Free chapter · Read without an account
Episode 1-2
*INA DA DALILI...!*
_✍🏾Naanah M Sha'abarn_
*_(Dijarty❤️)_*
*Wattpad account*
Naanah2021
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
***
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
🔗 _*بسم الله الرحمن الرحيم*_🔗
_Posting day & Posting time_
_2-1-2024🤞🏾1:25pm_
*Free page*
*1_2*
#Shield🥹
Babu abin da ka ke ji yana tashi a dokar dajin sai ƙarar harbin bindiga, wani kyakkyawan saurayi ne zaune a kan wata kujerar ƙarfe yana girgiza ƙafa ɗaya kan ɗaya, kallon gawar mutum da ya harbe ya yi babu alamar da na sanin abin da ya yi domin zuciyarsa a ƙeƙeshe take, babu imani ko tausayi a tare da shi, "Dogo".Ya kira sunan wani yaronsa cikin kakkausar murya, wani ƙaton mutumi ne ya je kusa da shi tare da tsugunnawa a kusa da shi, yana cewa "gani Boss".Gold ya miƙe tsaye tare da cewa "ka je ka fito min da duk wanda muka yi da 'yan'uwansu yau za'a turo da kuɗin fansarsu, dan idan lokacin da na gindaya musu ya yi ba su turo ba, tabbas zan kirasu domin su ji yadda zan tarwatsa kawunansu kowanne daga cikinsu".Dogo cikin ladabi ya miƙe ya nufi gurin da suke saka mutane idan sun yi kidnapping ɗinsu, Dogo ya ɗauki kusan mintina biyar a cikin wannan akurkin gurin, ba tare da ya fito ba, sai chan ga shi ya fito hannunsa riƙe da wata murtukekiyar igiya yana janta, mutane ne suka fara fitowa mata da maza kowannansu hannayensu a ɗaure yake, gabaɗaya a galabaice suke, saboda irin wahalar da suke sha a hannunsu Gold, kullum cikin dukansu suke, kuma kullum sai sun bi su ɗaya bayan ɗaya suna saita musu bindiga a tsakiyar goshinsu, ba sa ba su abinci sai dai su ba su ganyen bishiya su ci, wani lokacin ma ganyen bishiyar ba sa ba su, ruwa kuwa rabin wani ƙaramin kofi suke ba su kullum sau ɗaya, ba za su ƙara ba su ba sai washegari a irin lokacin da suka ba su sannan za su ƙara shan ruwa, Allah sarki! wasu daga cikinsu suna tafiya suna faɗuwa, jikinsu gaba ɗaya babu kuzari, motsi ma ba sa iya yi sosai, a haka suka ƙarasa gurin Gold suka jeru a gabansa, su ashirin ne, har da tsofaffi da ƙananan yara wanda ba su huce shekaru tara zuwa bakwai ba, ga 'yanmata da samari, gaba ɗayansu sun gama karaya kuma sun riga da sun saka a ransu yau kam mutuwa za su yi idan har ba'a biya kuɗin fansansu ba, dan kuwa Gold bashi da imani ko kuma tausayi bai ɗauki kisan kai a matsayi babban abu ba, idan har ya gindaya lokacin da yake son a ba shi kuɗi ba'a ba shi ba, kashe mutum yake yi ko kuma ya kira 'yan mafiya ya siyar musu da mutane.
Mikewa ya yi tsaye tare da ɗaukar glass ɗinsa a kan hannun kujerar ya saka, ya riƙe bindiga da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuwa wayarsa yake kallon dan baya son ya ɗaga musu ƙafa dai-dai da dakika ɗaya ace sun cigaba da shaƙar iskar duniya ba tare da ya gama da su ba "ku yi addu'a 'yan uwanku ko da sata ne su yi su kawo min kuɗin fansanku nan da awa ɗaya, domin kuwa idan ba su kawo min kuɗin nan ba, ko minti ɗaya ba za ku ƙara a duniyar nan ba, zan aika ku garin da ba'a dawowa, ina matuƙar girmama lokaci kuma ina bashi dukkanin haƙƙinsa". Yana gama fadar haka ya kowa ya zauna ya na bin su da kallo, fuskarsa a ɗaure tam. Cikin ikon Allah kafin lokacin ya cika 'yan'uwan mutanan nan suka dinga zuwa kawo kuɗin fansa, Gold ya yi musu kwatancen inda zasu a jiye kuɗin, ya tura ɗaya daga cikin yaransa ya tsaya a wajen yana karɓar kuɗin, gaba ɗaya an biya kuɗin fansarsu kuma ya sakesu, ya rage sai wasu ƙananun yara su biyu da ba su fi shekara bakwai ba da alama 'yan biyu ne, Gold ya saita bindigarsa akan ɗaya cikin ɓacin rai ya fara magana 'yanuwanku ba su da cika alƙawari, kuma ba sa girmama alƙawari, sun ɓata min lokacina a banza, kuma wannan ya nuna min alamar cewar ba sa buƙatarku, dan haka yanzun nan zan gama da ku gaba ɗayanku" Ɗago kai ɗayar ta yi hawaye na zuba daga idanuwanta tace "ka yi haƙuri, idan kana ƙaunar mamanka da Babanka karka kashemu, ba mu da kowa a duniyar nan".
Gold ya kalleta yana murmushin mugunta yace "ya sunanki yarinya?".
"Hassana!". Ta faɗa a hankali.
"Hassana! wato idan ina ƙaunar Mamana da Babana kar na kasheku! to ai baki sani ba, wannan furucin da kika yi ne zai sa na kasheku ko da kuma ban yi niyyar kasheku ba! domin kuwa ba na ƙaunar iyayena na tsanesu fiye da tunanin mai tunani! A yanzu ban da wani masoyi sai Papi a duniyar nan". Ya ƙarasa maganar cikin zafin rai, Usaina ta ce "ka yi haƙuri dan Allah, ba haka take so ta ce ba, ka yi haƙuri ba mu da kowa, ba mu da waɗanda zasu biya kuɗin fansarmu, Inna da Baffanmu sun mutu, Kawu Tasi'u kuma yana da kuɗi amman ba zai taɓa biyanka ba, saboda ba ya sonmu"
Gold ya miƙe tsaye tare da cewa "ba wai bayani nace kuyi min ba, ku zaɓa a cikinku wa zan fara kashewa, idan kuma ku ka ɓata min lokaci yanzun nan zan azabtar da ku sannan kuma nayi muku kisa mafi muni wanda ban taɓa yi wa wani ɗan adam ba!"
Hassana ta miƙe tsaya cikin ƙarfin zuciya ta ƙarasa gabansa tare da cewa "ina so na nemi alfarma a gurinka"
Gold yace "da alama dai Hassana kin mai da ni abokin wasanki, ki kalleni da kyau kin ga alamar ni za'a nemi alfarma a wajena na yi wa mutum? Ai alfarma ɗaya zan muku na sadaku da mutuwarku"
Hassana jikinta na rawa ta kama hannunsa tace "na san baka taɓa yi wa wani alfarma ba, amman dan Allah ina so mu kayi mana!"
Gold bai tsaya yin wani tunani ba yasa bindiga ya harbi Hassana a goshi, ta faɗi ƙasa Usaina ma harbinta yayi a goshin, Gold cikin ɓacin rai ya ce "ni ba'a neman alfarma a wajena domin kuwa ko mutum ya nema ba zai taɓa samu ba, duk abubuwan da na ke yi *INA DA DALILI!"*
Sauran yaran Gold ɗin suka saka dariya tare da cewa "Wannan haka yake Oga, babu wata alfarma anan wajen, domin bamu santa ba sam"
Gold ya ce "ku shirya za mu je farauta, sannan kuma kamar yadda muka saba, zamu chanza guri zamu tattara kayanmu zamu koma dajin Sama!"
Dukkansu suka amsa da cewa "An gama oga!"
Gold ya ce "Yanzu akwai sauran mutane?"
Dogo ya ce "A'a! babu, daman su kaɗai ne suka rage mana!"
Gold ya ce "ku je ku shirya za mu je farauta yanzun nan!"
"To Oga Gold!"
*** *** ***
Bindigoginsu suka ɗauko a cikin 'yar bukka da duk wasu abunda su ka zo da shi dajin sannan suka fito kowannansu ya rataya bindigarsa a kafaɗarsa, Gold yana ganin sun fito ya fara tafiya cikin nutsuwa da isa, sun yi nisa sosai dan sun kusan fita daga dajin, Gold ya juyo ya kalli yaransa, su goma ne har shi sha ɗaya yace "Tsagiri, Faro, Tsigi ku ƙarasa bakin titi ku hango mana idan motoci sun fara hucewa sai ku zo ku faɗa mana, amman kada ku tafi da wannan bindigunnaku"
Suka amsa da "To Ogo", Dukansu suka saka bindigunsu a wani buhu suka ba wa Dogo, Sannan suka nufi bakin titi, su kuma suka ƙarasa gurin wata bishiya, suka zazzauna a gindin bishiyar.
Tsigi sun kai kusan awa ɗaya ba su dawo ba, suna bakin titi, har su Gold suka fara gajiya da zama, sai chan ga su sun dawo a kan wani tsohon mashin, Gold yana ganinsu ya miƙe su ma sauran suka miƙe, tun kafin su ƙaraso kusa da su Gold Tsigi yayi musu alamar motoci sun fara hucewa.
Murmushin jin daɗi Gold yayi yace "Yes! Dogo ka kira Papi ka ce ya turo mana mutane za mu yi farauta, mu haɗu da su a bakin titi".
Dogo ya ce "Oga ai na kira shi, tun muna cikin tafiya".
Gold ya ce "Yauwa Dogo".
Gaba ɗayansu suka hau kan mashin ɗinsu da yake mashin ɗin guda uku ne, kowannansu hsnnunsa riƙe da bindiga suka nufi bakin titi domin tare hanya, suna isa bakin titi su ka yi sa'a da motoci sosai, dukkansu suka sauka daga kan mashin ɗinsu.
A tsakiyar titin suka jeru kowannansu ya saita bindigarsa, Mutanan da Papi ya turo su ma, suka fito daga in da suka 'buya, kowa da bindigarsa, Gold ya ɗaga bindigarsa sama ya yi wani irin harbi mai razanarwa, sannan cikin kakkausar murya yace "dukkaninku ku fito daga cikin motocinku, kafin na zo na fito da ku da kai na, na san kun san labarina a gidan radio da na jarida ni Gold ba ni da imani ko kaɗan, idan ɗaya daga cikinku yayi gardama bai fito ba har na ƙaraso, na duba na ganshi to wallahi ko second ɗaya ba zai ƙarayi a duniya ba zan kasheshi"
Jin furucin da Gold yayi yasa kowa ya shiga fitowa daga cikin motarsa, sai da kowa ya fito Gold yasa yaransa su duba duka motocin su ga ko akwai wani wanda yayi taurin kai bai fito ba, motoci kusan hamsin ne a gurin, sun gama dubawa gabaɗaya ba su ga kowa ba, suka dawo suka faɗawa Gold cewar kowa ya fito babu kowa a cikin motocin, haka Gold da yaransa suka tisa waɗannan mutanan da suka fi ɗari da hamsin da bindigogi, suka shiga cikin daji, sun yi tafiya ta kusan awa ɗaya, kafin su isa dajin sama, dan haka sukeyi idan sun yi kidnapping ɗin mutane suka gama cinikinsu suka kashe na kashewa, idan sun ƙara samo wasu sai su chanza daji, domin suna tsoron ka da sojoji su kawo musu hari.
Suna isa sukasa su suka jeru, sannan Dogo ya bi su ɗaya bayan ɗaya yana ɗauresu da igiya, duk wanda ka kalla a cikin mutanan zaka gansu duk a tsorace suke, hankalinsu a tashe yake, zuciyarsu jinta suke kamar zata tarwatse sbd firgici.
Gold wanda yake zaune a ƙarƙashin wata bishiya da take nesa dasu kaɗan yana binsu da kallo yana sakin wani irin lallausan murmushi "tabbas a cikin satin nan zan tara makudan kudade".
Dogo ne ya ƙaraso gurin da yake yana cewa "Oga! ya kamata mu sakasu su bamu number 'yan'uwansu domin mu yanka musu adadin kuɗin da za su bada na fansarsu"
Gold ya ce "ku je ku karɓi number, sannan ku kirasu ku faɗa musu kuɗin fansan kowanne daga cikinsu milliyan ashirin da biyar, sannan kuma su turo mana dubu ashirin kuɗin da zamu dinga kiransu!".
Dogo ya ce "Angama Oga!"
Yana gama faɗan haka ya kowa wajen mutanan nan ya bi su ɗaya bayan ɗaya yana karɓar number 'yan'uwansu, yana kiransu yana faɗa musu kuɗin fansar da kuma kuɗin da zasu turo musu na kiran waya.
**** **** ****
Kallo ɗaya za ka yi musu ka tabbatar da cewar yana cikin matsanancin tashin hankali mara misaltuwa.
"Aliyu! Aliyu!! Aliyu!!!"
Wani matashin sarauyi wanda ba zai huce sa'arsa ba ya shiga kiransa saboda ganin irin yanayin yadda yake tafiya kamar baya cikin hayyacinsa.
Abin ya matuƙar ɗaure masa kai da mamaki ganin duk kiran da yake yi masa bai juyo ba, yana ƙarasa ya sha gabansa tare da dafasa kafaɗarsa yace "Aliyu lafiyarka kuwa?"
Cikin rawar murya hawaye na zuba daga idanuwansa yace "Mahmud 'yan kidnapping sun tare su Naanarh Khadija a hanyarsu ta dawowa gida, sun ce kuɗin fansarta milliyan ashiri da biyar ne, kuma kafin nan sai an fara tura musu kuɗin katin da za su dinga kira na dubu ashirin, nan da kwana sati biyu suke son a tura musu kuɗin fansar Mahmud ya zan yi, ya zanyi na haɗa kuɗin da zan ba da na karɓo Naanarh Khadija, kana gani fa, abincin da zamu ci ma kullum fama muke wajen ganin mun ci ko da garin kwaki ne".
Mahmud ya yi matuƙar firgita jin abinda Aliyu ya faɗa masa, ba abinda yake furtawa sai "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un!". yake ta faman maimaitawa, cikin muryar rarrashi Mahmad ya ce "Aliyu ka ɗaure kayi haƙuri ka ji abokina, in sha Allahu Naanarh Khadija zata kuɓuta daga hannun wanchan azzalumi"
"Ni tashin hankalina ɗaya Mahmud kuɗin da zan tura musu na katin sun ce zuwa gobe idan ban turo ba, za su yi mata azaba mai tsanani kuma za su rabata da budurcinta ya zanyi, ina zanje na samo wannan maƙudan kuɗaɗan da sukace na kati, har dubu ashirin, wallahi Mahmud ko naira biyar ban da ita, nayi kusan kwana biyar ban riƙe ko da dubu ɗaya tawa ba, Naanarh Khadija ita kaɗai ce ta rage min, 'yan uwan mahaifinmu da na mahaifiyarmu duk sun gujemu, ni kuma ba wani aikin yi ne da ni ba, dako ne nake zuwa, kuma wani lokacin haka zan wuni ban samu kayan da zan ɗauka ba, haka zan dawo gida ba tare da ko sisi ba!"
Mahmud ya ce "Abokina karka damu, ni zan ba ka dubu ashirin ɗin kyauta gobe idan sun kira sai su faɗi yadda za'a tura musu kuɗin, kuma zan je a tura musu kuɗin fansa bai ta so ba, yayana soja ne, zanje har gidansa na faɗa masa duk abubuwan da ka faɗa min, zasu shiga bincike har sai sun gano inda suke!".
"Amman kana ganin idan an faɗa masa ba damuwa, kar su je su kasheta fa, idan sun gano an faɗawa sojoji halin da ake ciki".
"Haba abokina ba za su taɓa ganowa ba, duk sanda ku ka yi waya kada ka sake ka nuna musu ka faɗawa wani ma!"
"Hauka nake! ai ba zan taɓa faɗa musu ba!" Aliyu ya faɗa cikin rawar murya.
Haka suka rabu da Mahmud zuciyarsa cike da tausayin Aliyu da kuma Naanarh Khadija.
Shi kuwa Aliyu gida ya nufa yana tafiya yana haɗa hanya, wani irin jiri yake ji yana koƙarin faɗar da shi.
••••• ••••• •••••
A ɓangaren Gold kuwa......
Zaune yake yana busa sigari, idanuwansa a cikin wani baƙin glass, kallonsa ya kai gurin Kyakkyawar yarinyar da ta sunkuyar da kanta tana zubar da hawaye ya yi, glass ɗin fuskarsa ya cire, tare da ƙura mata ido, duk da ta sunkuyar da idonta, amman hakan bai sa kyawunta ya ɓuya ba.
"Wow so beautiful, wannan kyakkyawar yarinyar ai duniyar nan ba za'a taɓa samunta mai kyawunta ba, ina ganin kyawawan mata da suka amsa sunansu na masu kyau, amman yau idanuwana sun nuna min wacce ta fi su kyau, sarauniya ce a cikin kyawawa!" Magana yake a fili, zuciyarsa na bugawa da sauri da saura, ya kasa ɗauke idonsa daga kallonta, ko kifta ido baya so yayi.
"Dogo!"
Dogo da yake bayansa ya amsa da "Naam Oga"
Gold ya ce "ka je ka taho min da wacce kyakkyawar yanzun nan, ba na so second goma tayi ba tare da na ganta a gabana ba!"
Dogo ya gane wacce yake nufi, domin kuwa shima ita yake kallo tun ɗazu, yana jin da ace zai samu dama yau sai ta jiyar dashi daɗin zumarta, amman yasan Gold ba zai taɓa bari hakan ta faru ba, nufar gurin da take yayi, ya kunce mata hannu da ƙafarta da ya ɗaure da igiya, ya tisa ta a gaba suka nufi gurin Gold suna zuwa Dogo ya daka mata tsawa tare da cewa "tsugunna anan!"
Gold ya kalli Dogo tare da cewa "ya da haka? kyawawan mata ba'a musu tsawa, ai sai ka razana min ita! karka ƙara ka ji na faɗa maka!"
Dogo yace "To oga!"
Gold ya kalli yarinyar tare da sakin murmushi cikin daddaɗar muryarsa yace "Allah sarki! kukan ma da takeyi ƙara mata kyau yake, ka ga sarauniyar mata komai na ki yana da kyau, shiyasa nake da tabbacin cikinki ma haka yake da kyau da kuma daɗi!"
Miƙewa tayi tsaye jin abinda Gold yake faɗa tace "Dan Allah kuyi haƙuri, karku lalata min rayuwata"
Gold cikin fushi yace "ce miki akayi rayuwarki zamu lalata, koma ki tsugunna idan ba haka ba, yanxun nan ranki yayi mummunar ɓaci"
Jikinta na rawa ta koma ta tsugunna, ƙafafuwanta gaba ɗaya kasa ɗaukarta sukayi dan haka tayi zaman dirshan a ƙasa jikinta sai ɓari yake.
"Kyakkyawa! a gaskiya kina da matuƙar kyau sosai"
Gold yayi maganar yana ƙoƙarin dafa yarinyar, da sauri ta kauce tare da cewa
"Dan Allah karka taɓani, na shiga uku, Allah ka ɗauki raina, ya Allah na roƙeka ka kasheni na huta!"
Wata irin tsawa Gold ya daka mata, haka ta ɗankule guri ɗaya tare da kifa kanta akan gwiyoyinta jikinta sai ɓari yake kamar mazari.
"Har kin isa, wacece ke da za ki zo gabana kina yi min addu'o'in banza da wofi, to yanzu kafin Allah ya ɗauki rannaki zan keta miki rigar mutuncinki, idan yaso sai ki ji daɗin yi addu'ar banza 'yar talakawa! tashi muje ko yanzun nan na fasa miki kai"
Wani irin kuka ta fashe dashi ta shiga roƙonsa da Allah da Annabi, akan kada ya keta mata rigar mutunci, "Ka sani fa, ka na da ƙanwa idan ba ka da ita, za ka yi aure ka haihu, zai iya zamana idan matarka ta haihu ta haifar maka mace, duk abin da ka yi wa 'yar wani za'a yi wa ta ka, ka tausaya min dan dajarar annabi karka ɓata min rayuwata, da ka yi min fyaɗe gwanda ka kasheni sai ya fi min kwanciyar hankali"
Gold yace "Wato ke uwar masu baki ko? kin zo kina wani kukan munafurci, kina faɗa min maganar banza, bari ki ji in faɗa miki, wallahi ko da mutuwa ki ka yi yanzu, sai na sha zumarki na ji yadda kike da daɗi, zaki tashi mu shiga buƙƙar chan ko sai na fasa miki kai!"
"Wallahi sai dai ka kasheni, amman ba zan je ko ina ba, ba zan taɓa yarda ka lalata min rayuwata ba"
Gold ya yi murmushi tare da ɗauko bindigarsa, ya dora mata akan goshinta yace "zaki tashi ne, ko yanzun nan ki ga aiki da cikawa!"
"ba zan tashi ba, sai dai ka kasheni wallahi, ni ba na tsoron mutuwa in dai zan mutu tare da budurcina ba zan taɓa damuwa ba!"
Wani irin harbi yayi ransa a ɓace, dukkaninsu ƴan gurin sun yi tunanin wannan yarinyar ya harbe, saboda jin ihunta da su ka ji, sai daga baya sannan suka fahimci sama yayi harbi, ba ita ya kashe ba.
Gold cikin zafin nama, ya saka hannunsa ya ɗagata ta miƙe "kin yi tunanin zan kasheki ne, ba tare da na cika burina akanki ba, yau za ki gane cewar ni Gold ni kika ɓatawa rai, ni kika ɓatawa lokaci!" Haka ya dinga janta ta ƙarfin tsiya, tana kuka muryarta gaba ɗaya ta dashe saboda kukan da ta sha.
Suna shiga bukkar yayi wurgi da ita a ƙasa, bai tsaya wani jinkiri ba, ya cire dukkanin kayan jikinsa, ya faɗa kanta domin aiwatar da ƙudurinsa.
*Littafin kuɗi ne.*
5451173955
Khadija Muhammad
Moniepoint MFB
₦500 kacal
*NAANARH M SHA'ABAN.*
_*** Whatsapp only dan Allah banda kira_