Free chapter · Read without an account
26
Kwanaki da yawa bayan nan, Yaya Naziru an yi masa canjin aiki zuwa Legas cunkus ɗakin tsumma kenan. Wannan zuwan da yayi gida ya zo ne domin ƙara saurin maganar shi da Surayya, yanda yana tarewa a Lagos ɗin babu daɗewa za ta biyo shi.
Shi da Yaya Zainabu suka yi ta zirga-zirgar siyayyar kayan sa ranar, sai dai su tambayi Mama me ya kamata a ƙaro ko abin da suka manta ba su siya ba. Ko ni kayan sun burge ni bare ita Surayya da dama sarkin kwalliya ce kuma kayan sun dace da ita.
An tsayar akan wani satin me kamawa za'a kai kayan, da alama sun gama shiryawa da gidan su Surayyan a haka. Tsakani da Allah rawar kan Yaya Naziru bala'in haushi yake ba ni kawai, don ma ya ci sa'a akan ƙawa ta yake yi, da ba don haka ba da yanzu mun fara tsanar ta ina ga.
Rabon da mu haɗu da Surayyan ma tun ranar sunan Fatima, sai dai muna yawan magana ta WhatsApp. Kullum hotunan ta tare da Yaya Naziru ake sawa a status ko a sa na shi shi kaɗai a yi ta rubutun kalaman soyayya, shi kuma babu rubutun soyayya amma yana sa hotunan ta ba laifi. Ina sane da su duka, kuma abun na mun daɗi ganin ita ma tana son ɗan uwana kamar yanda yake son ta.
Ranar wata juma'a muna zaune a falo kafin masallaci sai ga Yaya Mahmoud ya iso, ko gama ɗokin murnar zuwan shi ba mu yi ba, ya juyo kaina tare da miƙo mun ambulan babba kalar ruwan ƙasa. Bai yi ƙarin bayani ba don haka sai na buɗe don ganin menene a ciki. Takarda ce kawai guda ɗaya, ina zaro ta gaba na ya faɗi domin takardar ɗauka na a makaranta ce. A taƙaice dai makaranta ya nemo mun, kuma ɗaya daga cikin makarantun da na raina a faɗin Kano watau Sa'adatu Rimi College of Education, a take na fasa kuka har ina ɗora hannu saman kai ina faɗin na shiga uku.
Afusace ya fara magana da alama dama jiran haka yake yi "Dama na faɗa maki zan ba ki mamaki ai, gabaɗaya kin ƙi mayar da hankali a game da batun makaranta don kawai an kore ki? Ke kaɗai aka taɓa kora daga makaranta? Ke ba za ki ma godewa Allah ba wai rashin ƙoƙari ba ne ya zama sanadiyyar korar ta ki ba? Wasu fa suna can ƙwaƙwalwar karatun ma ba'a basu ba kuma suna matuƙar son karatun. Butulci za ki yiwa wanda ya ba ki? Ke ba makaranta ba, ke ba aure ba. Kuma gara ma ki sani wallahi sai kin je makarantar nan ko da kuwa za ki yi kukan jini, infact in sane nace kar wanda ya faɗa maki lokacin da ake neman admission ɗin. Kuma idan kin ga dama ki bari a kore ki a chan ki ga irin kala ta. Mts!" Ya fice daga falon. Mama duk tana jin mu ƙala ba tace ba, sai ma sabgar gaban ta da take yi.
Har dare kuka nake kuma na ɗaukewa kowa na gidan wuta, su ma ba wanda ya shiga sabgata. Har Yaya Naziru da ya iso da yammacin ranar, shi ma faɗan yayi mun sannan ya kama sabgar shi na shirin kai kayan sa ranar shi gobe.
Ranar asabar da sassafe na kira Yaya Muntari ina kuka na yi masa bayani tare da roƙon shi ya sanya baki su ƙyale ni, na rantse da kuɗi na ma zan siya Jamb wannan shekarar na zana, wallahi ko BUK ɗin ne zan iya komawa akan naje Sa'adatu Rimi. Shi bai yi mun faɗa ba illa na lallashi na da yayi akan na yi haƙuri na fara zuwa makarantar, daga baya sai mu san abun yi amma bai kamata mu watsar da ƙoƙarin Yaya Mahmoud ba, ta dole na haƙura don dama shi ne hope ɗina na ƙarshe.
Ina kallo aka tafi kai kayan Yaya Naziru, dukkanin su haushin su nake ji, ga ƙarin su ma sun share ni yanda na share su. Ina jiyo waya ta na ƙara amma ko ta kanta ban bi ba. Duk sa'ilin da na tuna cewar ni Ummu Kulsum ce zan je Sa'adatu Rimi sai na ƙara fashewa da kuka.
Ina daga ɗaki nake jiyo hira da dararrakin su bayan sun dawo daga kai kayan amma ko leƙowa ban yi, su suka sani. Sauda ce ma ta leƙo da turtsetsen cikin ta tana tambayar damuwa ta. Ita ma haƙurin ta ba ni sannan ta tunatar da ni faɗin Allah maɗaukakin sarki na cewar 'sai ɗan adam ya so abu, sai abun ya kasance ba alheri ba ne a gare shi ko kuma ya ƙi wani abu sai abun ya kasance alkhairi ne a gare shi'. Maganganun ta ne suka sanyaya mun zuciya har na haƙura na tashi domin yin wankan da ban yi ba gabaɗayan ranar.
Sai da aka yi magriba sannan na duba waya ta, missed calls ɗin Fa'iz yafi na kowa yawa, don haka kiran shi na fara mayarwa.
"Ummu lafiyar ki ƙalau yau kuwa?" Da haka ya amsa kiran wayar da nayi masa.
Bansan lokacin da murmushi ya suɓuce mun ba "Ba na kusa da wayar ne, ka yi haƙuri ka ji?"
"Kin gan ni na kusa ƙarasowa gidan ku ma, kin firgita ni sosai. Nan da minti biyar zan ƙaraso." Bai jira amsa ta ba ya kashe wayar.
Don haka da hijabin da nayi sallah na fito waje domin jiran shi. Ta cikin mutanen da basu tafi gidajensu ba da suke zaune a falo na bi na fito waje, ba wanda na kalla balle na yi gaisuwa, dama haushin su nake ji ai. Duk cikinsu an rasa wanda zai neme ni ko irin ɗan haƙurin nan a ba ni, kai ai ko rarrashin na a yi ko?
Ina gama ajiye kujera wurin zaman mu yana shigowa harabar gidan, tunda ya shigo kuma idon shi yana kaina, kamar yana laluben ganin wani abu daga gare ni. Kulawar da fuskarsa ta nuna a kaina sai da naji zuciya ta ta rusuna sosai, raguwar damuwa ta sai naji tana fita, nutsuwa ta sosai tana maye gurbin ta.
Murmushin jin daɗi nayi nace "Fa'izuna me kake nema ne? Ko rahoto aka kai maka na ɓata?
Daga gefen mu muka ji an ce "Ya Fa'iz ina wuni?" Hassana ce ta gaida shi, ban san daga ina take ba, suka gaisa ta wuce cikin gida.
Sannan ya juyo kaina "Ai da ɓata ma kika yi, ni ma da yanzu cigiya ta ake." Alamun rashin wasan da na gani a fuskar shi ne ya sanya na fara dariya.
"Kin san me?...." Zuwan Hassana ne ya katse maganar shi. Snacks ta kawo mashi da lemo da alama na gidan kai kaya ne. Ni yanda suke son shi har mamaki yake ba ni, Hussein ma yanzu haka yake yi mashi bare Sauda da Yaya Zainabu kuma.
Ya cigaba bayan ta tafi "Haka kawai ɗazu da rana kika dinga faɗo a zuciya, ko yaya na motsa sai na ji na tuna ki kuma gaba na yayi ta faɗuwa, nace anya wannan lafiya ƙalau take? Ga shi na dinga kiran ki a waya ma naji ko lau kike, ba ki ɗauka ba. Gabaɗaya na rasa me ke damu na, dauriya na yi na bari sai dare amma da tun da yamma za ki gan ni a gidan nan." Fuskarshi ɗauke da gaskiyar maganar shi.
Murmushi nayi tare da ƙura mashi ido, wani irin so da ƙauna shi na ƙaruwa a zuciya ta, ni yanzu akwai abin da zan nema sama da zama na tare da Fa'iz? Yana da matuƙar kulawa sannan yana da fahimta. Tunda muke tare da shi bana jin na taɓa ɓata mashi rai, ƙarewa ma yanzu kalli abin da ya faru, ba ma tare amma damuwa ta ta same shi daga wata hanya da ni kaina ban gane ba.
Hannuna na ji ya girgiza "Ummu talk to me mana, kina ba ni tsoro. Akwai abin da yake damun ki ne?
A hankali na zayyane mashi komai sannan na tabbatar masa a halin yanzu ba ni cikin damuwa, zuwan shi ya wanke mun komai.
Ya sauke murya ƙasa ƙwarai yace "to me yasa ba kya son can ɗin?"
"Sai fa da na kai mataki na uku a BUK kafin na bar makarantar."
"Level 3?" Ya buɗe idanunsa cike da mamaki "Me ya faru?"
Sai a sannan na tuna ashe ba shi da masaniyar komai da ya danganci rayuwa ta kafin shi, a take na zayyane masa komai.
Ya ji ciwon abun nan ƙwarai da gaske, haka kawai ya dinga faɗa har abun ya koma ni ce ke ba shi haƙuri. Sai kuma ya sakko ya ƙara kwantar mun da hankali har ya ƙara da cewa "Ki yi haƙuri ki fara wannan, daga baya sai ki rubuta Jamb mu sake makaranta. Daɗin ta gida na za ki dawo kuma sai abin da kike so za'a yi a zancen makaranta. Kar ki wani damu kan ki, kin ji Ummu na?" Yana mun magana kamar wata shekara biyar, abun kuma daɗi yake yi mun.
Na amsa da gyaɗa kai ina murmushi
Ya ƙara faɗin "za ki yi ko?"
"Um"
"Ba za ki ƙara damuwa akan haka ba ko?"
"Fa'izuna ka kwantar da hankalinka, na daina da gaske. In shaa Allah ba zan ƙara damuwa." Sai daɗina nake ji.
"Amma ba ke kika yi abun nan ba ko?" Ya tambaya bayan ya gutsiri samosa.
"Ni ce nayi" na amsa ina dariya ƙasa-ƙasa.
"To ni dai sai naji kaman da bambanci, kin san duk wanda naci sai nace Ummuna ta fi iyawa."
Na ƙyalƙyale da dariya nace "Ba ni ba ce nayi."
"Yes! Ai dama na sani!"
A haka muka yi ta hirar mu har sai da goma tayi ya tafi, shi ma don baya son Baba yayi mana magana ne, amma yau ji yake baya son tafiya ya bar ni. Yana kuma isa gida ya kira ni har sai da dare ya fara nisa tukunna sannan muka yi sallama. A zamana da Fa'iz wannan ranar ta shiga ranaku mafi soyuwa a wurina.
**************
Ranar Alhamis ina ta sauri na isa Game stores da ke Ado Bayero Mall, Zoo Road, kayan girkin da zan yi wa wasu ne gobe ne nake neman ƙari, ban lura nawa sun ɗauko ƙarewa ba ga shi yamma ta yi balle na tafi kasuwa wurin da na saba soyayya, Allah ma yasa na duba ɗazun da gobe ban san yaya zan yi ba, domin bana son neman abu ranar da zan yi amfani da shi duk sai na zama disorganized. Sai bakwai da rabi na samu sararin baro store ɗin, hankali na yayi gida gabaɗaya kafin Mama ta fara wayar ina na tsaya haka.
Ai ban yi nisa ba naji ana ƙwala mun kira daga bayana "Anty Ummu! Anty Ummu!"
Da sauri na waiga, na kuma hango Amir yana bi na da gudu domin cimma ni. Cike da farin ciki na tsugunna domin tarbar shi, yana ƙarasowa na rungume shi, Allah ma ya sani ina son yaron nan.
Cikin murnar gani na yace "Anty Ummu ina kwana?"
Nayi dariya nace "Ina wuni dai ko Amir? Ko ba ka ga dare yayi ba? Lafiya lau. Tare kuke da su mummy da Maama?" Na tambaya.
"A'a. Daddy ne yace na jira shi a mota yana zuwa."
A take gaba na ya faɗi, don haka na fara shirin guduwa kafin ya dawo ya iske ni tare da ɗan shi. Amma sai ya kama hannuna ya fara ja yana cewa "Anty Ummu zo mu je ki ga Uncle Jamil, shi ma yana mota."
Ganin wanda ya kira Uncle Jamil ɗin yana kallon mu shi yasa na yarda na ƙarasa muka gaisa. Amir sai damu na yake wai na tsaya sai daddy ɗin shi ya zo tukunna amma sai na lallaɓa shi akan sauri nake yi. Har na fara tafiya bayan na yi masu sallama, sai na ji shi ya biyo ni a guje wai na tsaya mu yi hoto zai nunawa Maama da mummy idan ya koma gida.
Wayar ya miƙo mani tare da cewa "Anty Ummu yi mana selfie." Dariya na dinga yi wai kamar Amir ya san selfie, don haka da dariyar na ɗauki hoton, na kuma ɗaga tawa wayar na ɗauke mu. Da kyar na samu ya bar ni na tafi.
Da daddare bayan na ƙare dukkanin abubuwan da zan yi sai na sanya hoton a status ɗina. Hoton yayi mun kyau domin kamar Amir yana matuƙar yanayi da Fa'iz, ganin fuskar ɗan da zan haifa tare da Fa'izuna nake yi masa.
Fa'iz yana ganin hoton ya tambayi a ina muka haɗu da Amir haka? Daɗin yanda su Amir suke so na yake ji sosai. Haka lokacin da na faɗa masa yanda nake kallon Amir a ido na, sai ya ɓige da magiyar na haƙura kawai mu haɗa bikin mu da nasu Yaya Naziru ko ya samu ya ba ni irin Amir ɗin. Dariya kawai na yi ban amsa ba.
Washegari ko ta kan Fa'izuna ban bi ba saboda yawan aiki, domin wannan karon har sai Hassana da mai aikin Mama suka sanya mana hannu. Sai yamma liƙis muka kammala aka zo aka ɗauka, don haka a masifar gajiye nake. Ina da idar da Isha na kwanta bacci don ba ni da wani saurin ƙarfi kuma. Yanda aikin ya gajiyar da ni, haka na samu kuɗi mai tarin yawa.
Bayan mun kammala aikin ranar ne, bayan na zauna nake yi wa Mama mitar ni aikin nan ya ishe ni kamar na daina yi gabaɗaya. Tayi murmushi tace "Ummu kenan, ai kowa da kika gani yana aiki dauriya kawai yake yi amma shi ma yana gajiya. To har gara ki yi aikin da kika san kin ƙware akai kuma kina so, hakan ne zai sa ki yi shi ba tare da damuwa ba. Kuma a ina tabbata succeeding babu resilience?" Mama dai kullum ita take motivating ɗina duk lokacin na ji kamar na bari, hakan yasa kullum ci gaba nake samu.
****************
Shirye-shiryen makaranta ba ni nake zuwa ba, Hussein ne yake yin komai kuma ina kyautata zaton Yaya Mahmoud ne ya sanya shi. Ganin da gaske yake yi sai na je makarantar hakan ya sanya naje kasuwa na siyo yaɗin hijabai ya kai kala goma sha biyu, na kai aka ɗinka mun dogayen riguna da hijabai zuciya ta na ƙuna. Na kuma nemo wurin da ake siyar da niƙabi na siya kala biyar duk baƙaƙe. Ina sane Mama da Hassana dariya suke mun a bayan ido na, na share kaman ban sani ba, kuma daɗin abun ba wanda yake zancen makarantar a gaban ido na kaf gidan.
Kasancewa ta aminiya ga Surayya dole tare muke shirye-shiryen bikin ta, don haka ba zama muka cika yi ba. Idan kuma muka fita, Yaya Naziru ya dinga damu na da waya kenan domin jin me muke yi, na haƙura na daina jin haushin su na saduda kawai. Kulawar da suke ba wa juna nake addu'a Allah ya ba ni wanda za mu yi wa juna fin hakan ma.
Mun je wurin masu ƙunshi/lalle domin tuntubar su game da kuɗin yi da zancen kama layi. An kuma nuna mana kala-kalan lalle da kuɗaɗen su, tsabar ruwan ido ba ƙaramin lokaci muka ɓata a shagon ba, sannan da kyar muka samu muka zaɓa ɗin. Kasancewar daga wurin lalle zuwa gidan Yaya Zainabu ba nisa sosai sai kawai muka taka domin direban su Surayya yana sauke mu a shagon ya wuce kasuwa, hajiyarsu ta aike shi, sai ya gama sai ya kira ya ji ina muke sai ya zo ya ɗauke mu.
Tafe muke muna hira irin ta ƙawaye muna ta dariya kamar ba'a titi muke ba. Kwana kaɗai ya rage mana mu shiga layin gidan Yaya Zainabu. Ban lura da wucewar wata mota ba kwata-kwata, burkin da aka ja da ƙarfi ne ya ja hankalin mu zuwa ga motar, a yayinda ita motar kuma take dawowa da baya.
Gaba na sau uku yana faɗuwa a jere bayan na hango fuskar Aliyu. Cike da dauriya na kau da kaina tare da nuna halin ko'in kula, fata na ɗaya Allah ya sa Surayya ta ɗau haske don kar ta ɓata mun plan ɗina.
Ganin mun wuce shi ba tare da mun tsaya ba ya sanya yayi parking tare da biyo mu da sassarfa, ya kuma sha gaba na. Titin ba mutane sai motoci da suke wucewa jefi-jefi.
"Ummul? Ko ba Ummu ce?" Ya tambaya cike da mamaki.
"Na'am?" Fuskanta ba alamar sanyaya, kallon wanda ban taɓa gani ba nake yi masa.
Da alama ya lura da irin kallon da nake yi masa yace "Ummu ba ki gane ni ba ne?" Ya zaro idanu.
Na amsa "Don Allah ka yi haƙuri, na kasa shaida fuskarka, sai dai kaman kana mun yanayi da wani."
Sau uku yana buɗe bakin shi yana rufewa saboda mamaki, sai kallon ƙwayar idona yake yi domin son tabbatar da zance na. Sai kuma ya hau laluben aljihunsa ya fiddo wayarsa, cikin sauri ya buɗe wani abu ya juyo da fuskar wayar zuwa gare ni yana faɗin "Ke ce wannan?"
Hoto na da Amir ne na rannan kuma tabbas wannan wayar Amir ya kawo mun domin ɗaukar hoton, don haka sai na canza yanayin fuska ta tare da cewa "Eh, ni ce da Amir. But wait.....ko kai ne babansu Maama?"
Kamar ba zai amsa ba, yana kallo na da mamaki a fuskar shi sannan ya motsa yace "Iya wurin da kika sanni kenan?"
Sai nayi murmushi nace "A'a, ai nasan kai yayan Fa'izuna ne. Ashe shi yasa nake maka kallon sani, kuna fusgar yanayi da Fa'iz."
Fuskarshi kamar an zuba mashi tafasasshen ruwan zafi yace"Shi ke nan sanin da kika mun?"
A take na mayar da fuska ta babu wasa na amsa "Am i supposed to know you from somewhere?" Na ƙarasa maganar kaman ina cikin ruɗani, ina kuma watsa hannaye.
Ya tsare ni da ido na daƙiƙa kusan goma, ni ma na tsare shi da nawa. Nasan mamakin yanda nake kallon cikin idon sa yake yi, saboda da komai zai faru ba na taɓa iya kallon shi, sai ya juya yana sosai ƙeya da makullan mota cikin ɓacin rai sannan ya sake juyowa kuma lokacin idon shi ya sauka kan Surayya da take tsaye tana ƙare mana kallo, fuskarta sam ba ta nuna komai ba. Yace "Yauwa...um...ummm....Fat....no... Zara'u Darma ko?"
Ba ta amsa da baki ba, kai kawai ta girgiza alamar a'a.
Ya sake juyawa tare da doka hannun shi na dama a na hagu yace Shit!
Sai kawai na kama hannun Surayya na kuma ce masa "Daddyn Amir za mu wuce, ka gaishe mana da su Maama. Sai an jima."
Sai ya katse mun hanzarin "Ku tsaya na kai ku gidan mana."
Na amsa "Babu buƙatar hakan ai, don nan baya ne." Girman da nake ba shi a wannan lokacin saboda Fa'iz ne kuma hakan nake so ya fahimta.
"Ina ne babu nisa? Gidan naku ne anan baya?" He is clearly confused right now kam.
"Eh. Sai an jima."
Ban ƙara sauraron komai na jawo Surayya muka tafi muka bar shi da ruɗani a fuskarsa yana bin mu da ido. Har muka ƙarasa gidan Yaya Zainabu babu wanda yayi magana tsakanin mu da Surayya.
"Ke dakata!" Ko zama ba mu kai ga yi ba Surayya ta fara magana bayan shigar mun falon gidan Yaya Zainabu, "Wannan ba Aliyu ba ne?"
Cikin halin ko'in'kula nace "Shine, me ne?"
"Ji nayi kina danganta shi da Fa'iz, yayansa ne?"
"Eh mana."
"Kambu! Dama kin san hakan tun lokacin da kuka haɗu?"
Shigowar Yaya Zainabu falon ya sanya ban amsawa Surayya ba, sai da muka shiga ɗakin da na zauna lokacin ina BUK domin yin alwala sannan na amsa "Ban daɗe da sanin haka ba fa."
"Me yasa to har yanzu kike tare da Fa'iz ɗin?"
"Saboda tsananin so da nake yi masa. Surayya ke fa mai ba wa wani labari ce, kin fi kowa sanin Aliyu tarihi ne yanzu a rayuwa ta da ba zai gogu ba."
"To ai ni abun ne ya ɗaure mun kai. Me kika yanke akan yanda za ki yi mu'amala da su? Don kaman ban ga alamar Aliyu na ƙoƙarin barin ki a matsayin tarihi ba, to uwarsa yake son ki tuna ko yaya?"
"Kar ma ki kawo wannan maganar, mu'amala iyakar ta tsakani na da Fa'iz kuma zancen Aliyu ba daga baki na zai fara ji ba in shaa Allah. Sannan kar ki manta matar Aliyu wayayya ce ta nunawa a gari, me zai yi da ni?"
Tayi ajiyar zuciya tace "da alama kin gama tsarin yanda za ki tafiyar da Aliyu."
Dariya maganar ta ba ni "Kin ga laifi na? Ba fa zan taɓa nuna na gane shi ba ko da na daƙiƙa ɗaya ba ne, tafiyar da shi zan dinga yi kaman tunanina ya ɓace bayan rabuwar mu."
Bayan dawowa ta gida, idan na tuna arangama ta da Aliyu sai na fara dariya ni kaɗai. Ruɗanin fuskarsa was priceless, fata na Allah yasa abun yayi masa ciwo sosai da sosai. Mama gajiya tayi da dariyar da nake yi ni kaɗai ta fara faɗa, faɗan sai ya ƙara mun dariya ba shiri na koma ɗaki kafin ta kawo mun hannu.