Free chapter · Read without an account
12
"Barkanmu da safiya..."
Sakina ta furta sanda ta matso kusa dashi sanye cikin kayan makaranta, cikin sanyin muryarsa ya amsa mata da"lafiya lau dan Allah anan gidan kike..? "...."Eh! Eh ni 'yar gidan ce lafiya kake tambaya ? "
Fesar da wani huci yayi, hannunsa zub'e cikin aljihun wandonsa, yace"watakila kuna da labari, watakila kuma baku sani ba, to Nine wanda ya komo wannan gidan dake kusa da naku, jiya kun hanani bacci meyasa..? Me yayi zafi ? aganina duk abunda yayi tsanani maganinsa Allah don shi babu abunda yafi karfinsa, wacece Rahama kuma menene dalilin dayasa aka matsa mata akan aure don iya abunda na iya tsinta da fahimta kenan.."
Kafin takai ga bashi amsa, suka ji an bud'o kofa, k'yakk'yawar Fuskar Rahama ce ta bayyana agaresu amma fuskar fayau tattare da damuwa, sanye take cikin shigar malaman asibiti, sai da gaban Abdiel ya fad'i sanda idanunsa da nata suka harmutse cikin na juna, nan take yaji kawai wani irin mahaukacin tausayinta yana fuzgarsa don ko ba'a fad'a masa ba zuciyarsa ta bashi itace kawai Rahamar..
Fasa fitowar tayi sai kawai suka ga tana running tears sannan ta maida kofar ta rufe ta koma cikin gida wannan karon har suna iya jiwo sautin kukanta.
"Wait please...." Abdiel ya furta da karyeyyan murya ayayin daya dunkule hannu yana jin yadda mugun tausayinta yake dukan zuciyarsa, Girgiza kai Sakina tayi sannan tace;
"Uncle ka natsu ka saurareni, wannan ita d'in ce Rahama, yar'uwata ce wacce nake bi, jiyan nan ta fara aiki a Uduth, shekarunta talatin da uku kuma har yau batayi aure ba, ta kasa samun tsayayyen namiji abunda yasa kaga mahaifiyarmu ta tsananta mata kenan balle da wasu al'amura suke bullowa acikin kwanak'in nan masu hargitsa k'wak'walwa wanda ko kadan basu da dad'in ji, Uncle i can't tell you all amma daga ganin yadda ka nuna tausayi akanta lokaci daya nasan kai d'in kasan darajar 'ya mace, daga ganinka kana da nagartattun halaye kamar dai Uncle Yusufanmu, kana son kasan wanene Uncle Yusuf ? "
"Uncle Yusuf k'anin mahaifinmu ne, mutum ne me tsananin kaunar ya Rahama sannan kuma yana tsananin tausayinta, me kuma son cigabanta arayuwa "
Nufasawa tayi sannan ta cigaba;
"Na tabbata da ace akwai aure atsakaninsu da babu wanda ze auri Rahama face Uncle Yusuf ! ban sanka ba, ban san daga inda ka fito ba, yau ne farkon sanina dakai amma ji nayi kawai ka kwanta mun arai, Uncle please ka taimaka in baka da aure ka auri ya Rahama sabida ta fita daga halin takurar da take ciki agaban mahaifiyarmu." Ta karashe maganarta cike da yarinta.
Daidai nan Umar ya karaso wurin don ya kasa hakuri shiyasa ya karaso, shine ya fito daga mota ya nufo inda suke,
Harara ta watsa masa dan Allah ya sani sosai ta tsaneshi, tsana mafi muni kasancewar shine dan talikin daya jefa rayuwar yar'uwar nata acikin barazana. "Ke kina wasa dani ko ? "
Umar ya furta cike da zafin rai, Girgiza kai ya cigaba da yi yana fad'in "aduk randa zan sake ji ko ganin kina tallatawa wani banza matata to wallahi sai ranki yafi nawa mummunar baci, ki sani muddin ina numfashi babu wani mahaluk'in daya isa ya auri Rahama face ni Umar "
"Kai kuma aiki ne ya kawoka nan arewa ko kuwa lek'en asirin mutane ? " kala Abdiel bai ce masa ba ya juyar da fuskarsa ta wani shashin, hakan ya sake kufular da Umar, yasa hannu ya daki k'irjin Abdiel yana fad'in"dakai fa nake magana juyo ka dubeni ni ne nan ubangidanka akamfanin Dan'zaki Food, karka nuna mun cewa baka ji don asannan ne ni kuma zan gwada maka nawa kalar rashin jin, maza ka wuce ofis kar kasa in hada maka tuggun da bazaka iya kubutar da kanka aciki ba "
har Sakina ta bud'e baki zata bashi amsa da zafi, Abidel yayi saurin daga mata hannu amma kala bai ce mata ba ya juya ya nufi motarsa yana gani dishi dishi tsabar bakin cikin daya rufe masa idanu, Umar ya bishi da kallon tsana yana mai jinjina girman kai da kuma miskilancinsa kan ya juyo ga Sakina wacce take ji duk duniya babu wanda tayiwa karan tsana kamar Shi Umar d'in, ba don tana tsoron haduwarta da mahaliccinta ba to babu abunda zai hana ta dauki takobi ta tsoke dan banza har lahira.
Da gudu ta juya ta koma cikin gida sanda ta tuna cewa ai sunga fitowar Rahama amma basu san dalilin sake komawarta ciki tana kuka ba.
"wallahi Rahama indai ni Halimatu Sadiya in har nice na tsugunna na haifeki to kin gama Zuwa aikin asibitin nan agidan nan, kinyi zuwan farko kuma kinyi na karshe agidan nan, in kuwa kinga har kinsa kafarki acikinsa da nufin aikin sai in agidan mijinki ne, dan haka kukanki bazai sosa mun zuciya ba in kin ga dama ki had'iyi Zuciya ki mutu babu abunda ya dameni, Ki shiga ki tub'e kayan nan ki Fito ki kamamun wasu ayyukan ba wai tsayawa zakiyi kina zubad da hawayen banza da wofi tsaye awurin bafa ...."
Addah ta ida magana akufule ta dauki bokitin kayan Papa data wanke tayi wajen igiya zata shanya, Wani abun burgewa da Addah kenan kayan mijinta bata tab'a bari wani ya wanke da hannunsa sai ita.
ina nan tsaye awuri daya har Sakina ta shigo tana tambayata abunda ya faru nak'i tafiya wurin aiki.
Kafin nayi magana Addah ta hayyak'o mata itace hadda dakko Sanda tayi kanta"Ubanki aka mata kina jina ko ? Zaki wuce makaranta ko kuwa saina mommokeki tukun ?" Da gudu ta Fice tana waiwayenta ranta duk ba dad'i.
Ban ankara ba naji saukar sandar agadon bayana, Wani kara na k'wala na nufin inda Papa yake da sauri rik'e da briefcase d'insa yana shirin Fita Wajen aikinsa..
"in bazaki shiga ki tub'e kayan ba to maza ki Fita na baki daga yanzu zuwa faduwar Rana ki kawo mun Mijin aure gidan nan in aurad dake Juma'a mai Zuwa in ba haka ba tashin hankali yanzu kika fara ganinsa ! Yusuf kuma tun wuri ki Fara ciresa aranki don ko kina mutuwa kina tashiwa ne aure bazai tab'a yuwuwa atsakaninku ba, da inga aurenki da Yusuf gwara akawomun gawarki ta dalilin mummunar hatsari, Ki fita kamanninki har ma ba'a iya ganeki ......"
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun Ya Allah wannan wani irin Masifa ne ! Ya Allah kadau raina in huta da irin tashin hankalin da nake gani ? babu abunda yafi tab'a Zuciya kamar kaga Uwar data tsugunna ta haifeka tana kwashe maka albarka da kuma maka muguwar addu'ar karewa awulak'ance...." Kuka yaci mugun K'arfina...
Addah tana cigaba da Shanyanta tace"ai baki ga komai ba Rahama! muguwar addu'a yanzu na fara miki shi har sai kin cire wannan haramtacciyar soyayyar da kikewa k'anin mahaifinki Azuciyarki, Sannan ki Fitar da miji ko shine Fir'aunan Tantirai babu abunda ya dameni burina inganki agidan aurenki Rahama kafin in kwanta hannun dama karkisa Duniya tamun dariya, kodayake dariyar harna nawa ? an dad'e ana min shi ab'oye na Fili kawai ya rage
To ki sani Zuciyata bazata juri ganin hakoransu akaina Afili ba, Ki taimaka in samu in aurad dake in ba so kike ki kare awulak'ance ba Rahamatu..."
"Papa kana jinta ko ? Kasa baki in ba so kake in fara tunanin ko kai d'in ba mahaifina bane "
abun mamak'i sa kai kawai naga yayi kamar badashi nake magana ba yayi hanyar Waje .
Adaidai Lokacin kuma mukaji ana buga kofar gida, da sauri Papa ya karasa ya bud'e.
Idanunsa ne ya sauka akan Fuskar Umar Wanda yasha takunkuni (Face mask). Tunda tsantsin tiyils ya kwasheshi ya maka akasa har ya kumburar masa da baki tun aranar ya koma amfani da takunkuni don b'oye halittarsa data canza. Duk da dai ayanzu kumburin yana d'an sacewa amma still bai bar amfani dashi ba.
Tsab! Papa ya shaidashi, Nan take Wani irin muguwar tsanarsa dake kwance akasan ransa ya taso masa, ko kafin yakai ga magana Tuni Umar d'in ya duka dan munafirci yana gaisheshi wai shi nan yaga siriki abunda bai tab'a yi kenan ba tsawon zamarsa a unguwan, haka zai wuce babban mutum ko uffan bazai ce masa ba, amma ayau shine har da tsugunnawa har kasa yana gaidashi.
Papa bai amsa gaisuwar ba yace"Meya kawoka gidana ko ince me kazo daukawa ? dan a iya sanina babu abunda ya tab'a hadani dakai kuma insha Allahu ina rok'on Allah kar ya kawo sanadin abunda zai sa mu shiga gonar juna " Murmushin yak'e yayi yana mai fesar da iska cikin takunkuninsa.
Yace"Baba dama magana ne nazo muyi akan 'yarka Rahama, Nasan abunda nayi ban k'yauta ba, kun bawa 'yar ku tarbiya sannan ni kuma nazo kawai daga sama na rusashi, tun farko naso aurenta ne amma sai ta nunamin bazata iya aurena ba sabida alakar dake tsakaninta da Matata Ubaida, babu yadda banyi dan in shawo kanta ba amma taki bani hadin kai muyi aure, ba'a san ranmu ba muka fad'a kazamar rayuwa kuma har ga Allah ban san ina Ubaida ta samo labarin muamalar da mukeyi asirrance har tazo gidanku taci muku mutunci ba, Shine naga dacewar inzo in baku hakuri kuma wallahi in har zaku bani ita ina kan bakana har yanzu nason aurenta tunda nine na b'ata mata Rayuwa " Da sauri papa ya katseshi "kaga wannan maganar bada ni zaka yita ba, ka sami mahaifiyarta....."
daga bayansa yaji ta tsoma musu baki dan tana ganin Papa ya bud'e kofa ta matso don azatonta Yusuf ne ta karta masa rashin mutuncin da har yakoma ga mahaliccinsa baze tab'a mantata ba.
Sai kuma taga sabanin hakan, arba tayi da k'wayar idanun Umar, afarko bata shaidashi ba sai data gama sauraron bayanin da yike wa Papa.
"Abdulmalik dama ni bani da bukatar kasa baki acikin lamarin Rahama, ka cire kanka aciki babu abunda ya shafeka! Kai kuma dan guntsun uwarka dama nemanka nake inci uban daya haifi kakanka na goma sha daya dan iska mayaudari me lalata wa mutane tarbiyan yara " Ta furta da zafi gami da hankad'e Papa gefe ta cakumo kwalar rigar Umar ya fad'o cikin gidan.
Sosai hankalin papa ya tashi haka kuma Ransa yai mugun baci, besan sadda ya daga hannu ya kifa mata wawan mari yana fidda huci ba.
"Halima na gaji da wannan sabbin halayen da kike shimfid'amun agida, shin meya tab'a k'wak'walwarki ne ? Rashin auren 'yarki akan lokaci is the the end of the world ? meyasa bazaki sarara mata ba ? kuma meyasa bazakiyi bincike kafin ki yanke hukunci ba ? ke dayakamata ace kinfi kowa sanin abunda 'yar taki zata iya aikatawa da wanda bazata iya ba amma kece mutum ta Farko daya nuna zargi akanta. Shin ke kin fi Allah wayau ne ko kin fishi sanin abunda ya dace ne da har kike neman aurad da ita ta karfi da yaji har kina ikrarin kowani irin miji ne ta kawo babu abunda ya dameki ? Halimatu Sadiya ki Zauna ki sake Tunani kar kizo ki aikata abunda zai saki cizon dan yatsa nan gaba
Sannan gwara kibi bawan Allahn nan asannu ku wanye lafiya in ba haka ba dab kike da tarawa kanki jama'a kuma kece da kunya bashi ba "
Yana gama Fad'in hakan ya rab'a gefensu ya Fice, awaje yaci karo da Yusuf wanda kana ganinsa kasan hankalinsa ba'a kwance yike ba. yana zaune gaban motarsa yana jiran Fitowar papa da yike sanda ya karaso ya kirashi awaya yace yana waje zai jirashi bazai iya shigowa ba.
Rufeshi da fad'a papa yayi
"akan me Zaka k'i shigowa sabida kun sami sabani da Halima ? Shin gidanta ko gidana ? Zamana takeyi dan haka bata da ikon hanaka zuwa gidan dan'uwanka aduk sanda kaso, ka sani ita ina iya rabuwa da ita kuma in musanya da wata innaso amma kai fa ?
dan'uwana ne wanda bazan tab'a iya musanyashi da Wani ba, Ka tashi ka shiga mota mu tafi ka fara ajjeni lokaci na kurewa "
Jiki asanyaye Yusuf ya diro daga saman motar idanunsa sun cicciko da hawaye, hankici ya zaro daga aljihunsa ya cire gilashi ya goge sannan ya mayar ya makale, har kasa ya duka yana gaida yayan nasa kana ya shige mota suka bar wurin.
*ADDAH*
Ranta ne yayi bakikirin da abunda papa yayi mata agaban idon Umar, Sakin k'walar rigarsa tayi da k'arfi gami da tureshi yayi taga taga Zai fadi da sauri ya mik'a hannu ya dafe gate yana tasbihi ga Allah.
Ido ya zuba mata ganin ta juya da gudu ta nufi Rahama inda nake tsaye gani dai kamar mutum mutumi.
Finciko hannuna tayi da wani irin mugun karfi ta shiga jana Zuwa inda Umar yake, Fashewa da sabon kuka nayi ina ji inama Allah ya dau raina nan take in huta da wannan masifar.
bata tsaya ko'ina ba sai gabansa ta wurgani nayi tangal tangal Zan fad'i akansa, shi kuma abun haushi ya bud'e hannaye yana shirin in fad'o jikinsa inda yake nan aduk'e.
Fadawa nayi jikin nasa abun ya min ciwo sosai na kwaci kaina na mik'e tsaye ina zabga masa hararar tsana kan na mayar da kallona kan sabuwar mahaifiyata datayi wannan danyar aikin.
Cike da masifa take fadin
"Bazan tsaya wani cin Zarafinka akan batamun 'ya da kayi ba dan hakan baya Faruwa sai da had'in kan Juna Tunda na tabbata ba dole kake mata ba, amma inso ka sani in har da gaske d'in kake kamar yadda naji kana fada cewa dama kana da kudirin aurenta itace ta k'i ka, To inaso ranar Juma'a kazo da sadakinka adaura muku aure Mun yafe komai kai dai kawai kazo da sadakin dan Sadaki shine auren, kazo zan nemi malami ya daura muku aure ana sakkowa juma'a "
Kansa akasa yace"Insha Allahu Mama zan taho da tawagata in an sakko juma'ar da kuma Sadakin nawa ..."
"Ni bance ka Taho da wani tawaga ba! Sadaki da kai kanka kawai nake da bukata sai kuma waliyyinka, in kuma ka kawosu Ruwanka ne bukatata kawai inga an daura muku aure in huta da ganin kayan Takaici agabana, kuma kar in sake jin ka kirani da Mama ni ba Mamanka bace ban haifi dan iska ba..." Tana gama fadin haka ta juya tabar wurin duk muka bita da Kallo. Zagin data masa yadan tab'ashi amma kawai ya fuske tunda shi ke neman abu awajenta dole ya kwantar dakai ya kuma bi asannu.
Cike da Tsana na maida kallona gareshi nace"Umar me na muku kaida matarka da kuke neman ganin bayana ne haka ? rannan kayiwa zancena mummunar fahimta kace ina tallata kaina ne agareka da wayau har kasa matarka taci Zarafina, hakan be isheku ba ta sake wanko kafa tazo har cikin gidanmu ta kulla mun sharrin ina bibiyarka awaje wai har ma na tab'a Zubar da cikinka...Umar wallahi bazan tab'a yafe muku ba Allah ya isa tsakanina daku kuma wallahi ka janye batun aurena dakai don na rantse da sarkin daya busamin numfashi ko kai daya ne namijin daya rage aduniya bazan tab'a aurenka ba gwara na koma ga mahaliccina ahakan babu auren! in kuma ka sake aka daura mana auren nan to nayi alkawarin hana muku kwanciyar hankali daga kai har dabbar matarka...."
ina gama fadin haka na juya afusace nayi cikin gidan. Umar kuma bin mazaunanta da ido yayi yana hadiyar wani irin yawu na feelings, Wani irin fitinannen shaawarta ne ya taso masa......da sauri ya kama kansa ya fice daga gidan daqyar yana mai farin ciki da komai yazo masa asaukak'e ba tare dayasha wahala ba. infact be ma kai ga kunna record na makircin da suka shirya shida shama ba, muryar Rahama tayi inda take gaya masa cewa ai tana dauke da cikinsa ya za'ayi ?
makirci dai suka shirya da Shama, amma cikin ikon Allah besa su Addah sun kai ga saurara ba.
Yana Fita ya kira Zali awaya tana dagawa yace"Ki fasa zuwa gidana komai yazo mana asaukake fiye de zatonmu, zanzo har inda kike da albishir me dadi."
washe haqora tayi tana fadin"Allah ko Namijin duniya ? to ina jiranka kayi sauri Fita zanyi."
kit ta katse wayar.
amaimakon yayi ofis Kai tsaye gidanta ya nufa inda take zaman kanta, So yake kawai su fara tsare tsaren yadda aurensa da Rahama zai kasance nan da kwanak'i uku kacal da aka dibar masa, akuma cikin kwanaki ukun zai tabbata yayi mata mahaukatan kayan lefe ta yadda zai gogewa mahaifiyarta Laifin da take tunanin yayi mata.
YUSUF
Ahankali yake Tuk'i amma sam hankalinsa ba'a jikinsa yake ba, ikon Allah ne kawai ya tsaresu har suka iso ofishin Papa, amaimakon papa ya bud'e kofa ya Fita sai dad'a gyara zamansa yayi ya kirayi sunansa ahankali "YUSUF..."
"Na'am yaya..."
ya amsa kansa akasa ayayin da gabansa ke bugawa da sauri da sauri.
"Yusuf tambayarka nake son inyi, wai da gaske ne abunda naji Halima tana fad'a cewa son d'iyarka Rahama kake ? ka Fahimceni ba irin son da d'a yake yiwa abunda ya haifa nake nufi ba, So wanda zaka ji kana son ka mallaki wannan abun, So wanda kake Fatar ku kasance a inuwar aure! hakane Yusuf ?"
Papa ya furta cike da tashin hankali don be masan zancen da yike zazzarowa ba.
an kwashi dakik'u sama da talatin Yusuf na Fesar da huci, da alamun rasa ta inda ma zai Fara magana yayi.
Sai hawaye masu Zafi sosai ne kawai ke kwaranyo masa Zuciyarsa na kuna kamar zata fasa k'irjinsa ta bayyana awaje.....