Free chapter · Read without an account

32

by Fareeda Aliyu · KOWA DA ƘADDARARSA


    BAYAN SHEKARA ƊAYA


A shekarar nan ko ban faɗa ba kun san abubuwan da yawa sun kasance. Jarabawar Jamb ta fito har Zaria na je nayi post UTME kuma na samu abin da ake nema, amman da aka kafe list na admission babu sunana a ciki, nayi kuka nayi ƙunci sannan kuma na rarrashi kaina domin haka Allah ya so.

Sa'adatu Rimi kuma mun yi jarabawar zango na farko da na biyu kuma duka na wuce (na san ba sai na faɗa maku haka ba, tunda kun san yanayin ƙwaƙwalwar tawa).

Tsakani na da Fa'iz sai jefi-jefi muke waya, haɗuwar mu zuwa yanzu ma tayi wahala. Surayya ta haifar wa Yaya Naziru 'yan biyu, ko ban ce komai ba kun san dai zai yi rawar kai. Kano ta dawo sai da tayi wata biyu cur sannan ta koma, shi kuma kowanne ƙarshe sati yana tafe wurin ta da 'yan biyun shi kyawawa. Yaya Zainabu ma ta yi wa Najwa ƙanwa mai suna Noor.

*****************

Kasancewar ganin aiki na na makaranta ba wani yawa ne da shi ba, sai na fara fashi domin yanzu sai nayi sati Uku ban na taka ƙofar makarantar ba. Damu na da Mama ta fara yi dangane da fashin makaranta sai hakan ya sanya na fara tunanin wurin da zan dinga zuwa ina rage lokaci domin ba na ƙaunar abin da zai sa naje makarantar.

Rannan akan hanya ta ta dawowa daga makaranta zuwa gida akan Maiduguri Road na hangi wani babban wuri an sa EL-BASHIR TRAVEL AND TOURS. Ban san ya ake aiki a traveling agency ba, amma nasan ko ma mene ba zai gagare ni ba. Washegari na fito kamar makaranta zan je sai na wuce can kai tsaye wurin ƙarfe goma, na kuma buƙaci ganin manaja ɗin. Buƙatar neman aiki a wurin na je masa da shi.

"Ina ga ba mu da buƙatar ɗaukan sabbin ma'aikata." Ya faɗa mun.

Tunanin zaman da zan yi a gida ya sanya ni yi masa magiya, ni fa ba kuɗin ba ne damuwa ta so nake na zama engage. Har na ƙara da cewa "Yallaɓai a bani trial na wata ɗaya kawai, idan ban yi yanda ya kamata ba sai a sallame ni." Na yi masa kalar tausayi, ina ta addu'a a raina Allah ya sa ya yarda.

"Kawo takardun ki na gani."

Cikin hanzarin na miƙa masa nace "Za kaga transcripts ɗina na level 1 da 2, matsalar makaranta na samu ne amma na yi diploma da wasu specialities akan kwamfuta."

Bai yi magana ba, ci gaba da duba takardun yayi sannan yace na rubuta lambar waya ta a saman su, zai tuntuɓe ni daga baya idan ya bincika wurin na gaba da shi idan akwai yiyuwar ɗauka ta aikin.

Duka sati biyu tsakani na samu wayar shi akan na zo an bani aikin. Alhamdulillah! Maa shaa Allah! Na samu wurin fakewa.

Kullum sai na shirya na yi tafiya ta wurin aiki duk a zaton Mama makaranta nake zuwa. kasancewar akwai aikin safe da na rana a wurin, hakan ba ya takura ni wajen yi wa mutane girki. Kuɗin kawai zuba su nake a account har ma da salary ɗina tunda kullum sai Baba ya ba mu kuɗin makaranta ni da 'yan biyu.

Haka nan kaf wurin aikin mu ba wanda yasan ina zuwa makaranta. Idan ina da buƙatar zuwa makaranta idan lokacin bai yi mun daidai ba sai na roƙi wasu mu yi canjin lokutan aikin ma'ana idan ina aikin yamma sai mu canza da me aikin safe. Ba sa damuwa don haka ba ni da matsala. Haka manajan mutumin kirki ne, ba ya da takura matuƙar za ka yi aikin ka kuma akan lokaci.

******************

Haka rayuwa take ta tafiya amma abin mamaki shine Sa'adatu Rimin da na raina wa wayo tasa na samu carryover har guda biyar. Ni abin ma sai ya bani dariya, ban kuma damu ba saboda nasan rashin maida hankali na ne ya ja mun, kuma ba ni da niyyar canzawa don ba barin aiki na zan yi ba.

Duk lokaci nake aikin rana/yamma ina kai wa dare ai kuwa Mama ta sani a gaba da tuhuma, wannan ne kuma sanadin da aka san aiki nake zuwa. Yaya Naziru yayi faɗa har ya so a hana ni saboda a tunanin shi neman hanyar zamewa daga makaranta nake nema, amma sai Yaya Muntari ya shiga maganar, ya ce a barni ai yasan ba zan ba shi kunya ba, a haka ya ɗaure ni dole na na dinga maida hankali akan makarantar.

Manajan mu ya kasance ya ɗauke mu kamar 'ya'ya ko kuma ƙanne, ya kan yawaita yin raha da mu idan ya iso wurin aiki ko kuma idan zai fita ma'ana idan ya shigo wurin da muke, nan ne kuma farfajiyar ofishin kafin a ƙarasa na shi.

Kasancewar ƙawaye na sun yi aure sai zumunci tsakanin mu ya ragu sosai kamar yadda hakan take kasancewa ga kowacce mace saboda canji ra'ayi. Matar aure abinda yake gaban ta dabam ne da na 'yan mata, kowa matsalar sa dabam ce. Abokan aiki na sune ƙawaye na a halin yanzu domin da su muke kusan yini ko da yaushe.

Ranar Laraba kasancewar aikin yamma zan je ranar, sai na yanke shawarar na dafa abinci na tafi da shi domin nasan kafin mu taso sai yunwa ta sa mun fara kame-kame. Rahina da Habiba ne kaɗai mata muke tare da su a aikin yamma na yau kuma mun fi kusa kasancewar mu kusan kai ɗaya (a shekaru) sannan dukkan mu ba mu da aure, ragowan kuma maza ne. Adaidaita sahu na samu ya ɗauko ni tun daga ƙofar gida saboda warmers kala-kala na ɗauko yau.

Akwai wani ƙaramin ofis ko in ce ɗaki da mu mata ke amfani da shi domin sallah, zallar kafet ne aka malala a wurin da wata sallayar mu da ke ninke an ajiye ta can gefe guda, anan cikin wurin muka ajiye warmers ɗin maimakon wurin da muke yin ayyukan namu.

Abdul'aziz ne ya shigo ofishin mu ya ɗan yi jim sannan yace "Gaskiya ofis ɗin nan yana ba da wani ƙamshi me daɗi, ƙamshin kuma na abinci ne don ni har ya fara sa ni jin yunwa." Yana shafa cikin sa tare da yin hamma.

Rahina ce ta fara dariya kafin kuma tayi magana Mansur ya amshe da cewa "Bari kawai Abdul'aziz, tun ɗazu nake ji amma shiru kawai nayi, ni ma cikina juyawa yake yi wallahi."

Rahina da yanzu ta samu sararin amsawa tace "Kar ku damu, Ummu ce tayi mana gata yau da abinci."

Mansur yace "Ina abincin yake? Gaskiya a bani nawa yanzu kun sa sai hamma muke ta zaɓawa "

Habiba tace "Kusan dai yallaɓai yana ciki kuma magana zai yi mana tunda ba lokacin break ba ne, ku bari idan mun tashi sallar la'asar sai a ci kawai."

Rahina ta amshe da cewa "Ni ma tun ɗazu nake mita, ni su bar ni na buɗe ko ɗanɗano nayi sam Habiba ta hana. Wannan ƙamshi don Allah ki ba ki sirrin mana" ina dariya nace NAJNINO SPICES Hajiya, sannan na hau warware bayani game da spices ɗin.

Kasancewar Habiba na hutun sallah, kafin mu yi mu idar har ta gama fitar wa kowa nashi, abincin kala uku ne kuma duk da haka akwai ragowa. Ita ta kai wa yallaɓai na shi can ofishin sa sannan ragowan mazan bayan dawowar su daga wurin da suke sallah (ƙasan benen ofishin mu) sai suka shigo ƙaramin ofis ɗin. Sanin ku ne ni gwanar girki ce don haka an sha santi ba laifi.

Muna hayaniyar cin abinci manaja ya leƙo yana neman Habiba, nan ya iske mu gabaɗayanmu duk da lokacin da ya kamata mu ƙare break ɗin mu ya wuce.

Yace "No wonder na ji ofishin ku tsit, ashe kowa yana nan. Na fito a faɗa mun wurin da aka samo abincin nan, Oga ne ya iso yanzun nan, amma shinkafar yake so da kayan ganyen kaɗai."

Rahina bakinta na sauri tace ai nice ma nayi girkin, a take kuma a ɗibarwa Oga watau Yaya Bash, sune masu ainihin traveling agency ɗin, in da shi kuma manajan ya kasance me kula da wajen.

Wuraren ƙarfe biyar Yaya Bash (dukkanin matan wurin haka muke kiran shi, mazan kuma suna kiran shi kamar yanda manaja ke kiransa watau Oga) ya fito domin tafiya, sai a lokacin muka haɗu. Ni ban taɓa ji da ganin mai kuɗi me masifar sauƙin kan Yaya Bashir ba, idan ka zo ka iske shi yana raha da ma'aikatan wurin sai ka ɗauka abokin mu ne. Ba ya nuna alamar suna da kuɗi bare yayi wulaƙanci, kana ganin kuɗin shi daga yanayin tufafin da yake sanyawa, manyan agogon Rolex da yake yawaita amfani da su sannan uwa uba motocin da yake amfani da su. Ba'a Kano yake da zama ba, yana zagayowa dukkanin lokacin da ya samu sarari ko idan wani abun ya taso tsakanin shi da Manajan mu.

Bayan gaishe-gaishe yace da ni "Ummu wai ke ce kika yi abincin nan?" Ina murmushi na gyaɗa masa kai. Ya cigaba "Ashe muna da great cook. Na rasa dalilin da yasa idan na zo garin nan bana jin daɗin abincin gidajen abincin garin nan, shi yasa nake barin gari da wuri. Kyan ki ki buɗe gidan abinci ai."

"Ai ina da personal kitchen ɗina da nake yi wa mutane abinci, irin kamar masu buki ko wani abun, restaurant sai na gaba idan zan iya." Na amsa. Sai a wannan lokacin abokan aiki na suka san ina yin girke-girke.

Tun daga ranar kuma muddin Yaya Bashir ya zo Kano ni ce ke yi masa girki. Kuɗi a dunƙule yake ba ni sannan ya faɗa mun iya kwanakin da yake gari. Duk da baya wuce kwana biyar.

Bana yi masa abincin safe, na rana ne kawai amma ban taɓa yin ƙasa da kala huɗu ba, hakan yasa babu buƙatar ayi abincin dare. Direban shi ne yake zuwa gidanmu koyaushe ya ɗaukar masa. Kuɗaɗen da yake bani sun fi ƙarfin abubuwan da nake shirya masa na abincin haɗi da ladan aikin nawa, kuma ba ya karɓar canji duk naci na. Ni yake bar wa zaɓin abinci sai dai idan yana son na sake masa wani daga cikin irin waɗanda na taɓa yi masa ya faɗa ko kuma idan yana marmarin wani kalar abincin.

Yanzu ina shekara ta biyu kenan a makaranta zango na ƙarshe, ga shi muna gama jarabawa za mu tafi gwajin koyarwa (teaching practice), matsalata yanzu shine ban san yaya zan yi da aiki na ba. Idan nayi tunanin karɓar hutun wata uku sai na tuna su ba na gwamnati ba ne don haka sai na yanke shawarar roƙon Manaja ya taimaka mun a bar ni aikin yamma gabaɗaya na wata ukun, yarda idan na je makarantar da zan koyar da safe sai na wuce wurin aikinsu, ko a iya haka na tsaya nasan zan wahala ba ƙarya.

'yan biyun Mama suna shekarar su ta ƙarshe su ma, kaf gidanmu nice kaɗai nake yin NCE, kautar da abun kawai nake yi daga zuciya ta amma ba daɗi yake mun ba.

**********************

Ranar Litinin ta kama ina aikin safe, wuraren ƙarfe sha ɗaya Alhaji Hamisu ya iso ofishin mu. Yana ɗaya daga cikin manyan kwastoman mu da Agency ke ji da su, ofishin Manaja ya wuce kai tsaye sai kuma aka aiko na je. Manaja yayi mun bayanin dukkan abin da Alhaji Hamisu yake buƙata, tafiya ce tare da iyalansa zuwa Dubai, ya kuma umarce ni da nayi sauri na yi abinda ya kamata (bai cika zuwa ofishin mu ba sai idan hanya ta biyo da shi kaman yanzu, yawanci kawai waya yake yi a yi masa dukkan abin da yake buƙata).

Cikin hanzari na kammala abinda ya rage nayi ɗin, abin da ya ɓata mun lokacin ma favorite hotel ɗin sa da yafi son sauka a ciki ne aka kasa samun ɗakin da ya dace da su sai da kyar na samo masu wani makamancin waccan, sannan na koma na shaida masu duka arrangements ɗin na kammala. Cike da jin daɗi Alhaji Hamisu ya karkace tare da zura hannu a aljihu ya zaro kuɗaɗen da ko ƙirgawa bai yi ba, ya miƙo mun. Idona na zazzaro tare da ƙin karɓar kuɗin ina faɗin "A'a Nagode Alhaji, aiki na nayi ba sai na amshi komai ba."

Manaja ne yayi magana "Ummu zo ki karɓa, Alhaji baya son yayi kyauta a ƙi karɓa." Cike da tsananin jin nauyi na karɓa tare da godiya, na koma ofishin mu.

Rahina na ganin kuɗi a hannuna ta zaro ido "Ina muka samu bugun Abuja Hajiya?"

"Alhaji Hamisu ne fa, ni da na ƙi karɓa shine Manaja ya matsa na amsa." Na faɗa tare da miƙa mata kuɗin ganin ta miƙo mun hannu.

"Dubu sha takwas cas!" Ta faɗa bayan ta gama ƙirgawa ta kuma maido mun kuɗin.

Dubu ukun sama na miƙa mata nace ta sa kati, ga zato na za ta raina amma sai ta bani mamaki da ta nuna jin daɗinta tare da godiya. Shi yasa nake ƙara son Rahina.

Ba ni da wata matsala a wurin aiki na in banda abu guda ɗaya. Abinda ya faru kuwa watarana ne muna ofis, an ci sa'a shift ɗin duka mata ne a ranar watau ni, Rahina, Habiba da Anty Samira, aikin safe ne ma. Wurin goman safiya Yaya Bashir ya iso, ni ya fara amsawa gaisuwar da muke masa kafin su sannan ya tsokane ni da cewa "Inye ka ga su Ummu gaban kwanfuta kamar an ga oven."

Su Anty Samira suka fara yi mun dariya, ni kuma a shagwaɓe nace "Kai kai kai don Allah Yaya Bashir." Shi ma murmushin yayi ya wuce ofishin Manaja. Haka ma da ya kammala abin da ya kawo shi, bayan sun fito tare da Manaja yace "Ummu zo mana" sannan yayi sallama da ragowan ma'aikatan.

Bayan mun fito nan corridor ɗin ofishin kafin a sauka ƙasa daga bene yace "Ummu ga wannan" ya miƙo mun kuɗi sannan ya cigaba "ba zama zan yi ba wannan karon, ina ga ma gobe zan juya. Dankalin nan da kika yi mun waccan zuwan nawa nake so sai farfesun kifi. Sa'adu (direbansa) zai zo ya karɓa wurin magriba, ina jin zuwa wannan lokacin kin gama ko?"

"Eh, in shaa Allah. Idan kuma su kaɗai zan yi kuɗin ya yi yawa Yaya Bashir, don Allah ka rage."

A take ya ɓata fuska "Ummu kullum sai mun yi ta yin magana ɗaya? Zuwa yanzu ya kamata a ce kin gama gane ni, kar ki sake mu ƙarayin maganar nan, kin ji? Kin cancanci fin haka ma, don ba ki san nawa nake kashewa ba ne akan abinci idan nazo. Je ki kawai." Duk zancen nan da ake yi Manaja na gefe bai sa mana baki ba, sai dai murmushi kawai da yake yi.

Ko da na koma ciki sai da na tsargu da irin kallon da su duka suke yi mun, don haka ban ce komai ba na zauna a teburina tare da zubar da kuɗin a saman tebur ɗin.

Anty Samira ce tayi magana kasancewar ita ba ta cika yin shiru akan abin da idon ta ya gane mata ba tace "Ummu iyayen farin jinin kuɗi, miƙo mun rabo na nan." Maganar da tayi ya sanya dukkan mu muka dara saboda kowa ya san wasa take. 

Na amsa "Kuɗin abincin Yaya Bash ne, idan kuma kin ce mu kashe sai mu kashe ɗin mu bar Ogan Manaja da yunwa."

Rahina na gefe a hanzarce ta tsoma baki "Au! Ashe cook ɗinsa kika zama."

"Kai Rahina, ke sai yanzu kika sani? Abinda an daɗe ana yi?"

"Mu nan ba wanda ya sani sai...." Shigowar Manaja ya katse maganar har sai da ya wuce tukunna Anty Samira tace "Bature dai yace 'a way to a man's heart is through his stomach', kar ki yi wa matarsa ko budurwar shi fashinsa dai."

Habiba cikin hanzarin kamar dama abin da take jira ta ji kenan tace "Hmm! Bari kawai Anty Samira, ƙila ma sun daɗe da jonewa. Ba mamaki mu kaɗai ne ba mu sani ba kamar dai zancen abinci."

Har wannan lokacin dariyar zancen Anty Samira nake yi sannan na amsawa Habiba "Ba wani abu da ya wuce zancen abinci tsakanin mu. A matsayin Yaya yake gare ni kuma hakan ba canzawa za tayi ba." Da haka aka rufe zancen.

Ƙarfe biyu mun fara shirin kammala shift ɗin mu domin tafiya da bawa masu aikin yamma fili, ina ɗan ƙaramin ofis ɗin mu da muke sallah, fuskanta nake gogewa saboda kasuwa zan je siyo kayayyakin girki, waya ta na baro ta kan teburina. Habiba ce ta miƙo mun saboda kira na da aka yi sannan ta zuba mun ido alamar tuhuma, ban lura da irin kallon da take mun ba na amsa wayar.

"Assalamu alaikum Yaya Bashir?" Sannan na kasa kunne alamun sauraro.

Ya amsa "Ummu sorry don Allah, zama na a Kano ba zai yiyu ba yau, impromptu abu ne ya taso mun, don nan da minti talatin zan wuce, so ba sai kin dafa komai ba."

"Toh, ba damuwa. Allah ya kiyaye hanya, Allah kuma ya tsare." Na kashe wayar

Kashe wayar da nayi ne ya sanya na lura da irin kallon da take mun. Sai kawai na tsargu a take zuciya ta ta raya mun son Yaya Bash Habiba take yi, shi yasa ta damu da ta san abinda yake faruwa tsakani na da shi.

Ƙarfe uku daidai muka fito domin tafiya, Rahina za ta je sabon gari sai muka yi sallama da su Anty Samira. Mun rabu ana raha, tana cewa mu koma ce mata Ummu Aminatu ni kuma ina cewa Aminatun ta ta ma me goshi haka dai har muka tafi.

Habiba kuma sama-sama ta amsa mu kamar wadda aka yi wa laifi, ni da Rahina kam muka share kamar ba mu ga abin da tayi ba. Tun daga ranar sai na kasance ina baya-baya da ita ganin ba ta son yin hulɗa da ni sosai. Rahina ta sha tambaya ta abin da ke faruwa tsakani na da Habiba, na kuma shaida mata ni ba ni da masaniyar alaƙarmu da Habiba tayi baya.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.