Free chapter · Read without an account
Page 2
by BIL-SAN · MUTALLAB ASAD
MUTALLAB ASAD MUTALLAB
{MAM}
NANADISOBILLYSFARI
2.
Ƙarar da wayarsa dake gaban aljihun jallabiyar dake jikinsa tayi yasa shi miƙewa yana ɗaga wayar da sunan ARYAAN babban abokinsa ya fito ɓaro-ɓaro a jiki tare da ficewa daga ɗakin.
MUTALLAB ASAD MUTALLAB shine cikakken ainahin sunan yayan nata da take matuƙar ji da kuma alfahari dashi, su uku mahaifiyarsu data kasance mace ta biyu ga mahaifin nasu shahararren ɗan kasuwar da yayi suna lungu da saƙo wato ALHAJI ASAD MUTALLAB MAI TAYA ta haifa kafin Allah yayi mata rasuwa lokacin tana da shekaru huɗu a duniya sai ɗaya yayan nata kuma abokin faɗanta JALIL ASAD MUTALLAB, Mahaifinsu na matuƙar son mahaifiyarsu data kasance cikakkiyar buzuwa data fito daga jamhuriyyar Nijar saboda yanayin kulawa da soyayyar da take nuna masa, wanda hakan ya haifar da matsananciyar tsana tsakaninta da duka matan nasa musamman Hajiya Zainabu uwar gidansa wato Ummah, sun goga kishi sosai da ita duk da kuwa mahaifiyarsu macece mai haƙuri da don zaman lafiya, sai dai fahimtar da tayi kulawarsa ga mijin nata ce ke haifar da rashin zaman lafiyar tasu ta nuna tabbas indai har sai ta dena yin hakan zasu samu zaman lafiya to ashirye take da fuskantar duk wani abu da Hajiya Zainabu zata zo mata dashi, gogaggiyar macece Hajiya Zainabu da tasan kissa da kuɗina da kuma makirci kala-kala sai dai duk da haka rakasa yin nasara akan mahaifiyar tasu Hajiya mariya, hakan yasa tafara bin malamai kala-kala da shiga bokaye don ta raba tsakaninsu, sai dai riko da ibadar mahaifiyar tasu ya shamakanceta daga duk wani kaidi da kuma asirce-asircenta har zuwa lokacin da mai rabawa ta raba su. Duk da haka Hajiya Zainabu bata dena jin wannan tsanar da take yi mata ba ganin yanda soyayyar da maigidan nasu ke yiwa Hajiya Mariya gaba ɗaya ta koma a kan yaranta har sai data shiga tsakaninsa dasu ta kasar masa da hankali akansu tare da kokarin cire masa duk wata soyayya da yake yi masu, lokaci ɗaya suka koma abun tausayi saboda rashin kulawa da kuma banbancin da yake nunawa ƙarara tsakaninsu da sauran ƴan uwansu, a ɗaya ɓangaren itama Aunty amarya tunda ya aurota lokacin Hajiya Mariya nada cikin Jalil taga irin rawar jikin da yake yi da ita da yanda yake nan nan da ita sai kace itace amarya ba ita ba taji ta tsaneta, don kuwa gaba ɗaya bata gabansa baya da zance sai na Hajiya Mariya da cikin dake jikinta tamkar shine na farin, hakan yasa Ummah tayi nasarar shiga jikinta tayita ƙara cusa mata tsanar Hajiya Mariya da yaranta tana nuna mata cewa ai ta asirce Alhaji Asad ɗin ne bai ganin kowa sai ita, bata gasgata hakan ba sai da taga ta kwashe kusan shekara biyar da aurensa ko ɓatan wata batayi ba amma ko kaɗan abun bai dansa ba, nan da hankalinta ya tashi a lokacin Hajiya Zainabu ta sake haihur ƴar ta ta ta huɗu wato Jiddah, ita kuma Hajiya Mariya ta sake haihuwa ta haifi Afrah wacce sunan mahaifiyarsa ne ya saka mata wato khadija. JAMIL shine babban ɗanɗan Hajiya Zainabu, yanzu haka yayi aure kuma anan cikin gidan yake zaune a can ɗayan part ɗin dake gefe da yaransa biyu Nihla da Sameer, Sai Aunty Asiya itama tayi aure tana da yara uku, sai kuma Aunty Luba da aurenta shekara biyu yanzu, sannan auta Jiddah.
Aunty amarya kuwa bata haihu ba sai bayan rasuwar Hajiya Mariya mahaifiyar su Mutallab da shekara ɗaya ta haifo ɗanta yaci sunan Khalil, hakan yasa ta sake amanna cewa mahaifiyarsu Mutallab asiri take yi tunda gashi daga mutuwarta itama ta samu nata jinin kenan asirin ya karye, bayan shekara uku ta sake haifo ɗanta yaci sunan Walid, daga nan haihuwa ta tsaya don har yanzu ko ɓatan wata bata sake yi ba.
Wannan shine.
**********
Cike da rashin kunya da tsiwa take magana cikin ji da kai da kuma izza, sam babu alamun girmamawa ko kuma mutuntawa acikin kalamanta da take jefawa wacce ta zamo jigo kuma matsayin uwa a gurbin rayuwarsa. duk da bata haifeta ba ba kuma tasan wahalar ɗaukar cikinta ba ta amsa sunan uwa kuma nagartacciya agunta da ako yaushe ba tada wani buri sama da taga ta saita gobenta ta kuma bata kyakkyawar rayuwa, sai dai ita hakan baisa ta zama mai alkunya da kuma nuna karar amsa sunan ƴa a gina ba daidai dana second ɗaya shi yasa take iya kallon tsakiyar idanuwanta ta faɗa mata duk wata magana data fito daga bakinta komai ɗacinta kuma komai muninta don ita ɗin ƴar gata ce kuma ƴar gaban goshi ga mahaifin nata ALHAJI ABDULMALIK MU'AZZAM da ko ƙuda ya taɓa masa ita to tabbas da sai yaji ɗacinsa.
"Nan ɗin gidan ubana ne babu uban daya isa hanani nayi yanda nake so, su ɗin kuma ƙawayena ne suna da damar shigowa suyi duk abinda suke so, don haka kija jikin saboda ba kida iko a kaina, haka kuma ba kida hurumin sa mani iyaka a gidan ubana, ki barsu suci arziƙi suma kamar yanda kema kike ci bana son sa ido kin fahimta ko?"
"Meenal.." cikin tsawa matar mahaifin nata dake ƙoƙarin tausar zuciyarta akan munanan kalaman da yarinyar data rena da hannunta ke caɓa mata a gaban ƙawayenta da suka zo suka baje mata a tsakiyar falo suka ƙure volume na home theater suna kwasar rawa ihu da kuma shewa ta kira sunanta, wani kallo meenal ta jefa mata haɗe da juyawa tana cewa, "ƙawayena ku ƙara sauti kuyi yanda kuke so, nan ɗin gidan ubana ne babu mai hanamu". Tanayi tana kwasar rawa abinda, don kuwa indai kiɗa ne Meenal baza ta taɓa bashi kunya ba duk inda ta jishi sai takai jiki kuma sai ta taka balle ace acikin gidan ubanta ne kamar yanda take iƙirari.
Ran Momy a ɓace ta nufi wajen kayan kiɗan ta kashe sannan cikin kakkausar murya ta shiga ba ƙawayen Meenal ɗin umurni dasu tattara su fice mata daga gida kafin takira masu jami'an tsaro suyi mata gaba dasu, jin hakan yasa jiki na rawa suka shiga ɗibar jikunkunansu da takalmansu a hannu suka fice da sauri Meenal na faman kiransu amma ko saurararta basuyi ba, wata irin ƙara ta saki tare da ɗaukar abun ƙawar dake kan center table na glass tayi jifa dashi ta fashe da kuka, dai-dai lokacin motocin mahaifin nata suka kutso kai cikin farfajiyar katafaren gidan, suna yin parking sautin ƙarar data saka ya dira a kunnensa, kafin kace me tuni ya ɓalle marfin motar tun kafin guards ɗin da su buɗe masa kamar zai tashi sama ya nufi cikin gidan...
#Mutallab Asad Mutallab
#Tagwaye biyar
#Billy S Fari
#Nana Diso.