Free chapter 路 Read without an account

Part 14

by Maman Nusaiba 路 ABBA NE

_*馃尰ABBA NE 馃尰*_





_Hakkin Mallakar_


_*Sarat Alk'asum (Maman Nusaiba)*_



_馃敂馃摎JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 馃摎_




_*Saura one fage a gama free fage, kada ku bari a baku labari masoya*_


*Littafin na kud'i ne only N300 No. +966577675904*



亘爻賲 丕賱賱賴 丕賱乇丨賲賳



1锔忊儯4锔忊儯


Taja da baya jikinta na rawa cikin kidima take binshi da kallo bakin ta na rawa tace K..kai.kaine? Wani k'ayataccen murmishi yayi baice mata komai ba sai ya samu guri a kusan ta ya zauna" Had'e rai Ashma tayi tace Wai lafiya ka wani zauna min anan? Wata gwauruwar ajiyar zuciya ya sauke san nan yace" Kin san kuwa wahalar da nake ina neman haduwa dake? Wani kallo ta watsa mishi tana hura hanci tace" Kamar ya ya ban gane ba? Gyara zama yayi yana marairaice fuska kamar zai saka mata kuka yace Ashma ina matuk'ar k'aunarki ina miki son da ko kaina bana yiwa, don Allah ki Soni kema kinji na jima ina neman hanyar da zan had'u dake amma ban samu ba. Dariya Ashma tayi dan ita bata ma san me ake kira da so ba" Yatsar ta guda biyu da ta saba sha ta sanya a baki tayi shuru tana kallon shi ba ko k'iftawa. Tuni ya susuce ganin yadda ta zuba mishi idanunta masu kama da madara, cen ta matsa kad'an sai kuma ta miki tana duba wayarta tace Kaga Malam nifa ban san akan me kake magana ba, na san ma ko meye wani So ka dena kulani ko na hadaka da Abbana ko Papi na" Ta karashe maganar tana murgud'a mishi baki. Mik'ewa yayi yace Kiyi hakuri Ashma kar kice bakya sona Wallahi zan shiga wani hali" ya fad'a da iya gaskiyar shi. A fusace Ashma ta juyo cikin masifa tace" To ka mutu mana ina ruwana dakai, ka manta lokacin da kake ce min mai kama da aljanu? Ta fad'a tana dannawa Khalil kira. Mansoor dake tsaye yana kallon ta ji yayi kamar ya sace ya gudu yabar k'asar sai dai ba zaiyi hakan ba, so yake kamar yadda yake sonta itama tace tana sonshi dan haka yace" Yi hak'uri karki kira Abba kinji Ashma. Bata saurareshi ba jin Abba ya d'aga wayar yace My princess ya karatu? kawai ta saki baki ta soma kukan sakalci. D'aga cen b'angaren Khalil kuwa yana zaune a harabar Office d'in shi jin ta sanya mishi kuka ya miki yana cewa, Meya faru kuma? Nifa bana son kina sakani damuwa ke wai yaushe zakiyi hankali ne don Allah? Turo baki tayi kamar yana ganinta tace" Yo Abba Direba yak'i zuwa ya daukeni kuma yunwa nakeji har na soma ganin jiri" Ta fad'a tana zama a inda ta tashi. Shi ko Mansoor kamar wani sakarai haka ya saki baki yana kallon Ashma sai hadiyar yawu yake ganin yadda take juya jikinta ko ina na motsawa kamar wata babbar Mace.. Khalil yace" Pardon Princess din Abban ta yanzu zan kirashi naji dalilin daya hana shi zuwa ya dauke ki akan lokaci. Yauwa Abba yayi sauri gaskiya bacci nakeji, to yace mata san nan suka kashe waya" Yana kashe kiran ya dannawa Direba kira cikin fushi, ko amsa gaisuwar dayake mishi baiyi ba yace Wani dalili ne yasa baka je ka dauko min Y'ata ba a Makaranta? Shin ka zare ne ko ka manta gargadin dana yi maka, to ka maida hankali kaje ka dauko ta tin d'azu sai jiranka take.. Allah Sarki Direba shi kuwa shuru yayi dan tuni ya jima da Makarantar su Ashma yana jiran fitowarta sai waigawa yake yaga ta ina zata bullo amma shi ya dauka ma ko an basu Jarabawa ne" Cikin girmamawa yace Oga Wallahi ka ganni nafi awa anan a tsaye ina jiranta amma shuru bata fito ba, kace mata ina waje a inda na saba tsayawa. Khalil yace To shikenan ka shiga ka duba ta tace jiri takeji bana so ace ciwon ta ne zai tashi shiyasa ko ta fita hankalina baya kwanciya har sai na ganta a gida.. Na gane Oga bari naje na dubota sai anjima, Kashe kiran yayi ya kira Ashma tana dauka yace Ki fito inda zai ganki Princess ashe ma ya jima yana jirank矛 ina kika shiga da kuka tashi? Abba ina bayan Class din mu na zauna bari naje" To shikenan ki kulamin da kanki Princess banda wasa da Samari banda jan fad'a ko banza, maza ki wuce kije ki koma gida ko na samu nutsuwa.. Dariyar jin dad'i tayi tace" In kula da kaina Abba ai ni nawa kan ajikina yake to a ina zan kula dashi? Ta fad'a tana mik'ewa tsaye.. murmushi yayi kawai ya kashe kiran" Ita kuwa wayarta ta sanya a jakar ta zata wuce Mansoor ya mik'e yace Muje na rakaki ko! Tsayawa tayi cikin jin haushin ya takura mata ta nuna shi ta hannu tace Idan ka sake min magana Hmm ba saina fad'i sauran ba banza kawai dan giya, a haka kake so nace ina sonka kana shan giya kalle ka fa kamar ba Musulmi ba, tana fad'in haka ta wuce fuuu...


Direba na ganin ta ya iso da sauri yace" Ranki ya dad'e ina kika shiga ina ta neman ki ? Murmishi tayi tace jiri nakeji muje gida" Da sauri ya iso bakin motar ya bud'e mata ta shiga san nan shima ya zagayo ya shiga suka wuce...


*Nigeria*


Hisham ne zaune da Khalifa suna hira sosai kowa yake ganin d'an Uwanshi ya rame, murmishi Khalifa yayi yace" Friend lafiya naga ka rame ? Ko dai wani abu ke damun ka? Hararar shi yayi yace To ai kaima ka rame kama fini rama. Ajiyar zuciya ya sauke yace ba dole na rame ba Kawu yak'i ya bani Layla amma jin wanda za'a baiwa ita sai na taya ta farin ciki dan nasan shima zai kula da ita fiye dani ma. Hisham ya kalleshi cike da tausayawa yace Ka kwantar da hankalin ka ni ba zan tab'a yarda na auri Layla ba alhalin kai kake son ta" Nayi magana Da Daddy kuma ya fahimceni Insha Allah Layla taka ce ba tawa ba, ni kaga ba son aure nake mata ba na Y'an uwantaka nake mata kaine masoyinta wanda zata aura akan me zan yarda a raba wannan soyayyar? Kasha kurumin ka komai yayi ready.. Cikin tsananin farin ciki yake kallon Hisham yace" Ban san dame zan saka maka tabbas kai Aboki ne na kwarai. A'A karka damu ai mun zama d'aya ni da kai" Hira suka shiga yi kamar yadda suka saba a koda yaushe idan sun samu lokaci..


Sallama sukaji anyi musu daga bayan su, Khalifa ne ya amsa shi kam Hisham bai ko kalli wajan ba bare yasan waye ya iso inda suke.. Khairat ce d脿 K'awarta cikin shiga ta atamfa super an kashe dauri ta yafa mayafi dan karami sai wani yauki takeyi har suka iso. Khalifa ya kalle su yace Sannun ku da zuwa! Khairat ta samu guri ta zauna tana facing din Hisham tace Doctor wajanka mukazo K'awata bata da lafiya. Bai d'ago ba yace Kuje ciki a duba ku ni bana duba Mata, ya fad'a rai a had'e dan kar ma ta kawo mata wargi. Khalifa ya mike tsaye yace To ni bari naje ciki tinda kayi bak'i sai munyi magana" Tsaki Hisham yaja yaci gaba da duba wayarshi, Khairat ta kalli K'awarta tace ki zauna mana nasan fushi yake dani zan bashi hak'uri,zama tayi ta k'urawa Hisham idanu sai taga ai yafi Mijinta komai da take ganin kamar ba wanda yakai Mijinta kwarjini da jan aji, ashe dai natan ba komai bane akan Hisham, a hankali tace" Doctor kayi hak'uri abinda K'awata tayi maka nasan bata kyauta ba kuma ba halinta bane, kasan ance zuciya bata da kashi. Ko kallon inda suke baiyi ba ya mik'e tsam ya wucewar shi ciki. Ciza lips Khairat tayi tana cewa" Hmm Doctor idan ka shigo hannuna saina rama duk abinda kake min Wallahi kaci bashi, ha艜 wannan Yarinyar data min rashin kunya sai na sa an kakkarya ta. Dafata K'awarta tayi tace kawo kunnen ki kiji" mik'a kunnen nata tayi ta rada mata magana da su kad'ai suka san mai suka fad'a. Da sauri ta d'ago ta kwashe da dariya tana cewa Gaskiya K'awa kin iya kawo shawara muje tinda kince Mijin ki yazo. Mik'ewa sukayi suka fita ko waccen su na murmushi har suka doso shi.. Tin daga nesa Mijin K'awar Khairat ke binta da kallo sai wani lashe baki yake yana jinjina kai har suka iso bakin motar. Tsayawa Khairat tayi tana k'iftawa Mijin K'awarta ido shima yana mata, tace To sai wani lokacin bari na shiga Napep na wuce gida ko. B'ata fuska tayi tace Haba ki shigo mana mu ajeki a gida" Yatsina fuska tayi tace Ai gidan mu yafi naku nisa taya zaku kaini? Kinga bana son jan magana ki shigo kawai. Murmishi tayi ta shiga baya ta zauna yaja suka bar wajan..


Suna cikin tafiya tace" Sameer ya kamata ka fara ajeni sai ka kaita saboda nayi maka girki kafin ka dawo" Wani k'ayataccen murmishi Sameer yayi yace To shikenan ai duk yadda kikace ayi haka za'ayi Uwar gida Sarautar mata, murmushin jin dad'i tayi tace nagode. Suna isa gidan ya aje ta tace Khairat sai sunyi waya ta amsa da to san nan suka wuce ita kuma ta shiga ciki" Dariya sukayi a tare suna tafawa Sameer yace Kina lokaci Baby Wallahi. Wani Farr tayi da idanu tana yauki har suka isa h么tel din da sukeson zuwa. Haka suka kama d'aki na kwana biyu suka wuce cikin kamar wasu Mata da Miji, ita ko Khairat burinta bai wuce ace Hisham ya aureta ba ,amma tinda yaki yarda ta lallami zata bishi ta tsiya-tsiya tinda taurin kai gareshi..


*Niger*


Sanjina na zaune tayi tagumi ta lula duniyar tunani, Inna ce ta fito tana buga sauri kamar zata tashi sama har tuntube takeyi. Ganin Sanjina a palo yasa taja ta tsaya tana rike baki tace" Ke dai mai sunan Jimina ankai Jarababbiya yo in banda haka meye na wani shiga damuwa dan Mijin ki yace zai kwana a wani garin? Ke bari kiji in gaya miki ni nan da kike ganina Uban shi Umaruru ma haka yakeyi kuma Matarshi babu ruwanta sai dai tayi ta mishi Addu'o'in samun nasara, ke kuma da yake kin rako mata duniya shine kika zauna kina kuka da tunani ko? To tashi maza kije kiyi wanka ki ci abinci inaso ki sake rakani gidan Musalle. Goge hawayen ta tayi ta d'ago tana kallon Inna da take zuba, a sanyaye tace Inna kinga idan na kira wayarshi bata shiga fa, sai ace min a kashe take tin safe nake kiranshi amma shuru. Zama Inna tayi tana kad'a kai tace Yo banda abinki shi da yake shawayi a sama ina shi ina daukan wayarki, ko kin mata su nasu aikin akasari a sama suke yinshi? Kiyi sauri ki tashi mu tafi.. shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya, ita dai tsoro takeji bata son wani abu ya samu Mijin nata.. Inna rafka tagumi tana kallon Sanjina dake shashekar kuka sai kawai ta tuno da Abban Khalil da Salma Matarshi kawai itama sai ta rushe da kuka.


Mamy ce ta shigo palon jin koke-koke yasa ta waiga sai taga Inna da Sanjina nata kuka kamar ba gobe, Gabanta ne ya fad'i ta dafe k'irji cikin tashin hankali ta soma fad'in" Inna lafiya kuke kuka? Ko wani abun ya faru ne? Tsayar da kukan Inna tayi tana fad'in yo ba Dole kiga muna kuka ba, ita Kukan Mijin ta take ni kuma kuka kewar Umaruru nake da Salamatu, Allah sarki mutanen kirki Allah ya jikan ku da rahama duk da Salamatu na min rashin kunya in tayi abinci sai ta cika yaji ko gishiri amma a hakan ma tafi Uwar Arufullah narkekiyar Kazama. Mace kamar jaka ba wanka ba wanki kina dosar inda take za kiji tana wari, ke har tsami take yi shine dan ta daukeni tsohuwar banza ta girka abinci tacemin naci, nace ai da Uwata Dije zata mutu bata min baki ba.. Cire dan kwalinta tayi ta goge hawayen ta saukowa k'asa tayi ta kuma sanya kuka ta kalli Mamy da take kunshe dariyarta tace" Kin san ma me akayi lokacin da ina Nigeria? Jin haka yasa Mamy zama tace A'a sai kin fad'a Inna.. gyara zama tayi tace Wannan Matar ta Amadudu muguwar kazama ce ,tinda nake bana cin abinda ya fito a hannun ta ko muna zaune sai dai kiji tana sakin tusa mai shegen tsami. Ba dan Allah ya Soni da rahamar shi ba, to da Matar Amadudu zata kumburani haka kawai sai ta wani je min d'aki tace wai tazo muyi hira,kiji fa kamar wata sa'arta, yo Ko lokacin data hadu da Amadudu ba hakoranshi talatin cif-cif a bakin shi ta ganshi bari ni har take had'a kanta dani.

Mamy tayi murmishi tana kallon Sanjina da take dariya tace" Gaskiya bata kyauta ba ai shiyasa muka dage sai kin dawo nan muyi zaman mu gaki ga Ashma da Sanjina a waje d'aya. Murmishi Inna tayi ta mayar da dan kwalinta ta daura mik'ewa tayi ta dauki hijabin ta zata saka a bai-bai Mamy tace Inna ba dai-dai bane.. tsuke fuska Inna tayi tace Bana son iyayi ni makauniyace aka ce miki? Mamy tace Yi hak'uri" Hak'uri kaya be nad'a ganmo ki dauka, Ta fad'a tana sanya hijabin..


Dariya sosai ta kama Sanjina ganin Inna ta sanya hijabin wajan wiyan shine a sama wajan kan kuma shine a k'asa, shuru sukayi dan kar Inna ta sauke miki lodi.. Zata sake magana sukaji an banko k'ofar, A firgice dukkan su suka juyo ganin abinda yake bakin k'ofar yasa suka firgita, Mamy tace" Kha...





_*Taku har kullum Maman Nusaiba c

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.