Free chapter · Read without an account

28

by Azizat Hamza · Mutum Mugu Ne

*MUTUM.....Mugu ne*



                     28



Anty Zahra na gama tura text d'in ta fito ta tari Napep sai gidansu Nazira.

Nazira na kallo a falo ta shigo, bayan ta mata sannu da dawowa ta tambayeta ya interview, tace mata ba wahala sai dai akwai mutane dayawa tana tsoron zata iya rasawa.

Shiru shiru har Azahar Abba bai dawo ba.

"Dan Allah Nazira Yaya zai dawo da wuri ne?"

Nazira tayi murmushi tace "Anty kina jiran yazo ya baki kud'in mota ne?"

"Lah! Ba haka bane fah, inaso na wuce Azare ne ayau d'in kuma yace na jirashi"

"Ayya! K'ila kud'in mota zai baki ko kuma sak'on da za ki kaiwa su Baba"

" Nima abinda nayi tunani kenan"

Sai K'arfe hud'u Abba ya dawo, ya yi mamakin ganin Zahra agidan dan ayadda ta gaya mishi tana gama interview zata wuce Azare saboda sai ran Monday za'a kira wanda suka d'auka. Bai tambayeta mi ta tsaya yi ba ya dai mata fatan samun sa'a.

'bangaren Anty Zahra kam ganin har Abba ya yi wanka ya ci abinci bai nemi magana da ita ba tace wa Nazira zata wuce.

Nazira duk ta rasa yadda zatayi ta san dai idan ta kuma yiwa Abba maganan k'ila ma ya daketa saboda tunda ya saki Laure baya son maganar aure.

Ta samu Abba a d'akinshi tace masa dama Anty Zahra ce zata tafi tanaso suyi sallama.

"Ita kuma tafiyar dare zata yi?"

"Abba dama wai kai take jira kuyi sallama shiyasa bata tafi tun da rana ba kuma sai baka dawo da wuri ba"

Ya d'ago ya kalleta idonsa da alamun mamaki yace " d'auka mata dubu biyu a side drawer d'in nan ta sha ruwa a hanya. Ta amsa da toh.

Ko da ta shiga d'aki Anty Zahra na waya dan haka ta yi saurin fito da purse d'inta ta ciro dubu takwas ta had'a da dubu biyun da Abba yace ta dauka.

Bayan ta gama wayan ta mik'a mata kud'in "gashi inji Abba wai ki hau mota"

"Yaya kuma har da wahala gaskiya kice nagode bayan d'awainiya da kuka min tun jiya kuma har da kud'in mota"

Nazira ta yak'e baki tana dariya " Wai d'awainiya, ai yanzu an zama d'aya Insha Allah"

Anty Zahra ta d'au jakarta suka fito, Nazira ta shiga ta yiwa Abba magana ya fito suka yi sallama bayan ta masa godiya.

Nazira ta rakata suka hau Napep har park, bata sha wahala ba dan da suka isa mutum d'aya ake jira motar ta cika.

Nazira na ganin motarsu ta tashi ta samu waje ta zauna ta rubuta mata text da wayar Abba dama da shi ta fita.

*Kiyi hak'uri My dear na barki kin sha zaman jira, aiki ne yamin yawa a office ban dawo da wuri ba. Sannan maganar da nace zamuyi tana nan sai dai Ina ganin zai fi sai kin je gida kin huta tukunna muyi maganar. Allah ya tsaremin ke ya kiyaye hanya amin, wishing you journey mercy, dear*


Tana tura message d'in ta nemi Napep ta kama hanyar dawowa, minti biyar da tura message d'in reply ya shigo.

*Yaya ba komai idan na isa zan sanar maka*

Nazira tayi murmushi a zuciyarta tana addu'ar Allah yasa plan d'inta yai aiki.

Da ta je gida Abba ya buk'aci wayarsa ta mik'a masa wayar bayan ta goge messages d'in da tayi. Bayan sunyi sallar Isha ta samu Arif ta gaya masa plan d'inta shima ya bata goyon baya 100%.

Tsoron kar Anty Zahra ta kira wayar na hannun Abba ta je ta sameshi tace ya bata aron waya zata yi wani assignment wayarta ba data.

Minti goma da k'ar'ban wayan message d'in Anty Zahra ya shigo *Alhamdulillah Yaya na isa gida lafiya, fatan kuma kuna lafiya agaida Nazira da Arif*

Bayan ta karanta text d'in ta nunawa Arif shima ya karanta.

"Yanzu mi zaki rubuta mata kin san dole muyi yadda Abba ba zai gane ba har sai ta amince"

Nazira tayi murmushi "kar ka damu na riga na shirya komai, Insha Allah komai zai tafi normal"

Ta tura mata reply da haka *Masha Allah Gaskiya na ji dad'i da Allah ya saukeki lafiya, mu ma anan muna nan lafiya sai dai kewarki da ki ka barmu da shi, musamman ma NI, saboda ganinki tsakanin jiya da yau ya kawar min da kashi hamsin cikin matsalolina.*

*Fatima, dukkanmu ba yara bane, na san duk abinda kika ji na faɗa miki zaki min adalci akai. Ina so na shiga cikin jerin manemanki, kuma bana so ki dubeni a matsayin abokin yayanki, fa ce a matsayina na Dr Sulaiman Muhammad wanda yake rok'on ki taimaka ki zama haske cikin rayuwarsa da a yanzu ta yi duhu saboda mugunta irinta mutum.*

Sunata jiran reply amma shiru har sun tsorata ko dai bataji dad'in maganar bane.

"Amma Anty Nazira kina ga ba ta da wanda takeso kuwa? Kusan 20mins babu reply"

" Da bakinta tace min har yanzu bata tsaida kowa ba"

Nazira! Abba ya kirata daga falo ta amsa tareda fita daga d'akin da sauri.

" Kin kira Zahra ta isa lafiya?" Ya tambayeta

"Ee Abba ta isa lafiya tace a gaisheka"

" Shikenan toh, idan baki gama amfani da wayar ba ki barta a wajenki ni zan je na kwanta"

"Toh Abba nagode"

Tana shiga d'aki ta sauke ajiyar zuciya dan harta tsorata da kiran.

Arif yace "ta turo reply fah"

"Allah! Mi tace?" Ya mik'a mata wayar ta karanta

*Yaya ka bani lokaci nayi tunani* shine abinda ta turo.

Suka kalli juna suka yi murmushi sannan Nazira ta tura mata *shikenan dear Ina jiran amsar ki zuwa gobe da dare*

Ba ayi minti biyu ba ta yi reply *Yaya gobe yai sauri, nan da kwana uku zaka ji amsar ka*

Nazira ta tura mata da *shikenan Allah ya kaimu, agaida mutanen gida*

Ta goge duka messages d'in sannan tace wa Arif " gobe kafin na maidawa Abba wayar zan mata morning message" .....



......LAGOS........

Tunda ya bud'e k'ofan gidan wani k'anshi ya bugi hancinsa, kenan sun dawo daga church ya shiga ciki amma ba kowa a parlor zai wuce guest room ɗinsu ya ji wak'a na tashi daga kitchen dan haka ya lek'a dan da alama wanda ke gidan bai ji shigowansa ba. Wanke wanke takeyi ta kunna wak'ar Celine Deon na yaren french mai suna ' pour que tu m'aimes encore'

"Did you know the meaning of the song?'

Da sauri ta juyo dan ta tsorata bata yi tsammanin zasu dawo yanzu ba, kuma bata ji shigowar sa ba.

" So that you'll love me again" yace yana jingina kanshi da k'ofa tareda hard'e hannunsa biyu a k'irji.

Ta d'an zaro ido dan bata gane mi yake nufi ba.

"Baki ma san ma'anar wak'ar da kike ji ba?"

Ta yi shiru tana kallon k'asa "so that you'll love me again shine ma'anar sunan wak'ar, I think 1995 ko 1996 aka releasing ɗinsa, oh yes 1995 ne ma na tuna"

Ba tace komai ba ta juya ta cigaba da wanke wanke. Takowa yayi har wajen da take tsaye jikin sink d'in yace " Ziha kin gaji da ganinane a gidanku?" Ta girgiza kai alamar a'a

" Matata ta miki laifi ne?" Nan ma ta girgiza kai

"Toh miya faru? Miyasa kika chanja, bakya son ma magana dani"

Shiru tayi hannunta rik'e da wani roba ta wanke amma bata d'auraya ba.

"Saboda ni ba Bayarabe bane shine baza ki iya gayamin damuwarki ba?"

Ta d'an ja numfashi tace " uncle ba haka bane, ni ban chanja ba"

"Hmmm liar, I can see it in your eyes, kina fishi da ni ne koh? saboda na miki fad'a jiya koh?"


Shiru tayi tana kallon k'asa

" I'm sorry"

ta yi saurin d'agowa ta kalleshi shima d'in ita yake kallo.

"Yes Ziha kiyi hak'uri, I went too far yesterday, bai kamata na miki fad'a haka ba at least ba lokaci d'aya zaki iya hana Timothy da Gbenga ta'ba jikinki ba but try kin ji, ki yi k'ok'arin hana su"

Ta gyad'a masa kai

"So kin fasa rakiyan ne ba dai har kun dawo daga Ibadan ba"

At least yanzu zuciyarta yai sanyi ta dena fishi da Uncle Sajid d'inta. Tace "dama Daddy ne ya kira yace akwai wani abokinshi da suka had'u a church yau so kuma idan sun gama service zasu zo dashi gida shine yace na tsaya na musu girki, Boda Gbenga ne kawai yai rakiyan"

"Ayya! Kin sha aiki kenan"

Ta yi murmushi

"Yawwa Ziha Ina ki ka cika a Jamb ɗinki?"

"UI" ta amsa masa

"Why University of Ibadan?"

"Akwai k'anin kakana ta side d'in mommy nah, Dean ne a UI shiya samawa Boda Gbenga da Tim admission to nima shi zai sama mini"

"I see, dukkanku zaku je ku taru a Ibadan kenan. Why not ke ki chanja ki yi karatunki a Arewa tunda kinfi sabawa da chan"

"Uncle kenan, ai yanzu na saba da nan kuma"

"Ban yarda ba, Arewa ya fi k'ar'ban ki". Dariya tayi shima d'in ya d'an murmusa saboda koba komai yanzu ta sake jiki da shi ba kamar jiya zuwa yau da safe ba.

Haka ya tsaya a wajen suna d'an tad'i wanda duk yawanci shine ke mata tambayoyi musamman gameda karatunta. Shi ya ma manta cewa Ishola na jiranshi a waje zai je ya d'au kayan Azra.

Sai da ta k'arisa wanke wanke suka fito falo ya tuna maganar.

Ita ta d'auka masa kayan Azran kala biyu ta bashi ya fita.

..... K'arfe shida na yamma ya dawo bayan yai alwala ya fita sallah har lokacin Zaytunah bata dawo ba kuma bata kirashi ba. A inda yai sallar maghrib ya tsaya har sai da yai Isha sannan ya dawo. Ya tarar da Daddy da iyalenshi suna kallo, bayan sun gaisa Daddy ya kuma yi masa godiyar kyautan da ya yiwa Timothy.

Yana shiga d'aki ya tarar Zaytunah na sallah shima d'in band'aki ya shiga yai wanka ya fito dama ya gayawa Ziha kartayi girkin dare dasu saboda Azra ba za ta kwana a gidan ba ga Zaytunah dama ba cin girkinsu zatayi ba.

Yana d'aure da towel Zaytunah ta zo ta rungumeshi tana k'ok'arin had'a bakinsu, ya kau da kai gefe.

"Karka shiga hakkina my one because I need you tonight"

Duk yadda yaso ya kauce mata wannan karan bai iya ba abu da mata da miji ta riga tasan lakonsa dole ya biye mata suka raya sunna.

Washe gari ....

Bayan sun idda sallar asuba yace mata ta shirya kayansu harda na Azra saboda ya riga yai musu booking flight d'insu zuwa Abuja k'arfe takwas na safe .

"Yanzu Dan Allah my one ba za ka bari mu zauna tare har a gama case d'in nan ba"

" Kamar yadda ba ki bi maganata ba kika kama hanya kika zo, this time around ma kar ki ji maganata ki zauna a Lagos tunda ban isa dake ba"

Ta langwa'be murya "Dan Allah nasan nayi kuskuren zuwa ba tareda na sanar

da kai ba, amma please ka bari na zauna kusa da kai na zama maka support"

Wannan karan muryarsa ba wasa yace "the only support da zaki bani shine ki bi abinda nace ba wai kiyi san ranki ba"

Ajiyar zuciya tayi tana tunanin shawaran da Sady ta gaya mata jiya.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.