Free chapter · Read without an account
32
*MUTUM.....Mugu ne*
32
"Wannan shawara shine kawai abinda ya kamata ka yi amma babu wata mafita gareka, domin daga sama babu wanda zai sa maka hannu ka binciki Alhaji Kadi"
SY ya ce "Nagode Sir zan yi abinda kace and kafin wata uku su cika I'll get to the bottom of this" shaking hannun Ogan nashi yayi sannan ya fice daga office d'in.
Nasa office d'in ya shiga sannan ya fara typing request letter da zai bayar kamar yadda Oga ya bashi shawara, shekara uku kenan rabon da yaje leave dan haka zai nemi leave na wata uku idan har an granting masa, zai yi amfani da 3 months d'in nan ya binciki Alhaji Kadi da kuma abinda ya samu AY...
....... BAUCHI.......
Laure tunda Shamsiyya ta fita sai da ta yi awa uku kwance ta kasa tashi ga bak'in cikin abinda 'yarta ta aikata mata ga mummunan labarin da ta ji wai Sulaiman zai yi aure. Da rarrafe ta ke tafiya bayan ta mirgino daga kan gadon, ta samu ta fita daga d'akin ta isa kitchen ba abinda ta gani da zata iya ci batareda ta girka ba, gashi bayanta ya rik'e daga ta yi k'ok'arin mik'ewa sai ta ji wata irin azaba na fizgarta.
Kwalin Indomie da ta gani ta jawo ta bud'e ta fasa ledar d'aya ta fara ci k'urmus k'urmus sai da ta ci Leda biyar sannan ta hak'ura ta rarrafa da k'yar ta koma d'aki, tana so ta wanke jikinta saboda najasar Chief Augustus dake jikinta amma tana tsoron mik'ewa. Wata Umbrella ta gani acan k'uryar dak'in dan haka ta rarrafa ta je wajen ta dafa lemar ta samu ta d'an mik'e sai da ta k'walla k'ara saboda azabar da ta ji, ta samu ta shiga band'aki a daddafe ta fara wanka.
.......
Rana bata k'arya yau Asabat kuma yau ne d'aurin aure. A masallacin dake unguwarsu Zahra aka d'aura auren Dr Sulaiman da amaryarsa Fatima Zahra k'arfe shad'aya na safe bisa sadaki dubu ishirin.
Mafi yawancin abokanan Zahra lokacin da ta yi ATBU sun zo d'aurin aurenta mazan da matan, wasu sai lokacin suke jin ashe ita bazawarace.
Mai kwalliya Nazira ta d'auko ta zanzara mata kwalliya. Wata farar lace Zahra ta saka anyi d'inkin gown, sai head golden color, purse d'inta da silhouette takalminta suma golden ne.
Bayan an dawo daga d'aurin aure ta fito ana hoto da 'yan uwa da abokan arzik'i 'yanuwan tsohon mijinta ma ba a barsu a baya ba duk wanda suke mutunci har yanzu sun zo, Yayan mijinta wanda ke rik'e da yaranta shima ya zo auren gudummawar dubu talatin ma ya bata.
Malaman makarantan da take koyarwa ma ba a barsu baya ba suma sunzo kuma sun had'a mata gudummuwa suma.
Anyi hotuna sosai na tarihi Amarya tayi kyau sosai ba k'arya saidai kash ba angon a wajen.
Nazira tana kiran Abba ko zai zo ayi hoton da shi amma bai d'auka ba, shima din yana chan k'ofar gidan Baba ana 'yar kwaryakwarya reception a k'ofar gidan saboda abokanansa da suka zo.
Da yamma aka yi walima, Malama Juwairiyya suka kira ta yi wa'azi sosai gameda zamantakewar aure.
Abba bai samu hutawa ba sai kusan sha biyun dare saboda hidiman bak'i da yai ta yi. Kaman da wasa ya bud'e datar shi ya shiga WhatsApp, messages suna ta shigowa wanda yawanci sak'on taya murya ne. Sak'on Nazira ya bud'e hotuna ne sun fi talatin a hankali network ke bud'e masa su, hotunan amarya Zahra ce da aka yi safiyar yau dana wajen walima. Yawancin ita kad'ai ne sai wasu kuma da 'yan uwanta da abokananta mata. Wani hoto da ya bud'e yanzu ne ya sashi tashi zaune ya lalumo reading glasses ɗinsa ya saka ya cigaba da kallon hoton, Zahra ce da wasu maza biyu sun d'an manyanta tana tsakiyarsu akayi hoton, daga nan kuma ya sake ganin wasu hotunan tareda maza wasu ita d'aya cikin maza wasu kuma da k'awayenta. Wani kishine ya tasammasa ba shiri, yaushe Zahra ta yi wannan bai sani ba. Haka kawai ya rasa dalilin jin haushin abinda ya gani. Ya fi minti goma zaune ya kasa yin komai, yana son kiran Zahra ya mata fad'a wata zuciyar na hana shi. Daga k'arshe dai kasa hak'uri yai ya kira numbarta har yanzu sunan da Nazira ta masa saving da shi ne ajiki bai chanja ba.
Kiran farko ba a d'auka ba, hakan ya sake kufular da shi sai a na biyu aka d'auka, yanayin muryanta ya tabbatar masa barci take yi sa'ilin da ta mai sallama tana gaishe shi.
Bai amsa ba kawai ya fara masifa, da agabanta yake k'ila sai ya maketa.
" Yanzu Fatima da iliminki da hankalinki ki shiga tsakiyar maza ki yi hoto, ba hijabi ajikinki ba komai, kamar ba Hafiza ba, Ina amfanin Islamiyyar da kika yi tunda da aurenki zaki shiga tsakiyar maza kiyi hoto"
" Tukunna su wayema wadannan d'in? Miye hadinki da su? "
Tun da ya fara fad'a idonta ya ciko da hawaye, muryanta na rawa tace " Yaya kayi hak'uri Dan Allah"
"Su waye nace?"
A hankali ta furta "Baffansu Fadil ne da abokinshi"
"Kin san iya kacin wajen da hotonki zai tsaya? Ko kin san mazaje dayawa zasu gani su ji sha'awarki a haka ba hijabi ba komai kowa ya kallemin mata ya ga tsarin k'irar da Allah ya mata. Allah wadai da abinda kika yi, ban yarda ki sake d'aukan hoto da kowa ba, idan har ya zama dole sai anyi hoton koda da macene to ki wadata jikinki da hijabi"
Hak'uri ta fara bashi cikin kuka, Bai so ya sa ta kuka ba sai dai dole ne ya taka mata birki tun yanzun kar ya zamto idan ta tarema ta samu aiki zata rink'a sakaci da irin wannan.
"Shikenan ki dai kiyaye" daga haka ya kashe wayar.
Nazira da ke d'akin ta dafa kafad'arta saboda gado d'aya suka kwanta. Tace "Anty kiyi hak'uri, kishi alamar so ne, Abba kishinki yake yi, he didn't mean what he said "
Zahra ta goge hawayen fiskarta tace "lah ba komai wallahi, ai gaskiya ya fad'a mini"
Text ta tura mishi tana mai bashi hak'uri. Murmushi yai bayan ya karanta text d'in dan bayan ya amayar da abinda ke cikinsa sai ya ji sanyi a ransa.
Washe gari Lahdi da yamma Abba zai wuce amma Nazira sai Tuesday zata dawo.
Abba ya shigo ya gaishe da Inna da wasu manyan 'yanuwansu da suka zo hidimar biki,tareda Ibrahim ma yake bayan sun gama gaishe gaishe suka fita. Ko inuwar Zahra bai gani ba agidan har suka fita.
Har ya koma ma dai ba wani communication tsakaninsu. Yau Nazira zata dawo saboda itama ta sake kintsa gidansu kafin amarya ta tare. Su biyune a d'akin, a hankali Nazira ta warware mata abinda ke faruwa agidan nasu tun daga abinda Laure ta musu har yadda Waheeda ta rasu da rashin lafiyar Abbansu da kuma abinda suka yi har Abba ya amince da auren.
Tun da ta fara labarin Zahra ke zubda hawaye har ta gama. Jin rashin imani da Laure ta gwada musu ya girgiza Zahra matuk'a.
Cikin kuka take cewa " ashe akwai mugayen mutane aduniya irin Laure, ya Allah kasa mu fi k'arfin zuciyarmu amin"
Nazira ta sa hannu tana goge mata hawaye tareda cewa " Haka Allah ya tsara mana, ni dai rok'ona Dan Allah ki taimaka ki zama mace ta gari a wajen Abbanmu, ki maida masa farin cikin da ya rasa. Na san Abba yanzu yana d'ari-d'ari da maganar mace amma ina so ki daure ki jawoshi gareki domin idan kika ce sai ya nemeki tukunna, bana tunanin nan kusa hakan zai faru sai dai ki d'aura d'amaran shiga zuciyarsa kota halin k'ak'a ne, da wannan za ki yi nasara saboda Abba mutum ne mai saukin kai da tausayi"
"Insha Allah Nazira zan kawo farin ciki a rayuwar Abbanku"
Rana bata k'arya yau Jumu'ah, ranar da Zahra zata tare. Mota ce d'auke da kayanta sai ita da Uwargidan Yaya Ibrahim da kuma wata k'anwar Inna. Shatar motar suka yi daga Azare har k'ofar gidan mijinta dake Bauchi. Da wuri suka iso sha biyu ta gota kad'an, aka sauke kaya aka shiga da su. Nazira da Anty Amina k'anwar Abba su suka tar'ba amarya Zahra, kayanta wasu sun shiga d'akin da aka bata wasu kuma dole d'akin da Shamsiyya ta zauna aka jibgasu, saboda dama d'akin da furnitures aciki. Da yamma wanda suka rako amarya suka wuce Azare.
Abba bai dawo ba sai bayan Isha ya tadda Amarya ta iso. Bayan gaisawa da suka yi bai ce komai ba ya wuce d'akinsa. Duk yadda Nazira ta yi akan ta kai masa abinci d'aki ta k'i wai kunyar Anty Amina take ji.
Bayan sun ci abinci anyi hira ta shige d'aki ta kwanta tana tunanin ta inda zata fara jawo hankalin Abba kanta.
Washe gari bayan sun karya Anty Amina zata wuce ita da Nazira.
"Amma Dan Allah Nazira mi zakiyi a Kano har na sati biyu ni da ban saba da gidan nan ba ki barni ni d'aya"
Nazira tayi dariya "ai ba ke d'aya bace ga Abba. Ni dai kafin sati biyun nan Dan Allah ki tabbatar komai ya kankama" Zahra ta harareta.
***
ABUJA
Zaytunah da yamma ta iso gidan su, abin mamaki tana fitowa daga mota ta hango Aamir da Nurain suna ball, basu ma ganta ba sai da ta k'walla musu kira sannan suka taho da gudu wajenta suka rungumeta. Tambayar Aamir ta yi mi ya same shi yace mata ba komai. To mi Mommy take nufi da ta min k'aryan wai Aamir ba lafiya?. Ta dai daure ta k'arasa ciki su kuma suka ci gaba da ball d'insu.
Direct d'akinta na gidan ta shiga ta ajiye bag d'inta sannan ta fito ta nufi d'akin Mommy, bata sameta a ciki ba dan haka ta kira wayarta sai ta ji wayar na ringing a d'akin ta d'an ja tsaki ko ina mommy ta shiga kuma oho. Ta fito ta nufi sashen Daddy, a falonsa ta samu mommy na wajen dining tana jera abinci. Ta k'araso ta rungumeta "Mommy ke dai koda yaushe sai kice da kanki zaki shiryawa Daddy abinci bayan ga masu aiki"
Mommy tace " ba zan bari mai aiki ta shigan mini turakar Mijina ba, ta yi aiki a ko ina amma banda nan"
"Kayya mommy an girma fah"
" To sai me"
Mommy bata nuna mata ta san mi ta je yi a Jalingo ba, sai ma ce mata tayi akwai sak'on da zata bata ne shi yasa tace ta zo yanada muhimmanci shiyasa ta mata k'aryar Aamir ne ba lafiya.
Sai bayan sun ci abincin dare sannan ta kira Zaytunah d'akinta. Fad'a sosai ta dinga yi mata bisa wautarta.
" Haba Zaytunah Allah ya ba ki miji irin Sajid amma kina chan kinata yin shirme, mi kika nema kika rasa, babu ta inda Sajid ke tauye miki hak'k'inki sai ke ce za ki dinga bijire masa kina abinda kike so. Yanzu inba wauta irin taki ba at his age wai har kina kai k'aran Sajid wajen iyayenshi. Su mishi me?"
" Amma mommy...."
" Ki min shiru, Wallahi idan baki nitsu kin gyara halinki ba, nan ba America bane cikin sauk'i wata zata zo ta k'wace miki miji, kin tsaya kina shirme"
"God forbid Mommy, Sajid nawa ne ni kad'ai"
" Kin iya Sajid nawa ne amma baki iya yadda zaki rik'eshi ba. Wallahi ki gyara halayenki, ina jiye miki tsoron ki tura Sajid bango ya miki abinda ba ki so"
Shigowar Daddy d'akin ya sa duk suka yi shiru, Zaytunah tana tsammanin Daddy zai goyi bayanta sai ta ga shima zama yai ya fara mata nasiha sai dai shi a hankali yake mata ba kaman Mommy da take magana kamar zata maketa ba.
Abu d'aya ya shiga k'wak'walwar Zaytunah a duk maganan da suka mata shine zuwa kai k'aran Sajid da tayi bai dace ba, wannan kam tayi dana saninsa, musamman yadda Daddy yayi ta mata misali da zaman aurensu da Mommy duk abinda ya faru tsakaninsu suke zama su warwareshi ba wanda ke jin kansu. Amma sauran kam bata yarda tayi abinda bai dace ba, miye aciki idan kayi missing mijinka ka je ka sameshi, miye aciki idan mijinka yace ka tafi amma kuma sai ka ga zaman naka shi yafi dacewa ba tafiyarka ba.
Bayan sun had'u sun mata nasiha mai kama da fad'a ta basu hak'uri. Bayan fitan Daddy, Mommy ta sa dole ta kira Sajid ta bashi hak'uri bai d'auka ba har sau biyu sai ta tura masa text, text d'in ma sai da Mommy ta gani tukunna ta yarda ta tura masa, tace kuma ta sake gwada kiransa anjima.
......LAGOS......
A kamfani sun samu matsaloli sosai, babban abinda Sajid ya fara shine meeting da wasu investors da ke shirin janye shares ɗinsu, sai da ya tabbatar sun janye kudirinsu kafin ya koma ga sauran abubuwan. Gaba d'aya shi da 'yan biyu basu samu dawowa gida ba sai kusan k'arfe goma na dare, dan ma Azra agidan Barrister ya barta anan zata kwana. Lokacin da Zaytunah ta kira shi ma meeting yake yi shiyasa bai d'auka ba.
Har ya kwanta kiran Zaytunah ya sake shigo masa bai d'auka ba sai ya tura mata text:
*Na ga text ɗinki, maganan nan bata waya bace sai na dawo zamu zauna ayi ta*
Daga haka yasa wayar a silent sai bacci.
......
Daddy ya kira Ziha ya gaya mata abinda Sajid yace da kuma abinda AbdulBar ya gaya masa kuka ta saka jin AbdulBar ya san tana nan har shekara d'aya amma basu ta'ba waya ba, tayi missing d'insa sosai. Anan Daddy ya kira shi ya bata wayan suka yi magana. Sun jima suna magana kafin daga bisani ta kashe wayar.
Abinda ya faranta mata rai shine bata riga tacewa Uncle Sajid zata kar'bi kud'insa ba, da yanzu zai dinga mata wani gani gani.
Daddy ya zauna da iyalensa sunyi shawara bisa maganar da Sajid ya kawo, yana neman ya bar aikin da yake yi ya koma kamfaninsu Yamin da aiki. Bayan tattaunawa da yayi da iyalinshi ya concluding zai bar aikin amma sai bayan wata d'aya idan ya bada notice a Mai hotel din.
Sajid bai samu komai ya daidaita ba sai ranar Jumu'ah, duk wani abinda ya kamata yai ya yi shi har wata rama yai saboda zirga zirga. Office din Daddy ya je da Ishola akan ya musu kwatancen gidan Alaji AbdulWasi'u Saboda Saturday da sassafe zasu wuce Ilorin.
***
ILORIN
Gida ne babba irin ginin da, Ishola ne ya yiwa wasu yara da suka gani a waje magana da yarabanci, suka ce ai Alaji yana masallaci saboda sun zo daf lokacin Azahar ne. Yaran suka raka su har masallacin ba nisa sosai ma da gidan, ana shirin shiga sallah suka iso dan haka Sajid shima ya nemi buta yai alwala saboda Ishola ba musulmi bane. mutanen wajen sai kallonsa suke yi suna gulma da yare. Da yai alwala ya shiga masallaci aka yi sallah da shi bayan an idar ya tashi yai nafila yana rok'on Allah yasa Alaji AbdulWasi'u ya amince masa.
Azkar yake yi yana lura da yadda ake kallonsa ana k'usk'us, mutane k'alilan ne suka rage a masallacin. Wani saurayi ya ta'ba kafad'arsa ya masa magana da turanci wai ya k'arasa wajen wani tsoho dake chan gefe yana jan tasbaha. Ba musu ya tashi ya je wajen, mutumin ko kallonshi bai yi ba ya cigaba da abinda yake yi tun Sajid na ganin time har ya hak'ura ya turawa Ishola text cewa zai kira shi idan ya fito yaje ya ci abinci kawai.
Sajid ya yi tunanin tsohon nan shine Alaji AbdulWasi'u, ko ba shi bane ma dai ya kai ya jira shi d'in dan ak'alla zai yi 85yrs. Shiru shiru Alaji bai kula shi ba kawai ya gyara zama ya fidda tasbaha shima ya cigaba da Azkar. Suna nan zaune har ya saura su biyu cikin masallacin still Alaji bai ce komai ba haka Sajid bai tafi ba. Suna nan har la'asar ta yi, aka shiga Sallah sai da aka idar kusan 15mins sannan masallacin ya watse saura su biyu still. Sai a lokacin Alaji ya juyo ya dubi Sajid ya ce masa cikin harshen turanci ko shi Arab ne.
Sajid yai murmushi ya ce masa Babanshi Bafulatani ne mamanshi 'yar k'asar Ethiopia. Alaji yai murmushi yace su tashi su je gidanshi. Ba musu ya tashi suka tafi, a falonsa wadda rug ne kawai shimfid'e a wajen sai tarin littattafai da jaridu aka kawo musu abinci da ruwa mai sanyi. Alaji ya masa Bismillah yace kodai bai iya cin amala ba yasa albarka a naman dake cikin miyan. Ga mamakinsa sai ya ga Sajid ya nad'e hannun riga ya wanke hannunsa cikin roban wanke hannu da aka ajiye, ya ɗebi loman Amala ya fara ci, Haka suka sa hannu suka cinye abincin tas. Bayan an tattare wajen Sajid yai bayanin koshi waye da kuma abinda kawo shi. Alaji ya riga ya san da zuwan nasa dan Daddy ya riga ya sanar da shi.
Alaji yai gyaran murya sannan yace " na gwada hak'urinka d'azu kuma na same ka mai hak'uri. Domin zama da d'an da ba naka ba sai da hak'uri kuma na yarda zaka rik'e Naziha rik'on amana, na sameka marar girman kai, mai girmama d'an Adam, kuma qualities ne da yake da wuyan samu musamman awajen masu arzik'i irinka"
Murmushi bayyane a fiskar Sajid ya shiga yiwa Alaji godiya daga bisani Alaji da kanshi ya rakashi waje inda Ishola ke jiranshi su wuce Lagos
......LAGOS......
Basu shiga Lagos da wuri ba sai kusan 11 na dare dan ko shi Isholan agidan Marigayi ya kwana.
Washe gari Sunday ya kira Zaytunah akan ranar talata yana nan tafe da 'yan biyu yace tasa a gyara d'akin k'asa sannan a gyara d'akin sama na gefen Azra.
" Wa zai zo kuma bayan 'yan biyu?"
"Just do as I say, idan kuma abinda kika saba za ki yi Bismillah" daga haka ya kashe wayar.
Da dare ya je ya d'auko Azra suka wuce gidansu Ziha, ya sanar da Daddy yadda suka yi da Alaji, Daddy ya riga ya sani saboda AbdulBar ya gaya masa komai. Daddy godiya ya masa tareda cewa "na san Funmilayo bata da matsala amma idan ka ga tana abinda bai dace ba ka mata fad'a" Sajid yai alkawarin kula da Ziha tamkar yadda zai kula da Azra.
Sajid ya sanar dashi ran Tuesday za su tafi saboda akwai meeting da zai yi Monday sannan jirgi zasu bi Monday d'in zai booking flight wa dukkansu. Daddy ya sake yi masa godiya.
Azra ya kira amma ta k'i fitowa, daga baya data fito tace a nan zata kwana ba za ta bishi ba. Dole ya amince yana son ganin Ziha amma tun da ya zo gidan take d'aki. Haka ya musu sallama zai fita Daddy yace ya tsaya Ziha ta mishi godiya, ya fara wani fulaku wai a barta kawai ai ba komai yai ba nan kuwa k'asan ransa yana so ya ganta dama.
Daddy ya k'wala wa Ziha kira yace maza ta fito ta mawa Sajid godiya. Ta riga ta saka kayan bacci dan haka ta d'au hijab ta fita, karo suka yi da Gbenga dake shirin shigowa d'akin. Wani kallo ya mata dan tunda Daddy yace mata Alaji AbdulWasi'u ya amince ya ga tana wani annashuwa da maganan shi kuma haushin hakan yake ji, da yana da iko da zai hana tafiyar Ziha Abuja.
Tsaki ya mata sannan yace" awon iyawo Sagid" kamar yadda yake kiran sa Sagid instead of Sajid.
Murmushi ta yi sannan ta ra'ba gefenshi ta wuce, da ta fito Sajid ya riga ya fita dan haka waje ta bishi. A gindin motar da ya zo da shi ta sameshi yana jingine. Sai da ta iso kuma ta ji wani kunyarshi ya kamata. Ta sunkuyar da kai ta gaida shi.
" Wato da ba za ki fito mu gaisa ba ko, saboda na je na nemi izini dole za ki bini Abuja ko, saboda bakison zama da d'an Fulani"
Ta girgiza kai
Yace " to minene?"
" Uncle ....Thank you"
"Naziha....ki cigaba da zama yarinya mai hankali kamar yadda na san ki kin ji, tsakanina da ke babu godiya"
Shiru ne ya biyo bayan maganarsu ba wanda yace komai, ita dai ta sunkuyar da kai amma shi idonsa kyam akanta.
Chan yace "tafiyarmu ranar Tuesday, idan na sayi ticket zan gaya miki time d'in da jirginmu zai tashi"
Sai lokacin ta d'ago " uncle flight za mu bi! Ban ta'ba shiga jirgi ba"
Murmushi yai sannan yace " to zaki fara daga Tuesday Insha Allah" bani numbarki so that na kiraki na gaya miki.
Ta shiga karanto masa numbobin yana dannawa da ya gama ya saving da suna *Zeeha*
" Je ki kwanta dare yayi, zan aiko Ishola ya zo ya d'auki Azra gobe da safe" tace to
Binta yai da ido har ta shiga gida sannan shima ya shiga mota ya wuce.
......