Free chapter · Read without an account

30

by Azizat Hamza · Mutum Mugu Ne

*MUTUM.....Mugu ne*


                     30


Da k'yar suka samu suka rabu da 'yan jarida. Sajid, Ishola ya kira yace ya zo ya kai Azra gidan Barrister dama tareda shi aka zo court yana jiranshi a waje, saboda akwai abubuwa dayawa da zasu yi gashi ba Zaytunah ba dalilinta, ya ma yi tunanin zai ganta cikin court amma ba ta nan.

Lokacin da Ishola ya iso yai mamakin ganin Azra dan dai ya san ya saukesu a Airport da sassafe. Sajid yace " my princess Uncle Ishola will take you to Salim's house now, Daddy will come and see you soon, okay?"

Ta girgiza kai tana fad'in " No, I want to go to Nazzy's house, I miss her"

Murmushin gefen baki yai yace " it's ok, he'll take you to Nazzy" 

Ta yi tsalle tana fad'in " yeeee!" hannunta ya kama ya mata pect a goshi sannan Ishola ya d'auketa suka tafi.

Duk d'okin ganin Yamin da takeyi sai jikinta yai sanyi ganin duk cikinsu babu wanda ya nuna alamun ya ganta, balle su mata magana, gashi ta kasa gane wanne ne Yamin wanne ne Yassar aciki saboda dama da maganansu take ganewa sai kuma Yassar ya d'an fi Yamin Fari amma sai ka lura sosai ka gane hakan. To yanzu kuma zaman prison ya dishashesu gaba d'aya.

Sajid da ya gama magana da Azra ta samu ta tambayeshi waye Yamin acikin su. Ya nuna mata shi, magana suke yi da Barrister da sauri ta k'arisa wajensu ta rungume Yamin tana fad'in " I'm sorry dear, I'm very sorry..." ba ta k'arasa maganar ba taji an turata gefe cikin 'bacin rai yake magana " wannan wani irin iskancine, kar ki sake ta'ba min jiki" da mamaki ta ke kallonshi ko dai Yassar ta runguma ne? Ta bayanta taji an ce "Iran lollipop" sannan aka k'yalek'yale da dariya, sunan da Yamin ke kiranta kenan ta juya cike da farinciki tace "Yam".

"Dalla bana son 'bata suna wai Yam kamar wani doya" ta ji Yassar ya fad'i wanda ta runguma d'azun.

Sokoko ta tsaya tana bin dukkansu da Kallo to wannene Yamin wannene Yassar a cikinsu.

Sajid ya murd'a kunnen Yassar yana fad'in "har yanzu ba ka ji ko"

"Ouch, ouch, Uncle Saj da zafi fah"

Sajid ya jashi har gaban Irene yace "wannan da kike gani shine Yassar. I guess he fooled you into believing shine Yamin"

Lallai ma all this while da suke tare ashe Yassar ne take d'auka a matsayin Yamin.

Sajid ya masa k'aramin rank'wasa a kai yace "Oya apologize to her now"

Yassar yai wiki wiki da ido yana kallon Irene bai ce komai ba.

Mr Isaac ya katsesu da cewa shi da iyalinsa zasu wuce hotel tunda komai ya warware yanzu. Sajid yace ai ba sai sunje sun kama hotel ba su wuce kawai gidan Alhaji Aliyu su sauka acan su ma idan sun gama duk wani paper work daya kamata nan zasu je.

Mr Isaac ya kama hannu Irene suka tafi bayan ya yiwa Sajid godiya.

....... A bangaren Zaytunah kuwa ta samu Amira matar Ahmad itama 'yar surutu ce, nan suka shiga hira tama manta da wani fishin da taga Sajid yayi da ita a court. Bayan tayi sallar Azahar taci abinci kiran Sady ya shigo wayarta. Sady ta tambayeta ko Sajid ya sauko daga fushin da yake mata.

"Lah wallahi wani close friend d'ina ne lokacin muna school muka had'u dashi a restaurant shine ya kawoni gidansa Muka gaisa da iyalinshi, yanzu nake shirin kiran My one d'in ma kika kira"

Sady tayi saurin cewa " Babez kar ki kirashi yanzu, he's probably busy now, ba kulaki zai yi ba ki bari irin da yamma d'in nan lokacin dai duk wani hidiman kotu ya gama"

Zaytunah tai murmushi " af kice dana tafka shirme, Thank you Babez duk yadda muka yi da shi za ki ji"

Lokacin da Sady ta ajiye wayar tayi murmushin mugunta tace " da sannu Zaytunah sai kin fitar da kanki a gidan Sajid"

***

..... Tana kwance kan gado tana karanta wani novel na James Hadley Chase mai suna ' Figure it out for yourself' ta ji muryan Azra na k'walla mata kira "Nazzy, Nazzy" mamaki ya kamata Ba Uncle Sajid yace yau Azra zasu koma Abuja ba, bata gama rufe baki ba Azra ta shigo d'akin da gudu, tazo ta fad'a jikinta tana dariya. Zihan ma dariyan take yi tana tambayarta ya basu tafi ba.

Azra ta sanar mata ai Mommy ce tace su dawo. Ziha ta mata murmushi, tana son yarinyar sosai d'an kwana biyu da suka yi tare yarinyar ta shiga ranta sosai.

Bayan sallar Azahar Ziha da Azra na zaune a falo suna zane a k'asa sunan Dr Sajid da Madam Bridget ta ji an fad'a a tashar silverbird da aka kunna, dama Mama ce ke kallo kuma ta tafi church. Ta yi saurin d'aga ido tana kallon TV d'in. Videon fitowarsu daga kotu aka saka sannan ana fad'in hukuncin da Alkal'i yayi. "Alhamdulillah" ta fad'i a zuciyarta lokaci guda kuma jikinta yai sanyi, kenan yanzu Uncle Sajid ya gama abinda ya kawo shi Lagos zai koma Abuja, shikenan ba zata sake ganinsa ba. Hawayene ya fara zubo mata k'ok'arin gogewa take yi kar Azra ta gani ai kuwa caraf Azran ta d'ago kai tana ce mata ta kalli zanen gidansu na Abuja data yi. Ganin Ziha na goge hawaye tace " Nazzy why are you crying?"

Murmushin dole Ziha tayi tana fad'in "I'm not crying dear, I'm not crying"

Azra ta cigaba da nuna mata tsarin gidansu amma hankalin Ziha baya wajen.

Chan ta tashi ta shige guest room, abubuwan da suka faru tun had'uwarsu da Sajid ta fara tunawa tana murmushi, ta isa wajen kayansa ta d'auko wani Jacket ɗinsa ta runguma tana shak'ar k'amshin turarensa, tabbas wannan Jacket ita ta saka mishi farkon zuwansa lokacin ciwonsa bai warke ba.

"Shikenan Uncle Sajid da ka tafi ba za mu sake had'uwa ba" ta limshe idonta hawaye na zuba. Ta sani cewa Allah ne kawai ya k'addara had'uwarsu amma Dr Sajid yafi k'arfin ta nesa ba kusa ba.

Ta tuno wasu maganganu da Papa ke yawan gaya mata lokacin yana da rai "Ife mi" (pet name nata kenan it means 'my love') "Rayuwa da kike gani rubutacce ne daga Rabbil Aalamin, komai da zai faru da d'an Adam an riga an rubutashi tun kafin a halicceshi. Kada ki ta'ba tunanin ba za ki kai wani matsayi ba ko kuma ba za ki rasa matsayin da kike dashi ba domin yau da gobe sai Allah. You can be what you never expected, you can meet whom you never expected, and your life could change from what you have to something you've never imagine. A koda yaushe ki kasance mai yawan godiya wa Ubangiji domin duk yadda rayuwarki ta kasance hakan shine k'addararki" ajiyar zuciya ta yi sannan ta shiga had'a masa kayansa tabbas ta san yanzu kam zamanshi ya k'are a gidansu.

***

.....Hajiya Zaytunah daga gidan Ahmad Dawaki gidan k'awarta Saudah ta wuce nan ma basu tsayaba suka shiga gari, k'arfe hud'u Mommy ta kirata tana tayata murnan case da suka winning dakewa ta yi kaman ta san zancen dan matuk'ar ta nunawa Mommy batasan zancen ba zata sha fad'a a wajenta.

"Yanzu yaushe zaku dawo Abuja?" Mommy ta tambaya.

Kame kame Zaytunah ta fara yi k'arshe tace " gaskiya Sajid bai yi maganar dawowanmu ba saboda akwai ayyuka da zai k'arasa"

Mommy taso gano wani abu amma ta yakice tunanin aranta tace " ki dai bi a hankali Zaytunah, banda yawo ki zauna kusa da mijinki ki bashi kulawar da ya kamata musamman yanzu da d'awainiya zai masa yawa" Zaytunah ta amsa da toh.

Maganan Mommy yasa ta d'anji jikinta yai sanyi tabbas Sajid yana buk'atarta yanzu. Kiran numbarsa ta yi har sau uku ba a d'auka ba, k'arshe ta ce da Saudah zata je gida.

Gidan Barrister ta fara zuwa ba sa nan matarsa tace ai tun safen basu dawo ba, gidansu Ziha take tunanin zata sameshi dan haka nan ta nufa......

...Koda suka zo gidan sun samu masu aiki basanan wani tsohon maigadin gidan kad'ai suka samu shima d'in idonsa baya gani sosai ne yasa aka mai da shi gardener.

Tun daga parlor Irene take mamakin yadda masu aikin suka yashe gidan, haka suka dinga bi suna duba satar da aka musu, ga gidan yai kaca kaca, harta kayan abinci na store duk an kwashe. D'akin da kawai basu iya shiga ba shine kawai ba a d'eba komai aciki ba, amma tun daga d'akin Madam B, Uncle Joe da matarsa, Emily har d'akin da Nickolas yake zama duk sun kwashe musu kayan sawansu da kayan amfani. D'akin su Yamin da Yassar dana Alhaji Aliyu kad'ai ba a bud'e ba suma saboda tun rasuwar Aliyu da aka kulle d'akunan ba a kuma bud'ewa ba keys d'in a hannun Madam B yake.

Dukkansu suna tsaye a falo cirko cirko, sun ma rasa mi za suyi. Mr Isaac yace ko zasu wuce su kama hotel kawai.

Irene tace ai idan suka yiwa Uncle Sajid haka basu masa adalciba at least tunda yace gidan zasu dawo gara su gyara musu gidan. Mr Isaac ya ce to sai dai a kira cleaning company suzo su gyara dan ba za su iya ba gidan yana da girma. Nickolas ya d'au waya ya kira cleaning company ya basu address d'in gidan.

Wajen garden suka fita kafin masu gyaran su zo.

Zama ta yi gindin wata bishiyar guava ta tafi duniyar tunani. Motsin mutum ta ji a bayanta ta juya da sauri. Murmushi ya mata sannan ya k'arasa turo kekensa ya iso saitinta yace " naji Daddy na cewa gobe zaku koma so I come to say goodbye"

Ta zaro ido tace "gobe kuma?, taya zan tafi na barka a wannan halin bayan nice silar faruwar hakan gareka"

" Kar ki damu nima jibi Mom da Sister Pearl za su zo daga South Africa so zan bi su chan"

" What of Aunt da Emily ya zasu yi?"

"Nayi waya da Aunt d'azu tacemin suna Imo wai Granny ba lafiya basu samu sun wuce America ba and tayi farin cikin da aka kama Uncle Joe saboda zama da criminal irinsa had'ari ne"

" It must be hard for her" Irene tace. Hannunta guda biyu ya kamo sannan ya kissing nasu duka biyu yace " I'm here for you my love" tayi saurin zare hannunta tace " you should be by Emily's side now, ta fi kowa buk'atanka yanzu"

Murmushi ne ya kubce masa dan ya gano kishi take yi, zaman jinyarsa da tayi a asibiti yasa sun saba sosai har yana ganin kota fara sonsa ne.

Tsokanarta yai yace " and you should be by Yamin's side now" ta d'aure fiska tace kar ya sake kiran sunan Yamin a gabanta. Yace " ok Yassar" wani ganye ta d'auka ta jefa masa yana ta mata dariya.

   Masu gyara sunzo sun gyara ko ina, gidan yai kyau. Mr Isaac ya musu order abinci suka ci sannan Irene da Nickolas suka fita siyan kayan abinci da kayan sawanta saboda dik kayan sawanta itama an kwashe.

.... Sajid sai k'arfe uku suka zo gidan nanma dai kawai dan yasan Yamin da Yassar suna son hutu ne yasa suka dawo amma ba wai sun gama abinda ya kamata su yi bane, daga kotu kamfanin Marigayi suka je saboda Nan ma akwai crisis gashi wasu major investors d'insu suna son fitar da shares ɗinsu. Brief meeting suka yi ya tabbatar musu da cewa gobe zasu zauna a tattauna duk abubuwan da suka faru da kuma yadda za a magance koma bayan da aka samu a kamfanin.

Yana zuwa Mr Isaac ya sanar dashi halin da suka samu gidan da kuma gyaran da aka yi. Mr Isaac yace ya sanarwa police a nemo masu aikin nan, Sajid yace ya barsu rabonsu suka ci kawai, ba abinda suka sata da zai ja hankalin mutum bane a k'yalesu kawai.

Yamin da Yassar wanka suka yi suka chanja cikin wasu k'ananun kaya da Sajid ya tsaya suka siya kafin su iso gidan, dama tuni sun ci abinci sai baccin gajiya kuma ya d'ebesu rabon da su kwana a gado haka tun kusan wata shida da suka wuce.

Irene suka dawo suka shiga da kayan abinci ciki ganin Sajid agidan yana aiki da Laptop a parlor ta san su Yamin sun dawo gaba d'aya haushinsu take ji musamman Yassar daya mata k'arya.

Yana duba wasu documents na kamfani da aka tura masa kiran Zaytunah ke shigowa ya share, kusan 30mins sannan ya rufe laptop d'in ya kira Zaytunah.

" My one kana ina Dan Allah yanzu na bar gidan Barrister ina hanyar gidansu wad'ancan Arnan"

"Kin gama yawo da auren nawa?"

"I'm sorry My one and only, wallahi d'azun da kace idan na kuma ta'baka zaka mareni nasan ranka ya 'baci shiyasa na baka time ka sauko, Dan Allah kana Ina?"

"Zaytunah" ya kira sunanta da kakkausan murya. Jin irin kiran daya mata yasa ta nitsu ta san matuk'ar ya kirata da irin haka he's very serious.

" Akwai jirgin da zai tashi Lagos zuwa Abuja k'arfe shida na yamma yau d'in nan, idan ni Sajid Usman nina biya sadakinki shekara goma da suka wuce toh ki bi jirgin nan ki koma Abuja ki je ki kularmin da Nurain da Aamir kafin na dawo idan kuma kin gaji da amsa sunan Matar Sajid to kiyi zamanki a Lagos kiyi duk abinda kike so"

Wani yaar taji ajikinta jin kalaman Sajid, kawai ta fashe da kuka tana cewa " haba my one mi yai zafi da irin wannan magana haka"

"Azra zata zauna dani har na dawo" abinda yace kenan ya katse kiran.

Sake kiranshi tayi amma yak'i d'auka k'arshe ma numbarsa ya dena shiga, cikin kuka tace taxi driver d'in ya juya da ita airport.

Zuciyarta cike da tunani kala kala wai mi ta yi nema da Sajid zai gaya mata wannan mummunan maganan kawai dan yace ta koma Abuja ta k'i. Ta share hawayenta tace gaskiya k'aran Sajid za ta yi wajen Alhajinsu ya mishi magana ya dena threatening d'inta da rabuwa da ita, haba!...

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.