Free chapter · Read without an account

18

by Aishatu Abdullahi Idris · Sawun Giwa

*SAWUN GIWA*

_Ya take na Raƙumi_





_By_

*Aishatu Abdullahi Idris*

_REAL ESHAA_


_Ayyah am masu nema daga farko dan Allah kuje Wattpad ko Arewabooks zaku samu acan_🙏🏻🙏🏻



*F-R-PG 18*

Amsawa Dattijon dake sanye cikin babbar gariya da rawani yayi kana wuyansa sanye da ƙaton Carbi yayin da yake zaune akan wani baƙin buzu gabansa kuwa wani ƙaramin farantine dake ɗauke da ƙasa sai wasu ƙwarya biyu dake gefen hagu da damansa wanda suke ɗauke da ƙullin magunguna.

Cikin alamun gajiya da tarin damuwa Lateefa ta kallesa tare da cewa

“Allah gafarta Malam ba komai ke tafe dani ba sai”...

Cikin sauri ya ɗaga mata hannu alamar tayi shiru kana ya dauƙo wani ƙaton Carbi yace.

“Ki zaɓi ɗaya anan”.

 Hannunta na rawa ta zaɓi ɗaya murmushi yayi tare da ɗauko wani ƙaramin farantin silver dake ɗauke da ƙasa yayi wasu zane-zane akai tsawon minti goma sha biyar.

Kallon Lateefa data tsira masa idanun yayi kana yace.

“Ba wata matsala kike tafe dashi ba face akan mijinki”.

Cikin sauri ta gyaɗa masa kai.

Wasu zane-zane ya karayi na minti biyu kafin yayi saurin dafe kansa kana atake idanunsa suka kaɗa sukayi jawur cikin haki tamkar wanda yayi gudu yace.

“Mijinki zaiyi Aure nan da kwana biyu sannan kina so atarwatsa Auren tare da cire masa sha'awar ko wacce mace?”.

Kai fa gyaɗa tare da cewa.

“Tabbas hakane,Dan Allah Malam ka taimaka min kada ayi Auren.Wallahi muddin akayi Auren nan mutuwa zanyi bazan iya juran zama da kishiya ba Ina son mijina bazan iya haɗa wata dashi ba”.

Meenah ce ta karɓe da cewa.

“Kuma Wlh Malam mijinta na masifar sonta kawai sharrin Uwar mijine da ƴan uwansa suke son ganin ya ƙara Aure saboda ya wulaƙantata!”.


Wani rubuce-rubuce ya sake yi kafin ya ɗago kai ya kallesu cikin rashin walwala da zufa dake keto masa yace.

“Tabbas wannan auren sai anyi domin akwai rabo mai karfi idan kuma kuka matsa akan dole sai an fasa zaku iya mutuwa dukan ku”.

Atsorace suka zare idanu cikin rawan baki da tarin tsoro Meenah tace.

“Mutuwa?,Caɓ ɗijam in dai hakane kuwa to wallahi Malam ban shirya masa ba,Ba ƙira babu abinda zai ci gawayi Allah ya sanya Alkhairi”.

Zazzafan ajiyar zuciya Lateefa ta sauƙe cikin tsananin tashin hankali da kaɗuwa gami da ruɗu tace.

“Toh yanzu meye abinyi Malam?”.

Kai ya gyaɗa tare da sake yin wasu rubuce-rubuce na tsawon wasu mintuna kana ya kalli Lateefa tare da cewa.

“Shawarar da zan baku ku bari ayi Auren idan yaso daga baya sai mu san abinyi domin ganin an lalata tsakaninsu amma ayanzu babu wani abu da zan iya yi kuma duk wanda kukaje wajensa sai dai ya cinye muku kuɗi amma baza ku samu biyan buƙata ba”.


Kai suka gyaɗa tare da miƙewa Meenah ce ta iya yi masa godiya Lateefa kuwa wasu hawaye ne masu masifar ɗumi suka wanke mata kuncinta jin cewa tabbas sai anyi Auren wani irin tsanar Indu da Ummu ce ke sake nun kuwa azuciyarta tabbasa sai ta tarwatsa musu farin ciki da jin daɗi kamar yanda suka tarwatsa mata nata ahaka ta dawo gida nan ta tarar da da set ɗin akwati huɗu ko wanne ashake da kaya na faɗar kishiya sam ko kaɗan wannan bai burgeta ba hasalima wani irin takaici ne ya mamaye ta.


**

Ranan Laraba Zonbi suka gabatar da Bridal Shower Alhamis akayi Ƙauyawa da kuma Arabi'an night ranan juma'a da safe aka gabatar da walima ana sauƙowa daga Juma'a sallar aka ɗaura Aure.

Tsananin tashin hankali da damuwar da Lateefa tashiga asanda taji an ɗaura Aure ba zai misaltuba sosai taci kuka ta godewa Allah kafin daga bisani Meenah da sauran ƙawayenta suka rarrasheta tare da yimata huɗu bar banza.

Misalin ƙarfe huɗu da kwata aka kawo Amarya Zonbi gidan Mijjnta inda kai tsaye aka wuceta da ita wajen Ummu sosai Ummu tayi mata nasiyya ita da Lateefa mai ratsa jiki.


Bayan nan aka ɗauke ta aka kaita ɗakin Lateefa da ƙawayenta sukayi mata buɗar kai kamar yanda al'adan garin yake cikin alamun rashin nuna damuwa Lateefa ta riƙa jan Zonbi ajiki ana musu hotuna duk inda zata yi hannun Zonbi na cikin nata yayin da mutanen wajen ke sanya mata albarka da kuma yabon kyawun halinta da rashin kishinta yayin da wa'anda suka san halayyar ta suke tausayawa Zonbi Manyan Speaker aka kunna tare dasa ka waƙar  Lateefa taja hannun Zonbi cikin fili yayin da ake musu liƙi sosai Lateefa ke tiƙar rawa tamkar Auren kanwarta akeyi ganin haka yasa Zonbi sakin jin jikinta cikin jin daɗin yanda Lateefa ta saƙƙo...


Ahankali Zonbi ta juya bayanta jin an dafa kafaɗarta idanunta ne suka sauka akan Meenah murmushi Meenah ta sakar mata tare da faɗin.

“Amarya kin gaji acikin fili ga Madara mai sanyi kisha”.

Kai Zonbi ta gyaɗa tare da amsa tace.

“Nagode”.

Kana ta kafa bakinta akai dai-dai lokacin kuma Matar Babanta mai Suna Aunty Maimunatu fito daga Falon Zonbi Idanunta suna sauka akan Zonbi dake riƙe da Cup a hanunnta tana ƙoƙarin kaiwa bakinta cikin sauri ta wafce tare da faɗin.

“Ina kika samu wannan abin?”.

Idanunta alumshe tace.

“Aunty Meenah ce Ƙawar Aunty Lateefa ta bani”.


Cike da ɓacin rai Aunty Maimunatu tace.

“Zonbi ashe baki da hankali ban sani ba akan me ƙawar kishiya zata baki wani madara ki amsa kisha?”.

Dai-dai lokacin Indu dake sanye cikin shiga na alfarma ta ƙaraso wajen sosai tayi kyau cikin danƙareren less din da sukayi Anko da Zonbi.

Cike da kulawa tace.

“Aunty Maimunatu meke faruwa”.

Cike da ɓacin rai Aunty Maimunatu tace.

“Ina kuwa lafiya Saboda gidadanci da rashin hankali irin na Zonbi wancan Ƙawar Kishiyar tata takawo mata Madara wai ta amsa tasha!”.


Ganin yanda Aunty Maimunatu ke ɗaga murya baki ɗaya ta tashi hankalin ta yasa Indu cewa.

“Laaaa bakomai ai Aunty dan akwai madaran da yawa a Fridge hala aciki ta ɗebo mata”.

Ƙwaffa kawai Aunty Maimunatu tayi tare da barin wajen.


Misalin tara na dare duk kowa ya watse ya rage saura su kaɗai agidan ko wacce na ɗakinta.

Imraan yashigo tare da Dr Khameel daya rakosa direct ɗakin Lateefa ya wuce Dr Khameel kuma ya zauna falon yana latsa wayarsa.

Lateefa na ganinsa tayi saurin miƙewa tare da faɗin.

“Ba sai ka zauna ba muje kawai lokaci ya ƙure".

Murmushi yayi kana ya langwaɓar da kansa tare marairaice murya yace.

“Yau kuma ni ake kora Ƴan nata?”.

Ji tayi kamar ta kwaɗa masa mari amma sai ta daure tare da sakar masa da murmushi kana tace.

“Ai ban isa korin kaba Sojana kawai dai na barwa ƙanwata lokacin tane itama ta nishaɗantu da wannan dare mai cike da tarihi”.

Sajensa ya shafa tare da sassauta murya kana yace.

“Bayan kin gama da komai”.

Sarai ta jisa Amma sai tashare juyawa yayi ya fita yayin da take biye dashi.

Ganinsu tare yasa Dr Khameel cewa.

“Uwar gida Sarautar mata Uwar gida ran gida Uwar gida Shalelen Mata”.

Cikin ranta tace.

“Allah dai ya tsinewa munafuki algungumi".

afili kuwa cewa.

“Tayi godiya nake Dr ”.

Kana suka shiga ɗakin Zonbi bayan sun gaisa da Dr Khameel.

Lateefa na gaba,Sai Imraan yayin da Dr Khameel ke biye biye da su.

Zaune atsakiyar gado suka sameta cikin wata bugaggiyar Shadda Pinc da aka yi masa ado da coffe yayin da gyalenta ma yakasance coffee ga kuma kishinta sosai tayi kyau sai wani fitinennen ƙamshi ke tashi ajikinta wanda yasa zuciyar Lateefa tsayawa na wucen gadi.


Zama gefenta na dama Imraan yayi yayin da Dr Khameel ya zauna akan stool Lateefa kuma ta zauna gefenta na hagu ya zama sun sata tsakiya Dr Khameel ne ya buɗe taron da addu'a.

Kana yace.

“Lateefa ga Zonbi ƙanwace agareki ki riƙe ta da amana domin aduk inda kika ɗaura ta ahaka zata kasance kiyi ƙoƙari ki tarbiyyantar da ita ta hanyar daza kiji daɗin zama da ita.


Sai da ta jefa masa kallon tsana ta kasan ido kafin tace.

“In sha Allahu zan riƙe ta da amana da gaskiya”.

Kallon Zonbi dake shesh-sheƙan kuka yayi kana cigaba da faɗin.

“Zonbi ki ɗauki Lateefa tamkar Yayarki duk da cewa tun da ma matsayin Yaya take agareki so a yanzu ma ki riƙe ta da amana sannan ki riƙe ƴaƴan ta hannu bibbiyu domin kema ƴaƴan ki ne koda kuwa ba Aure tsakanin da Captain”.

Kai ta gyaɗa cikin Muryan kuka tace.

“In sha Allahu zaku sameni fiye da haka”.

Sosai ya sake yi musu nasiyya mai ratsa jiki daga nan yayi sallama ya fita Lateefa ma ta wuce ɗakinta ya rage daga ango sai Amarya matsawo kusa da ita yayi ya shiga share mata hawaye daga nan labari ya canza launi...


Fitowar Dr Khameel yayi dai-dai da fitowar Indu dake sanye da dogon hijabi har ƙasa kallonta yayi kana ya duba agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa da mamaki atare da shi ya matsa daf da ita tare da faɗin.

“Autah Ina zaki?”.

Cikin sanyi murya da damuwa tace.

“So nake naje gidansu Neenah rabona da ita tun ana gobe za'a kwantar da Ummu a asibiti kusan sati Uku kenan”.

Kai ya jinjina tare da cewa.

“Toh meyesa bakije tun rana ba sai yanzu?”.

Muryarta na rawa tace.

“Koda naje gidan bana samun kallonta Mamanta kori na take sannan na faɗawa Gate Man idan ya ga zata je School yazo ya faɗa min shima still yace wai baya ganinta Yah Khameel am so Confused”.


Numfashi ya fesar kana yace.

“Ok yanzu idan kinje kina da tabbacin zaki ganta?”.

Kai ta girgiza still muryarta araunane tace.

“I don't know but I will try”.

Tafin hannunta ya riƙe tare da cewa.

“Ok muje In raka ki”.

Kai ta gyaɗa kana suka tafi da kafa suka taka har ƙofar gidan hannunsa na sanye cikin nata Duk da bata so hakan ba.


Suna zuwa ƙofar gidan ta janye hannunta daga cikin nasa tare da tsirawa ƙofar gidan idanu.

Da mamaki yake kallon gidan kafin yace.

“Nan ne gidan?”.

Kai ta gyaɗa ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.

“Ok ki shiga ki fito am waiting you”.


  Cikin Muryan kuka tace.

“Am so scared Mamanta tace idan ta sake kallona saita karya min ƙafana saboda yawon banza muke zuwa muna bin maza”.

Rai aɓace ya kallete tare da faɗin.

“Ok tunda ta faɗa miki haka why not ki fita sabgar ƴarta”.

Kai ta girgiza masa cikin sauri ta furta.

“I can't Yah Khameel she's my best friend my secret she's means alot to me itace Aminiyata da nake baka labari ko yaushe”.

Kamar zai ce wani abu sai kuma ya fasa tare da nuna mata ƙofar gidan alamar ta shiga.


Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da tura jememmen ƙauren da aka laƙanya cikin Sa'a ya buɗe tare da ƙara ƙiiiiyyyyy...Atsorace ta leƙa sauron gidan da duhu ya mamaye babu alamar haske sai wata baƙar kuliya data zuba mata idanu cikin sauri ta juya tare da fita da gudu kallon Dr Khameel daya tsira mata idu tayi cikin ƙasa da murya tace.

“Yah Khameel babu haske fa ga wata baƙar kuliya awajen sai kallona take”.

Dariya ce taso kamashi jin yanda tayi maganar amma sai ya masge tare da sanya hannunsa acikin aljihu ya ciro ƙaramar wayarsa ƙiran Nokia ya Mika mata amsa tayi tare da shiga cikin gidan da babu kowa sai iska dake faman kaɗawa kai tsaye ɗakin dake mallaki Neenah da Maryam ta nufa kana ta tura ƙofar cikin Sa'a ya buɗe.


Cikin ƙasa da murya tayi sallama tare da haske cikin ɗakin da sauri Neenah da kanta ke du ƙunƙune cikin Hijabinta ta ɗago.

Zare ido Indu tayi kafin cikin tsananin tashin hankali ta durƙusa agabanta muryanta na rawa tace.

“Blue eyes meyesa mi idanunki suka kumbura sukayi jaa”.

Faɗa wa jikinta Neenah tayi ta saki Marayan kuka mai tsuma zuciya.

Kasa daure wa Indu tayi itama sai hawaye da ƙyar Indu ta iya tsaida hawayen ta tashiga sharewa Neenah nata kafin tace.

“Dan Allah Blue eyes ki daure ki sanar dani abin ke faruwa dake ko zan samu natsuwa dubi yanda baki ɗaya kika fita hayyacinki acikin kwanaki ashirin da ɗaya”.


Murmushin daya fi kuka ciwo tayi kana ta gyara zamanta tare da faɗin.

“Indu nasan cewa nayi sallama da farin cikin,Farin cikina yazo ƙarshe rayuwata ta gama salwanta nida rayuwar farin ciki har abada domin ana neman tarwatsa min rayuwata ko da yake rayuwata ta gama tarwatsewa!meya ragemin duk abinda ɗiya mace mai mutunci take alfahari dashi Ni ba rasa”.

Cikin sauri Indu ta girgiza mata kai kana tace.

“Kada Kice haka ko so kike kiyi saɓu?,Dan Allah ki share hawayen ki sannan ki sanar dani abinda ke damunki jikina na bani kina cikin damuwa”.

Zazzafar ajiyar zuciya ta sauƙe tare da riƙe hannunta kana ta shiga zayyane mata duk abinda ya faru har zamanta agidan su Sir Abdallah da irin tainakon da ya bata,maganar fitar ta karatu Izayar da Mamawo ke mata sai dai ta ɓoye mata Abinda Malam Sa'idu ya mata kamar yanda Sir Abdallah ya buƙata.

Ta ɗaura da cewa.

“Baba ya hanani fita koda nan da ƙofar gida sannan sau ɗaya Mamawo ke bani abinci sai dai Maryama ta faki idonta ta kawo min data gane ta bani abincin shine ta hanata kwana aɗakin baki ɗaya Baba ya canza min kuma zasu Aura min Malam Sa'idu dan har an kawo sadaki nan da Sati ɗaya za aɗaura Auren”.

Kallon ta Indu keyi cike da tsananin tashin hankali yayin da hawayen tausayinta ke kwaranya daga idanunta

Cikin shesh'sheƙan kuka ta cigaba da cewa.

“Ko da na second ɗaya ne Baba baya buƙatar kallona kuma yaƙi bani damar wanke kaina babu abinda yafi ɗaga min hankali kamar hanani zuwa makaranta da yayi sannan duk zuwanki ina ji sai dai bani da halin fita Indu taya kike tunanin zan iya rayuwar Aure da mutumin daya ruguza min rayuwata! duk wani abu daya sameni arayuwar nan Malam Sa'idu shine sanadi”.


Cikin zubda hawaye Indu tace.

“Kiyi haƙuri tabbas Kinga jarrabawar rayuwa amma ki kwantar da hankali zan faɗawa Yah Imraan halin da kike ciki kuma nasan zai fahimtar da Baba bazai bari ayi wannan auren ba”.

Murmushin Neenah tayi tana jin sassauci ahankali tace.

“Ina so in haɗu da Yah Imraan nayi missing ɗinsa”.

Ta ƙare maganar tana lumshe idanunta.

Murmushi Indu tayi kana tace.

“Iyeeeee wato wariya zaki nuna min ni bakiyi missing ɗina ba sai shi?kodai?,Kodai?”.

Ɗan hararanta Neenah tayi sai kuma tayar murmushi cike da so ta rungume kana tace

“Kodai me?,Aike wata sashe ne na rayuwata,Kafin zuwanki na fidda rai da sake rayuwar farin ciki amma yanzu naji ƙarfin gwiwa, sannan akwai wata magana mai muhimmanci da zan sanar miki”.

Ɗan ware idanu Neenah tayi tana mai jin tausayin Aminiyarta tabbas ya zama dole ta faɗawa Imraan ya ɗauki mataki Neenah ta buɗe baki da niyyar magana ta fasa ciki tashin hankali ta zare idsnunta jin Mamawo na cewa. 


_“La ha'ila ha'illlahu Muhammad Rasulullahi (S.A.W),_ Mai zan gani haka Ni Saude ƴan Maɗigo acikin gidana Malam zo kaga kwartaye”.

Atsorace Neenah ta janye jikinta daga na Indu jin furucin Mamawo cikin tsananin tsoro take zazzare ido.

Wani banzan kallo Indu ta watsa mata cike da rashin walwala tace.

“Ban fahimci me kike nufi ba Malama ƙazafi kike son yi mana!?”.


Zare Ido Mamawo tayi cikin hargagi da tsawa tace.

“Kutmar Ubanki nake nufi shegiya Karuwa ƴar maɗigo tsinanniya Watanin mai siffar Agwagwi”.

Sai kuma tayi saurin fashewa da kuka jin motsin Baba na ƙoƙarin shiga tace.

“Watanin ni kike cewa tsohuwar banza da ƙafa kamar Lauje Hindatu saboda na faɗa miki gaskiya akan abinda kuke aikatawa haramunne”.

Sheƙeƙe Indu ke kallonta cike da mamakin furucinta da kuma sharrin da take ƙoƙarin yi musu Neenah kuwa lumshe idanunta tayi cikin sallamawa rayuwar farin ciki ta Runtse idanunta.


Cikin tsananin fushi Baba ya kalli Indu hannunsa rike da Inji Belt daya saba dukan Neenah dashi afusace ya buɗe baki tare da faɗin.

“Fito ki barmin gida lalacacciya daga yau na yanke duk wata alaƙa dake tsakanin ki da Neenah ashe dama lalatar da kuke aikata wa kenan yasa ko yaushe kuke na niƙe da juna yau kam na sake tabbar da abinda Saude ke faɗa min akan Neenah babu yanda za'a yi kina yarinyar kirki ki fito adaren nan wato dana hanata fita shine ke kika biyo sawunta ko?”.

Cikin raunin murya Indu ta buɗe baki da niyyar magana Afusace ya dakatar da ita tare da faɗin.

“Fito ki ficemin agida kafin na lahanta ki lalacacciyar yarinya badan kinci darajar yayanki ba ai saina miki shegen duka”.

Cikin tsananin mamakin sauyin Baba Indu ta miƙe tare da ficewa da gudu tana wani irin kuka mai gunji karo suka buga da Dr Khameel dake niyyar shiga jin hayaniya.


Riƙe ta yayi ajikinsa tare da cewa.

“Mai ya faru? Autah yana ganki arazane me suka miki??”.

Kasa bashi amsa tayi sai hawaye dake kwaranya daga idanunta yayin da baki ɗaya ilahirin jikinta ke rawa.

Da ƙyar Dr Khameel ya iya rarrashinta tare da janta ta wuce gida tana shiga bedroom ɗin ta ta faɗa kan gado tare da fashewa da wani irin kuka mai gunji bakwai ƙazafin da Manawo tayi musu bane yasa ta kuka sai tunanin halin da Neenah zata kasance.


Aɓangaren Neenah kuwa Indu na fita Baba ya ɗaga Injin Belt ɗin hannunsa ya riƙa dukanta dashi dukanta kawai yake batare daya san inda yake zubawa ba kana yana cewa.

“Allah wadaranki Neenah da haihuwar ki gwara ɓarinki lalacacciya Allah yasa ki mutu in huta Allah ya haɗaki da masifa da bala'i da zai lalata Miki rayuwa!”

Wani irin kuka mai gunji Neenah keyi sam ba zafin dukan bane yake sata kuma kamar zafin kalamansa yafi dukan da yake mata raɗaɗi.

Maryam da ihun Neenah ya tada ita da dugu ta fito tare da durƙusawa akan gwiwoyinta cikin raunin murya tace.

“Dan Allah Baba ka ƙyaleta kada kayi mata lahani meyesa kuke azabar da rayuwar ta ne? mufa ƴaƴanku ne kuma amanar ku meyesa kuke son wofantar da amanar da Allah ya baku har kayi mana baki”.

Wurgi yayi da bulalar kana yace.

“Allah yayi wadaranki Neenah wlh na tsaneki gwara ɓarinki da haihuwarki nayi dana sanin kasancewar ki ƴata nayi dana sani dana bari kin mutu awulaƙance karnuka su cinye gawarki”.

Ya kalli Maryam dake kuka tamkar ranta zai fita kana yace.

“Maryama kada ki sake alaƙanta kanki da wannan ballagazar domin ke mai daraja ce”.

Cikin rauni Neenah ta ɗago rinannun idanunta da suka kumbura ta kallesa zuciyar ta kamar zai fashe kana tace.

“Dan Allah Baba duk hukuncin da zaka min kayi min amma kada kayi min mugun baki mummunan furucinka agareni masiface”

Harbi ya kai mata da ƙafa kana yace.

“Dan Ubanki Gobe gobe zan Aurar dake na fasa bari satin Sam bazan bari ki jamin abin kunya ba gwara na sadakar dake”.

Ya ida maganar tare da ficewa yayin da Mamawo tabi bayansa ranta fesss burinta zai cika adaren Baba ya kira Malam Sa'idu ya sanar masa ya bashi Neenah kuma ya kwana da sanin gobe da safe za aɗaura Auren....


   Yanda Neenah taga dare haka taga rana idanunta sun Kumbura sunyi luhu² dasu yayin da fuskarta tayi fayau ramar ta ya sake fitowa.

Afirgice ta ɗago kanta jin sauƙan Abu da kallo tabi Baccon cikin tsawa Mamawo tace.

“Dan Ubanki ki daina kallona da wannan munafukan idanun naki masu kama dana Mayyar kuliya maza ki buɗe ki duba kayan Aurenki ne aciki”.


Kasa furta komai tayi haka zalika ta kasa janye idanunta daga kan Mamawo.

Afusace Mamawo tasa ƙafa ta hamɓareta kana tace.

“Da zaki kafeni da munafukan idanunki shin darajar ki ya kai ki samu wannan ɗin ne?,badan zuciyar musulunci da tausayi ba!?,Maza ki buɗe su”.

Shiru Neenah tayi tare da sanya hannu ta janyo Bakkon ta buɗe turmin Matsone guda biyu(Atamfa robber)sai Shadda Ishirunka Maraya guda ɗaya da hijabi ɗaya gyale ɗaya Pant biyu Brazia biyu Under wear ɗaya sarƙa ɗaya da kuma takalmin robber biyu.

Wasu zafafan hawayene suka zubo mata cikin dashash-shiyar muryarta tace.

“Nagode Allah ya saka da Alkhairi”.

Tsaki tayi tare da ficewa ganin fitar ta yasa Maryam dake rakuɓe tayi saurin shigowa ɗakin da sauri ta ɗauko leda tare da buɗe Ghana masgo Neenah ta zuba mata kayanta cikin ƙasa da murya tace.

“Sister Neenah ki fito ki gudu kada ki bari su lalata miki rayuwa ga wannan kuɗin dubu ɗaya ne ba yawa ki riƙe hannunki lokacin da Baba ya saƙƙo sai ki dawo”.

Kallon Maryam tayi da rinannun idanunta tace.

“Ina zanje Sister Maryama bani da wani waje da zan je ya wuce wannan gidan Allah ne gata na Baba shine gatana bansan su waye dangin Mahaifiyata bare inje wajen su hala zalika bansan su waye dangin mahaifinmu ba bare suka womin ɗauki zan zauna in rungumi ƙaddara ayanda tazo min ”.

Kai Maryam ta girgiza kana tace.

“No Sister Neenah kada kice haka maza ki shirya ki tafi koda gidan ɗaya daga cikin ƙawayenki ne kada ki bari a ɗaura wannan Auren domin Mamawo so suke su ruguza miki rayuwa nikam bazan iya juran haka ba”.

Wani bahagon mari Maryam taji agadon bayanta wanda yasa ta dungurawa ƙasa aruɗe ta ɗago kanta.

Cikin fushi Malam Sa'idu ya nuna mata hanya tare da cewa.

“Fita baƙar munafuka ko mutuwa tayi sai an ɗaura Auren da gawarta babu wanda ya isa ya hanani cikon burina shegiya da baƙin fuska kamar ta kare”...

Miƙewa Maryam tayi tare da ficewa zuciyarta tamkar ya fashe Neenah kuwa cikin sauri ta runtse idanunta domin tamkar dodo haka take kallonsa bata ƙaunar ganin fuskarsa lokaci ɗaya jikinta yashiga rawan

Kallonta yayi tare da faɗin.

“Keeee kuma na dawo gareki ki sani bana sonki bana ƙaunarki Hasalima babu wacce na tsana duk duniya saboda kee zan aureki ne saboda gyara duniyata domin taurarin ki sun kasance masu karfi da haske ina Aurenki zasu haskaka min nawa tare da dishashar da naki”.

Ya ida maganar tare da ficewa lumshe idanun tayi kafin ta buɗe su ta

Kalli agogon dake manne ajikin bango wanda duk ya babure wanda kuma ke nuni da saura minti 15 aɗaura musu Aure da Malam Sa'idu cikin gajiya wa da rayuwar ta ɗaga hannunta sama cikin matsanancin kuka da ƙuncin zuciya tace.

“Ya Allah ka ɗauki rayuwata in huta gwara min mutuwa da wannan baƙar rayuwar”...


*My dear Fan's Free page ya kusa ƙarewa ku hanzarta wajen biya domin mu kai Limit da ake buƙata mu samu mu kutsa cikin labarin gadan-gadan*


_Sawun Giwa na kuɗine 500 hundred zaku tura ta wannan account number 6030406548 Abdullahi Idris Aishatu keystone bank ko kuma katin Mtn ta wannan number *** tare da tura shedar biya ta wannan number ***._


_Ya Allah Ubangji kajiƙan mahaifina ya Allah kagafar ta masa zunubansa ya Allah ka kai haske kabarinsa ya Allah kijakan duk kan musulman da suka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mucika da Imani..._


*@Follow me on Arewabooks realeshaa*


*@Follow me on Wattpad realeshaa*



  _Ayi shearing saboda Allah ƴan Uwa Masoya da abokan arziƙi_


*👭GARKUWAR MATA👭*

*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka  kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*

*GA*

*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*

Rage tumbi💯

Nono💯

Sanyi💯

Karin kiba💯

girmar hips💯

Ni'ima💯

Sabulai💯 

Humra💯

Turarukan wuta💯

Matsi💯

Miski💯

Dilka💯

Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki

GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI

***

***


       *ESHAA CE*🤙🏻

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.