga Kano sai Zaria d'in ne"
A hotel d'in ya parker suka fito hannunsu rik'e da juna ita dai tasan take takensa yanzu baza a wanye lafiya ba. Suna zuwa ya k'ar'ba key da alama ya riga ya booking d'akin tun tuni.
D'aki ne da aka k'ayata shi kamar na masu honeymoon, an decorating ɗinsa da flowers da candles.
"Wow! dak'in yayi kyau, amma dear why all this trouble bayan ba anan zamu kwana ba"
Kallonta yayi yace "bani minti biyar ina zuwa"
Ta zauna gefen gadon tana wasa da roses d'in dake kan gadon. Kiran Daddy ya shigo wayarta, ta d'auka tana tunanin mi zai ce.
Fad'a ya mata ta tafi Hadeja ba tare da saninsa ba, ya k'ara da cewa " idan ma kina tunanin zuwanki Hadeja shi zai sa na fasa abinda nayi niyya to kisa a ranki once lokacin dana d'ibar miki ya cika aure ba fashi ko kink'i ko kin so" da haka ya kashe wayar.
Duniyar tunani ta fad'a ' Anya idan gaskiya ta fito Daddy ba zai yi k'ok'arin cutar da AY ba' ta girgiza kai 'No Daddy will never do that'
Bata ma san har AY ya shigo ba, sai da taji yasa hannu ya tallafota jikinsa.
"Tunanin mi kike yi?" Yana magana yana shinshina jikinta.
"Ina tsoron Daddy, Dear baza mu bari sai na samu ciki ba kafin mu gaya musu gaskiya"
'yar k'aramar dariya yayi sannan yace "talking of ciki, Bari mu fara k'ok'ari tun yanzu"
Tayi saurin zaro ido "ni fa ba yanzu nake nufi ba sai mun je Zaria"
"Ni kuma nace yanzu"
Tayi saurin jan jikinta tace " ai da dare akeyi ba da safe ba"
"Wa ya gaya miki?"
" Ba ana cewa first night ba"
"We'll change the rules then, namu zai zama first morning kenan"
Tayi saurin tashi daga kan gadon dan taga k'ok'arin rungumeta yake yi. "Allah dear ba yanzu ba"
Ganin zata masa gardama yace "ok shiga bathroom ki yi alwala mu yi addu'ar samun zaman lafiya ko"
Ta amsa da toh
Ta cire gyalenta ta ajiye kan gado sannan ta wuce band'akin, tana tafiya yabi bayanta da kallo yanajin wani matsananciyar sha'awar ta. Shekara biyar kenan rabonshi da mace, gashi yau Allah ya sake mallaka mishi wata halaliyarsa. A da gani yake shi da aure kuma har abada, amma yanzu ya k'aryata ik'irarinsa.
Bayan ta fito shima ya shiga yai tasa alwalar, kafin ya fito ta bud'e akwatinta daya shigo dashi d'azun ta fito musu da sallaya.
Sallah raka'a biyu ya jasu bayan sun idar yayi musu addu'ar samun zaman lafiya da zuri'a dayyaba.
Tana ninke sallayar ya rungumeta ta baya yana kissing wuyanta. " Dear Allah ba ayi da safe fah" tace mishi
Warware zaninta ya farayi yana cewa "a wani hadisin aka ce haka?"
Kafin tayi wani magana ya fara kissing d'in ta, sabon karatun da yake bata ita ma ta fara amsawa.........
Ta d'an d'ani pleasure+pain, saboda AY ba k'aramin jijjigata yai ba, sha'awarsa ta shekaru yau ya sauke akanta, da farko ma bai d'auka budurwa bace kasancewar tayi zaman k'asar waje gashi yadda yasanta da rawar kai, amma sai ya jita zan zan, hakan ya k'ara masa k'aunarta.
Shi ya taimaka mata ta yi wanka bayan ta gasa jikinta. Haka suka wuni ranar yana lalla'bata yana nuna mata kulawarsa . Da dare tausayinta yasa bai mata komai ba suka kwanta ta huta gajiyar safiya.
Washe gari da safe fah hak'urinsa ya gaza ya lalla'bata suka sake raya sunna.
Kwanan su uku a hotel d'in suna kwasan amarci, ana hud'u suka wuce Zaria.
Tar'ba mai kyau Layla ta samu wajen 'yan uwan AY, gidansa na chan suka sauka da shike anguwa d'aya ne da asalin family house ɗinsu.
Satinsu uku suka wuce Kaduna, makarantarsu Aaliyah suka fara zuwa, ta fi kowa murnar aurensu. Bayan sun bata tsarabarta suka wuce gidanshi na Kaduna.
Washe gari suka shirya da safe ya mayarta gida da zimmar zata rok'i Daddy ya k'ara mata lokaci.
Tana fitowa AY ya fito mata da jakarta saboda Daddy da suka gani a k'ofar gidan shi da wani.
Tare suka jera suka isa wajen, ta fad'a jikin Daddy tana cewa tayi missing d'inshi sosai, bayan ta janye jikinta ta gaishe da mutumin da suke tare da Daddy.
"AY ka shigo min da kayana" ta fad'i tana kallon yadda mutumin ke wa AY mugun kallo. shima AY d'in ya gaishesu sannan ya bi bayan Layla.
"Alhaji Kadi mi nake gani haka, waye wannan?"
Alhaji Kadi yace "Direban Layla ne kasan tayi tafiya yau ma ta dawo"
Mutumin yace "lallai kayi sake, kasan ko shi wanene kuwa?"
"Alhaji Sabo ka sanshi ne? kasan Hajiya ce da kanta ta d'aukeshi aiki"
" Wannan da kake gani tsohon d'an bincike ne, a lokacinsa yayi tashe sosai, ba aikin da aka bashi da ya gagareshi. Aikinshi na k'arshe daya jawo mutuwar iyalinsa yasa ya ajiye aiki, amma ko shakka babu zuwan Agent AY gidanka ba alkhairi bane"
Alhaji Kadi ya bushe da dariya yace "idan kuwa hakane abinda yake nema agidana ba zai ta'ba samu ba sai dai ko a lahira idan ana samun shi a can"
Alhaji Sabo yace "ka dai san yadda ka rabashi da gidanka and be very careful with him"......
Alhaji Sabo na tafiya Alhaji Kadi ya kira Jameel yace mishi ya sameshi a office akwai aikin da zai bashi.
............ LAGOS.........
"Ban gane ba, my one wai me nayi maka ne?" Ta fad'i tana kallon k'wayar idonsa da ta ke ganin tsananin 'bacin rai a tattare da shi. Girgiza kai yayi dan tsabar takaicin da ya ji.
Ya wuce cikin bathroom dan yin alwala, idan yace zai sauke fushinsa akanta ba za ta ji da dad'i ba gashi a gidan mutane suke, ba mutuncin sa bane aji yana fad'a.
Ta zauna gefen gado tana tunanin mi zaisa Sajid fushi da ita. Caraf zuciyarta ya bata dalilin.
Sajid ya fito daga bayin ya cire coat ɗinsa ya ajiye, da sauri Zaytunah tazo ta rungumeshi ta baya tana fad'in "my one nasan kishinka ne ya motsa but I swear to God ba abinda suka min, basu yi abinda kake tunani ba, ka kwantar da hankalinka you are the first and the only person"
"Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oon, Zaytunah ki barni haka hak'uri na zai iya k'arewa"
" My Sajid na rantse da Allah ba abinda suka min"
Yanzu duk tunanin Zaytunah bata iya gane girman laifin da tayi ba, ita inda take ma kallo kenan wai kishi yake yi. Lallai dole ya gyara yanayin zamansu idan suka koma Abuja.
"Zanje Sallah, idan kin ga dama ki walak'anta mutanen gidan nan za ki ga matakin da zan d'auka akanki"
"Sajid akan arnan banzan kake cewa zaka d'au mataki akaina" ta k'arasa maganar da "hmmm"
Bai kulata ba ya fita a d'akin. Mama ta masa tayin abinci yace sai ya dawo daga masallaci, yaso ganin Ziha kafin ya fita amma bata falo.
Yana shiga mota Ishola ya mik'a masa wata leda yace masa Funmilayo ce ta bashi. Da sauri ya k'ar'bi ledar. Ishola ya ci gaba da yaba halin Funmi yana cewa tanada hankali kamar tasan yunwa yake ji ta kawo masa abinci.
Yana bud'e ledar Apples guda uku ne aciki sai ayaba da goran ruwa.
Baisan sadda murmushi ya ku'buce masa ba ta riga ta san bazai tsaya cin abinci ba amma zai iya cin fruits koda a motane.
...... Zaytunah da k'yar ta iya rama sallolinta k'arshe ma a zaune ta k'arasa, ta kwanta gefen Azra sai bacci.
Azra ce ta fara tashi ta kalli Zaytunah taga bacci take yi ta fara bubbugata tana kiranta amma ina, Zaytunah ko ji batayi saboda baccin gajiya.
Ta sauka daga kan gadon tayi hanyar k'ofa tana kiran Dad d'inta.
Ta bud'e ƙofa ta fita.
Suna zaune a dining table suna cin abincin rana, suka jiyo muryanta tana kiran Dad.
Naziha tayi saurin tashi taje wajenta, zata rik'e hannunta, Azra ta matsa baya da sauri tana fad'in "who are you?"
"Azra dear, come"
Ta mak'e kafad'a tace " how do you know my name?"
Tayi murmushi tace "your Dad told me"
"Are you my dad's friend?"
Naziha tace "yes"
"Then where is my Dad?"
Kai wannan yarinya da shegen tambaya, koda shike kwanansu biyu a tsare dole ta ji tsoron baƙin fiska.
"He went to pray, he'll be back soon"
Sai alokacin ta yarda ta k'araso wajenta. Ce mata tayi za tayi fitsari, Naziha ta d'auketa tayi band'akinsu da ita, da suka fito ta kaita dining d'in ta d'aura ta cinyarta. Tuwon shinkafa aka yi da miyar egusi sai dai batasan ko Azra zata iya cin miyar ba, sai ta ɗebi stew d'in kifi ta fara bata da shi. Sosai Azra taci abincin tana ci tana musu surutu.
Da suka gama ta tattara wajen, d'akinsu suka koma ta ci gaba da bata labari wasu ta gane wasu labaran kuma idan ta fara daga nan ta had'o da wani wajen duk sai ka rasa kan labarin. Cikin k'ank'anin lokaci har sun saba.
Sajid bai dawo gidan ba sai da yayi sallar la'asar. Mama da Ronke sun tafi church, Gbenga kawai ya samu a falo yana kallo. Ya wuce guest room, bacci ya samu Zaytunah na yi bai kulata ba, bai ga Azra ba amma yasan k'ila tana tareda Ziha, ya shige band'aki yai wanka, bayan ya fito ya sanya jallabiya bak'a. Dariyan Azra ya tsinkayo a falo ba shiri ya fito da sauri. Guje guje yaga sunayi a falon abin ya sashi nishad'i, ya tsaya yana kallonsu yana murmushi.
Azra ce ta fara kallonshi ta k'araso da gudu ta rungumeshi.
Ziha tana ganinsa tayi saurin samun kujera ta zauna.
Surutu Azra ta fara mishi har da cewa Nazzy ta bani abinci mai dad'i kuma ta min wanka.
"Who's Nazzy?" ta nuna masa Naziha.
Ya k'araso shima ya zauna sai a lokacin ta mishi sannu da zuwa, ya amsa yana sauraron surutun Azra.
"My one yaushe ka dawo?" Muryan Zaytunah ya doki kunnensa
Bayason ta dizgashi a gabansu Ziha dan haka da murmushi a fiskarsa yace "ban jima da dawowa ba Zaytunah"
Zagayowa tayi ta zauna gefensa tace "My one yunwa nake ji ka mana order pizza mana"
"Jirani a d'aki ina zuwa" yace mata
Ta rik'e hannunsa "my one, muje tare"
Ba musu ya tashi suka tafi. Gbenga yace wa Ziha "Kai halin matar nan ba kyau" dan ma bai ji mi take cewa bane.
Suna shiga d'aki ya kira sunanta "Zaytunah"
Bata amsa ba sai daya kira na biyu ta amsa, yace " idan kin nitsu tsakanin yau da gobe zan barki ki kai Monday ki bi jirgi ki tafi, idan kuma shirme zaki yi gobe zansa a wuce da ke da mota"
"Wallahi ba zan je Abuja da mota ba, Lagos to Abuja a mota cha'b"
"Dare me Zaytunah, and I'll show you what I can do"
Jikinta yai sanyi jin maganarshi ta k'arshe, tasan halin kayanta ba duka ba zagi amma tasan fushinsa ba kyau.
Ta sassauta murya tace " I'm sorry my one"
"Zaytunah kin san girman laifin da kika yi kuwa?, Na baki sharad'in ban yarda ki zo Lagos ba amma kika bi ra'ayinki kika tafo and....."
Bata bari ya k'arasa maganar ba tace "but I wanted to surprise you, my love"
"Wani irin surprise d'in banza ne wannan, putting your life and my daughter's life in danger"
" I miss you Sajid, kusan sati biyu bama tare what do you expect me to do?"
"Ya Allah!" Ya fad'i tare da dafe kansa. Tabbas akwai gyara mai yawa a zamantakewarsu.
"Na dai gaya miki hukuncin da na yanke"
Fita yayi daga d'akin zuciyarsa na k'una.
"What is happening? Sajid ya fara chanja mini saboda d'an wannan abin shine ya d'au fishi haka".
Yana fitowa Naziha ta lura da yanayinsa ya chanja, sai daya zauna tace "Uncle na kawo maka abinci yanzun?"
Kai kawai ya ɗaga mata, ta tashi da sauri ta nufi kitchen ta d'auko abincin ta ajiye a dining taje ta d'au paracetamol ta ajiye.
"Uncle na gama" tace mishi.
Ya taso daga inda yake zaune yazo dining area d'in ya zauna, ta serving ɗinsa, zata tafi yace " zauna"
Gaskiya tsoron Zaytunah take ji idan ta fito ta ga ta zauna kusa da mijinta zata sha walak'anci dan ta lura Zaytunah na da tsananin kishi.
"Uncle akwai abinda zanyi a d'aki" ta bar wajen da sauri.
Bai wani ci abincin sosai ba dan baya jin dad'in jikinshi.
Kusan minti talatin aka k'wank'wasa k'ofar gidan, Gbenga yaje ya bud'e pack na pizza guda hud'u aka bashi ya k'ar'ba yai signing.
Gurin dining da Sajid ke zaune ya dafa kansa Gbenga ya kawo packs d'in ya mik'a masa. Sajid ya d'au d'aya yace sauran nasu ne.
"Azra...Azra....."
Gbenga yace suna d'aki bari ya kira masa ita.
Data fito ya mik'a mata pack d'in pizza yace ta kaiwa mommy.
Tashi yai yace wa Gbenga zai je masallaci.
Tunda ya fita sai k'arfe goma saura ya dawo, ya samu su Daddy tuni sun dawo. Bayan sun gaisa ya masa godiya akan taimako da suka mishi musamman Ziha.
Ya sanar dashi gobe zasu bar gidan.
Da mamaki Daddy ya tambayeshi ko an mishi laifi ne,
Sajid yace " No, d'awainiya da kuke yi dani yayi yawa kuma ga family na sun zo"
Daddy yace " haba sai dai ka gaji da mu amma mu da kai da iyalenka you're all welcome here"
Duk sai ya ji ba dad'i dama saboda Zaytunah yake so su koma hotel saboda ya ga take-takenta zata iya musu rashin mutunci idan baya nan.
Shima kanshi bayason barin gidan yanzu at least ya fiso idan zai bar gidan to sai ya musu abin alkhairi, amma yanzu cikin abinda ya tsara da saura tukunna.
Ya mawa Daddy godiya sannan ya shiga d'akin da aka basu.
Yana shiga ya samu Zaytunah tana waya, bai kulata ba ya shiga ya watsa ruwa, ya fito ya yi shirin bacci ya kwanta kan gado ya juya wa Zaytunah baya.
Bayan ya kwanta ma sai da tayi kusan minti biyar kafin ta kat'se kiran ta ajiye wayar ta kashe wutan d'akin.
Rungumeshi ta baya tayi tace " tun tuni naketa jiranka my one"
" Ina Azra?" Ya tambaya ba tareda ya juyo ba
"Tana wajen wancan yarinyar Mazzy ne ko Nazzy nema naji Azra ke kiranta"
"Tasha magani kafin ta kwanta?"
" Yes na bata" ta amsa
" Sai da safe"
"My one kamin massage mana, har yanzu jikina na ciwo"
Kamar da pillow take magana dan bai ko kulata ba.
Ganin ya k'i kulata ta fara k'ok'arin tak'aloshi , sai dai me tashi yayi ya d'au pillow ya shimfid'a sallaya ya kwanta.
"My one I'm sorry, ka dawo ka kwanta akan gadon"
Shareta yayi ya kwanta abinsa.
Ya jima yana tunani kafin bacci yai awun gaba dashi......