Free chapter · Read without an account
Shafi na uku
_*🌻TANI DA MANU 🌻*_
_(Labarin TANI DA MANU jikokin mai gari tsabiban yara masu bada nishad'i soyayya da kuma zallar dariya domin nishad'in ku masoyana)_
LABARI DA TSARAWA
_*SARAT ALK'ASUM ( Maman Nusaiba ce)*_
*Marubuciyar*
_AMEER DA AMEERA_
_ALJANAR JARUMAI_
_HAFSAT_
_K'ADDARA CE_
_and new book_
_TANI DA MANU_
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
Wannan shafin na sadaukar gareku
_*Khadija s Abudullahi: Tsohuwa mai ran k'arfe ki dade kiyo k'arko💃🏼*_
_*Ummu Ahamed: My Aminan Addaty na😍*_
بسم الله الرحمن الرحيم
5️⃣⏩6️⃣
Suna k'arasawa bakin kofar gidan sukaji d'an Yarbawa yana zindima ihu a kawowa Matar shi dauki zata haihu.
TANI tace" Yauwa yanzu abinda za'ayi zan shiga kamar ni ingozoma ce zan karb'i haihuwa, to daga nan kuma sai ku shigo.
MANU yace" Shegiya tawa ashe dai kin iya dibara to yanzu fara shiga sai mu biki a baya ko, kuma kinga Iyatu na koya miki yadda ake karb'ar haihuwa ai kin iya, kije ki taimaka mata ni kuma sai mu shige d'akin shi. ( Kasancewar Iyatu ita ke karb'ar haihuwa a k'auyen ,to in zata je tare suke zuwa da TANI tin bata so har ta saba wani abun ita ke yi, ta iya yanke cibiya har Yaro ta iya mishi wanka).
Murmishi TANI tayi tace" Eh mana sosai na iya yanzu zan shiga na taimaka mata, ku kuma sai ku shige d'akin shi, naji wannan mahaukacin d'an Yarbawan yana kwarara mana ihu" Tana fad'in haka tayi
cikin gidan tana sallama.
Da gudu d'an Yarbawa ya fito yana fad'in" Waiyo Allah mun shiga bakwai yo shikenan Matan mu zai mutu ya barmu, dan Allah mai dauka haihuwa ki taimaka min Matan mu ne zaiyi kashin Yaro shine duk ya fita ganinshi, yanzu haka baya magana sai juya kai yake yak'i yayi kashin Yaron ko ya huta .
TANI kunshe dariyar ta tayi jin abinda yake fad'a wai Matar shi zatayi kashin Yaro abin dariya ma.
Kallon shi tayi ta canja murya tace" Karka damu bari naje wajan ta yanzu jeka ka samo mana reza da sabulun wanka tinda dare baiyi sosai ba.
D'an Yarbawa yace" Waiyo Maman mu ki taimaka wa Mata namu yayi kashin Yaron nan.
Murmishi TANI tayi tace" To maza fita ka siyo abinda na fad'a maka.
A guje ya fita yana fad'in" Maman mu kiyi k'okari abin bauta ya taimake ki Matan mu kiyi kashin Yaro, ina sonka bana so na rasa ka abin bauta ya hana ka mutuwa.
Dariya TANI tayi tace" Kai Wallahi D'an Yarbawa sai a hankali.
Dakin ta shiga ta samu Matar d'an Yarbawa tana nishin haihuwa, duk ta jigata.
Da sauri ta matso kusan ta tace" Dafani kiyi nishi da k'arfi.
A galabaice ta dafa TANI tana sumbatu tana fad'in" Yesu ka taimakeni yesu ka fito min da Yarona lafiya.
TANI tace" Ke dalla cen bahuwa waye kuma wani yesu koda yake ai ku ba irin mu bane dole ki kira yesu kinji azaba, gobe ma sai ki sake komawa ya miki cikin kwartuwa kawai, ince dai shekarar ki d'aya da haihuwa amma wai har kika sake haihuwa, wato kwanika ma kike yi ai kuwa zaki sha wahala da K'ananan Yara.
Haka tayi ta masifa ta riketa gam tana fad'in tayi nishi ko ta haihu.
************************
Su MANU ne suka shigo ganin D'an Yarbawa ya fita da gudu yana sumbatu.
Suna shiga TANI tace" Yauwa munafikin naji yanzu ya shiga bandaki kuje Bintalo zo mu zauna a nan tare da ke.
Bintalo shiga d'akin tayi ,su kuma suka shige d'akin Malamin nasu.
Suna shiga suka rakube a bak'in k'ofa suna jiranshi.
Ya fito daga bandaki ya wanke hannun shi tukun ya shige d'akin.
Yana shiga yaji an banko k'ofar an mata key.
A tsorace ya soma k'okarin lalibo wayar shi dan ya haska yaga meye ya rufe mishi daki.
Lalibe ya soma amma baiji wayar ba, yana juyowa yaji an wanke shi da mari guda biyu masu shiga Fata.
Ihu ya kurma ji yayi ance mishi shiiii.
Da sauri ya kyale yana zare ido.
MANU ne ya lalibo farar faudar dake aljihun shi ya shafa ya ba su Furera suka shafa, fitilar shi ya dauko ya haske fuskar su suka zaro mishi ido kamar Aljanu.
Zabura Malamin nasu yayi yace" Innahu Suleimanu wa innahu Bismillahi rahamani Rahim ku kuke ganin mu ba mu muke ganin ku ba, dan Allah me na muku ne haka?
MANU ne ya soma magana da kakkausar murya irin ta garadan Maza yace" Kai dakata mugu waye yace ka daki jikokin mai gari? To yau sai mun kashe ka.
Baya ya soma yi yana girgiza musu kai yace" Kuyi hak'uri ban san su Abokan aljanu bane, kuma daga yau nayi muku alk'awari bazan sake dukan su ba.
Furera ce tayi muryar tsofaffi tace" Kai ja'irin Malami yau sai mun dauka musu fansa na dukan daka musu, gobe idan ka gansu ka durkusa har k'asa ka basu a Hak'uri.
Da sauri yace" To shikenan zan basu amma karku dakeni wallahi na tub..
Baik'arasa ba suka rufeshi da duka tako ina.
Ihu yake yana neman taimako amma sai MANU yace" Idan ka kuma yin ihu to zamu kaika cen duniyar mu ta aljannu , idan kaje kai da ganin bil'adama har abada.
Da sauri ya kama bakin shi yayi gum yana ji suna zane shi sai hawaye yake saboda dukan yana shigarsa sosai, gashi Kuma ba dama yayi magana su daukeshi daga duniyar mutane.
Saboda tsananin mugunta irin ta su MANU sai da suka dauko Riza MANU na wata mahaukaciyar dariya yace" Ka rufe idonka zamuyi maka kwal akwabo, idan kuma ka bude ido to zamu fille maka kai ne.
Kwalalo ido yayi yana girgiza kai jin wai shi d'an gayu za'a yiwa askin tsofaffi, rufe idon shi yayi yana k'yarma.
Murmishi mugunta MANU yayi ya fiddo Reza sabuwa fil, dama sun dauko sabulun su tin daga gida, ruwan da ya aje zaisha da shi suka jik'a mishi sumar kanshi.
Sabulun suka goga mishi nan MANU ya bawa Goga fitilar yace ya hasko mishi.
Amsa yayi ya haska mishi nan suka aske mishi sumar kanshi tass kamar tsoho.
Suna gamawa suka kashe fitilar MANU ya maki kan yace" Kwal Uba aradu kafi kyau a haka wa yaga Sale, kaga kanka yadda yake walk'iya kamar kayi wankan man gyada.
Shi dai baice komai ba inba hawaye ba ba abinda yake yi.
Furera tace" Rufe idon ka dan Ubanka.
Da sauri ya rufe kanshi da bargo ya k'ank'ame jikinshi, saboda wani mugun tsoro ne ya shige shi, yau shine Aljanu suka yiwa aski.
Fita sukayi da sauri suka ce mishi karya kuskura ya leko waje inba gari bane ya waye, idan ya kuskura ya leka to duk abinda ya gani ji shiya jayo.
Da sauri ya shiga bargo ya rufe duka jikin shi.
************************
A b'an garan TANI da Bintalo kuwa, su MANU na shiga d'akin sabon Malamin su Matar d'an Yarbawa ta haifo Y'ar ta Mace, cike da murna TANI ta dauki Yarinyar daga cikin jini ta yanke mata cibiya, wani zane dake kusan ta ta dauka ta gogewa jaririyar jikin ta Yarinyar sai tsala kuka take.
Bintalo tace" Kut kaji Yarinya daga zuwan ki duniya sai kuka dama haka kowa yake zuwa?
TANI tace" To sangadan ware wayace miki idan jariri yazo duniya baya kuka, ai in baiyi kuka ba ma har ruwan sanyi ake zuba mishi dan yayi kuka, tashi ki daura tukunya ayi ruwan zafi a wanke jaririyar Uwar itama tayi haka nake gani Iyatu nayi idan muka je karb'ar haihuwa.
Bintalo tace" To tukun ta dauki babbar tukunyar Matar d'an Yarbawa ta daura akan murhu ta had'a ita ce ta zuba ruwa dayawa, wuta ta kunna tukun ta dawo d'akin.
Bata jaririyar TANI tayi ta gyara wajan da akayi haihuwar itama Uwar ta bata wani zanan ta daura sai layi take saboda babu k'arfi a jikin ta.
TANI tace" Bude idonki kiga Y'ar ki k'atuwa da ita mashaAllah.
A k'yar ta iya bude idonta ta kalli jaririyar ta maida kanta ta kwantar.
Suna nan zaune ruwa ya kusa tafasa TANI ta samu babbar robar wanka da ta gani a d'akin takai bandaki.
Ruwan tazo tana dauka a k'aramar roba tana kaiwa sai da yayi saura kad'an tukun ta bari, ruwan sanyi tasa ta silka ruwa yadda zata ita wanka.
Dakin ta dawo ta tasheta ta rakata har bandaki, kallon Ta tayi tace" Ga kujera ki zauna sai ki kiyi wankan zaki ji karfi, kuma idan ruwan yayi rabi sai ki shiga ki zauna sai ya huce tukun ki fito, haka naga Kakata nayiwa duk wanda muka je karb'ar haihuwa.
Gyad'a mata kai kawai tayi a'lamar to" Tukun TANI ta fita d'aga bandakin.
Tana dawowa ta zubo ruwan a d'ayar robar ta k'ara na sanyi taji yayi yadda take so sai ta shigo d'akin da ruwan.
Bintalo tace" Wai dama shima wankan jaririn kin iya shi?
Murmishi TANI tayi tace" Sosai ma ai Iyatu na koya min ko kuma tace nake kallo dan wataran na gaje ta , tinda d'iyan ta sunki su gajeta.
Bintalo tace" Ai kuwa kinji dad'i nan gaba ke zakike karb'ar haihuwa a nan garin.
TANI jaririyar ta dauka tayi Bismillah kamar yadda taga Kakarta na yi in zata wanki jariri, tukun ta saka ta ciki a hankali.
Wanke mata sauran jinin jikinta tayi tukun Bintalo ta karo mata wani ruwan, shi kuma tasa sabulu ta wanke jaririyar tass tukun ta k'ara dauraye ta da wani ruwan.
Su MANU ne suka shigo suna ta dariya.
TANI kamar wata Uwa ta rumgume jaririyar tana goge mata ruwan jikin ta , kallon su tayi tace" To har kun gama dashi kenan.
Zama MANU yayi ya basu labarin komai su kuma suna ta dariya.
TANI tace" Yassen kana burgeni MANU na , shiyasa nake son yawo dakai, yanzu ku tafi gida gani nan zuwa, daga Matar nan ta fito sai mu biyo ku a baya.
MANU yace" Hahaha Alkur'an kinyi TANI yanzu dai kinyi gadon Iyatu, to zo muje Goga kema Furera muje mu barsu idan suka gama sai su tarar da mu a bakin hanya.
Fita sukayi da sauri dan kar d'an Yarbawa ya dawo ya samesu.
**********************
Mik'e k'afa TANI tayi ta sakawa jaririyar kaya a jikin ta, Tukun ta zauna tana jiran fitowar Uwar.
D'an Yarbawa ne ya iso gidan da omo a hannun shi da sabulu da reza duk ya kawo.
TANI tace" A'a ka barshi ai Matar ka ta aje komai a wajan ta ga Y'arka sai kuma ka bani kud'ina.
Cike da farin ciki d'an Yarbawa ya anshi jaririyar ya soma taka rawa yana yaren su na yarbawa, kud'i ya fido N200 ya bata yace" Sannu Maman mu nagode yesu ya k'ara miki lafiya na godeyo kana da circi.
Amsa tayi tana murna yau ta samu jaka guda tace" To shikenan sai an jima mu zamu tafi gida, amma ni Allah zai taimakeni ba Yesu ba kai ka san wani Yesu.
Shi dai godiya yake mata har ta fita daga d'akin.
Suna fita daga gidan TANI ta ringa dariya kamar wata zararriya.
Bintalo tace" Ke wai lafiya kike dariya?
TANI tace" askin da aka yiwa Malam mana.
Itama dariyar tayi tace" To ai shikenan munyi maganin dan iska.
A hanya suka tardo su MANU ta nuna musu kud'in da d'an Yarbawa ya bata, ai kuwa suka kama muna kowa na rumgumar na kusa da shi.
Haka sukaci gaba da tafiya suna hira har suka k'araso gida.
TANI tace" Yau ma sai mun raka ku ne ko kuwa?
Furera tace" A'a ai yau dare baiyi ba irin na jiya zamu tafi gida kawai.
Sallama suka musu kowa ya nufi hanyar gidan su.
Kamar kullum wannan dogon abinda suka saba gani yau ma shi suka gani.
MANU yace" Hmm ikon Allah wai shi wannan mutumin meyasa yake zaman mana a k'ofar gida? Kuma sai yaga dare yayi tukun sai yazo.
TANI tace" rabu da shi muke Addu'a kullum Mai Gari yace idan mun ganshi muyi Addu'a.
Addu'ar suka fara nan suka ga ya b'ace b'at .
Dariya TANI tayi tace" shegen yayi layar zana ya b'ace ji yake tsoro zamuji.
Shima MANU dariya yayi yace" Ki bari wataran sai mun kama shi munga waye , kilama b'arawo ne zaiyi sata sai yaga munzo.
Ciki suka shiga nan suka samu Mai gari yana bacci sai minshari yake.
MANU ya lallab'a ya matsewa Mai Gari hanci.
Mai Gari kamar daga sama yaji an toshe mishi k'ofar da yake fitar da numfashi ya janyo iska, da sauri ya tashi yana kiciniyar kwacewa.
Dariya suka saka suna fad'in" Munshari ne kakeyi.
Mai Gari ganin jikokin nashi ne baiyi fad'a ba yace" Har kun dawo daga dandalin?
MANU yace" Eh mundawo nan suka bashi labarin haihuwar da TANI ta masa, amma basu fad'a ba sun zane sabon Malamin su.
Washe baki Mai Gari yayi yace" Iyee Yarinyar kirki kin kyauta da kikayo gadon Kakar ki yanzu kawo kud'in na aje muku.
Kunto kud'in tayi daga jikin zananta ta bashi.
Mai Gari yace" Kuyi Addu'a da salla tukun ku kwanta.
To suka ce tukun suka bi hanyar da zata sada su da d'akin su.
Kamar yadda suka saba salla raka'a biyu sukayi, tukun suka yi Addu'a kowa ya shafawa dan Uwansa a jikin sa, tukun suka kwanta a gadon su na k'arfe irin na da, da babbar katifar shi..✍🏻
Idan kin karanta ki daure kiyi comments sister🤝🏻
_*Taku har kallum Maman Nusaiba ce alk'alami yafi takobi ⚔️*_