Free chapter · Read without an account

45

by Azizat Hamza · Mutum Mugu Ne

*MUTUM.....Mugu ne*


                     45


Ya na cikin tafiya wayarsa ta yi ringing, ya ɗauka ganin Alhaji ne.

"Me ke faruwa Sajid? Mi na ke ji yau ɗin nan?"

In brief ya sanar da shi abinda ya faru. Shi ma Alhaji ya yi mamakin abinda Zaytunah ta yi. Ya kwantar masa da hankali tare da cewa ya dinga sanar da shi update ɗin abinda ya faru, In Allah ya yarda za a ga Naziha.

Police station ya je ya ba da report daga nan ya wuce gidan Television dan bada sanarwa. Yana tafiya kiran Mr David ya shigo, rasa ma mi zai yi ya yi. Har kiran ya katse bai ɗauka ba, kiran ya sake shigowa a karo na biyu wannan karan sai ya ɗauka. Bayan sun gaisa da Mr David wanda Sajid duk cikin fargaba ya yi shi. Mr David ya tambaya ko yana tare da Funmilayo ya yi ta kiran numbar ta baya shiga.

Sajid ya yi gyaran murya sannan ya masa ƙaryar ba sa tare kila ta sa wayan a chaji ne. " is something wrong Mr David?" Ya tambaye shi zuciyarsa na ɗar-ɗar.

"No sir, it's actually a good news. Yayanta AbdulBasid ne ya zo, He came to beg for her forgiveness"

"Masha Allah" Sajid ya faɗa yana ajiyar zuciya

" Sir, jibi za a yi family meeting a Ilorin and ya kamata Funmi ta zo gida "

'An zo wajen' Sajid ya faɗa a zuciyarsa a fili kuma ya ce " ko za a bari zuwa next week, saboda tana zuwa computer training"

" ba daga ni bane, Alaji AbdulWasi'u ne ya saka, kuma AbdulBar zai shigo Nigeria gobe"

"Ok Sir, zan kawota Insha Allah"

Yana kashe wayar ya nemi waje ya yi parking motarsa, ya kwantar da kansa kan stiyari yana hawaye "Ya Allah ka bayyar min da Ziha kafin na zama mutumin banza a idon duniya"

Wayarsa ta sake ringing da sauri ya ɗauka saboda tunaninsa za a kira shi ace anga Ziha. Ganin sunan Nadia ne sai ya yi ajiyar zuciya kafin ya ɗauki kiran

"Ya Saj, yanzu Ummi ta gaya min abin da ya faru. Gaskiya Allah wadai da halin Zaytunah, rashin imanin na ta ya yi yawa. Kaman ba ta san zafin haihuwa ba"

"Auta ki taya ni addu'a, har yanzu babu labarin Ziha, 'yanuwanta na son ganin ta jibi ban san ya zan yi ba...." Muryar shi ya sarƙe

"Ya Saj dan Allah ka dena kuka, Insha Allah za a same ta alive and healthy"

"Allah ya sa Auta" ya ce da ita.

Ba zai iya tuna yaushe rabonsa da yayi kuka har da hawaye ba. Yau gashi da girmansa Zaytunah ta saka shi kukan dole.

Yana cikin tuƙi wata baƙuwar number ta kira shi da sauri ya ɗauka saboda tunanin ko Ziha ce

Sallama yai bayan ya ɗau kiran, daga ɗaya ɓangaren aka amsa tareda tambayar "ina magana da Dr Sajid ne?"

"Yes"

"Suna na Muhammad, ina da information akan yarinyar da ka ke riƙo"

Da sauri Sajid ya ce "Naziha?"

"Yes, bincike ya nuna min ka dawo Nigeria so ya kamata mu haɗu yanzu a gidanka"

"Of course, gani nan zuwa...dole mu haɗu. Dan Allah Kana tareda Ziha ne?, is she alright?"

Muhammad ya yi murmushi ya ce " kar ka damu Dr, za mu yi maganar idan na zo" daga haka ya katse kiran.

Sajid cikin sauri ya juyar da akalan motarsa zuwa gida saɓanin gidan talabijin da zai je. Yana ƙoƙarin ƙiran numbar Muhammad dan ya tambaye shi ko ya san gidansa amma ba ta shiga....

***

Ta kwantar da bayanta jikin seat ɗin mota tana tunanin ba dan Yaya Muhammad ba da yanzu rayuwar ta ya lalace "in dai saboda zaman gidan Uncle Sajid ne zai sa rayuwarta ta lalace, na haƙura. I will leave your house Anty Zaytunah" ta ɗan rintse idanunta abin da ya faru jiya na dawo mata.

*wani daga cikin mutanen ya fara ƙoƙarin cire ma ta kaya sai rotse-rotse ta ke yi da ƙafa amma sai da ya zare skirt ɗin jikin ta ya sa hannu yana ƙoƙarin zare ma ta pant kamar daga sama ta ji an ce " if you do it i will shoot your head" mutumin ya juyo ya kalli Muhammad da ke tsaye a kansa da bindiga sauran 'yanuwansa ma an saka musu bindiga a ƙeya sun ɗaga hannu sama alamar surrender. Shi ma ɗin ya tashi a hankali ya ɗaga hannu sama, Muhammad ya garƙama masa handcuff a hannu, ɗaya daga cikin police ɗin ya ingiza ƙeyarsu waje. Muhammad ya kwance mata baki da hannu. Ta fashe da kuka jikin ta na rawa. Ya ɗauko skirt ɗin ta da ke gefe ya miƙa ma ta. Jikin ta na rawa ta ƙarɓa ta saka. Yadda ta ke takawa a tsorace sai ya riƙe hannun ta ya ce "dont worry ba abinda zai same ki"*

Ba dan abubuwan ta da za ta ɗauka ba, da ba abinda zai sa ta koma gidan Uncle Saj. Saboda Uncle Sajid shi yasa ba za ta yi ƙaran Anty Zaytunah ba.

Suna tafiya Nazira ta kira shi.

" 'yar gidan Abba ya aka yi?"

" Yaya ni kan ka dena kirana yanzu"

Ya yi murmushi ya ce "toh Naziratu 'yar bincike"

Nazira ta fara masa kukan sakalci shi kuwa ya fara dariya.

"Allah Yaya it's not funny"

"Shi kenan baby, ya makarantar?"

"Yaya ba abinda na gane yau ɗin nan, Allah ba dan Abba ba ba zan koma school ba"

"Oh aure kike so kenan?"

"Yaya Shabbir Allah ka dena tsokala ta" ta faɗa cikin shagwaɓa

" Bari zan kira ki da dare, sai mu yi maganar nan da kyau"

Yana ajiye wayar ya i murmushi. Shi kansa yana mamakin yadda ya saba da Nazira cikin kanƙanin lokaci, kullum sai sun yi waya da ita idan ma bai kira ta ba za ta kira shi, bayan Raudha ita ce mace ta farko da zai ɗau waya ya kira dan su yi taɗi, shi dai ya san tausayinta ya ke ji kuma he's trying to encourage her kar ta zama depressed....

Bayan Nazira ta ajiye wayan sai ta kwanta kan gado tana tunanin halin da ta tsinci kanta yanzu. "na san ka min nisa Yaya Shabbir, ba abinda zai sa ka so mace irina mai gurɓataccen rayuwa haka. Allah ya isa Inna Laure kin cuce ni" ta jawo filo ta rungume tana tunanin ranar da ya rungume ta a asibiti.

***

.......Asibiti....

"Yanzu Zaytunah ba kya tsoron haɗuwarki da Allah, kafin a je nan ma ba kya tsoron abinda ki ka yiwa 'yar mutane ke ma ayi wa ta ki 'yar" mommyn Zaytunah ta faɗa ranta a ɓace Yamin ne ya sanar ma ta sun kawo ta asibiti shi yasa ta wuco asibiti direct.

"Mommy please ki gaya min mafarki nake, ba da gaske ba ne ko? my one bai da ke ni ba ko?, I'm just hallucinating, my one yana ƙasar waje, bai dawo ba ko?"

Mommy rai a ɓace ta daka ma ta tsawa "kina da hankali kuwa, you better snap out of this nonsense and pray a ga Naziha, idan ba haka ba Sajid ba duka kaɗai zai tsaya ba sai ya sa an ɗaure ki, shasha kawai"

Zaytunah ta ƙwalla ihu tana kuka. Mommy ji ta yi kaman ta make ta tsabar haushi.

Yamin da Yassar gida suka koma lokacin da Mommy ta iso asibitin. Dama tun da Zaytunah ta farfaɗo ta ke musu kuka su kuma ba za su iya da sakalcin ta ba. Yamin ya kira Mommy ya faɗa mata.

Suna isa ba su jima ba Sajid ya iso, ya jima cikin motan kafin ya fito yana takawa a hankali ya shigo gidan addu'arsa Allah ya sa Muhammad da ya kira shi da gaske ne yana da labarin inda Ziha ta ke.

A falo ya tadda su sun yi jugum. Su na ganin sa su ɗka miƙe. Yassar ya ce " Uncle akwai labari kuwa?"

Sajid ya zauna kan kujera yana sauke ajiyar zuciya akai-akai. Suma ɗin ganin bai ce komai ba sai suka ja suka yi shiru.

Min ti sha biyu da isowar Sajid gidan suka ji shigowar mota, da sauri ya miƙe tsaye yana shirin fita suma suka bi bayan shi da sauri.

Ganin ta ƙi fitowa ya zago ya buɗe mata ƙofa ya ce "Naziha ba abinda zai faru ki fito ina tare da ke"

A hankali ta fito daga cikin motar tana kallon gidan Uncle Sajid, ta hango shi yana takowa wajensu da sauri, ta rintse idanunta saboda yanzu bata son ganin 'yan gidan. Ba ta ankara ba ta ji an rungume ta. " I'm sorry Naziha, I failed to protect you, ki yafe min, Ziha" ya fi minti uku yana rungume da ita yana sunbatu, har lokacin bata buɗe ido ba sai hawaye da ke kwararowa a idanunta.

Muhammad ya ɗan taɓa kafaɗarsa sai a lokacin ya dawo hayyacinsa ya kalli Muhammad ɗin ya ce "Thank you, Allah ya saka maka da alkhairi "

Muhammad ya ce "Dr akwai maganar da za mu yi a gurguje saboda ina da aiki a gabana"

Sajid ya janye Ziha a jikinsa ya ce "Yassar, take her inside"

Bayan sun shiga ciki Sajid ya kalli Muhammad ya ce " mu shiga ciki ko"

"No kar ka damu nan ma ya yi ai magana kawai za mu yi"

A gurguje ya sanar da shi yadda aka yi ya kuɓutar da Naziha, ya ƙara da cewa "ka gode wa Allah Naziha na da haƙuri ba dan haka ba da matarka na kulle yanzu. But Naziha ta hana ni shigar da ƙara. Sannan thugs ɗin nan sunan matarka suka sani ba su san fiskar ta ba so bayan Naziha ta testifying ba laifin matar ka ba ce sunan matarka is cleared. But still ka jawa matar ka kunne kar ta kuskura ta sake irin haka saboda ba lallai ta tsira ba"

Sajid ya sake yi masa godiya.

"Naziha ta yi niyyar komawa Lagos yau amma bai dace ace ta koma ita ɗaya ba saboda har yanzu akwai tsoro a tattare da ita, I will advise ka maida ita gidansu da kanka for her safety, kar matarka ta mata illa" ya miƙa masa card ɗinsa ya ce

" ni zan wuce, idan akwai matsala sai ka kirani"

Jujjuya card ɗin ya yi a hannunsa ya ga an rubuta Agent M. S. Yunusa a katin.

Musabaha suka yi sannan Muhammad Shabbir ya shige mota ya tafi.

A ɗakinta ya same su duka, Ziha na haɗa kayanta a jaka su Yassar na bata haƙuri akan kar ta tafi.

"Leave us" ya ce da su, suka bar ɗakin da sauri.

Ya kira sunanta a hankali "Naziha"

Ba ta amsa ba ta cigaba da saka kayan a jaka, bai yi mamaki ba da ya ga kayan ma tsinta ta ke yi, iya wanda ta taho da su daga Lagos ta ke sawa a jaka.

"Naziha" ya sake kiranta wannan karan da ƙarfi ya kira, ta ɗan ɗago ta kalle shi sannan ta sauke ido. A hankali ya ƙaraso wajen ta tana riƙe da wani gown ya ƙarɓi gown ɗin ya cilla gefe. Ya sa hannu ya riƙe hannunta duka biyu ya ce " na san kina fushi da mu, but you can't leave like this"

Ta jima tana tunanin maganganun da za ta gayawa Uncle Sajid saboda matuƙar bata nuna ma sa ɓacin ranta ba, zai shawo kanta ne ta haƙura da komai ta zauna.

Ta bangaje hannunsa ta ce " Uncle you don't understand, matarka ta tsaneni, sawa fa ta yi a raping ɗina and you want me to stay. Uncle har abada na gama zaman gidanka"

"Naziha!" Ya daka mata tsawa. Ta yi shiru tana goge hawaye

"Please Ziha, I will fix this, zan gyara komai, amma dan Allah kar ki yi gaggawar tafiya haka" ya faɗa muryarsa a sanyaye

"Matarka ta kira ni karuwa, gold digger, mayya, 'yar matsiyata and many horrible names amma na cigaba da zama a gidanta, but yesterday ta yi abin da ko ɗaure ni aka yi a gidanka sai na tafi. Na gode da alkhairi daka min a rayuwata, amma yau zan bar gidan nan babu dalilin da zai sa na sake zama"

" na ce miki zan gyara komai koh, I will marry you so that za ki zama dai-dai da Zaytunah a gidana, so that Zaytunah za ta dena hantarar ki, so that I can protect you"

Idan har kunnenta ya ji dai dai Uncle Sajid na son aurenta ne saboda yana tausayinta. Ba za ta iya auransa akan haka, Ba zata taɓa yin auren alfarma ba, Ba zata ma iya kishi da Zaytunah ba. Ta daure ta ce " Uncle wannan ba ɗaya daga cikin dalilan auren mace bane"

Ya dafa kafaɗan ta duka biyu ya ce "marry me, Naziha"

Kirjinta ya fara bugawa da ƙarfi murya na rawa ta ce "Uncle ba zai yiwu ba"

Ya matso daf da ita ya ce " na mi ki tsufa koh?" Da ƙyar ta haɗiye yawu ta ce " ba haka bane"

" Yassar ki ke so?"

Ta girgiza kai

"Toh minene?"

Muryanta na rawa tace " I want to marry someone that loves me"

Ya matso daf da ita ya rage tsayi, fiskarsa na dai-dai da nata. Level of closeness ɗinsu ya yi yawa, kasa jure irin kallon da ya ke mata ta yi, ta rufe ido ƙirjinta ya cigaba da bugawa da sauri-sauri.

A hankali ya manna mata light kiss a lips ɗinta wanda yasa ta yi mutuwar tsaye, ba dan ya dafa kafaɗarta ba ƙila da faɗuwa za ta yi a wajen.

*"I love you Naziha, I really love you"* kalmomin da ta ji su kaman a mafarki bayan shock ɗin da ta tsinci kanta. Ƙwaƙwƙwaran motsi ta kasa yi saboda komai nata ya tsaya.

Yassar da Yamin da suke bakin ƙofa suka rungume juna saboda murna, dama tun fitansu suke laɓe jikin ƙofa daga baya kuma suka buɗe ƙofar kaɗan su na leƙa su.

Shi kansa bai san ya aka yi ya iya furta wannan kalmar ba amma ya san idan akwai mace da ta cancanci kalmar to Naziha ce.

"zan kai ki Ilorin gobe, saboda kuna da family meeting, ki yi tunanin akan abinda na faɗa miki" ya mata peck a goshi ya fice daga ɗakin.

Ta fi minti biyar tsaye a wajen ta kasa motsawa daga baya ta zauna gefen gado ta kai hannu ta shafa lips ɗinta zuciyarta na maimaita mata kalaman Uncle Saj *"I love you Naziha , I really love you"*......

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.