Free chapter · Read without an account

004

by Jeeddah Aliyu · KURMAN ALLO

*KURMAN ALLO*

(A beautiful Love story)


NA

JEEDDAH ALIYU

&

ASMY B ALIYU


#Love story

#Gwagwarmaya

#team tagwaye novels


004.


Wuraren sha biyu na rana Mami ta kalli su Siyama tace su tashi su wuce gida ta juya kan AB da Aydah ke gwadawa wani abu a wayarsa sai murmushi ya keyi "Abba me za a haɗo maka na lunch?" Ya rausayar da kai yana faɗin "mami komai ma kika yi zanci. murmushi jin daɗi mami tayi ganin yadda ya sake lokaci ɗaya. "Yayanmu dan Allah ka faɗawa Mami ta barni a wurinka.

Aydah ta faɗa murya kasa-kasa ta yadda Mami, ba zata ji ba shima murya can ciki yake faɗin."kuje tare dai nasan damuna za kiyi da surutu kuma anjima akwai islamiyya tunda ba ki samu zuwa ta safe ba."lokaci ɗaya Aydah ta wani haɗe rai ta yi folding hands ɗinta akan ƙirjinta shi dai murmushi kawai ya yi yana ɗauke kansa tunda ya yi haka tasan ya gama magana kuma ba zai ƙara fadar komai ba. Baki buɗe Mami ke kallonta tana faɗin."ko adaidaita za ki nema muyi tafiyar mu? Ta ɗan kalli gefen AB ganin ya ma rufe idanuwansa tamkar zata yiwa Mami kuka cikin sanyin murya take faɗin."Dan Allah Mami ki barni anan tare dashi sai ku tafi da Siyama.

Da sauri Siyama tace "Nima mami zan zauna nasan abunda take yiwa gudu dan kar a shiga kitchen tare da ita.

"Yaushe na faɗa miki haka yayanmu ka yiwa yaya Siyama magana ta daina sakamin ido a lamurranna ta daina bana so.

A hankali Abba ya buɗe idanuwansa yana kallonsu kafin ya kalli Aydah yana faɗin."Tashi ku tafi bana son rigima. Ai yana faɗar haka ta miƙe ta nufi kofa a mugun fusace. daman Mami ta daɗe da fita ganin ta fita yasa Siyama ta juya tana yiwa yaya Abba, sai anjima daman wani kallo yayi mata wanda ta riga tasan meyake nufi ganin Mami ta nufi gidan yaya Abba, da mota yasa siyama dake zaune a front seat faɗin."Mami yaya Sadiya zamu dauko ne?" shiru Mami ta yiwa Siyama ko magana bata son yi

har suka iso ƙofar gidan Ab mami bata furta uffan ba.

A bakin get tayi parking ta kalli Siyama tana faɗin."taje ta shiga ta kira mata Sadiya kai tsaye Siyama ta fice daga motar a bakin get ta tsaya tana knocking ta ƙaramar kofa a tsorace maigadi ke faɗin."wanene dan har lokacin daren jiya bai daina gilma masa cikin idanunsa yadda aka dauki mai gidansa rai a hannun Allah kwana yayi yana zagayawa a banɗaki ya tsinewa Sadiya Kwando-kwando a wannan daren. Ya buɗe ƙofar yana kallon Siyama wanda duk a tsorace yake haushi sosai Siyama taji tamkar bai ganeta ba "malam Barau ka buɗemin ƙofa mana.

"Babu fa kowa a gidan Hajiya. Da mamaki siyama ke faɗin."matar gidan nake maka magana.

"Ai matar gidan tun jiya da ta cakawa maigidan nan wuƙa aciki bata kwana gidan nan ba.

Wani irin bugawa ƙirjin Siyama ya shiga yi jin kalaman Barau maigadi wato kenan sanadin yaya Sadiya yaya Abba ya kwanta gadon asibiti, yadda Mami taga Siyama ta nufo su babu wata natsuwa a tattare da ita yasa ta tsaya tana kallonta shiga kawai ta yi cikin motar har hawaye sun cika mata idanuwa cikin rawar murya ta ce."Mami ashe dama yaya Sadiya ita ce silar kwanciyar yaya Abba,a gadon asibiti ?

Siyama ta ƙarasa maganar cikin rawar murya batare da Mami ta bata amsar tambayarta ba take faɗin ya akayi kika tsaya wajen maigadi ba ki shiga cikin gidan ba? Anan Siyama tasake faɗawa Mami, abunda taji abakin maigadi na cewa yaya Sadiya bata kwana a gida ba kai tsaye Mami ta yiwa motar key batare da ta ƙara bin takan Aydah da Siyama ba dake mai da zance cike da mamakin yar uwar tasu.

Wanda ko a mafarki ko a gaske basu taɓa tunanin zata aikatawa yayansu haka ba. Har suka isa gida jikin Mami sanyayye maigadi ta fara tambaya ko Sadiya tazo gida ?"anan ya tabbatar mata da tazo sai dai kuma bata jima ba motar police tazo ta tafi da ita wani irin tashin hankali Mami taji ya cika zuciyarta still tana kallon motar Daddy, da har lokacin tana cikin compound cike da ƙarfin hali Mami ta sake kallon maigadi tana tambayarsa Alhaji yana nan lokaci da aka tafi da Sadiya? Ya tabbatar mata da yana nan. kai tsaye Mami cikin gidan ta nufa lokaci ɗaya jikinta yayi mugun sanyi tasan Daddy ,da zuciya idan aka bata masa rai babu wanda ya isa ya tankwasa shi ko kaɗan hukuncin da Daddy ,ya ɗauka bai yi ba duk da tasan Sadiya bata kyauta ba tana bukatar a hukunta ta Amma bata hanyar kaita jail ba, tunda ma an samu abun yazo da sauki ta kalli su Siyama da har lokacin jikinsu ke a sanyayye tana faɗin."su fara yin breakfast sai su tashi su riƙawa su Huwaila girkin rana. Daman mutanen gidan indai ranakkun weekend ne basu cikayin breakfast da wuri ba sai idan sun san suna zuwa islamiyyar safe. Wacce ba kullum suke zuwan ta safe ba sunfi zuwa da yamma, ta samu Daddy a katafaren parlornsa yayi wanka still yana sanye da jallabiyya ajikinsa yayi nisa cikin tunanin da yake Mami ta shigo dauke da sallama a bakinta ya amsa sallamar batare da ya kalleta ba. zama tayi a gefensa Mami ta rasa ta inda zata yiwa Daddy zancen Sadiya cike da ƙarfin hali Mami tace "Alhaji Amma kamar hukuncin da ka daukarwa Sadiya sai nake ganin kamar baiyi ba kar ayi ta yawo damu a gari.

Wani kallo Daddy yayi mata

A matuƙar harzuƙe yake faɗin."Ita abunda tayi ta kyauta? Sadiya ƙaramar Yarinya ce ko me?"shekarar Sadiya 25 a duniya shine kike kiranta ƙaramar Yarinya?"ki daina batamin rai dan Allah. Idan kin san ba magana mai muhimmanci zaki faɗa ba ki tashi ki fita ki barni da damuwar da nake aciki. Ran Mami ya gama ɓaci akan hukuncin da Daddy ,ya dauka tasan tana ƙaunar Abba, fiye da 'ya'yan da ta haifa da cikinta ita kanta bata ji daɗin yadda Daddy, ya yanke hukunci haɗa yaran nata aure ba.  musamman Sadiya da tayi gadon kafiya a wajen mahaifinta. kai tsaye Mami parlorn tabari ta wuce ɗakinta sai kai da kawo take a tsakiyar ɗakinta da gaske daddy yana ƙoƙarin jawo masu abunda ba zai iya gyarawa anan gaba ba,duk wanda yaji yadda Sadiya tayi a daren aurenta ba zai yarda ya aureta ba ko kaɗan bata so maganar nan ta kai wurin yan sanda ba. Tafiso su da suka bata komai su warware komai, mutum na farko da ya faɗo mata a wannan lokacin shine Abba, Amma kuma da kunya ta kira Abba ta shaida masa Daddy ya miƙa sadiya a hannun hukuma mutum na ƙarshe da yazo mata wannan lokacin shine Abdulkarim za tayi magana dashi su tattauna da Abban, ko za a iya samun mafita da sallama Abdulkarim ya daga kiran Mami, ya gaisheta ta amsa shiru ya ɗan biyo na wani lokaci kafin Mami ta soma yiwa Abdulkarim bayani abunda ke faruwa, shima Abdul ɗin shiru yayi yana ta nazarin maganganun Mami kafin yace mata Abba yanzu ya samu bacci idan ya tashi zasu tattauna godiya Mami tayi masa gamida sauke wayar. Wannan ƙaron driver Mami ta haɗa da Siyama da kuma Aydah su suka je asibiti kaiwa Ab abincin rana suma basu jima ba Ab ya uzura musu akan su kira driver ya mayar dasu gida lokacin islamiyya ya kusa shiru Aydah tayi tare da bata rai sosai da alamar ko kaɗan zancen bai mata daɗi ba tasan haka yayan nasu yake ko kaɗan baya son ayi fashin islamiyya ko biki suke basa fashin zuwa islamiyya. Bayan isowar driver Siyama kawai ce ta yiwa Ab sallama daman Aydah tafiyarta tayi ko kallon gefen da yake bata sake yi ba yasan fushi tayi bayan tafiyarsu Abdulkarim dake zaune akan soofa din dake girke acikin ɗakin kallon AB yayi da ya rufe idanunsa ɗan gyaran murya ya yi da yasa AB buɗe manyan fararen idanuwansa yana kallon Abdulkarim "da tun farko wannan yarinyar Siyama ya aura maka ba wannan shashashar mahaukaciyar yarinyar

Wani kallo AB ya riƙa yi masa,murya a shaƙe yake faɗin."ka manta cewa Siyama tana da wanda take so very soon za a sa musu rana ko Sadiya da aka auramin kasan yadda igiyoyin aurenta sukayi min tsaye akai?

  "To ba ga Aydah ba amma wannan Sadiya tun farko ni dai bata kwanta min a rai ba ta cika rawar kai.

"What! Aidah fa kace?

"Kwarai kuwa Aidah.

"Duka-duka yaushe aka haifi Aydah da har za a aura min ita? She's just 15-16yrs fa.

"Koma jaririya ce gara ita sau duba da Sadiya.

"Wallahi gara in dawwama da auren Sadiya da in auri yarinyar da nike mata wanka na canja mata diaper.

Yadda AB yayi maganar ya kusan saka Abdulkarim dariya sai dai baiyi dariyar ba, lokaci ɗaya AB ya juya masa baya alamar dai kwata-kwata  bayason maganar.

Da yamma da Daddy ,ya shigo cike da ƙarfin hali Abba ke faɗin."Amma Daddy sai nake ganin kamar kai Sadiya  jail bashine mafita ba kayi hakuri Daddy duk da nasan bata kyauta ba ƙaddara ce da kuma sharrin zuciya ayi mata alfarma acikin alfarmominka Daddy, indai ta nine na yafewa Sadiya duniya da lahira.

AB ya karasa maganar da respect a muryarsa kallon da yaga Daddy nayi masa ne yasa yayi saurin saukar da kansa ƙasa."idan ba a hukuntata ba taya kakeso ta karɓi laifinta?

"Amma Daddy macce fa taya za ayi ta shiga irin wannan wurin?"murmushi mai ciwo Daddy yayi kafin yace."idan ba a hukunta ta ba bazata gane kuskurenta ba ka bar yar banza ta kwana a ƙarkame gobe ko da kuɗi aka bata akace ta nunawa wani wuƙa Bama ta caka masa baza tayi ba. A razane Abba, ke faɗin."Ta yaya zata kwana a irin wannan wajen daddy ai sai ta kwaso cuta. A fusace Daddy ya dube shi "Ka daina magana haka Abba, na rantse Sadiya sai ta kwana acikin a hannu hukuma sai tayi nadama sai ta azabtu ko ina yin belinta.

Jin rantsuwar da Daddy yayi jiki a sanyayye Abba yayi shiru bai ƙara faɗar komai ba, koda magarib da Mami tazo tana jiran Abba yayi mata maganar Sadiya sai dai Abban bai ce komai ba har lokacin tafiyarta gida yayi tasan Abba da miskilanci ba zai mata magana ba haka mami ta dawo gida jiki a sanyayye kuma har lokacin Daddy baiyi mata izinin tafiya police station ba. Wasa-wasa sai da Sadiya tayi sati guda a cell aka fito da ita ga baki ɗaya Kamanninta sun canja tamkar ba Sadiya Bashir ba yar gayu da kwalisa duk wannan gayun babu shi, shima a ɓangaren Abba, yana samu sauƙi sosai har ciwon ya fara ƙamewa saboda irin maganguna da yake sha, daga Mami har Daddy babu mai amsa gaisuwarta haka ma ƙannenta da take hango tsanarta acikin idanuwansu har lokacin kuma babu wanda yake yi mata maganar AB ko yayane tana son taji wani hali yake aciki sai dai bataga fuskar tambayar kowa ba a gidan, a bakin Huwaila mai aiki ne ma taji ai yaya AB yana asibiti. Satinsa biyu aka bashi sallama kai tsaye gida aka dawo dashi daga Siyama har Aidah tamkar zasu mayar da AB ciki dan ganin ya samu sauƙi sosai a kuma daren Abba,ya haɗa dukka 'ya'yan nasa

Tun kafin Daddy yayi magana zuciyar Mami ta shiga bugawa tana ta addu'ar Allah yasa abunda Daddy zai yanke mai sauƙi ne. Kai tsaye Daddy ya miƙawa Abba takarda da biro fuskarsa babu walwala balle wani annuri yace."Abba ka rubutawa Sadiya takardar saki yanzu ka bani umarni nake baka ba shawara ba.

Babu wanda kalaman daddy basu girgiza shi ba ,cikin rawar murya Abba ke faɗin."Amma daddy.!

Saurin ɗaga masa hannu Daddy yayi "Abba ko kaima za ka bi bayan Sadiya ne kamar yadda ta zama shaiɗaniyya cikin 'ya'yana kaima haka zaka zama?Da sauri Abba ya girgiza kai hukunci Daddy bai wai ya masa wani irin tsauri  bane sai dai yana gani kamar Daddy ya yi gaggawa kaman yadda ya yi gaggawa haɗa auran nasu bayan yasan dole su sami rauni zuciya kafin su karbi junansu a matsayin mata da miji. A  maimakon yayi farin ciki da wannan sakin sai ya samu kansa cikin tashin hankali da muguwar fargaba  sai da ya haɗiye wasu busassu miyau kana ya ɗora hannunsa a takardar cikin minti ɗaya ya gama rubutun Daddy ya ƙarbi takardar ya duba ya kalli Sadiya ta miƙa mata takardar fuskar Daddy tamkar hadari wasu irin hawaye masu zafin gaske suka balle acikin idanuwanta sai da Daddy ya daka mata tsawa sa'annan ta karɓi takardar babu inda baya rawa cikin jikinta. Ya kalleta ido cikin ido yace "wata biyu na baki ki fitar da miji ba za ki yimin zawarci acikin gidana ba.

Parlorn tsit yayi banda shesshekar kukan Sadiya babu abunda ke tashi cikin parlorn , Daddy ya kalli Mami yana faɗin in-sha-Allah nan da sati guda zan nemo wa Abba matar da ta dace dashi muddin ina raye Abba ba zai taɓa wulaƙanta ba. Abba zai taɓa kukan rashin iyayensa ba.


#love story 2023/2024

#Jeeddah Aliyu

#Asmy b Aliyu

#Team tagwaye novels

#kurman Allo

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.