Free chapter · Read without an account

1

by Maman Nusaiba · A HAKA NAKE SON SHI

~_*A HAKA NAKE SON SHI*_~






Daga Alƙalamin


_*Sarat Alƙasum ~(Maman Nusaiba)~*_



_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_


_Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Gargadi! Ban yarda wani ko wata su juya min labarina ba ta kowacce fuska, yadda na fara lafiya Ubangiji ka ba ni ikon gamawa lafiya, Allah ya tsaftace mana Alƙalaminmu._


*بسم الله الرحمن الرحيم*


Mabuɗi *(1)*



Sassanyar iskar yammaci da ke kaɗawa haɗi da sanyin ƙasa suka haɗu suka bada wata kalar ni'imtacciyar iska mai daɗin shaƙa. Daidai kwanar wani layi cikin wata unguwa wata budurwa ce ta yanko layin a guje, gudu take irin na ceton rai tana yi tana waiwayen bayan ta har ta ƙaraso bakin titi. Waiwayawar da za ta yi ta hango wasu garadan maza uku suna nufo ta, cikin tashin hankali ta rasa inda za ta nufa kasancewar wajan shuru sai wata ƙatuwar bola dake gefen hanyar. Can gaba kaɗan da bolar wani kango ne wanda ba a ƙarasa ginin shi ba, hakan yasa ta kwasa a guje ta hanye kan bolar tana huci ji take kamar numfashi zai daina aiki, bakinta a manne yake da gam haka ma hannunta a ɗaure yake, amma a haka take ƙoƙarin tsira da rayuwarta.

Wani kalar wari da ke fitowa daga cikin bolar ne ya kawo wa hancinta ziyara, ta taka wata leda mai ɗauke da wani abu mai kama da ruwa ai kuwa ta yi baya luu ta faɗi a cikin bolar, Kafin ta yi wani yunƙuri sai ga su sun iso bakin bolar suna kallon ta, ita kuma ban da kakarin amai babu abin da take ta sallama cewa lalle fa ruwa ya ƙare wa ɗankada, tun da har suka cin mata duk gudun da ta yi ya tashi a banza sun kama ta.


"Kai Dagus maza ka saro min kanta yanzu, dan na lura yarinyar nan gudun bala'i ne da ita ta gajiyar da mu sosai. Dan haka yanzu mu sassare mata gaɓoɓin jiki." Ɗaya daga cikin su ya faɗa yana dafa na gefen shi.

Ita kuwa ta kasa tashi ballantana ta taimaki kanta sakamakon wani ɗanko mai kama da ƙara ya manne mata kafarta a kan bolar, duk da kuma iskar shaƙa ta yi mata kaɗan hakan bai sa ta daina kiciniyar tashi daga kan balar ba. Duk numfashin da za ta ja sai ta ji kamar ana yankar zuciyarta ne gaf take da rasa ɗan sauran numfashin da take kai-kawo da shi.


Wanda aka ce ya je ya saro kanta ne ya nufo kan bolar a fusace, cikin tashin hankali take kallon shi har ya ƙaraso ya zaro wata wuƙa mai baki biyu ya ɗaga cikin rashin imani zai sauke mata ita a ciki aka dakatar da shi. A fusace ya juyo ya dube su, wanda ya ba shi umarnin ya ɗaga masa hannu tare da nuna masa wannan kangon da ke gaba da su, hakan yasa ya gane mai yake nufi ya sunkuya ya ɗauke ta ya nufi cikin kangon.


Ihu take kurmawa wanda da shi da babu duk ɗaya, saboda bakinta da yake a manne da gam tana ji tana gani suka shigar da ita kangon har cikin wani guri wanda alamu ya nuna ɗaki ne za ayi a wajan. Jefar da ita ya yi a wajan ta runtse idanu saboda wani kalar azababben zafi da ya ziyarci kunkurinta, Dagus ya sa hannu ya cire mata gam ɗin da suka rufe bakin da shi ya warware mata ɗaurin hannun. Ganin yadda take numfashi ya yi saurin kallon sauran ya ce "Gaye kar fa mu bar yarinyar nan ta wulla kawo wannan abin nata a ba ta dan shaƙa dan mu samu abin da muke so." Ya faɗa yana miƙa wa Gaye hannu ya ba shi wani abu a laulaye cikin wani tsumma. Warwarewa ya yi sai ga magani ya fito a matso kusa da ita ya kafa mata shi a baki, ita kuma cikin rawar jiki ta shaƙi maganin sau uku sannan ta ji ta dawo daidai. Tana riƙewa ya fisge kwalbar maganin ya sa a aljihunsa yana dariya ya ce "Ke har kin isa ki shiga gonar Oga ki zauna lafiya." Ya yi maganar yana kai mata mari mai shiga jiki. Kuka ta fasa a fusace ya ce "Shiii!"

Ɗif ta shanye kukan tana haɗe hannu alamar roƙo, gabaɗaya jikinta rawa yake idanunta sai neman rufewa suke saboda tsabar gakabaitar da ta yi, shatin yatsun Dagus ya bayyana akan kyakyawar fuskarta kamar an zana shi, wani kalar numfashi take fitarwa cikin gajiyawa da daddage ta janyo numfashi tare ta rufe idonta cikin tashin hankalin rashin sanin yadda za ta tsira. A sanyaye ta sauke hannayenta daga haɗe sun da ta yi hawaye na zarya kan kuncinta, da ƙyar ta iya haɗiye yawu baki na rawa ta ce "Do..n.. girman Allah ka yi haƙuri kar ku cutar da ni alhalin ban muku komai ba, ka sani idan kuka zalince ni kuma wata rana za a yi wa ɗiyanku ko ƙannanku ko matayenku. Ban san me na muku ba kuka sace ni, don Allah ku faɗa min ko nawa kuke so zan sa Abbana ya ba ku amma karku taɓa min mutumcina, ni ko fita daga gida kuka ce na bari zan bar fita har abada na zama a gida." Ta ƙarashe maganar tana fashewa da kuka mai tsuma zuciya, lalle yau ba mai kwatarta sai Sarki Allah, cikinta da ke kukan yunwa ta kai hannu ta dafe ji take kamar ba a duniya take ba, tsabar yunwar da take ji ko gamin kirki ba ta yi bibbiyu take ganin su Dagus da suke tsaye a kanta.


A fusace Gaye ya ce "Ki bamu wannan abin na wajan ki sai mu rabu da ke ki tafi gida."

Kwalalo idanu waje ta yi cike da rashin sanin inda maganar su ta dosa, ta ce "Wallahi ni babu wani abu a wajena wanda yake naku, wayata ma ai kun amshe ta ba ni da komai ku rabu da ni." Ta ƙarashe maganar cikin fitar haiyaci, ji take komai ma duniyar ya mata zafi yadda suke gana mata azaba.


Jin ta faɗi haka yasa Gaye ya ce "Buɗe hannunki."

Kallon shi ta yi cikin tsoro da fargaba taƙi ba shi hannun, sai ma ƙara matse hannayenta ta yi tana gunjin kuka dan magana ma kanta ta kasa yi, shi kansa numfashin da ƙyar take iya janyo shi in da fitar, Dagus ganin ta yi shuru ya daka mata tsawar da ta sanya 'yan hanjinta kaɗawa.

"Za ki buɗe ko sai na sare miki hannun!?" Ya faɗa yana mai ƙara kusanto ta.


Babu shiri ta buɗe hannun jikinta na rawa tana jin kamar ta zo gangarar mutuwa. Babu komai ya gani sai kawai ya kwashe da dariya, "Hahaha! Yarinya man kaza ai shi mun gama mi shi nashi aikin, yanzu kuma namu ne za mu yi kin gane?" Ya faɗa yana matsowa kusa da ita.


Saurin ja da baya ta yi tana girgiza kai tana roƙon su da su rufa mata asiri kar su ɓata mata rayuwa, amma sai suka dinga dariya suna nuna ta.

"Ya Allah ka kawo min ɗauki, Ubangiji kar ka bari mutanen nan su ci zarafi na ban musu komai ba Allah ka kawo min ɗaukin gaggawa." Ta faɗa tare da ƙanƙame jikinta tana gunjin kuka.

Dagus ya kamo hannunta yana aje wuƙaƙensa biyu ya cire rigarsa yana bin ta da kallon za ki gane ba ki da wayo, ita kuma duk Addu'ar da ta zo bakinta yi take tana rawar jiki gabaɗaya ta sallama wa duniya yau za ta barta.. A gabanta Dagus ya cire riga da dogon wadonsa ya rage daga shi sai na ciki shi ma iya gwiwa, abin da ya ƙara gigita duniyar tunaninta ta cure waje ɗaya tana faɗin "Oh God, help me in my life."


Daga can gefen su wani ne sanye da kaya yagaggu yana bacci, jin hayaniyar ta gama hawa kansa sai ya buɗe idanuwansa wanda suka yi jajur saboda bacci. Ganin abin da yake faruwa ya zabura ya juya gefe ya ɗauki wani rabin taɓarya haɗi da wata mulmulalliyar sanda mai kauri da tsayi ya ɗaura wata hula a kansa duk ta yage. Sai da ya zagaye inda ya tashi ya kalli wannan gardawan ya kwarara ihu.


"Waiyihuhu! Waye nan ya shigo min gida?" Ya yi maganar yana nufo su.

Dukkan su suka ja da baya a kiɗime sai kuma suka ja suka tsaya tare da fito da wuƙaƙen dake ƙugunsu suna nuna wannan mahaukacin da shi. Shi kuwa bai kula su ba wajan ta ya nufa ya yi tsayauwar 'yan dambe yana dariya tare da zagaya ta, leƙa ta ya yi ita kuma ta ƙara mannewa a jikin bango taoro na ƙara lumkuwa a zuciyarta, dariya kuma yi ya soma magana.


"Hahaha Anty dama ke ce? Waɗannan babanninki ne da iyayenki da ubanninki?" Ya faɗa yana zama a gaban ta suka yi facing ɗin juna. Da ƙyar ta iya ɗago da kanta ta kalle shi, ganin shigar da ke jikinshi ta ji gabaɗaya ta firgice, hannayensa ta kalla ta ga taɓarya sai kawai ta rufe idanu tana yin duk Addu'ar da ta zo bakinta.


Ganin wannan mahaukacin zai ɓata musu lokaci yasa Dagus ya kai masa sara kan kafaɗarsa, ya kuwa ci sa'a ya same shi a daidai. Wani irin ƙara mahaukacin nan ya yi wanda yasa ta ƙara mannewa a jikin bango tana kuka tare da roƙon su.

"Don Allah kar ku cutar da shi tun da ba shi ba kuka biyo na roƙe ku." Ta yi magana tana matsowa kusan Mahaukacin wanda jini ya soma ambaliya daga kan kafaɗarsa, sosai ta ƙara ruɗewa har shidewa take tsabar tashin hankali..


Dariya suka dinga mata Dagus ya yi saurin wawurar ƙaramar wuƙarsa bai jira komai ba ya yanki Mahaukacin nan, ya dawo ta gefe ya ɗamko hannunta ya janyo ta kii! Shi ko Mahaukacin nan sosai yankan ya shige shi duk jini ya wanke masa kafaɗar,

hakan yasa kansa ya sara nan-da-nan ganin shi ya ɗauke na ɗan lokaci. Sai da ya jima can sannan ya buɗe idanunsa ya ga wayam ba ta gaban shi, a zabure ya ce " Anty!" Tare da miƙewa ya nufi ɗayar ƙofar.


Ita kuwa tuni sun yayyaga mata doguwar rigar dake jikinta, kaɗan ya rage su gama cire mata rigar ta ji muryarsa ai kuwa ta daddage ta kwarara ihu da ɗan sauran kuzarin da ya rafe mata. Kafin ta rufe baki Dagus ya faɗo kanta, wani irin nauyi ta ji yayin da Dagus ya rikito bisa kanta ta dinga kiciniyar kwace kanta amma ina ta kasa, wata dabara ta zo mata ta juya da fuskarta ta samu daidai ta ci kuncinsa ta gatsa masa cizo, ihu yasa ba shiri ya kai mata mari ita kuma taki sakin kuncin nasa har sai da ta ji ya kawo jini sannan ta sake masa kunci..

Cikin magagin zafin cizon da ta masa ya tashi daga kan ta ya kai hannu zai damko ta ya ji saukar duka a gadon bayansa. Cikin kiɗima ya juyo dan ya ga waye ya dake shi a cikin abokan aikin nasu, sai dai kuma ya ga saɓanin hakan, dan kuwa Mahaukacin nan ya gani tsaye a bakin ƙofar yana wurga idanunsa ko'ina ya ga inda take.

Tana ganin shi ta miƙe da ƙyar ta nufi inda yake, hakan yasa Dagus ya kuma kai hannu da niyar dawo da ita ta yi saurin yin ƙasa da rarrafe ta dawo bayan Mahaukacin. Ganin jini a bakinta yasa ya zazzaro idanu ya kalli Dagus fuskarsa na nuna tsananin ɓacin rai ya ce "Ka daki Anty ko?" Yana gama faɗin haka ya nufe shi da rabin taɓaryar dake hannunsa.

Duk da Dagus a tsorace yake amma ya tsaya yana jiran Mahaukacin ya iso gareshi, shi kuma yana zuwa ya wurgo masa rabin taɓaryar dake hannunsa ji kake Tim! Ta same shi a ruwan ciki. Bai tsaya yin komai ba ya hau kansa ya dinga kai masa naushii ta ko'ina, abokan tafiyar Dagus su dama tuni ya sumar da su, dan haka Dagus ya rasa me ceton shi a hannun wannan Mahaukacin.


Sai da ya ga baya motsi sannan ya dakata da dukan shi, huci yake yana faɗin " Ka fito mata da jini sai na kashe ka."

Ita kuwa tana gefe tana kallon shi zuciyarta cike da mamakin wannan Mahaukaci da ya cece ta a hannun mugaye. Dawowa ya yi wajan ta yana kallon ta bai ce da ita komai ba, sai da ya sauke numfashi sannan ya koma kan Dagus ya ja ƙafarsa ya fitar da shi daga cikin kangon ya dawo ya fitar da sauran wanda a lokacin suka dawo daga sumar da suka yi, yana fito da su suka lallaɓa suka miƙe suna ƙoƙarin gudu. Yana tsaye yana kallon su har sun soma tafiya suna waiwayen shi, shi kuma ganin haka yasa ya koma ciki da sauri ya ɗauko makaminsa ya biyo su a guje..


Ganin mutuwa na tunkaro su yasa suka kwasa a guje sai ga su a bakin hanya, shi ma ya iso yana nuna su da taɓarya ai kuwa suka ƙara wa gudunsu mai tuni suka bar wajan. Kaiwa da komowa ya dinga yi a bakin hanyar kamar mai yin pareti, sai da ya jima a haka sannan ya juya ya koma..

Tana ganin shi ta miƙe tsaye tana kallon shi har ya iso ya zauna a kan wani kwali mai faɗi, wata leda ya buɗe sai ga masa da miya har ta soma tsami sai tashi take. Da sauri ta done hancinta ganin ya sa hannu ya ɗauko guda ɗaya yana murmushi ya kai bakinsa, kakarin amai ta dinga yi shi kuma ya kwashe da dariya ya janyo kwalin ya matso kusa da ita ya tura mata masar yana dariya..



"Anty za ki ci ko?" Ya faɗa yana ɗaukar masar ya nufi bakinta da ita. Da sauri ta janye fuskarta ta ce "A a na koshi ka ci abinka."

Dariya ya kuma yi ya ci gaba da ci har ya cinye tas ya suɗe ledar, bayan ya gama ya janyo wata ledar ya bude ya ɗauko ruwa ya sha. Duk tana kallon shi har ya gama sannan ya ce mata "Anty yunwa nake ji." Ya faɗa yana ɓata fuska. Ita abin sai ya ba ta dariya ma dan haka ta yi murmushi abin da yake ba ta mamaki ma da yake ce mata Anty bayan kuma bai taɓa ganin ta ba sai yau, lokaci ɗaya taji zuciyarta ta yi rauni tausayin shi ya tsarga mata zuciya. "Yanzu kila iyayensa suna can suna neman shi, ko kuma sun gaji sun haƙura da nema, ko kuwa dai daga gidan mahaukata ya gudo yake zama a wannan waje mai mugun ƙazanta da wari?" Ta yi magana a sanyaye kafin ta sauke ajiyar zuciya ta dube shi ta ce " Ya sunan ka."


Dariya ya mata yana goge sandarsa da wani ɓakin tsumma, sai da ta kuma maimaitawa sannan ya dakata da abin yake ya ce " Ya sunanka?" Ya mayar mata da tambayar da ta masa. Waigawa gefe ta yi ta hango ɗankwalinta da isa wajan ta ɗauko, warware shi ta yi ta kalle shi ganin yadda jini ya ɓata masa jiki sai ta matsa a hankali cike da tsaro ta ce "Kawo na ɗaure ma wajan ciwon."

Maƙale kafaɗa ya yi yana turo baki sai kuma ya ce "Ni fa sarki ne a faɗar nan."

Sakato ya yi tana kallon shi, ta yi juyin duniyar nan amma fir ya ce shi sarki ne ba za a taɓa masa rawani ba, ita kuma tausayin shi ya cika mata zuciya sai kawai ta rabu da shi ta ce " Zan fita waje dan na koma gida." Ta yi magana tana bin hanyar fita..


Shi ma bayan ta ya bi suka fito a tare har bakin hanya, sai da ta juya ta ga ya biyo ta ta yi fuskar tausayi ta ce "To na gode ka koma."

Shi ma fuskar tausayin ya yi ya ce "To na gode ka koma."

Murmushi ta kuma yi a karo na biyu.

Duk wanda ya zo wucewa sai ya kalle su kallo irin na mamakin yadda ta tsaya a kusan mahaukaci ga shi kuma riƙe da makami amma bai ce mata komai ba, wasu kuma in sun ɗan yi gaba sai su ce mata 'Baiwar Allah wannan mahaukacin zai iya miki illa.' Murmushi kawai take musu ba ta cewa komai tana kuma mamakin yadda in mutane sun zo wucewa sai ya kare ta ya shiga gabanta yana muzurai.


Wani Dattijo ne ya zo wucewa ya yi shigar shi ta zuwa Masallaci ta yi saurin tarar shi sai ya tsaya. "Baiwar Allah lafiya?" Ya faɗa yana kallon ta.

"Baba ba lafiya ba don Allah ka taimaka min da waya zan kira Mamana su zo su dauke ni." Ta faɗa tana durkusawa, shi ma ganin ta durkusa ya durkusa a gefen ta ya ce "Baba ba lafiya ba don Allah ka taimaka min da waya zan kira Mamana su zo su dauke ni."


Dattijon nan ya dubi Mahaukacin ya ce "To amma mai ya haɗa ki da wannan Mahaukacin?"

Labari ta ba shi na ceton ta da ya yi ta kuma ce masa sace ta aka yi shi ne ta gudo har ya ceceta, jin haka yasa Dattijo ya cika da mamakin Mahaukacin ya dinga kallon shi ganin yadda ya durƙusa kamar yadda za yi, girgiza kai kawai ya yi fuskarsa na nuna tsananin damuwa ya fito da wayarsa Nokia ya ba ta. Amsa ta yi ta sa wata number ta danna kira, sai da ta kusa yankewa sannan aka ɗauka tare da yin sallama.

"Mommy!" Ta faɗa tare da sa kuka wani irin farin ciki na lullube ji na jin muryar mahaifiyarta da ta yi.


Daga cikin wayar matar ta dinga salati ta ce "Abir ke ce? Ina kuka shiga muke ta neman ku hankalinmu duk a tashe?"

Sai da ta goge hawaye ta ce "Mommy don Allah ki zo ki ɗauke ni Wallahi in suka kama ni kashe ni za su yi."

"Su waye za su kashe ki?"

Ganin za su ja magana yasa Abir ta ce "Mommy ki bari sai na zo gida, hurry up and come so that the person on the phone doesn't leave."

"Now you are somewhere?" Mommy ta faɗa murya na rawa.


Tambayar Dattijon ta yi ya faɗa mata inda take, tana jin mai suke faɗa dan haka ta roƙi tsohon da ya tsaya a wajan ba ta da nisa sosai da wajan za ta iso. Ba dan ya so ba ya ce ya amince..


Kamar an tsikare shi ya buga sanda a ƙasa ya juya ya shiga kewaye su yana dariya, da ido kawai suke bin shi tsoro ya cika musu zuciyoyi kar ya ce zai kai musu duka. Yana gama zagaye su ya wuce ya bar wajan yana faɗin " Anty bari na kawo miki kaya."

Suna kallon shi ya tsallake bolar ya shige cikin kangon nan sai ga wata dalleliyar mota ɓaka ta yi packing a gaban su, a razane Abir ta ja da baya ta koma bayan Dattijon nan..





_Littafin nan na kuɗi ne ƴar uwa nomal ~N~ 300, vip ~N~ 500 ne. Ina kuma sanar da ku ga masu buƙatar Littafin ABBA NE complete ayi min magana ta WhatsApp number na 👉🏻🥏+966577675904_





*Kada ku bari a ba ku labarin wannan littafi*



_Maman Nusaiba ce🫶🏻_

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.