Free chapter · Read without an account

47

by Fareeda Aliyu · KOWA DA ƘADDARARSA

Kuka na ci abu na zuciya ta tana suya, da sahur ma ruwan bunu na sha kaɗai. Yinin ranar gabaɗayan shi a ɗaki na nayi sannan na ƙi kunna waya ta. Mama ma ta ɗauka rashin lafiya nake yi don haka sai tace nayi zama na a ɗaki kawai zasu yi kayan shan ruwa. Na so ta bar ni nayi girkin ma ko hakan zai ɗauke mun hankali damuwa ta ta ragu amma ta dage sai na koma ɗaki, dole na haƙura, ai kuwa tunani ya ƙara lulluɓeni.

Ana cikin shan ruwa, wayar Mama ta ɗau ƙara, Yaya Naziru ne. Surayya ce ta haihu an samu mace. Wannan sabon labarin ne yayi nasarar ɗauke mun tunani, farin ciki ya mamaye gurbin wancan. A gurguje na ƙarasa cinye abinci na na koma ɗaki domin kiran mai jego. Waya ta na zaro daga ƙarƙashin filo na kunna, saƙonnin Nu'uman ne suka yi ta shigowa, amma ban buɗe ko ɗaya ba sai lambar Surayya da na kira. Ta dinga lallaɓa ni da yi mun daɗin baki cewa na zo Legas, tunda suke ban taɓa zuwa ba, yanzu dai ko ban zo domin su ba na zo domin baby. Yanzu dai ba zan iya zuwa saboda aiki ya chuɗe mana a 'yan kwanakin nan sannan muna gab da fara jarabawa a makaranta, amma in shaa Allah ina gama jarabawa zan taho na tabbatar mata.

Kafin mu gama wayar da ita sai ga kiran shi ya shigo. Don haka ina gama wayar sai ban kashe wayar ba na tsaya duba saƙonnin da ya turo, dukkan su abu ɗaya suke magana a kai watau 'me ya same ni ko me ya faru' cike da nuna damuwa.

Kwanciya nayi na buɗe Whatsapp ɗina nayi masa magana ta can, na sanar da shi ciwon kai ne ya addabeni shi yasa ban kunna wayar ba kwata-kwata. Ya amsa mun da "Ummu ji nake yi kamar da wata sabuwar Ummu nake magana daga jiya da daddare zuwa yanzu ɗin nan. Me kika yi wa ainihin Ummu na?"

Duk da raina ba daɗi sai da maganar ta sanya na fara sauka don haka na amsa da cewa "Ummun ce dai ba bambanci, me ka gani sabo?"

"Babu. Jikina ne tun jiya yake bani akwai matsala. So, ya ciwon kan naki? Yayi sauƙi yanzu?"

"Yeah. Alhamdulillahi."

Sai na tsinci kaina da son tambayar shi, so nake na samu hujjar da zan gamsar da zuciya ta cewar ya kamata ta saki Nu'uman haka nan. Sai na tura cewa "Ɗazun nan ina kwance da rana sai kawai na lura ba wani sanin ka nayi sosai ba. Zan iya tambayar abubuwa da suka dangance ka?"

Ya amsa mun da "Lol! Ummu tambayi ko me kike so."

Na tura "Kar fa ka yi complain domin zan iya tambayar bazata."

"Kar ki damu, tambaya kowacce iri ce daga wurin ki ba ta tsorata ni. Oya ask, i'm all ears."

Da ya bani dama kuna sai na rasa da wadda zan fara, dukkan abinda nake son sani bai shafi ahalinsa ko aikin shi ba. Dangantakar shi da wasu 'yan matan kaɗai nake son sani, sannan bana son tambaya kai tsaye wace ce Asmaa. Da idona naga yanda yake zamewa maganar ta sannan zai sanya hakan a matsayin kishi. Ba ni da buƙatar ba shi haske na sanin yawan son da nake mashi bare yayi burga da shi idan mun rabu. Na fi kowa sanin zan wahala, zan shiga hali kwatankwacin wanda na shiga a lokacin da Aliyu yayi aure. Tunani na ya tsaya akan cewar Nu'uman soyayya kaɗai ta kawo shi ba aure ba, ni kuma a shekaru na ina naga damar wannan wasan saboda Allah?...."

Saƙon shi ya ƙara shigowa "Kin yi shiru kuma ko duk girman tambayar ce haka?"

Na amsa nan take "A'a. Tell me about your relationships."

Ya ɗan yi jim kafin ya turo mun amsa, a jiki na naji dariya yayi mun. "Gabaɗayan su? Hakan na nufin na da da na yanzu. Me yasa ba ki tambaye ni lokacin da muna tare ba? Amma bari nayi maki wani alƙawari, duk lokacin da muka haɗu, idan kin tambaya to tabbas zan faɗa maki komai."

Da naga haka sai na juya akalar tambaya ta zuwa "Toh wasu qualities kake so matar da za ka aura ta kasance da su?"

Ya rubuto "Qualities wasu abubuwa ne da ba lallai na same su duka ba, ga misali idan ina buƙatar guda goma, da wuya ki ga mace ɗaya ta haɗa su gabaɗaya. Abu ɗaya na sani dai, idan matar da zan aura ta kasance mai girmama ni da bin umarni na sannan da gujewa ɓacin raina zan iya zama da ita. Ba kuma hakan na nufin wai ni kaɗai ne zai dinga yanke decision wa family ɗin mu ba, ai we are partners."

Na mayar masa "Da so samu ne ka auri wadda ka girma ko?"

"Shi rashin kunya ai ba'a shekaru yake ba, amma waɗanda ka girma ai sun san ko banza an girme su, probably su yi biyayyar. Besides ma, ina ce shine culture ta nan haka ko?" Hirar ta ishe ni don haka nace "Kar tarawee ya wuce ka, naji ana ta sallah."

Ya amsa "Ni ma ina ji, sai dai nayi tawa a gida don tun ɗazun aka fara ai." Ban gama ƙarasa karanta saƙon ba sai ga wayar shi, abinda ya faɗa kuma shine "Ki daina tunani mai yawa Ummu, ciwon kan nan naki na tunani ne. Tambayoyi kamar lauya. Sai na dawo." Ya kashe wayar ba tare da ya jira ni nace wani abu ba.

Har na kwanta bai kira ni ba, hakan kuma bai yi mun magana a WhatsApp ba alhali ina kallon shi online. Kawai sai na tsinci kai na da tafasar zuciya. Na rasa wani irin kishi nake ji akan Nu'uman, kishi irin wanda ban taɓa ji ba akan ɗaya daga cikin samarin da nayi a baya ba. Haushin haka ya sanya ko sallama ban yi da waɗanda nake amsa maganar su ba, na kashe wayar na kwanta.

A ƙarshen satin ranar da ba na aiki sai aka yi sa'a ma azumin bana yi ranar. Ana gama shan ruwa, lokacin har an fara kiran sallar isha nace da Mama ina son zan je ɗan koli stores nan tarauni akwai abinda zan siya. Ba ta hana ni ba. Ni gabaɗaya ma ba'a mun kulle ko takura a gida daga ɓangaren Mama har Baba. Passport ɗin Nu'uman kaɗai na ɗauka don na mance da coat ɗin shi sam. Hussein ma cewa yayi na jira shi akwai abinda yake buƙatar siya shi ma, amma sanin cewar ba can zan je ba kafin ya fito har na ja motar na harba sai Nasarawa GRA.

A harabar gidan nayi parking bayan maigadin ya buɗe mun ƙofa. Cikin sa'a a harabar gidan na iske shi da wasu 'yan mata biyu. Su ne kuma suke fuskantar hanya da na biyo, shi kuma ya juya mun baya. Kallon da ya ga 'yan matan na yi ne ya sanya shi juyowa. A take idonshi suka ƙara haske alamar murnar gani na. A take ya baro wurin su zuwa wurina tare da ƙoƙarin karɓar jakar hannu na amma sai na hana shi.

Ɗaya daga cikinsu tana dariya tace "NB wannan ce Madam ɗin ko?" Yana kallo na yana dariya amma bai ce komai ba. Suka yi mana sallama har ɗayar na ƙarawa da "NB kar ka manta saƙon Mama." Ya amsa masu da kai.

Bai jira sun gama wucewa ba ya ja hannuna zuwa cikin falon gidan. Duk dagiyar da nake yi na son ƙwace hannuna amma bai bari ba sai da ya dangana ni da kujera mai zaman mutum biyu, sannan ya juya ya nufi firinji yana faɗin "Me zan kawo maki Ummu? Juice? Fura? Ko Yoghurt?

Na amsa a lokacin da nake ƙoƙarin canza kujera zuwa ta me zaman mutum ɗaya "Ba ko ɗaya, a ƙoshe sosai nake. Alhamdulillah." Nasan musu na ba zai hana shi ɗauko abinda yayi niyya ba, lemon gwangwani ya ɗauko guda ɗaya sannan ya zo hannun kujerar da nake zaune tare da karkato wa yana fuskantata, yace "Ummu me ya faru? Fuskar ki tsorata ni take yi."

Na yi murmushin ƙarfin hali nace "Nu'uman kenan. Babu komai. Ga abinda na kawo maka." Na miƙa mashi international passport ɗin shi.

Ya karɓa yana cewa "Ayya! Ashe a wurinki na bar shi, har ina ta ƙoƙarin sake yin wani don na ɗauka na ɓatar da shi." Ya ɗan yi shiru sannan ya sanya hannun shi a kaina ya juyo da kaina yanda zai kalli fuskata da kyau. Yace "Faɗa mun abubuwan da suke faruwa da ke."

"Abubuwa? Wani irin abubuwa kuma?"

Ya amsa "Abubuwan da suka sanya kike janye wa daga gare ni, kiri-kiri kin nuna mun kina buƙatar distance kuma shi ɗin na ba ki don ki gama warware abinda ya shige maki duhu."

Sai kawai anyi amfani da damar na danne tunanin abinda zai biyo baya nace "Me yasa kake so na?"

Ido ya zaro yana kallo na cikin mamaki, sai ya saki kaina tare da tashi daga hannun kujerar ya dawo gaba na ya tsuguna yana leƙen fuskata da na duƙar ƙasa. Ƙila gani yayi tsugunon ba zai yi mashi ba sai ya zauna kawai tare da riƙo hannaye na yace "Ummu? Tantamar so na a gare ki kike yi? Wai meye asalin waɗannan sabuwar halayyar nan ne? Kin rikice mun gabaɗaya na kasa gane maki."

Ina ƙoƙarin janye hannuna nace "Har yanzu ba ka bani amsa ta ba."

Ya ƙara riƙe hannun ya kalli idona, ko ba'a faɗa mun ba nasan ranshi a ɓace yake, duk da ban taɓa ganin ɓacin ransa ba amma wannan kam tabbas shine. Yace "Ni ban taɓa so mara dalili ba sai akan naki, kawai na san ina son ki da son kasancewa tare da ke, saboda koyaushe nake tare da ke ina tsintar kaina cikin farin ciki da nishaɗi."

Na kawar da kaina daga gare shi nace "Ka na da tsarin zamar da ni matar ka kenan?"

Ya sanya hannu ya juyo da fuska ta gare shi yace "Aure kike magana ko? Ummu ki sani ba'a matsayin girlfriend kaɗai nake kallon ki ba tun ranar da na gane yanda nake jin ki a raina. Amma yanzu ba mu daɗe muna fuskantar juna ba, wanda ke ma kin san shine abu ma fi mahimmanci a gare mu gudun da na sani nan gaba. Mu ɗan ba wa juna lokaci, kin ji?" Duk fa wannan bayanin yayi, yayi shi ne cikin ɓacin rai da rikicewa, hakan na zayyane bisa fuskarshi. Na miƙa hannu na cire hannun shi daga haɓa ta da ya riƙe tare da miƙewa amma ya sanya hannun shi ya mayar da ni zaune.

"Amma kasan yawan taɓa ni da kake yi ba abu me kyau ba ne ko?"

Ya amsa "Bana iya ajiye hannu na muddin ina kusa da ke. Da kike shirin tafiya, ai ba ki sanar da ni abin da ya kawo waɗannan tambayoyin ba. Relationship has to be fair, idan ba haka ba ta ina zan fahimce ki?"

Na miƙe tsaye, wannan karon bai hana ni ba, ya cigaba da kallona har na ɗauki jaka ta sannan nace "Abu ɗaya nake son ka sani, I'm older than you."

Yayi dariyar takaici yace "Ke ɗin ce kika girme ni? A wace duniyar kenan?" Ya miƙe tsaye.

Na ɗaure fuska ta a wani yanayi na nuna cewar ba wasa "Wallahi da gaske nake, wata sha ɗaya ne tsakaninmu. Na ga ranar haihuwar ka a jikin passport ɗin ka."

Shi ma ya ɗauke fuska yace "Sai me to? Shekaru ba lambobi ba ne?"

"A tunanin ka."

"A tunanin kowa ma. Amma dakata tukunna, menene manufar ki?"

"A bayyane amsar take, we can't be together! Kai ma kasan hakan bare ni."

A fusace yace "Da za ki nemi wani dalili na rashin kasancewar mu tare da nayi maki uzuri amma kafin mu yi nisa ma, kin san Allah Ummu, duk ranar da kika kuma kuskuren faɗin kin girme ni sai kin raina shekarun da kike taƙama da su. A shekarun da kike jin kin girme ni da su, a halin yanzu wa yake nuna halin yara? Ni ko ke?! Yi magana mana!" Ya ƙarasa maganar cikin ɗaga murya.

Duk da na tsorata da yanayin fuskarshi amma sai nayi ta maza na share nace "Kai ne! Ka fi kowa sanin muna rayuwa a wata al'umma da aure a tsakanin irin mu abu ne me wahala ne. Sanin da nayi cewa na girme ka ba zai bar ni ka dinga juya ni yanda kake so ba."

Hannun shi rungume a ƙirjinsa yace "Haka kike gani? Kin san kuwa ni namiji ne? Namijin gaske ba wai a suna kawai ba? Ki tafi ki gama shawarar ki domin ni ina kan baka na babu chanji."

Ban ƙara magana ba balle musu na kama hanyar waje, ko kallo ban samu daga gare shi ba balle rakiya. Cikin sanyin jiki na ja motar na koma gida Hotoro.

Kwana biyu ba wanda yayi wa wani magana a tsakanin mu. Ban daina addu'a ba, kasancewar ban san me zan roƙa ba, kawai cewa nake yi Allah ya yi mun zaɓi na alheri kawai.

Abubuwan da suka faru a ranar da naje wurin shi sun daɗa tabbatar mun da cewa wasa ya zo yi wurina. Idan ba haka ba, ta yaya zai ce mun ba maganar aure a halin yanzu sai mun fuskanci juna? Ina ma laifin yace yana da tsarin mayar da ni matar shi nan da lokaci kaza. Idan kuma ba mu fuskanci juna ba hakan na nufin rabuwa kenan. Sannan ga shi har yau ɗin nan bai ƙara nema na ba, hakan ya tabbatar mun da cewa dama hanya me sauƙi ya ke nema, tunda kuwa na ba shi sai ya bi hanyar ya zame. Ya Allah! Ni kuwa zan taɓa yin aure a duniyar nan kuwa? Sai kuka nake yi kamar zan shiɗe, ba mu daɗe tare da Nu'uman ba amma ya addabi zuciya ta, na so a ce shine ya ba ni wata goma sha ɗayan nan ko yaya zan iya daurewa.

A ranar kwana na uku ina wurin aiki, ya iso kafin a yi isha. Waya ta ta ɗau ƙara lokacin da kiran shi ya shigo, gaba na yayi mummunar faɗuwa. Da so samu ne na share kiran amma zuciya ta ba zata iya ba, don haka na amsa kiran. Bai amsa Hello ɗin da nace ba, kawai cewa yayi "Sauki ƙasa ina jiran ki." Da kamar ba zan je ba, amma sai nayi wa kaina faɗa na sauka. 

A mota yake zaune, kuma ko da na buɗe motar na shiga na zauna ban yi masa magana ba bare gaisuwa, hakan ya sanya muka yi shiru gabaɗaya. Bayan kamar minti biyar yace "Ummu har yanzu ba ki tsayar da shawara ba?"

Sai na samu kaina da cewa "Zan iya canza shekarun mu ne? Yanda na girme ka ba canji haka nan....." Bai bari na ƙarasa ba ya damƙo hannaye na da ƙarfi har sai da nayi ihu saboda azabar zafi kuma bai saki ba. Ya girgiza ni cikin ɓacin rai yace "Au! Ashe ba ki ji gargaɗin da nayi maki ba ko? Ummu ki haɗa shekarun ki ki wuce ni a komai. Kin ji?! Get out!" Ya saki hannayena tare da sunkuyowa domin buɗe ƙofar motar, ya sake nanata wa "Fita!!". A tsorace nayi waje, da sauri ya rufo murfin motar shi har ya kusa ture ni sannan ya fisgi motar kamar me shirin barin duniya. Na tsorata iya tsorata, na dinga kiran wayar shi amma ya ƙi amsawa. Da ƙyar na ƙarasa aikina na ranar.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.