Free chapter · Read without an account
006
*AZAAD JUNAID*
_{ The young Billionaire}_
Na
Jeeddah Aliyu
Haske writers Association.
006.
Aslamiyya ta miƙe zubur ta nufi ƙofar gida, wannan fitar da tayi shine karo na shidda da taje ƙofar gida tayi tsaye tana kallon hanya ta inda Amrah za ta bullo. Tun fitarta take jin matsanancin tsoro haɗi da faɗuwar gaba.
Ta je makota inda take sa ran gani Amrah yafi a kirga gashi kuma tana tsoro ta fita daga unguwa zuwa nemanta, ta bar Amal ita Kaɗai saboda yanayi jikinta. Abin ka da ruwa-ruwa babu juriya sai afki kuka, lokaci zuwa lokaci take sharar hawaye gashi tun safe babu abinda suka ci, inda Allah ya taimaketa akwai raguwar sachet ɗaya na madarar da jiya Amrah ta sato, ta kaɗawa Amal. Da batasan inda za ta nemowa Amal abinda za ta ci ba.
Sake komawa tai cikin gida tana shiga ɗaki ta tarar da Amal zaune, da alama yau jikin nata da sauƙi jiki a sanyyaye ta zauna kusa da Amal ƙoƙari take ta boye mata hali da ake ciki. Saidai kashh! Tuni Amal ta gano damuwar da take ciki ga kuma idanuwanta da suka nuna tayi kuka.
"Meke faruwa Miyya naga kamar kina cikin damuwa?"
"Ba komai.
Ta faɗa a takaice tare da kauda kanta tana kallon bangon ɗakin.
Amal ta matsa dab da ita ta kwantar da kanta akan kafaɗarta cikin sanyi muryarta mai kama da ta Aslamiyya sak tace.
"Miyasa za ki 6oye min Miyya bayan ga idanuwanki nan sun nuna kin yi kuka?"
"Amal tun safe da Amrah ta fita bata dawo ba. Wani irin fargaba haɗi da tsoro ke damuna. Ina tsoro kada wani mummuna abu ya sameta.
Ta ƙarashe magana tana hawaye. A hankali Amal ta sauke ajiyar zuciya kana tace "Ki kwantar da hankalinki da yarda ubangiji ba abin da zai same ta. in-sha-Allah za ta dawo cikin ƙoshin lafiya.
"Allah yasa!
Aslamiyya ta faɗa tana goge hawayen fuskarta.
***************
Cakk! Abdulhakeem ya tsaya yana kallon Amrah wacce ke ta faman rusa kuka, duk da yadda wani tsamurarre constable ke mata tsawa da hargagin ta rufe musu baki ko ya maketa da kulkin hannunshi. Bata fasa kuka da magiya ba.
Ya dawo da ganinshi akan inspector Sa'eed wanda rashin gaskiya ya bayyana ɓaro-ɓaro akan fuskarsa gaba ɗaya ya ruɗe sai wani kame-kame yake yi.
"Ranka ya daɗe sata tayi shine aka kawo ta nan.
"Waye ya kawo ta, me kuma ta sata?"
"Wani mutum ne yace kuɗinsa ta sace har kimani naira dubu ɗari, yarinyar tana da kafiya da taurin kai, taki ta faɗi inda ta ɓoye kuɗin.
Ɗan murmushi gefen baki Abdulhakeem ya yi.
"Gaskiya inspector ba kasan aikinka ba wannan ƙaramar yarinya ce za ta iya satar dubu ɗari?"
"Ranka ya daɗe haka mai shago ya faɗa.
"Kai kuma da yake kidahumi ne sai ka yarda.
Kafin inspector Sa'eed yai magana Amrah ta riga shi ta hanyar cewa.
"Wallahi-tallahi Abba ban ɗauki kuɗinsa ba. Biredi na dauka kuma ya karɓe abinsa, Don Allah Abba ka taimake ni yadda Allah ya taimake ka, ka fitarda ni wurinan.
Sosai Abdulhakeem ya ƙura mata idanuwanshi babu ko kyaftawa, kyakkyawar yarinya fara tass! a shekrunta na haihuwa ba za ta zarce goma sha biyu zuwa sha uku sa'ar Sadiq ce second born ɗinsa. Tausayinta ya yi mishi dirar mikiya, sai kawai ya rufe police ɗin da faɗa kaman zai dake su musanmman inspector Sa'eed, kasancewar D.P.O baya nan shine babba a wurin. Kamata ya yi ya tsananta bincike haka kawai daga kawo mishi 'yar mutane ya ƙargame ta. Sai Kiran mai shago aka yi da ya zo shima rudewa ya yi gani attajirin mai kuɗin da ya tsawa Amrah, daga ƙarshe sai faɗan gaskiyar al'amarin ya yi. Ya dawo yana ba wa Amrah haƙuri.
"Ka ga irinta ko inspector yanzu ina za ku da hakki yarinya nan kun zalince ta ba Kaɗan ba?"
"A yi haƙuri Ranka ya dad'e sharrin shaidan ne.
"Rufemin baki ba wani sharrin shaidan so zuciya ne da karɓa cin hanci da har abada ba za ku bar shi ba. Ke zo mu tafi Allah ya saka miki, yadda suka yi miki Allah yai musu haka nan.
Jikin Amrah yana rawa ta fito ɗaya daga cikin constable ya miƙa mata hijabinta da slippers, ta saka da sauri Abdulhakeem ya riƙo hannunta har sun kai bakin ƙofar fita, ya juyo ya dube su yana faɗin.
"Maganar nan ba wai ta kare iya nan ba, ku jira abin da zai biyo baya.
Daga mai shago har inspector cikinsu ya hau ƙugi da mugun sauri suka bi bayan Abdulhakeem, wanda har ya kai wajen da ya yi parking motarsa.
"Ranka ya daɗe Don girman Allah kayi haƙuri ka rufa mana asiri"
Cewar inspector har yana durkusawa ƙasa. Amrah ta dubi Abdulhakeem da kumburarrin idanuwanta tace.
"Abba ka yafe musu dukkansu na fiso laifi domin da na bi nasihar da Miyya take min a kullum da hakan bata faru dani ba.
Ta ƙarashe magana wasu zafafan hawaye masu zafin gaske, suka gangaro saman kuncinta. Jikin Abdulhakeem yai sanyi ya kalle inspector da har lokaci ya ke a durkushe.
"Shi kenan ku tashi ku tafi Allah ya so ku tana da kyakkyawar zuciya ta yafe muku da sai na koya maku hankali.
Godiya suka shiga yi masa bai bi ta kansu ba ya buɗewa Amrah backseat ta shiga, saboda har lokaci takaicinsu bai karashe sakinsa ba. Zainab dake front seat wacce tun a police station bata furta uffan ba sai lokaci ta Sami damar waigawa gefen da Amrah take tace.
"Ya sunanki wacce unguwa kike?"
"Sunana Amrah a kawo nake.
"Ke kuwa me ya kai ki satar biredi?"
Shiru Amrah tai ta rasa amsar bata sai kawai ta shiga wasa da yatsu hannunta.
"Amrah ki yi magana mana?
A wannan karon Abdulhakeem ne ya yi magana.
Cikin zazzaƙar muryarta tace.
"Saboda ba mu da abin da za mu ci nida 'yan uwana.
"Ina iyayenki?"
"Abbana ya rasu tun Ina da 2yrs mamanmu kuma naji Dadda tace bayan mutuwar Abbanmu ta gudu tabar mu nida twins sisterna da Yayata Miyya, wacce ita ce take kula damu tun baya da muka rasa iyayen mu.
Ƙarfaffiyar ajiyar zuciya Hakeem ya yi sosai tausayinta ya ƙara lulluɓe shi. Cikin sanyi murya yace.
"Ina dangin mahaifinku dana mahaifiyarku da za su bar ku da yunwa Amrah za su iya kula da ci da shan ku, ba sai kin yi sata ba?"
"Hannun kakarmu wacce ta haifi Abbanmu muke ita kuma bata sonmu. Kullum cikin gana mana azaba take, dangin mahaifyarmu kuma ba musan su ba. Asalima ba musan gari da suke ba.
Tsabar ruɗani da Hakeem ya shiga yasa ya kasa magana Zainab ce tai ƙarfin halin cewa.
"Innalillahi wa'aina illahim raji'un! Ki ka ce mahaifiyar Abbanku, ke kuwa Amrah me ku ka aikata mata har haka da ta tsane ku.
"Saboda Abbanmu ya aure mahaifiyar mu ba da saninta ba sannan kuma mahaifiyarmu ba Musulma bace.
"Amrah wannan ba hujja bace da za ta dogaro da ita har ta tsane ku, ai ba laifinku bane na mahaifinku ne saboda shine ya yi mata ba dai-dai ba. Kuma babu inda addinin musulunci ya yi hani da aure wacce ba Musulma ba. Kawai dai kakarku muguwa ce azzaluma sai Allah ya yi muku sakay....
"Ya isa haka Zainab!
Hakeem ya katse mata numfashi daga haka ba wanda ya sake magana a cikinsu, wani super market ya tsaya ya yiwa Amrah shopping na kayan tea da bread haɗi da indomie har dasu chocolate cake da biscuits. Tun a farkon layin unguwarsu tace ya sauke ta bai ce komai ba, ya yi parking ta fito shima fitowa ya yi Amrah tai mishi godiya har ta juya ya kira sunanta ya fito da shopping bags da kwalin indomie ya ajiye a gabanta bai ce komai ba ya shiga mota har ya yi reverse sai kuma ya tsaya ya kira ta, da ta zo ya miƙa mata complementary card mai dauke da phone numbers tare da company address ɗinsa. Ta koma wajen tulin kayan da ya ajiye mata ta ɗora kwalin indomie aka ta dauki shopping bags, ta nufi gida sai da ta fara lekawa tsakar gida kamar yadda ta saba ta ga babu kowa tai wuff ta shige ɗakinsu kasancewar su ne a farkon shigowa...
*****************
Yau ma da wuri Azaad Junaid ya shigo gida, sai da ya leƙa ɓangare Jadda saboda ya zame mishi al'ada duk dare sai ya je yaci abinci a wajenta sannan ya dawowa apartment ɗinsa.
Sai da ya duba lafiyar yaranshi kafin ya nufi nashi ɗaki, yana cikin online meeting ya ji an turo ƙofar ɗakinsa. Ko bai ɗago ba yasan ko wacece ke da zarar shigo mishi ɗaki a dai-dai wannan lokaci, shiyasa bai damu da sai ya kalli wanda ke shigowa ba.
Cikin dakon ƙasaita da nuna ita ɗin wata ce ta shigo ba ko sallama sai wani yatsina da take yi, sai uban ƙamshi na fitar hankali dake fita daga jikinta sanye take da sleeping gown wacce ta sauka izuwa gwiwarta, cike da izza haɗi da taƙama ta nemi gefen gado ta zauna. Ta ɗora ƙafa daya kan daya, har ta zauna bai da niyar ɗagowa ya kalle ta balle tasa ran za tanka mata.
Ta aika mishi da malalacin kallo, mai nuni da batasan darajarsa ko kaɗan ba. Sai wani kaɗa ƙafafuwanta take yi. Cikin gadara tace.
"Azaad inaso nai magana da kai please can I have your attention?"
Ya cigaba da magana da yake da colleague ɗinsa da suke online meeting yai banza da ita, hakan ba ƙaramin sosa mata rai ya yi ba. Abin ka da mai hurt temper har ta harzuƙa.
"Da kai nake magana Azaad ka yi wani kunnen uwar shagu dani. kuma kasan na tsani ina magana ayi banza dani, kai kuma abin da ka fi kwarewa dashi kenan.
Ta karashe magana cikin ɗaga murya, da sauri ya yi disconnected video call ɗin tare da rufe laptop ɗin. Gudun kada hankali colleague ɗinsa ya dawo kansa har su fahimci abun da ke faruwa, A tsanake ya ɗora manyan idanuwanshi masu masifar daukar hankali akan kyakkyawar fuskarta da batada make up amma sai glowing take abinta. Yayin da hasken blue colour bulbs dake ɗakin suka ƙara haskaka fuskarta ta, ya jefa mata kallon nan nashi mai sanyi da kashe jiki yana faɗin "Me kike nema a bedroom ɗina a dai-dai wannan lokaci?"
"Na zo ne muyi magana akan sauyawa Aneesah school ɗazu na aika P.A ɗina ya je school ɗinsu su ya karɓo min transferring letter ɗinta, sai ya dawo min da zance wai kayi magana da principal Aneesah za ta cigaba da karatu a school ɗinta har da saka Aneesah ta rubuta apologies letter for what reason za ta ba da haƙuri me za ta yi da za ka cilasta mata bada haƙuri?"
Tun sanda ta fara magana idanuwanshi ke kafe akanta babu ko kyaftawa yayin da wani tuk'uk'in baƙun ciki haɗi da takaicinta suka mishi dirar mikiya a karo na ba adadi, duk da ba yau ne ranar farko da ya fara jin hakan akanta ba.