Free chapter · Read without an account
Shafi na Biyar
by BIL-SAN · MUTALLAB ASAD
*MUTALLAB ASAD*
NA
*BILLY S FARI*
&
*NANA DISO*
5.
Hakan yasa Aryaan ya tayar da motarsa ya ja yabar wajen, a hankali Mutallab ya buɗe idanuwansa daya lumshe ya juyo da kansa yana kallonsa, duk da baiyi magana ba Aryaan ya fahimci ko me yake nufi, don haka ya ɗag masa kafaɗa haɗe da cewa, "A gun Mamma zan kaika ita sai ta tambayeka kome ke damunka tunda kaƙi sanar mani, ko makaho ya kalleka MAM yasan kana cikin damuwa amma shine zan tambaye ka kace mani nothing, na rasa sai yaushe zaka fara ɗaukata a matsayin dani na ɗauke ka". Runtse idanuwa Mutallab yayi tare da dakatar da Aryaan daga tuƙin da yakeyi, sai daya ji ya tsaya sannan yace, "Kai matsalar dakai kenan Aryaan, sai kace komai saika sanar da Hajiya kuma kasan tabbas baza taji daɗi ba".
"Eh mana, ni an faɗa maka ina jin daɗin ganinka acikin irin wannan yanayin ne? Kai ko tsoro baka ji wani ciwon yazo ya sameka?".
"Meke tafe dakai?" ya jefo masa tambayar har lokacin idanuwansa na arufe, "Ban sani ba". Aryaan ya bashi amsa a hasale yana maka masa harara, wanda yayi daidai da lokacin da Mutallab ɗin ke buɗe idanuwansa akansa, murmushi ya saki yana gyara zamansa kafin yace, "Allah ya baka haƙuri maida wuƙar mana". banza Aryaan yayi masa hakan yasa Mutallab yaci gaba da cewa, "Karka damu kawai matsalar gidanmu ce da a kullum ƙara gaba takeyi, a ɓangare ɗaya ga larurar Afrah da duk safiya nake kwana da ita kuma nake tashi da ita". cike da tausayinsa Aryaan ya dafa gefen kafaɗarsa yana cewa, "MAM kaci gaba da haƙuri watarana duk wannan abun zai wuce har yazama tarihin da kai da kanka zaka bada labarinsa, Afrah kuwa muci gaba da yimata addu'a cuta ba mutuwa ba, wlh ina har muna da rai itama sai ka bada labarin wannan lalurar tata ta yau ciwo gobe lafiya, kuma idan ka lura wannan ciwon nata tamkar ruwan dare ne yanzu, mutane na fama dashi sosai kuma ana samun lafiya".
"Aryaan typoid da athma fa akace lokaci ɗaya ajikin mutum, kaima kasan abin ba mai sauƙi bane da hankali zai iya kwanciya bayan hango tarin barazanar da ako yaushe suke yiwa lafiyarta". "Haka ne amma ai ba abinda yafi ƙarfin Allah ko?".
"Ehmm. ka faɗi gaskiya kuma, Yanzu dai mu bar wannan maganar ya ake ciki?"
"Dai-da wlh dama nazo in sanar maka da cewa na samu aiki kuma zuwa Monday zan fara zuwa in Sha Allah". wani irin ƙayataccen murmushi Mutallab ya saki cike da farinciki lokaci ɗaya damuwar dake kan fuskarsa na gushewa yace, "Alhamdulillah, kace mun samu aiki Aryaan, at least kaga ɗayan mu yarage zaman banzan da muka shekara biyu muna yi ba aiki ko kuwa?"
"Haka Mamma tace, saura kai inshaa Allahu na tabbata naka na zuwa daya zarta nawa". Murmushi Mutallab yayi yace, "idan akace Allah angama komai, amma ni nafara fidda rai saboda ban hango alamun haka ba, kana fa ganin yanda Abba yayi banza da zancen nan nawa, ga ƙasar nan ta koma yanzu waka sani waye ya sanka, tunaninsu kawai yanzu nakoma na ƙarasa masters ɗina, in har Abba zai amince mani to hakan zafi mun daɗi a yanzu."
"Gaskiya kayi tunani ƙara ka shata gaba ɗaya in zai amince tunda yaƙi saka maka hannu a zancen samun aikin naka. Hakanma shawara ce mai kyau Allah yasa ya amince ta wannan fannin ya saka mana hannu".
"Amin ya rabbi Aryaan". sun jima suna tattaunawa akan matsaltsalun Mutallab ɗin da mahaifin nasa da ako yaushe ke nuna halin ko inkula ga lamurransa shi da ƴan uwansa tamkar ba shine ya haifesu ba kafin suyi sallama ya wuce shi kuma ya koma cikin gidan. Sai daya koma ya duba Afrah da har bacci ya ɗauketa sannan ya sauko ya koma sashensu. gugar kayansu ya tadda Jalil nayi ya nemi gefen katifar dake cikin ɗakin nasu ya zauna yana cewa, "Ba nace kabar gugar nan ba zan bayar ayi mana ko nagoge mana da kaina? me yasa kake son wahalar da kanka da yawa, kai ne wanki yanzu kuma kaine guga".
Ɗago kai Jalil yayi ya kallesa sannan ya maida hankalinsa ga gugar da yakeyi haɗe da cewa, "Allah ya tsare ya Mutallab ace ina raye kana guga da kanka, kabarni kawai nariƙa yimana ba wani abubane, nan har na mutane zan iya karɓowa nayi idan zasu biyani yaya don na rage maka tarin matsaltsalunmu dake kanka, ai kasan bahaushe na cewa babu maraya sai rago". sosai tausayin ɗan uwan nasa ya kanshi jikinsa duk yayi sanyi, addu'a yakeyi cikin zuciyarsa Allah ya sama masu ƴancin da Mahaifinsu zai basu kulawa da gata tamkar yanda yake yiwa ƴan uwansu domin zuciyarsa tafara raunata da kallon yanda ƴan ƙannen nasa ke haɗar baƙin ciki da damuwa a zukatansu saboda shi suga farincikinsa, a ɗaya ɓangare na zuciyarsa kuwa addu'a yakeyi Allah ya nuna masa hanyar da zai tsaya masu koda basu samu hakan a wajen Mahaifinsu ba har zuwa ƙarshen rayuwarsa.
Afrah kuwa sosai baccin yayi mata nauyi saboda rashin runtsawar da bata samu tayi ba daren jiya, can cikin barci ta taji an turo ƙofar ɗakin nata da ƙarfi, Muryar Umma taji da ƙarfi saman kanta tana kiran sunanta, "ke Afrah idan kin gama baccin naki na asara sai ki tashi kije Alhaji na kiranki".
Ɗan yamutsa fuska Afra tayi tana tashi zaune saboda nauyin da kanta yayi mata haɗe da cewa, "Umma banida lafiya ne bawai baccin kawai nakeyi ba." tsaki Umma taja haɗe da cewa, "Allah dai ya waddaran halin maƙaryaci, ke wai ko kunya bakya ji ki riƙa ƙaryar ciwo don tsabar jawowa kai mugun abu, da wani shegen fari kamar na aljanu, waya sani ma ko hakan ne ke hanaki lafiya, zaki tashi ne ko sai na mammakeki kin wani zo kin bararraje akan gado."
A hankali ta sauko kan gadon tanufi toilet ita kuma umma ta fice tana surutanta, fuskarta ta wanko ta shiga tunanin shin yaushe ne matan ubansu zasu so su? Yaushe zasu daina nuna masu tsana alhalin wacce sukeyi masu hakan dinga ta riga tabar masu duniya? taƙare wannan tunanin cikin ranta tare da fitowa toilet ɗin tana gyara ƙaramar hularta dake kanta, ƙasa ta sauko ta nufi zuwa shashin mahaifin nasu, sallama tayi masa kamin tashiga yana zaune akan lafiyyan farin carpet ɗin dake cikin palourn ta gaida mahaifin nata cikin girmamawa, Umma dake zaune gefensa tana masa hira ta taɓa baki haɗe da cewa, "Sai yanzu kika ga damar zuwa Afrah anya kina so ki gama lafiya kuwa?"
"Ƙyaleni da ita shashashar yarinya, ya kike so nayi miki akan makaranta kullum kece latti saboda lalaci kina bacci baza ki tashi ki shirya ba har lokaci ya wuce ki jawa ƴan uwanki duka a school, shin ke kika fi kowa jin daɗin bacci ne da baza ki tashi ki shirya akan lokaci ba?, ko kuwa dai aure ne kike so na aurar dake kowa ma ya huta?" tunda mahaifin nata ya fara magana bata yanka masa ba kanta ke ƙasa har sai da taji yayi wannan zancen da sauri ta ciri kai tana kallonsa tare da girgiza kai tana cewa, "A'a Abbana kayi haƙuri ba haka bane".
"To menene Afra? yanzu ma ƙarfe ɗaya saura da akaje bacci aka isko kinaji, shikenan fanɗare Mani zakiyi keda ƴan uwanki ku koma marasa ilimi da tarbiyya acikin gida? sai an fara magana ku riƙa sissinne kai ƙasa sai kace munafukai", "Kayi hakuri Abbana jiya banyi bacci ba banda lafiya, yau ma a kwance na wuni bawai bacci nakeyi ba, ka tambayi Umma kaji".
"A'a Afrah me zai tambaye ni kuma Ni da na iskoki kwance kin bararraje akan gado kina kwasar baccinki hankali kwance, yanda kika shirgo masa ƙaryarnan yanzu nima haka kika shirga mani ita ba don na tabbatar ba tunda hali nan dai zaune lafiyarki kalau".
"Yaya Mutallab ya bani magani daya shiga dubani shi yasa jikinsa yayi sauƙi Abba". Afrah ta faɗa cikin sanyin murya tana son mahaifin nata ya yarda da gaskiyar ta, sosai yake jin tausayi ta a ƙasar zuciyarsa amma ya rasa dalilin daya sa sam baya iya riƙe kansa da nuna mata fushinsa, Umma data gama cika da takaicin Afrah ɗin tace, "Kedai ki fadi gaskiya don su iyaye ba'a yi masu ƙarya", " barni da ita Hajiya sun maidani ɗan iska kullum sai dai nayi asarar kuɗina amma basa karatun, shi yayan nata ma ya gagara tsayawa da ƙafafuwansa yaje ya nemi aiki duk kuɗin dana kashe a karatunsa sun tashi a banza, shi kuma ɗayan naga ya dawo ya zauna wai ni yake jira na sake dunƙular kuɗina biya masa kuɗin registration ga Asad ɗin ƴan iska ko?, to na gama wahalar da kaina akanku tunda baku kaɗai na haifa ba, in zasu je su nema da kansu suje su nema idan kuma baza su iya ba su suka sani, ke kuma ki buɗe kunnenki ki jini, daga yau na cireki daga wannan makarantar da kukeyi *Leaders spring international* take ko meye? don na gaji da asarar kuɗina tunda bakya son karatun na mayar dake makarantar bakin titi ya sunanta ma hajiya?" Umma da daɗi ya kasheta tana murmushi cike da mugunta tace, "Academy". "To kinji academy dan haka na tura yayanku Jamil yau yaje yayi mako duk abinda ya kamata, jibi idan sun kawo maki uniform zaki fara zuwa". take taji zazzaɓin daya kwanta mata na neman dawo mata saboda tsananin tashin hankalin data shiga jin kalaman da suka gama fitowa daga bakin mahaifin nata, wannan wacce kalar masifa da bala'i ne ace makarantar ma baza'a barta tayi inda ƴan uwanta keyi ba ta samu ilimi ingantacce, wasu zafafan hawaye taji sun zubo mata a fuska da sauri tasa hannu ta goge tunowa da yadda yayansu kullum yake masu nasiha akan duk hukuncin da mahaifinsu zai yanke tsakaninsu da ƴan uwansu kada su taɓa yimasa musu ko gardama domin baza a taɓa canzawa tuwo suna ba shi ɗin dai mahaifinsu ne kuma su ƴaƴansa ne, Cikin rauwar muryar dake nuni da tsantsar damuwar da kalaman suka haifar mata tace, "Shikenan Abbanmu zanyi yanda kake so duk da nafiso nayi karatu inda ƴan uwana suke, nagode Allah yaƙara maka lafiya ya tsareka.." tun kafin ta ƙarara rufe baki Umma da takaicin yanda Afrah tayi maganar cikin girmama mahaifinnata ya rufe ta tace, "Ai kuwa sai dai kiyi hakuri baza su zauna kina cutar su ba haka kurum, tunda ke karatun ba da gaske kikeyi ba to su kama sai abinda ya turewa buzu naɗi, muguwa kawai".
"Ya isa haka, tashi kije Afrah". Abba ya faɗa tare da dakatar da umma ga batutuwa da takeyi don sam ba haka taso abun ya kasance ba, har Afara takai bakin ƙofa Abban hakura sunanta, wani irin takaici ne ya sake dunƙule zuciyar umma don sam bata don yarinyar ta kuma tsaneta sosai, "Ki dafomin tea mai kayan spices wanda kikeyi kiyi maza ki kawomin". Abba yafaɗa yana kallonta, "Tohm Abba". Ta faɗa haɗe da juyawa da sauri, Umma kuwa dake cike da baƙin cikin rashin nasararta na ganin ta jefa yarinyar a ƙunci abinda tasa ayimata tayi kwafa tana tsittsine masu ita da ƴan uwanta aranta, duk da tayi nasara akansu ta fuskoki da dama amma wannan shegiyar biyayyar da suke yiwa mahaifin nasu dake baƙanta mata rai ta rasa yanda zata rabasu da ita ta yadda zasu fanɗare masa ya koresu daga ciki gidan gaba ɗaya.
Afrah kuwa tana fitowa sashen Abba ta ƙarasa babban kitchen ɗinsu, kettle ta ɗakko ta ƙarfe ta wanketa sannan ta ɗakko blender ta saka cup ɗin niƙan gari ta zuba citta da kaninfari da cinnamon ta saka cardamom ta saka rosemary ta ɗan niƙasu sama-sama ta zuba a cikin kettle ɗin, can bayan gidan nasu ta zagaya gurin flowers ta tsinko Mint leaves da Lemon grass da scent leaf ta dawo kitchen ɗin ta zubasu acikin kettle ɗin suma sannan ta ɗakko Lipton ta saka ta zuba ruwa ta ɗora akan gas, shashin su ya Mutallab ta nufa kafin ya ƙarasa dahuwa tana ƙoƙarin ɓoye damuwar dake kan fuskarta, duk da ɗakin nada ɗan girma amma kana kallon nasu khalil da ɗan uwansa dake gefe da daya sha gyara zaka fahimci tazarar banbancin da mahaifin nasu ya nuna ƙarara a tsakaninsu, don jiya-jiya ba da nisa bama aka canza musu kayan gadon amma yayun nata babu komai acikin ɗakin nasu bayan ƙatuwar katifa da ƙaramar wardrobe, Suma tun kayan mahaifiyarsu ne data rasu Umma ta bada shawarar a saka masu su cikin ɗalibai don kar mahaifin nasu ya saya masu wasu, a hankali ta shiga bubbuga ƙofar haɗe da cewa, "in shigo?" ya Mutallab da fitowarsa wanka kenan ya gama shiryawa cikin ƙananan kaya da suka matuƙar karɓarsa yace, "shigo mana". Yana ɗaura agogo a tsintsiyar hannunsa, turaƙofar tayi ta shiga bakinta ɗauke da sallama, ɗago kai yayi ya kalleta haɗe da cewa, "Auta har kinji sauƙin? Yanzu nake cewa na biya na dubi jikin naki". Murmushi tayi fuskarta a cunkushe ta tsaya bakin ƙofa tana tacewa, "na ji saukin sosai yaya, ina wuni?" "Lafiya klw ya jikin?"
"Alhamdulillah" ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya haɗe da sadda kanta ƙasa tayi shiru,
"Menene Afrah?" Mutallab ya faɗa ganin yanda ta su ne kai ƙasa takasa magana, abinda sam ba ɗabi'arta bane indai a gabansa take tofa ta dinga yi masa surutu ne har sai ya gaji, kamar wadda ke jira ta fashe da kuka tana cewa, "Yaya me yasa Abbanmu tsanemu? Me nayi masa daya cireni a school ɗin da mukeyi ya maidani Academy?" Gabanta ya tako ya riƙo hannuwanta ya zaunar da ita a gefen katifarsu ya ɗora hannayensu akan fuskarta ya goge mata hawaye dake zubowa yana cewa, "Wannan ai ba komai bane Afrah, su iyaye aduk lokacin da kika ga sun yiwa ƴaƴansu abu mai daɗi ko al'adun haka duka sunayi ne saboda suna son sa, ina ga yanayin jikin naki yasa Abba yayi tunanin sauya maki makarantar da tafi kusa ga gida saboda abun yazo maki da sauƙi, abun buƙata kawai shine ki dage kiyi karatu domin duk inda kike matuƙar kika sa himma kukayi ƙoƙari to zaki samu fiye da ilimin da kike tsammani, fata kawai Allah yasa hakan yazame miki alkhairi kin ji ko?" Ya ƙarshe zancen yana kallon cikin idanuwanta haɗe da jan kumatunta, goge hawayenki kafin mutumen ki ya shigo yanzun nan ya fara tsarguwarki, Murmushi ta saki tana share ƙwallan sai ga Jalil ya shigo, cikin sigar tsokana ya mangaremata kai yana faɗin,"ya akayi tsinkui kike kuka naga fuskarki tayi ja kamar angasa buredi". Ɗan turo baki tayi tana maka masa harara haɗe da cewa, "yaya ka ganshi ko?"
"Manta dashi, dama shi inda yafi gwanewa kenan". Kamar an tsikareta ta miƙe tana cewa, "wayyo yaya bari natafi nabaro tea ɗin Abba akan wuta". Tafice da sauri ba tare data jira amsar da zai bata ba, a ƙasar zuciyarta kuwa taji abinda ya faru ɗin tamkar ba komai ba ɗin, tabbas yayanta jarumi ne da ako ina zata iya nuna shi, kuma shine asalin ƙwarin guiwar da ako yaushe take ji mutane na faɗa tare da amfani dashi a matsayin katanga ga kowace irin matsala, duk shekarun nan da suke fuskantar abubuwa kala-kala agidan mahaifin nasu bai taɓa ingizasu su aikata wani abun marar kyau ga mahaifinsu ko kuma matansa ba sai dai yace suyi haƙuri tare da basu kalaman ƙarfafa guiwa. ciƙin mintunan da bazasu huce goma ba Nagama Na wanƙe tea cup Na dakko masa zumarsa Nasaka Na nufi shashinsa Na ƙaimasa hajiya sai faman murmushi taƙeyi tace " Afrah ban hanaku idan babanku ya aikeku kudinga daɗewa ba? Da laila ce da bazata ƙai wannan loƙacin ba tadawo." " Ina suka dauƙeni da girma bayan sungama raina ni." " DanAllah babanmu kadain faɗin haka, kaicon ɗiyar data raina mahaifinta asara zata tabbata agareta, kayafemin Nabiya gurin Ya Mutallab ne kafin Na dora maka." " To ai sai kitashi kitafi ko? Hajiya tafaɗa.
#Mutallab Asad
#Tagwaye Biyar
#Nana Diso
#Billy S Fari.