Free chapter 路 Read without an account
p-9
_*馃崌SILAR AURENA馃崌*_
TAKU NA 1
Book 1馃摉
*NA*
Rabiatu Bashir Abdullahi
*_UMMU MAHER(MRS GREEN)_*馃崈
_*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*_
*KOYON MAYAFI DA HULUNA DA RIBOM*
Kiyi shiga wannan grp 蓷in domin dogaro da kai.馃憞馃憞馃憞馃憞馃憞馃憞馃憞馃憞
***
D6g00p1DxttAtHH1vmh54i
*ku sauke apps na palmpay domin 茩aruwa, kuyi joining 蓷in link 蓷innan domin ku 茩aru馃憞馃憞馃憞馃憞* >>***
SHAFI NA 9
________________ ko da suka shigo garin Zaria wani irin sanyi da da蓷i yaji, yayi shiru yana jin sanyi da da蓷in garinsu wanda ya shafe shekaru har kusan biyu da rabi ba tare daya je ba.
Mubarak ya juyo ya kalli ogansa ya ce" yalla蓳ai mun fa shigo gari? kana ganin bazamu kira Hajiya mu fa蓷a mata ba saboda ta shirya zuwanka?".
Ya yi shiru ya 蓷an kalli Mubarak sannan ya ce" ba sai na sanar da ita ba Mubarak, idan na fa蓷a mata zata iya barin gidan ma baki 蓷aya saboda gudunta da nayi, amman kaga idan naje xai zo mata abazata".
Mk ya 蓷aga kansa da gamsuwa sannan ya hau tu茩i cike da murna saboda yau ogansa zai ha蓷u da iyayensa, yana 蓷aya daga cikin mutanen da suke cike da haushin abinda yake faruwa tsakanin AD da kuma mahaifansa.
suna zuwa dai dai 茩wanar gidansu AD yaji wasu hawayen farin ciki sun cika masa zuciya, ya ce" Mubarak ina cike da farin ciki yau 蓷innan, saboda ganin iyaye na da zanyi Familin me 茩amshi". Mk yayi 蓷an murmushi cike da murna ya ce" 茩warai kuwa uban 蓷akina, nima ina tayaka murna sai dai ni murna biyu nake, na farko ni dai ban yada su Hajiya kamar yadda kayi dasu ba, duk bayan wata ina zuwa don 蓷iban tabarakin Hajiya da Baba Me 茩amshi".
AD ya 蓷an fito fa idanuwansa sannan ya ce" are sure? kana zuwa? shi ne ni baka janyoni munzo ba"?.
Mk ya 蓷anyi murmushi sannan ya ce" to ai oga awannan lokacin kamar baka cikin hayyacinka, shiyasa na barka ka 蓷an huta sannan sai in fa蓷a maka, amman ka gafarce ni idan na fa蓷i abinda ya 茩ona ranka".
kasa ce wa uffan yayi, duk sai yaji babu da蓷i abinda ya aikatawa iyayen na sa wa蓷anda suke matu茩ar so da 茩aunarsa, basa son ko da 茩uda ya ta蓳a sa shi ne namiji 蓷aya tilo agidansu wanda har yau ba'a samu wata ta haifi namiji ba sai shi ka蓷ai Shattima sunan da mahaifinsa ya ra蓷a masa kenan, tun daga ranar da yayi kukan farko acikin gidan duniya, saboda sunan Babansa yaci wato Me 茩amshi wanda ake ce masa Shattima, da yake su 拼an asalin 拼an meduguri ne Borno.
tun daga kan 茩wanar gidansu ya fara hango jama'ah, sosai gabansa yayi wani mummunan bugawa, yaji kansa na sara masa sai dai ya daure ne saboda shi namiji ne, kuma dukkanin namiji an sanshi da jarumta da mi茩a kai balle shida yake soja mazan fama ga wuta ga harbi.
Har suka iso 茩ofar gidan jama'a ne tam茩am, tuni yaji ya yar da jarumtar tun kafin ma Mubarak ya bu蓷e masa ya kama murfin zai bu蓷e.
da sauri Mubarak ya yi fakin ya fito da fitinannen sauri ya bu蓷e yana 茩amewa tamkar asalin soja, ko da yake shi sabo ai turken wawa ne tunda dai masu yiwa uban gidan nasa hidima duk sojoji ne.
sosai aka bi motar da kallo tun kafin ma ya fito, kamar sun san shi ne acikin motar yana fitowa kuwa kowa ya tsura masa ido, wasu har murza idanunsu suke saboda suna son su 茩ara tabbatarwa ce war shi 蓷inne ko kuwa ba shi bane?.
ya 茩arasa gabansa yana fa蓷uwa, mutane aka tattaso ana gaishesa da yake unguwar tasu ta jama'ace sosai, nan da nan aka baibayesa yana 蓷aukar gaisuwa wasu kuwa ce wa suke shikkenan yau miyar gidansu zatayi za茩i, don mutum ne shi me matu茩ar bautatawa al'umma ko dama can idan yazo ku蓷i yake basu bana wasa ba, don duk mutum 蓷aya zai iya samun dubu hamsin na kansa, samari kuma dubu ashirin matan dake gidajen aurensu na layin suma dubu hamsin.
bai samu damar amsa musu wannan gaisuwar tasu ba, ji yake tamkar 茩afafuwansa ba zasu iya 蓷aukarsa ba, kar dai ace wanine ya mutu agidan? ras gabansa ya fa蓷i tuno da yayarsa wacce ya bari ahalin jinya, dukkanin jikinta kuwa babu inda yake motsawa don tunda aka yi mata kishiyasa sai ya zamana kullum tana gidansu babu lafiya, zato zunubine ko da ya kasance gaskiya, amman yana jin mutane suna fa蓷ar albarkatun bakinsu kan cewa wannan kishiyartata itace tayi mata asiri, duk dashi bai yarda alokacin nan ba sai da ciwon yayi nisa don ko dubata bata zo ba, shima mijin baya zuwa gashi suna da yara har ba茩wai da mijin na ta.
Tunowa da Anti Badi'a sai yaji zuciyarsa ta tsinke, da dama ma kuka yake bu茩atar yi sai dai kafin kaga yayi kuka to ba abune na wasa ba domin shi yanada zuciya me taurij gaske.
makara yaga an fito da ita daga cikin gidansu me masifar girma, don gidansu irin gidan yawan nanne kusan part ashirin ne agidan nasu kuma pary hu蓷u na mahaifinsa ne, sauran na 茩annensa da kuma yayyinsa sai 蓳angaren tsohuwa me ran 茩arfe wato Jadda, wato kakarsu tsohuwa me tarin ni'ima da 茩warjini yaranta 15 ne aduniya kuma dukkaninsu suna nan da ransu, kuma bazaka ta蓳a cewa ita ce ta haifesu ba saboda yadda Allah yayi mata jiki me kyau jikin Fulanin usul.
Ganin wannan makara bai san lokacin da ya kusa subewa awajen ba, har sai da Mubarak yayi sauri ri茩e hannunsa don kada ya kai 茩asa, Mubarak ma tsoro da firgici ya kusa sanyasa daskarewa awajen, yaji wani tsoro ya 蓷arsu aransa Allah dai yasa ba wanine ya rasu ba? sai kumq gashi yaga Makara wato ta tabbata rasuwa akayi kenan? indai kuwa haka ne wani babba ne ya rasu agidan, biyo bayan tarin al'ummar daya gani wa蓷anda idan 茩irgasu za'ayi sun kai dubu koma fin hakan.
~~~~~~~
Har nayi 茩wana uku Baba hari bata le茩o inda nake ba, amman don takaici Sulaiman ya sanyawa 拼ata sunanta? duk da nasan sunan mahaifiyarsa ne kuma kowani 蓷a daya taso da soyayyar iyayensa musamman ma mahaifiya yana da burin sanya sunanta, to sai akayi katari ita wannan mahaifiyar bata damu da damuwar 蓷anta ba, balle ma har ta damu da damuwar wani? Baba hari irin mutanen nanne da babu abinda suke so suka kuma damu dashi irin ku蓷i, tana da masifar son ku蓷i wanda ko a茩watance ban ta蓳a ji ko labarin me irin 茩watan 茩wacin irin nata kalar son ku蓷in ba.
ni har mamaki ma take bani, ba kunya ba tsoron Allah ta bu蓷e bakinta tace wai ita bata san Sulaiman saboda ba shida 茩ashin arzi茩i ya auro me farar 茩afa. abin ya girgizani sosai to ta cewa 蓷anta wannan balle kuma kai.
Ina cikin wannan tunanin naji muryar Sulaiman, tamkar dai yana ka蓷amin muguwar algaita ya ce" kiyi ha茩uri Maryam, nasan ban shawarce ki wajen sanyawa yaran nan suna ba, kiyi ha茩uri idan na 蓳ata miki nan gaba zan baki dama ki sanyawa yaranki duk irin sunan da kike so".
na kasa ce masa komi, sai dai haryanzu ina jin zafin sunan daya la茩abawa 拼ata, ko da yake da 蓷a da mahaifi sai Allah na manta komi na ce" ba komai mijina, abinda kayi 蓷in ai shi ne dai dai duk namiji wanda ya isa da gidansa ai ba sai ya nemi shawar matarsa ba, don zaiyi wani abu wannan ai shi ne mazantakar ko"?.
murmushi yayi, azuciyarsa kuwa cewa yake Allah sarki maryam, ita kullum bana laifi sai dai ita tayi lallai Allah ya bani mace tagari.
Halima ta ce" gaskiya nima yaya banso ka sanya sunan Baba ba, ka duba fa ka gani yau 茩wana uku fa bata zo ba sannan kuma sai asanya sunanta? jiya fa har Saddi茩a na zugata wai ko ta dawo kada tayi mata barka".
na lura Halima irin mutananne masu fa蓷ar gaskiya, kuma marasa rufi idan da nice ko mahaifiyata tayi ba dai dai ba bazan iya koda 蓷aga kaina wajen kallonta ba, saboda bansan abinda zataji ba idan na fa蓷a mata gaskiyar.
Sau tari muna samun matsalane da mahaifanmu idan har muka zamo masu fa蓷a musu gaskiya, sai kiga koda su suka haifeka sun sanya maka karan tsana, ta yadda koda magana suke sai suce ga munafukar nan, kalmar da Innata take yawaita fa蓷a kenan idan ta ganni ni kuma ban zamo me wannan halin ba, amman ban san me yasa tunda na kawo Sulaiman amatsayin miji ta tsaneni ba, tamkar dai ba yarda ta haifa acikin cikinta ba wai don duk na kawo talaka amatsayin mijina, abinsa taso shi ne in kawo mata me ku蓷i kamar yadda yayyina suke kawowa.
Sulaiman ya kasa magana, sai dai na lura maganar tayi masa zafi amman bai ce komi ba na lura Sulaiman irin mutanan nanne masu masifar 茩ulafucin uwa, ko unguwa Baba taje sai kiga Sulaiman cikin damuwa sosai, ko fara'a baya yi indai ba Baba ce ta dawo ba.
muna haka Ummu jafar ta shigo, ma茩ociyarmu ita da mijinta Abu jafar wanda ya biya mini ku蓷in asibiti har dubu hamsin, sosai nake ganin girman mutanen, don suna sona sosai mijin ya 蓷aukeni 茩anwarsa, matar ma hakance daga 蓳angarenta domin ni nakewa Jafar lesson na karatun turanci, don Allah ya horemin karatu na arabi dana boko ina da ilimin boko sosai duk da iya makarantar secondary na tsaya amman ilimina har malamai nakewa gyara idan suka fa蓷i wani abun, jin turanci kuwa tamkar ni na 蓷inkewa bature cibiya, saboda tunda na taso ina son turanci sosai shiyasa na dinga siyan littafin koyon turanci har nazo nima na iya sosai na zama 茩wararriya.
Jafar yayo kaina da sauri, Mamansa tayi saurin ri茩esa tana dariya ta ce" to Jafar baka ga babies ahannunta ba? da girmanka ka fa蓷a kansu".?
Jafar 蓷an shekara tara ya kyalkyale da dariya yana 茩arasowa kusa dani ya dinga ta蓳a yaran yana dariya, ya ce" yauwa Ammi zaki kai mana yaran gida ko? kada ki bawa Anti mimi ki tafi dasu gidanmu tunda nima kin茩i kiyimin 茩annai, kisha wake kema ki haifosu tunda kince sai ansha wake ne ake haihuwa"?.
sosai aka sanya dariya, Halima ta ce" ai kuwa bazamu baku ba wallahi, ka matsawa Ammin ka tasha wake itama".
dariya akayi ta masa Sulaiman da Abu jafar suka fita suna hira, ni kuma muka cigaba da hirarmu da Ummu jafar.
Halima tayi mana sallama ta tafi gida.
Ummh jafar ta matso kusa dani ta ce" uhm ni kuwa wani abin al'ajabi na gani 蓷azu?".
gabana ne ya fa蓷i na ce" me kuma kika gani"?...............
*MRS GREEN CE馃*
Atayani sharing 拼an uwa.
*AMMEY LAYLERH DETA SERVICES*
*Azo asai DATA kan farashi mai sauqi, cikin rahusa馃憣馃徎馃*
*MTN*
500MB-180
1GB -280
2GB - 550
3GB - 750
5GB - 1250
10GB -2500
*AIRTEL*
300MB - 170
500MB - 200
1GB - 300
2GB - 550
5GB - 1350
10GB - 2600
*GLO*
200MB - 120
500MB - 180
1GB - 300
2GB - 550
3GB - 850
5GB - 1350
10GB - 2600
*9MOBILE*
500 - 180
1GB -280
2GB - 550
5GB - 1300
10GB - 2500
Account number: 3206656358
Account name: Maryam Nasiru first Bank
*MORE Information ****