Free chapter · Read without an account
55
Ruwan da naji a fuska ta ne ya farkar da ni daga baccin da nake yi, Nu'uman ne tsaye daidai kaina da alamu daga wanka ya fito, ganin yana neman ya shafe mun ruwan jikin shi ba shiri na tashi, ni ma wanka nayi. Lokacin da na gama na fito na iske har ya jera mana kayan da muka zo da shi. Na kalli kayan nace ni kam kwana nawa za mu yi ne? Ya amsa "Kayan mu ko? Anjima kaɗan za mu fita mu siyo wasu." Na zaro ido nace don asarar kuɗi? Ina fa da sabbin kaya a gida, da ka bari na kwaso su ai."
Yace "Jigila za mu sha kenan. Ai duk mai wayo idan zai zo irin wuraren nan ya taho hannu rabbana, kayan ai da sauƙi. Bari dai mu je ki gani."
Ƙarfe uku muka sauko daga ɗakin mu muka taka zuwa boutiques ɗin da ke kusa da hotel ɗin mu, ni kawai biye da shi muke. Yana ta zaɓar mana kayayyakin da ya kamata nayi amfani da su a tunanin sa. Na shi bai fi kala biyar ba ya ɗauka sannan ya riƙe dukkan jakar kwalin da aka sanya su a ciki, muka koma hotel ɗin mu.
Biyar muka sake fitowa, amma wannan karon Bellaria restaurant and wine bar da ke kan layin Fitzrovia a 71 Great Titchfield muka isa domin cin abinci. Shi ma duka ba ya buƙatar abun hawa don da ƙafa muka gangara. Nu'uman na ba ni labarin wurin da muke zuwa, yace sau biyu suke buɗewa a rana watau sha biyun rana zuwa uku sannan biyar da rabi zuwa goman dare. Don haka muna isa basu daɗe ba suka buɗe. An kawo mun battered squid a matsayin mafarin (starter) cin abinci, shi kuma na Nu'uman ya kasance Tuna Carpaccio amma ni sai da na ci har na shi, dole sai na ɗanɗana ai. Sun ba mu shawarar cin open ravioli da fish ragout sannan muka cikashe cin abincin da apple pie watau dessert kenan. Har ina cewa da tare da Papa muke da ya fi kowa jin daɗin abincin saboda kifin da aka haɗa da shi. Muna gamawa nace na gaji mu koma ɗaki na huta kafin mu fara yawon ganin gari.
Tunda cikin mu ya ɗauka, ba mu ƙara fita ba. More ɗakin mu da junan mu kawai muke yi abin mu, ko TV ba mu iya kunnawa ba kwata-kwata tun zuwan mu. Nagode wa Oba fiye da sau miliyan tunda muka iso ƙasar nan a zuciya ta, don ta dalilin zuwan nan namu ne nake ganin wani sabon salon shaƙuwa da yake wanzuwa tsakani na da Nu'uman, 'kunya' na daɗe da manta wannan kalmar tun zuwan mu, wallahi Nu'uman ba ya bari na, ko na dage ban iya abu ba haka yake sanya ni na koya dole, don yace shi ba dutse ba ne, dole nake reciprocating efforts ɗin shi, ga shi ma har na saba na fara gwana.
Kasancewar hotel ɗin ke bada abincin karin kumallo, ta shi nayi na ga an jera shi a falon mu cikin tsari. Wanka na fara yi, a ɗakin na iske shi bayan na fito ya dawo daga gudu, bai shiga wankan ba sai da ya taya ni shiryawa sannan ya shiga yin na shi wankan. Abubuwan da yake mun yana sanyawa nake ji na kamar wata baby, lallaɓa ni kawai yake fiye da yanda na zaci zamantakewar mu za ta kasance.
Bayan breakfast sai ya ja mu wurin spa da suke kira da Chuan Spa. Couple's spa suite muka shiga yanda daga ni sai shi za'a yi wa. Muna shiga ya umarce ni da na shiga ɗakin canza kaya na ɗauro towel ɗin da suka ba ni, na zaro ido ina kallon shi amma ya kawar da kan shi, haka na lallaɓa nayi yanda yace. Kafin a ƙarasa mun ma tuni naji jiki na ya nutsu, ba alamar gajiya bare naji ta sannan ji nake kaman an canja mun fata ta.
Akan hanyar mu ta fita domin komawa ɗakin mu na hango swimming pool amma indoor ne, suna kiran shi indoor pool saboda kasantuwar shi cikin gini ba'a sarari ba. Na rinƙa jan Nu'uman zuwa wurin, ni so nake ya koya mun swimming amma sai yace na yi haƙuri mu je mu shirya mu tafi wurin cin abinci, kafin mu koma Najeriya zai koya mun in shaa Allah. Ranar kam a Burger and Lobster restaurant muka ci abincin a Fitzrovia.
Bakwai da rabi na dare kuma muka gangara London palladium watau theater ce, mun je kallon irin drama ɗin da suke yi da sauran abubuwan da suke nunawa, ni dai da na gaji da zama sai na kwanto jikin shi, shi kuma har da gyara zaman shi yanda zan ji daɗin kwanciyar. Yau kam ban ma ji gajiyar sabgogin da muka sha yau ba sam.
Ido na ya buɗe da abubuwa da yawa a zama na a can. Babu kusan wurin da bai kai ni ba, ba zan iya tuna kala-kalan restaurants da muka ziyarta ba, tun daga kan waɗanda sai an yi making reservation, da waɗanda kana zuwa kai tsaye za ka samu, da waɗanda takawa kawai za ka yi kawai, har na hawa mota, na ci abinci har ba zan iya ƙirgawa ba. Har Sauna ya kai ni naje na sha steam.
Ranar Alhamis kam zagayen kafa muka yi, na daɗa da gane yanayin garin. Ranar da safe kam saloon ya kai ni aka yi mun gyaran gashi. Yau shigar da nayi da wuya ku gane ni, yayi mun hotuna har ban san kala nawa ba ne. A wannan zagayen ne muka ci karo da wani gidan abinci mai suna The Terrace Garden a 1C Portland Street, kusa sosai da layin da hotel ɗin mu yake kai. Shukokin wurin ne suka ɗauki hankali na, mun yi hotuna nan ma. Na daɗa kallon wurin nace masa ka ga yanda tsarin wurin yake? Sai kawai ya sanya ni naji sha'awar buɗe nawa gidan abincin."
Da ƙarshen sati kuma muka fita can waje gari, a Paddington street station muka hau jirgin ƙasa, underground ma kuwa. Mun sha yawo. Na ga abokan shi da suka yi makaranta tare, ya nuna mun makarantar, wurin da yake cin abinci har ma gidan da ya zauna lokacin yana karatu. Kallon komai nake with interest, kamar yana walking ɗina through his past life. A Bar muka haɗu da friends ɗin shi, mun ci abinci, su sun sha giyar su mu kuma lemo. Sai washegari muka koma hotel ɗin mu da yamma liƙis, don haka ina isowa sai bacci.
A farkon sati na uku wanda a ƙarshen shi ne za mu dawo Najeriya, a wannan daren mun ziyarci The Gorge Pub. Ba yunwa nake ji ba amma ganin ire-iren abubuwan da suke da shi na abinci a take naji yunwar. Daga ƙarfe sha ɗayan safe zuwa na dare ne lokacin buɗe su. Nu'uman yayi odar chicken in hot sauce, blue cheese dip, spring onion and celery. Ni kuma ruwan ido, ji nake kamar a kawo mun kowanne abincin a plate na ɗanɗana domin menu ɗin su yawa ne da shi. Shi kuma ɗan taya ɓera ɓari wai naci iya wanda zan iya ci yau, ragowar kwanakin mu sai mu dinga zuwa nan kullum har sai naci komai na menu ɗin. Nama da salad ɗin su naci kawai a ranar sannan na ci daga plate ɗin Nu'uman, ya ma riga ya saba, komai yayi order sai na ɗanɗana har ma na koya masa.
Mara ta ce ta cika fal da fitsari don haka na doshi restroom ɗin restaurant ɗin. Na gama abinda ya kai ni na tsaya wurin madubi na ɗan gyaggyara kwalliya ta sannan na fito domin dawowa. Ido na ya sauka akan Nu'uman zaune sannan ga wata ta dafa kafaɗar shi da alama sun san juna don haka sai na laɓe ina kallon su. Ina son ganin me zai faru a tsakanin su, I'm trying my best to give him benefits of the doubt.
Ina kallon shi ya juyo ɓangaren restroom ɗin, ina kyautata zaton tahowa ta yake dako, sai kawai na ƙara laɓewa. Sai na ga ya miƙe tsaye tare da cire hannun ta daga ƙafaɗar sa sannan ya ja kujera ya zaunar da ita. Ko daga wurin da nake tsaye nasan a buge take sosai da sosai. Sai kawai na ƙarasa hanyar fita na ɗauki coat ɗina daga wurin da muka rataye su na fito waje kawai, I need air to clear my head, lokacin ƙarfe goma da arba'in biyu hakan kuma na nufi bai fi minti goma sha takwas a rufe wurin ba.
Duka minti biyar a tsakani na hango shi ya fito yana haki, da alama tuntuni nema na yake yi. Nayi kamar ban ganshi ba, sai da ya ƙwala mun kira na ɗago kaina ina kallon shi, har lokacin bai gan ni ba shi yasa ya cigaba da kiran sunan nawa yana juye-juye, sai a kusan kira na biyar sannan na amsa. In a rush ya ƙaraso wurin da nake zaune yana cewa "Me yasa kika fito ba ki faɗa mun ba? I've been searching for you Kulsum! Ɗaya daga ma'aikatan ne yace mun kin fito. Are you okay? What's wrong?" Ya zauna kusa da ni yana dudduba ni sai kawai kuma ya rungumo ni ta gefe tare da ajiye haɓarsa bisa kaina, yayi ajiyar zuciya. Duka muka yi shiru.
Bayan wasu 'yan mintuna sai ihun matar da na hange su ɗazun tare ya cika wajen, hakan kuma ya jawo hankalin mu zuwa gare ta. Ɗauko ta aka yi daga cikin Pub ɗin aka watsar anan waje, suka juya suka rufe wajen nasu kuma. Har lokacin muna zaune shiru kafin daga bisani yace "Kulsum kin ga waccan? She was my classmate, ba za ki damu ba idan mun taimaka ma ta ba? Barin ta anan hatsari ne ga ƙarin cewa ita mace ce." Ni dai ban ce komai ba don ban san tunanin da nake yi ba.
Ya miƙe tsaye tare da ɗago ni muka doshi wurin da ta ke yashe a ƙasa, tana ta ƙoƙarin rufe jikin ta da alama sanyi take ji. Ya tsuguna tare da tallabo ta domin ta miƙe tsaye sai kawai muka ji ta sa dariya tace "You are finally back to me."
Ya amsa "Told you I'm already married. Where do you live? So i can get a cab to take you there"
Tace "Duk wurin da kake nan ne wurin zama ba" sannan ta jawo hannun shi na hagu, ta cigaba da magana "Ina zoben auren naka?"
Ya ja tsaki sannan cikin faɗa yace "Ki faɗa mun address ɗin ki." Bana jin ma ta ji me yace don a take ta fara bacci.
Daga shi har ita haushin su nake ji, wai shi gentleman, don haka sai na kama hanyar komawa hotel ɗin na bar su su ƙarata tunda nasan hanya ai. Sai da na isa da kusan minti goma sannan na hango shi riƙe da ita ya doso hotel ɗin. Watau dan rashin mutunci a ɗakin mu zai sauke ta kenan, don haka ban jira zuwan shi ba na wuce wurin da indoor pool ɗin nan yake, don na tabbatar yanzu ba kowa a wurin.