Free chapter · Read without an account
SHAFI NA TARA
by Ummiaisha · SO DA ALAƘA
©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*SO DA ALAƘA......!*
*NA*
*UMMI A'ISHA*
TAURARI HUƊU
free page
Wattpad:@Ummishatu
9
***Da taimakon umaima da na hajiya ya samu ya kai ga kan gadon hajiya domin bedroom ɗinta shine mafi kusa daga inda ya samu attack ɗin,
Ita dai Ruhaima gaba ɗaya ji tayi tausayinsa ya kamata lokaci guda, ita dai ta san sau da dama Imran ya kan ce mata Sameer ne baida lafiya ko kuma yasamu attack amma idanuwanta basu taɓa gani ba sai yau, wani irin kai komo taga numfashinsa nayi, lallai in dai hakane masu irin wannan lalurar suna buƙatar tsananin kulawa ta musamman,
Yanda su hajiya suka ruɗe ita ɗinma a ruɗen take dan jikinta gaba ɗaya in banda karkarwa babu abinda yake yi. Hankula basu kwanta ba har sai da aka yi masa allura bayan an kira likita, bacci ya ɗan samu na tsawon wani lokaci,
Tagumi Ruhaima tayi tana kallon umaima wacce ke cin abincin da suka bari, ita kam gaba ɗaya tama kasa ci,
"wai in law dama haka yake fama da wannan ciwon?"
"wallahi in law... Kuma kinga shi kaɗai keda shi duk familynmu,ƙaddara dai kawai"
"Allah sarki, Allah ya bashi lafiya ya yaye masa, amma maganin ba ayi masa na hausa?"
"amin, ana yi mana ai yanzu ne ma hajiya ta ɗan lafa amma ada duk inda taji mai maganin hausa ko aka ce wannan maganin asthma ne sai ta karɓowa Sameer, tazo su yi ta daru shi baya son maganin hausa amma haka zata tsare shi sai ya sha"
"to Allah ya bashi lafiya yasa a dace"
"amin"
Tashi tayi ta sake leƙawa bedroom ɗin hajiya dan ganin halin da yake ciki dan ita wallahi haka kurum taji ya bata tausayi, wannan shine leƙawarta na wurin biyar tun bayan da ya samu bacci, har yanzun bacci ta ganshi yana yi ya wani ƙanƙame jikinsa wuri guda kamar mai jin sanyi, fita tayi ta koma wurin umaima wadda har lokacin bata gama cin abincin ba,
"wai in law dagaske ba zaki ƙara abincin nan ba?"
"wallahi duk ya fita a kaina inlaw"
Dariya kawai umaima tayi ta san dan ruɗewa ta ruɗe amma kuma kamar Ruhaima ta fita ruɗewa tunda gashi ko abinci ta gagara ci, sannan mintuna kaɗan sai taje ta gano halin da yake ciki da haka har la'asar tayi, sake shiga ɗakin tayi bayan ta idar da sallar la'asar yana zaune kan gadon hajiya ya tashi daga baccin ya ziro ƙafafuwansa ƙasa yana shirin saukowa ta shiga, bata yarda sun haɗa ido ba duk da dai taga bai kalleta ba dama, tsaye tayi ta kasa yi masa magana kamar yadda shima baiyi ba, ganin ya tashi ya shiga toilet yasa itama ta fita daga cikin ɗakin, ganin umaima bata idar da sallar da ta tafi ta barta tana yi ba yasa ta komawa falo, wayarta ta ɗauka wadda ta isheta da ƙaraji tun ɗazu kuma ta san maganar gizo dai bata wuce ƙoƙi bazai wuce mukhtar ba domin shine ke addabarta da masifar kira yanzu tun daga lokacin da ta bashi dama, saka wayar tayi a silent bayan kiran ya katse ta mayar da ita cikin handbag. Ita kanta bata san takamaimai me take tunani ba sannan ta rasa wanne irin tausayi take ji game da Sameer, a iya saninta dai babu wata shaƙuwa ko kulawa tsakaninsu in ka cire ƴar shan ƙamshin dake wanzuwa tsakaninsu tun daga ranar da ta fara ɗorashi a idon ta har kawo yanzu, fitowar shi ce ta katse mata tunanin da take yi game dashi nan tayi ƙasa da idanuwanta kamar yadda ta saba gudun kada asamu rashin dace su haɗa idanuwa, sai da ta tabbatar da ya wuce sannan ta ɗago tabi bayanshi da kallo lallai babu abinda ya kai lafiya, duk abinda mutum zai yi ko zai samu sai da ita, tunani tayi a ranta tunda har taga marar lafiyar ya tashi ai gara itama ta tattara sawunta a likkafa ta koma inda ta fito dan dama anan ɗin a takure take a duk lokacin da akace yana nan, shiyasa da mukhtar ya kirata tace yazo su tafi kamar yadda ya buƙata amma yace sai yayi sallar magrib, bata sake saka Sameer a idonta ba har lokacin da suka fito zasu tafi,
Shi kuwa Sameer duk abinda yake faruwa akan idonshi sune basu ganshi ba amma shi yana hangosu daga inda yake zaune cikin motarsa wacce ke ajiye cikin farfajiyar gidan, a ransa kawai sake jaddada taurin kan Ruhaima yake, yayi mata hannunka mai sanda akan mutumin nan, yayi mata wanka mai kama da jurwaye akan mutumin nan amma duk a banza dan tsabar jaraba ta toshe kunnenta, ko idan sunyi auren me wannan mutumin zai bata oho, tsaki yaja ya cigaba da daddanna wayarsa, shi bashi ma ko lambar wayarta kuma ya dace ace yana da ita fa, "me zanyi da no dinta ma" ya fada cikin zuciyarsa kamar da wani ne yace sai ya mallaka, akan idonsa suka bar gidan wanda bai wuce dasu gida direct ba sai da yafara biyawa da ita wurin wani gashin kaza yayi musu take away sannan ya mayar da ita gida, ita dai ta gama amincewa zuciyarta cewa kawai zata yarda ta auri mukhtar ba wai dan tana sonsa ko tana ƙaunarsa ba, ba kuma wai dan yayi mata ba a'a kawai dai halayensa sunyi mata dan mutum ne mai haƙuri da rashin fushi sannan ga barkwanci da fara'a,
Lokacin da tayi shirin bacci sai taji ta gagara domin babu abinda take tunawa a wannan lokacin sai halin da Sameer ya kasance ɗazu, ko yanzu yana cikin wanne hali oho? Ko ya samu yayi bacci ko kuma har yanzu yana cikin damuwar ciwon Allahu a'alamu, Ajmal ta rungume wanda ke gefenta yana bacci, a can ƙasan zuciyarta kuma tana yi masa addu'ar rabuwa da wannan ciwon rabuwa ta har abada. Shima Sameer a nasa ɓangaren lokacin da ya hau kan gadonsa domin yin bacci ji yayi Ruhaima ta faɗo masa gaskiya ya zama dole ya sanar da hajiya yakamata a tattaro Ruhaima ta dawo gidan nan ko dan kare mutuncinta da darajar ta, yanzu tana can tana rayuwa ita kaɗai sannan ta baiwa wani fuskar da zai je mata hira gida tofa komai zai iya faruwa yanda mutane yanzu basu da tabbas, shi tausayi ɗaya take bashi idan ya tuno irin yanda tayi sabo da mijinta yanzu kuma tazo ta rasa shi, lumshe idanuwanshi yayi amma ya san bacci kam ba yanzu ba, wani ɓangaren na zuciyarshi kuma alla alla yake gobe tayi domin yaje ya sauke nauyin da yake kan shi.
Kasancewar bata yi bacci da wuri ba shiyasa ta kasa tashi dan sai bayan da tayi sallar asuba sannan ta samu bacci, shima Ajmal ɗin da ya saba tashi da wuri har ya dameta yau bai tashin ba bare ya hanata rawar gaban hantsi,baccinsu suke kamar za a sake yi musu wani daren. Agogon hannunshi ya kalla misalin ƙarfe 10 har da rabi na safe agogon ya nuna masa, sake gyara tsayuwarsa yayi yana tunani a ransa to ko dai sun fita ne? To amma tayaya zasu fita ba tare da maigadi ya sani ba? Maigadi ya tabbatar masa da suna ciki, ƙofar falon ya sake zuwa a karo na huɗu ya ɗan bubbuga, cikin bacci taji muryar Ajmal yana cemata,
"mommy inje in buɗe? Ƙofa ake bugawa"
"uhmmm jeka" ta faɗa tare da sake jan bargo dan jin maganganun Ajmal ɗin take yi kamar a mafarki, da gudu ya sauka daga kan gadon ya fita, saida ya jima yana murɗe murɗe sannan ya buɗe, ganin Sameer tsaye hannayensa cikin aljihun wandonsa yayi saurin rungumeshi, ɗaukarsa Sameer yayi yana kallonsa dan ya fahimci daga bacci ya tashi, falon yake bi da kallo ganin komai a karkashe alamar itama Ruhaiman bata fito ba, wuri ya samu ya zauna yana gyara zaman face mask ɗin dake fuskarshi dan tun jiya numfashinsa babu ƙarfi,
Kimanin mintuna 15 ya shafe zaune a falon amma babu ko motsinta kai babu ma ko alamar cewa zata fito hakan yasa shi duban Ajmal dake lilo akan ƙafafunsa,
"mommy bata da lafiya ne?"
"uhmm.... Uhmmm...."
Kasa gane amsar da Ajmal ya bashi yayi, ehh yake nufi ko a'a? Cikin azama ya miƙe shi kansa bai san lokacin da ya tashin ba yana tambayar Ajmal tana ina? Tiryan tiryan yake biye dashi har cikin bedroom ɗinta inda take kwance tana bacci......
*_Ummi Shatu