Free chapter · Read without an account

13

by Fareeda Aliyu · KOWA DA ƘADDARARSA


Cikin hanzari har ina ƙarawa da sassarfa na doshi kitchen ɗin mu domin ɗauko ruwan sanyi, roba da ƙaramin tawul. Har na fito sai na tuna ai ba ruwa na firinji ake amfani da shi ba, don haka sai na mayar sai kawai na tari ruwa a robar hannuna na koma wurin da na baro shi. Duk wannan abin da nake yi babu kowa a falo abinka da garin azumi kuma ranar ƙarshen mako.

A yanda na bar shi a hakan na iske shi, numfashin sa yana fita a wahalce. Na sake jan bargon da niyyar cirewa, sai ya sake riƙe hannuna da hannun sa ɗaya sannan ya sa ɗayan ya sake jan bargon. Ban haƙura ba na sake kamawa ina magana a hankali "Yaya Rufa'i kayi hakuri ka bari, bargon ba sanyi yake rage maka ba illah dama da yake ba wa ƙwayoyin cutar suke daɗa yaɗuwa yanda cutar za ta kama ka sosai.

Bai yi magana ba amma ya sakar mun bargon, ina gama zare shi ya dunƙule alamun sanyin har wannan lokacin yana damun shi ƙwarai, don haka ban tsaya ɓata lokaci ba na tsoma tawul ɗin a ruwa haɗi da matsewa na kuma ɗora masa akan goshi tare da zama gefen gadon. A wahalce yace "Ummu sanyin nan yayi mun yawa, ki taimake ni na lulluɓa please." Ban da ina kusa da shi da ba zan ji me yace ba. Sai kawai na ƙara azamar daddana mashi tawul ɗin ina kuma maidawa cikin ruwa ina sabonta danshin, shi kuma ya fara karkarwa ya kuma kasa magana. A hakan zazzaɓin ya fara sauka sai kuma bacci ya ɗauke shi, don haka na ƙyale shi tare da tattara kayan na matsar gefe guda.

Ƙasa barin ɗakin nayi na zauna ina ta kallo tare da nazarin baccin da yake yi. Ganin ina ɓata lokaci na sai na doshi ɗakin Yaya Naziru don shine mafi kusa na ɗauko Al-ƙur'ani. A can na iske kayan sahur da aka kawowa Yaya Rufa'i da alama ko loma ɗaya bai ci ba. A sanyaye na koma ɗakin da na baro shi na zauna na fara karatu da murya a ƙasa.

Gyara yayi mun a wurin da nayi kuskure, hakan ne yasa nasan ya farka don haka ina ƙarasa ayar na rufe ƙur'anin tare da dawowa kusa da shi ina cewa "Ya jikin Yaya?

"Alhamdulillah. Ashe ƙanwar nan tawa ta iya bada taimakon gaggawa haka? Dama ɓangaren likita kika karanta ai." Cikin sanyin murya ya ke maganar.

Murmushi nayi, zuciya ta cike da tausayin sa don ganin ƙarfin halin da ya sa a yayin maganar, don haka ban amsa shi ba sai hannu na miƙa na dafa goshin sa domin jin yaya zazzaɓin, kuma cikin sa'a babu zafin.

"Na ɗauko maka magani da abinci?"

"Don ke ba kya azumi sai aka ce maki kowa ma irin ki ne?"

"Kai Yaya!" Na zumɓura baki "Ni wallahi ina azumi. Gani nayi ba ka da lafiya kuma ba ka yi sahur ba, ai ba laifi domin ka sha magani."

"Kar ki damu Ummu na zan iya kai azumin nan in shaa Allah. Zaman ki anan da wannan kulawar ma sun fi mun kowane irin magani aiki a halin yanzu. Na yi maki alƙawarin bin ki a sannu amma ban da na rabuwa da ke. Ki ce Yes kawai ni kuma idan kika bani wannan damar in mijin kan tace kike so nayi maki alƙawarin samun haka ba ma mijin tace ba."

Ganin na miƙe tsaye ya sa ya riƙo gefen rigata tare da cewa "Kar ki yi saurin yanke hukunci, ki bani dama na nuna maki cewar maza suna suka tara." Ya saki rigar tare da juyawa ɗayan ɓangaren.

Tun wurin shan ruwa nasan ya gama warkewa don tare muka yi dashi gabaɗaya a falo, amma har ya faɗa kana kallon shi za kaga ramar shi ta farat ɗaya, hancin na nan kaman an kafe biro. Karaf sai idanun mu suka haɗu, ko kunyar su Baba bai ji ba yace "Kallon me kike mun?"

Ban yi wata-wata ba na amsa don kauda zargi daga zuciyar su da cewa "Gani nayi ciwon yini ɗaya har ka rame."

Baba ya amsa "Subhanallahi! Ba ka da lafiya ashe? Na ɗauka ramar azumi aka fara ne ai." Dukkan su da ke fakon suka fara yi masa sannu da jiki, Mama kuma na tambayar ko ya sha magani.

Ɗan wannan abin da ya faru sai na lura da cewar ya canzawa 'yan gidanmu tunani akan alaƙa ta da Yaya Rufa'i. Ni kaina akan kaina na fara tsoron zuciya ta kar ta rusuna ko don saboda iya zance da bi da mutane ta hanyar laluma da Yaya Rufa'i ya gwanance a kai. Gudun haka sai na ja baya da shi ga ƙarin sanin da nayi miskilancin sa ba zai bar shi ya bi ni kamar jela ba. Ba zan iya cewa kai tsaye baya naci ba amma nashi nacin da salo yake zuwa da kuma aji.

Ana gobe sallah ya kawo mana ɗinkunan mu Ni da Sauda. Irin dariyar da muka yi wa Yaya Zainabu ranar sai da cikin mu ya kusa ciwo. Ta fi mu yawan kayan sallah amma ɗinkunan mu sun fi nata kyau, sai mita take Yaya Rufa'i yayi son kai, kamar za ta yi hawaye shine ma ƙarfin dariyar tamu har da su Mama da Yayan. Ya lallaɓa ta da cewa zai kai ta wurin telan ta kai kayan bikin ta tunda kafin babbar Sallah ne bikin.

Tunda aka shiga sabgar sallah ban yarda na zauna a gidan nan ba duk dai cikin salon ƙaurace masa. Ranar talata kuma na dawo na iske ya bar saƙo gurin Mama wai gobe kar nake ko'ina na jira shi akwai wurin da zamu. Cikin sa'a kuma washegarin sai ga Yaya Munnir wai zai kai Yaya Zainabu ta gaishe da yayar shi da Maman shi. Tuni ma na shige gaban mota duk da ban mance da sallahun da Yaya Rufa'i ya bar wa Mama ba, infact ina sane ma.

Ba mu dawo ba kuwa sai da magriba cike da tsaraba. Gidansu akwai 'yan mata kusan sa'o'i na shi yasa ma muka daɗe, don Yaya Zainabu ba zata iya cewa mu taho ba, ni kuma da ya kamata nayi na bi su muka fita don haka sai bayan la'asar ma muka baro gidansu. Yayar shi kuma me son mutane ce, tunda muka je gidanta take ƙoƙarin ganin mun saki jiki da ita sosai da yaranta. Da alama dai suna son Yaya Zainabun.

Na zauna a falo bayan mun idar da Sallah ina ta yiwa Mama bayanin kayayyakin da muka zo dasu tare da labarin abin da ya faru har ban lura da Yaya Rufa'i da yake kwance kan kujerar ba yana da riƙe da remote. Tsabar labari wurin kwatanta yanda Yaya Zainabu ta dinga sunƙe fuska a lokacin da zata zauna da muka je gidan su Yaya Munnir, na dangana da wurin da yake kwance fuskata ƙunshe cikin hijabin da nayi sallah don nuna masu zaman. Ina jin Yaya Zainabu na dariya amma sai na shareta a tunani na rufe fuskar tawa take yiwa dariya.

Zama na ke da wuya na lura a sama nake maimakon daidai tsayin kujerar sannan wurin da nake zaune akwai laushi da ɗumi, da wani irin hanzari na yaye fuskata na kalli kujerar. Yana nan yanda yake, idonshi kan talabijin ko da wasa bai nuna alamar ya san ina zaune a saman shi ba. Da ƙarfi 'yan biyu, Yaya Zainabu da Sauda suke ƙyalƙyala dariya kamar zuciyar su za ta fita. Zumbur na sauka, hakan ya daɗa ƙara ƙarfin dariyar su, Hassana har da hawaye don haka sai kawai na juya na bar falon zuwa ɗakinmu ina ƙunƙuni, ta gefen ido na hango Mama tana danne dariyar ta.

A ƙarshen satin hutun shi zai ƙare, Yaya Naziru ma ya zo Sallah ina kuma zaton tare zasu koma. Don haka na ɗora daga inda na tsaya wurin wasan ɓuya tare da fatan kar mu haɗu har ƙarshen sati yazo.

Tsaye nake a kicin ina goge kwanukan da na wanke, kunnena na saƙale da earpiece muna magana da Surayya akan wani da ta haɗu dashi lokacin Sallah, nishaɗi kawai nake yi don haka dariya nake yi sosai. Kowa ya san a stage ɗin da muke babu abinda ke gaban mu face maganar samari, waƙoƙi, finafinai, litattafan nishaɗi da kuma fashion.

Shagaltar da ni da wayar tayi ya sanya ban jera kwanukan wurin da ya kamata ba, kawai gefe nake tura su. Sai da muka gama wayar na juyo zan kwashe su na ga wayam sai fili, kai, na juyo sosai cikin sa'a na hango ƙyallin kaya ana barin kicin ɗin, don haka na yi azama na yo waje, ina isowa falon shi kuma yana zama hannunsa ɗauke da robar ruwa. Na riƙe ƙugu ina kallon shi ina mamaki wani irin rashin motsi yayi da ban ji motsinsa ba sam.

Bai kalle ni ba yace "Na taya ki aiki, ba kice kin gode ba kuma kin zo kin kafe ni da ido."

Na ƙi amsawa sai ma juyawa da nayi zan koma kicin ɗin, amma sai yayi mun umarnin zama tare da nuna kujerar gefen shi. Babu musu na zauna don fuskar shi ba wasa.

Yace "Na yanke shawarar yi wa Baba maganar mu, ƙila baki son mu fuskanci juna ni da ke. Na ba ki dama ke kuma kin zubar da ita akan fuskata da alama kin fi buƙatar mu kasance tare kawai."

Zufa kawai ke fitar mun a bisa goshi na kasa magana. Iyakar tunani na ya tsaya akan yanda zan hana hakan faruwa, na gaji da nacin nan na Yaya Rufa'i. Na yi hannunka mai sanda ya fi sau shurin masaƙi amma yana sane yake kauda ido. A take raina ya ƙuntata, zuciya ta ta hau bugawa da gudu saboda halin da na samu kaina, kai, wani abu ne ya zo ya tsaya mun a wuya saboda ɓacin rai ina kuma tambayar kaina yanzu duk irin ajin Yaya Rufa'i ya rasa wurin da zai zubar da shi sai a kaina? Tunda nace bana yi ba sai a kai kasuwa ba saboda Allah?

Don haka a zafafe na miƙe tsaye fuskata a ɗaure na ɗauke idona daga gare shi na fara balbale shi da masifa kamar yanda raina yake tafarfasa "Ka ga Yaya Rufa'i ka ƙyale ni! Na yi maka kawaici, na yi maka kara a ƙarshe ma na yi maka hannunka mai sanda amma a iska. Yau dai bara na faɗa maka gaskiya ko Allah ya sa ka fahimta." Na maido gani na gare shi na kalle shi ido cikin ido na cigaba "Bana son ka Yaya Rufa'i, ba na son ka! Ba na son ka! Ka ji da kunnen ka sau uku ai ko?"

Yanayin fuskarshi ce ta dakatar da ni ba don nayi niyyar tsayawa iya nan ba. Emotions kala kala ke flying a fuskarsa da ma wani abu da bansan menene ba. Cikin dauriya na ƙara da cewa "don haka sai ka sakar mun mara nayi fitsari. Ga 'yan mata chan birkij sai bin ka suke yi, ni kuma ka zo ka dameni anan."

A fusace na juya da nufin na koma ɗakinmu, ban ƙara sanin me ke faruwa ba sai ganin wani haske da nayi ya gilma ta idanuna, sannan na ji kaman an samu earthquake (girgizar ƙasa) domin ji nayi an wulwula ni an yasar da ni a ƙasa wani raɗaɗi yana ratsa jiki na ta ɓangaren hannuna na dama da kuma gefen fuskata."

Tabbas a yashe nake a ƙasa sannan hannun da yake mun raɗadi buge shi nayi a Centre table, shi kuma Yaya Rufa'i yana nan zaune ko daidai da inci ɗaya bai motsa ba bare nayi ko shine ya ture ni, kafin na ƙarasa fahimtar me ke faruwa naji an rufe ni da duka ta ko'ina.

Fuskata nake ƙokarin karewa daga bugun da Mama ke kawo mun tana faɗa kamar za ta ari baki. Tace na zama mara kunya, Yayana ne ko ba komai amma tsabar raini gatsal nake yi masa magana.

Janye ni ya yi daga dukan yana ba wa Mama haƙuri, ganin tana bi na da dukan duk wurin da ya matsar da ni sai kawai ya ɗauke ni a hannunsa yayi ɗakin Yaya Naziru da ni ya fara rarrashi na.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.