Free chapter · Read without an account

20

by Fareeda Aliyu · KOWA DA ƘADDARARSA

Ban san me yasa tunda muka koma gida nake ta murmushi ni kaɗai duk sa'adda na tuna abin da ya faru, ga shi har muka rabu ko sunan shi ma ban sani ba. Aminu kam dariya yayi mun bayan na ba shi labarin abin da ya farun, har da cewa zai so ya ga Idris Elban Kano duk kuwa da nasan tsokanata yake yi domin yace ni na fiya zuzuta abubuwa (exaggeration).

Haka lokutta ke ta shuɗewa with my life without purpose, ba ni da aiki sai hira a social media platforms da canjin wurin zama tsakanin gidan Yaya Zainabu da Hotoro can wurin su Mama. Sannan wannan karon nayi dauriyar zuwa gidan su Yaya Rufa'i gaishe da Ummi amma ko da wasa bana kallon ɓangarensa bare ma naje, kwana biyu na je da niyyar yi amma su sister Samiha suka dage sai da nayi kwana uku. Ganin Abdallah (dama na faɗa maku su huɗu ne ai ko?) ne yake ɗaga mun hankali, kamar su ɗaya shi da Yaya Rufa'i har muryar su bambancin kawai shi Abdallah akwai surutu da rawan kan yarinta domin yanzu ne ma yake aji shida a sakandare.

Kwana kaɗan tsakani shirin bikin Zara'u Darma ya taso, waya ma suka yi mun zasu biyo su ɗauke ni mu je kasuwa ɗauko anko. Tun goman safe muke yawo a kasuwar nan, kowanne aka zaɓo sai an samu wani a cikin mu ya kushe, haka muka yi ta wahalar sa kai. A ƙarshe dai wurin ƙarfe biyar muka ci sa'a aka samu wanda ya kwantawa kowa a zuciya, masu shagon ma ƙoƙarin rufe shagon suke yi, bandir biyu muka fara ɗaukowa bayan mun daidaita da su mun kuma bar wasu kuɗi deposit kar su sayar mu zo muna nema babu. Kamar an yi mana duka muka fito daga kasuwar don tsabar bala'in gajiya, iyayin mu ne ya ja mana ai.

Muna cikin saka kayan a adaidaita sahu sai Fatima ta taɓo ni wai ana yi mun magana. Ko da na juya bansan lokacin da na tafi da gudu na rungume mai mun maganar ba, Badariyya ce!

"Ummu Kulsum dama kina nan? Wallahi na ji haushin rashin musayar lamba da ba mu yi rannan ba."

Na amsa "Allah Sarki, ni ma wallahi, sai da na taho na yi ta regretting. Ya na gan ki a kasuwa? Ko dai kin zama 'yar Kano ne yanzu?"

"Ayya, kaya na zo siya. Rannan ne muka zo tare da wasu 'yan ajin mu sai na sanya aka ajiye mun, shine na yau na dawo siyan kayan"

"Tun daga Kaduna wai? Na ɗauka babu wanda kika sani a Kano ai."

"A'a daga makaranta dai. Me ya hana ki zuwa ne? Ga shi ba abinda ba ki ci ba. Allah na ji haushin rashin zuwan ki, abun yayi days yana damu na ban san ma ta ina zan fara neman ki ba sai na haƙura daga baya kawai."

Sai na tsaya ina kallon ta cike da mamaki "Ki na nufin har an fara zuwa?"

"Chab! Tun yaushe?! Saura sati fa kawai mu fara exams ɗin intro."

Duk da makarantar ba ta dame ni ba amma sai da na ji babu daɗi har wani abu ya taɓa raina. Na so na fara ko ba komai wannan zaman gidan da na daina, kullum kowa fita yake sai ni da Mama kullum, idan ma a gidan Yaya Zainabu ne sai mu kaɗai da Najwa da mai aikin ta tun da tana zuwa aiki ai. Ɗan keke napep da su Fatima sun ƙosa da jira na suka fara mun horn, hakan yasa ta tako mun har wurin su, suka gaisa muka yi sallama bayan mun yi musayar lambar waya wannan karon ban manta ba.

A hanya aka sauke Zara'u Darma wurin da direban su yake jiran ta sannan muka wuce gidanmu domin anan Fatima ta bar motar ta, Surayya kuma nan gidanmu za'a zo ɗaukar ta. Ni dai tun da muka taho ban ƙara magana ba, abun zancen makarantar nan ya dame ni fiye da yadda na zata.

Mama ma sai bayan su Surayya sun yi sallah da cin abinci sun tafi tukunna na faɗa mata. Har waya tayi ta tambaya ko akwai yadda za'a yi don ta san i can catch up in a week, Amma an tabbatar mata an riga an kammala komai sai dai na jira wata shekarar kuma. A daren na daure na zubar da komai da yake damu na dangane da zancen makarantar, na yardarwa kaina ita ma ba ta cikin abin da aka ƙadarta zan yi a rayuwa ta.

Kafatanin 'yan gidanmu ni ce komai nawa ya fita daban, makaranta ba ni da sa'a haka ma aure. Haka ma cikin ƙawayena tun na sakandare ni aka bari a baya a komai. Hankali na naji ya fara tashi da na fara kwatanta rayuwa ta da mutanen da ke zagaye da ni ko na sani, a take na fara istigifari tare da tunatar da kaina kowa fa da ƙaddararsa, da alama nawa lokacin ba na kusa ba ne.

Ban gama farfaɗowa daga reality ɗin rayuwa ta ba sai saurayin Sauda, Abubakar, ya zo gaishe da su Mama tare da neman izinin turo da magabatansa, ita kam Alhamdulillah komai na tafiyar mata a daidai kamar ita ta tsara.

Ga shi dai a ƙwaƙwalwa na fi ta haka ma a kyau, amma lamarin rayuwa duka ba'a kan haka yake tafiya ba. Yanzu haka tana second semester level three ne, daga kuma yanda yanayi yake nunawa da za'a bi ra'ayin Abubakar ɗin zai so a yi bikin su ne kafin ta kammala makaranta. Duk yanda na so kar naji babu daɗi sai da naji ɗin, ba kuma don ina yi mata bakin ciki ko ina kishi da ita ba ne, a'a ko ɗaya. Sai dai nayi nasarar kawar da hakan daga raina sanin cewa damuwar ba abin da za ta canza, komai fa sai idan Allah ya so.

Aminu kam har gida ya zo taya ni jimamin rashin samun shiga makarantar duk da ya san dama ba so nake ba. A kuma ranar ne yake faɗa mun cewar hankali na yasa na fita daban daga cikin yara masu irin shekaru na, raina hankalin su da shirmen su ne yasa baya ƙaunar wani abu deep ya shiga tsakanin sa da su, nice kawai daban. Ta ɓangarena ni kuma na sake da shi fiye da duk samari na na baya, kallo ɗaya za kayi mana ka san cewar mu ɗin abokan kusa ne kafin kayi zaton soyayya a tsakanin mu.

Duk da cewa ina Kano kuma unguwannin mu na kusa da juna, ban cika barin shi yana zuwa gida ba, ni na gaji da zance da samari, shi ɗin ma ya ɗau haske bai cika tambayar zuwa gidan ba, kuma har yanzu ba mu cika waya ba sai chatting ko da yaushe wanann kam, hakan ma sai idan ya koma gida tunda aikin banki yake yi ba koyaushe yake da lokaci ba. Kuma ko nayi abu bai yi masa daɗi ba sai dai na karanci yanayin sa (a fili ko ta amsawar saƙo na), amma ba zai buɗa baki ya faɗa ba.

Su Darma suna kammala jarrabawar ƙarshe na gama makaranta (sun zama graduate), sai sabgar buki ta taso gabaɗaya, kuma tsakanin su da Fatima sati Uku ne kacal. Don haka shiri bibbiyu muke yi, daidai da kayan da zamu sa duka a wannan lokacin muka siya. Nan gida ma maganar Sauda ta tsaya sosai.

Wannan zirga-zirgar shirin bikin nan na ji wahala sosai da sosai, to bana zuwa ko'ina koyaushe ina gida ina pretending ba abin da yake damu na. Don ma an ci sa'a jiki na ba jikin ƙiba ba ne, da tuni na kusa bindiga saboda tsabar ƙiba. Haka tunda satin bikin ya kama shi ma ba ni da wani hutu, a ƙarshe ma sai gidan su Zara'u muka tare.

Mun sha biki, Darma ta zama ta Umar ɗin ta, kowa ma tare ya san su. Ko da wasa ban gayyaci Aminu bikin ba, shi ma bai tanka ba amma da yake bawan Allah ne har gudunmawa ya turo mun da shi. Surayya ma ta ƙari surutun ta ta bar ni 

Amma deep down yanda yake nunawa yana damu na. Nasan mun sake da juna sosai da sosai, amma irin kulawar da yake nuna mun ita ce mafi koma baya a cikin dukkanin samarin da na taɓa yi, baya magiya, baya naci sannan idan nace a'a a abu baya ƙara bi ta kai. Kai ko a chatting ya ga ina shasshare shi bai fi ya tambaye ni damuwa ta sau ɗaya ba, idan na amsa ya taya ni warware matsalar idan yana da hali, idan kuma abun ya fi ƙarfin sa sai ya kwantar mun da hankali ( ya iya kwantarwa da mutum hankali duk kuwa girman matsalar). Idan kuma na yi niyyar jan aji sai shi ma ya share ni da lamari na gabaɗaya.

Akwai wani lokaci da sai da muka kai sati ɗaya cur ƙala ba mu cewa juna ta chatting ba. Yana kallo ina canza hoto na da updates amma ko sannu 'yar banza bai ce mun ba. Ni ban saba ana share ni ba don haka ranar da sati ta cika na gaza jurewa, zuciya ta na tafasa na zazzaga masa masifa ta chat ɗin, irin saurin rubutun da nayi a ranar ban san na iya typing da sauri haka ba. Tuhuma ne akan cewa watau yana nufin idan ni ban fara yi masa magana ba, shi ba zai yi ba kenan? Kusan koyaushe ni ce nake maganar ƙarshe idan mun yi magana da shi, amma don rashin adalci irin na shi ni yake tsammani gobe na fara yi masa magana again?

Cikakken minti ɗaya ba'a yi ba sai ga nashi saƙonnin na amsa suna shigowa. Hotuna (screen shot) ne suka fara shigowa na hirarrakin mu na baya, kuma abun mamaki duk shine yake fara mun magana a rana Sannan ya amsa da "Haba Hajiya ta, duba hotunan nan ki tantance wanda yake fara yi wa wani magana a tsakanin mu. In dai kin ga wanda kika fara magana a ciki to tabbas akwai wani abu da za ki tambaya ko kuma faɗi. Duk da haka, Allah ya ba ki hakuri sannan ki san cewa Wallahi ban taɓa ba wani haƙuri akan tuhumar abin da ban aikata sai ke, yanzun nan." Wannan saɓanin ya sa muka ƙara efforts na neman juna.

Kafin haka kuma sati Uku har ya cika bikin Fatima ma ya kama. Umar kam yayi mana kara domin ya bar Zara'u ta kasance tare da mu don sai dare yake zuwa ɗaukar ta kullum. Irin nishaɗin da na samu kuwa har bana son bikin ya kammala.

Ranar dinner party kuwa tun safe muke wurin gyaran jiki, ni da Surayya muka dage mu ma sai anyi mana, to haka kawai? A can aka yi mana kwalliya kuma muka shirya gabaɗaya kuma aka zo aka ɗauke mu.

Yaya Zainabu da Yaya Munnir sun yi mun kara, sun zo har da taho da su Sauda da Hassana, kuma sun yi mata kyautar burgewa kamar yanda suka yi wa Darma. Najwa kam tunda ta ƙyalla ido ta gan ni sai ta ƙi zama wurin Yaya Zainabu ta maƙale mun, ai kuwa haka nake ta sama da ƙasa da ita.

Wannan karon kam na gayyaci Aminu kuma tare da abokinsa ya zo don yace tunda bikin mu ne yasan da wuya na samu lokacin sa sosai (understanding boyfriend). Kuma hakan ne ya kasance sai dai ina yawan zagayawa wajen da suke zaune bini-bini.

Ina riƙe da Najwa wani abokin ango yana mun bayani akan abin da ya shafi dessert ɗin da za'a raba a ƙarshe, ina sauraren shi, sai Surayya ta ƙaraso kusa da ni tana nuna mun wani ɓangare wai ana magana da ni ta chan, sai da na gama maganar da nake yi sannan na doshi wurin, chan ta wurin ƙarshen hall ɗin ne, ni ban ma gane waye yake mun maganar ba. Kuma ina tafe ina tsayawa muna gaisawa da 'yan ajinmu da na gani ina taya su murnar gama karatu.

Lokacin da na isa wurin shi hankalin shi na kan wayar shi yana ɗan dariya, kallon sani nake yi masa amma na kasa tantance waye tunda kan shi na ƙasa. Hayaniyar hall ɗin ta hana shi jin sallamar da nayi har sai uku. Har na juya zan tafi na ga rashin dacewar hakan sai kawai na zare wayar daga hannunsa. Cikin zafin nama ya riƙe hannuna tare da gaggawar ɗago kan shi domin ganin wani mai ƙarfin halin ne?

A hanzarce ya saki hannuna yana dariya kaɗan-kaɗan da alama ya ji kunya yace "Sorry please! Wallahi na ɗauka ƙanwa ta ce Humaira" tare da nuna wadda ke zaune ta gefen shi tana ta zaba surutu da wasu su uku, da alama ƙawayenta ne don baya ta juya mashi.

Fuskarshi a take ta dawo mun nima na fara dariya nace "The Nigerian Idris Elba! Wow! Ashe kana nan!" Da ɗan karfi nayi maganar saboda surutun wurin.

Yana murmushi ya miƙowa Najwa hannu, abin mamaki sai kawai na ga ta je wurin shi duk da a zaune yake, yace "Wannan fa ba Idris Elba sunan shi ba, iya kama kawai aka tsaya don Fa'iz nake."

"Fa'iz? Kasan kai ne na farko da na haɗuwa da shi mai sunan nan?"

"'yar jarida ta fa? Ya sunan ta?"

"Ita ma sunan ta Fa'iza" Ina dariya

Fuskar shi da alamar seriousness yace "Anya kuwa haka sunan ki? Ban da wasa please."

"Toh shikenan. Suna na Ummu Kulsum."

Sai ya kalli Najwa da ke hannun shi yace "Wannan babyn mu ce? Ya sunan ta?"

"Najwa." Ban yi ƙarin bayani akan wace ita ba don ba ni da dalili.

Kira na aka yi hakan ya sa na miƙa hannu domin karɓar Najwa tare da faɗin ina zuwa, amma sam ta ƙi zuwa har maƙalƙale shi ta ƙara yi. Hakan ya sanya yace naje na dawo babu damuwa zai riƙe ta, na ɗan yi jim alamar rashin yarda sai kuma a hankali na juya na tafi ina tunanin an ya ya kamata na bar wa wanda ban sani ba yarinyar mutane? Ban yi taku goma ba na gan shi a gefe na yana faɗin "Bari kawai mu raka ki, I hope ba za mu ja maki matsala ba." Ban amsa ba sai dai murmushi da nayi. Yana biye ni na gama abubuwan da ya kamata, Najwa kam ta wani kwantar da kanta a kafaɗar shi don kar na karɓe ta ko kuma sai kace irin baban ta ɗin nan.

A wurin su Yaya Zainabu muka rabu da shi, suna gaisawa ta gane waye. Yaya Munnir shi ma ya tuna maganar kuma da alama jinin su ya haɗu daga haɗuwa ko kuma ba mamaki don sun ga yanda yake riƙe da Najwa ne, domin an ce me ɗa Wawa, kujera suka sa masa ya zauna har suna dariya da Yaya Munnir ɗin. Ni kuma wurin su Aminu na sake komawa, bai nuna komai ba ni ma ban ce komai ba, after all I have an understanding boyfriend.

Na waiga wurin su Yaya Zainabu na ga ko ya bar wurin, sai na gan shi yana kallon wurin da nake yana kuma yi wa Yaya Munnir magana. Shi ma ya waigo ya kalle mu sannan ya amsa yana ɗan taɓe baki, don haka nasan dole magana ta ake yi.

Aminu goma daidai suka yi mun sallama domin tafiya. Har wurin motar su na raka su ni da Hassana. Tafiyarsu babu daɗewa su ma su Yaya Zainabu suka taso zasu tafi, kuma har wannan lokacin Najwa na hannun Fa'iz sai dai an ci sa'a ta yi bacci, a tare muka raka su mota suka tafi.

Muna hanyar komawa ciki ne Fa'iz yace "Wai yau ina jaridancin ki ya tafi ne? Ko busy ɗin biki ne?"

"Ai waccan lokacin ma don ina tunanin na san ka kuma na kasa gane a ina ne, so kawai nake na sani."

"Yanzu kuma babu abin da kike son sani game da ni? Kamar irin ko ina da aure? 'ya'ya?" Ya ɗaga gira.

Hakan sai ya sanya ni dariya sosai, nace "Jaridancin nawa bai kai haka ba ai domin haka na nufin shiga sharo ba shanu."

Kafin ya kai ga amsawa sai ga ƙanwarshi ta fito waje neman shi. A take ya gabatar da mu "Ummu Kulsum ga Humaira, Humaira ga Ummu Kulsum." Muka yi musabaha tare da gaisawa ta kuma ƙara da cewa "ɗinki ya yi mun kyau." Ina murmushi nace Nagode.

Tafiya take so su yi amma yace ta ba shi minti biyar yayi sallama da ni, sai tace bari ita ma tayi sallama da ƙawayen ta sai ta dawo su wuce.

Tana barin wajen yace "Ku dai mata abin sabo ba ya maku wahala, yanzu fa faɗin ɗinkin ki yayi kyau sai ya sa ku saba ko?"

Na ɗan kalle shi, kamar ba zan yi magana ba sai nace "sabon ne ba ka so nayi da ƙanwar ka? Kar ma ka sa na je nace ta ba ni lambar ta."

"A'a! Kar ki mun sharri ni ba haka nake nufi ba. Kin ma tuna mun, ba ni lambar ki." Ya faɗi yana laluben aljihunsa tare da fiddo wayar sa.

"Ba sai na ba ka ba, ita ma wasa nake ba karɓar ta ta zan yi ba."

Ya tsaya sororo yana kallona kamar irin he is lost ɗin nan, yace "Ko don nace kin tuna mun ma? Ba wai ina nufin shine dalilin da yasa na tambaya ba, dama ina da niyya kuma ai kin ga tun ɗazun ba mu kasance cikin rashin hayaniya ba sai....."

Surayya ce ta katse maganar shi ta dalilin kiran suna na da tayi, mu duka muka juya muna kallon ta. Ta cigaba da magana "Ki zo da sauri please..." Ta kuma kalli na gefe na amma ba tayi masa magana ba, kuma tana tsaye ta ɗan girgiza alamar so take nayi sauri na taho.

Na juya kawai na doso wurin ta, sai kuma ga Humaira ita ma ta fito tare da ƙawarta domin tafiya. Muka yi sallama a gurguje da su, ni na shige cikin hall ɗin su kuma suka doshi wurin motar su.

Sabgar buki ta hana mu sakat har sai da muka kai amarya gidan angon ta sannan su Darma da mijin ta suka sauke ni da Surayya a gidajen mu kafin su wuce nasu. Maa shaa Allah, Allah ya kawo na 'yan baya lafiya. Amin.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.