Free chapter · Read without an account
31
Ganin biyar ta kusa cimma ni a asibiti sai na yi wa Humaira sallama akan cewar zan dawo anjima da daddare. Akan hanya na tsaya na siya kifi domin sanin cewar Fa'iz ya fi son shi fiye da nama kafin na ƙarasa gida.
Ko wanka ban yi ba, ina gama faɗawa Mama zancen ciwon na shi (kawai ba shi da lafiya an kwantar da shi) na wuce kicin ɗin ta. Biyu na raba kifin, rabi na gasa masu shi sai kuma nayi farfesu da ragowan. Na yi wanka na koma ina jiran a kira magrib na yi sallah na koma asibitin.
Tare da Hussein muka tafi a motar Baba, yana kuma duba jikin Fa'iz ya tafi yawon shi tare da ce mun na kira shi idan na kammala sai mu koma. Nasan dama don an ba mu aron mota ya sa ya biyo ni jikinsa na rawa don ya samu abun yawo.
Wannan karon ban sake ba, domin yanzu har gwaggo na wurin tare da wasu mata kusan su biyar, Anty Hawwa kaɗai na shaida a cikin su. Sannan ga wasu 'yan mata da na san na gansu a birthday ɗin Amir, kunya gabaɗaya ta lulluɓeni. Fa'iz kuma idon shi a buɗe yake kuma ya zuba mun su don ni yake kallo ko yaya na motsa, sai na daɗa takura. A gefen Humaira na zauna tare da ajiye ledar abincin a gaban ta bayan na gaishe da kowa tare da tambayar ya me jiki?
Wannan karon Anty Hawwa ce ta ga Ummu fa, sai naga duk sun sake kallona, ni kuma na ƙara saukar da kaina ƙasa.
Humaira ce ta miƙe tare da ɗaukar ledar da na ajiye ta ƙarasa bakin gadon da Fa'iz yake tana faɗin "Wannan karon duk rashin daɗin bakin ka ba za ka kasa cin abincin Ummu ba na sani." Ta yi maganar ne a lokacin da ta fiddo warmers ɗin guda biyu tare da bubbuɗa su tace "wanne za ka fara da shi to?"
Anty Hawwa tace "Eh lallai dole ki so tarewa a gidansu, ji yanzu daga buɗe warmers har ƙamshi ya cika ɗakin, ina kuma ga an ɗanɗana?" Su duka suka sa dariya har ɗaya daga 'yan matan na cewa "ko dai a ba ki ɗanɗano ne Anty Hawwa?" Shi kan shi Fa'iz ɗin sai da ya yi murmushi bare kuma ni me son a yabi girki na.
Harabar asibitin muka dawo ni da Humaira, ta kuma ɗora daga wurin da ta tsaya da magana ɗazun da rana "Bayan kowa ya hallara sai Hajiya Ma'inna ta fara da cewar zancen auren Fa'izu dole ne a fasa shi. Baba da kowa na falon cikin mamaki aka fara kallon juna kafin daga bisani Baba ya nemi jin ba'asi. Kai tsaye tace saboda yarinya dai budurwar Aliyu ce da yake shirin aura, a take kuma wuri yayi tsit! Baba cikin zafin rai yace Yaya Aliyu yayi bayanin ta yanda aka yi suka haɗa nema shi da Fa'izu, to duka-duka watan shi nawa da dawowa ƙasar da har hakan zai kasance? Kuma a take Yaya Aliyu ya miƙe ba kunya ba tsoron Allah ya bayyana cewar ke ce wadda aka taɓa kai masa kuɗin aure gidan ku. A take kuma Baba ya hassala ya hau bambamin faɗa yace kai Aliyu! Kar ka maida mu ƙanana yara, ina ce muna zaman zamanmu ka bugo waya tare da tabbatar mana cewar an ƙara yi maka bincike akan su, kai da bakin ka ce an ce basu da tarbiyya, kuma an ce tana yin abubuwa a ɓoye da bai kamata a ce ta cancanci zama matar ka ba, ko ba haka kace ba? Ka kuma ƙara da cewa ni da kaina zan iya sake bincika wa na ji, ka kuma sanar mana cewa ai ka samo madadin ta. An yi haka ko ba'a yi ba? Kowa da ke falon yace an yi haka. Baba ya ƙara da cewa ai ga Kawun ka nan, shi ne ya daɗa tausa ta a lokacin, yace aure ana yin sa don a zauna, kuma don gudun kar a ce mu ƙananan mutane ne ba zai sa a tursasa ka ka auri wadda da hannunka ka kawo kuma ka dawo ka ce ba ka yi. Ƙ!"
Nace "Oh! Dama shine abin da ya sanya ba mu ji wani bayani daga gare ku ba sai auren sa kaɗai na samu labari."
Humaira tace "Don't be offended, so nake na samar da ke komai domin ba ni da tabbacin ko Fa'izunmu yana da ƙarfin sake maimaita abin da ya faru a yanzu."
"Ba damuwa cigaba Humaira, ina sauraron ki."
"Buɗar bakin Yaya Aliyu sai yace to ai Baba ai ita kan ta ta kasa haƙura da ni ne shi yasa har ta nemo Fa'iz ɗin a madadina, ko da sun yi aure ma a matsayin ni za ta zauna da shi. Tun da kuma Allah yasa ina da halin yin mata biyu a yanzu ai gara na taimake shi na karɓeta, dama can tawa ce. Wannan maganar ce ta ƙara ɓatawa Baba rai domin cewa yayi au yanzu ita yarinyar ta cancanta a zauna da ita a matsayin mata? Ta kuma zama mai tarbiyya ko yaya?"
Ta ja numfashi na ɗan hutawa sannan ta cigaba "Yaya Aliyu ya amsa da cewar a gafarce shi, a waccan lokacin kawai son ki ya daina idan kuma ba haka yayi ba ba za'a bar shi ya auri wadda yake so ba. Hajiya gajiya ta yi da ja-in-ja tsakanin Baba da Ya Aliyu tace ya isa haka nan, kuma wani satin kayan Aliyu za'a kai gidan ku ba na Fa'izu ba. Dukkannin zancen nan da ake yi Fa'izunmu na zaune gefe guda yana ta kiɗa da 'yan yatsun sa sai kuma a daidai wannan lokacin ne ya ɗago kan shi cikin firgici yace Wallahi ba'a isa ba! Hajiya ta fara faɗa tare da cewa dama can Fa'izu ya raina ta kuma iyayen sa na kallo ba su taka masa burki ba, ga shi yanzu ma a gaban su ta kafa doka ya wancakalar da ita kuma suna zaune babu wanda ya kwaɓe shi."
Fa'izu ya amsa "Yo Hajiya ai kowa ya san wannan lamarin naki ba gaskiya a ciki sai ma tsabar son kai. Kaf ɗin mu ba wanda zai goyi bayan ki bare na wani Aliyu" sannan ya juya kallon shi zuwa ga Aliyu yace "How could you be so selfish?! How could you?! Don't you have conscience? Don't you have a heart or something?!..."
Hajiya ta katse shi "Ai ba shi za ka zaga ba mara kunya, ni ya kamata ka zaga, eh! Ni ɗin nan ba? Kuma ba yardar ka nake nema ba dolen ka ka bi abin da nace ko kuma yanzun nan na tsine maka."
Fa'izunmu yayi wata dariyar ban mamaki yace "Lallai Hajiya ruɗin tsufa na damun ki. Ke a tunanin ki idan kin tsine mun kama ni za tayi? Ashe akwai aiki a gaban ki. Shiru-shirun fa da nake yi ba wai yana nufin tsoron ki nake...." Kawu ne yayi masa tsawa wanda hakan ne ya katse maganar da yake yi.
Kawu ya cigaba "Fa'izu yaushe ka zama mara kunya haka? Uwar mu ce fa, kuma a gabanmu? Ko mutuwa na tsoron idon mahaifi...."
Hajiya jin Kawu yana kare ta sai kawai ta fara kuka tana mitar ai a idonsu Fa'izu yake mata rashin kunya, su suka ƙara masa ƙarfin gwiwa har rashin kunyar ta sa ta kai haka.
Ya Mustapha ne ya katse ta "Ke Hajiya wallahi kin cika matsala, in ban da ke da abin ki meye a cikin maganar nan da har za ki fara kuka, bayan ke ce mara gaskiya. Ai wallahi Yaya Fa'izun ma yayi maki da sauƙi don ni ko taron naki ma ba zan saurara ba bare har naji shirme irin wannan." Duk kwaɓar shi da zungurin shi da gwaggo take yi sai ya karea faɗin maganarsa sannan yayi shiru.
Yaya ma cewa tayi "Hajiya kin fa san gaskiya, son kan Aliyu yayi yawa. Shi fa yanzu haka yana da mata har da 'ya'ya biyu, shi kuma Fa'izu fa? Ya kamata a lura da hakan da wannan. Shi Aliyu idan aure yake son ƙarawa ya je ya nemo a wani wajen mana, Ummu ce kaɗai yarinya a duniya da za'a zo ana ta ja-in-ja a kanta? Tunda ma waccan karon shi ne ya fasa auren ta, yanzu kuma ta zaɓi Fa'izu, shin ba ta gan shi ba ne bayan ya dawo? Ko kuma ita tace shi take so ne? Ko an ce maku ba ta da ra'ayin kan ta ne?" Gabaɗaya falon kowa sai gyaɗa kai alamar amincewa da batun Yaya.
Ai sai Hajiya Ma'inna ta ƙara fashewa har da ɗora hannu saman kai wai yara sun haɗe mata kai kuma iyayen su na kallon su, a na nuna mata cewar ba ita ta haifesu ba kuma ba ta da iko a kansu. Baba ya shiga rarrashin ta sai wani sabon salo kuma ya bullo, wai idan har ba'a bi abin da tace ba, shi da Kawu duka ba ta yafe masu ba. Hakan ya sanya kowa yayi tsit a falon.
Fa'izu ya miƙe tare da cewa "Hajiya wannan fa ba abu ba ne mai yiyuwa, gara ma ki sake sabon lale."
Kawu ya sauke ajiyar zuciya yace "Ina ga abin da ya kamata a yi shine kawai gabaɗayansu su haƙura da yarinyar...."
A tare kuma Fa'iz da Aliyu suka ce "Na'am?!!!" Ya kuma sake maimaita masu abin da ya faɗa ɗin.
Humaira ta ci gaba da magana "Daga nan sai muka ga Fa'izunmu ya doshi hanyar fita daga falon a zuciye yana magana ƙasa-ƙasa da shi kaɗai ya san me yake faɗa, ba'a ankara ba sai gani aka yi yayi karo da ƙofa, buguwa ba ta wasa ba yayi ba kuwa, domin sai da yayi baya ya faɗi a ƙasa tare da doka ƙeyarsa a tayil, a take kuma ya komai ya ɗauke mashi. Yaya Aliyu kam tsaki ya ja ya tsallake shi ya fice daga gidan ma gabaɗaya."
Ta ɗora "Duka wannan ne abin da ya faru Ummu, amma ki yi haƙuri ina son na tambaye ki, tsakani da Allah ki faɗa mun gaskiya kuma maganar za ta tsaya a tsakanin mu ne kawai. Don Allah idan aka ba ki zaɓi wa za ki ɗauka a cikinsu?"
Kai tsaye nace "Fa'izu mana. Kin ga, Aliyu iyakarsa tarihi ne a gare ni tunda hanyar rayuwar mu ta taɓa haɗuwa, kuma iyakar ta kenan. Shi Fa'izu kuma shine buri na sannan kuma gara ma kowa ya sani a gidanmu ba wanda zai yi mun auren dole, atoh."
Dawowar Hussein ce ta ƙwace ni sannan muka yi sallama da ragowan mutanen da suka saura a ɗakin. Na kuma riski Fa'izu ya samu bacci a wannan lokacin.
Kashegari a gida nayi zama na ban je makaranta ba, abinci na girkiwa Fa'izu da kuma masu jinyar shi domin da yawa na yi. Da na isa kuma wannan karon ɗakin da sauƙin mutane, shi ma jikin nashi ya fara ƙwari domin har zama da kanshi yana yi, ya kuma ci abinci ba laifi a yayinda nake zaune kusa da shi. Amir da mummyn su a nan suka iske ni, ina ta tsoron yanda za ta fuskance ni tunda kowacce mace na kishin mijin ta. Amma ga yanda ta nuna mun, imma ba ta san abin da ya faru ba ko kuma tsabar iya zama da mutane ne da ita, don kwata-kwata ba ta canza a yanda take mu'amala da ni ba.
Da yamma bayan Baba ya dawo sai ga Kawu Habibu, har ga Allah na ɗauka zumunci ya zo sai da Baba ya aiko a kira ni sannan nasan zancen Aliyu ne ya kawo shi. Shi ma dai Kawu Habibu, idan maye ya ci ya manta bai kamata a ce uwar ɗa ta mance ba.
A bayanin Kawu Habibu wai Aliyu ne ya je har gidan shi ya same shi, ya kuma roƙi gafarar abin da ya aikata a baya. Wai misinformation ya samu a kaina shi yasa aka ji shi shiru, don yayi tunanin faɗin dalilin barin aurena zai zamo kamar cin fuska ne a wurin su Baba. Amma yanzu da ƙarfin shi ya dawo, idan an ce nan wata ɗaya ne ma bikin, wallahi a shirye ya ke. Ya kuma san bai kyauta ba, shi yasa bai zo kai tsaye ba da kan shi ba, amma zuwan Kawu Habibu sharar fage yayi mashi shi ma yana tafe ko da zuwa gobe ne.
A take nace "To Kawu Habibu ba ka faɗa mashi akwai kuɗin wani a kaina ba ne? Duk ba ma wannan ba, ni ce fa na kawo shi gidan nan don ina son shi ya kuma bula mana ƙasa a ido don haka yanzu I'm so over him, ba yanda za'a yi na komawa wanda ya bar ni saboda wata mace wallahi ko da ɗan gwal ne!"
Kawu Habibu yace "Amma Ummu ai the devil you know is better than the angel you don't know."
Na yi murmushi nace "Abin da yayi Aliyu shine yayi Fa'iz ai, cousins ne. Aliyu is a selfish bigot, ba wanda yake sauraro idan akan batun son kan shi ne. Idan har ban auri Fa'iz ba sai dai kowa ya rasa. Wai kai ma Kawu Habibu ba a gari ka tsinci maganar auren sa ana gobe za'a ɗaura ba? Ai ina ce a gidan nan nazo na iske ka lokacin ka zo da wasu daga abokan ku lokacin bayan ka ji maganar? To an ce maka waccan mara kirkin Aliyun ya sauya ne?"
Baba ne ya dakatar da maganar yace na tashi na tafi, dama yana son sanin me ke faruwa ne. Kuma a musulunci haramun ne neman aure cikin aure sai dai idan ɗayan ya janye ko kuma yayi maka izinin nema ɗin. Aliyu dole ya haƙura domin Ummu ce me zaman auren kuma ita ta zaɓawa kan ta wanda hankalin ta ya kwanta da shi.
Bayan tafiyar Kawu Habibu Mama ta kira ni domin sanin kan zancen don ita ba ta gane me Baba da Kawu Habibu suka faɗa mata ba, a take kuma na warware mata komai. Haushin Aliyu ya cika mata ciki, ta hau faɗa tana cewa har laifi na ma, da ban ba shi fuska ba da ba zai samu audacity na abin da yake yi ba, kuma naje na kama magana na haɗiye na ƙi faɗawa kowa da kyar ta haƙura ta bar maganar bayan ta faɗa mun na dage da istikhara da addu'a, in shaa Allah komai zai warware a hanya mafi sauƙi.
Kwanan Fa'izu huɗu a asibiti bayan farfaɗowar shi aka sallame shi, ba wanda ya ƙara tayar da maganar a gidansu ko da daga wurin ita Hajiya Ma'inna ma. Don haka har yanzu ba mu san matsayar zancen auren mu ba.
Ta ɓangaren Aliyu tun sanda ya ji labarin kullum sai na je asibiti na kaiwa Fa'iz abinci ya dame ni da waya, abun haushi shi ne ya kasa tsayawa turba ɗaya, Idan ya lallashe ni ya ga abun ya ƙi ci sai ya hau ni da sababi kamar wani uba na. Wannan sabon halin na Aliyu ya sanya na tsane shi, tsanar da ban taɓa yi wa wani ba. Haushin sa kawai nake ji, kaf ɗin rayuwa ta ban taɓa ganin mutum mai tsananin son kan shi ba irin Aliyu ba, watau in dai shi zai samu, kowa ma ya rasa shikenan.
A satin su Yaya Naziru suka ziyarce mu tare da Surayya, a ɗakina ta sauka. Shi Yaya Naziru a ganin shi kamata ya yi na mance da su duka, tunda alamu sun nuna Aliyu ba shi da niyyar barin mu, zai iya kasa tawakkali bayan aure na da Fa'iz. Don rannan ma da ya kira ni a waya cewa yayi "Ummu kina tunanin idan ban aure ki ba zan bar ku ku ci gaba da zama tare da Fa'izu? Ai sai dai kowa ya rasa, don ba zan iya barin shi ya samu abin da yake nawa ba ne, shawara ta rage gare ki."
Yaya Naziru yana ganin Aliyu zai iya kashe mun aure ko ya hana ni zaman lafiya, hakan kuma zai iya jawo nadamar auren a zo ana da na sani. Gara ma da komai ya nuna kan sa kafin a yi auren, don babu amfanin zuwa da dawowa gida a matsayin bazawara. Surayyan kam mamakin sabon halin Aliyu kawai take yi, don tace da a wani wajen da ta ji hakan a take za ta ƙarya ta
A ɓangaren Fa'iz ma Kawu (babansa) ya kira shi tare da rarrashin shi akan ya haƙura da aure na, in shaa Allah Allah zai ba shi mafiyi na amma Fa'iz ya dage kan cewar ba zai bar wa Aliyu ni ba, ko don yanda ya biyo ta hanyar Hajiya Ma'inna ma, so yake ya koya masa hankali ya koma ɗanɗana masa irin ɗacin da ya sa masa. Amma ya kwantar wa da Kawu rai kan cewar ya taya shi da addu'a kamar yanda shi ma ya dage da yi, in shaa Allah komai zai warware a kurkusa.
Aliyu kuma Baba ne ya zaunar da shi yayi masa faɗa sosai akan abin da ya ɓullo da shi da har aka samu rabuwar kai. Ita na gwaggo tayi masa na ta faɗan sannan suka umarce shi da ya janye komai ko kuma su ɓatar masa. Amma bawan Allahn nan yana tashi sai ya koma ɓangaren Hajiya Ma'inna ya faɗa mata ana takura mashi da maganar wai sai ya janye, a take kuwa ta hau bala'i da sabani sannan ta hau barazanar duk wanda ya sake masa maganar janyewa tsinuwa ce za ta raba su. Daga nan sai kowa ya sa masu ido. Ita taurin kai, haka ma jikokin nata guda biyu watau Aliyu da Fa'iz.
Addu'a kam ta sanya tsananin lamarin gare ni yayi sauƙi sosai, muna tare da Fa'iz duk da komai a tsakanin mu yayi sanyi ƙwarai. Kaf 'yan gidanmu shawarar rashin auren Fa'iz suke ba ni, ina ga abun ni ma ya shiga kaina don na fara jin fasawar kamar ita ce maslaha. Oh ni Ummu, da alama wannan karon ma shirin auren nawa ma ya lalace.
Tsakani na da Fa'iz mun yanke shawarar tunda rayuka sun ɓaci ta kowanne ɓangare, mu jingine maganar auren mu zuwa wani lokaci, ƙila zuwa lokacin rayuka da abubuwa sun ƙara sanyaya. Sannan ya sanya ni nayi masa alƙawarin ba zan taɓa ba wa Aliyu fuska ba, domin ɗan da ya hana uwarsa bacci to ko bai kamata ya runtsa ba shi ma. Na kuma yi masa alƙawarin hakan.
Wannan shi ne asalin taɓarɓarewar maganar aure na da masoyin ƙwarai Fa'iz. Allah Sarki Idris Elban Kano. Wannan ya sa ina dai fim da Idris Elba a ciki ba na kalla, haƙura nake yi domin fami yake mun a zuciya. Ɓangaren Aliyu kuma, shi ma ya ji jiki a matsalar da ya kunnu mana, domin har matarsa ce ke mun waya tana roƙo na da idan ba zan aure shi ba to na saurare shi (nayi blocking ɗin sa a ko'ina), amma ko ta kan su ban bi ba. Hakan ya yanke mana mu'amala da su, haka na haƙura da ƙaunar da nake yi wa su Amir.