Free chapter · Read without an account

5/6

by Maman Nusaiba · A HAKA NAKE SON SHI

[10/25, 3:35 Yamma] My Addatyna: ~_*A HAKA NAKE SON SHI*_~






Daga Alƙalamin


_*Sarat Alƙasum ~(Maman Nusaiba)~*_



_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_



_+966577675904_



*بسم الله الرحمن الرحيم*


Shafi na biyar (5)



Tallah !! Tallah !!


Shahararriyar Marubuciyar nan Ikilima Adam (kyauta daga Allah) wacce ta nishadantar daku a littafin ta mai suna *Kanwata* *kaikajawa kanka , Rai daya janzaki, yau na sake dawowa domin muku Domin tallata muku Littafaina mai Suna *(RUDANI )* Da kuma *Makauniyar Shari'a* littafine mai kunshe da Butulci , cin amana ,zagon Kasa , soyayya irin ta gani kasheni , aminci da saura n su basai n'a cika Ku da surutu ba Hausawa sukace Gani yakori ji.


Karku Manta *Makauniyar Shari'a* sabon littafi ne mai bibiyar Ma'anar sunan sa.


RUDANI littafine mai cike da Rudani da ban Al'ajabi , duk wacce kika fi buƙata zaki biya kudin sa Naira ɗari biyar kacal.


Farashin kowannen su Naira Dari biyar ne 500 kacal

Domin Karin bayani Ku tuntubeni a lambata kamar haka (*** ko Kuma + 22953726162 ) wacce Bata shirya Siya ba kada mu batawa juna lokaci.

Domin aikawa da kudi kai tsaye . 3115484026 ikilima Adam first bank

Turo shaidar biya akan wannan *** sai najiku.





A kiɗime ta yunƙura cikin kuzarin da ba ta san tana da shi ba ta miƙe tsaye, ba ta ma tsaya ganin abin da ta ci karo da shi ba ta nufi ƙofar Asibiti da gudu sai dai kafin ta isa ta ga an sha gaban ta, ware dara-daran idanuwanta ta yi a kan ɓakar ƙafarsa wadda taɓo da ƙura suka mata fenti, saurin kallon shi ta yi gabanta na faɗuwa kamar yadda shi ma ita ɗin yake kallo.. Kamar kullum yau ma sanye yake da gaggayen wandonsa wanda tun farkon haɗuwar su ta gan shi da shi, ƙafarsa ba takalmi haka yake yawo, riga biyar ce a jikinsa ɗaya kan ɗaya kowacce ta yi mugun yin dauɗa. Wani irin sanyi ne ya ziyarci zuciyarta har ba ta san lokacin da ta saki murmushi ba ta gyara tsayuwarta tare da lumshe idanu, buɗe idanuwanta ta yi ta juya bayan ta suka haɗa idanu da mazan nan har yanzu suna inda suke a tsaye sai daddana waya suke lokaci zuwa lokaci suna kallon agogon dake hannunsu..

Ganin ta juya tana kallon su ya yi saurin sunkuyawa ya ɗauki sandarsa ya sakala a kafaɗa tare da yin dariya ya shiga zagaye ta yana cika sadar a ƙasa, sai da ya dawo gaban ta ya ɓata fuska ya ce "Imm Anty tafiya kike yi?"

Murmushi ta yi ganin yadda ya harɗe kamar ɗan fulani, ƙura mana idanu ta yi shi kuma ya dinga tambayarta ina za ta je amma ba ta ji mai yake faɗa ba dan ta yi nisa a kallon da take masa, sai da taɓa hannunta sannan ta yi firgigit ta saki murmushi ya kuma tambayar ta ce "A a ina jiran yayana ne." Ta faɗa tana dawowa gefen shi, haka kawai ta ji yau so take ta zauna da shi su yi hira duk da ta san ba ma zai gane inda maganarta za ta dosa ba..

Sauke sandar ya yi yana dariya ya shiga zagaye ta yana faɗin " Anty ta yi tafiya! Anty ta zauna! Anty ta miƙe!"


Murmushi Abir ta yi jin yadda yake kiran ta da Anty har da waƙa abin sai ya ba ta nishadi, Jakarta dake riƙe a hannunta gam sakamakon tsoron da ta ji lokacin da za fito a razane ta buɗe ta ɗauko gorar ruwa mai sanyi ta miƙa masa, shi kuwa ya tsare ta da kallo idan ya kalle ta sai kuma ya kalli gorar. "Ga shi maza ka sha ruwa." Ta faɗa tana nuna masa ruwan.

Amsa ya yi ya ɗaga gorar yana duddubawa yana faɗin "Allah sarki abokina kai ne haka? Ina kwana? Dama haka kake ban sani ba?" Ya faɗa yana shafa rubutun dake jikin gorar.

Ƴar dariya ta yi ƙuncin da ke zuciyarta na yayewa, sosai ta shagala da kallon shi yana nuna mata gorar tare da tambayarta.

"Anty ga abokina nan ya ce ki bani kayansa zan kai masa."

To kawai ta ce masa ya ci gaba da surutai barkatai wata maganar ita kanta ba ta gane me yake nufi sai dai ta bi shi da to ko a a.. Duk da hankalinta ba a kwance yake ba amma haka take biye masa in ya yi magana ta amsa masa, juyowa ta kuma yi dan ta ga mazan nan ko suna nan sai ta ga wayam ba kowa. Ajiyar zuciya ta sauke ta dube shi ta ce "Ya sunanka wai?"

Dariya ya mata ya ce "Ya sunanka zai ci abinci." Ya faɗa yana ɗaga gorar tare shafa bayan.


Suna a haka sai ga motar Salim ta iso bakin Asibitin, da sauri ya fito ganin ta tsaye da Mahaukaci riƙe da makami, a ɗan naisa da su ya tsaya ya ce "Baby waye wannan ɗin?" Ya faɗa a tsorace. Murmushi ta yi ta ce "Shi ne wanda nake ba ku labari, kawai na fito ne na haɗu da shi."

"Kwalalo idanu waje ya yi ganin yana kallon shi nan-da-nan tsoro ya cika masa zuciya, shi kuma kallon shi kawai yake yana dariya abin da ya ƙara tsoratar da Salim. Baki na rawa ya ce "To..To zo mu tafi gida."

Kallon shi ta yi cikin wani irin yanayi, ji take kamar su ɗauki lokaci mai tsayi a haka tana hira da shi, sai da Salim ya sake maimaita maganar sannan ta rausayar da kai kamar za ta yi kuka ta ce" Sai an jima." Ta faɗa tana juyawa ta soma tafiya.

Da sauri ya biyo ta ya ce "Anty abinci nan ci." Ya faɗa yana kama mayafinta yana marairaicewa kamar zai sa mata kuka. Ita kuma sai ta ji wani irin abu ya soki zuciyarta ta ji ba za ta iya tafiya ta bar shi ba.


Kallon Salim ta ya yi sai ya ce "Baby bari na sayo masa abincin."

Girgiza kai ta yi ta ce "Yaya don Allah taimako nake so ka min." Ta faɗa tana narkar da murya.


"Indai ba a kan wannan Mahaukacin ba ne zan taimaka, amma in dai akan shi ne ba ma zan iya ba." Ya faɗa yana haɗe rai.

Saurin kallon shi ta yi cikin rashin sanin abin yi ta ce

"Don girman Allah Yaya mu ɗauke shi a kai shi Asibiti, duba ka ga yadda kayan jikin shi suke fa, ina so na taimake shi kamar yadda ya taimake ni." Ta faɗa tana goge hawayen da ya zubo mata.


"Wallahi ba zan ɗauki Mahaukaci a cikin motata ba, so kike ya kashe mu gabaɗaya? Ke wai ma meye damuwarki a kan wannan Mahaukacin wanda bai san kansa ba bare ya san abin da ya dace da shi ba?" Ya yi maganar yana nuna shi da yatsa.

Hawaye ne suka cika mata ido murya na rawa ta ce "Don Allah fa Yaya Salim ka taimaka mu ɗauke shi a motar nan, ina so zan kula da shi na kai shi Asibiti ko Allah zai sa a dace ya samu lafiya, ka ga in na yi haka na samu lada kai ma kuma ka samu lada mai yawa na taimako." Ta faɗa tana durƙusawa a gaban shi ta kama ƙafafuwansa tana kuka.

Duk wanda ya zo wucewa sai ya tsaya yana kallon su har wani da ya zo wucewa ganin tana kuka ta riƙe masa ƙafa ya tsaya, kallon Salim ya yi cikin nuna tausaya mata ya ce "Haba bawan Allah kai wani irin azzalumi ne? Ta ya yarinya za ta durƙasa a gabanka tana kuka, amma dan rashin sanin darajar mata ka kasa yi mata abin da take buƙata? Ni a gani na ko ba ka son ta bai kamata ka nuna ba ka son ta ba a gaban idanunta, don Allah ku samu waje ku zauna ku fahimci juna." Yana gama faɗin haka ya wucewar shi bai ma tsaya ya ji mai Salim ɗin zai faɗa masa ba. Shi kuwa Salim in ransa ya yi dubu yau Abir ta gama ɓata masa shi, ta zubar masa da mutumci har mutane na tsayawa su ce ya ci zarafin ta bayan ba su san akan Mahaukaci take wannan roƙon ba. A fusace ya ce "Kin san Allah in ba ki tashi ba muka tafi zan bar jin tausayin ba ki da lafiya na lafta miki mari a bakin titin nan, za ki tashi ko sai na miki duka?" Ya faɗa yana ɗaga murya.


Idan akwai abin da Abir ke matuƙar tsoron ayi mata ya gigita mata rayuwa to bai wuce a mata tsawa ba, hakan yasa ta miƙe da sauri duk da tsoron da take ji amma ba ta fasa faɗin abin da take son faɗa ba.

"Shi kenan kar ka taimaka min Yaya Salim, nasan yau da Yaya Abdul ne na nuna masa wanda ya ceci rayuwata na kuma nemi ya taimaka masa ba zai min wannan wulakancin ba, ni ce fa Ƙanwarka Yaya Salim ko ka manta ne?" Ta faɗa tana fashewa da kuka tare da rufe bakinta dan kar sautin kukan ya fito...


Shi kuwa ganin tana kuka ya matso kusan Salim ya durkusa shi ma yana kuka kamar yadda ya ga tana yi, ganin ba ta fasa ba sai shi ya daina ya yi zunbur ya miƙe tsaye ya dubi Salim tare da ɗaga sandar da ke hannunsa ya ce "Kai ne kasa Anty kuka ko?" Ya faɗa yana ɗaga sandar zai sauke masa.


Saurin miƙewa Abir ta yi ta shiga tsakanin su tana kallon shi sai ta girgiza masa kai, hakan yasa shi ma ya girgiza mata kai sai kuma ya sauke sandar ya ɓata fuska ya ce "Anty yunwa nake ji, wa ya dakeki Anty? Shi wannan ɗin waye?". Ya jero mata tambayoyi yana yin kamar zai faɗa jikinta.


Salim da yake zare idanu ganin za a kassara shi ya ce "Baby mu tafi."

Ko kula shi ba ta yi ba ta kalle shi ta ce "Kana jin yunwa ne?"

Murmushi ya yi sai kuma ya dafe kafaɗarsa yana yarfa hannu ya ce "Anty ciwo nan yake." Ya faɗa yana narke mata fuska irin na ƙananan yara. Cikin tausayawa ta dinga jero masa sannu shi ma yana maimaita abin da ta faɗa sai kawai ta yi murmushi, Salim kuwa ya cika ya yi fam ganin ma ta manta da zaman sa a wajan sai biya Mahaukaci take suna shashanci, faɗa mata ya yi zai tafi ya bar ta a wajan, ita kuma ta kafe akan lalle dole sai sun tafi da Mahaukacin nan, shi kuma ya ce sam ba zai ɗauke shi ba ya shaƙe shi yana driving, ƙarshe ma ya shige mota ta biyo shi tana roƙon shi yaƙi kallon ta. Ɗago kai ta yi sai ta ga wayam ba kowa a wajan, cike da mamaki da al'ajabi ta ce "To ina ya tafi kuma?"


"Tsuwwww! Dalla malama ki zo mu tafi kin tsaya kina ɓata min lokaci a banza saboda wani Mahaukaci. " Ya faɗa yana kunna motar. Ba dan ta so ba ta shiga amma gabaɗaya zuciyarta na can tunanin wajan da ya nufa, Salim kuwa ta gama ɓata masa rai dan haka bai ce mata uffan ba har suka iso gida. Ko packing bai gama yi ba ta ɓalle marfin motar ta fito da sauri ta nufi ciki su Maigadi na mata barka da zuwa amma ba wanda ta amsawa saboda kukan da take ta shige ciki...



Grandma na zaune sai ganin ta ta yi ta shigo mayafi a hannu tana kuka, hakan yasa ta kwashi salati.

"Muhammadu (S.a.w) ɗan Abdullahi jikan Abdulmuɗallibi ni Hauwa'u! Me zan gani haka ƴar nan?"

Zama ta yi tana shashshekar kuka sai ga Salim ya shigo Abdul da Daddy da Abba na biye da shi, suma duk suka dinga tambayarta lafiya take kuka?


Goge hawaye ta yi ta ce "Ba Yaya Salim ba ne."


Da sauri Abdul ya kalli Salim fuska a haɗe ya ce "Me ka yi mata har ya saka ta kuka?"


Tsaki ya ja ya samu waje ya zauna yana hura hanci bai ce komai ba, hakan yasa Abba girgiza kai ya ce "Mamana me ya faru?"


"Ba shi ba ne na gan shi ya hana mu ɗauko shi."


"Shi wa kenan?" Cewar Abba. Labarin komai ta ba su tana yi tana sharbe hawaye har da majina. Da sauri Abba ya kalli Salim ya ce "Amma Salim ka bani mamaki, madadin ka samu a kama maka shi in ya so ma tun da ba ka son a saka shi a motarka ka samu wata motar ka sako shi a kawo shi, sai kuma ka nuna kai ba za ka yi hakan ba. Duk da kun ce Mahaukaci ne ai za mu iya taimakawa a kai shi Asibiti ko ka manta shi ya ceceta?" Ya ƙarashe maganar cikin fushi.

Daddy ya ce "Rabu da shashasha mana, wani lokacin kana abu kamar wanda bai waye ba Salim. Da ta faɗa ma haka ai za ka iya yi wa Abdul waya ya kira yaran shi su zo su ɗauke shi, amma sai ka hau faɗa."


Shi ko Abdul bai ce komai ba ganin iyayen nasu sun yi magana, amma tabbas yau ya tabbatar da Salim ba shi da tausayi ya saka ta kuka, wanda yake da yaƙinin sai ta yi ciwon kai ganin yadda idanunta suka yi jajur. Lumshe idanu ya yi yana jin ba daɗi sautin kukanta yake ji har ƙasan zuciyarta, ji yake kamar ya je ya rumgume ta ya rarrashe ta ko ta daina kukan, amma kuma ba zai iya ba tun da su Abba suna wajan..


Ana haka sai ga Mami da Umma sun kawo wa Grandma abincin rana kowacce da mai aikinta dauke da abincin sun sha ado, suklna isowa suka aje abincin suka gaishe su Abba sannan suka fita..


"To me ake tattaunawa ne haka na ga duk ranku a ɓace?" Cewar Umma tana zama kusa da Daddy.

Ammi ta taɓe baki ta ce "Kin san dai tatsuniyar gizo ba za ta wuce ta ƙoƙi ba."

Jin haka yasa Salim kallon Mami ya shiga faɗa mata abin da ya faru, ta riƙe baki tare da kallon Daddy ta ta yi mitsin-mitsin da idanu cikin masifa ta ce "Ai ban san ba kuna ɓakin ciki da ɗana Salim sai yau, ashe haka kuka tsane shi? Taya zai ɗauko rikakken Mahaukaci a motarsa ya je ya kashe min shi ko ya masa illa? To Allah ko da wasa wani abu ya faru da Salim sai na ɗauki mataki a kanku musamman kai wannan mai suffar kwartayen." Ta faɗa tana nuna Abdul, shi kuma ya yi saurin sunkuyar da kai..



Cikin jin zafin maganar Umma ta zaburo ta ce "Ke Farida kike ko fari? To Wallahi hawauniyarki ta kiyayi ramata! Idan kina cin ƙasa,ki kiyayi ta shuri na faɗa miki. Ko kusa kar ki ƙara alakanta mini ɗa da mummunar kalmar kwarto, kin yi na farko kin yi na ƙarshe Wallahi in kika sake faɗa sai na miki abin da har ki mutu ba za ki manta ba." Ta faɗa tana huci.


Kallon banza Mami ta yi wa Umma tana karkada ƙafa ta ce "Òk dukana za ki yi in na sake faɗa? Kamar ke kika haife shi har kike wani hayayyako min ke ga uwarsa ko? To an ce masa mai suffar kwartaye." Ta faɗa tana hararar ta.


Umma na shirin yin magana suka ga Maigadi afujajan ya faɗo palon yana zare idanu, a harzuƙe Mami ta ce "To mitsiyaci me ya shigo da kai nan?"


Maigadi ya ce.....




🥏 *WhatsApp number* +966577675904




_Taku har kullum Maman Nusaiba ce_

[10/25, 3:35 Yamma] My Addatyna: ~_*A HAKA NAKE SON SHI*_~






Daga Alƙalamin


_*Sarat Alƙasum ~(Maman Nusaiba)~*_



_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_


*بسم الله الرحمن الرحيم*



An kusa gama free fage duk mai bukatar ci gaba sai ya min magana ta wannan number. *+966577675904*



Shafi na shida (6)




Tallah !! Tallah !!


Shahararriyar Marubuciyar nan Ikilima Adam (kyauta daga Allah) wacce ta nishadantar daku a littafin ta mai suna *Kanwata* *kaikajawa kanka , Rai daya janzaki, yau na sake dawowa domin muku Domin tallata muku Littafaina mai Suna *(RUDANI )* Da kuma *Makauniyar Shari'a* littafine mai kunshe da Butulci , cin amana ,zagon Kasa , soyayya irin ta gani kasheni , aminci da saura n su basai n'a cika Ku da surutu ba Hausawa sukace Gani yakori ji.


Karku Manta *Makauniyar Shari'a* sabon littafi ne mai bibiyar Ma'anar sunan sa.


RUDANI littafine mai cike da Rudani da ban Al'ajabi , duk wacce kika fi buƙata zaki biya kudin sa Naira ɗari biyar kacal.


Farashin kowannen su Naira Dari biyar ne 500 kacal

Domin Karin bayani Ku tuntubeni a lambata kamar haka (*** ko Kuma + 22953726162 ) wacce Bata shirya Siya ba kada mu batawa juna lokaci.

Domin aikawa da kudi kai tsaye . 3115484026 ikilima Adam first bank

Turo shaidar biya akan wannan *** sai najiku.





Maigadi ya durƙusa a gaban su Abba ya ce "Alhaji wani mutum ne ya zo a ƙofar gida ya ce Uwar masu gida yake son gani."

Da sauri Abir ta dafe ƙirji tana kwalalo idanu waje ta ce "Ni kuma Baba Maigadi?" Ta faɗa tana kallon Abba.

Kallon Maigadi Daddy ya yi ya ce "Ka je ka masa iso ya zo nan mu ga waye haka yake neman ta?"


Kwaɓe fuska ta yi jin abin da Daddy ya faɗa ta ce "Yanzu Daddy ba ka san ko waye ba kuma sai ka ce wai ya shigo mana har ciki? Ni dai ko ya zo ba zan bari ya ganni ba." Ta faɗa tana yin raurau da idanu dama ita indai ta wannan ɓangaren ce to ita ce shugabar ma su kuka a cikin familyn Maitama, hakan yasa wasu daga cikin su indai sun haɗu to fa sai sun saka ta kuka..

Abba ya gyara zama ya ce "Mamana ki bari mu ga waye shi mai neman naki." Gyaɗa kai kawai ta yi ba ta ce komai ba, burin ta kawai ta ga waye haka wanda yake neman ta da gabannin Azuhar ɗin nan? Tuna text ɗin da aka mata yasa ta ji gabanta ya faɗi rass! Ta yi saurin runtse idanu tana karanto Addu'ar neman tsari da waɗannan azzaluman mutanen, wanda suke neman kashe mata rayuwa tun kwananta bai ƙare ba a duniya.

Da Sallama Maigadi ya shigo shi kuma yana biye da shi har suka iso cikin palon, Maigadi ya koma bakin aikinsa shi kuma ya tsaya a tsaye tare sa cewa "Assalam alaikum."

Saurin kallon shi Abba ya yi ya ce "Wa alaikum salam! Wa nake gani kamar Barrister Huzaifa? To iso ka zauna mana ga guri."

Murmushi ya yi tare da ɗago da fuskarsa ya samu waje ya zauna, Ɓaki ne dogo mai matsakaicin jiki wanda shakarunsa ba su wuce 35 ba, yana da kyakyawar ƙirar jiki kana ganin shi ka ga ɗan gayu mai ji da kansa, sanye yake da ɗinkin shadda gizna

blue color ta samu ɗinki mai kyau, hakan yasa ta ƙara haskaka shi. Cire glass ɗin da ke manne a idanunsa ya yi tare da cewa "Am Alhaji ya muka ji da wannan ifitila'i da faru?"

"Alhamdu Lillah Barrister yanzu haka ma daga office ɗin Ogan su Abdul muke ni da Yaya." Cewar Abba.


Girgiza kai Barrister ya yi cike da alhini ya ce "Ni ma yanzu nake ganin ana maganar a TV, shi ne hankalina ya tashi na kasa zama na ce sai na zo naji daga bakinku da gaske Abokina an yi kidnapping ɗin sa? Kasan na kai wata takwas bana ƙasar na tafi ƙaro karatu a ƙasar Turkiyya."

Daddy da bai ce komai ba tun zuwa Barrister ya kalle shi ya ce "To ya muka iya da ikon Allah Barrister, gardama ce irin ta Yaya Ibrahim na faɗa masa in zai fita yake tafiya da masu tsaron lafiyarsa, amma gani yake kamar suna takura masa ƙarshe ma ya ce iya aikin su su bi shi office da kuma tsaron cikin gida ,ya fi so ya tafi shi kaɗai ƙarshe duk wasu officer ya mayar da su yin aiki, yanzu ga shi an ma rasa a wani hali yake a yanzu."


Mami da tun dazu take jan tsaki ta miƙe ta ce "Sai an jima ni zan je ɓangarena tun da maganar nan dai ba ta shafe ni ba."

Sake da baki Abba ke kallon ta har ta fita daga palon, haka ita ma Umma ta miƙe tsam ba ta yi magana ba ta bar palon. Duk ba wanda ya ce wani abu sai da suka bar palon sannan Barrister ya ce "My daughter za ki iya gane mutanen da suka kama ki?"

Dam! Ta ji zuciyarta ta buga ta sunkuyar da kai, to ita me ake so kuma ta faɗa bayan wanda ta faɗa? Shi ma ɗin dan ba ta da yadda za ta yi ta haɗa da ƙarya ta faɗa. Ganin taƙi cewa komai yasa Abdul gyara zama ya ba wa Barrister labarin da ta ba su, shi kuwa ya yi shuri yana nazarin maganar ko zai samu amsar da yake son samu, amma sam abin ya kulle masa kai hakan yasa ya kuma cewa "Uwar masu gida, za ki iya tuna kamannin mutanen?"


Goge majinar da ta fito daga hancinta ta yi sannan ta ce "Ni fa ban taɓa ganin fuskar ɗayan su ba, duka kullum fuska a rufe suke shigowa ɗakin da suka saka ni."

Ajiyar zuciya Barrister ya sauke ya ce "Ok to kukan ya isa haka yi haƙuri, in sha Allah zan ci gaba da bincike akan lamarin, akwai wani abokina D.P.O. ne na masa bayanin ɓatan amma tun da kes ɗin na hannun Abdul zan masa magana na ce an amshi kes ɗin, sannan in sun kira ku sanar da ni Alhaji ni zan koma, amma kafin nan ina son yin magana da Uwar masu gida. "Ya faɗa yana kallon ta.


Grandma ta ce "To Huzaifa mun gode kwarai ke kuma tashi ku je waje in kuma mu ba ku waje to?" Da sauri ta ce "A a Grandma mu je bakin motar shi kawai."

Ba ta musa mata ba ta tashi ta gyara mayafinta sai kuma ta ga daga gefe wajan da Mahaukaci ya taɓa mata ya yi dauɗa. Ajiyar zuciya ta sauke ta bi bayan Barrister suka fita..


Bayan sun fita Abdul ya ce "Anya kuwa Daddy ba akwai abin da Baby ke ɓoye mana ba?"

Murmushi Daddy ya yi ya ce "Haba kai kuwa taya ma za ta ɓoye mana wani abu bayan ta san ba ta wanda za ta faɗa wa damuwarta sai mu iyayenta, ka daina wannan maganar kar ma ka tarbe ta da ita."

Ba dan ya yarda ba ya ce da Daddy to kawai dan a bar maganar...


Suna fita bakin motar Barrister ya dubi Abir yana ɗan murmushi ya ce "Abir ki yi haƙuri in sha Allah mahaifinki zai kubuta kin ji. Sannan ina so ki faɗa min gaskiyar komai da kika gani bayan an sace ku."

Cikin ƙosawa da maganar ta ɗago da idanunta wanda suka yi jajur saboda kukan jda ta ci ta sauke su a kan Barrister, shi ma ƙura mata idanu ya yi sosai yarinyar ke ba shi tausayi ita kuka ba ya mata wahala ballantana wannan mai dalili ne. Shi ya fara ɗauke idanunsa daga kanta tare da ɓala yatsu biyu, da sauri ta sauke nata idanun a kunyace ta ce "Uncle iya abin da na sani shi na faɗa maka ku yarda da ni mana." Ta faɗa tana rufe fuskarta da mayafi..

Wani iri ya ji ba daɗi ya ce "OK zan kira ki idan na samu lokaci je ki ciki." Turo baki gaba ta yi ta tsaya ba ta tafi ba, har ya buɗe marfin motar ya ga tana tsaye sai ya dakata ya dube ta tare da cewa "Ya dai? Ko akwai magana ne?" Ya jero mata tambayoyi.

Saɓa baki ta yi cikin Shagwaɓar da ta zame mata jiki ta ce "Uncle ai ba ni da waya sun kwace min ita."

Murmushin gefen ba ki ya yi ya ce "that is very good my little, zan sa a bibiyi number in dai wayar a buɗe take tabbas za mu gano inda suke, yanzu ba ni number da kike da ita." Ya faɗa yana miƙa mata wayarta tsadaddiya

Ajiyar zuciya ta sauke ta amsa ta sa masa number sannan ta masa sallama ta shige ciki...

Ko da ta dawo Abdul ya tsare ta da tambaya.

"Baby me ya ce miki?"

"Ƙarin bayani ya nema." Abin da ta faɗa kenan ta ɗauki jakarta ta nufi ɗakinta.

Kwafa ya yi yana nufar ɗakin Grandma ganin duk sun tashi daga shi sai Grandma da Laraba ke mata tausa, ganin ya nufi ɗakinta ta daddage ta ce "Kai Abdullahi uban me ka aje min a ɗaki da za ka shiga? In ce ba da kuɗin uwarka Sa'ade aka gina min ɗakin ba dai ko? To maza ka yo baya ƙaton banza tuzuru sai warin balaga kake ka zama rikakken namiji ba mata, to ni ba ƴar banza ba ce irin iyayen naka da suka saya ka sai abin da ka ga dama kake yi. Yanzu ba dan ba ma ni zuciyata a tsakake take ina zan yarda ka zauna kusa ma da ni kana warin balaga." Ta ƙarashe maganar tana gutsirar goron da ke hannunta ta ƙara masa da harara.

Sai da ya tsaya ta gama sannan ya ba wa iska ajiyar ta ya shige ɗakin. Ganin ya shiga ta kwashi salati "Muhammadu Rasulullahi sallallahu alaihi wa sallama ni Hauwa'u! Wannan wacce irin fitina ce haka? Na ce kar ka shigar min ɗaki amma dan jafa'i sai ka shiga, za ka fito ka sameni a palon nan sai na ma wankin babban bargo."

Ita dai Laraba ƙunshe dariyarta take kar ta fito ta yi laifi Grandma ta yi mata tatas kamar yadda ta saba mata...


Labari ya karaɗe cikin garin Yola da kewayanta na ɓatan Alhaji Ibrahim Maitama, hatta social media duk inda ka nufa maganar sace shi kawai ake yi, har ma da masu ƙarawa labarin gishiri. Wasu su ce ai abokan kasuwancinsa ne suka haɗa masa tuggu aka sace shi, wasu kuma su ce kawai mahassada ne abin dai kowa da kalar ƙagen da yake faɗa..


Abir duk ta ƙara ramewa ta yi zuru-zuru kamar ba ta cin abinci, tunanin Abie ɗinta take ba dare ba rana ga tunanin yadda za ta ga mahaukacin nan duk ya addabe ta..

Yau ma kamar kullum tana zaune ta lula duniyar tunani can ta tuna number dattijon nan, da sauri ta miƙe ta fito zuwa ɗakin Mommy. Da Sallama ta shiga inda ta samu Mommy ba ta ɗakin, jin ƙaran ruwa a banɗaki yasa ta gane wanka ta shiga, cikin sauri ta ɗauki wayar Mommy ta duba ɓangaren kira ta shiga neman number, sai da ta sha wahala sannan ta samo number ta yi saurin ɗauka ta fita..

Cin karo suka yi da Yasmin ita ma tana sauri, saurin kallon Abir ta yi ganin ita ce yasa cikin ɓacin rai ta ce "Ke wata irin mahaukaciya ce? Ta ya za ki buge ni ko ki bani haƙuri kike ƙoƙarin wucewa?" Ta faɗa a fusace.

Ko uffan Abir ba ta ce da ita ba abin da ya ƙara tafasa zuciyar Yasmin ta ɗaga hannu ta zabga mata mari ji kake tass!

A ruɗe ta juyo tare da dafe kuncinta saboda wani irin zafi da ya ziyarci dukkan ilahirin jikinta har sai da ganinta ya ɗauke na wucin gadi.

"Last warning! Idan kika sake min irin haka sai na kakkarya ki mai ƙirar aljannu jikar mayu, ban san me Yaya Salim ya gani a tare da ke ba har yake wani rawar jiki a kank...

Kafin ta ƙarasa ta ji saukar wani gigitaccan mari kan fuskarta, ta juyo a ruɗe dan ganin wanda ya mare ta sai suka haɗa idanu da Abdul nan-da-nan jikinta ya ɗauki rawa, shi kuma tun lokacin da ta mare ta yake tsaye a kofar palon yana kallon ƙarfin hali irin Yasmin, ta bangaje ta kuma ta mare ta ɗan iya shege. Abin da ya ɓata masa rai ya harzuƙa shi da ta haɗa ta da Salim nan-da-nan ya ji zuciyarsa ta ɗauki wani kalar zafi marar iyaka..

Da sauri Abir ta dawo bayan Abdul ta kwanta a bayansa ta saki kuka, ita ba marin ba ne ya ɓata mata rai da take haɗa ta da aljannu shi ya fi taɓa mata zuciya, duk da ta saba jin wannan kalmar a wajan su Mami da sauran yaran gidan.

Dawo da ita ya yi gaban shi ya shiga goge mata hawaye yana ba ta haƙuri har ta daina kukan sannan ta zare jikinta daga nasa ta wuce ɗakinta, ita kuma Yasmin ta yi ƙiƙam tana musu kallon ɓakin ciki, sai da ya daka mata tsawa sannan ta fice da gudu..


Shirin Makaranta take ta yi cikin ɗan kuzarin da ya rage mata ta fito inda ta samu Mommy zaune ita da Laraba tana ba ta labarin ƙauyensu, kallon ta Mommy ta yi ta ce "Kin shirya?"

"E Mommy zan wuce ayi mana Addu'a."

"Allah ya kiyaye ki a dawo lafiya."

Murmushi ta yi tare da matsowa ta yi kissing ɗin Mommy sannan ta wuce waje. Direba ta samu yana jiran ta, sai da ta gaisa da su Maigadi sannan ta shiga suka tafi..



Tsaye ya yi a bakin hanya yana goge sandarsa yara na tsokanar shi yana nuna musu sandar, kamar an ce ta waiga ta gan shi cikin sauri ta ce "Direba dakata please." Ta faɗa tana waigen shi

Saurin taka birkin ya yi ya tsaya ya juyo ya kalle ta ya ce "Ranki ya daɗe lafiya dai."

"E lafiya lau buɗe min na fita akwai abin da nake son yi a nan."

"A a gaskiya ki yi haƙuri Maigida ya ce nake kula da ke kar na bari ki tafi wani waje."

A fusace ta ce "Za ka buɗe min ko sai zabga maka mari?"

Jin abin da ta faɗa ya sa ya buɗe mata ta fito shi ma ya fito, nufar inda yaran suke suka yi sai sauri take kamar za ta tashi sama. Suna isa suka ga yara ne kawai suka yi gungu suna ta wasa, tambayar yaran ta shiga yi.

"Ku ba ku ga wani Mahaukaci a nan a tsaye ba?"

Wani yaro daga cikin su ne ya ba ta amsa "E amma ai ya yi tafiyar sa yanzu."

Da sauri ta riƙe hannun yaron ta ce "Don Allah ina ya nufa?"

"Ni ma ban sani ba, na ga dai kawai ba ya nan."

Dafe kai ta yi cikin damuwa ta juya ta nufi motar shi ma Direba ya bi bayanta suka koma motar ya tada suka tafi. Wasu irin zafafan hawaye ne suka zubo mata, mutum kamar aljani ta gan shi amma kuma a ce mata ya ɓace wa ganinta kamar walkiya? Lalle dole ta sa a nemo mata shi ko ta nema masa lafiya. Tuna ta ɗauki number Dattijo na ta kira shi ba yasa ta ji ɗan sanyi a ranta tana aiyanawa da ta je gida za ta kira Baba Dattijo...


Babban get ne wanda aka buɗe wasu motoci guda biyar suka shige cikin gidan, gida ne na gani na faɗa ya tsaru iya tsaruwa, motar ta tsakiya aka buɗe wani hamshakin mutum ya fito cikin shiga shi ta alfarma ya yi gaba suka bi bayansa. Wani sashe ya shiga na gidan sai ga shi a wani ɗaki mai dubu-dubu wanda babu komai a cikin ɗakin wata kujerar roba a bakin ƙofar ɗakin. Makunnar haske ya laliba ya kunna sai ga ɗakin ya ɗauki haske tauu, wani mutum ne kwance ya takure a waje ɗaya kayan jikinsa duk a yage ga jini a jikin fufafin, ƙara ɓata rai mutumin ya yi ya ce "Babba maza tashe shi."

Wanda aka kira da Babba fuska ba annori ya fita waje, bai jima ba ya dawo da ruwa a wata roba yana tururi ya kwamaya wa mutumin nan.

A gigice ya tashi yana mayar da numfashi cikin mawuyacin hali ya soma buɗe idanuna, da sauri ya ƙara buɗe su ganin wanda yake tsaye gaban shi, ya ɗaga hannunsa da ƙyar ya ce Jar...




Yanzu ma aka fara masoya ku dai kar ku bari ayi tafiyar nan ba da ku ba, ki hanzarta biya kuɗinki domin ayi wannan tafiya mai cike da sarkakkiya tare da ke my sister ..






_Taku har kullum Maman Nusaiba ce_

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.