Free chapter · Read without an account
22
Wannan karon kuma 'yan biyu sun samu admission, Hassana za ta karanci biochemistry, Hussein kuma engineering a yayinda Sauda ta shiga shekarar ƙarshe kuma alamomi sun nuna tare da ita za'a haɗa bikin mu.
Duk wata damuwa a raina na cire ta domin har makaranta na yafe, ba wata alamar zan sake neman wata. Ganin ina ta zaman banza ba arabi ba boko sai na sake komawa islamiyya. Baba da Mama ma ba wanda yace da ni komai don haka na daɗa sakin jiki abu na.
Da 'yan gidansu Abubakar suka zo sa rana wata biyar suka tsayar, da na faɗawa Aminu sai shi ma yace wata biyar ɗin yayi masa daidai.
Kasancewar kullum daga ni sai Mama ake bari a gidan sai na fara gajiya da komai, karance-karancen ko chatting duk ba ya wani mun daɗi kamar da. Kawai sai hankali na gaba-daya ya karkata ga ɓangaren girke-girke. Ni ce siyan littafin girki ko na kalla, haka yanzu amfanin waya ta zagayen websites da YouTube na girke-girke, ga shi Baba ba ya taɓa gajiya da ba ni kuɗin siyan kayayyakin girkin. Su Hassana kuwa, har ƙin cin abinci suke yi a makaranta ko da sun yini ana rige-rigen dawowa domin ganin wani iri na dafa a ranar.
Akwai ranar da Yaya Zainabu suka biyo gida ita da abokan aikin ta, wai sun je barka can ƙasan layin mu. Tunda suka shigo take cewa wai wannan wane irin ƙamshi nake ji ne tun daga ƙofar gida? Ranar snacks na yi kala-kala, don haka shi na kawo masu. Yaya Zainabu kam ta dage sai na faɗa mata me nake sawa a ciki, don taste ɗin wasu irin spices masu daɗi take ji. Ina dariya na kwaso NAJNINO spices (***) na zube a gaban ta. Suna da kusan kowanne spice har special mix da zaka zuba a kowanne girki, pepper soup spice ɗin su kuwa? Chab! Ni har a noodles nake zuba shi, idan ka doso kitchen idan ina dafa noodles da shi sai ka ɗauka wata duniya nake dafawa. Ina ganin ta fara tattarewa na san kwashewa za tayi, da gudu na shammace ta na kwashe kaya na, nace gaskiya a'a Yaya Zainabu, just call or Whatsapp the number, suna yin delivery har ƙofar gida. Kafin su tafi kuma wata daga cikinsu ta tambaye ni idan zan iya yi masu snacks ɗin nan ranar sunan barkar da suka je, sai kawai su kai wa me jegon a matsayin gudunmuwar su. A nan take muka yi lissafin kuɗin komai, nace su bawa yaya Zainabu kuɗin kawai.
Da farko ina tunanin wahalar abun don haka da sassafe na tashi na fara, na dinga roƙon Allah ya sa su yi kyau, kar a samu matsala, cikin ikon nasa kuma kafin azahar na kammala komai kuma perfectly done. Ina fitowa daga wanka suka zo ɗauka har da ajiye mun ladar aikin a envelope. Na yi masu godiya.
Abu kamar wasa duk lokacin da za'a yi abin da ya danganci snacks a wurin aikinsu ni suke kawowa aikin ta dalilin haka ya sanya suka fara haɗa ni da masu tambayar a ina ake yi masu, bana cikakken sati biyu ban yi wa wasu aikin snacks ba.
Mama gajiya tayi tace ina cika mata kitchen, domin duk ranar da zan yi aiki mai yawa har rasa wurin ɗora girki ake yi. Sai kawai tace da Baba a bani ɗakin Yaya Muntari ya zama nan ne kitchen ɗin da zan dinga aiki a ciki tunda ba'a amfani da shi kawai a kulle yake.
Ƙarshen sati, kasancewar su Sauda da 'yan biyu duka suna gida sai muka yi aikin kwashe kayan ɗakin muka kuma mayar da su zuwa ɗakin Yaya Mahmoud na da, sannan Mama ta sa Yaro ya kwashe abubuwan amfani da yawa don tace ba amfanin ajiye su kuma. Kamar haɗin baki sai ga Yaya Muntari yayi mana zuwan yamma shi ma, abubuwan da ya ɗauka babu yawa sai ma ƙarawa Yaro da yayi wasu kayayyakin. Kuma har taya mu aikin yayi yana tsokanata wai na cika son kuɗi, dukkanin mu muka yi dariya.
Washegari Lahadi kuma kafin ya tafi ya bar kuɗi a hannun Mama wai a siya mun kayayyakin aiki da su, Allah kuma ya sanya alkhairi ya sa kasuwancin ya buɗe sosai.
Ranar Litinin da Baba ya dawo daga tafiyar da yayi, ya kawo mun saƙon kuɗi daga Yaya Mahmoud, wai shi ma ga gudunmawarsa nan. Da gani nasan Yaya Muntari ne ya faɗa masa tun da ni mun kwana biyu ba mu yi magana ta waya ba. Da gudu na kira shi domin yi masa godiya, ƙara kwantar mun da hankali yayi yana cewa ƙila abin da Allah ya so nayi kenan shi yasa komai ya ƙi tafiyar mun daidai sannan yace na kula, ban da cutar da abokan sana'ata ko ha'inci domin samun kuɗi sosai sannan kuma kar na tsawwala.
Kafin sati ya ƙare kuwa, Baba ya sanya an yi wa wajen kwaskwarima ya koma fankacecen kitchen, an sanya tayil, sinks, gas cooker, chimney da durowoyi na zamani sannan ga manyan winduna. Haka kawai nake tsayawa na kalli wajen yanda yayi kyau, ya yi ta sani nishaɗi ina kuma yi wa family ɗina addu'a, ba su taɓa gajiya wa da ni ba, suna bani support da jikinsu da aljihunsu.
Tare da Mama muka je muka siyo kayan aikin amma priority muka bi, waɗanda na fi buƙatar su, su aka siya akan daga baya idan abun nawa ya buɗe sosai sai a ƙaro wasu, mun haɗo da manyan robobi dai duk wannan saboda kuɗaɗen ba zasu isa ba ne.
Yaya Zainabu cikin abin da ba mu siya ba ta siya mun wasu sannan Yaya Munnir ya aiko mun da babban buhun fulawa guda ɗaya da na sukari sai katon ɗin baking powder. Farin ciki ya lulluɓeni ganin irin ƙwarin gwiwar da kowa ya ke bani, duk da basu da tabbas ɗin zan yi nasara. Allah yayi wa 'yan uwana albarka, ka kare su daga sharrin maƙiya, Allah ka yawaita masu arzikin su da alkhairin su.
Ranar juma'a na fara gwada aiki a sabon kitchen ɗina, amma ba na customers ba ne, gwajin cake ɗin birthday nayi. Guda uku na gasa masu girma da fasali mabanbanta sannan kowanne kwalliyar shi (decoration) daban. Na duƙufa aiki kunnena na sa earpiece so nake na ga design ɗin ya fito sosai. A hankali na ji an zare earpiece na kunnen dama, ban ɗago ba nace "Sauda ashe kun dawo."
"Yayi chef! Kin duƙufa aiki ko kai ba kya iya ɗagawa." Yace da ni
Cikin murna na ɗago kaina, ban da hannu babu kyau na san da rungume shi zan yi ma "Kai Yaya Naziru! Ban zace ka a kusa ba, na ga ba ka samun sarari kamar da. Sannu da zuwa." Ya haye kan work space ɗina ya zauna, ina aiki muna hira ina ba shi labarin abubuwan da suka wanzu a bayansa.
Da daddare bayan an gama cin abinci ana zazzaune a falo na ɗauko biyu daga cake ɗin domin a taya ni ɗanɗanawa ko yayi ko akwai abin da zan yi adjusting a gaba idan zan yi. A ƙaramin na rubuta 'welcome home Yaya Nazy' ɗayan kuma happy family kaɗai na rubuta.
Yabon da Yaya Naziru yayi mun har sai da ya fasa mun kai. Kuma dama tun asali ina da handwriting mai kyau sosai, anan ma ya nuna don yayi kyau ga decoration ɗin sosai da sosai ya fito. Mama har tana cewa "ni abin ma ya daina ba ni mamaki, ranar muna zaune aka yi miya irin ta inyamurai a TV, washegari kasuwa kawai ta shiga ta siyo abun da babu kuma tsaf tayi miyar, ina ga dai she's born for this."
Da Yaya Naziru zai koma sai ya sanya nayi mashi cupcakes na kwano ɗaya domin tafiya da shi kuma ya matsa mun ta dole sai da na karɓi kuɗin aiki, yace haka ake supporting business ɗin family member, idan ba haka ba sai a kashe wa mutum kasuwa ai. Asali da tushen fara snacks ɗina kenan.
Ranar Litinin da yamma Fa'iz ya kira ni a waya kan cewar zai zo mu gaisa ya taso daga wurin aiki ne yanzu. Ganin mun daɗe ba mu haɗu ba sai na ba shi izinin duk da cewar a gajiye nake domin nayi samosa da spring rolls har na kwano biyu an zo an ɗauka.
Gab da magrib ya iso, ko gaisawa cikakkiya ba mu yi ba aka kira sallah, don haka na raka shi wurin famfon farfajiyar gidan yayi alwala ya kuma wuce masallaci.
Bayan dawowarsa kuma sai na taho masa da samosa da spring rolls ɗin haɗi da lemo mai sanyi. Yana ci yana mun santi ina dariya nace "ashe na iya abun nan sosai." Ai sai ya ƙara haramar ci yana ƙara tambaya ta akan sana'ar tawa, domin sai a lokacin ya san ina yi wa mutane, kawai dai yana yawan kira ya ji ina kitchen ina aiki.
Ban ankara ba sai ganin Aminu nayi yana shigowa harabar gidan da wayar shi a kare a kunnen shi da alama ni yake kira ga shi na baro wayar a ɗaki. Sai da gaba na ya faɗi lokacin da muka haɗa ido, ina ganin lokacin da guntun murmushin fuskar shi ya ɓace gabaɗaya lokacin da idon shi ya faɗa kan Fa'iz da yake ciye-ciyensa, a take kuma ɓacin rai mai tsanani ya lulluɓe fuskarsa, karon farko da na fara ganin haka.
Shirun da nayi ne ya sanya Fa'iz juyawa don ganin me ya ɗauke mun hankali haka. Ganin Aminun da yayi ne ya sanya shi miƙewa yana cewa "Bara na tafi amma fa da plate ɗin nan zan tafi, don ba zan iya barin abun ciki ba but I'll return it sha, bye matsoraciya." Yana murmushi kaman yanda ya saba ya juya ya kama hanyar fita ba tare da ya kalli ɓangaren da Aminu yake ba bare na sa ran za su gaisa.
Shi kuma Aminu ya ja tunga ya tsaya tare da harɗe hannayensa a ƙirjinsa yana kallo na, ɓacin ran fuskarsa yau kam ya ƙi ɓoyuwa. Ni kuma sanyin jiki da rashin gaskiya ya hana ki motsawa, kawai jiran shi nake ya ƙaraso domin na niyyar jure dukkan ɓacin ran da zai nuna mun yau saboda nasan ko ma mene laifi na ne.
Idanuna suna kanshi yayin da naga ya juya alamar tafiya zai yi, gaba na ya cigaba da faɗuwa ina jin bugun zuciya ta dum dum domin ban san ta wurin da zan fara bada haƙuri ba, irin wannan fushi haka? Kamar almara kuma sai na ga ya juyo ya doso ni, gudun kar na ƙara laifi sai na tashi daga kujera ta na koma kan wadda Fa'iz ya tashi a kai na zauna.
Ko da ya ƙaraso sai ya ja ya tsaya, ya sanya hannun shi na hagu ya dafa kujerar da na tashi a kai, yace "Ummu Kulsum! Ummu 'yan matan gari. Ga ni na iso, tsara ni yanda kike so." Na zuba masa ido don ban gane tsarin da ya ke faɗa ba.
Ya cigaba "Ya muka yi da ke akan saurayin nan naki? Ni munafurci ne bana so. Kin nuna kamar ba kwa tare amma idona ya gane abu daban. Hmm! Mata!
Kalmar munafurci da ya ambata ta yi mun zafi, amma na daure na cije na share ganin cewa nice na yi masa laifi nace "Ka yi haƙuri Aminu, wallahi waya kaɗai nasan muna yi and kuma ba saurayi na ba ne kamar yadda ka zata, infact yana sane ka kawo kuɗi kuma lokacin bikin kawai ake kira. Allah ya ba ka haƙuri, yau ma zuwan tsautsayi....."
Ya katse ni "Malama kar ki raina mun hankali mana, ba ga shi daga ganin tahowa ta ba kika canza kujera zuwa wadda ya tashi, watau sabon salon haɗa jiki ko?"
Tsananin mamaki ya sa na saki baki ina kallon Aminu, ashe ba gwaninta nayi ba? Na ɗauka zai ce ba zai zauna akan kujerar ba, shi yasa na tashi na ba shi tawa. Sau uku ina buɗe baki da niyyar amsa maganarsa amma na rasa amsar ma balle na faɗa.
Raina na ƙuna nace "Don Allah Aminu ina ce ita mace allura ce cikin ruwa, ni ban ga ta wurin da Fa'iz ya tare ka bare har ka ɗaga hankalin ka. Da kaina na zaɓe ka fa bayan nasan da shi, kuma ba saurayi na ba ne na daɗa jaddada wa. Wait... Ina ce bikin mu bai wuce wata ɗaya da satittika ba?...."
Irin kallon da yake mun shi yasa maganar ta katse iya haka na cigaba da kallonsa ina ƙoƙarin fahimtar sa amma jumla ɗaya yake maimaitawa kamar yana ƙoƙarin tuno ma'anar ta watau 'allura cikin ruwa'. Ya kuma juya bai ƙara kallona ba ya doshi gate ya fice yana ta maimaitawa.
Ko da na shiga cikin gida nasan ya kyautu a ce na kira Aminu na ba shi haƙuri amma ganin kamar bai yarda da ni ba, sai kawai na share shi tare da kashe wayar gabaɗaya (learn to say sorry whenever you are at fault, kar girman kai ya sa ka watsar da abu mai mahimmanci a rayuwar ka).
Da safe ma sai wurin sha ɗaya na kunna wayar. Duk ilahirin saƙonnin da suka shigo waya ta na gama buɗe su babu ko ɗaya daga Aminu. Tsananin mamaki ya kama ni, watau jira na yake yi na fara yi masa magana don haka sai na dake, na kawo ido na zuba masa domin na ga iya gudun ruwan sa duk kuwa da ina ganin shi online yana ta posting da canja hotuna.
Girman kan da muka ɗaukarwa kan mu sai da ya kaimu sati guda, ba waya (dama ba koyaushe muke yi ba) ba saƙon waya bare kuma chatting ɗin da muke kusan raba dare muna fama.
Kasancewar kusan kullum tare muke a gida da Mama tana ankare da abubuwa na. Ina jin lura ta yi akwai sauyi a tattare da mu, domin ranar talata muna zaune a falo daga ni sai ita a gidan sai masu aiki. TV a kunne amma hankali baya kai duk da waya ta tayi tsuwwa alamar shigowar saƙo ko kallon wayar ban yi ba bare na duba. Kasancewar tunani na yayi nisa ban ji maganar da take mun ba sai da ta kira suna na da ƙarfi sannan na farga.
Na kalle ta nace "Mama magana kike yi ne?"
"Me ya same ki haka kike tunani?" Da alamar tsoro a muryar ta.
"Ba komai fa. Wasiƙar jaki nake yi kawai."
"Kin manta, wasiƙar dila kike yi ba na jaki ba. Ina ce abin da suke yi a TV yana ɗaya daga favorite program ɗin ki ba kya son ya wuce ki?"
Dariya faɗan na ta ya bani sannan nace "Kai Mama, dama akwai wasiƙar dila?
"Eh mana, dila sarkin wayo ba."
Ai kuwa na cigaba da dariya, kamar a sama sai naji tace "Ko dai wani abu ya faru tsakanin ke da Aminu ne?"
A take komai ya dawo mun har fuska ta sai da ta nuna rashin jin daɗi, sai kawai na warware mata abin da ya farun, domin nasan faɗar zai rage mun takaicin abun a raina.
Ta yi tsaki tace "Mts! Yaran zamani, na rasa wane irin tunani gare ku. Watau ke da shi duka kun sa girman kai ko? Idan fa ana buƙatar zama ya ɗaure, gyara abin da ya kusa karewa ake yi, ba wai a karya shi a watsar a fita can wani wuri neman sabo ba. You must fix what's broken. An ce maku mu duk da kuka ga mun kai waɗannan shekaru tare da mazajen mu, an ce ba ma samun sabani ne? Ko an ce maku we are living in ice cream truck ne? Dole akwai good and bad days, sirrin shine ba ma barin bad days ɗin su lalata zaman mu, we are always fixing it. Kuma don ka ba wa abokin zaman ka haƙuri me ye abun faɗuwa a ciki? Ke duk kin fi kowa laifi, me yasa ba ki neme shi kin ba shi haƙuri ta waya ba tun da lokacin da yazo yana cikin ɓacin rai. Kuma me yasa kika ce Fa'iz ɗin ya zo? Shi ma tunda ya san an kawo kuɗin ki ai sai ya rabu da ke."
Na ce "Mama to ta yaya kika gane Aminu ne damuwa ta?"
Ta amsa "Ni na haife ki fa Hajjaju, kuma kwana biyu na daina ganin kina ɓata lokaci akan waya kina ta murmushi kamar bi ta can."
Da gudu na tashi da waya ta ina dariya zuwa ɗakin mu ina faɗin "Kai Mama, kai Mama don Allahhhhhhh."
Ta ɓangaren Fa'iz yanzu kuma gabaɗaya na daina sakar masa fuska sosai bare ma mu yi ta hira irin yanda muka saba. Hakan bai hana shi kira na yanda ya saba ba, amma sau ɗaya jal nake amsa wayarsa a rana ko zai kira sau nawa yanzu bana ɗauka.
Abu kamar wasa, Abubakar har sun fara maganar kawo lefe. Ni kuma bansan matsaya ta ba ga shi yanzu saura wata ɗaya, ni da Aminu muna gasar wa yafi wani iya fushi da shariya.
Ranar da Baba yace gobe Yaya Zainabu ta zo domin tafiya da mu zaɓen kayan ɗaki, a ranar Mama ta rutsa ni a ɗaki akan lalle sai na nemi Aminu domin sanin a wane babi muke ciki kafin zuwa goben da yaya Zainabu za ta zo.
Raina ba ya so amma haka na daure na kira wayar shi wurin ƙarfe tara da rabi na dare saboda ina kyautata zaton yanzu free ya ke ba ya komai. Zuciya ta sai bugawa take yi da ƙarfi sannan numfashi na yana fita da sauri-sauri, sai cewa nake Allah ka sa kar ya wulaƙanta ni. Har na fitar da ran za'a ɗaga wayar sai naji kuma ya ɗaga.
"Alo? 'yan mata ran gari."
Muka gaggaisa ba wani alamun mun yi kwanaki ba ma magana, har ma yana ba ni uzurin abin da ya hana shi ɗaukar wayar da sauri, ya je kitchen neman abinci ne.
Sai yace "Ya aka yi ne Madam de Madam?"