Free chapter · Read without an account

Har abada

by Maryam Abdul'aziz · HAFSATUL-KIRAM

*HAFSATUL-KIRAM*


 ©Mai Ƙosai


Babi Na 17-18


'Ni ce ajalinka' Na tuna wasu kalamai nata, a game da baba.

   Tana fita daga ɗakin, na miƙa hannu tare da janye kwanon abincin daga gabansa. Tare da furta,

   "A'a baba, ba zan bari ba, sam ba za ka ci abincin nan ba"

  Baba ya kalle ni, cike da neman ƙarin bayani game da abin da na yi furucinsa a kai, kana ya ce,

   "Saboda me Hafsana?"

Na sake janyo kwanon ina mai ɗora shi saman cinyata tare da furta,

   "Saboda ta ce ita ce ajalinka. Baba ni kwata-kwata ban gamsu da abincin nan ba, sam hankalina bai kwanta da shi ba."

   Baba ya murmusa, gami da gyara zamansa har da tanƙwashe 'yan ƙafafuwansa kana ya ce,

   "Har abada Hafsana! Ki sani babu wanda ya isa ya ɗauki ran bawa sai dai Allah, wanda shi kaɗai ke kashewa da rayawa. Idan har kika ga na mutu to ajalina ne ya yi."

    Na numfasa ina mai sake ƙanƙame abincin cikin jikina tamkar zan mayar da shi cikina. Hawaye ya soma silalowa daga cikin kurmin idanuwana zuwa saman kumatuna, na soma girgiza masa kai.  

   'To ke Hafsa ba ta baki abincin nan kin ci ba wai? Idan har da guba a ciki to ai ke ce ta farko da za ki fara margayawa(mutuwa) kafin baba.' Na ji wani sashi na zuciyata yana ankarar da ni haka.

  'Idan kuma ba ta saka miki ciki ba, saboda daman ai ba ta ce za ta kawar da ke ba baba ta ce? Kada ki kuskura ki ba shi abincin nan domin zai iya zama ajalinsa!' Wani bigire ya ankatar da ni haka.


   Na miƙe tsaye zumbur! Tamkar wacca aka tsikara, hannuna ɗauke da kwanon na shiga girgiza wa baba kai.

  Baba ya miƙe ya kamo hannuna, ya zaunar da ni a inda na tashi.

   "A'a Hafsana! Zan ci abincin, kuma kisa a ranki babu abin da zai sami babanki da izinin Ubangiji"

   Ya janye kwanon da na garƙame jikina da ƙyar, sai ka ce mayen ƙarfen da ya shekara jikina. Ya buɗe murfin kwanon ya zura hannunsa ciki tare da ɗeɓo lomar abincin ya kai bakinsa tare da ambaton sunan Ubangiji.

  Ganin haka ya ba ni damar zurma hannuna cikin kwanon da sauri, tare da kwaso lomar abincin na kai bakina tare da bisimilla. A zuciyata ina jin cewar mu yi mutuwar kasko.

   "Ni dai koma mene ne mu yi mutuwar tare baba." Na ce cikin wata iriyar murya wacca muryar har rawa take yi tamkar ana buga mandiri.

  Baba bai ce mini komai ba, har sai da muka kammala cin abincin kana ya dube ni cike da zallar soyayya ya ce mini,

  "Ki na tsoron na mutu ne Hafsana ko?"

  Na yi saurin ɗaga masa kaina, domin ba shi amsar tambayar da ya mini.

  Ya jingina jikinsa da bango, yana ɗan ɗaga kansa sama kamar mai nazarin wani abun kafin daga bisa ni ya ce,

  "Tabbas zan mutu, ko ba daɗe ko ba jima, sai na mutu. Ki sani cewa mutuwa tana kan kowane bawa matsawar yana numfasawa. Ubangiji da kansa ya ke faɗa mana cewar, 'kowace rai sai ta ɗanɗani zaƙin mutuwa.' Kin ga kuwa ke nan kowane ɗan adam sai ya mutu. 

   Hafsana ki ɗauka idan na mutu kika wayi gari babu ni, to ajalina ne ya riske ni ba wai kashe ni aka yi ba, ki yi sani ya ke 'yata kowane abu da na sa lokacin, kamar: Mutuwa, aure, haihuwa duka suna da lokacinsu kuma idan lokacin ya yi tabbas ba makawa sai sun tabbata."

   "Ni dai ina matuƙar jin tsoro baba" Na ce masa.

  Bai ba ni amsa ba, sai ma miƙewa da ya yi yana mai faɗin,

   "Je ki yi alwala, magriba ta kawo kai."

   Ya sa kai yana mai ficewa daga ɗakin.

   Na ɗauke kwanon abincin da muka ci, jikina duk babu laka na shige madafa(kicin) na ajjiye shi, na dawo ina mai wanke hannu tare da ɗaura alwala kamar yadda baba ya umarce ni da yin haka.

   Ina cikin wanke ƙafafuwana Inna ta fito daga ɗakinta, tana mai miƙa alamar barci ta tashi daga shi. Ido huɗu muka yi da ita, ni dai na yi saurin yin ƙasa da kaina ita kuma ta wuce kicin.

  Na miƙe bayan na idar da alwalar na koma ɗakin baba na tayar da sallah kasancewar an soma kiran sallah a masallaci.

  Baba bai dawo ba, sai da aka yi sallar isha sannan ya shigo, lokacin har barci ya fara surata.

  Shigowarsa ta sanya shi tashina, na gyara shimfiɗata can nesa da shi na kwanta, ina ta saƙe-saƙe kafin bacci ya yi awon gaba da ni.


  Da safe bayan na tashi, na share gidan tas! Na wanke kwanukan da muka ɓata daren jiya. Inna na barci ba tasan wainar da ake toyawa ba.

   "Baba me zan dafa maka ka karya da shi?"

  Baba ya murmusa kana ya ce,

    "Innar ta ki, ta tashi ne?"

  Na girgiza masa kaina gami da furta,

    "A’a, ba ta tashi ba."

  "Je ki taso ta, sai ki ji me za a dafa sai ki ɗora ko?"

    "Na tashe ta kuma?"

Na watsa tambayar da sauri.

  "Ƙwarai kuwa! Ki je ki tashe ta, sai ki ɗora abin da ta ce. Kada ki damu babu abin da za ta yi miki Hafsana, ita ɗin fa uwa ce gareki."

   Ba na son yawan musa masa, wannan ya sa na yankewa zuciyata aikata abin da ya umarcenin akai, haka na shiga ɗakin da Inna ke ciki domin tadota kamar yadda ya ce da ni.

  Sai faman sharar barci take yi hankalinta kwance, wani gauron munshari na tashi.

  Na ƙarasa daidai ƙafarta na tsaya, na ranƙwafa na kai hannuna na taɓa ƙafar da niyar na tashe ta.

  Kamar jira take a taɓa ta, ai kuwa ta farka tare da zube idanunta cikin nawa, ta miƙe zaune tana mai haɗe fuska sai ka ce an mata aiki da mutuwa.

  Na ɗan sha jinin jikina har ina ɗan yin baya kaɗan.

  "Me ya kawo ki ɗakin nan?"

  Na soma in-ina, ina mai furta,

    "In..ba...baba ne ya ce na zo na taso ki, ki..."

Kalamai na suka tsinke sakamakon wata uwar harara da ta wurgo mini, har sai da na haɗiyi yawun da babu shiri.

   "Shi uban na ki ne ya ce ki zo ki tashe ni? Ta yi furucin, tana kafe ni da na mujiyarta.

    Ni dai duk na tsure na tsorata, don wallahi ni sam ko kaɗan ba na son masifar Inna firgita ni take yi.

   "Ki yi haƙuri" shi ne abin da na iya furta ma ta kawai.

   Ta ɗan yi jim! Kamar mai tuna wani abun, ganin ba ta da niyyar ce mini komai ya ba ni damar juyawa don komawa inda na fito.

   Har na isa bakin ƙofar ɗakin, na jiyo tashin muryarta na faɗin,

        "Dawo"

   Babu shiri na janyo 'yan matan ƙafafuwana na dawo tare da tiƙewa gabanta.

   "Je ki haɗa mini wuta, ki ɗora mini ruwan koko. Saura na fito na ga kin mini ba daidai ba."

   Ni dai amsawa na yi da, "To" ina mai ficewa daga ɗakin. Na ƙarasa gaban murhu na soma haɗa wutar kokon kamar yadda ta umarce ni zuciyata cike da mamakin sauyin Inna.

    Baba yana kishingiɗe yana jan casbaha(carbi), na shiga ɗakin bakina ɗauke da sallama.

   Baba ya ɗago yana mai bi na da kallo, na ƙarasa daf da shi na tsugunna ina mai faɗin,

   "Baba na dawo”

Ya yi ɗan guntun murmushi tare da gyara zamansa daga kishingiɗen da ya yi.

    "Sannunki ɗiyar arziƙi"

  Na ɗan murmusa ni ma ina mai faɗin,

   "Yauwa babana! Amma duk na mene ne wannan ɗin haka?"

   Rashin fahimtar tambayar tawa da ya yi ya ba shi damar jefo mini ta sa tambayar ta hanyar furta,

        " Me fa?"

  Na ɗan tanƙwashe ƙafata ɗaya, ɗayar kuma na miƙar da ita. Na zubawa babana na mujiya wato idanuwana kana na ce,

    "Yarda da ita mana baba. Amincewa da sauyin Inna tamkar kwanciya a ƙasan gadar jirgin ƙasa ne. Baba tabbas akwai kasada a cikin haka."

   Baba ya yi dariya mai 'yar yawa kafin daga bi sa ni ya ce,

   "Ai don ka yarda da wani ba shi ke nuna cewar zai cutar da kai ba."

   "Amma baba yardar wani cutarwar wani ce fa. San da kai za ka bawa mutum yarda ka amince masa ɗari bisa ɗari shi a lokacin zai yi ƙoƙarin ganin ya kai ka ƙasa, a wannan dai lokacin ne zai yi ƙoƙarin ɗakkoka daga inuwa ya kai ka rana."

   Na ɗan nisa kafin na sake furta,

   "Uhm! Baba kada dai mu sake mata da yawa, domin har abada ita ɗin macuciya ce domin ita wata uwa ce da bata san..."

    Baba ya yi saurin katse mini zancena ta hanyar furta,

    "A kul! Kar na sa ke ji. Ina tarbiyar da na ginaki a kai ne Hafsana? Ki yi ma za ki yi gaggawar tuba ki nemi gafarar Ubangiji, domin kin yi mummunan lafazi kan mahaifiyarki. Ki kiyaye harshenki a kan kowa, ba ga mahaifiyarki kaɗai ba hatta da wanda ya girme miki."

  Na miƙe tsaye, na nufi hanyar fita ina faɗin,

    "Shi ke nan baba! Bari na je na duba tukunyar ko ta tafasa?"

      "Dawo ki zauna" Baba ya dakatar da ni ta hanyar furta haka.

   Ban musa masa ba, na koma na zauna kamar yadda ya buƙata. 

  "Kin yi fushi ne don na yi miki faɗa Hafsana?”

Na girgiza kaina, alamar a'a.

   "Ko kaɗan babana, ba zan taɓa fushi da kai ba." Na ce.

   "Ai na ri ga na fahimci haka, ta sauyawar fuskarki. Idan har kika yi fushi to ki sani, ni ne mutum na farko da zan fara shaidar haka. Idan har kina cikin ƙunci da damuwa to ni ne mutum na farko shi ma da zan soma sani. Na san mece ce dariyarki, fara'arki, walwalarki. Sai kawai yanzu ki ce mini ba fushi kika yi ba. Haka ne ya sa kika tashi fuuu! Tamkar wacca iska ke kwasa za ki fita? Ko iskar ce ta ja ki?" Ya ƙarasa yana 'yar dariyar tsokana. Sai kawai na tsinci kaina da sakin murmushi.

   "Babu komai, ni sam ban yi fushi da babana ba ko da abin ya faɗa mini. Ka sani kai kaɗai nake kallo na ji taskar zuciyata ta yi sanyi, raina ya yi fari ƙal-ƙal. Ta yaya to zuciyata za ta iya fushi da kai? Ai kuwa duk san da ta yi gangancin haka to tabbas sai na tsaga ƙirjina na cirota na yi jifa da ita ko na yi gunduwa-gunduwa da ita."

   "Ba ma za ayi haka ba"

Baba ya ce yana dariya.

   Muka saki dariya lokaci ɗaya, dariyar da ta shiga saka mu nishaɗi. Muna haka muka jiyo muryar Inna na ƙwala mini kira, na miƙe zumbur! Tare da ficewa daga ɗakin.

   Na isa ga gabanta, har lokacin dariya ke shimfiɗe saman fuskata.

     "Ga ni Inna!"

  Da faɗar maganata, da miƙewarta tsaye kusan duk a tare ne. Cikin rashin rabo irin nawa na ji an juye mini tafasasshen ruwan zafi a jikina.

  A zaba, zafi, zugi da raɗaɗi suka haifar mini da daka wani wawan tsalle da na yi ina mai susa jikina tare da sakin ihu, gami da sakin ƙara mai gigita kunnuwan mai sauraro.

  Ƙarar da na saki, ta isa kunnen baba, ya yi azamar fitowa, don son ganin abin da ya sa ni sakin ƙara.

   Tsallen da nake yi wanda ya gaza inganta tsayuwata kan dugadugaina, shi ya bawa baba damar isowa gare ni da saurinsa, ya kamo hannuna yana faɗin,

     "Me ke faruw..."

  Maganar shi ta maƙale jin wani zafi da ya ratsa hannunsa. Haka ya ba shi damar bi na da kallo, fata ta kuwa har ta tashi, inda ya riƙe ni kuwa har fatar ta ɗaye, haka inda na soma susawa shi ma fatar ta ɗaye.

    Baba ya gigice, cikin tsananin tashin hankali ya sake tunkaro ni kafin ya yi wani yunƙurin sake riƙe ni ko tallafo ne na zube ƙasa a sume, ban sake sanin me ya sake faruwa ba sai farkawa na yi na gan ni kwance saman katifa, babu riga a jikina, jikina duk a buɗe sai kawai ƙirjina da gabana da aka saka ƙyalle a ka sakaye mini shi.

   Ruwan kokon da Inna ta ce na ɗora mata shi ne ta juye mini shi a jikina, ashe ruwan ƙona ni ta ce in ɗora mata ba na koko ba. Ai kuwa ta ci galaba a kaina domin kuwa ruwan ba ƙara min ta'adi ya yi mini ba, na yi tsantsar mamaki duk da rashin kulawar da take ba ni, sai dai a wannan takin tabbas idan har ba idanuna gizo suke yi min ba to babu shakka na hango na dama a idanun innata na abin da ta aikata min, sai dai ban kai ga gama tantance haka ba na sume. Kaka ta ce mini malam Barau a ka kirawo, ya zo ya yi mini tofi, da yi mini taimakon da zai iya.

    Ina jiyo hirarsu kaka a tsakar gida suna ta tattauna al'amarin, da rashin imani irin na Innata.

  Wasu ruwan hawaye masu zafi sosai suka shiga silalowa saman kumatuna. Takaici nake yi kawai na zamantowata ɗiya a wajenta, ina ma a ce ba daga tsatsonta na fito ba. Shin wace irin uwace ita?

   Na lumshe idanuwana, hawaye na sake ambaliya daga cikinsu , haka nan wani ɗaci na sake ɗawainiya a cikin yawun bakina.

  Ina cikin wannan halin ne na jiyo sallamar baba cikin gidan. Na runtse idanuwana tamau domin sam bana son ganin baba cikin tashin hankali.

  Ina jiyo shi, shi da kaka da baba Iro. Baba Iro na yi masa jaje, yayin da suke ta zantawa a kan baƙin halin Inna kafin ya shigo inda nake.

  Har baba ya shigo, idanuna a rufe suke. Ya tsugunna saitin kaina tare da shafa sumar gashin kaina yana mai tofa mini addu'a.

   "Ki gafar ce ni Hafsana! Na aikata kuskure, da har ya janyo miki kwanciya a halin yanzu. Tabbas da na san za ta aikata miki haka, to da babu abin da zai sa na takura miki har na tura ki izuwa gareta domin ki taimaka mata." Ya ƙarasa cike da sakin wani marayan kuka, wanda ya haifar mini da karyewar zuciya ban san lokacin da ni ma na saki nawa kukan da ya yi sanadin tsayar da na baba.

  "Hafsana! Kuka kuma? Me ya faru? Jikin ne?" Duka ya jefo mini tambayoyin lokaci guda.

  Kafin na iya furta komai su kaka sun yi wa ɗakin tsinke, su ma cike da tambayar jikin nawa.

   "Ba zan taɓa gafartawa kaina ba, muddin baba ka sake zubar da hawayenka! A kan me za ka dinga neman gafarata alhalin ba ka yi mini komai ba? Ba kai ne ka ke ce mini duk abin da ya samu bawa rubutaccen al'amari ne daga Ubangijinsa ba?"

  Maimakon baba ya ƙarfafa mini guiwa a wannan karon, sai kawai ya sake fashewa da wani irin kuka. Ganin haka ya sa kaka saurin faɗin,

  "Indai kai za ka yi kuka, to wa zai rarrasheta ita kuma?"

   Tamkar ɗaukewar hasken lantarki, haka kukan babana ya tsaya, sai dai numfashinsa sai sassarfa suke yi.

   "Ki yi haƙuri Hafsana!" Ya sake furtawa cikin murya irin ta masu kuka.

  Ina shirin yin magana Baba Iro ya katse ni ta hanyar faɗin,

   "Addu'a kawai za mu ci gaba da yi mata, amma kuka ba namu ba ne ba. Ni zan wuce gida zan turo Dije ta zo ta taya ta hira."

   Baba ya tsagaita da kukan da yake, yayin da baba Iro ya fita.

  Kaka ta ƙaraso daf! Da ni ta duƙa tana faɗin,

    "Shaƙiyiya ya jikin?"

Na ɗan yi dariya kaɗan irin ta yaƙe kana na ce,

   "Ni ai ba raguwa ba ce irin ki, na warke."

   Ta yi dariya irin tasu ta tsofaffi tana mai miƙo mini daƙuwa da yatsu biyar.

  Kamar yadda baba iro ya ce, sai ga Dije ta zo taya ni hira.

  "Sannu Hafsa, yaya jikin?" Cewar Dije.

  Na faɗaɗa fara'ar da ke shimfiɗe saman fuskata kana na ce,

 "Alhamdulillah! Ai na ji sauƙi, don haka ke zan yi wa sannu."

  Ta zaro ido waje kamar za su faɗo tare da faɗin,

   "Ni kuma? To sannun me za ayi min?"

   "Sannu da zuwa mana, za ki dafa min abinci" Na ce da ita.

  Ta yi 'yar dariya kana ta ce,

  "Wato ke rashin lafiyar ma ba za ta sa ki rissina ba ko? Ba za ki sauya hali ba?"

   "To me za a fasa, mutuwar ko Hisabin?" Na ce da ita.

   "A'a babu ko ɗaya" Ta ba ni amsa tana ɗaga hannayenta biyu a tare.

  Kaka ta katsemu ta hanyar furta,

  "Kin ga Dije je ki yi abin da za ki yi, don idan ta wannan ce to ba za ki yi komai ba, muddin kika ce biye mata za ki yi."

  "Shi ya sa ai kema kaka na ga kullum bakinki ba ya rasa abin faɗa, tun da ance zama da maɗaukin kanwa shi ke kawo farin kai." Ta ƙarasa tana mai tuntsirewa da dariya.

  Kaka ta watsa mata yatsu biyar alamar daƙuwa kana ta ce,

   "Kin ci gidanku, wato taron dangi za ku yi mini ko? Ni ina kare ki shi ne za ki yi mini shaƙiyanci"

   Dije ta miƙe tsaye tana 'yar dariya kana ta ce,

   "A'a ni ba da ni ba ni dai, kin ga ma na yi nan."

   Ta fice daga ɗakin tana 'yar dariya. 

   Haka muka wanzu muna samarwa junanmu farin ciki, har baba ya shigo ya iske mu muna dariya da tsokanar juna.

   Na kuma lura baba ya samu farin ciki sosai, sai dai har ya yi wata rama dalilin ciwon nawa, tausayinsa da ƙaunarsa duk suka sake mamaye zuciyata.


Ƙofar sharhi ko gyara a buɗe take.


Mai ƙosai✍️


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.