Free chapter · Read without an account
010
by Jeeddah Aliyu · KURMAN ALLO
*KURMAN ALLO*
(A beautiful Love Story)
JEEDDAH ALIYU
ASMY B ALIYU
#Love Story
#Gwagwarmay
#Team tagwaye novels
10
*RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU
*TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA
#Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye novels
*MASARAUTAR KUDU$
Masarauta ce mai ɗimbin tarihi duk wani jinin sarautar da ya fito daga masarautar za kaga yasha bamban da normal mutane. Jinin masauratar suna da wata irin izza, taƙama, ƙasaita, za ka ga duk wanda ya fito daga wannan masauratar ɗabi'un da halayensa ba kamar na sauran mutane ba, ga su da girman kai da ɗagawa wayayyu ne suna da ilimin boko dana addini kuma gasu da wani irin kyau na ban mamaki da matuƙar wahala ka ga mummuna cikinsu sai dai abinda ba a rasa ba saboda mutum ɗan tara ne bai cika goma ba. Allah ya yi musu arziki sarauta da kuɗi gasu da mulki ga kuma tarin dukiya da Allah subhanahu wata'ala ya albarkace su da ita. A halin yanzu mai martaba sarkin kudu Mahmood Mustapha na uku shi ke mulkar wannan daula shine a matsayin sarkin kudu mahaifinsa Margayi Alhaji Usman Mustapha na uku shine Sarki bayan ya rasu aka naɗa ɗansa Mahmood Mustapha na uku. Sarki Mahmood su shidda mahaifiyarsu ta haifa wacce suke kira da mai babban ɗaki wato ita ce uwargidan sarki Usman, mai martaba sarki Usman ya mutu ya bar mata huɗu da sadaka uku tare da tarin 'ya'ya arba'in da bakwai a halin yanzu talatin da tara ke raye takwas daga ciki sun rasu
Kafin Sarki Usman ya rasu kan zuri'arsa a haɗe yake sai ya rasu ne aka fara samun rabuwar kawunan su wannan kuma ya samu asali ne daga wurin matarsa ta biyu Hajiya Kilishi, a dalili sarautar Sarkin sabon birnin kudu da margayi Sarki Usman ya bai wa Aliyu tun yana da rai kasancewar Aliyu shine ɗansa na shidda a ganinsu
bai cancanci wannan sarautar ba tun da akwai na sama dashi. Wannan sarauta da sarki Usman ya ba wa Aliyu ita ce silar haddasa ƙiyayya tsakani yaran mai babban ɗaki da yaran Kilishi. Shi kuma Sarki Usman ya yi hakan ne a dalili fahimtar da ya yi Aliyu baya da ra'ayi sarauta ko kaɗan idan aka ɗora masa nauyi mulkin jama'a dole ya fara saka sarautar aransa. Dama shi Aliyu abarsa da kasuwanci domin kusan dukkan kamfanonin su shi ke kula dasu
Alh Aliyu yana baro bangaren mai babban ɗaki ya wuce gidansa kaitsaye ɓangaren sa ya shiga yana shiga katafaren parlorn sa ya nemi ɗaya daga cikin royal cushion da suka daɗa ƙawata parlornsa ya zauna, ya cire rawani kansa ya ajiye kusa dashi ya tsani rawani sai dai doka ce ga duk wani jini masarautar ya saka naɗi kafin ya shiga faɗa, shiyasa yanzu ma da zai shiga faɗa ya saka ba don haka ba da ba abinda zai haɗa shi da rawani
Hajiya Safiya ce ta turo ƙofa ta shigo cikin parlorn, ta hango mijn nata ya lafe jikin cushion idanunsa rufe tasan ba bacci yake yi ba kawai dai damuwar nan ce da ya ɗorawa kansa tasaka shi cikin irin wannan yanayi. Tambayar duniya nan idan za ka yi masa zai amsa maka ne da ba komai rana da baya ji so magana sai ya yi banza da mutum. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta nemi dab da ƙugunshi ta zauna tana matuƙar son mijinta irin son da fatar baki ba za ta iya faɗarsa ba, sai dai ta misalta. "Abbu
Ta kira shi da sunan da yaransa ke kira shi dashi, dama a wasu lokuta haka take kiransa dashi. Bai matso ba balle ta sa ran ya ji kira da tai masa sake lankwasa muryarta ta yi ta koma kiransa "Abbu
A hankali ya ɗage idonsa guda ya kalleta na 'yan wasu daƙiƙu kafin ya maida idonsa ya rufe, ya yi hakan ne don tasan ba bacci yake ba balle ta dame shi da kira. Sanin hali yafi sani kuma tasan halinsa fiye da yadda tasan yunwa cikinta muddin ba shi yaso yin magana ba duk nacinka dole ka kyaleshi don ba tanka ka zai yi ba.
"Abbu har sai zuwa yaushe zan daina gani wannan damuwar akan fuskarka? Dan Allah Abbu ka faɗa min idan ni ce ba ka jin daɗin zama dani ko ina maka wani abu da ba ka so wallahi a shirye nake da na gyara
Shiru ya yi alamar ba tanka mata ba "A matsayina na matarka makusanciyarka ina da damar da zan san damuwarka idan ina da hali taimakawa Abbu sai na taimaka ma idan babu kuma sai na tayaka da addu'a. Ni da kai abu ɗaya ne damuwarka nima tawa ce hakazalika farin cikinka shine nawa matuƙar kana cikin damuwa ba yadda za a yi na kasance cikin walwala
Har ta kai ƙarshen zance ta idanunsa suna a rufe "Safiya ina buƙatar hutawa za ki iya tafiya
Ya yi magana still idanunsa na rufe
"Amma Abb.
"Safiya please
Yai sauri katse mata hanzari a wannan karo ya buɗe idanuwansa suka fara canza launi, jikinta a sanyayye ta miƙe ta baro ɓangaren nasa, ba tun yau ba take ayyana cewa gangar jikinsa ta aura ruhinshi yana wani gun daban
*RUMAISA MADAWAKI
Rumaisa ta fito daga cikin gida jikinta sanye da straight gown na lace pitch in color gaban rigar har zuwa ƙasanta an mata beads work, sosai shigar tai mata kyau hannunta riƙe da purse ɗinta wacce tayi match da heel ɗin ƙafarta ɗayan hannunta ke ɗauke da car key ɗinta. Fitar nan da za ta yi za ta je gyaran gashi da body waxing da take zuwa duk ƙarshen wata yadda take tafiya tamkar wacce bata kashi sai wani yatsine fuska take yi ga idanuwanta ta lulluɓe su da sunglass. Ta shiga motarta tare da yi reverse ta fito da ita daga parking lot kana ta daidai motar ta ja ta zuwa gate wanda tuni maigadi ya buɗe mata. Kai tsaye Aj beauty palace and spa ta nufa dama can ake mata duk wani gyaran jiki, tana shiga wurin ta haɗu da old friend ɗinta Aneesa Baffa wacce suka yi karatun sakandare tare tun daga lokaci basu sake haɗuwa ba sai yau da suka haɗu a Aj beauty palace and spa
Aneesa Baffa kyakkyawar matashiyar budurwa wacce ke ji da naira saboda mahaifinta Alhaji Baffa ya mutu yabar musu tarin dukiya wannan yasa ta fara business ɗinta tana da manya-manyan boutiques na siyar da expensive clothes na mata da maza har ma dana yara Aneesa Baffa she's independent woman wacce ke cin kashin kanta sai dai har yanzu bata yi katari da namiji da take gani ya dace da ita ba duk da tana da farin jini wurin maza. Cike da wayewa ta mata da idanuwansu suka gama buɗewa suka rungume juna ita da Rumaisa daga nan hira ta barke a tsakanin su daga nan suka yi exchange ɗin contact, da yake ita Aneesa har an kammala mata abunda ta zo yi saboda haka suka yi sallama tare da alƙawari kai wa junansu ziyara
*ALH BASHIR MANSION
Sosai Sadiya ke rera kuka kaman ba gobe Allah na tuba ko uwarta da ubanta suka mutu iya kukan da za ta yi kenan, wani kololon abu take ji ya danne mata zuciya saboda tsanani kukan da take yi she can't even breathe sai wani irin sheɗewa take yi tasha baƙar wahala kafin ta samu numfashinta ya daidaita a jikinta, she didn't think Hafeez would break her heart like this ta ɗauki soyayya da yarda ta bashi sai gashi ya barta da dafi a ƙahon zuciya, wani kalan mahaukaci so take mishi shiyasa ta kasa karɓa Ya Abba a matsayin mijinta sai gashi tayi biyu babu ta rasa Ya Abba shi kuma Hafeez Sale ya guje ta
*AYDAH
Hankali kwance take karanta novel ɗinta duk gun da ya yi mata daɗi sai tai wani lumsashe idanu, tana rausayar da kai kiran sallah magarib ya tashe ta ba don ranta ya so ba ta ajiye littafin sai lokaci ta cire uniform ɗin jikinta ta ɗaura light pink towel ɗin ta ta shiga wanka agaggauce ta fito ta zura plain cotton gown mai gajeren hannu tayi sallah bata tashi ba sai tayi sallah isha kana ta fito main parlor, babu kowa sai mai aikinsu da ta hango a dining area tana arranging table, saboda haka ta wuce ɗakin Siyama tana tura ƙofa Siyama was busy with her laptop turo ƙofar ɗakin nata da Aydah tayi yasa ta ɗagowa Aydah ta ƙaraso ta zauna kusa da ita "me kike yi ne yaya Siyam?
"Ina ruwanki da abunda nake yi
Siyama ta faɗa tana mayar da idanuwanta kan laptop ɗin
Sai da Aydah ta galla mata harara a fakaice ta wani turo baki tare da leƙa screen ɗin laptop ɗin ita a dole sai ta ga abunda Siyama take yi cikin sauri Siyama ta janye laptop ɗin tana faɗin "what's wrong with you?
"I just want to see what you are doing in the laptop ko haramun ne don na ga abinda kike yi
Wani kallo Siyama ta wulga mata sosai iskanci Aydah ke sauri hasala ta kalli yadda tai mata magana kaman wata sa'anta "Get up and get out of my room before naci ƙarniyarki
Miƙewa Aydah ta yi tana gunguni ƙasa-ƙasa magana ne take mayar mata, rai ɓace Siyama ta kalleta taga sai da take da ɗan mitsitsi bakinta ko ba tambaya ba tasan maganganu banza ne take faɗa mata "Why don't you respect me, Aydah?, I am your sister ina gaba dake you have to respect me
"Haba dallah Yaya Siyam sai faɗa kike kina nanata wa sai kace wasu shekaru kika bani masu yawa
"Iyeee! Aydah yau kuma iskancin naki akaina ya dira
Kallo sama da ƙasa Aydah ta yi mata hakan ya ƙara harzuƙa Siyama ta zabura ta miƙe tsaye da zimmar idan ta kama Aydah sau ta yabawa aya zaƙinta, Aydah tana ganin yadda ta miƙe ɗinan da gaske za ta iya dukanta saboda haka ta juya da gudu ta buɗe ƙofa ta fita, ita ma Siyama da rashin haƙuri ta biyo ta da gudu suka sakko ƙasa dai-dai Sadiya tana fitowa kitchen hannunta riƙe da mug ta haɗo tea, ta gaji da kukanta na rashin dalili ta fito yunwar da ta dinga naniƙar hanjinta yasa ta fitowa babu shiri sai dai ta rasa appetite babu ɗanɗano ko kaɗan a bakinta wani ɗaci-ɗaci ma yake mata shiyasa ta yi deciding ta sha tea. Sai kuma ga waɗannan rigimammun siblings ɗin nata da basa gajiya da rigima, Aydah da ta zo da gudu bata lura da Sadiya ba tai bala'in bangaje ta mug ɗin hannunta ya subuce ya faɗi kan marbles ya tarwatse tea ɗin ya zuba a ƙafarta, duk dai bai da zafi sosai hakan bai hanawa Sadiya tsandara ihu tana kira ƙafarta sai tsalle take Siyama ta nufe ta, tana ƙoƙari kamata Aydah tana gani yadda jikin Sadiya ke motsawa sai kawai abin ya bata dariya ta fashe da dariyar harda su riqa ciki .a fusace su dukka biyu Sadiya, Siyama suka yi kanta ta sake kwasa da gudu ta fice zuwa compound tana dariya abinta, a bayyane ta ce "Cabdijam! Wallahi yaya Sadiya buhun banza ce dallah kalli yadda naman jikinta ke rawa dama za ta ɗauki shawara ta fara rage fat
Ta ƙarashe magana tare da kwatanta yadda Sadiyar ke tsalle sai kawai ta sake sheƙewa da dariya. Motar Ya Abba da ta hango yana shigowa ta nufi wurinsa tana ƙoƙarin haɗiye dariyarta saboda tasan halinsa ba kasafai yake son dariya ba.
"Sannu da dawowa Ya Abba
Ta faɗa sa'ili da ya fito briefcase ɗinsa ta karɓa ya sakar mata yana faɗin "Me kike yi a waje Aydah?
"Yaya Sadiya da yaya Siyama ne za su yi min duka shine na gudu waje
Sai da ya ƙare mata kallo kafin ya furta "Hauka suke yi da za su yi miki taron dangi? Ban da mugunta me za su daka anan? Sai dai in kasusuwan ki za su karya
Ya ƙarashe magana yana nuna jikinta cunno baki tayi "A'ah! Ya Abba bangane ba wannan yabo ne ko zagi
Murmushi mai sauti ya yi tare da dungure mata goshi "bansani ba
Ya yi magana tare da nufar flat ɗinsa tayi tsaye tare da bin sa da ido tana kallon yadda yake tafiya cike da izza da ƙasaita a zuciyarta tace "Anya kuwa Ya Abba ɗinan ba daga royal family ya fito ba? OMG! ji tafiya irin na hamshaƙai sarakuna. Tuni AB ya yi gaba yabar ta tsaye tana sambatunta na shirme yana dab da isa entrance ɗin flat ɗinsa ta kwasa da gudu ta cimmasa tana "Ya aka yi yau yaya Abba ka yi saurin dawowa?
Bai bata amsa ba har sai da suka shiga parlornsa ya ce "Ko na koma ne
"Ni na isa na ce ka koma
Ya ajiye wayoyinsa kan centre table yana faɗin "Ki jira ni zan yi wanka
Ya ƙarasa magana gami da karɓar briefcase ɗinsa dake hannunta ya nufi master bedroom ɗinsa "A fito lafiya
Aydah ta faɗa tana mai zaunawa akan cushion
#Love Story 2023/
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye Novels
#Kurman Allo.