Free chapter · Read without an account

Page 7

by Rahma Kabir · ABIN DA CIWO

*ABIN DA CIWO*


Na

©Rahma Kabir MrsMG.

Wattpad @rahmakabir


Page 7.


Ikram da ta dawo kitchen ɗin ta cewa Jamila taje ta gyara falo inji Anty Sameeha saboda gobe ba za shi sharaba sai zuwa yamma in baƙi sun tafi, Jamila ta miƙe ta fita Ikram ta zauna suka cigaba da aikin suna hira da Najwa, har suka gama suka a dana komai kafin suka fito Jamila ta soma gyaransa. Suna zaune a falo sai ga Anty Sameeha ta fito cikin doguwar rigar material da hula akanta, ta zauna a cushing tana cewa.


Ikram yanzu na gama waya da Aminu yace in kulle ɗakina dana rana kar na bari a shiga ayi mana barna, dama bana gaya miki haka zanyi ba to shima yanzu ya gama faɗa mini, dan haka ku shirya da wuri ku ɗauki duk abinda kuke buƙata ku kai shi ɗakin Jamila dan a can zamu tare, shima key ɗinsa yana hannunna koda zaku ɗauki abu sai ku faɗa mini.


Gaskiya gwara ayi haka dan bamu san mutanen da zamu zo ba Anty, tunda wannan ne karo na farkon taro da za kiyi a gidan, sannan ma a farfajiya za ayi walimar.


Cewar Ikram Sameeha tace.


Sosai ma ni da ban san ya halinsu yake ba gwara in yi wa abin tufkar hanci a rabu lafiya da kowa, ni wlh na ƙosa ma ayi a gama na huta.


Ai Anty kunyi ƙoƙari a wannan marra da muke ciki zaku yi shagali ba biki ba suna ba, kawai dan kun dawo kaduna ne fa.


To Najwa Aminu yace za a yi haka shiyasa nima na mara masa baya, gwara ayi ɗin a sada zumunci dan da yawan 'yan uwansu ma ban sansu ba.


Cewar Sameeha sai ta cigaba da yi musu bayanin yadda take so su saka mata ido a gidan dan ita ba lallai ta samu damar yin haka ba saboda tarban mutane. Sai da aka kira sallamar magrib kafin suka miƙe kowa wanne ya nufi ɗaki domin yin salla. Jamila tana ɗakinta zaune tana huta gajiyar aiki data kwasa, sai kira ya shigo wayarta ta duba taga Hauwa ce sai ta mike ta zo ta rufe ƙofarta da key ta ciki ta koma ta zauna a bakin gado ta ɗauki wayar da sauri dan ta kusa tsinkewa.


Jamila meke wakana a gidan?


Jamila ta shiga karanto mata shirye shiryensu tana cewa.


Hajiya ai wlh na ci nama sosai wata 'yar uwar Anty Sameeha ta ce na ɗiba na ɓoye saboda tasan anty da baƙar rowa, itama sai zaginta take da alama 'yan uwanta suma basa jin daɗinta.


Hmmm ba mamaki suma ba mutunta su take yi ba, In Sha Allah da wuri ma zan zo gidan.


Daga haka suka yi sallama, a lokacin ne aka shiga buga ƙofar Jamila, a zabure ta miƙe tana dafe kirji da fargaban Allah yasa ba a ji wayarta ba, ta isa ƙofar ta buɗe sai taga Najwa ce ta saki dariyar yake tana cewa.


Amty ashe kece?


Sunana Najwa dan ban kai matsayin anty ba.


Amma ai Ikram cewa ta yi itama anty ce karna ƙara kiran sunanta, kedai kina da mutunci sam ba ruwanki da girman kai.


Halinsu guda da Sameeha ai, ga kayana zan ɓoye anan saboda gobe rufa ɗakuna zadu yi wai kar ayi musu sata.


Innalillahi... yanzu zargin mutane take yi da zasu yi musu sata, to in hakane sai ta fasa yin taron.


Ke ni bar wannan zancen dan ƙona mini rai yake, bani wayarki na saka miki number ta.


Jikin Jamila na rawa da zumuɗi ta miƙa mata wayar, Najwa ta amsa ta saka number ɗinta ta yi filashin sai ta yi mata saving da Anty N ta nuna mata.


Kinga sunan dana aje a wayarki sai ki riƙe da kin ga haka inna kira to ni ce.


To nagode, kuma ina jin daɗin yadda kike kulani, wlh tunda na zo gidan nan rayuwa nake kamar marainiya, Allah yasa zaki jima baki tafi ba.


Wa! Taf a gobe In Sha Allah zan tafi ba zan zauna ba ana yi mini wani gani gani ba da kafa mini dokar da ba zan iya bi ba.


Tana gama faɗar haka ta juya ta fice bayan ta adana kayanta a ɗakin, da kallo Jamila ta fita tana mamakin halin Najwa yadda take da kirki da sauƙin kai, nan take ta yiwa Hauwa flashing ba jimawa ta kirata sai take shaida mata Sameeha zata rufe ɗakunanta dan kai'r su zo suyi mata sata har da karin gishirinta, Hauwa kuwa ta mulmulo wani ashar ta kashe wayar cike da takaici da irin matakin da zata ɗauka in sun zo ta hanasu shiga ɗakunan, dan dama da burin haka a zuciyarsu saboda basu san kalar ɗakunan ba. Najwa kuwa da ta fita falo ta amsa wayar Ikram da sunan zata tura app saboda ba tada abubuwa a wayarta, data gama ta mika mata tana duban anty Sameeha tace cikin karya wuya da marairaicewa.


Anty dan Allah ki bani wayarki na tura abubuwa kinga wayar tawa ba wasu abu saboda sabowa ce sai nayi mata lodi.


Najwa nifa wayata bata zuwa hannun kowa saboda ban gama sanin kanta ba tunda Abban Amrah ya siya mini, ko su Abi sai dai su ɗauki tsohuwar tawa.


Kai anty xender kawai zan shiga na tura app.


Sameeha bata kuma magana ba ta cire mata key ta miƙa mata, Najwa ta amsa ta shiga xender ta duba inda hotuna suke, sai taci karo da hotunan Aminu dama wanda suka ɗauka tare da Sameeha, wasu cikin kayan barci wasu kuma cikin shiga mai kyau, nan ta shiga turawa iya son ranta, kana ta koma app ta tura sai ta shiga In da ta yiwa kanta sending ta goge hutunan data tura dan kar Sameeha ta ganota, sai ta fita a xender ta shiga contact sai dai duk dubawan data yi bata ga sunan Aminu ba sai ta shiga wajen dailing call nan taga ansa Hasken Meeha, tana ƙoƙarin duba number ɗin ta ɗauka sai kira ya shigo wayar, da sauri ta fita daga gurin da ta shiga ta miƙa mata wayar, Sameeha ta amsa taga umma ce sai ta miƙe ta wuce ɗakinta tana amsa kiran, Najwa ba ƙaramin haushi taji ba wato rijiya ta bada ruwa amma guga ta hana, sai dai kuma hotunan Aminu data tura a wayarta zai rage mata damuwar da take ciki na rashin ganinsa a nan kusa, ta sauke ajiyar zuciya ta miƙe tana cewa Ikram ita zata kwanta sai da safe, Ikram ta yi mata addu'ar a tashi lafiya sai ta wuce ɗakin Amrah ta shiga ta kwanta a gefe dan Amrah tuni tayi barci. Rigingine ta kwanta ta shiga inda hotuna suke ta soma kallon hotunan data tura, wanda yake tare da Sameeha sai taji wani ƙululun baƙin ciki ya tokareta kamar ta mayar da gurbin Sameeha da nata hoton, ji take kamar ta samu wuƙa ta sokawa hoton Sameeha ko zata samu sassaucin kishin da take ji a zuciyarta, ganin ba zara daure ba yasa ta goge hotunan da yake tare da Sameeha ta bar nashi shi kaɗai da wanda ya ɗauka da yara, ta ɓata lokaci mai tsayi tana ƙarewa Hotunan Amimu kallo wanda hakan ƙara tunzura soyayyarsa take yi a zuciyarta tana jin idan bata sameshi ba mutuwa kawai zata yi, zata yi duk abinda ya dace dan ta mallakeshi a matsayin mijinta, sosai shaiɗan ya cigaba da ƙawata mata shi a zuciya wanda take ganin itace ma kaɗai ta dace da shi da gidan gabaɗaya ba Saneeha ba, text ɗin Nafeesa ya shigo wayar akan ta hau online, da sauri ta kunna datarta ta duba Nafeesa sai taga tana kai, dan haka ta tura mata hoton Aminu guda ɗaya wanda yake sanye da ƙananun kaya, Nafeesa tana buɗewa sai ta turo da imoji mai zare ido tana cewa.


Ba dai wannan bane Aminun.


Wlh ƙawata shine, yanzu na turasu a wayar Sameeha.


Amma gayen nan ya yi fitinannen Haɗuwa ƙawata, dole ki rikice domin ni kaina ya burgeni, dan haka wlh ki riƙe wuta ki sameshi dan kunyi matuƙar dacewa da shi.


Hmmm ina nan zuciyata kamar ta faso ƙirjina saboda sonshi dake bugawa, wutar sonshi ruruwa yake kamar zai tarwatsa zuciyata, Nafeesa numfashina har waji ɗaukewa yake ya dawo in na tuna shi, ki gaya min ya zanyi na aure shi a yanzu ina jin zan iya yin komai, ina nufin mai zan aikata in dai zai zama nawa, ban damu da duk wani abu da zai biyo baya ba, ni dai na same shi kawai.


Ki kwantar da hankalinki ki saka a ranki kin same shi kin gama, kedai ki kama kafa da 'yar uwarsa Hauwa, na tabbatar zaki samu saukakkiyar hanyar samunsa, kuma ki dage da addua sosai nima zan taya ki, kuma ranar lahadi kiyi ƙoƙari ki zo makaranta akwai maganar da zamu yi.


Najwa tace mata to kana suka cigaba da hirarsu, tana kallon maganar Zaidu amma taƙi kulashi dan yanzu bata shi take ba, gani take koda a ƙafa aka ɗaura mata shi ba zata iya ja ba dan tafi ƙarfin ajinsa, yanzu ne take ƙara kallon kanta a matar babban mutum ita ba matar yara bane ko talakan da bai iya ciyar da kansa ba balle yace zai kula sa ita.


****


Washe gari.


Da wuri suka gama shiryawa suka tanadi komai da suke buƙata suka saka a ɗakin da Jamila ke ciki, Sameeha ta kulle ko ina ta saka key ɗin a ƙaramar fos ɗinta sai ta bawa Ikram ta saka a ƙaramar jakarta ta rataya a kafaɗa, wurin takwas da wani abu mutane suka fara zuwa dan duk danginsu Aminu ne ciki har da Hauwa ta zube akan carpet ɗin falo tana matsa ƙafarta dan a ƙafa ta tako wai ta motsa jiki, Sameeha ta zauna tana yi mata sannu suka gaisa kana Hauwa tace


Me da me kuka tsara ne.?


Sameeha ta sanar da ita abincin da ta bayar ayi da bayanin komai daya dace ta faɗa mata, sai ta ɗaura da cewa.


In kin huta sai muje kitchen na nuna miki naman kajin da muka soya ki cire naku dan kar azo ayi ta rabowa mutane ya ƙare.


Aiko kinyi kyan kai mu je na gani dan ba wani hutu zanyi ba yau ba zama an saci ɗan barawo, ta miƙe suka wuce kitchen, Sameeha ta nuna mata ta samu guri ta raba kajin biyu sai ta juye a leda mai zane zane tana cewa.


Wannan yayi mana, sauren kya bawa baƙi.


To Sameeha tace mata amma har zuciyarta bata ji daɗi ba tunda anyi abu dan mutane ne amma ta kwashe rabi, sai ta adana sauran, Yaya Hauwa ta ce.


Buɗe mini ɗakinki na ɓoye shi sai zamu tafi na amsa.


Yaya na ɗauka na ɓangaren mutane ku ne kike ɗiba ko da sun zo ki saka musu a abincin.


A'a wannan namu ne na gida in mun je babban gida zamu raba.


To shikenan kawo in aje miki a ɗakin Jamila dan key ɗin ɗakina baya hannuna.


Ina kika kai keyy ɗin? ki amso mana ki buɗe ki saka mini a ciki.


Key ɗin yayi nisa gaskiya.


Sameeha kina nufin ba zaki nuna mana ɗakin muga yadda yake bane ko me?


Ba haka nake nufi ba, na dai rufe su ne saboda kar a samu matsala.


Saboda kun tara ɓarayi ba a gidan dole zaki ce haka, Allah dai ya kyauta miki, da kin san hakane da baku shirya walimar ba kowa ta zauna a gidansa tunda baki yarda da mutane ba.


Hauwa ta faɗa cikin ɗaure fuska, Sameeha bata ce mata komai ba tayi waje cike da damuwa dan bata so suyi abinda bai dace ba yasa ta fita bata bata amsa ba, A lokacin Najwa ta shigo tana kallon yaya Hauwa da fuskarta a ɗaure, Najwa ta matsa gabda ita tana cewa a hankali.


Yaya iya abinda tabaku kenan? Wlh ta ɓoye wani ba iyakar yawan kazar ba kenan. Hmmm anty Sameeha ta bani da rowa.


In dai ita ce zata aika, tunda ba ƙaunarmu take ba.


To wai ma kinji me tace, rufe ɗakinta zata yi kar ayi mata sata, hatta ni da nake 'yar uwarta wlh fitar mini da kayana tayi daga ɗakin ta kaishi ɗakin 'yar aiki, sam bata so a raɓeta kamar ita kaɗai ce mai arzikin duniya, ni badan innata ta takura mini ba wlh da ban zo ba.


Lallai ta cika butulu tunda har ta iya yiwa 'yan uwanta, mu ma ba zamu sha ba. Ya sunanki 'yan mata.?


Najwa sunana, jiya na zo amma sai wani shan ƙamshi take yi kamar bata so zuwana ba, 'yan uwanmu da yawa sunce ba abinda zasu zo suyi a gidan dan karta wulaƙanta su saboda in tazo garin nan bata zuwa gidan kowa sai ɗakin umma take maƙalewa. 


Ashe haka take? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun gaskiya Allah ya wadaran halinta wannan ba matar aure ba.


Allah yaya Hauwa ku saka shi ya ƙara aure kawai domin kuma a dama daku a gidan ɗan uwanku in kun zo ba ruwanku da ita. Jiya ina ji tana magana da Ikram akan irin tanadin rashin mutunci data yi muku idan kuka nima shigo gonarta.


Hmmmmm Hauwa tace tana cije gefen lebenta tare da ƙanƙance ido ɗaya tana girgiza kai.



*Zaku jini shuru a kwana biyu saboda muna da biki sai mun kammala da yardan Allah zaku jini. Ina godiya da addu'arku da kuma soyayyar ku garemu Allah ya saka da alkhairi ya bar kauna. Rahmarku ce*


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.