Free chapter · Read without an account
Capter 5-6:Damuwa
*HAFSATUL-KIRAM*
©Mai Ƙosai
Shafi Na Biyar Da Na Shida
Masu cewa typing ya yi kaɗan ku ma ai comment ya yi kaɗan, idan kuna so ku ƙara yawan comment sai na ƙara muku kaɗan.
Ba a fara komai ba ma, idan za ku ɗaura ɗamara tam.
Durƙushewa ta yi tana toshe kunnuwanta da hannayenta biyu, yayin da Afna ta durƙushe ƙasa ita ma tana ƙoƙarin tallafa mata.
"Ki je Afna, ki je ki kwanta kawai."
"Aunty ke fa? Kin ga halin da kike ciki kuwa? Ba zan iya tafiya na barki ke kaɗai ba aunty."
"Ki je kawai Afna" Ta yi maganar a tsawace. Babu shiri Afna ta miƙe tsaye, ta soma tattakawa don barin ɗakin, daf da bakin ƙofa ta ja tunga ta tsaya,
"Ki daure ki runtsa aunty." Daga haka ta juyawa ɗakin baya.
Ta jima a durƙushe, kafin ta yi zaman dirshen, hannunta ta miƙa saman kanta ta shiga yamutsa gashin kanta tana mai cizar fatar leɓen ƙasan bakinta. Duk yadda take so ta kawar da abin da ke mintsinar zuciyarta ta kasa, miƙa hannunta ta yi jikin lokar da ke kusa da gadon ta buɗe tare da janyo wata kwalba, ɓalle murfin kwalbar ta yi ta zazzago magani, ɗaya ta ɗauka ta afa a bakinta tare da korawa da ruwa, cikin abin da bai fi mintuna ba ta soma ajjiyar zuciya idanunta suka soma lulluɓewa ta silale ƙasa.
Sanyayyiyar iskar da ke kaɗawa ta asuba ce ta farkar da ita, kallon ɗakin take yi kamar yanzu ta soma ganinsa, da hanzari ta miƙe tana tallafar kanta, tare da mitsittsike idanuwanta.
"Ya salam!" Ta furta, tana mai miƙewa tare da faɗawa bayi. Wanka ta yi, tare da ɗauro alawa kana ta fito. Dadduma ta shimfiɗa ta shiga gabatar da salla, ko da ta idar zaune ta yi kan sallayar ba ta motsa ba, har gari ya gama wayewa. Jefi-jefi take jin kanta na sarawa ga kukan yunwar da 'yan hanjin cikinta ke yi mata sai dai bata jin za ta iya sanya komai a cikin. Jin ƙarar buɗe ƙofa ya sata kallon wanda ya shigo, Afna ce cikin shiga ta kayan makaranta.
"Kar dai ba ki runtsa ba aunty, na ga ba ki tashi da wuri ba don na ga hakan ta hanyar ganinki zaune kan sallaya?"
Ba ta amsa mata, ta miƙe ta hau nunke sallayar, ma'adanar ajjiyar kayanta ta buɗe ta zaro kayan da za ta sanya ta shiga kimtsa kanta, kafin ta ɗau mikullin motarta tare da saɓar rigar lauya da jakarta ta fice daga ɗakin. Ganin haka ya sa Afna take mata baya.
Ba ta ganta wajen motar ba, hakan ya tabbatar mata da je wajen kaka, kai tsaye ɓangaren kaka ta nufa, sai dai kicibus suka yi da Hafsa.
"Wuce mu je, ba ki ga kin makara ba." Cewar Hafsa, Afna kuwa ba dan taso ba ta wuce simi-simi.
A hankali take tuƙa motar, bayan ta cillata kan saman kwalta. Karatun ƙur'ani ne ke tashi cikin ƙira'ar sheik Sudais, har suka isa bakin makarantarsu Afna babu wanda ya ce da wani kanzil.
"Don Allah ki rage damuwa aunty, damuwarki na jefa ni cikin tashin hankali." Faɗin Afna daf da take buɗe murfin motar, tana zirara ƙafafunta waje, bata jira amsar Hafsa ba ta fice tare da rufe motar. Ita kuwa Hafsa ta jima a haka, kafin ta iya murza mukullin ta tashi motar tana kokarin bawa waje fili. Allah Ya gani ita ma ba a san ranta abubuwa da dama suke faruwa ba, to yaya za ta yi ta sani tabon ƙasan zuciyarta ba zai taɓa gogowa ba. A haka ta ja motar ta bar wajen, tana tafe tana tufka da warwara har ta ƙarasa gidauniyar ta su.
"Yau dai kin makara Hafsa?"
Kallon mai maganar ta yi, tamkar ba zata ce wani abu can kuma ta ce,
"Saboda yau ɗaya kin riga ni zuwa ko Dija?"
"Allah ba haka ba ne, kema kin san ina ƙoƙari, da me zan ji da tarairayar mijina ko da rainon cikin da ke jikina."
Mitss! Ta ja wani siririn tsaki, kafin ta ce,
"Yana ɗaya daga cikin abin da ya sa aure baya gabana, don ba zan iya wahaltawa namiji ba ƙarshe ya zo ya sanya ni a kushewa don mugun baƙin halinsa."
"Ai ba duka aka taru aka zama ɗaya ba. Sau tari nakan gaya miki kowane ɗan adam da irin nasa halin. Ki yarda da ni Hafsa, ki bawa yaya damar da zai sake ingan..."
"Ya isa malama, kin san bana haka da ke bar ganin kin girmemin ai girman da kaɗan ne , bambancin ba shi da yawa kin san tamkar ƙanwata haka na ɗauke ki don haka ki sarara min. Idan ma ya aikoki ne don ki yi fadanci to ki koma ki sanar masa cewa jinsin baya gabana."
"Hm!" Dija ta sauke numfashi, tasan duk abin da za ta gaya mata a banza wai jefa agwagwa a ruwa. Don inda ace zata ɗauka ya ci a ce zuwa yanzu ta fuskanci abin da take sanar mata, ba ma haka ba ko iya zancen da Nisha ta mata ya wadatar ya sassauto da zuciyarta, amma ta lura su suke kiɗansu kuma suke rawarsu.
"Mijinki ya zo jiya, mun yi magana mai girma, sai dai ina so ki taka masa burki daga yanzu bana son sake ganin jinsinsa gabana, dujk abin da zai faru ki dinga ƙoƙarin sanar mini, idan babu hali ki bari duk randa muka haɗu kya faɗa min, kin san babu maza a lamarin nan, me ya sa kike son dagula min lissafi ne Dija?"
"Ba dagula miki lissafi nake son yi ba Hafsa, ina son tunasar da ke abin da kika manta. Kar ki manta Allah Ya halicci jinsin mace da namiji don su samu kyayyawar alaƙa da dangantaka da juna, ki kuma tuna da wannan haɗuwar jinsin ne ake samar da zuri'a, idan ba dan haka ba da muma ba mu wannan duniyar. Kar ki bari shaiɗan ya miki karatun kurma yadda za ki kasa ji balle ki gane abin da ake faɗa miki."
'Aikinki ke nan, kullum magana ɗaya' ta yi maganar asan zuciyarta.
Yayin da ta yi mata banza, na'urar da ke ajjiye kan teburunta ta janyo, ta kunna tare da fara aiki a cikinta.
"Yaya za mu yi da yarinyar nan ne Hafsa?"
"Zan je na dubata, idan ta warke kuma zan dawo da ita gabana, sannan za mu tsaya mata kamar yadda muka saba."
"Ok hakanma ya yi, ni zan wuce wajen aikina, sai kin ƙaraso."
"Alright."
Tun bayan fitar Dija daga ofis ɗin take tufka da warwara, me ya sa abubuwa ba sa zuwar mata yadda take so? Yaushe ne za ta ji daɗin rayuwa? Ta sani farinciki ɗaya ne gareta na samun ilimin da ta yi, amma sauran abubuwan suna nan tsaye cak kamar bishiyar da aka dasa.
Ji ta yi komai ya tsaya mata cak, bata jin zata iya ci gaba da aikin da take yi, hakan ya bata damar tattara duk komatsanta ta fice daga gidauniyar tasu. A hankali take tuƙa mota, daidai titin da zai sadata da layinsu ta hango wata budurwar yarinya zaune kan wani dakali, gabanta farantin gyaɗa ne, sai wasu maza su biyo sai faman tsokanarta suke yi suna kai mata cafka, ɗayan ma har da shafa fuskarta yana dariya, yayin da itama take washe musu haƙora tamkar mai tallan makilin. Wani takaici ne ya daki zuciyarta, ashe har yanzu ana samun yara irin waɗannan wanda iyayensu suka gaza ɗaukar ɗawainiyarsu su ke ɗora musu talla ba tare da sanin yadda rayuwarsu zata ɗore ba. Ba ta san lokacin da ta yi paking ɗin motarta ba ta fito a fusace ta nufi wajen. Daidai ɗayan ya ɗaga hannu zai kai saman ƙirjin yarinyar, kasancewar waje ne da mutane ba su cika wuce wa ba sai jefi-jefi.
Caraf ta damƙe hannun nasa, tana cizar laɓen ƙasan bakinta. Wani kallo yake bin ta da shi, cikin rashin kunya da murya irin ta 'yan yau ya ce,
"Yaya aka yi lady?"
Tass! Ta wanke fuskarsa da kyakkyawan mari, tana mai frurzar da huci daga bakinta. Kan ya sake magana ta ɗaga masa hannu tare da faɗin,
"Idan aka yi wa 'yarka, mahaifiyarka ko ƙanwarka za ka ƙyale wanda ya yi? Na ce za ka ƙyale wanda ya yi? Ina cewa ba sai inda ƙarfinka ya tsaya ba? Me ya sa kuke yi wa mata kallon rashin arziƙi? Ba mace ce ta kawo ka duniya ba? Me ya sa ba zaka daraja mace ba."
Ta ɗan numfasa, tana mai kallon yarinyar.
"Ke kuma ba ki san darajar kanki ba ne ko me? Da kika zauna wani ɗan iskan namiji na taɓa halittarki? Shin ke ba mace ce mai daraja ba?"
Tuni idanun yarinyar ya kawo ruwa, ta shiga neman afuwar Hafsa.
"Don Allah ki yi haƙuri wallahi ni ma ba a son raina ba ne, ki gafarce ni don Allah"
"Ba a son ranki ba? Ba a son ranki ba kika ce fa? Kina da hankali kuwa? Kin san me kike faɗa min?"
"Da gaske nake, ba ni da hujjar da zan miki ƙarya ki yarda da ni." Cewar yarinyar.
"Amma kina da hujjar da za ki bari ƙaton gardi ya dinga wasan banza da ke, yana ɗora miki ƙazamin hannunsa kan surar jikinki ko?" Faɗin Hafsa a matuƙar zafafe.
"Ku kuma, idan na sake haɗuwa da ku da irin wannan baƙin halin, na rantse ba zan ƙyale ku ba sai kun ƙare rayuwarku cikin gidan yari. Ku ɓace min daga gani. Ke kuma wuce mu je." Ta ƙare maganar tana yi wa yarinyar umarni da ta shiga mota. Babu musu yarinyar ta bi umarninta, don ita yanayin Hafsan tsoro ya soma bata. A guje ta figi motar ta bar wajen.
"Fito mu je." Ta yi furucin sa'ilin da ta gama daidaita tsayuwar motarta. Sashinta ta nufa da yarinya, wani ɗaki daban ta nuna mata ta ce ta shiga, bayan sun shiga ta nuna mata bayi ta shiga ta yi alwala ta zo ta yi salla tun da lokacin la'asar ya yi, sai dai ga mamakinta ganin yarinyar ta yi tana yin alwala wata iriya, hatta da sallar ma bata iya ba, abun ya ɗaure mata kai, sai dai bata ce mata komai ba ta fice daga ɗakin zuwa nata ɗakin don kimtsawa.
Tsawon mintuna masu ɗan yawa ta shafe kafin ta kammala abin da za ta yi, gefen gado ta samu ta zauna, tana mai ɗaukar wayarta da ke ta faman ruri.
"Assalamu alaikum" Ta yi sallama bayan ta amsa kiran.
"Wa'alaikumussalam. Besty kina lafiya, i call u so many times but u didnt pick"
Yamutsa baki ta yi, tamkar wacce ta yi arba da kashi, kafin ta ce,
"Abubuwane suka taru suka min yawa Nisha, ban san da wanne zan ji ba. Komai sake kwance min yake yi. Yaushe za ki dawo? Ina buƙatarki a kusa da ni."
"Ki ci gaba da haƙuri da sannu komai zai wuce. Zan ɗau wata biyu kafin dawowa ta, saboda ni ma nan na zo na tarar da wani al'amari mai girma."
"Me ya faru Nisha plz tell me"
"Mahaifina ne ya rasu Hafsa, and komai ya sake dagule min domin..."
Shiru ta yi tana sauke ajjiyar numfashi, ta kasa ƙarasawa.
"Sorry Allah Yana tare da ke na sha faɗa miki, duk abin da za ki yi kada ki karaya, ki yi ƙoƙarin saita al'amuranki da kanki Nisha"
Tana jiyo zuƙar majinar Nisha alamun kuka take yi mara sauti. Da ƙyar ta yi mata magana,
"Zan ƙoƙarta Hafsa, ina jin ƙwarin guiwata a lokacin da nake tare da ke."
"Shi ke nan ki daina kuka, ki ci gaba da addu'a kin ji ko. Za mu yi waya anjima ina da wani uzuri yanzu."
"Thank you so much besty. Ba ki tambayeni ɗanuwa ba"
"Ba na so Nisha, ba na son maganar na sha gaya miki ba tun yau ba, me ya sa kike da kafiya ne? Me ya sa kike da na ci Nisha. Idan ba kya ƙaunar ɓacin raina kar ki sake yi min wannan banzar maganar."
"Hmm!" Nisha a sauke numfashi kafin ta ce,
"Me ya sa kike ɓoye abin da ke ƙasan zuciyarki, so kike ki yi ta binne shi ne Hafsa? Na sani na san kina sonsa ki bawa zuciyarki dama kawai ta amshe..."
Kit Hafsa ta kashe wayar, huci take saukewa. Runtse idanuwanta ta yi tana jin wani abu na zagaye zuciyarta. A haka ta miƙe ta nufi ɗakin da yarinyar ke ciki. Zaune ta isketa gefenta farantin abinci ne wanda ta bada umarni akawo mata, da alama kuma ba ta taɓa ba.
"Ba kya jin yunwa ne?"
Girgiza kanta yarinyar ta yi alamar a'a.
"To me ya sa baki ci ba?"
"Na ƙoshi"
"Ƙarya kike yi, na ga hakan a cikin ƙwayar idanuwanki. Oya maza ki ɗauka ki cinye shi tas." Ta yi maganar tana haɗe rai tamkar magribar ɗinya.
Hannu na rawa yairinyar ta sa ta ɗau farantin ta soma cusa abincin, Allah Ya sani da man cike take da yunwa sosai don haka ta hau cinsa hannu baka hannu ƙwarya, sai da ta cinye tas.
"A ƙaro miki?" Hafsa ta watsa mata tambayar tana duban fuskarta.
"A'a na ƙoshi"
"Me ya sa kika zaɓi barin namiji yana taɓa ki bacin ba muharraminki ba ne?"
Jin tambayar Hafsan ta yi a bazata, hakan ya sata kallon fuskar Hafsan.
"Bana maimaita magana al'adata ce, na tambayeki ne ki faɗa min gaskiya kuma idan ba haka ba hm..." Ta ja numfashi, tana runtse idanuwanta.
Nan da nan yarinyar jikinta ya ɗau rawa, tsoro ya cika idanunta.
"Ke nake jira"
"Ki yi haƙuri bazan iya sanar da ke komai ba, kashe ni zata yi don Allah ki yi haƙuri."
"Ita wa? Wace zata kasheki? Ki sanar da ni komai yanzu"
"Mama, mamana ta ce indai na faɗi gaskiya sai ta kasheni ta huta da ganina."
Take Hafsa ta ji kanta na juyawa, jin maganar yarinyar ta yi wani iri, yayin da maganar ta fama mata wani gibi daga cikin giɓoɓin rayuwarta.
Domin sharhi, ko gyara: ***